Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanta allura amma yaya zatayi? Bata so ta zama meson kai bakuma taso ta raba wannan soyayyar, Kifa kanta tayi akan cinyarta tana ci gaba da kukan dukda tasan abinda hakan ze iya haifar mata.

Tausayinta ne ya shafe haushin daga zuciyar Hamdah, wannan wace irin mace ce da zata iya sadaukar da Mijinta, mijin ma irin Abdul'ahad alfaharin kowacce mace. Se ta zamo daga kan kujerar da take, bata damu da lallen Hannunta ba ta qarasa ta dagota tareda rungumeta itama tana zubar da Hawaye.

" Ni'ima kodan wannan sadaukarwar da kikayi bazan iya auran sa. Taya ma kike zaton zan iya qara kallonki bayan na aurar miki miji? Nasani son da kike masa ne yasa har kike qoqarin nema masa nasa farin cikin koda yaci karo da naki amma ni bazan so kaina ba, Naso Abdul'ahad ada amma na haqura dashi daga lokacin dana ganki a cikin rayuwarsa. Bazan iya shiga na rusa muku ginin da kuka faro ba......" Seta yi saurin rufe mata baki tana cewa

"Aa karkice haka ke din kece cikon farin cikin gidan mu. Our home is incomplete without you, we been living a sorrowful life, ki taimaka ki kawo farin ciki a tsakaninmu we want you in our life" Tayi maganar tana qara qanqameta.

Seta janye jikinta a hankali ta koma kan kujerar zuciyarta na mata wasi wasi kala kala. Meya kamata tayi? Shin ta amince da buqatar Ni'ima ko yaya?
"Wannan matar bata cancanci haka ba Hamdah, tsaya ma wa kike tunanin ze dakatar da wannan auran amma dae ba Abba na ko?" Zuciyarta ta tambayeta.

Inteesar data kai qololuwa a mamaki ta sauke numfashi tana kallon Ni'ima da ta dena kukan se ajiyar zuciya takeyi tace

"Sannu da qoqari yar uwa gaskiya gobe dole inyi publishing labarinki Jarumar mace tazo nemawa mijinta aure amma sedai anyi rashin sa'a kin makara dan wani ya rigaku zuwa".

Seta kalleta sosai dason jin qarin bayani.
"Kwarai kuwa da alama baki san gobe ne daurin auranta ba wannan qunshin ma da kikaga ina mata na biki ne gobe iyanzu mun kaita Garin Gwamna insha Allahu" Indo me lallece ta qarasa mata bayanin ganin kamar bata gane me Intee take fada mata ba.

Seta bude baki da alamar mamaki take binta da kallo, kai ta gyada mata cikin tabbatarwa kafin ta nemo Invitation card din daurin auran a wayarta wanda harda picture dinta dana Abdurrahman din a gefe ta miqa mata jiki na rawa ta karba ta duba.

"Ubangiji Allah yasa hakan shi yafi alkahiri idan kuma akwai sauran dama muna nan bamu hakura ba" Ni'ima ta fada bayan data miqa mata wayar dan ta tabbatar babu sauran wani abu ayanzu kuma ya qara makara kar na wancan lokacin. Jakarta ta dauka ta miqe da kyar saboda nauyin da taji kafafuwanta sunyi mata daidai da shigowar Safeena da ta gaji da jira a waje, saurin tareta tayi tana tambayarta lafiya
"Mutafi gida bana jin dadi Safeena" nan da nan hankalinta ya tashi dan ko kadan basa son abinda ze jawo motsawar jikin yayar tata. Kamata tayi suka fita bayan sunyi musu sallama tana ta mita wai ta zauna tana ta magana gashinan ta jawo wa kanta wahala ita dai bata ce mata ta tafasa ba tunani takeyi kawai a zuciyarta Halinda Abdul'ahad ze iya shiga. Rabonta dashi tun jiya a bakin Fadila taji wai ya dawo a dakin Ammi ya kwana tun daga nan tasan babu lafiya. Koda safe waya yayi mata takai masa kaya yayi wanka acan ya fita bata da tabbacin ina ya tafi ko ya dawo gidan yanzu. Wani irin sharp pain taji tundaga kafarta har maqoshinta se tayi saurin riqo hannun Safeena dake tuqi tana ci gaba da Mita

"Safeena mu wuce hospital please its getting worse" cikin karfin hali tayi maganar dan haka Safeena tayi saurin chanza wa motar direction. Kafin suje asibitin ta gama galabaita dan har ta fara aman Jini ga jikinta da yayi wani mugun zafi kamar an anjona heater. Kuka Safeena take kamar me lokacin da aka shiga da ita ICU ta shiga kiran number Mamansu amma busy, Abdul'ahad ta kira akayi sa'a yana kusa da gurin dan haka ba shiri ya tafi asibitin.

Hankalinsa yakai kololuwa gurin tashi ganin yanayin da take ciki, likitoci uku ne akanta suna qoqarin ceto rayuwarta to wai ma meya sameta of sudden haka? Matar da suka rabu lafiya dazu babu wani alamar ciwo a tare da ita.
"Daga ina kuke" ya jefawa Safeena dake kuka hannuwanta dukka biyu aka tambaya.

"Nima ban sani ba Yaya kawai cewa tayi nazo na rakata gidansu wata friend dinta da mukaje ma korata waje tayi sukayi magana shikenan fa da muka taho tace na kawota asibiti bata jin dadi".
Safa da marwa ya shigayi, wace qawarta taje gidansu da bata gaya masa ba? A kwanakin nan he is suspecting that she is up to something amma koma mene ba wannan bane damuwarsa a yanzu, samun lafiyarta shi ne first priority dinsa daga nan se yaji koma mene a bakinta. Yafi awa daya a gurin sannan yan gidansu suka qaraso harda Amminsa da qanwar tata Maman Ni'ima ta kira ta sanar da ita. Haka suka zauna jigum jigum kowa da kalar tunaninsa fatansu kawai Allah ya tashi kafadunta. Se mu tayasu a Amin.

****************
A bangaren Hamdah duk yanda su Inteesar suka so suyi maganar qi tayi qarshe ma tace musu tana so maganar ta zama sirri bata yarsa su gayawa kowa zuwan Ni'ima ba, sukuku aka gama lallen ta wanke ta koma main house din anan ta tarar da mutanen da suka taru. Daurewa tayi aka shiga gaisawa kowa yana mata Allah sanya alkhairi da fatan zaman lafiya ta ringa amsa musu da Amin tana murmushin da bekai zuciya ba.
Dakinta tashiga tayi wanka bayan ta fito tana zaune agan dressing mirror, wayarta ce a hannunta tana jujjuyawa tunani take ta kirashi ko Aa? Zuciyarta ce tafi tafiya akan ta kirashin ko ba komai tana so taji dalilin dayasa ya turo mata matarsa. Seda tayi masa 5 missed calls be amsa ba lokacin yana can ana dibar jininsa wanda za'a qarawa Ni'ima da suka ce volume na jininta yayi qasa sosai.

Tsaki tayi tareda jefar da wayar akan gado, dan rainin wayo ita zata kirshi ma yaqi answer wa to yayiwa kansa haka ta ringa mita har ta gama shiryawa ta shiga sabgoginta. Har dare tana sauraron ko ze kirata, lokacin da agogo ya buga karfe shabiyu daidai ta cire rai takuma tabbata baze kirata ba a wannan lokacin ma. Seta tuna waccen ranar data ringa jiran kiransa irin haka wanda shi ya bata qarfin guiwar yanke decision dinta a wancan lokacin, yau ma ya qara tabbatar mata baya buqatar ta a cikin rayuwarsa. Ya tabbatar mata daya rabu da ita a karo na biyu, se kawai ta fashe da kuka, kukan da bata san dalilin yinsa ba.












🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 3⃣3⃣


Karfe Biyu da rabi na rana bayan an sakko daga Masallacin dake cikin BUK old site Dubban mutane suka shaida daurin auran Abdurrahman Ibrahim Khalil da Hamdah Ahmad Ammani a karo na biyu. Ko kusa ko alama batayi farin cikin da tayi tunani ba da auran ga wata kewa da soyayyar Abdulmalik data taso mata lokaci daya.

A Ranar Mumcy tayi nata wunin Amarya tayi kyau sosai iya dauriya tayi dan hana Kukan da takeyi cikin zuciyarta ya fito fili amma ina dole seda tayi dab da ana shirin tashi daga wunin tunowa tayi da ranar kamun auranta da Abdulmalik a daidai irin wannan lokacin ana shirin tashi ya shigo gurin da Abokanansa bata san lokacin da kuka ya kwace mata ba duk wanda ya kalleta yasan kukan me takeyi se haquri suke bata rayuwa kenan. Ranar raba dare sukayi da Mommynta tana mata nasihohi akaro na biyu zata kuma rabuwa da favorite daughter din nata Gashi a goben da sassafe za'a wuce da ita kaduna. Washe gari kuwa kamar yanda Abbah ya fada Karfe shadaya motocin kai Amarya suka fara hawa titi domin yi mata rakiya zuwa gidan angonta, sai muce Allah ya bada zaman lafiya.
*************************************

Malam guru kuwa a asibiti ya kwana gurin Ni'ima da har wayewar gari bata san waye akanta ba. Allura me qarfin gaske akayi mata dan ta samu isashshen hutu kwakwalwarta ta goge duk wasu tunani da suke ciki sannan kumburin da zuciyarta tayi ya sace. Wuraren shabiyu ya koma asibitin bayan yaje gida yayo wanka da ka ganshi kasan bashi da Nutsuwa, rashin lafiyar Ni'ima yana dagula masa lissafi gaba daya hankalinsa baya kwanciya har seyaga ta dawo yanda take. Amina ce ta miqa masa wayarsa daya bari a asibitin ya tafi gida

"Yaya gashi tun dazu ake ta kiranka a waya". Karbar wayar yayi, missed calls ya gani barkatai se kawai ya bi na Fahad
" Oga ya ake ciki" Fahad ya fada bayan ya daga wayar
"Fine ina ka shige ne wayarka baya shiga".
"Wallahi Somalia naje in gaya maka shiga wani kauye babu network Allah ne ma ya fito damu lafiya".
"Ok kana ina yanzu" ya tambayeshi
"Ina gida oh namanta Mimi ta haihu dazu da safe (yana nufin matarsa)
"Masha Allah me aka samu"
"Abdul'ahad Dan Galadima"
Besan lokacin daya fara dariya ba duk da yanayin dayake ciki sannan yace
"Kai dai you will never be serious in your life".
"Wallahi I'm serious nayi masa huduba da sunanka" se yayi shiru for some time kafin yace
"Thank you Man Allah ya masa albarka kayiwa Mimi sannu Insha Allah later zan shigo yanzu in Hospital jikin Ni'ima ne ya motsa".
"Ashsha Allah ya bata lafiya bari nima yanzu shirin fita nake insha Allah zan shigo Allah ya bata lafiya" da Amin ya amsa masa kafin sukayi sallama. Within few minutes ya qarasa asibitin, nan suka zauna suna tattaunawa akan ciwon nata. A cikin BUK old site sukayi sallar Juma'a sunata mamakin yanda masallacin ya cika da Jama'a yau, a bakin wani da suka zauna kusa dashi sukejin wai Daurin auran Dan wani tsohon governor za'ayi sudai basu zauna ba dan kowanne yana da uzuri suka tafi batare da an daura auran ba.

Cikin ikon Allah Ni'ima ta samu sauqi kwanaki uku bayan kwanciyarta a asibiti. Dokoki sosai likitocin suka qara kafa mata idan har tana son rayuwarta kenan ita dai sedai tayi murmushi a zuciyarta tana cewa "Wace rayuwa ce kuma ta ragemin a yanzu ai na riga na siyi kasada daga ranar dana auri wanda baya sona" da haka aka sallameta suka koma gida.
Be wani takura mata ba dan yanzu kaffa kaffa yake da ita duk da har yanzu yana so yasan ina taje a waccen ranar, shi se yanzu da hankalinsa ya kwanta ma ya tuno da ita amma se ya danne abin, yana ganin lokaci yayi daya kamata ya kalli rayuwa a yanda take, har zuwa yaushe ze cigaba da zama haka? He is 33 already ya kamata ya nutsu yayi setting family full of Love and Happiness "Amma your key to the happiness is missing" zuciyarsa ta raya masa.

Kashe motarsa yayi dan yafi minti goma da shiga gidan dawowarsa kenan daga Abuja yaje gurin Baba dayai masa wani kiram gaggawa amma be shiga gidanba. Ya gaji zuciyarsa da gangar jikinsa suna da buqatar hutu a yanzu amma dole ya shiga ya gaida Ammi kafin ya qarasa nasa part din. Tana zaune kamar koda yaushe jikokinta sun zagayeta ko me sukeyi oho dayake ana hutun makaranta ne yawancinsu suna gidan harda Saudah dake US itana tazo da yayanta. Gaba aya yaran suka gaishe shi banda little da adole fushi take da Dadyn nata wai yaqi kaita gurin Berbie shima se ya shareta dan baya cikin walwala a lokacin.

Kallon tausayi Ammi take masa, gaba dayansa ya rame ga wata qasumba daya tara kana ganinsa dai kasan baya cikin nutsuwa sosai amma zurfin ciki irin nasa baze bari ya fadi damuwarsa ba.
"Galadima" Ammi ta tsayar dashi bayan daya juya yana shirin barin palour se ya dawo da baya ya zauna.
"Shiga dakina ka jirani ina zuwa" se ya miqe ita kuma ta shiga qarasa rabawa yaran Tatacciyar Madara me dumi da takeyi a glass cups. Lokacin data shiga dakin yana kwance rabin jikinsa akan gadon qafafuwansa kuma a qasa, idonsa a rufe ya riqe kansa da dukka hannunsa biyu. Try din data zubo masa kayan abinci ta ajiye akan madaidaicin centre table din da yake tsakiyar dakin qarar haduwar farantin da try ta sakashi ya bude idonsa yana kallonta.

Abincin ta shiga zuba masa daidai yanda tasan ze iya cinciyewa sannan ta tsiyaya masa ruwa da lemo ta ajiye komai a kan carpet tace ya sakko. Seda ta wanko hannunta a toilet sannan itama ta zauna kamar qaramin yaro haka taringa Feeding nasa da hannunta ya ringa karba kuwa dan rabonsa sa abinci tun daren jiya kafin kace mene har ya cinye ta kuma qara masa wani.
Seda ta tabbatar da ya qoshi sannan tabarshi tana kallonsa fuskarta dauke da murmushi tace
"Ko kai fa Babana amma da ka zauna da yunwa kaganka kuwa yanda duk ka firgice" jinginar da kansa yayi a jikin gadon wata soyayyar Amminsa na qara shigarsa. Tafi kowa damuwa dashi haka tafi kowa saninsa a duniya ita kadai ce take gane abinda yake zuciyarsa a kallo daya batare da ya bude baki yayi mata magana ba.
"Yanzu kaje kayi wanka se ka dan kwanta ka huta in ka fita anjima a samu a dan rage wannan sumar tayi yawa" murmushi yayi yana shafa kansa da gemunsa sannan ya miqe bayan ya rungumeta kadan yace "Thank you Ammi, you are the best" seta shafa kansa itama tace
"Allah yayi maka albarka yaba abinda kake so Babana" binsa tayi da kallo har ya fita daga dakin a zuciyarta tana fatan abubuwa su daidaita, lokaci kadan take jira ta kammala shirinta da kanta zata nemo masa farin cikinta tunda taga shi baze iya ba. Ta rigada ta samu address din gidan dan shine me wahala kuma gobe insha Allahu zataje da kanta ba aike ba.

Kamar yanda tayi alqawari kuwa haka ce ta kasance da safe wurin shadaya ta dauki Little da Faheema yarinyar Saudah Driver ya kaisu Gidan Prof Ammani. Cikin girmamawa da sakin fuska Mumcy ta karbeta dukda bata santa ba. Seda ta cika mata gaba da kayan tande tande da lemuka sannan ta zauna suka gaisa sosai.

"Sedai ban gane ki ba Hajia" ammi ta fada tana wasa da hannun Little data riqeta dan ta ganta Fara kamar Aunt Berbie.
"Eh nasan baki sanni ba Hajia ni yar uwarki ce dan nazo neman arziqi ne gurinku". Cikin rashin fahimta take kallonta kafin tace
"To haka ne amma ban gane abinda kike nufi ba wane abu kike nema haka Hajia?
" Ni sunana Hajia Aisha Matar Yarima Abdullahi Aliyu"
Cikin mamaki Mumcy take kallonta "Yarima Abdullahi dai wanda na sani ko wani daban" ta tambayeta. Se tayi murmushi tace
"Shidai wanda kika sani din" nan da nan Mumcy ta qara Fadada Fara'arta kafin tace
"Sedai kinyi rashin Sa'a Megidan bayanan dazu wurin 7 jirginsu ya daga sun tafi Switzerland na zata ma harda se Yallabai din a tafiyar tasu tunda kamar yace shine ze wakilci Masarautarsu ko"
"Eh hakane amma shi se gobe in Allah ya kaimu ze tafi tukunna sedai zuwan naki ne bana megidanba".
"To ina jinki Allah yasa dai ba laifi mukayi ba"
"Ko kadan Hajia Alfarma dai nazo nema a gurinku ina fata zaku taimakamin" Ammi ta fada tana gyara zamanta dan taji dadin magana.
"Haba Hajia ai babu zancen Alfarma a tsakaninmu, a irin Alkhairan Da Yarima yayiwa Prof Ai bana zaton akwai abinda zaki zo nema a cikin gidansa dai a kasayi muku sedai idan yafi qarfinmu kuma.
Murmushin jin dadi Ammi tayi dab kalama mumcy sun qarfafa mata guiwa sannan ta fara magana.

"Yaron gurina ne me sunan Galadima yaga yarinyar gidan nan yake so, to kinsan halin yaran yanzu da wutar ciki bata barinsu su samu abinda suke so inaga hali yazo daya ita zafi shi zafi dan haka sun kasa fahimtar juna to shi yasa naga gara mu shiga ciki tunda sun kasa daidaita kansu". Farin ciki ne fal ya mamaye zuciyar Mumcy, dukda Hamidah Sulaiman ne dan gidan Kanwarta Anty Mami yake sonta amma tasan ba wata matsala bane zata iya fahimtar da Mamin kuma ita kanta zatayi Na'am da abun saboda Nagartar Yarima Abdullahi da Ahalinsa, dangine da kowa zeso ya hada zuri'a dasu dan ma Allah be bashi Yaya Mazan da yawa ba se mata dan haka tace
"Wannan ai ba komai bane Hajia da Har se kin taso da kanki amma tunda anyi hakan ma babu komai Allah ya tabbatar mana da alkhairi insha Allahu da munyi waya da Abbansu zakiji yanda mukayi tunda yaran suna tare namu kawai tsaida lokacine amma kuwa bata taba gayamin ba yarinyar au kin ganta ma ana maganar ta" ta fada daidai lokacin da Hamidah tayi sallama ta shigo, se Ammi ta waiwaya ta kalleta,
"Granny look at her she looks exacly like Aunt berbie but our berbie is more beautiful than her" Hamdah da tayi sauri ta isa gurin Hamidah ta riqe hannunta tana kallonta ce tayi maganar, murmushi Ammi tayi bayan da ta qaraso ta shiga gaisheta kafin ta samu guri ta zauna dan ta gaji. Surutu Little ta ci gaba daya tana fadar differences din Aunt Berbie da wannan ita ma Ammi kallonta takeyi dan dai kamar wannan tafi wadda take gani a hoto jiki sannan bata kai Hasken Hamdah ba amma bata sani ba ko dan Hoto ne dan haka seta kalli Mumcy take ta faman murmushi a ranta tana godewa Allah akan irin baiwar da yayiwa Yaranta.

"Hajia nace wannan itace Hamdah ko?"
"Aa Hamidah dai ko ai babbar ce Hamdah wannan kuma ita ce qaramar" miqewa Hamidah tayi dan bata san me suke tattaunawa ba ai kuwa little da Faheema suka bita. Seta maida hankalinta sosai kan Mumcy kafin ta ciro wayarta ta nemo hoton Hamdah sannan ta miqa mata wayar
"Kalli kiga wannan nake nufi". Seda ta qarewa hoton Kallo sosai, Hamdah ce seta miqa mata wayar tana cewa
"Wannan Hamdah ce kwarai itace gaba da wannan akwai ma Farouk a tsakaninsu kafin Hamidah"
"Masha Allah itace wadda yake so to". Se mumcy tayi shiru na dan wani lokaci, taya zata fara gaya mata Hamdah tayi aure, dukkan nutsuwarta ta tattaro kafin ta fara magana

"Hajia amma kinsan ita wannan din ta taba aure kuwa?" Gyada mata kai Ammi tayi tace
"Nasani ta auri Marigayi Abdulmalik dan gurin Hajia Fattu Dala ko" Ammi ta bata amsa.
"Kwarai haka ne to Hajia base mun tsaya wani dogon magana ba gaskiya ita wannan yau kwananta biyu kenan da sake daura wani auran jiya ta tare a Kaduna" se Ammi ta bude baki cikin mamaki tana kallonta, ta tabbatar Abdul'ahad bashida wannan labarin dan haka tace
"Ya subhanallahi Hajia Maryam kiyi hakuri dan Allah wallahi bansan da wannan al'amari ba da babu abinda zesa nazo kuma na tabbata shima be sani ba dan da ze gayamin"
"A ba komi Hajia nima kuma nayi mamaki Gaskiya dan ban san ma suna tare dashi ba mene sunansa na gaskiya?"
"Abdul'ahad" ta bata amsa.
"Ikon Allah ko shine yayi lecturing a BUK" Mumcy ya qara tambayarta.
"Kwarai kuwa shine ae tsohon malaminsu ne tun tana budurwa kuwa suke tare". Se mumcy ta girgiza kai cikin tabbatarwa kafin tace
"Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi tabbas nasan shi idan ban manta ba ma shine wanda ta dakkowa mota shekara biyar tana nan a ajiye bezo ya dauka ba, akwai ma kyaututtukansa da yawa da yayi mata duk sunanan anan gidan sedai gaskiya banida labarin ya qara dawo wa nemanta a karo na biyu da ban bar wannan al'amari ya faruba".

"Babu komai Dukkanmu babu wanda ze kaucewa hukuncin Allah shikadai yasan meya boye cikin al'amarin shima din yayi aure wannan qaramar yarinyar yarsa ce kuma sunan ita Hamdah ma ya saka mata Nagode Kwarai Dr Allah yasa hakan shi yafi mana alkahiri zanje in gaya masa yayi haquri Allah ya zaba masa wata"
"Amin Hajia muke da godiya wanda ya nuna yana son naka mun gode kwarai sannan kofar mu a bude take idan har da yuwuwa yana son Yar uwarta". Daga haka ta haura sama dan ta kirawo mata su little. Babbar leda ta cika musu da tarkacen yara irin wadanda take siyawa su Amrah harda turamena atamfofi da riguna yan kanti se Turarukan wuta da kuma kayan gara data zuba mata a bokiti. Sosai Ammi ta ringa godiya haka ta tafi da jimamin yanda Abdul'ahad ze karbi wannan al'amarin, tana fatan ya karbi qaddarar data zo masa da hannu bibbiyu. To her surprise koda ta gaya masa

"Allah yasa hakan shi yafi mana alkhairi" kadai ya fada yana murmushi, da Amin ta amsa masa har zuciyarta taji dadi haka ya tashi ya tafi abinda bata sani ba daurewa kawai yayi, dakyar ya qarasa dakinsa ya kwanta yanda yajeji kamar zeyi hauka. Be taba jin kishin wani abu a rayuwa irin yanzu ba yanzu seda ta auri wannan mutumin, ada ya hakura ko ba komai Abdulmalik baya duniya be kuma bar masa wata sheda da zata sa ya ringa tuna wani ya rigashi saninta ba amma yanzu fa a haka ze aureta wata rana su hadu dashi a matsayin tsohon mijinta.
"Da kake iqirqrin zaka aureta ce maka tayi zata fito ko yaya" zuciyarsa ta kwabeshi, se ya miqe a fusace, cikin akwatin magungunan Ni'ima ya bude ya nemi wanda ya tabbatar ze saka shi bacci yasha dan yaga alama shima ciwon zuciyar yana barazanar kamashi.

*******************************************
*Muleqa Amarya Hamdah*

















🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 3⃣4⃣


Amarya Hamdah ta tare a gidan angonta da yayi matuqar tsaruwa kai da gani kasan an kashe kudi gurin gina shi. Sama da qasa ne matan gidan suna qasa shi kuma me gida a sama sedai kowacce tana da daki a part din nasa. An gwangwaje Amarci kwanaki ukun nan kamar karsu qare a gurin Abdurrahman dan Amaryar ta zarce yanda yai tunani babu sakat ko yaushe yana manne da ita abinda yake qara rura wuta kenan a zuciyar Uwar gida Hajara.

Kwanaki sun fara mikawa Dan gashi har ta share watanni uku cikin gidan Abdurrahman. A cikin wannan lokacib ko sau daya bata taba biyewa Hajara sunyi wani sa'insa ba Dan data fahimci halinta mace ce mai sa ido da tsegumi akan abinda be shafeta ba sannan tana da baqin kishi da neman rigima ta wani bangaren kuma tana da sauqi dan idan akayi katari suka hadu a babban palour data mayar gurin zamanta daga safe har dare dan taji dadin Sa ido wata rana har yar hira suke dan ita Hamdah tafi ganewa zaman daki ko part dinta ka shiga bazaka tarar da ita a plaour ba se in baqi tayi ko ita keda girki to shine zaka sameta a babban kitchen tunda tare suke cin abincin dare gaba dayansu. A bangaren Abdurrahman ko bata da wata matsala dashi Dan tsakani da Allah yake kulawa da ita. A koda yaushe kokarinsa ya kyautata mata Kaman yanda itama take masa, ta fahimci yana da son yan uwa dan hak bata gajiyawa da hidimtawa mahaifiyarsa da kannensa da dukkan wani mutum daya rabeshi abinda yake kara mata kima a idanun yan uwan sa da abokansa kenan Dan su sha banban da Hajara domin ita irin matan nan ne da suka dauki miji kadai zaki kyautatawa duk wani bayansa to banzane koda yake mijin ma se a hankali Ai.

Shigarta wata na hudu da Aure sabon shafin KADDARAR ta ya kara budewa. Wata safiyar Lahadi ta tashi da zazzabi tareda ciwon kai kasancewar Yana gida ya sakashi saurin daukarta suka tafi asibiti ganin yanda ta galabaita lokaci daya. Suna zaune a office din likitan daya kasance abokinsa tare sukayi karatu shi yayi specializing a bangaren Psychiatry ko zama sosai bata iyayi seda ya jinginata da jikinsa tukunna. Tambayoyi yake yi mata akan yanayin da takeji tana bashi amsa. "When last did you see your period" Dr Hafiz din ya tambayeta lokaci daya zuciyarta ta shiga bugawa, idan bata bata lissafi rabonta da period tun tana sati biyu a gidan yanzu wata uku da kwanaki kenan cikin rawar murya ta gaya masa. kwalba ya bata yace tashiga toilet tayi fitsari ta kawo masa, karba tayi ta shiga bayan yan mintina ta fito ta bashi, jininta ya dauka sannan ya saka ta kwanta a gadon da yake duba marasa lafiya ya

Please Login or Register in order to submit comment