Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka shirya tahowa Nigeria. Surprise suke son basu dan har ranar ko picture daya basu dauki Abdulmalik ba yace wai in suka dauka baze iya ba seyayi posting kuma zeyi ruining surprise din. Ta shirya tsaf cikin baqar Abaya abinka da danyen jiki tayi wani fresh kamar ka wanke hannu kafin ka tabata. Daga ita se yar jakar hannunta ta sakko daga jirgin Tana shakar iskar Nigeria data dade rabonta da ita Abdul'ahad na biye da ita dauke da Baby Abdulmalik daya sha mother suits farare qal. Tunda suka shiga jirgi duk wnada yagansu seya tanka dan aka ringa zuwa masu so su dauka amma qememe ya hade rai sedai ka leqashi ka qara gaba.

Khaleefa ne yazo daukarsu daga Aiport, su khaleefa anyi hankali dan tuni ya gama service har ya fara aiki a FIRS dan shi seda ya gama Msc ma tukunna yayi service wai har ya fara zancen aure at 25 saboda kudi sun fara zauna masa. Yana tsaye ya hango Abdul'ahad dan shi bema gane Handah ba seya nufeshi da sauri yana masa sannu da zuwa da tambayar wai ina ya samo Baby ko na waccen Balarabiyar ne daya gani a bayansa. "Ba balarabiya ba ka manta India ce com on budewa mutane mota su shiga zafi sukeji" ta fada tana fizge key din daga hannunsa, seya buga tsalle yai gefe besan sanda bakinsa ya subuce ba ya saki wata ashar ta mamaki "Wallahi mutuniyar ce kutmar wai Hamdah ce ta haihu" ya saki wata dariyar farinciki. Yanda ya cukuma dan seda Abdul'ahad ya zare ido yace "kai Easy garinsu da nisa shiga mota se na baka shi" ai yai wuf ya shige baya bakin nan kaman kofar gari ya miqe hannaye a dole zaa dauko Nephew, seya girgiza kai kawai ya miqa masa shi kafin ya zagaya ya tada motar dan tuni ta koma gaba ganin Khaleefa ya shiga baya wato su zasu ja shi.

A storyn Khaleefa Hoton Abdulmalik ya fara yawo kafin ya dannawa Hamida Face time call dan ya kirata ta WhatsApp bata daga ba tana can kitchen an kachame anawa Yah Hamdah girki dan gidan kowa yayi missing nata over ta daga wayar da masifa ko uwarme ze mata daya kira Video call oho tana daga wa kuwa yace "Banza a haka kiran arziqi ze wuceki kinacan kina hauka ai dai Salim ya shiga uku da kudinsa ze dauko mahaukaciya kalli nan ki gani" ya fada yana mayar da cameran fuskan Babyn bayan ya gama tijara. Hamidah data shaqa haka suke kamar masu ganin Hanjin juna, tunda Hamdah tai auran farko fadan ya koma kan Hamidah zata bashi amsa idonta ya sauka kan yaron da indai kasan Babansa baka buqatar bayani ta kuwa taqarqare iya qarfinta ta saki ihu da sedq Abdulmalik ya farka kit kuwa ya kashe wayar.

"Kingani ko ai wallahi ku daga auran yarinyar nan gashinan zata kurmantar mana da Da" ya fada yana jijjiga Abdulmalik, Hamdah da ke dariya kaman ta kifa ta juyo tarefa karbar danta ta shiga jijjiga shi tana ci gaba da dariya tace "A ga wanda yafi wani hankalin a tsakaninku ai".

Acan gida kuwa da gudu suka shiga kitchen harda Abbah dake shirin fita suka jiyo ihunta a zatonsu wani abun ne ya sameta amma se ganinta sukayi tana tiqar rawa kamar sabon hauka. Yah Farouk no nonsense yayi kanta ta kwasa da gudu tayi Bayan Abbah tana ci gaba da dariya tace "Abbah albishirinka"

"Hamidah Allah ya shirya ki dai Goro wane abun farin cikine yasa zaki bamu heart attack mu kuma"

"Nidai Abba promise me zak semin iPhone 12 in na gaya maka"

"In dai Albishir din ya cancanta zan qara miki harda I Watch kuke kiransa ko" ai ko ta qara daka tsallen murna tace "wallahi harda sabon Aipod duk seka siyamin indai kaji muje palour duk in gaya muku. Abbah dai se dariya yake, yasan Hamidah bata fiya irin wannan wasan ba dole wani abune me muhimmanci ya faru.

"Yaya Hamdah ta dawo...." Dallah yimana shiru waye be sani ba, junior ya katseta, seta harareshi kawai tace "Banza mara kunya" taci gaba.

"Abbah ta taho mana da Mini version din Yah Abdul'ahad wallahi little tayi qani yanzu Yah Khaleefa ya kirani Face time da kunzo da wuri da kun gani ma kafin ya kashe" bata rufe baki ba horn din mota ya karade kunnensu ta kwasa da gudu tayi waje.

Abbah dake tsaye ya kalli Mumcy data kasa motsi se raba ido take yace "se kije ki sake gyara daki ga sabon ango nan kafin Hajia Aisha ta rigaki" yai waje dan shima baya jin ze iya jira su shigo ciki. Yanaso yaga jikan da yake ta cira ta bangaren Favorite daughter dinsa.

Kamar Assembly haka suka zagaye motar Abdul'ahad da Khaleefa sun fito tana ciki ta saka Lock ji kawai take ina ma kawai qasa ta bude ta shige tsabar kunya, se yanzu ta gane shigo shigo ba zurfi ya mata dayace su sauka anan dama can gidansu ya kaita da sauqi tu da dama bata saba dasu ba amma yanzu da wane ido zata kalli Ammani's???

"Mamana bude ki fito Abbanki yaga Abokinsa kinji karkisa na fadi saboda murna" Abba ya fada yana kwankwasa glass din, Allah kadai yasan farincikin da yake ciki a lokacin, sauke glass din tayi kanta a qasa ta miqo masa Dan zo kaga hannaye dukka Abbah ya doke su ya karbeshi kafin yace mata "fito Mamana kema ai ina so na ganki" seta bude motar ta qara jawo mayafinta ta rufe har fuska ta fada jikin Abbah ya hada ita da jikansa ya rungumesu. It was an emotional moment, Hamdah kuka Abbah kuka haka suka shiga gidan Mumcy dake waya da Ammi tana shaida mata abinda ya faru amma wai bata tabbtar ba tukunna tace

"Ta tabbata Hajia Aisha wallahi ga Da ko Ya nan A hannun Abbansu amma wadannan yara anyi shakiyyai" wayar ta kashe hannunta har rawa ta nufi Abbah tana "Abbah kawo shi ai ka dauka"

"Kinga jeki ba yanzu ba hira zamuyi irinta Aminai mu tattauna muhimman batutuwa" gaba daya suka saka dariya. Kiri kiri ya hanata Dan, Hamdah data samu ta fece sama da sauri ta shige dakinta da aka sake gyara mata saboda zaman jego dama ta kwanta a gadon tana maida Numfashi.

"Noory sun manta damu, kowa ta Abdulmalik yake ko sannu da zuwa fa ba'a mana ba" Abdul'ahad ya fada bayan ya shiga dakin ya maida kofar ya rufe. Seta tashi zaune tana kallonsa da murmushi tace "bansan haka kunya take ba, Ni Hamdah ya zanyi Ace bada aure muka haifi yaron nan ba??"" Seyai saurin qarasawa ya rufe mata baki

"Karki kuma fadar haka, kina zaton zan iya neman ki bada Aure ba? Da nayi tun lokacin da nake da quruciya akaina. Ke nake so Hamdah ba wani abu na jikinki ba"

"Dadyyyyyyyyyyy" Little ta tunkudo kofar ta shigo da gudun tsiya ta haye jikinsa, kamar wadda aka sawa pause ta tsaya kafin tayi tsalle daya ta dane Hamdah tana cewa "Finally Aunt Berbie is home I'm so happy Aunt Berbie na ta dawo" ta ruqunqumeta iyakar qarfinta. Seta rungumeta ita ma, tausayin yarinyar na ratsata. "Aunt Berbie da zamu tafi school Aun Hamidah tace yau zaki dawo, zo muje kiga wani little Cahmp wai Dady nane ya siyo shi" ta fada tana jan hannun Hamdah, se ya riqeta yace "Kai ke ina kika koyi hausa"

"Uncle Junior ne yake koya min hada french da Arabic Dady dukka na iya and i can speak them both fluently, Dady ka siyo Boy saura Girl i want a twin sis just like Yah Amra and Yah Afra" se ya nuna mata Hamadah yace

"Here is your new Mumy ita zata kawo miki" seta riqe hannunta, "really you are my new Mumy? My other Mum is Gone, Uncle Junior ne ya gayamin bazan sake ganin Mumy ba amma yace indai ina yin sallah kullum kuma inayin Addua Allah ya jikan Momy na wai zan ganta a Aljanna wai haka ne Daddy?" Gaba daya tausayin ta ya kamasu, Hamdah har idonta ya kawo ruwa. Seya daga mata kai tareda janyota jikinsa yace "Yes Darling Momy tana aljanna tana jiranmu but we got another Mom here she will take care of us" gaba daya suka shagala da hira da little.

"Iko se rabbani, ashe kuna nan kin kunna Ac ko ta tashi maza Babana sannunku kun kyauta kaji" muryar Ammi ta daki kunnensa, ai se aka rasa waze boye wani dan shima kunyar yaji, tunda Mumcy ta sanar mata da zuwansu ta kasa zama seda ta taho ta ganewa kanta itama. fatattakar sa tayi suka fara mata shirin jego sahihan dama kunyar bataje har zuciya batuni ta ware ta shiga hidimarta. Tana kunna layinta na Nigeria kira suka fara shigowa harta rasa wanda zata Daga. Family, Friends, Abokanan aikinta a Poly haka ta ringa amsa kira a jere a jere duk na taya murna. Anty Mami qanwar Mumcy ce ta mata wanka, kafin a Gama Hamdah tasha kuka dan bata mata da sauqi ba. Sega Yellowish skin ya koma Red lol.

Tun tana cikin toilet din take jiyo karadin Afeeya, Maryam da Aysha. Qawayenta na raida rai na Amana. Allah sarki Afeeya da Aysha saukar su kenan dukka a Abuja suke zama yanzu haka sukayi boarding jirgi suka taho saboda zumudi. Finally Hamdah tayi dan kanta after 7 shekaru bakwai masu cike da damuwa da tashin hankula kala kala. Tana fitowa suka zagayeta kamar su cinyeta kowa na mata sannu kafin suka zarce da tsokana an tafi karatu an dawo da digirin digirgir.

Se bayan sallar isha ya kuma dawowa gidan da zugar Abokansa da suka zo ganin Baby. Abdulmalik na bayan Anty Mami ta goyeshi suka shigo kusan su goma suka zube a palour gogan kuwa kan sa. Tsaye ya haye sama dakin da take suna ta masa tskya wai ko kunyar idon surukai bayayi yace ai shi bashida suruki a gidannan, iyayensa ne. Hamdah na zaune tana shan fatan jelar Sa da Ammi ta mata dakanta kafin ta tafi suna Hira da Anty Intee da Maryam dake jiran Yusuf dan tare suka zo dasu Abdul'ahad din. Cikin sakin fuska suka gaisa dasu yana tambayarta ina Boy tace yana bayan Anty Mami ta goya shi, se ya bude ido "what goyo yaron da qashinsa be yi kwari ba so kukeyi yayi bow leg" seya juya ya fice yana ta mita shi kadai ya shiga neman Anty Mami.

Da ido suka bishi kafin Maryam ta kwashe da dariya tace "Lallai su Sir Guru anyi Da ina ma zamanin muna School lamarin nan ya faru kai da anga lamari, bari na kunna Data kiga messages din ALUMNI group every one body was shocked da aka ce Hakdah matar Sir Guru ta haihu harda masu kirana fa a waya wai yaushe kukayi aure dama kunyi soyayya ne a school nace nima bansani ba of sudden kawai abubuwa suka faru". Ita dai cin abincinta kawai take tana murmushi, bata san meya faru ba se ga Anty Mami dama ba daga nan ba gurin sababi ta fara wai mijinta fitsararre yaje ya kwace dansa daga bayanta tayi ta gama ta fita. Baccinta tayi cikin salama dan kwanaki biyu da haihuwar basa bacci, shegen kukan dare ne dashi yau kam yana can gurin Anty Mami wayarta ma da Abdul'ahad ze dameta wai shifa ba kaita yayi wanka ba dan haka ta fara shiri zata koma gidansa tace to, ze kuma magana ta kashe wayarta gaba daya a ranta tace ba kwana Arba'in ba ita sittin ma zatayi. To ina take da wani gida ita ma??

Haka dangi da abokanan arziqi sukayita zuwa ganin Babyn da aka qi fadar sunansa har yau kwana shida, duk wanda ya tambayeta se tace be gaya mata ba dan yace it should be a surprise. Ranar kwana hudu aka kawo kayan barka daga gidan Yarima Abdullahi ko muce lefen da beyi ba suka rama dan kayan sun zarce hankali. Akwati na dukan Akwati saiti me shida seda yai mata guda 6 pieces 36 kenan shaqe da uban kaya kamar me bude supermarket, Baby Abdulmalik ma haka aka yo masa akwati sha biyu banda uban nin kayan da suka siyo daga UK, tarkacen kayan Baby gadaje kansu guda uku suka sako masa. Pusher, car sit, Walker, motoci da baburan wasa masu tafiya da duk wani tarkace da ze iya nema seda suka sako musu a kayan Barka. Jaka daban aka sako kayan da zatayi amfani dasu na walimar suna wani Arnen Lace, takalmi, jaka, mayafi da sarka da Agogo gaba daya in aka hada kudinsu sun kai jarin wani babban Attajiri.

Daki guda aka jibge kayan Mumcy ranar har kuka tayi tsabar farinciki da murna. "Kin ga ribar hakuri ko? Kinga jin dadi da nake gaya miki yana tafe gashi tun ba'a je da nisa ba kin same shi. Kin samu soyayyar miji data yan uwnasa abinda kika rasa a baya da kikayi haquri gashi ubangiji ya saka miki da mafiyin abinda kika rasa a baya. Tabbas duk lamarin daya faru _RUBUTACVIYAR QADDARAH_ ce cikin kundin rayuwarki Hamdah insha Allah komai ya zama tarihi yanzu".

Ranar suna raguna hudu Baba ya bada a yankawa Abdulmalik banda guda Biyu da Abbah ya bashi ga nasa daya siya da kudinsa guda biyu suma. Qarshe aka yanka hudu yabar hudu. Yaro yayi goshi taro akai bana wasa ba Marhaba ya kama Hall inda za'ayi walimar suna plus shagalin bikinsu da baayi ba yace dole su hau high table tasa gwagwgwaro ya saka babbar riga ita dai dariya kawai take masa. Haka kuwa sukayi, Abdul'ahad da Hamdah suka hade a high table da dansu Abdulmalik daya fara zama wani attajiri tun a zanin Goyo. Kyautar Motoci guda biyu da Gida ginanne Alhaji Kamalu mahaifin Marigayi Abdulmalik ya aiko masa da ita lokacin daya ji karar da sukayiwa Dansa marigayi. Haka Abokanan Abdulmalik da yayyensa suka ringa aiko wa da kudade kyauta wa takwaran Abokinsu. Hajja Fattu kuka ta fashe dashi lokacin data zo da safe aka gaya mata sunan jaririn, ta ciko ledojinta da kayan Barka tace a mayar dasu mota wannan zuwa barkar na Musamman ne, tunda Abdulmalik ya rasu babu wanda ya maida sunan sa se Yanzu da Hamdah ta haihu lallai ta yarda soyayyar da take masa bata wasa bace, kuka da rokon yafiyar ta shiga kumayi da har seda ta saka Hamdah kuka ita ma.

Kwanan ta talatin da haihuwa tayi kyau saboda in gantaccen jegon datakeyi haka Abdulmalik yayi wayo sosai kyau da kamarsa da mahaifinsa ta sake fitowa. Tana zaune a palour tana bawa Abdulmalik din nono suna waya da Abdul'ahad da aka mayar Hayatyyyy yanzu satinsa daya da komawa London an kirashi wani aiki akayi sallama. Hajara ce kishiyarta a zamanin auran Abdurrahman da wasu yara da zasuyi sa'annin little kana ganinsu kasan yan biyu ne seta masa sallama ta kashe wayar tareda cire Abdul ta miqe tana mata sannu da zuwa. Seda ta gabatar mata da abin sha sannan suka gaisa se kallonta takeyi, ta chanza gaba daya tayi kyau sosai ga kiba da ta danyi alamar Hutu da kwanciyar hankali sun ratsata.

"Se mukaji abin alkhairi biyu a lokaci daya, bansan kinyi aure ba seda na hadu da Maman Amrah last week a Kaduna take cemin kin haihu, jiya na dawo Kano nace kuwa dole na zo naga Baby" ta fada tana kallon yaron with so much adoration. Da mamaki Hamdah take kallonta, meya kawota kano kuma dan tasan iyayenta dukka Yan Kaduna ne kuma can take aure, kamar wadda ta shiga zuciyarta fuskarta dauke da murmushi "tace kina mamakin me nake a Kano ko? Ai na dade da barin Kaduna inaga tsiranmu befi wata biyu ba Nima ya sakeni, gashi har nayi wani auran ma wata na biyar kenan Halan baki da Labarin Abinda ya sameshi ko??"

Seta gyara zamanta tana kallon Hàjara dason jin qarin bayani, yaran da tazo dasu Husna da Hasina tacewa suje suyi wasa a waje dan lokacin su Little ana school babu kowa a gidan Mumcy ma tana Asibiti Amarya Hamidah an tafi rabon IV se Mama tabawa da Hamdah kawai da Anty Intee dake fama da Laulayi tana daki tana bacci.

"Ai Hamdah bayan Abdurrahman ya sakeki tsiran sati daya aka kamashi a Qatar wai ya shiga da Cocaine, duk irin Kokarin da Babansu yayi amma a banza dan sunqi yarda shari'arsa ta dawo Nigeria saboda acewar Airport officials din bashine karo na farko ba dama yana safararta akwai wadanda suka tsaya masa yake wucewa da ita. To an samu chanjin ma'aikata acan din matsalar daya samu kenan kenan sukayi ram dashi. Dalili kenan yasa Babana ya nemamin takadda ta be musa ba kuma ya sakeni sema haquri daya ringa bamu akan wai cutar damu da yayi nidai nace Yaje shida Allah na yafe masa tunda nima da nawa kuskuren a ciki na kuma daukar masa alkawarin duk randa na ganki kema zan nema masa yafiyarki".

Numfashi Hamdah ta ajiye kafin ta janye tagumin da tayi tana jin jina lamarin, ashe da kudin Haram ya ringa ciyar dasu? Ta godewa Allah daya takaita Samuwar zuri'a a tsakaninsu yanzu da ta cewa Yayan da suka haifa me?? Hira suka ci gaba dayi zuwa wani dan lokaci kafin ta mata sallama ta tafi, basu da wani nisa ma daga nan gidansu a cikin unguwar take yaran da tazo dasu yayan kishiyarta ne wai sukayi exchanging Contact ta tafi" haka ta kwana da tunanin abunda ya samu Abdurrahman qarshe ta yakice tunanin ta shiga sabgoginta tunda aka ce tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa ze doka haka ne kam.

Kwanansu 68 Abdul'ahad ya dawo a ranar kuma yace zasu koma gidansu da tuni aka gama furnishing masu shi. Gini ne na alfarma yayi mata irin tsarin da tace tanaso Bene Hawa daya da palour uku, nata, nasa da kuma na yara wai idan sun girma da Bedrooms guda 8 a sama da qasa se BQ a bayan gidan. Gidan ya tsaru matuqa haka kayan da aka zuba masa sun dace dashi dan duk auran da tayi babu wanda akayi mata Jere irin na gidan Abdul'ahad Galadima duk kuwa da yanda yaqi akan shi ze saka komai Amma Abbah yace Aa haqqinsa ne yawa yarsa kayan daki dakyar aka raba suka saka mata Gadaje uku ya saka ragowan banda Na Abdulmalik da already yana dasu dakuna biyu aka zuba masa kayayyakinsa a ciki. Da rana yan ganin gida sukaje dan yace daga shi se matarsa zasu tafi, haka kuwa da Magriba yazo ya dauke su banda Little da tace bazata bisu ba wai zasu zo da Mumcy.

Duniya sabuwa Hamdah da Abdul'ahad suka bude me cike da tattali da kulawa da junansu. Ta koma aikinta amma a BUK take lecturing yanzu shi kuma yana ci gaba da running businesses dinsa da ada bata san yana dasu ba. Abdul'ahad Don ne me zaman kansa yaro amma ya taka matakin da manya basu je ba. Abdulmalik nada shekara daya aka masa Appointment as Minister of Youth na Nigeria saboda Baba yayi retire alfarmarsa da kuma cancanyar Dansa tasa aka bashi wannan matsayin, zo kaga Hajia Dr Hamdah matar minister, dole ta aje aiki suka koma Abuja saboda aikin office dinsa taci gaba da kulawa da Yaranta Little da Boy dan yanzu ta yarda ta koma gida saboda qaninta da suka matuqar shaquwa bata iya rabuwa dashi in ba school ba itama ya ringa kuka kenan har seta dawo gida.

10 Years Leap

Matashiyar Mace ce yar kimanin shekaru 37 sanye da convocation gown idanunta na zubda Hawaye, Ambassador Abdul'ahad Galadima jakadan Nigeria a qasar England na tsaye dauke da qaramar yarinya da bazata wuce shekara daya ba fara tas da kallo daya zakayi mata ka hango zallar kamanninta da Mamanta Hamdah sedai har tafi Hamdah Fari, murmushi yake yana kallonta yanda ta dage tana hawaye ya kasa tsaida ita dan yasan bazasu tsayuba.

"Yawwa Little, Boys come over here, kunga dai banma Mammi komai ba tana kuka nidai babu ruwana ku tambayeta me aka mata". Little kyakykywawar yarinyar data fara zama budurwa dan tana 14 years yanzu ta qaraso da sauri ta shiga goge ma Hamdah hawaye kaman zatayi kukan ita ma tace "Mammi stop it please we know you are over joy but Uncle Khaleefa will laugh at us, zece Mammin mu bata girma haryanzu bata dena kuka ba".

"Yes Mammi even yesterday he mocked me at the Airport that My Mum is still a kid just like Nihla" Abdul'ahad junior da bashida banbanci da Babansa hatta da skin color dinsa, voice and everything irin na Babansa ne yai maganan dakyar kaman an masa Dole. Abdulmalik na tsaye ya riqe qugu kaman mace yace "Lets go Fam The Ammani's and Yarima's are waiting for us" ya juya yai gaba abinsa. Haka yake shi yadakko halinta tsaf dan rigima ne. Dole ta share hawayen Little da Junior suka kama hannayenta daddaya Abdul'ahad na binsu dauke da Nihla dake ta gwarancinta yana amsa mata da Yes.

Kafatanin Iyalan Prof Ahmad Ammani dana Tsohon Ambassador Yarima Abdullahi na tsaue filin Convocation na Cambridge University sunzo taya yarsu Hajia Hamdah Abdul'ahad Galadima murnar zama cikakkiyar Professor in Genetics, mafarkinta ya zama gaskiya. Sakin yaran tayi ta shiga cikin yan uwanta suka fara Exchanging Hugs da taya murna. It was a memorable event, sun dauki hotuna aka ci abinci aka sha yara suna ta wasan su kafin daga baya suka wuce Galadima Mansion wato gidan Ambassador Abdul'ahad a yanzu. Likafa taci gaba, a shekaru Goman nan sun taka matakai masu nisa a rayuwa ciki harda matsayin Ambassador da Emaratus Professor Abdul'ahad Galadima ya kai at the of 45. Acan hidima taci gaba, kwana ki biyu suna fama da baqi sannan kowa ya fashe ya koma inda yake aka bar su kewar yan uwa.

Yayansu Hudu, Bayan Little da Abdulmalik ta haif juniori Abdul'ahad se Maryam Nihla da take Goyo yanzu dan Ammi tace anriga an mata Takwara ga Aysha Hamdah nan sedai Kuma Dr Maryam. Rayuwa kam sedai Hamdala domin Abdul'ahad ya isar mata Miji da za'ayi tutiya da tinqaho dashi. Kamar yanda ya mata alkawari ne shekaru goma sun wuce bata sake yin kuka ba in bana shagwabar da yake fada ba daga ita har Yayan da yake ji kamar tsokar jikinsa ya zame musu jigo, bango abin dogaro. A koda yaushe idan ta kalli Ni'imar da take ciki seta sake godewa Allah da baiwar da yai mata. Sam bazaka taba cewa ta taba fuskantar wani abu waishi matsi a cikin rayuwarta ba.

Dukda ko wanne aure da irin nasa qalubalen amma aka ce fahimta ita ke saita komai, akawai kyakykyawan fahimta da alaqa a tsakaninsu da ta saka suke iya warware dukkan matsalolinsu ba tare da wani ya shiga ciki ba, se kuma addu'a. Ta riqe Allah ta mayar da dare wurin neman Sa'arta. A kullum seta tashi ta godewa Allah sannan ta qara damka amanarta data yaranta da Mijinta abin alfaharin a gareshi, ta roqi kariyarshi a gare da dukkan wata Nasara ta rayuwa da cikawa da Imani, haka bata taba mantawa da Abdulmalik dinta ba haryau bata dena charity work saboda shi ba. Duk abin da ta samu da dukiyar daya barmata seta raba biyu tayi wani abun da tasan ze samu lada. Ni'ima ma ta shiga ciki yanzu haka kullum tana kan nuna ma Little muhimman cin yi ma mamanta Addu'a dukda bata ragi yarinyar da komai ba. Idan ba Family Members ba babu wani out sider daya san ba ita ta haifeta ba.

MURFI

Professor Hamdah Abdul'ahad Galadima na tsaye gaban dressing mirror tana taje kanta data gama busarwa. Allah Allah take ta gama shiryawa kafin yaran su waiwayota, suna can gurin Dady suna karatun qur'ani kaman yanda ya zamar musu al'ada kullum sukayi sallar Isha se sunyi tilawa. Gasa ya saka musu akan wata gagarumar kyauta da ze bawa duk wanda yayi haddar Izu goma a wata uku tsakanin Little, Abdulmalik da Junior shine suke ta Himma. Nihla ce ta turo kofar a hankali ta shigo kafin junior ya biyota a baya fuskar nan a hade kaman Guru lokacin yana lecturing a BUK.

"What happened sweetie" ta tambayeshi tana janyo shi jikinta ita

Please Login or Register in order to submit comment