Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaishi bango." I'm 17" ta bashi amsa. Hawaye na taruwa a idonta. "No wonder she is like this dan mutum me cikakken hankali bazeyi abinda takeyiba" ya raya hakan a zuciyarsa.
"And what about my car?"
"Ur car?"
"Yes or u want to fool me again"
"Oh sorry tana gida you can come and carry it when you are ready".
Dukka idonsa ya bude akanta yana kallonta gaba daya ta dinke masa kwakwalwa in banda Hmmm babu abinda ya iya cewa kafin ya nemi guri ya zauna. "Saboda ni na kaita Gidan naku?" dakyar ya furta maganar yana relaxing akan kujerar sa. Bata amsa ba daman be saka rai da zata amasa masa ba dan haka ya ci gaba "return it to where you took it inkinga dama kuma ko ki rike Danni ba tsiyar mota nakeyiba". Yana kaiwa nan ya Shiga tattara system dinsa da wasu takaddu yayi waje ya barta a tsaye a wurin yana jin lokacin data fashe da kukan daya fi kama dana takaici. "Kudos" ya fada yana murmushi ko ba komai tayi kuka ya rama abinda tayi masa.
Ina wuta HAMDAH ta jefa GURU, kuka Take kamar wadda ya daka, wato itace take tsiyar mota? Ai dai ya gani ba a kasa take yawo ba bare ya gaya mata wannan maganar. Su Maryam dake tsaye a waje suna saurarinsu tsab sukayi saurin shiga bayan fitar sa. Dakyar suka lallasheta "kinga abinda nake gaya miki ko gashinan yanzu kinja ya gaya miki magana kuma kiyi addu'a tunda yayi marking face dinki Allah ya raba ku kawae. Gida tawuce Dan batajin zata iya saurarar wata lecture again Wanda ko a gidan bawanda ya kulata illah khaleefa daya bita ya karbi key din motar Guru don ya cire Battery gudun samun matsala Dan wannan bashine karo na farko ba datayo awon gaba da motar mutane sedai babu wacce ta taba kwana. Tundaga wannan rana bata qara bari koda ido sun hada dashi ba, ko lecture yake zata kifa kanta a desk ne daya fahimci haka shima se ya tattarata ya watsar dan tana nema ta ja masa raini a gurin sauran Daliban ajin.
©️2⃣0⃣2⃣0⃣




🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 0⃣3⃣

Kwanci tashi ba wuya gurin Allah se gashi suna shirin fara first semester exam, sosai take karatu Dan duk fitinar Hamdah akwaita da gane karatu son boko a jininta Yake gashi kuma Allah ya mata kwakwalwa dan Haka take zuba sharafinta.
Cikin lokacin abubuwa da dama sun faru tsakani ta da Dr AA (Guru) Dan ayanzu sun zama tamkar annabi da kafiri, Sosai yake matsa mata kiris yake jira tayi badai daiba ya dizgata haka itama batayin kasa a gwuiwa wurin baje masa kolin tata fitsarar.
Dawowarta kenan daga school a matukar gajiye ga paper da sukayi tadan so tayi wahala, ita kadai taketa kalan fadanta akayi sa'a ba Wanda ya kulata dama Hamida ke biye mata suyi tayi Kaman kaji (Inji junior ). Da masifai ta dauko wayarta data isheta da kara tuntuni "wannan ko mayene ai se haka kayita kira ba'a daukaba sekace dole babban abin haushima anyi hiding Number mtsw" taja wani dogon tsaki. "Kyaji da jarabarki ke kadai tunda kullum bakida aikinyi se masifa" cewar khaleefa.
Rike qugu tayi tana kallon Khaleefa daya dauke kai kamar bashi yayi maganar ba tace "Lallaima yaronnan ni sa'ar kace ko da kai nake ehe dazaka kulani Ina ruwan mutum da mutum in ba abinba". Kedai kika sani dama inba Abdulmalik dinba waze iya da masifarki shima din Allah yasa ba lambo yamikiba se kinshiga ya moreki wallahi". Abincinsa ya dauka ya nufi kofa dan yasan bata gajiya yanzu seta haramta madmsa cin abincin yana jinta tana cewa "Ji banza tunda ance maka dolone irinka ko eh na maji din ahakan dai yagani yanaso". Fasa fitar yayi ya dawo suka cigaba da caccakar juna har wayar ta tsinke "wlh sena ci uban duk Wanda yakara mana magana anan tunda bakuda aikinyi" Yah Farouk ya katsesu.
Ta gefen ido ta harareshi Dan duk iskancinta tana shakkarsa dukda kasancewa shi take bimawa. Baya daukan wargi ko kadan Dan bata manta lokacin da suna secondary school intai neman tsokanarta haka ze rubuta ya hukunta ta dallah dallah shiyasa take shiga taitayinta. Dakinta ta wuce tareda kwanciya takira Habibinta suka fara soyewa. Number dazu ce dai aketa nacin kiranta da ita "Baby please bari na answer call dinnan tun dazu ake kirana da Number kuma bansan waye ba". "Ok dear I will be expecting your call". katse kiran nasa tayi sedai kafin ta kaiga answer wa har Wancan kiran ta katse, tsaki kawai tayi ta Mike dan gabatarda sallar Magariba da ake ta kira.
**************
Abdul-ahad ne kwance kan katafaren gadonsa daya sha shimfidu na alfarma, gefensa Babban amininsa ne Fahad da waya a hannunsa yanata faman dannawa "Hey dude wai mekake yimin da wayane since I told you I want to make a call". Kallon Abdul'ad Fahad yayi kafin ya goge call log ya mika masa wayar "Gashi dama I wanted calling one number ne". "You must be mad waya ce kakira wannan number" number wa ka kiramin da waya" yafada yana kafe abokinnasa da ido. Kusada shi Fahad ya dawo tareda dafashi "Hey relax Bafa wata na kira ba HAMDAH AMMANI ce" wani kallon zaka ci ubanka AA ya masa batare da yace komai ba. "Abdul'Ahad its a high time for you to understand your feelings we are not getting younger Girma muke so stop acting like a small boy be bold enough to face her and express your feelings to her kasan ance The Sooner the Better".
Shiru yayi for some time kamar ba zeyi magana ba sannan yace "No not yet she is still young banasan shirme kasani" ......."Ok then you wait till she grow up Allah ya taimaka "Fahad ya fada yana nufar Toilet din dake Manne da dakin. Sake kwanciya Abdul'Ahad yayi yana tuna maganganun Abokinnasa "ofcourse yagirma koda ba a shekaruba (he is 28) Amma yayi achieving abubuwa da dama arayuwarsa tunda a kananun shekaru irinnasa ya taka matakin PhD, more over zancen Hajiyarsa kanan kullum aurensa kasancewarsa da namiji tilo da Allah ya azurta iyayensa dashi ko ba komai tana so taga jikoki ta bangaren Abdul dinnata.
Murmushi yayi tunawa da halin mutuniyar yasan ayanda suke wannan takun sakar bakaramin kai ruwa rana zasuyiba."Wai ma dukda kake wannan tunani Kaman ance maka kai take jira kasani ko ta tsayar da miji?" Zuciyarsa ce ta raya masa hakan.da karfi ya furta "No it can't be she is mine" Nan take idonsa yakada yai jajir tsabar bala'in kishi dayake cinsa. Fahad dake gyara hannun rigarsa ya kalleshi kawai tareda girgiza kai Dan Lamarin na AA sai du'ai dan kuwa yana neman zaucewa kan macen da bata san ma yanayiba "Allah ya kawo sauki "yace tareda ficewa daga dakin. Dole shima ya mike yayo alwala sannan yanufi Masallacin dake cikin gidan nasu, har akayi Sallar isha suna zaune daga shi har Fahad babu wanda ya sake yiwa wani magana se bayan da suka idar da Sallah suka fita a Motar AA din. Still dae akan Hamdah yake ta masa magana yana nuna masa akan ya kamata tasan halin da yake ciki yana guje masa abin da ze iya zuwa ya dawo "Man did i tell you that I'm in love with this girl or what duk ka bi ka ishe ni da zancenta" baki bude Fahad yake kallonsa dan ya bala'in goge masa Hadda " Kai Alhamdulillah amma naji dadi dan wallahi dama tunda ka nunamin picture dinta naji kawae wata kibiya ta soki zuciyata dama na hakura ne saboda kana sonta amma yanzu tunda kace ba haka bane dan bani numberta I want to shoot my shot......." wawan birkin da AA ya taka ne yasaka Fahad yin shiru se innalillahi da yake ta maimaitawa, Allah ne ya rufa asiri basu daki motar gabansu ba. Be gama dawowa daga shock dinba yai parking a gefen titi cikin muryar dake nuna matukar bacin rai ya kalli Fahad din yace "Get out from my car".
Tsabar mamaki Fahad se ido kawae tsawar daya buga masa ce ta saka shi bude motar babu shiri dan yasan in ran abokin nasa ya baci to se Allah kawae yana fita kuwa ya zaburi motar a 360 ya bar Fahad kamar Gunkin da aka sassaka. "to me na masa da yayi zafi haka bashi yace baya sonta ba fisabilillahi" daga kafada yayi kafin ya tari Napep ya koma Gidansu AA ya dakko motarsa.
Yau kam farin ciki takeyi sosai kasancewar zasu gama exam ga kuma dawowar Habibinta datake saka rai a gobe. Cike da Fara'a take komai har ta manta da bacin ran Fadan da Mumcy tagama yi mata akan Motar da tun Farkon semester take a gidan. Genetics paper ne dasu A qarshe dan haka dole ta nutsu tayi karatu sosai dukda ta yarda da kanta a wannan fannin amma kodan gujewa wulakacin Guru Dole ta bashi mamaki. 9am zasu shiga exam din amma tun 7:30 tana cikin school din. A wani dan garden suka zauna tana kara yiwa su Aysha explanation kan abinda ya shiga musu duhu kafin su shiga Sedae karatu yayi dadi har basusan 9 tayi ba har anshiga an zazzauna A exam hall din.
Afeeya ce ta rafka salati lokacin da ta duba agogon wayarta tareda cewa "mun shiga uku yau shikenan duk karatun mu yatashi abanza". Aysha data kasan ce rudaddiya irin Afeeyan tuni idonta har ya kawo kwalla tace "kardai kicemin mun makara". "Ae Se ku tashi mu tafi kun tsaya surutu in kuma nan za'a biyo mu da Paper se naji "cewar Maryam. Sauri sauri suka karasa venue wanda tuni har an fara raba answer booklet ba shiri suka fada ajin banda Hamdah dake kokarin Ciro exam card dinta daga cikin jaka. A nutse tanufi kofar Bayan data dakki duk abinda take buqata tayi bismillah ta shiga. harta kai tsakiyar ajin tajiyo muryarsa cikin sanyi Kaman koda yaushe yace mata "Get out".
A farko batayi tunanin da ita yake ba hakan yasaka ta cigaba da tafiyarta takalmin kafanta nabada sound me daukan hankali." I said get out" Ya qara maimaita mata. Wannan karon tagane da ita yake Dan kuwa kallonta yake cikin ido lokacin da yake maganar. Iya kacin muzanta tayi wai yau ita Hamdah lecturer ke kora daga aji, hakan bakaramin dadi yayiwa yammata masu kishi da ita ba yayinda ragowar basuji dadin hakan ba musamman masu bin chain dinta (expo). Kallonsa tayi da Grey eyes dinta dake fitar da wani irin glam sakomakon kwallar data taru aciki sannan tajuya cikin sassarfa tabar masa ajin bata ko saurari prof Ndams dake tsayar da ita ba.
Jikin sa ne yayi sanyi dan Kwata kwata ba haka ya soba, so yayi ta tsaya ta rokeshi sannan yabarta ta zauna Amma yanzu gashi ta tafi. Basarwa yayi yacigaba da raba booklet amma dukka hankalisa baya tareda shi kwata kwata. Duk yanda yaso jurewa yakasa musamman inya tuno kwallar daya gani a idonta. waje yafito yana faman kalle kalle sedai ko alamarta babu. Hakura yayi da nemanta kuma baze iya tambaya ko an ganta ba dan haka kawae ya nufi Office dinshi dan bayajin ze iya ci gaba da invigilation din. shashshekar kuka yaringa jiyowa kusa da office dinsa, da sauri yadawo da baya ita dince kuwa. Kasa daurewa yayi ji yakeyi tamkar ana yayyafa masa ruwan zafi a kirji duk sanda hawayenta ya diga, samun kansa kawai yayi da durkusawa agabanta tareda kamo hannunta yace "I'm sorry HABBAH...."se kuma yai saurin mikewa cikin dabarbarcewa Dan maganar subuce masa tayi. Cikin dakiya irinta gogaggun Maza ya kalleta tareda cewa" Get in side " yayi gaba abinsa.Ta gane inda yake nufi Dan haka ta rakashi da Harara Kaman idonta zasu fado sannan taja tsaki tace "inbika kamin uwar me mugu Azzalumi wallahi se Allah ya sakamin in har nafadi course dinnan".
Dukda cikin kunkuni tayi maganar Amma tsaf ya jita Dan Allah yayi shi da ji."Karki tashi ki kuma bari nashiga na fito kiga meze biyo baya". "Eh seka fito ka daukeni ubana". Murmushi kawai yayi yasa kansa cikin office din. Ta Lula cikin duniyar tunani batayi auneba se kawai jitayi anyi Sama da ita, baki ta bude da niyyar yin ihu sedai bata samun daman haka ba Dan tuni yayi locking bakinta da nashi.
Rawa jikinta yakeyi tsabar kidima Allah ma yasa ba Wanda ya gansu makarantar tayi tsit kusan kowa na Exam. "Karamar mara kunya kawai kiyi Maza 1hour na baki kigama" ya fada dai-dai lokacin daya direta kan kujerarsa yai saurin ficewa, muryarsa kadae ta isa ta shaida maka da matukar karfin halin da yayi wurin hado kan kalmomin da yayi amfani dasu. She was just motionless and speechless kallo ta bishi dashi harya fita daga office din sannan ta kalli paper daya ajiye mata, kwakwalwarta ta cushe dayawa bata da damar yin wani tunani yanzu "he just kissed me?" ta tambayi kanta. "No he only prevent me from shouting at him" ta kuma bawa kanta amsa a lokaci daya. "But...."katse tunanin tayi tareda lasar lip dinta,This her first time of being kissed by some one duk irin soyayyar da suke da Abdulmalik hakan betaba shiga tsakaninsuba it only stops at hug or peck shikenan amma she don't know why instead of taji haushi sekawai ta tabe baki tareda daukan biro tafara rubutunta.
Sosai tayi mata dadi cikin mintina kadan ta gama, mikewa tayi da niyyar fita sedai me jin kofar tayi a kulle wato kulleta ma yayi a ciki kenan, sababbin hawaye ne suka zubo mata to uwar me zata masa da ze kama ya qulleta a office dinsa indae ba salon mugunta ba. Dole ta koma da baya resting chair ta hango daga gefe dan haka tanufi wurin, farar suit dinsa daya ajiye ta dauka ta shaki daddadan Kamshin turaren dake jiki, arayuwarta tana son kamshi dan haka kawai ta tsinci kanta da rungume rigar har bacci yayi gaba da ita batareda ta saniba.
Shigowarsa kenan ya tarar da ita tana baccin "Rigimammiyar kawai" ya fada afili yana janyo booklet din. "HAMDAH AHMAD AMMANI" ya gani a rubuce."Nice name just like the bearer". Ganin baccin na mata dadi yasa be tasheta ba illah rage mata karfin A.C. dayayi ganin yanda tadan takure akan kujeran sannan ya gyara mata rikon datayiwa coat din ta hanyar lulluba mata. fuskarta yake kallo da hannunta kasancewa rigar da tasaka me gajeran hannu ce. Befiya son farar fata ba Amma kalar haskenta ya tafi da imaninsa. Ganin yana neman shagala da kallonta yasashi saurin mikewa tareda cigaba da aikinsa. Tadauki kusan 1h tana baccin sannan ta farka. Idanunta suka sauka akan Dr AA dake danne danne cikin Apple laptop dinsa idonsa sanye da siririn farin medical eye glass. Ransa a hade se yadawo mata sak Guru da ta sani dan haka ta adana fitsarar da tayi niyyar zana masa illah harara ta watsa masa ta kasan ido. To her suprise se jitayi yace "ubanwa kike harara mara kunyar banza kawai". Bata kulashiba illah tashi data fara kokarin yi, Jakarta ta hango gefe wadda batasan waya kawo taba itadae bata kulashiba ta dauka "Are you Prof Ammani's daughter?" Ya tambayeta, "ka buga a labaran yau a tambayo maka" ta bashi amsa Sannan tayi waje Abinta. Se kawae ya tsinci kansa dayin dariya, yarinya kamar me aljanu ikon Allah.
Koda ta fito Babu Wanda ta kula dukda yanda coursemates dinnata ke ta kiranta Dan tazo sudauki hotuna kasancewar SIWES zasu tafi se bayan six month zasu dawo school Amman bata kula ba Dan ko su Afeeya bata nemaba ta karawa motarta wuta.
Abdul'Ahad kuwa bayan fitarta Daga office din zare glass Idonsa yayi yadaga kansa yana shakar daddadan kanshin da office din keyi sakomakon haduwar turarensa da nata, shi kadai yake murmushi Yake kamar wawa aransa yana tuna how soft her lips were. Dukda bawai yayi daniyya bane Aa sedan gudun karta tara masa mutane Amma jiyayi inama su dawwama a hakan" Yah Allah let her be my wife she is the perfect match for me". Tashi kawai yayi shima ya fita Dan gaba daya jiyayi office din yamasa girma da yawa. Sedae ko qurar Motarta be gani ba. Dafe kansa yayi yana tuna shawarar da Fahad ya bashi jiya bayan yaje ya bashi hakuri, yace masa ya nemi sabo da ita first ya dena takalarta fada "to ae yarinuarce bata da kunya ta fiya tsiwa" ya raya a zuciyarsa se kawae ya dauki motarsa if He is not mistaken gidan Prof Ammani anan cikin Tudun-yola yake.
Har kofar gidan aka nuna masa da taimakon wasu masu shaguna a bakin titi. Megadinsu ya tarar a zaune da wani dayake kyautata zato me yankan flower ne daga irin Scissors din dayake hannunsa. Hannu ya mika musu sukayi musabaha sannan ya tambayesu "Dan Allah ko Hamdah tana ciki?" cike da Fara'a megadin ya amsa masa "Eh ranka ya dade tana nan yanzun nan ma ta shiga kamar tare kuke bari ayi mata magana wa za'a ce mata". Mamakin surutu irin na Me gadin yakeyi da har ya mike dan zuwa kiran Hamdah se yai saurin dakatar dashi ta hanyar cewa "No yanzu lokaci ya qure zan dawo later" hannu yasa a aljihu ya ciro kudi masu yawa ya mika masa su raba, godiya suka ringayi masa sosai ya shiga motarsa ya bar gurin.
Idonta ne yake mata gizo a cewarta, motar Sir Guru ta hango ta bar kofar gidansu "in banda ke meze kawo shi gidan nan kuma inshine ae gurinki yazo da an aiko kiranki" zuciyarta ta raya mata hakan. Window kawae taja ta tufe kafin ta cire kayan jikinta ta kure sanyin Ac, kamar yarinya tayi tsalle ta dane gadon tana cewa "Finally some one is going to be free from studies for good 10 months"
2⃣0⃣2⃣0⃣


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 0⃣4⃣

Hankalin HAMDAH ya kwanta yanzu bata da Aikin daya wuce bacci se dan abinda ba'a rasaba. Tayi wani kyau na musamman dagani hutu ya zauna mata. Tuni ta watsar da lamarin wani Guru dan dama bawai ya dada ta da kasa bane kuma tun ranar dasuka gama exams bata sake ganinsa ba gara ma last week dataje submitting acceptance letter dinta ta IT taga motarsa a parking space din department dinsu. Bata da wata damuwa yanzu musamman ga Abdulmalik ya dawo Sabon babin soyayya suka bude babu kama hannun yaro. Sedai ba kamar Sauran lokuta ba Abdulmalik dagaske yake akan lamarin auran Hamdah. Tun farkon Haduwarsu da aure yazo wurinta amma seta kawo masa uzurin tafiso seta gama school tukunna, be matsa mata ba saboda shima din bawai he is all ready bane ba Aa kawai yana gudun rasata ne.
Lokaci da dama yakanyi tunani akan makomar soyayyarsu wadda haryanzun bata samu cikakkiyar karbuwa ba a gurin nasa Iyayen amma ya daukarwa kansa alkawarin ko duniya zata hadu babu wanda ya isa ya raba shi da Hamdah itace rayuwarsa.
Karfe 4pm Ranar tayi masa a gidansu Hamdah yayi kwalliya ta burgewa cikin wata hadaddiyar shadda dinkin Half Jamfa dark blue yau harda hula ya saka, Tabbas babu karya Abdulmalik ya hadu. Yana da kyau gashi dan gayu ajin karshe, murmushinsa kadai ya isa ya narkar da zuciyar dukka wata Mace da tayi arba dashi. Abdulmalik irin mazan nan ne masu Fara'a sosai, yanada matukarckirki abinda yake qara saka mutane sonsa kenan. Be dauki kansa da nisa, yanada matukar mu'amala me kyau ko acikin Yan uwansa maza. A Kasan rumfar Bunu dake gefen Cikin Babbar farfajiyar gidan Yazauna, kafarsa daya kan daya kafatanin hankalinsa nakan Main Entrance na Palour daga inda yasan Mutuniyar tasa zata fito. Cikin takunta me daukar hankali seka rantse tana sane take rausaya in tana tafiyar amma ko daya kawai halitta ce da Allah yayi mata. Riga da Skirt ne a jikinta na Lace Kalar sararin samaniya ta yafa siririn farin Veil a kafadarta Babu ko digon kwalliya a fuskarta inka cire chappet data shafawa lips dinta wanda ko kusa baa ganin kyallinsa. seta zama kamar wata Flower, kallonta yake a zuciyarsa yana qara godewa Allah akan irin zaben da yayi, yasani cikin mata dari babu kamar Hamdah she is just Unique. Salon gayunta daban ne Shi da kansa yasan yana da kwashe kwashen Yammata amma betaba haduwa da Mace me kwarjini da zati kamar taba. She is just different in her own ways haka ya dulmiya cikin duniyar wasikar Jaki, already yana hango ta a matsayin matarsa wai har ga Yarinya ta haifa masa me kama da ita..... Clapping Hannunta tayi akan fuskarsa abinda ya dawo dashi daga tunanin kenan.
"Hamdah Dan Allah Karki rabu dani wallahi mutuwa zanyi inna rasaki". Yanda yai maganar seya bata tausayi kamar wani maraya daya ke shirin rasa ragowar gatansa dan haka seta ja kujera ta zauna a gefensa. Jug din dake dauke da Favourite Lemon Juice dinsa ta jawo ta tsiyaya takai masa baki. Kamar dolo yaringa kurbar lemon yana kallon kyakykyawar fuskarta Har ya shanye.
"Babe Marry me" ya fada kalmomin a rarrabe
"Wallahi i love you with all my heart Kullum se nayi mafarkin munyi aure I'm afraid kar wani yazo ya dauke min ke......" hannu ta dora akan light pink lips dinsa tana kallonsa a cikin ido tace "God forbid bad thing hakan ma baze taba faruwa ba Insha Allah ni takace we are made to be pairs so kabarma wani tunani".
"But when?" ya tambayeta. "trust me JAAN" tabashi amsa.
"As you said my lady Allah ya mallakamin ke bansan irin murnar dazanyiba "yakarasa yana shafa fuskarta. Fari tayi masa daya kusan juya kwakwalwarsa sannan tace "I shall be yours Insha Allah dear karka damu zaka sameni yanda kake so". Hirar su suka cigaba dayi harzuwa wani lokaci kafin yamata sallama yatafi Saboda Magriba tayi.
Acikin satin tafara IT dinta nan cikin asibitin Malam Aminu kano (AKTH), Abdulmalik ke kaita kullum sannan in ta tashi ya dakkota. A cikin dan lokacin suka qara shaquwa da fahimtar juna, sun ruga da sun yardarwa kansu bazasu iya rayuwa babu junansu ba. Kawae cikar lokaci suke jira na tabbatuwar burukansu na mallakar Juna. Sauda yawa in bashi da abinyi a gida ze tafi asibitin ya zauna ya jirata in kuma tana da less aiki haka zasuyita zagaye asibitin suna hirar su tunda be riga yayi resuming aiki ba.
******************************
A bangaren Abdul'ahad kuwa tunda ga ranar dasuka gama exam be sake sakata a idonsa ba. Ya damu kwarai har wani Lokacin yana Ji kaman yaje gidansu ya ganta amma se zuciyarsa ta kwabeshi da ba yanzu ba. Kasancewar hutun da aka bada na makaranta ba meyawa bane two weeks ne kadae yai matukar daurewa acewarsa nan da sati biyu zata dawo ya cigaba da troubling nata Se daga baya ne ma yakejin labarin ai suna SIWES, Ai kuwa sosai yaji haushin hakan dan ko bakomai ganinta na rage masa abubuwan daya keji Akanta amma dukda haka be shirya bayyana mata kansa ba yanzu "Lokacin zezo amma bayanzu ba" zuciyarsa take gaya masa. Haka rayuwa taci gaba musu da tafiya.
5 months leave
A cikin wata Biyar da fara IT dinsu abubuwa dayawa sun faru ta kowanne bangare, soyayyar Hamdah da Abdulmalik, son masi wani da Abdul'ahad yakeyi ga kuma IT dinta daya fara nisa dan har an fara zuwar musu supervision. Suna tafe ita da Maryam dawowarsu daga kasuwa kasancewar bikin Maryam din saura sati daya Ya rage, seka rantse Hamdah ce Amaryar yanda ta kacame cikin hidimar biki. Maryam Kawarta ce tun ta Yarinta Iyayensu Abokai ne sannan tare suke makaranta tun daga Junior secondary har yanzu da suke University. Akwai shaquwa sosai a tsakaninsu sannan tasu tazo daya dadin da dawa unguwarsu daya dan haka kusan koda yaushe daya tana gidansu daya. hira sukeyi harta kai su inda Maryam din ke cemata "kinji wai Guru ne zezo mana supervision ko". Da karfi zuciyarta ta buga Wanda batasan dalilin hakan, tsakani da Allah tamanta da wani mutum me suna Guru ita. Ta rasa dalilin da ya saka aduk lokacin da aka ambaci sunansa se zuciyarta ta buga da karfi, se tayi shiru bata bawa Maryam amsa ba. Maryam data lura da sauyin yanayin lokaci daya ta kalleta cike da kulawa tace "yadai Hamdah

Please Login or Register in order to submit comment