Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jona mata drip saboda jikinta da yayi laushi kafin ya tafi lab running test din.

Bayan fitarsa Abdurrahman daya zuba mata ido tun dazu, dakyar ya bude baki yayi magana "Kina kuwa Shan Antibiotic din danake baki?" kai ta gyada masa kawai bawai dan tana sha din ba. Dukda bata san kwayar ta macece ba saboda seya ballo yake kawo mata da ruwa duk sanda zasu kwanta acewarsa wai zatana kara mata kuzari ne kuma shima agabanta yake shan nasa, a farko farko tana sha, period dinta na farko a gidan tayi wani ciwon mara da rabonta da irinsa tun kafin auranta na farko ta kuma zubar da jini sosai data gayawa Mumcy tace mata kodai tana shan wani supplement ne ta dena sai ta tsorata batare da ta gayawa masa ba ta dena sha in ya bata ma sedai ta makale a harshenta ta faki idonsa ta jefar a gefe da safe tayi flushing dinta a toilet.

Suna zaune jugum jugum kowa da abinda yake sakawa a ransa har Dr Huzaifa ya dawo. Cikin Fara'a ya miqawa Abdurrahman farar takardar hannunsa yace "Congratulation Man She is 3 month 8days pregnant".
Ai kamar wanda aka saka guduma aka rade haka yaji saukar maganar, how is that even possible? Cikin rudi da subutar baki ya juya ya kalli Hamdah data dora hannunta akan cikinta tana shafawa ta kasa koda magana tsabar mamakin wai ita ke dauke da ciki har wata uku bata sani ba.Allahu Akbar ashe rabone me zafi a cikin aurannan. Itama zata zama uwa, zata haihu kamar kowa, dama haka ake jin irin wannan farin cikin? lokaci daya hawaye ya shiga sakko mata Wanda ya kasance na tsantsar farin ciki da murna. Kallonta takai kan Abdurrahman daya bude baki tundazu sedai maganar ta kasa fitowa tsabar yanda ya rude, seta kama nasa hannun ta dora akan dan tudun cikinta da ada take zaton tumbi ta farayi se tace "Ogajee baby...wai babyn ka a ciki na, we are going to be parents soon".

Yanayin yanda tayi maganar dole ta baka tausayi domin kana gani kasan zuciyarta cike take da kuncin rashin samun rabon. Daurewa yayi ya hadiye abinda ya hanasa magana tundazu ya dauke hannunsa daga kan cikin kafin yace
"Wai dama kina haihuwa?" Seta bishi da kallon rashin fahimta ta kasa magana tsabar mamaki, dama ance masa Juya ce ita ko yaya? Bata dawo daga wancan tunanin da mamakin ba yasake jefa ta a wani, muryarsa ta jiyo yana cewa

"Look Huzaifa duk ba wannan ba please lets leave it to Some other time, you know I'm too young to be a Father now so as usual flush it out I'm willing to pay what so ever amount, zan yi tripling maka kudin dana saba biya amma a cire cikin nan kawai".
Tsabar mamaki seta kasa motsi, Baki, hanci, ido haka ta budesu idan ta kalleshi seta kalli likitan daya hade hannunsa biyu yana sauraronsa Dan ita sam bata fahimci inda ya dosa ma yau turancinma dena ganewa tayi gara kalmar Acire ciki daya fada daga qarshe ta ganeta amma tana fata bawai akanta yake magana ba.

Kallonsa Huzaifan yayi sannan yace
"Are you sure you are ok Dr kodai ka fara shan magungunan da kake bawa patients dinka ne kaima taka qwaqwalwar ta buga dan dai na zata ka sauka daga kan wannan muguwar akidar taka?"

Kallonrainin hankali yawa Dr Huzaifa kafin yace "Wow see who is talking ai bansan ka tuba da aikata hakan ba kaine zaka ma wani magana akan zubar da ciki, jarirai nawa ka markade a Asibitinnan?"

"What ever i did was between me and my Lord kuma Allah gafururrahim ne na tuba ina istigfari ze yafemin" Huzaifan ya bashi amsa. Tabbas gaskiya Abdurrahman ya fada, shi kansa be san iyakar cikin daya zubarba saboda a lokacin yana qoqarin yin kudi kota halin qaqa kuma a harkar likitanci bangare biyunnan sunfi kawo kudi dan haka suka zabi hanyar Bata suci Haram su sami abin duniya shiya na zubarwa da mata ciki Shi kuma Abdurrahman dayake da asibitin mahaukata me zaman kansa sedai abinda duniya bata sani ba behind asibitin nan Dr Abdurrahman qasurgumin dilan kwayoyine, yanda matasa ke tururuwar zuwa asibitinsa kadai ya kamata yasa ayar tambaya akansa amma dayake yanada daurin gindi babu wanda ya taba koda attempting bincikarsa, haka magani indai da sunansa ya shigo kasar nan babu wanda ya isa ya budeshi.
"Malam Matar ka ko mata ta infact kai kayi cikin ne ko ni dan haka in zakayi abinda nace kayi kawai in kuma bazakayi ba bakai kadai ne likita kwararre a wannan fannin ba ka sani" yayi maganar cikin halin ko in kula kamar ma besan tana zaune a gurinba.

"Ba ko daya a ciki nasan kaima zaka iya Amma ka sani ni na tubarwa Allah tuni na dena bazan kuma kara taimakawa wani wurin aikata sabo ba dan haka bazanyi ba kaman yanda kace akwai likitoci dayawa da aikinsu kenan Abortion you can take her to them". Se a lokacin ta dawo hayyacinta daga hutun rabin gadin data tafi, Ai zumbur ta Mike jin kalmar ABORTION wato dama duk wannan drama akan cikin jikinta sukeyi wae shi za'a cire to meya tsarewa wani daga cikinsu? Hannunta ya kama a fusace suka fice daga office din Huzaifa ya rakashi da
"A sauka lafiya" ya kulle kofarsa. Kamar wawuya haka ta ringa binsa har suka zauna a cikin motar se a sannan ta samu damar yi masa magana

"Abdurrahman wai maganar me naji kunayi ne nifa ban ganeba" kallonta yayi yana wani mayaudarin munafukin murmushi kafin ya riqo hannunta da dayan hannunsa yana murzawa, se ya mayar da hankalinsa sosai kan titi yace
"Cikin jikinki mana Baby a cireshi kawai ko tunda har yanzu ba mu girma ba fara tara yara yanzu ze iya zamar mana cikas cikin jin dadin rayuwarmu ko ba haka ba".
"Tunda ya fara magana take maimaita kalmar Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni kairan minha" shi take maimaitawa cikin zuciyarta har ta fito fili, dama wannan shine illar da GURU ya hango mata a cikin Auran? Wayyo Allahnta ina zata saka kanta da wannan tashin hankalin? Cikin muryarta da kuka yaci karfi ta shiga magana
"Aa Abdurrahman karkace haka wannan Ai butulcine ga Allah yayi mana kyauta muki gode masa baya ga haka inma kai baka shirya ba ni inaso, kuma nice zan raini cikin, kai inma kace baza ka masa komai ba duk nayarda a shuirye nake na haifi Yaya ko guda nawane wallahi ko duk wata akace in haihu na yarda" ta qarasa tana rushe masa da kuka ko zeji tausayinta amaimakon haka sema yayi murmushi yace
"Relax Yammata nasan ke zaki raini cikin and you knkw money is not the problem, kin gane haihuwarce kawai bana So, ni yayan ne banaso at all na aureki ne kawai dan naji dadi na dake you are the perfect wife for me amma daga zuwa zaki wani dauki ciki No ashe dama yaudara na akayi da akace baki haihuwa". Seta qarawa kukanta volume tana cewa
"Kaji tsoron Allah kaima fa haifarka akayi, kuma ni koda mijina ya mutu da ciki ya barni bari nayi daga baya kuma wallahi banga wanda ya isa ya ciremin wannan ba" seya kalleta kawai sheqeqe ya girgiza kansa nan take fuskarsa ta chanza
"To shikenan mu zuba mu gani ina nine me cikin kuma nace bana so ba kuma za'a haifeshiba in kuma kin dage seki nema masa wani uban tunda wuri seki bawa kanki zabi" daidai ya qarasa parking motarsa a cikin gidan se ya fice ya Barta cikin motar tana gunjin kuka.

"Allah na tuba kayafemin wannan jarabawar tayi tsauri, ya ubangiji taya zan butulce maka na kashe rai, abinda nayi shekaru ina kuka akansa yanzu in samu inyi butulci Allah ka kawomin dauki ubagiji ka bani mafita" haka taringa maganganu ita kadai dama jiki ba kwari nan da nan wani zazzabi ya rufeta ga amai dayake taso mata amma ta kasayi saboda cikinta babu komai, dakyar ta rarrafa ta shiga dakinta ta kwanta tana ci gaba da kuka. Bata san me kuma zatayi ba tunda ya fito fili ya nuna mata nufinsa, haihuwarce baya so.

Dakin ya shiga da kofin shayi dan yasan bataci komai ba, tana kwance tana kukan ya tarar da ita "Tashi kisa Tea" ya fada cikin sautin bada umarni. Seta miqe ta zauna bawai dan zata sha din ba dan ita yanzu tsoron duk abinda ya fito daga hannunsa take, Se a yanzy ta gane kwayar maganin dayake bata ashe ta hana daukar ciki ne ashe
"Ki karba kisha in ma kina tunanin zan saka wani abu a ciki ne you are mistaken dan base na bi ta wata hanya ba da hannuna zan kaiki a markade koma menene a mararki ya fita dan bana buqatarsa dan haka karba maza ki bani kofina" yanda yayi maganar dole ta karba kuwa dan dama yunwa takeji, tas ta shanye yana tsaye akanta wani bangare na zuciyarsa yana so yaji tausayinta amma dayan ya rinjayeshi, wanda yayi nisa baya jin kira.

"Wato dama munafunta ta kikeyi ba ki shan maganin dana ke baki ko" ya fada yana kallonta.
"Kayi haquri..."
"Shiii" ya katseta kafin yaci gaba
"Ke zan bawa hakuri dan dole ki rabu da abun nan ni babu haihuwa a gidana, in baki sani ba bayan kyau yana daga cikin abinda ya kara min sonki ance min baki taba haihuwa sannan yanzu kuma ni sekawai kizo kiyi ciki a gidana ko shekara bakiyi ba, to wallahi da sake na baki daganan zuwa gobe ki yankewa kanki shawara ki zabi jin dadin aure ko kuma Haihuwa and in kinzabi na biyun to ki tabbata kin tanadi amsar da zaki bawa mutane ranar da kika haihu dan nidai ba Dana bane" ya juya yafice ya barta cikin tsabar mamaki da tsoro. Batayi tunani rashin kirkin nasa har yakai haka ba, se kawia ta dora hannu aka tashiga kuka
"Allah ka kawo min dauki ka shiga lamarina" haka tayita kukan har bacci barawo ya saceta.

Tun daga wannan ranar zaman lafiya yayi kaura a tsakaninsu, haka bata qara yarda ta ci duk wani abu daya fito daga hannunsa harya kai ga Matar gidan ta fahimci halin da suke ciki. Tasan za'ayi haka, a da tunaninta kyau irin na Hamdah ze rude shi qila ma yaji yana son samun Zuri'a da ita amma se taga abin ba haka bane sai kuma tausayinta ya kamata.
Da safe ta shiga dubata kamar yanda ta mayar dashi dabi'arta yanzu kullum zata shiga safe rana dare ta dubata haka duk abinda ta dafa zata kai mata dukda strong warning din daya kafa mata akan hakan. Wani lokacin har in bata sha'awar abinda aka dafa zata bada kudi a siyo mata abinda take so taci cikin wannan yanayin suka saba har Hamdah ta bata labarin zaman auranta na baya da irin wahalar data sha da dangin miji duk akan rashin haihuwa. Bayan ta gama Cikin kuka mai cike da tarin nadama Hajara ta fara mata magana

"Ina mamakin yanda Abdurrahman ya iya boye wannan mummunan qudirin nasa ga kowa babu wanda ya gane hakan. Kafin ke ya auri mata har biyar duka sun fita kuma dalili daya ne yake korarsu nacewa baza'a haihu ba Amma kinga kowa ni yake dorawa laifi ace na hanasu zama tunda ita me kishiya bata mutuwar Allah da Annabi se ance kishiya ce ta kasheta. Hamdah ni kaina kaddara ce da rashin madafa ta zaunar dani a cikin gidan nan tunda na riga da na cuci kaina inma na rabu dashi nice da asara babu mai aurena a hakan".
Itama kukan takeyi tace " Ke kuwa Hajara wace irin cuta ce kika yiwa kanki haka da babu mai auranki kuma?"

"Munyi auren soyayya nida Abdurrahman, ina tsananin so da kishin sa Wanda ni kaina bansan iya karsa ba, tun kafin muyi aure ya sha gayamin shi bayason yara amma ban taba yarda ba kuma Son da nake masa da karancin tunani suka kaini na biye masa bayan munyi aure saboda alkawarin da yayi min bazeyi min kishiya ba har nayarda yaringa zubar min da ciki saboda nace bazan sha maganin family planning ba ina tsoron ya lalata min mahifa, abinda ban sani ba Abortion yafi planning Illah dan har seda takai mahaifar tayi raunin da cikin da kansa yake barewa daya fara nauyi, munyi hakan yakai sau takwas acikin shekara goma sha biyu da auranmu banda wanda yake zubewa da kansa ba tare ma dana sani ba. Hamdah ban tashi gano illar da nayi wa kaina ba har seda na kwanta wani ciwo saboda abortion din da nayi na qarshe kamar bazanyi rai ba a qarshema ya sa aka ciremin mahaifa dungurungun, duk wannan abin daya daru daga dangina har nasa babu wanda ya sani se La'anannen amininsa Dr Huzaifa dashi yake aiwatar da aikin. Seda ga baya na kasa daurewa na sanarwa da mahaifiyata wanda seda nayi dana sanin fada mata dan yanzu haka tayi fushi dani, ta fita daga dukkan sabgogina acewarta in har zan iya aikata irin wadan nan abubuwan ba tare da Shawara ba to zan iya rayuwa babu uwa da dangi. Yanzu gashi nayi biyu babu, ba haihuwar ban kuma tsira daga kishiya ba tunda seda yayi min biyar gaki ta shida Allah kadai yasan kuma nawa zeyi a gaba".

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un yanzu taqadirancinsa har yakai haka, shine yake lulluba da fuskar salihai yana ha'intar mutane" Hamdah ta fada cikin tashin hankali.
"Ai yafi haka a sannu zaki gano dukka wasu mugayen halayensa da ni ake shafawa kashin kaji komai ace nice yanzu kinga daya daga ciki kiyi fatan su tsaya a haka, nidai shawarar da zan baki komai rintsi komai wuya karki yarda ya raba ki da cikin nan dan idan nice a halin da kike ciki yanzu zan zabi mutuwar aurena akan zaman gidan nan tunda kina da sauran dama gaba wani auranki zeyi, ni kuwa fa, kona fita na auri wani na ha'ince shine" Hajara tayi maganar cikin kuka dayake nuna yanda take jin dacin abun har cikin zuciyarta, dana sani tayi tafi cikin kwando wadda bata da Amfani, gani lokacin dawowarsa ya kusa yasa tayi mata sallama ta koma nata part din tabar Hamdah da shawarwarin matakin daya kamata ta daukarwa kanta dan bata ga gurin zama na a gidan nan, gara ta tafi taje can inda take da masu sonta. Ita ta yarda zata riqe kome ta haifa zata zamar masa uwa da uba amma ya bar mata shi.

















🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 3⃣5⃣

Ana kiran sallar magriba tashiga gidansu shawarar data yankewa kanta kenan bayan dogon tunani, barin gidansa zuwa nasu gidan shine matsaya ta qarshe data fi kwanta mata a rai. Amma in taje me zata cewa Mumcy da sauran mutanen gidan? Ya kamata ta gayamusu mugun qudirin Abdurrahman akan cikin jikinta amma me hakan ze haifar, tasan se sun tsaneshi fiye da yanda tayi qarshema su rabata da cikin kamar yanda burinsa yake da wannan tunanin ta qarasa cikin gidan.

Bata tarar da kowa a main palour ba dan haka direct dakin daya kasance nata a lokacin yammatanci dakuma zamanin zawarcin da a yanzu yake shirin kara zama mallakinta ta bude ta shiga, kamar yanda tayi tunani komai yana nan inda yake fes kai kace akwai mutumin dayake rayuwa a cikin dakin saboda duk satin duniya Se Mumcy ta saka an share shi an gyara dukda babu me kwana a ciki Aa sedai dan kawai haka al'adarta take. Hatta dakin Zahra har yanzu yana nan in tazo anan take sauka, ba yanda Auta Junior beyi ba akan ya koma dakin Yaya Hamdah saboda yanda dakin nata yake da kyau amma Mumcy taqi, jakarta da muqullin motar da dakanta ta tuqo tundaga kadunan dukda yanayin jikinta ta ajiye sannan ta shiga toilet.

Alwala ta dauro, koda ta idar da dade akan abin sallar tana kaiwa Allah kukanta har akayi sallar isha tayi, bataji motsin kowa ba seta nufi kitchen dan samarwa kanta abinda zataci jin Dan cikinta wanda kusan kwanaki uku kenan daya fara motsi kamar dama jira yake a sanda zamansa a cikin ta dan yanzu a wata dayan nan har cikin ya dan fito in dai kana da lura zaka gane.
A kofar kitchen din suka ci karo da Mumcy kafadata sakale da farar rigar likitoci (lab coat) da alama shigowarta kenan ita ma seta bude ido tana kallonta kafin tace

"Oh ni Maryamu ashe dagaske musbahu yake yace min kinzo Allah dau yasa lafiya irin wannan zuwan bazata babu notice haka".

murmushi qarfin hali tayi ba tare da ta tanka ba ta raba gefen Mumcyn ta wuce cikin kitchen din dan a yanda takejin yunwa batada karfin yi mata wani bayani a sannan. Tayi sa'a kuwa Mama tabawa na kwashe tuwon alkama da miyar kubewa da tayi ita ma da mamaki take kallonta
" Uwar masu gida saukar yaushe jiya fa muke zance zuwa duboki Hajia tana cewa Kaduna tayi dadi an jiki dif".

"Yanzu Mama saka min tuwon dan Allah wallahi yunwa nake ji kamar nayi me" ta fada tana zama akan kujerun qaramin Dining din dayake cikin kitchen din saboda yanda taji kafarta ta fara rawa. Tuwon ta zuba mata takuwa hauci hannu baka hannu kwarya kamar wadda ta shekara bata ci komai ba

"Masha Allahu Ubangiji ya sauke ki lafiya Anty na nidai dama in ce wannan dau dakikayi ashe da Magana" Mama Tabawa ta fada cikin farin ciki kamar ita ce me cikin, haka taci gana da janta da hira ita kuma tana kwasar abincinta tana gyada kai dan ya mata dadi, seda taci kusan mara uku sannan taji ta dam bata haqura ba seda ta kora da Fresh Milk medium bottle sannan ta fita daga kitchen din tana tayi mata tsiyar wai ko Nomau zata haifo musu ne.

Da kallo Mumcy ta ringa binta lokacin data shiga dakinta tana karantar sauyin data gani a tattare da ita nan take ta gano cikin dake jikinta, saidai wannan uwar ramar datayi tazarta ace ta laulayi koda yake ya danganta da irin tsirfar cikin. Gefen gadon ta samu ta kwanta dan gaba daya jikinta ya mutu tace "Wash kai Nayi missing Gadon nan wallahi"

Se Mumcy ta kalleta tana murmushi "To ai gaki akansa yanzu maganar missing ta qare, wai meya faru da yamma haka kuma ke kadai ce ko tare kuka zu?"
Seta dan yi jim dan bilhaqqi har ta manta da matsalar data korota. Ganinta cikin gidansu yasa komai ya bace mata seta qirqiro murmushin da iyakar sa lebenta kafin tace
"Ni kadai fa Mumcy wallahi na kasa jurewa se samin lokaci yake yana fasawa saboda shi kullum yana ganin Hajiyarsa shine kawai daya barni wai gobe a kawo ni ni kuma yana fita nayi tahowata" ta shiryawa Mumcy qarya dan tana ganin hakan ce kawai zata ceceta. Bata damu da fadan data ringayi mata ba dan wannan me sauqi ne hartayi ta gama akan me zata hawo titi ita kadai bayan ga yanayin da take ciki ita bata son sakarci da wauta. Kulawa cikakkiya da tasan tana buqata ta shiga bata se gata a cikin kwana biyu da tayi a gidan ta dawo hayyacinta saboda kula da kuma kwanciyar hankalin data samu. Tayi fresh tayi mulmul bata da aiki seci da bacci dab seda Abbah ya dawo ne ma yake tambayarta gida da Mijinta wanda ta ma manta dashi dan tunda ta baro gidan ta kashe wayarta shima se tace masa ganin gida tazo Mumcy na kallonta amma har zuwa lokacin bawai ta gama yarda bane dan tana lura da ita tunda tazo ko sau daya bataga sunyi waya da mijin nata ba hakan yasaka ta fara zargin Akwai wani abu a kasa da bata so ta fada.


Se ranar data cika sati da barin gidan hajiyarsa ta samu labari ta bakin Munaya kanwarsa data je Hajara take gaya mata cewa Hamdah fa ta tafi gida kuma wayarta a kashe take sannan shi gogan kamar ma be damu ba sabgar gabansa kawai yake karma wani abu ya kuma faruwa ace ita ce, bata saurari komai ba ta rangada masa kira akan duk inda yake yazo tana nemansa, yasan Hajia sarai bata da sauqi dole ya baro meeting din daya tafi Abuja ya dawo Kadunan washe gari kuwa da sassafe ta tasoshi a gaba suka nufi Kanon Dabo. kasancewar week end ne Dan haka yawanci suna gida harda kuwa su yaya Abubakar da Baffa tareda matansu duk sunzo.

Lokacin da suka zo ma ita tana can baccin farillanta na safe bata ma san wainar da ake toyawa ba. Mumcy ce ta shiga dakin, ganin yanda tayi dai dai akan gado tana bacci yasaka ta tada ita

"Mumcy kin katsemin bacci na nasan yau haka zan wuni ba dadi" ta fada tana mikewa daga kwancan Dan cikinta ya fara girma har ya fito ana iya ganinsa."To tashi kya karasa a gidanki ga mijinki da surukarki nan sunzo daukarki". Setayi dif nan take hawaye ya fara ambaliya a fuskarta
"Yanzu Mumcy kun yarda na koma gidansa ko bakisan me yake shirin aikata min ba".

"Nasani Hamdah Amma kiyi hakuri ya gane kuskurensa yakuma biyoki ya bada hakuri ko ba danshiba Dan mahaifiyarsa gatacan ta ajiye girmanta tana rokarmu Dan haka ki dauka hakan ma yana cikin *RUBUTACCIYAR KADDARAR KI* ki kuma yi kokarin da hakuri gurin tsallaketa. Har akullum Ina miki nasiha da hakuri dominshi ne jagoran rayuwar dukkan Dan Adam, tashi kiyi wanka kinji suna jiranki" ta karasa tana kautar da fuskarta Dan dauriyarta ta kusa karewa. Kwata kwata hukuncin da mijin nata ya yanke beyi mata ba Amma yaya zatayi, yaqi barin sa yayi bayanin tahowar tata kawai yace wai sabani suka samu kuma ya gane kuskurensa ayi haquri ta koma amma bai fadi ainihin dalilin sabanin ba. Wani ban garen itama tana tunanin dawowarta gida ta zauna din da dadi ba dadi dai gara tana gidan auranta.

Zama tayi a gefen gadon tana jiran Hamdaj data shiga wanka. Lokaci lokaci tana share hawayen tausayin Yar tata, Allah kenan meshiryawa bawa rayuwarsa in ba haka ba Hamdah bata cancanci fadawa irin wadannan matsalolin auratayyar ba wancan Matsalar Dangin Miji wannan kuma Mijin dungurungun. Harta fito daga wankan ta shirya bata saniba seda ta girgizata tace

"Indai akai na kike tunani Mumcy ki kwantar da hankalinki nasan Allah be manta daniba kuma fa ni gidan ne kawai ma bana so matarsa setayi ta sa wasu turaren wuta mara dadi nayi ta amai shine fa nace ya raba mana gida yaqi amma bafa wani abu ne serious ba" dole ta kakalo murmushi ta rungumeta tana cewa "Ai kedai you are capabale of giving some one heart attack, dama dalilin kenan kice Allah ya taimakeni banyi abin kunya a gaban suruki ba. Allah dai yayi miki Albarka ya saukeki lafiya Insha Allahu inaji A jikina wata rana komai zai zamo miki labari zaki ji dadin zaman aure yanda baki tsammani ba A lokacin zaki kwashi sakamakon hakurin da kikayi" Farouk ne ya shigo kiranta, seyati jim ganin Mamansu tana kuka. Guri ya samu ya zauna kusada Hamdah ya janyeta daga jikin Mumcy kanta a kafadarsa yace

"Ki gayamin in har bakya son sa zan tsaya miki da Ilimina seya sake ki" se Mumcy tayi saurin dakatar dashi da cewa
"A kul ya saketa fa farouk wata hudu me kake zaton mutane zasu ce" cikeda takaici yake kallon Mumcy wai Mutane take tunani bata san hadarin da Yarta take ciki ba, se kawai ya mike hannun Hamdah a nasa suka fara tafiya. A zahiri ana ganin basa shiri amma yafi kowa lura da lamuranta. Yana sane yana kuma bin duk zaman da take da wannan mutumin da tun farko dama beso auranta dashi ba. Da ace shine Abubakar ko Baffa yasan ya isa yayi magana a saurareshi da bata auri wannan green snake din ba.

"Hamdah nasan zaman da kike, ki gayamin zaki koma ko bakyaso" ya qara tambayarta a hanya. Seta kalleshi kafin tace
"Yah Farouk Momy da Abbah nakeji, bana so hankalinsu ya tashi. Zan koma amma in naji ba daidai ba zan kiraka na shaida maka komai nidai kuyita bina da addu'a kawai" da haka suka qarasa palour. Har qasa ta durqusa ta gaida Hajiyar Abdurrahman se kallonta take baki yaqi

Please Login or Register in order to submit comment