Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rufuwa saboda Riga da skirt tasa yadan kamata haka yasa cikin jikinta fitowa. Suna hada ido dashi ta dauke kanta dan bata qaunat ganinsa ko kadan, shima a nasa bangaren ganin cikin yake kamar wani baqin kumurci dukda kyan da yayi mata shifa be hango ma kansa ya karbi cikinnan ba. Haka suka musu sallama shikansa Abban daurewa kawae yayi Amma har zuciyarsa gani yake kaman baiyi mata adalciba na rashin sauraron nata bangaren, haka suka kama hanyar kaduna bakin hajia bai rabu da saka mata albarka tareda yaba karamci irin na iayayenta ba har suka shiga garin kaduna.

*************

Abdul'ahad Abdullahi Galadima ne ya fito daga Conference Hall, hannunsa na dama dauke da laptop kirar kamfanin Apple a dayan hannun kuma wayace yake daddan nawa alamar kira zeyi.
"Barka da rana Ammi" yafada har yana Dan sunkuyawa alamar girmamawa Kaman yana gabanta

"Rana ko dare Babana ai mu yanzu karfe goma harta gota lafiya dai koh" ta amsa shi
"Oh namanta ne wallahi Dan mu nan shabiyun rana naga missed call dinki lokacin ina wanka tun bayanda na fito kuma inata ayyuka Se yanzu na samu saukinsu".

"Allah sarki to Allah ya taimaka dama najika shiru kwana biyu ne shi yasa na kira naji ko lafiya to Alhamdulillah tunda komai kalau" haka suka ci gaba da magana a zuciyar sa Addua yakeyi Allah yasa kartayi masa tambayar da baya so bai karasa tunanin ba yajiyo muryarta tana cewa "Babana wai yaushe zaka dawo ne na gaji da wannan saka ranar da kakeyi daga tafiya sati biyu ka share wata kusan hudu"

kansa ya dafe a ransa yace daya kenan a fili kuwa cewa yayi "Insha Allah Ammi very soon zan dawo Akwai shirye shiryen dana keyine inaso Dana dawo in cika miki burinki in qara aure"
Tuni ta washe baki ta hau murna Wanda har ya gane hakan daga muryarta "Allah ya nuna mana dakuwa ka gama min komai ita kanta matarka hankalinta ze kwanta dan kullum zancenta kenan ni har tausayi take bani wallahi badan ciwo ba da Kagama Sa'ar mata kaidai a rayuwa Dan Ayanzu banida wani buri daya wuce inga tarin jikoki na ta bangatenka ABDUL'AHAD Allah ya tabbatar da Alkari"

"Amin Ammi" ya amsa mata sannan sukayi sallama shidai yasan ya fada mata hakanne kawai Dan taji dadi bawai zeyiba Dan anan kusa bashida plan din komawa Nigeria, shirye shiryen yanda Ni'imah da Little ma zasu biyo shi yakeyi bai saniba ko a gaba kadan. Tafiya ya ci gaba dayi har ya karaso wani garden karami inda yawancin mata dalibai na makarantar masu goyo suke zama da yayansu idan babu lecture
"HAMDAH " yajiyo wata mata daga bayansa tana fada. A figice ya juya zuciyarsa na bugawa da sauri a ransa yana fata Allah yasa itace sedai koda ya juya wata yar yarinya yagani fara dagani ta hada jinsi da larabawa ko indiawa kodan yanayin mamanta dake yi mata wasa tana kara kiran sunanta HAMDAH love. Lokaci daya komai ya sake dawo masa, yayi kokari ya goge wannan memoryn daga kansa sai gashi yana dawo masa tamakar wanda akeyiwa restore.

Ya dade da goge babin soyayyata rayuwarsa ya yarda zuciyarsa Dan mace daya akayita kuma ya rasata Dan haka bashi da wani shiri akan kara karbar wata. Dukda yayi nisa da kowa da komai nasa daya danganci kasarsa ta haihu inda cikon farin cikin nasa take yadai samu rangwamen kashi 40% cikin dari a dole yabar london zuwa China dan gujewa abokansa dasuka san tarihin soyayyar tasa da suke dakon jiran ya dawo tare da Hamdah kamar yanda ya musu alqawari. dukda yasha wahala kafin kuma ya dangana yaci gaba da har kokinsa. A hankali ya dauke idonsa daga kan yarinyar yaci gaba da tafiya saima ya juya da baya kawai Dan yasan koyaje in da zashin baze iya aikata komai ba saboda tunaninta daya addabeshi.

***********************

Seda Hajia ta raka su har gida ta qara da musu nasiha sosai sannan ta tafi. Hajara taji dadin dawowarta dan dan sabon da sukayi kafin ta tafi tayi kewarta. Tayi tunanin chanzawar al'amura bayan ta dawo amma ina sema qara lalacewa da sukayi. Tun daga wannan rana Gaba daya rayuwar gidan tayi mata kunci ga kuma azabar laulayi datake fama dashi. Akullum ta Allah se sunyi tashin hankali dashi Dan be haqura ba har gida ya qara dauko wani likitan daban da zeyi aikin Amma taki yarda dama tuni ta dena yarda dashi bare abinda yafito daga hannunsa. Duk wannan zama da sukeyi babu wanda ya sani Dan bata fada ba haka shima to ta Ina ma ze fara fadar wannan ta'asa.

Kaman yanda Anty zahra ta saba takan turo mata su Amrah duk qarshen wata wani lokacin ma anan sukeyin weekend wannan watan ma sunzo. Dukda kasancewarsu yara Amma seda suka fahimci akwai matsala tsakanin Antyn tasu da Abokin Daddynsu dan haka da suka koma gida Afrah data fi yar uwarta kaifin hankali da lura, suna zaune bayan sun gama nuna mata kayan da Hamadah ta basu harma da Hajara dan wannan karan tayi abin arziqi ta basu 10k wai su siya sweet ta fara gaya mata
"Ummy, Mamy fa bata da lafiya kuma kin san me se uncle yai tayi mata fada kuma fa ita ma cikinta yayi babba kaman naki" se tayi shiru tana karantar yanayin yarinyar, tabbas itama ba tun yauba ta fahimci kamar Hamdan tana da damuwa. Dukda sun kwana biyu basu hadu ba ta fara shanshano matsalar tun lokacin da Aka ce taje gida tayi kwanaki kuma Kwana biyu Hamdah ita ma bataje mata ba haka bata ko kiranta a waya yanda suka saba to Shima Abdurrahman din ya dade beje ko gurin Abban su Amrah. Da wannan tunanin ta kwana washe gari kuwa da sassafe tana kai Yara makaranta ta wuce gidan yar uwar tata maganar cikin da Afrah tace tana dashi ya tsaya mata a rai.

Tun kafin ta shiga cikin dakin ta ke jiyo irin bala'in dayake surfa mata hade da cin mutunci, kalmar shi be shirya wahal tawa kowanne shegen Da ba dan haka tunda ta nace seta haifa to ga guri nan Amma karta kuskura ta alakantashi da cikinta ba shiri ta afka cikin dakin cikin tsananin tashin hankali. Abinda ta gani shi ya qara firgita ta, Hamdah na durqushe a kofar toilet cikin Aman da tayi shikuma yana zaune kan gado kamar da kudinsa aka siya yana tijara, bata ko bi ta kan saba ta karasa gurin yar uwar tata tana mata sannu ta shiga qoqarin dagata bata damu da Aman dake jikinta ba.

Ko kadan beyi tsammanin zuwan kowa ba duba da lokaci, kamar kazar da aka tsoma a ruwan zafi haka ya miqe yana kame kame ya kasa koda kallonta Dan wata muguwar kunya ce ta kamashi Kaman ya nutse a gurin haka ya ringa ji. Duk da haka be haqura ba se ya fara kame kame

"Sannu Bae bari na taimaka miki ki gyara jikinki wallahi amai take tayi na bari ne ta gama sena wanke mata gaba daya" ya nufeta da niyyar dagata. Hannu Zahra ta daga masa tana jifansa da mugun kallo tace
"Bata bukatar taimakon ka muda muka damu da lafiyarta muke son cikin jikinta zamuyi mata komai" sum sum ya juya ya fice daga dakin.
Ita ta taimaka mata tayi wanka ta hada mata tea me kauri tasha sannan ta kwantar da ita kanta akan cinyarta wani irin tausayin kanwar tata ke shigarta. Cikin kuka Hamdah tashiga bata labarin abinda ya faru

"Anty wai seya zubar min da ciki Abdurrahman bashida tausayi. Abinda akan rashinsa na fuskanci wulakanci da cin zarafi rashinsa ya jefani cikin halin da nake ciki a yanzu da ban aure shi ba, akan sa na Rasa Abdul dina sannan yanzu na samu a rabani dashi.....Anty Abdurrahman baya sona tunda bayason haihuwa dani....." Kuka takeyi dagaske dole ta baka tausayi wannan wace irin KADDARAH ce take bibiyarta haka acan an qita saboda bata haihuba anan kuma saboda zata haihun, ita ma Zahra kuka takeyi babu mai rarrashin wani a cikinsu, dakyar tayi shiru ta shiga bata haquri. A gidan ta wunar mata tana kwantar mata da hankali sai dare Abbansu Amrah data kira yazo gidan. Kallo daya yayiwa matar tasa yasan ba kalau ba bai kai ga tambayarta ba cikin kuka tashiga labarta masa duk abinda ya faru da Wanda ta gani.

Hankali tashe yake maimaita Kalmar Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wannan wace irin masifa ce haka, ashe haka Abdurrahman yake yasa ya wuce masa gaba aka bashi aure a gidan surikansa da suke ganinsa da mutunci wannan ai shi ya shafawa kashin kaji, shi wanne ibtila'ine ya fada masa ma Ace wasu na neman haihuwa da kudinsu shi ya samu ya ki Allah dai ya kyauta. Haka yaringa bata hakuri kamar, roqonsu ya ringayi akan karsu sanarwa kowa a gida insha Allahu zasuyiwa tufkar hanci dan shi besan da wane ido ze qara kallon Surukansa ba idan har wannan magana ta fito, haka suka mata sallama suka tafi.

Abu dai kamar wasa se gashi qaramar magana ta zama babba, tun tana jurewa har ta kasa. Tuni magana taje kunnan Maman Abdurrahman din. Ranar kamar zata ari baki tsabar fada,

"Wato zama da mahaukata sun washsheka kaima ka haukace ko, ba a haihuwa kai aka haifeka ni dama na dade ina zargin haka ban dai tabbatar bane shi yasa nayi shiru amma yanzu na tabbatar ka haukace yanzu" haka ta ringa sababi data gaji tashiga nuna masa rashin dacewar hakan sedai Kaman ta karawa wuta fetur haka ya koma gida yaringa surfa masifa ranar ba Hamdah ba Hajara ma ta karbi rabonta dan yace ita tavkaiwa Hajiyarsa Gulma, to ko Alhaji zasu gayawa bega uban da ze hanashi abinda yai niyya ba. Ganin kamar ta'ammali da mahaukata yasa shima ya fara taba haukan yasa ta tattara shi ta watsar, in ze kwana yana ihu bazata kulashi ba se tayi kwana uku bata ko leqo palour ta ba bare waje. Ta dai daura aniyar haife ko mene a cikinta koda kuwa duniya zata taru akanta Abdurraan dai Wanda yayi nisa bayajin kira.






🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 3⃣6⃣


Cikin Ikon Allah da ana so da ba'a so Cikin Hamdah dai yashiga wata na biyar kuma zuwa yanzu ta samu saukin laulayi se dan abinda ba'a rasa ba. Tayi kyau kwarai haka cikin yai mata kyau ga jikinta daya qara murje har wani kyalli take yi. Yanzu kam Tsakaninta da Abdurrahman sedai kallo Dan gaba daya ya fita harkarta kwatakwata anata bangaren ita hakan ma yayi mata dadi dan har mantawa takeyi da zamansa a gidan in dai ba haduwa sukayi ba yaringa kallonta kuwa kenan yana hadiyar yawu tareda hararar cikin dayai girma kai bakace wata biyar ne ba, ita dai sedai tace "nan gani nan bari wannan ciki se na haifeshi ya shaqi iskar duniya daga nan nasan inda dare yaimin Dan dama zamansa nakeyi, banzo da ciki ba bakuwa zan koma gida in rainesgi ba" Abdurrahman kam baya tankata sedai yayi murmushi Dan shi kadai yasan abinda yake kullawa zuciyarsa dan bafa wai ya haqura bane, shifa bakin da Hajiyarsa tace zata masa akan cikin ne fa yasa ya daga qafa amma jira yake ta manta ya aiwatar da nufinsa.

Tsakanin Dan Adam da zuciyaraa se Allah ana haka a farkon watanta na bakwai a gidan kuna cikinta ya shiga wata shida wata rana tana zaune ya sameta fuska cike da nadama akan abinda ya aikata, cikin lafuza masu taushi ya ringa bata haquri yana cewa

"kiyi hakuri Wife wallahi sharrin shaidan ne, dazu ina office naji wani wa'azi da wani malami yayi akan falalar rainon Yaya nima naji ina kwadayin ladan yanzu nayi nazari na gane cewa baiwa ce babba Allah yai mana kuma nagano Gaskiya kiyafemin ina son abi da yake cikin ki zamu raineshi tare insha Allah" haka yayi ta lallabata. Dukda dokin zuciyar data hau da irin tarin haushinsa datake ji akace zuciya bata da qashi sai gashi ta sakko ta kuma yarda musamman yanda ya marairaice yana mata rantsuwa akan ya tuba, nan da nan suka koma normal komai ya wuce tamkar babu wani abu daya taba shiga tsakaninsu. Yanda yake bata kulawa kuwa abin se ya baka mamaki, seda ya tabbatar ya wanke duk wani laifinsa a idon kowa dan har Kano ya dauketa suka je bayan sun dawo ya shiga nema musu Visa akan Dubai zasu tafi acan zata qarasa rainon cikin har ta haihu. Idan ya fita kuwa komai ya gani naci ko wanda ya shafi kayab jarirai seya siyo ya kawo mata.

Akace kishi kumallon mata nan da nan se Shaidan ya shiga zuciyar Hajara yake kitsa mata cewa abinda take gudu ya faru Hamdah ta kwace mata miji tunda gashi tun ba'a je ko Ina ba hankalinsa duka ya koma kan ta Ina ga ta haihu ai ita tata ta kare a gidan, seta chanza mata gaba daya, yar hirar da suka saba da girkin datake kawo mata duk ta dena. Datayi mata magana seta ce yanzu ai taga tana da me debe mata kewa shiyasa ta ja baya ta basu fili suci soyayyarsu da tsinke, murmushi kawai Hamdah tayi bayan dataji wannan furucin nata tasan kishi ne zallah yake damunta dan haka bataga laifinta ba ita ma setayi baya da ita kawai tunda wanda ya hada ya raba.

Wata ranar Tuesday da safe tana zaune Abbah yaje gidanta. Wannan shine Karo na farko tun auranta gidan Abdulmalik daya kaita da kansa be qara zuwa ba sefa ranar da Abdulmalik din ya rasu se yau kwatsam gashi a Kaduna gidanta. Ranar har kuka seda tayi dan dadi ganin mahaifin nata haka tashiga masa hidima duk abinda hannunta yakai kai seta dakko masa ta ajiye har seda ya gaji yana ta murmushi zuciyarsa fal farin ciki ganin ta kwantar da hankalinta. Sun dade suna hira, sosai ya kara mata nasiha akan dai hakuri sannan ya dan taba duk abubuwan data masa dan zama tayi zatayi kuka wai seya ci komai haka ya dinga yafitarsu kadab kadan yana ci. Se yamma ya tafi yabarta da tulin tsaraba da kuma kewarsa.

A yanzu bata da wata damuwa tunda ta samu kwanciyar hankali da nutsuwa a gidan auranta. Cikinta Dan kimanin wata bakwai ya fito yayi girma sosai a jikinta kamar wani wata tara yai bala'in yi mata kyau. Kamar kullum tana zaune acikin falonta sanye take da doguwar riga dinkin kasar Oman blue wadda ta bude sosai daga kasa hakan yasa bata takura ta ba, kankarar madara ce tuli a gabanta wadda Yusra kanwar Abdurrahman tayomata take ta faman dirka dadi da sanyin madarar ya dauke mata hankali har bataji sallamar da Abdirrahman yake ta famanyi ba seda ya janye kwanon Qanqarar sannan ta dago kanta a shagwabe tana jifansa da wani kallo. Murmushi me kyau yake mata yana qare mata kallo a ransa yace
"God I love this girl amma tayi fuck off ko wa yace mata seka haihu kake samun farinciki a rayuwa oho" seya zauna a kusa da ita bayan ya janye kwanon yana dubawa

"Sannu madam me kika samu haka babu tayi?" Ya fada yana kai hannunsa kan qanqarar, seyayi saurin daukewa yana harararta cikin wasa kafin yace

"Wato sanyin dana hanaki sha ne ko". Seda ta cire katuwar kankarar da ta tura abaki tana cije hakori saboda yanda sukayi sanyi sannan tace
"kankarar madara ce fa kawai nagani a gidan Yusra shine ta aikomin da ita dazu"

"Bana hana ba La la banyarda ba salon ki sa yarona yazo da mura ko to ba dani ba karna qara ganin irinta a gidan nan ita dai data qulla qawance da asibiti tayi tayi kina kallo dukka yaranta Pneumonia ne dasu" ya karasa yana kwashe qanqarar ya zuba a cikin wata baqar leda daya gani a gurin. Kukan shagwaba dake kara narkar dashi ta shiga yi masa tana cewa

"yanzu fisabilillahi Dan bakasan zafin da ciki na yakeyiba ka hanani shan ice cream yanzu kankarar ma ka kwace".
" An zo gurin" ya fada a zuciyarsa sanda wani tunani ya bullo masa sharp sharp, a fili kuwa se yace

"To yi hakuri indae Ice cream ne zan kawo miki roba daya dai amma ba da yawa ba kin yarda" kai ta daga masa alamar ta yarda da haka ya samu tabar shan kankarar. Ya kwashe dukka ya fita da ita sannan ya dawo suka ci gaba da hira yana mammatsa mata kafafuwanta da suka kumbura sosai, wani lokacin yakan tausaya mata ganin yanda cikin duk ya chanza ta lokaci daya duk ta kumbura dukda se yaga kamar kyau ma take qarawa. Se bayan magrib ya fita Kaman yanda yai mata alqawari kuwa tun daga ranar kullum da daddare se ya siyo mata Ice cream guda daya jal ya kawo mata haka suka ci gaba da rayuwa.

Kasan cewar girkin Hajara ne gashi har 9:30pm tayi bai kawo mata Ice cream din ba kamar yanda ya saba se tayi tunanin tayi tsiyar ne dan wata rana haka take ranar girkinta in ya dawo tun magribar nan bata barinsa ya ko leqa kofar gida se da safe, abin me ciki seji tayi ranar tafi kwadayinsa akan ko wanne lokaci. Dukda tana da dab sauran guntun na jiya amma ba flavour take so ba, ita Chocolate flavour take so yau yawunta har wani tsinkewa ya ringayi. Agogo ta qara kalla goma saura yan mintina seta yanke shawarar kiransa kawai a waya dab bazata iya haqura ba. Ringing biyu ya dauki wayar yana cewa
."heartbeat me ya faru kuma ko Baby yana Missing Dady ne?"

"D sweety baby yaki bacci yana jiran Ice cream"
Seya dafe kansa kamar yana gabanta kafin yace "Oops I'm sorry wallahi wasu abu suka sha kaina, Baby yayi haquri i will bring it to u right away" ya tashi jiki na rawa aransa yana cewa "this the right time" ko takan Hajara dake qorafin an shiga haqqin ta beni ba yayi waje abinsa.

Bayan da ta kashe wayar se zaman shirun ya dameta nan ta shiga kiran mutane dukda taga dare ya farayi, Maryam ta fara kira suka danyi magana sama sama dan har tafara bacci sannan ta kira Aysha, Mijinta ne ya dauka yake shaida mata Ayshan na bacci, an kuma gamuwa ta kuwa samu ciki me dan banzan wahala yau gida gobe asibiti. Dariya ta ringayi bayan da ya gama mata bayani cikin sigar tsokana tace "kace Dan baba yayi tsiya shikenan in ta tashi ka gaya mata na kira" sannan sukayi sallama.

Har ta ajiye wayar ta tuna da Anty Hadiza abokiyar aikinta a poly data haihu Dan haka ta kirata. Kaman yanda tayi tunani da korafine ta fara In da take cewa "haba Anty Hamdah shikenan kuma tunda kinbar aiki zumunci kuma ya kare sedai muji labarinki gurinsu Sadiya" kunya ce ta kamata ta shiga bata hakuri daga nan ta mata barka

"Amma dae kema mun kusa zuwa suna ko?" Ta tambayeta. Dariya ta shiga yi hakan ya tabbatarwa da Anty Hadizan tunaninta gaskiya ne nan ta shiga jero mata addu'oin Allah ya raba lafiya. Shigowar Abdurrahman ce ta katseta tayi mata sallama ta kashe wayar. Turo baki tashiga yi ta juya masa baya tana kunkuni a dole ita tayi fushi dan har abin ya fita akanta. Wani irin kallo yake binta dashi Wanda ta kasa fassara ma'anarsa kafin cikin sanyi sanyi yace
"is ok nasan fushin na me nene gashi na kawo ayi hakui na sanki yanzu ina iya kawowa ki maidani dan haka na siyo miki dukka flavour din da suke dashi".
Seda ta harareshi cikin wasa sannan tace "Ai na yafe baka kawo min ba tun dazu se Dana cika ciki na da youghout tukunna". Nan ya shiga lallabata akan tasha sedai duk yanda yayi da ita keme me taki karba tasha din har abin ya bata masa rai cikin fada yace

"kin san baza ki sha ba kika tasheni a daren na fita na siyo miki to gashi nan in kin ga dama ki dauka" a cikin fridge din dake dakin ya aje mata yayi waje fuuu abinsa. Bata ko bita kansa ba ta shiga wanka sannan tayi shafa'i da wururi, seda ta gama dukka shirinta na bacci, har ta kwanta kuma zuciyarta ta kwadaitu da Ice cream din sekuma ta sakko ta dauko roba daya ta bude tana mita a ranta nan da nan ta sha. Seda ta shanye shi tas harta bude wata wata robar tasha rabi sannan ta kwanta tana jin wani farinciki a zuciyarta.

****************************

Cikin bacci taji kaman ana tsikarar ta a mararta, kadan kadan ciwon yaringa gaba harta farka daga baccin babu shiri, lokaci daya mararta ta kulle mata kamar mejin fitsari ga kuma Dan cikinta da ya tsananta motsi kamar wanda yake wrestling. Dakyar taja jikinta ta Jingina kanta da Allon gadon tana Jan numfashin daya fara yi mata wahala. Ganin ciwon dagaske yake yasata diro da kafafunta kasa sai dai mikewar sam ta gagareta, Addu'oi tashiga karantawa a zuciyarta tana fatan Allah ya kawo mata dauki lokaci daya ta saki wani marayan kuka jin Dan cikinta na barazanar barin jikinta. Dole ta yunqura dakyar ta Mike jin kamar fitsari na Neman kufce mata ta fada toilet din.

Wani Abu mai dumi da take da tabbacin ba fitsari bane ya shiga zubo mata, cikin tunanin abinda zata gani ta leka dan taga ko menene sedai abinda ta gani din yayi matuqar daga mata hankali. Jini ne ke zuba daga jikinta kamar Wanda aka yanka wata qaramar dabba ba shiri ta miki bata ko damu da murdawar da cikin ya keyi ba ga kuma jinin dake zuba ta nufi part din Abdurrahman.

Bugun kofar take bana wasa ba abinda yai sanadiyyar farkawar Abdurahman da Hajaran a kusan tare. kiran sunansa take cikin daga murya da azabar ciwo
"Dear kaman fa Sunanka ake kira kodai Dan wata bakwai za'a haife mana ne" Hajara ta fada tana kokarin yaye bargon dasuka rufa dashi, Abdurrahman daya gama ayyana abinda ke faruwa ya mike yana cewa
"yes she might be the one kinsan sha'anin masu ciki kilan dai wani abu take da buqata" yayi waje abinsa sai kuma maganar tasa tayi mata zafi har ta fasa binsa da tayi niyya ta koma ta kwanta.

Da sauri yaja da baya ganin ta kwance male male cikin jini. Hankali tashe ya dagota ya shiga jijjigata ganin kaman bata motsi saboda ta zubda jini ba kadan ba. Kwantar da ita yayi ya koma dakin da gudu ya dakko mukullin mota, shigarsa da kuma jinin da Hajara ta gani a hannunsa ya sakata mikewa ba shiri suka fito a tare har suna kusan cin karo da juna. Daukarta yayi a hannu ya kwantar da ita a sit din baya sedai Saboda tsananin rudu Kasa tuka motar yayi dole se Hajara ce ta karba shi kuma ya koma baya ya rungumeta hannunsa akan cikinta daya ke jin yanda yake juyawa kamar ana yaki a ciki, irin motsin da Dan ciki yakeyi tun yanayi da karfi a hankali motsin ya fara raguwa hakanan har sannan jinin bedena zuba ba. A kafada yashiga da ita reception din Asibitin Dr Huzaifa dan bashida sauran zabi, shi kadai ze iya rufa masa wannan asirin be isa ya kaita wani asibiti a wannan yanayin ba dole a kamashi. Yanda ya shigo da ita dinne ya jawo hankalin ma'aikatan dake gurin suka nufeshi da sauri. Wani mugun Kallo Dr Huzaifan ya ringa binshi dashi lokacin dayake mika masa farar takarda domin yasa Hannu kafin a shiga da ita Theatre hanya daya da zasu iya ceto ta kenan kila da abinda yake cikin nata. "Burin ka ya cika amma kasani wallahi in ta mutu da hannuna zan mika ka ga hukuma" yayi gaba abinsa bayan ya fizge takaddar. Abdurrahman baisan kuka yake ba saida wani a kusa dashi yace "kayi hakuri Alhaji addu'a zakayi mata muma duk jiran tsammani mukeyi daka ganmu anan" amma a maimakon yayi shiru saima ya kara kukan nasa.

Tarin Nadama da Dana sani ne suka ziyarce shi lokaci daya, Meyasa ya zama mai sonkai a rayuwa? kwata kwata baiyi zaton kasancewar abun haka ba ko ba'a fada masa ba daga irin jinin data zubda yasan tana cikin hadari, meyasa be duba watannin cikin ba kafin ya yanke wannan danyan hukuncin kaiconsa kaicon zuciya irin tasa. Bashida

Please Login or Register in order to submit comment