Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi me ma'anoni da yawa san ma yace "Hamdah, I can't promise you that saboda Bansan KADDARAR da Allah ya RUBUTAMIN ba sedai na miki alkawari for better for worst Ina tareda ke". Yana kaiwa nan ya saketa ya mike dan tuni an kira sallar la'asar. Ita ma sallar ta shiga dakinta tayi, bayan ta idar ta sake wanka dan kayan jikinta dukka sun dameta. Shiru shiru har magriba babu Abdulmalik babu dalilinsa gashi tun yamma aka dauke wuta kuma ba'a kunno Generator ba kaman yanda aka saba. Hijab dinta ta saka har kasa ta leqa inda me gadin su yake zama.

Baba me gadi na zaune da yar radio sa a bakin gate yana jin labaran Dare. Cikin matukar girmamawa ya gaisheta dukda ya kusa yin jika da ita, yanda mutumin yake mata har kunya yake bata baya taba bari ta gaishe shi ze fara. " Kiyi hakuri hajia nasan maganar rashin zuwan murja ne yau wallahi ita Maman tasu ce ta tashi da jiki shine ta zauna da dan kula da ita dazu babanta yazo har nan ya gayamin kar aga shiru bata zo ba. Murja Yar Baba me gadi ce. Yarinya ce me matukar nutsuwa. Ita take taya ta ayyukan gida duk wata suna biyanta dan Abdul yace bayasan me aikin kwana yafiso tazo da safe tayi aikinta ta tafi. Se tayi murmushi tace "Ayya Allah ya bata lafiya dana sani ai da tunda rana na shiga na dubata kilan shima baka gaya masa ba nasan da zeyi maganar. Bama zuwanta bane dana naga har yanzu ba'a kunno Gen bane shine na leqo naji ko lafiya". Se ya rike baki yace " Au dan Allah hajia tuba nakeyi, tun da safe Uzairu yazo ya katse wayar dake kawo wuta daga can cikin gidan ban dai masa magana ba na zata ko Alhaji Karami (yana nufin Abdulmalik) ne yace ayi hakan, to kuma yau bamu hadu ba gaskiya naji shigowarsa ina kewaye kafin na fito kuma ya fita sedai in ya dawo ki sanar masa".

Cikin gidan ta koma da mamaki, to meya faru aka ciresu daga wutar Injin? Saboda tasan basa matsakar haske dan haka a gidan ko fitila me chaji bata da ita. Se wayarta ta kunna haske tana zaune duk tsoro ya isheta. Kazar data gasa musu tun da rana basu ci ba yace tayi warming base tayi girki ba ze taho musu da fura gashi yanzu babu wuta. Dabarar gashin Foil paper ce ta fado mata ta tashi ta shiga kitchen din ta qara shafe kazar da kayan hadi sannan ta nadeta sosai a cikin foil paper ta zuba ruwa a Pan ta dora. Tana tsaye tana jiran kazar tareda dan jujjuyata dan ko ina yayi zafi a ranta tana takaicin da standard Cooker gas gareta ba wadannan table stove din ba bata da matsalar oven. Duk iyayin Anty zahra ne wai 21st century Gas din ma soft touch. Har ta gama ta sauke ta hada musu duk abinda zasu buqata a kan dining sannan ta tada sallar Ishah. Gaba daya ta gaji da zaman, wayarta ta dauka ta shiga kiran Afeeya dan ta debe mata kewa. Sun dade suna waya kafin sukayi sallama karfe 9pm babu Abdul babu alamarsa se kawai ta shiga game a wayarta tana mamakin ina ya tafi tun la'asar ga shi in ta kirashima se wayar tayita ringing ba'a dagawa.

A bangaren Abdulmalik tun bayan daya dawo daga masallaci yana Palour Hajja a zaune. Kansa a kasa ya irga Tiles din dakin yafi sau cikin kwando dan tunda ya gaisheta ta amsa bata kara ce masa ko yaci kansa ba. Seda ta mula dan kanta bayan kusan awa guda sannan tace "Shanyayye sena biyo ka na tambayi result din test din naku kenan zaka kawo min". Beyi magana ba salin alin ya zura hannu a aljihu ya ciro brown envelope din da ko budeta beyi ba tun bayan da Nasir ya bashi ya miqa mata. Seda ta harareshi sannan ta karba ta bude sannan ta warware farar takardar dake ninke a ciki. Tsaf ta karance rubutun ciki bayan wasu yan mintina ta dago ta kalleshi sannan tace " Na gani amma be gamsheni ba dole ka qara aure dan mu tabbatar da lafiyar ka in dagaske ne".

Tamkar saukar aradu haka yaji maganar ta, shikenan ta faru ta qare wai anyiwa me dami daya sata. Babu abu daya daya tsinta a cikin babatun data ringayi har ta gama tace ya tashi ya tafi.
Kodaya fita daga dakin tsohon dakinsa na Boys quarters ya nufa dan baya jin ze iya tunkarar Hamdah cikin wannan yanayin, gani yake kaman zata gane abinda Hajjan ta fada. Shi taya ma ze fara ce mata wata Hajja tace yayi aure ai abin ma ya zama kamar da hadin baki. Komai na dakin yana nan yadda yake hatta da gadon a gyare yake tsaf se yar qura da gurin yayi, bed sheet din ya yaye ya kwanta kawai ya rasa wanne tunani zeyi a cikin kwakwalwarsa. A cikin dakin yayi magriba da isha duk kiran wayar da takeyi akan idonsa ne amma bashida kwarin gwuiwar dagawa. Har karfe goma yana dakin, Usman dayaji motsi a dakin ne ya leqa yana mamakin waye a dakin Yayan nasu dan sunsan babu wanda yake shiga dan dama Aliyu ne yaso komawa can din to yanzu yana turai karatu. "Yah Abdul kaine a ciki ashe" Usman ya fada cikin Mamakin me Abdul din ya keyi a dakin a wannan lokacin. "Yh nine fita zakayi ne?" Ya tambayi Usman din.
"Aa ba fita zanyi ba sedai in akwai wani abu da kake so sena karbo maka". Kudi ya ciro a aljihunsa ya mika masa " Please Fura zaka siyomin in ka dawo ka kai mata gida". Hannu biyu yasa ya karbi kudin musamman daya ga yawansu yasan ragowar nasa ne. Shi yasa yake son Yah Abdul akwai shi da kyauta. "Sallama yayi a kofar palour ta amsa minti daya a tsakani ta leqo dan seda ta dakko hijab dinta a daki, "Yi hakuri Yaya Sadiq" ta fada daidai lokacin data bude kofar. "Au Usman kaine senaji muryar kamar ta Sadiq". Gaisheta yayi sannan ya mika mata ledar Furar. Da mamaki ta karba sedai bata nuna masa hakan ba. "Anty ya akayi baku da wuta inaga dai yaya be sani ba bari na duba ko hanya ce ba'a chanza ba".
" Aa Usman base ka wahal da kanka ba connection din Gen din ne ya katse se gobe za'a kira me gyara" Ta fada har lokacin tana mamakin dalilin ciresu daga kan Gen din. "Ok amma da tun dazun ma kika aika ai Uzairu ya iya gyara se yazo ya gyara muku amma bari inna shiga se na turo shi ya duba".
" Nagode" ta amsa masa tana murmushi, halayyar Usman sak Khaleefa kaninta shiyasa suke shiri dashi. Sallama ya mata har ta juya ta jiyo muryarsa "Am Anty nace ba" seta juyo tana kallon yanda yake sosa kai. Dariya tayi "Ya akayi?" Ta tambayeshi.
"Nace yaushe Hamidah zata zo ne na kwana biyu ban ganta ba kuma ko last week da kika aikeni gida bata nan". Setayi yar dariya, dama tasan baze wuce zancen Hamidah ba dan tunda ya ganta shikenan Usman ya rasa sukuni a dole sonta yakeyi. " Hamidah na Kaduna inaga ma se bayan sallah zata dawo kano tunda sun gama SSCE". Seya bata fuska, "Nidai zan karbi number ta please Anty bari naje na turo miki Uzairun dare yana karayi"." Ok idan ka hadu da Yayanku kace ina jiransa".

Sanarwar ganin wata dayaji ce ta sakashi mikewa babu shiri ya nufi gidan, shaf ya manta da wai gobe za'a tashi da azumin ramadan. Shopling din da sukayi niyyar zuwa ma ba a jeba. Har ya gama uzurinshi tana zaune akan gado tana kallonsa. Furar kadai ya iya sha ita ma kadan dan dai kawai zeyi azumi ne. A nata bangaren ido ta saka masa tana karantar yanayin fuskarsa sedai bata ce masa ko kanzil ba har yazo ya kwanta ya juya mata baya tana jinsa se tsaki yake wai zafi. Se kawai ta saka masa kuka dan tunda sukayi aure be taba juya mata baya ba. Kullum a cikin jikinsa yake kwantar da ita koda kuwa ba bacci zasuyi ba. Tashi yayi ya fice daga dakin dan yaje yaga koda abinda ze iyayi ya maida connection din dukda ance masa wai order Hajja ce ta a ciresu daga kan Injin gidan cikin ikon Allah yana kaiwa tsakiyar palour aka kawo wuta.

Ruwa ya dauka sannan ya juya dakin. Har ya dawo tana nan inda yabarta tana aikin kuka, tsaki yaja ya dire ruwan kai tsaye ya wuce toilet Dan gaba daya haushin kowa yakeji wai me ma aka mata? Yanajin yanda ta karawa kukan nata volume ganin ya wuce ta dolensa ya juyo cak ya dagata, cikin minti biyu tayi shiru se numfashi da take saukewa.
Ranqwashinta yayi ta dafe gurin tana masa kukan shagwaba, get up jor in ba so kike mu rasa azumin ba tashi muyi wanka. A tare suka fito lokacin har wasu masallatan sun fara kiraye kirayen sallah dan haka da sauri suka sha ruwa sannan suka fara Nafila har aka kira sallar asuba suka gabatar. Addu'a suka duqufa yi tundaga wannan dare akan Allah ya biya musu buqatarsu.





🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 2⃣0⃣

Sun shiga watan Ramadana da cikakken yaqinin yayewar damuwarsu. Babu abinda ta fasa kamar yanda al'aar ta take a duk watan azumi, zatayi girki da yawa takai cikin gidan tunda gaba dayansu tare suke shan ruwa. Hakan da takeyi yasa sauran surukan ma suka koya zakaga kowacce da dafo nata kalar abincin ta kawo saboda yawansu yasa suka rarraba kwanakin da kowacce zata ringa kaiwa amma banda Hamdah da hakan ya zamar mata kamar ibadah. A bangarensa shima abokanan sa da wasu daga cikin kannensa duk anan gurinta suke shan ruwa shiyasa take zama busy sosai a watan azumi seta nemi yan tayin aiki dab ma bata da qiwa ko san jiki ko kadan. Tuni ta tsara ma kanta yanda komai ze tafi ba tareda ya kawomata cikas cikin aikinta ba. Ba kullum take zuwa ba dan haka duk randa zata makarantar to kafin ta fita seta tabbatar ta ci karfin aikinta ya rage qarashe kawai.

Kwanci tashi babu wahala se gashi har An kai azumi na goma. A al'adarsu a ranar Azumin goma sha daya a cikin gidan suke shan ruwa gaba dayansu mata da Mazansu. Ranar tun safe gidanta yake a ciki dan kusan duk wadanda suke a nesa nan suka taho aka hadu ana ta aikin abinci. Zainab tazo, tana hakimce akan kujerun palour tana binsu da kallo dan bata san sanda Hamdah ta chanza kujeru ba. Gyashi, hassada nata nuqurqusarta amma babu damar tayi magana dan bata manta da kyakykyawan warning din daya mata akan matarsa ba. Dole tayi shiru amma ta qudiri niyyar ko ba yanzu ba seta gaya mata maganar da tayi niyya. Sun gama aikin tsaf an shiga da komai cikin gida sannan suka fara wanka anan part din nata dai.

Khausar ce ta shigo kanta tsaye ta nufi daya daga cikin dakunan Hamdah wanda yake a matsayin master bedroom dinsu. Da kallo ta bita har ta qarasa ta murda handle din kofar sedai tajishi a kulle. "Malama ina key din dakin dan uwana zan shiga nayi wanka". Wani kallon takaici kawai ta bita dashi, wato har rashin mutunchin ya kai tace zata mata wanka a dakin miji dan tana taqamar ita kanwarsa ce? Se kawai ta girgiza kanta tana gyarawa Amir yaron Husna takalminsa. " Wai ke bada ke nake magana bane". Idan Hamdah ta kulata to ku da kuke karatun kuna gurin sema daga yaron da tayi ta nufi dakinta dashi in da Mamansa take. Cikim azama Khausar ta shiga gabanta tana huci kamar wata macijiya "Na rantse da Allah se kinsan ni kika yi wa banza ina miki magana zaki ga abinda ze faru". Fuu tayi waje Zainab ta rufa mata ba.
Murmushi tayi bayan da ta sauke yaron hannunta. Tanajin yanda Husna ke bala'i wai meyasa bata mari Khausar din ba ita wallahi bazata dauki irin wannan iskancin na kannen miji ba, yanzu in su akeyiwa nasu iyayen zasu zuba ido ne suna kallo basu dauki mataki ba. Babu wanda ya ce mata qala cikin Matan Yayyen nata da kanne dan gara ita Yar gida ce sukuwa dukka auro su akayi amma kowacce ranta babu dadi. Kusan dukansu sun fuskanci irin wadannan matsalolin amma nata yayi yawa. Kwata kwata Yaran basu da kirki musamman wadannan da suka samu daurin gindin uwarsu. Kayan da zatayi amafani dasu ta diba ta tafi dakin nasa dan tayi wanka. Tana saka kafarta a dakin ta jiyo hargowar Hajja ga Khausar dake rusa kuka kamar wadda aka daka Khairiyya da Zainab na take mata baya se Manubiya dake Faman riqe Hajjan. " Na rantse da Allah Munubiya kika qara cemin wani abu sena saba miki shegiya sallamammiya wato har dake aka hada aka kai sunan ku kan tsauni to ni babu bokan daya iya ya rufemin baki". Wannan magana da taji ta saka ta ajiye kayan hannunta ta fito daga dakin.

Kallon Su takeyi daddaya kafin ta sauke idonta akan khausar dake cewa "Hajja daga fa ce mata ke kika aikoni in dauko miki abu a dakin yaya shikenan ta hau zagina harda cewa ko ke baki isa ki shiga dakinnan ba bare wata ni Hajja bakiji irin cin mutunchin data ringayi mana ba wadannan na tayata" ta nuna matan yayyenta dake zaune kamar an dasasu tsabar mamakin karyar da take shararawa. Zainab ce ta amshe da cewa "Wallahi Hajja haka akayi nasan in nayi magana yanzu bansan irin sharrin dazata qullamin a gurinsa ba shi yasa kawai nayi shiru". Kanta a qasa tanajin irin cin mutunchin da Hajja takeyi mata ita da iyayenta. Babu abinda yafi baqanta mata rai irin kalmar Matsafa da take jifan su da ita, wai Mummynta ce Matsafiya sun shanye mata jinin da karshema tace Mayya ce dama tunda taga kyanta tasan Mayya ce ta lashe masa kurwa " waya sani ma ko kwayayen haihuwar taki kika bayar aka miki baqin asiri kika mallakemin Da baya ganin kowa da mutunchi se ke to wallahi ahir dinki tun wuri ki kunce wannan qullin in ba haka ba dakaina zan kunce shi.

Gani tayi bazata iya ci gaba da jure abinba. A gaban Faccaloli da Kannen miji ga masu aikin gidan duk da suka shishshigo dan Hajja bata magana a hankali. Mikewa tayi daga durqusan da tayi hawaye naci gaba da ambaliya akan fuskarta ta juya daniyar barin gurin, wasu taurari ta gani a idonta bayan da kunnenta yai mata dum na dan wani lokaci, bazata iya cewa ga aihihin abinda ya faruba. Sama sama take jin muryoyinsu akanta wasu na a kawo ruwa wasu kuma suna cewa akaita asibiti. Muryar Abdulmalik ce abinda taji ta qarshe yana cewa "Me kuka mata me kukayiwa matata? Narantse da Allah senayi sharia da dukkanku in har wani abu ya sameta". Kafin ya dauketa yayi waje da ita. Shan ruwan da ba'ayi a gidan ba kenan kowacce ta tattara ya nata yanata ta tafi gida.

Hajja ma part dinta ta koma jiji a matukar sanyaye babu ya Zainab da tuni cikinta ya juya. Batasan meya kaita har ta mareta ba, ta manta yanda hannunta yake ko Namiji ta mara seyaji a cikinsa bare wannan Nunar ranar. Wani irin zafin hannu Allah yayi mata, ko bisa kuskure ta daki abu ji zakayi kamar katako a ka buga maka shiyasa ko laifi yaranta suka mata sedai tasa wani ya dakesu badai ita dakanta ba. Khausar ta kalla sannan tace " Ke kirashi muji suna ina". Kiran Abdulmalik khausar ta shigayi sedai har wayar ta gama ringing be daga ba. Haka tayita gwadawa daga karshe ma ya kashe wayar gaba daya. Mikewa Hajja tayi da niyar daukar Mayafinta su tafi asibitin da tabbas tasan suna can lokaci daya taji wata sabuwar tsanar Yarinyar ta darsu a zuciyarta se kawai ta aje mayafin. "Hajja ya naga kin zauna ba Asibiti kikace zamuje ba" Khausar ta tambayeta. Seta tabe baki sannan tace "Ke dallah rabu dasu sekace wata yar gwal karya ma takeyi da zata wani langwabe taje in ma mutuwa zatayi tayi kowa ya huta". Se suka bita da kallo kawai suna mamakin abinda ya canzata lokaci daya kamar ba Hajjan data gama rikicewa yanzu ba. Munubiya ce ta shiga mata magana akan ya kamata taje yanzu in wani abu ya sameta suce me?
" Wallahi Munubiya kika qara magana sena tsine miki kindaiji me nace". Seta mike tsam ta dauki Mayafinta da mukullin motarta tai musu Sallama ta fice dan dama ita kadai tazo tuni ta dena zuwa da yaranta gidan indai ba ya zama dole ba. A cewarta yayanta sun fara girma bazata barsu suzo su koyi irin rayuwar da ake a gidan ba saboda Mata ne, duk masifar Hajja haka ta kyaleta yana daga cikin abinda yasa take qara takurawa Munubiyar dan har cewa take badan suna kama a fuska ba da seta ce musanya mata ita akayi a asibiti.

******************************
Har aka sha ruwa Hamdah na bacci bayan Allurar da akayi mata dan firgita ta ringayi. Ba karamin gigitata Marin yayi ba ita a duniyacma sau nawa aka taba marinta? Shafa fuskarta data kumbura suntum yake a duk minti ransa yana kara baci. Ya rasa me Hajja take nufi dashi, me matarsa ta tsare mata a rayuwa? Ko yau da safe seda ta qara masa maganar aure yai mata shiru to namene kuma da Zata saka yar mutane a gaba shida ya aurota ai shi ya kamata su takurawa ba ita ba. Wuyanta ya taba yanajin yanda zafin zazzabi kebin jikinta wani irin tausayinta ya kamashi. Me zata dorar a zaman gidansa in ba wahala da tsangwamar dangin miji ba?. A asibitin suka kwana bayan ya koma gida ya dakko musu duk abinda yasan zasu buqata dama daga gidan Nasir aka kawo masa abinci. Cikin ikon Allah kafin safiya kumburin fuskar ya sabe haka zazzabin ma babu sedai kanta datace yana ciwo har lokacin, beje office ba yazauna da ita har yamma sannan aka sallameta. A hanya ya siya mata abinci dan bata azumi sannan suka qarasa gidan.

Suna shiga ta fara masa kuka, gani take kwana dayan da tayi a gidan kamar ta fita daga ukubar bauta ne gashi yanzu ta dawo. Haka yaita rarrashinta ya bata abinci taci ta sha magungunanta kafin bacci ya dauketa. Gadinta yaringayi har seda yajiyo ana kiraye kirayen salla sannan ya fita dan ya nemo abinda zesha ruwa dashi. Kamar karamar yarinya haka ta dasa kuka lokacin data farka bayanan dan har ga Allah yanzu tsoron zaman gidan takeyi. Abincin hannunsa ya ajiye ya nufeta da sauri ta fada jikinsa tana cigaba da kukan "Shish I got you" ya fada a daidai kunnenta. Setayi shiru kuwa tana sauke ajiyar zuciya. "Shine ka gudu kabarni ko" ta fada a shagwabe. Seda yaja dongon hancinta sannan cikin kwaikwayon muryarta yace "To ba bacci kikeyi ba ni kuma bana so na tasheki tun da kin zama cry cry baby". Seta boye fuskarta a kirjinsa tana murmushi kadan. "Muje kiyi wanka se muci abinci" ya fada yana janta zuwa toilet din. Kamar yar baby haka ya nadot a towel sannan shima yayi wankan. Abaki suka ringa ciyar da junan su har suka gama.
Zaman kurame sukayi a gurin ba mai cewa kala kowanne da irin tunanin da yake yi a zuciyarsa, kusan tare bacci ya daukesu wanda basuyi aune ba se ji sukayi ana kiran sallar Asuba. Dore yayi ita kuma ya hanata yin azumi ranar a cewarsa ta bari se jikinta ya warware tukunna dole ta hakura.

Karfe shida ya shiga gidan bayan sun gama muhawara da Hajja. Tun bayan sallamar Hamdah daga asibiti se yau ya shiga gidan bayan kwana hudu. Sannu da zuwa tayi masa ya dago kansa dake barazanar tsagewa biyu ya kalleta tausayinta na kara shigarsa, duk se yaga ta rame se dogon hancinta daya kara fitowa da ido dama ga azumi. Kallonsa takeyi kaman zata fashe da kukan tace "Jaan an kusa shan ruwa gashi banyi maka komai tun dazu kaina yake ciwo na kasa shiga kitchen sedai bari nayi sauri ko chips da tea ne nayi maka".yunkurin sauka daga jikinsa ta shigayi, se ya kara rikota yayi yace "Relax bari muyi sallah se mu fita muci abincin a waje kawai...."
"Jaan muje gidan Mumcy to" ta katseshi da sauri. Seda ya karanci yanayinta sannan yace "Ok, but promise me you won't tell her anything..." "I promise" tayi saurin da katar dashi. Se ya mike da ita a jikinsa. Ruwa da dabino kadai suka sha sannan sukayi suka nufi gidansu Hamdah.

Kaman koda yaushe suna zaune gaba dayansu a Babban falon gidan, katuwar darduma ce shimfide se kalolin girke girken da Mumcy tayi cikin kwanciyar hankali suke Buda bakin suna yar hira jefi jefi. Da sallama suka shiga falon Adil(Dan Yaya Abubakar) ya tashi da gudu cikin gwarancinsa yana cewa "Ga Aunty Hamana" ya fada jikinta ta dagashi sama suna juyi a gurin itama tana "oyoyo Adalina oyoyo". Cikin girmamawa ya gaida surukannasa sannan suka shiga cin abincin Dan dama hakan ba bako bane a gurinsa, duk sanda zezo tare ake cin abinci gaba daya. Bayan sun kammalane mazan suka tafi masallaci Dan gabatar da sallar Isha'i tareda tarawi sukuma matan sukayi tasu a gida. Aunty Najma matar Yaya Abubakar ce ta kalli Hamdah cikin kasa kasa da murya tace "Mutuniyar yanaga kin rame kodai mun samu karuwane dan wannan ya wuce ramar azumi" se kawai tayi murmushi tana kokarin danne abinda yake a zuciyarta. "A'a wlh Maman Adil banida komai kawai dai azumin na bana ne yana Dan wahalar dani". bata matsa mata ba suka shiga wata hirar daban. Suna shirin tafiya ne Mumcy tayi kiranta daki, abin da da mahaifi tunda suka shigo gaba daya hankalinta ba'a kwance yake ba ganin irin ramar da Hamdan tata tayi Dan Haka ta tsare ta da tambayar meyake damunta inda ita kuma ta kafe akan azumine. Ganin bazata bata amsa ba yasaka tace "Toh ya batun asibitin kundai je kuma ba wata matsala ko". Se kawai ta saki kukan da take ta dannewa. Bazata iya cigaba da barin abun a zuciyarta ba taba buqatar abokin shawara. Kuka ta sakawa Mumcyn tana cewa "Mumcy na shiga uku ashe nice banida lafiya yanzu bansan yanda zanyiba Hajja ta tsaneni Mumcy a gurinsa kadai nake samun farin ciki a cikin gidan".

Cikin matukar tausayawa take rarrashin yar tata tana gaya mata kalamai masu kwantar da zuciya "Haba Hamdah kidena fadar haka. Bafa ke kika dorawa kanki ba kuma ai bacewa akayi baza ki haihuba kuma baya doraki akan magani ba" kai ta daga mata Dan bazata iya magana ba seta ci gaba da cewa "To kiyi hakuri ki fawwalawa Allah lamuranki komai kikaga ya samu bawa a rayuwa toh RUBUTACCE ne bawanda ya isa ya tsallakewa KADDARAR sa kima godewa Allah yaron nan yana sonki kuma dai bawani abin muzgunawa da yake miki, kiyita Addu'a nima kullum Ina miki kinji Insha Allah jinkirin alkairine kinji Hamdan Abba".

Share hawayenta ta shigayi sannan tace "Toh ni Mumcy fa bakomai ke damuna ba illah nasan yanzu zasu saka Abdul ya kara aure" dariya Mumcy tayi sannan tace "Kuji min ja'ira Ina anan ke kike cewa Abbanku ya yomin kishiyar se yanzu zakice ke bakya so toh indai wannan ne dakaina ma zance masa yayyo miki Amaryar". Se kuma tashiga yiwa Mumcy shagwaba kuma tabar kukan dama haka Mumcyn take so Dan haka tace "Kicire batun kishi daga ranki ba abinda ze kareki inba lalacewa ba ki dage da kyautatawa mijinki tunda yana sonki duk ma wacce ze auro da halinta zata zauna kinji bana son shirme ki kuma tsayar da hankalinki guri daya dan Allah kisamu ki Maida wannan kasusuwa". da haka sukai sallama suka tafi hankalinsa be kwanta ba seda tagaya masa yanda sukayi da mumcy
"Amma babe Meyasa kika gaya mata Baki tunanin hankalinta ya tashi"
"No Jaan I know my mum ko Abba bazata gayawa ba sannan tace na

Please Login or Register in order to submit comment