Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalar mint green da duwatsu Orange da silver, takalmin kafarta da kuma purse tareda sarkar da ta saka ta danyar azurfa suka kara kawata kwalliyar tata saifa beads manya Orange data kara akan sarkar tayi kyau tamkar ka sace ta ka gudu se walwalu takeyi . Zahra kuwa da code lace ne kalar light purple a jikinta da sukayi iri daya ita da Hamidah uwar rawar kai da tana hango su ta nud gurin da gudu suka saka HAMDAH a tsakiya sai ga Mumcy tana share hawayen dayakasance na tsan tsar farin ciki kallon Abbah tayi tace "Prof look at our kids" "All grown up " ya fada cikin muryar dake nuna tsantsar farin ciki dan gani yake kaman yafi Dr Maryam murnar wannan rana. Yayansu mata uku kenan da Allah yabasu su aurar da daya yau gashi suna shirin aurar data biyu addu'a yayi a ransa Allah ya bashi aron rai yaga auran Hamidah kamar yanda yaga na yan uwanta. Gurin suka qarasa suka shiga daukan hotuna da sauran Yayye da kannenau Maza da kowanne ya hade cikin shaddar da sukayi anko su Khaleefa babban abokin amrya harda babbar riga, ita kanta me gayyar Dr Maryam ta cakare ba kadan ba tayi kyau kai bazaka ce ita ta haifi wadabnan zan kada zankadan samari da yammatan ba. Ganin Khaleefa baze gaji da daukan hoton ba yasa Anty Amna taja Amarya suka fita zuwa harabar gidan inda ya dau decoration na kamu kai bazaka taba cewa cikin gidan Prof Ammani ne ba.

Wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata daidai lokacin da feshin turare na farko ya sauka a jikinta, wakar da aka saka mata domin kamun me taken Tazama tazama ita ta kara mata kaimi gurin kukan nata Wanda kowa yadauka a matsayin kukan da yawancin amare sukeyi ne awannan rana sedai a gurinta kukane irin Wanda mace takanyi yayi rabuwa da masoyi. Ta rigada ta cire rai a zuwansa lokaci ya qure mata. Kukan taringayi da tun ana rarrashinta har ta basu haushi suka rabu da ita kowa ya shiga sabgarta ganin babu sarki se Allah yasa tayi shiru tana kallon yanda ake gudanar da shagalin wai duk sabida ita. Masu cin abinci nayi masu rawa sunayi babu wanda ya kuma bi ta kanta.
Zuwan Ango ne yakara ruda gurin nan biki ya dau harami inda ko wanne bangare basuyi wasa ba gurin yiwa nasu ruwan Nairori har ma da daloli. Ranar kam an rubda galan galan na farin ciki, ango yayi rawa ya gyagije ya kuma nunawa duniya yana son Amaryarsa. Ita kanta tayi matukar karfin hali bata sake kuka ba tun bayan da Angon yai mata magana seda Mumcy ta shiga tana mata liqi ne ta samu wannan damar ta rungumeta tareda fashewa da kukan da take sonyi tun dazun, sai bayan isha aka watse daga kamun kowa nawa Amarya da ango fatan alkairi.

Filla filla tayi da kayan jikinta ta shiga wanka ta dauro Alwala, tana idar da sallah ta kwanta dukda baqar yunwar datake ji dan ta manta rabon cikin ta da abinci. Cikin baccinta tayi mafarki daya sakata farkawa A firgice, Abdul'ahad tagani cikin wani mawuyacin hali yana kiranta da ta taimaka masa se miko mata hannunsa yakeyi saidai kafin ta kama hannune Abdulmalik yashiga tsakiyarsu yana ce mata "Haba masoyiyata yanzu har zaki zabi wani akaina bayan tsahon lokacin Dana dauka Ina rainon son ki araina? Ki zo gurina zan baki dukka farin cikin da kike so".
Kallonsa takeyi takuma kalli Abdul'ahad dake fadin "karki gujeni nine masoyinki na hakika HAMDAH kizo" sedai kanta yi yunkurin wani abu Abdulmalik din yaja hannunta suka fara barin wurin. Tana kallonsa ya durkusa a kasa tareda rike saitin zuciyarsa yana numfashi cike da wahala hakan be hanashi kiran sunanta ba. wani irin bakin Amai taga ya farayi Wanda batasan sanda ta fizge daga rikon Malik din ba ta nufeshi sedai kan ta karasa harya cimmata yadagata cak yafara tafiya da ita.
Kiran sunan sa da tayi da karfi tareda sakin kuka ta bude idobta a firgice batasan a fili tayi hakan ba, Zahra da tun farkon fara motsin kanwar tata ta farka tayi saurin rikota tana tofa mata addu'a ganin kaman ba a hayyacinta takeba. Sundauki tsahon lokaci kafin ta nutsu se zufa da take ta sharewa dukda Ac dake kunne har lokacin tana jin sautin muryarsa akunnanta.
"Hamdah meyake damunki na fuskanci tunda aka fara bikinnan bakida walwala Wanda bamuyi tsammanin haka daga garekiba "Zahra tajefo mata tambayar bayan ta bata ruwa ta sha.
"Ba komai Anty me kika gani?"
"Abubuwa dayawa ga kuma mafarkin dakika yi yanzu daya kara sakani a kokonto anya kuwa Baki yankewa kanki danyan hukunciba".
"Kamar yaya kuma Anty?"
"Kaman yanda kikaji na fada mana wai ma sunan wa naji kina kira acikin baccinki?" Ganin tana neman tada zaune tsayene yasaka ta jan bargo sannan tace "Nifa Anty na gaya miki ba komai ni ban ma San abinda kike magana akaiba" ta kara sa tareda rufe har kanta gaba daya. Bata jin zata sake maganar sa da kowa ta daukarwa kanta wannan alkawarin koda kuwa kwana daya zatayi gidan Malik ta mutu zata je. dole badan zahra tasoba ta kyaleta itama ta kwanta ita dai Hamdah baccin da bata koma ba kenan har seda aka kira sallar asuba.
Karfe 11 na safe suka tsaya first transit dinsu, sedai yasan ko tsuntsu ze zama baze isa Nigeria a yau ba Agogon hannunsa ya kalla wanda ya nuna 11am tunowa dayayi da second Transit yakara dugunzuma hankalinsa bashida wani abin daya rage masa Illah addu'a dan yasan a yanayin da ake ciki Allah ne kadai ze iya chanza wannan Al'amari, dole ya tafi inda aka sauke su dan yana buqatar yin wanka da cin abinci. Tunda ya kuma hawa jirgin yake zare ido dan Sosai tafiyar ta kara nisa a idonsa dan gani yake kaman an nunka awanninne sedai abin takaici bayan saukar a Birnin Cairo ya tarar da babu jirgi zuwa Nigeria dole yai jiran awa shida. Kukane kadai beyiba, nemar guri yayi ya zauna yana saka da warwara ganin babu mafita tasa dole yanemi hotel koba komai yarama sallolin da ake binsa kafin ya kara daukar hanya.
A sakko Lafiya Alhaji Abdul'ahad Galdima
A bangaren Handah washe garin ranar suka gabatar da mothers Eve wanda mumcy ta hadawa yar tata. Kwalliyar yau kam Harta fi tajiya kyau wata hadaddiyar Fitted Gown ta saka kalar Blue black me adon silver yayinda angonnata yasaka wata dakakkiyar shadda kalar light Ash dinkin babbar riga. Yau kam yai abin azo a gani dan bakaramin kokari tayi ba ganin ta cire damuwa daga ranta kodan kaucewa kallon tuhumar da Anty zahra take mata se dan har dan qusqua dinnan na Amarya da ango sukayi. Tayi mamakin ganin friends dinta sunsha anko tasan dai ita bata gayya ce su ba, hatta Yan Group din *HAUSA NOVELS DA RUBUTACCIYAR QADDARAH 1 AND 2* yan adawa sunje cin bati suna cin kaza suna bata rai su a dole ba ayi musu daidai ba gashi har wani anko sukayi.
Zuciyar Alhajin su Abdulmalik fa ta danyi sanyi kodan ganin irin dukiyar da Prof ya Narkawa yar tasa tun daga kan furniture dan koshi kansa babu daya daga cikin yayansa data samu irin wadannan kayan duk kuwa da yanda yake zagewa yamusu kaya na bajinta ga uwar Gara treller guda da aka kai aka jibge tsabar sana be harda al'adar fulani ya aro wadda sujewa uwar miji gado uban miji kuma lefe a cewar Prof yayiwa Dr Maryam kara hakan kuwa ba karamin dadi yaiwa Alhaji Kamalu ba, hankalinsa be tashi ba seda yaga yanda harkokin bikin suke ta wakan. Be tsinke da lamarinba se sa lokacin da Excellency Governor yakirshi yake shaida masa zuwan me girma shugaban kasa daurin auran Dan nasa wanda uban Amarya ne ya gayyatoshi da kansa kuma ya amsa tuni ya koma se yan idanuwa ya rainawa kansa aji da kansa. Ashe shi duk burgar banza yake Masu iko na inda suke, a sannan ya kara yarda da lamarin na Prof yakuma yarda base ka nunawa duniya kana dashiba duniyar da kanta take dagaka ta nuna ka in har ka isa.

Wata irin faduwar gaba ta cinci kanta ciki, wai yau wannan dare shine darenta na karshe cikin gidansu a matsayin budurwa wai a gobe ake shirin mikata ga wani a matsayin miji, kawai seta mike da gudu tayi dakin Abbah inda ta tabbatar zata samu Mumcy a lokaci, ko takan mutanen dake tambayarta inda zata batayi ba ta shiga dakin.
Jikin Mumcy ta fada tareda sakin kuka me tsuma zuciya tana fadin "Mumcy na fasa wlh na fasa auran kuma yar musu da komai nasu nidai zan zauna dake" tausayin Yar tata ne ya kamata take itama tafara hawayen dan harga Allah duk cikin yayanta tafison HAMDAH soyayyarta daban ce cikin zuciyarta kodan ance yaron da yafi kiriniya yafi shiga ran mahaifa?
Abbah daya fito daga toilet ya dade yana kallonsu ganin kukan nasu bana kare bane yasashi matsowa yace "toh ya isa haka mana haba Maryam keda zaki rarrasheta kuma seki bige da taya ta kukan uhm"
"Hamdah na bakison mu samu ladan da kowane iyaye ke samu a lokacin da suka aurar da yayansu?"
Sassauta kukan nata tayi ta amsa shi da "Ina so mana"
"Yauwa toh kidena kuka kiyi kokarin gurin amfani da duk nasihar da mukayi miki ki kuma kara da hakuri da juriya Insha Allahu zakiyi Nasara a rayuwarki"nan suka shiga karayi mata nasihohi masu ratsa jiki tareda tsoratar da ita akan masifar dake tattare da sabawa miji.
"Karki amfani da damar cewa yana son ki ki wulakantashi ko ki tsallake umarninsa Allah ba ruwanshi da wannan ze hukun taki dai dai da lefinki" cewar Mumcy tana shafa lallausan gashinta daya sha gyara yana fitar da wani fitinannen kamshi.
"Nidai akarshe zan ce miki rayuwar mahaifiyarku tazame miki abar koyi Dan nasan inhar zaki kwatanta hakan to lallai zaki samu makullin aljannarki tun a duniya Kaman yanda na mallakawa Maryam dita nata "Abban yafada yana kallon Mumcy cikin sigar tsokana daga nan suka cigaba da yar hirarsu har bacci ya dauke Hamdan.zata tasheta ne yace
"Haba Haj ki kyaleta yau daya dai shekaru nawa rabon da ku kwanta gado daya da ita yau na yafe ki kyale yata taji dumin mamanta na yau kafin itama ta tafi inda zata fara bautar nata yayan"
Sai taji sababbin hawaye na zubo mata dole ta gyara mata kwanciya suka kwanta ranta fal da tunani tareda kewar Yar tata.
"Allah ya shigar dake a sa'a ya sa dawwa mammen gidan zamanki ne Yata".
"Amin" prof ya Amsa mata daidai sanda yake gyara pillow akan Sofa inda zai kwanta.
Asuba ta gari iyalan gidan Prof.







🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 1⃣4⃣

Karfe shadaya daidai na safiyar ranar lahadi 7th October dubban mutane suka shaida daurin auran *Abdulmalik Kamal Dala da Hamdah Ahmad Ammani* akan sadaki Naira dubu 100 kacal. sanarwar daurin auran tayi daidai da isowar Abdul'ahad a matukar galabaice saboda tafiya beko hutaba saukarsa kenan a Aiport ya garzaya gurin, dakyar ya isa bayan doguwar tafiyar kafar daya sha saboda hanyar a cike take babu ta inda abin hawa ze wuce. Sunan Allah ya shiga kira yana dafe da kansa dake barazanar rabewa biyu yai zaman dirshan a gurin dayake komai yana rabe masa uku uku. "Yah Allah ban butulce ba me yasa ka jarabceni ta haka, Allah meya sa ka hanani ita" kalaman dayake fada kenan cikin fitar hankali tuni hawaye suka gama wanke masa fukarsa. "Yan zu kin tabbata batawa ba shikenan na rasa Hamdah" ya fada da qarfi yana qara rushewa da kuka me ban tausayi. Kallonsa mutane suke wasu da tausayi wasu kuma suna mamakin zallar wautar sa, akan mace zezo da mutuncinsa yana kuka a cikin ja'ama me hakan ze amfana masa bayan aure dai an daura, wasu ne suka shiga dagashi suna bashi baki akan yayi hakuri ya qaddara cewa ba matar sa bace tun usuli kar yayi sabo se Allah ya bashi wata data fita alkhairi. "Babu bana tunanin har akawi wata mace da za'a musanyamin da ita da zata fi Hamdah, ku taimaka ku roqeshi ya barmin ita na tabbatar da nafishi buqatarta wallahi ku taimakeni". Se kuma suka fara masa kallon zautacce dan sunga abin nasa kuma ya zarta na hankali, ta ya zaayi mutum daga daura masa aure ya sakar maka matar ka aura dan haka kawai suka fara fashewa suka barshi a gurin. A cikin Haka Yusuf ya biyo ta gurin idonsa yasauka kan abokinnasa dake kuka tamkar Ammi ta mutu. Cikin matukar mamaki ya qarasa kusa dashi ya ma kasa bude baki yai masa magana, wai yaushe ma yadawo daga ina yake yanzu wama ya gaya masa ana daurin auran? Tambayar daya ringa wa kansa kenan amma babu damar yinta a lokacin dan haka ya shiga kokarin dagashi subar gurin dan tuni wasu har sun fara video Abin mamaki.


Wata irin matsanan ciyar faduwar gaba ce tazo mata daidai lokacin da Goggo Suwaiba matar Baban Mumcy ta rangada mata guda a tsakiyar kai hakan ya tabbatar mata da cewar tazama matar Abdulmalik, wayarta dake gefenta ce da dauki kara alamar alamar kira Malik din ne' yake kiranta kuwa jiki a matukar sanyaye ta kai wayar kunnenta bayan ta amsa ta mike dan gujewa hayaniyar gudar da suke ta rangadawa da Addu'ar zaman lafiya. Sallama tayi masa ya amsa cikin tsananin farin ciki "Hamdah ta a yau kin zama mallaki na kin zama matata Hamdah Allah ya amsamin addu'ata burina na duniya sun cika Hamdah banqi ko a yau Allah ya dauki raina ba nasan na taba mallakar ki a matsayin mata, Allah ya sada ni da dukkan alkhairan da suke a tare da ke Hamdah, Ina fatan Allah ya azirtani da zuri'a dake Hamdah inasonki bansan irin farin cikin da zanyi a yau ba i still can't believe it kin zama tawa". Haka kalaman Abdulmalik masu kama da feshin wuta suka ringa dukan kunnanta. Be damu da shirun data yi ba ya kashe wayar gaba daya babu ko digon damuwa a ransa Dan a yau jin kansa yakeyi he is the happiest person on earth to shi meze dameshi bayan Allah ya mallaka masa autar mata?

Jiki babu kwari ta isa jikin window dakin ta janye labule tana kallon harabar gidansu har zuwa kan titi mutane tamkar ana hawan sallah ga kade kade da bushe bushe harda Jiniya ta ko ina. Ko kadan bata kula tsokana da wakar Tazama tazama da cousins dinta da suka biyo ta suke tayi mata ba dan kwakwalwarta ta tafi hutun wucin gadi ne a lokacin. " Hasbunallahu wani'imal wakeel" ta fada tana dafe kirji, indai ba gizo idonta keyi mataba Abdul'ahad ta gani shida yusuf mijin Maryam suna kokarin shiga mota. "Yaushe ya dawo? Dama har yasan ranar daurin aurenta amma beyi komai akai ba? Kenan maganar Yah Abubakar gaskiya ce daya ce in har da gaske yana sonta baze barta na kusan shekara daya be waiwayeta ba ashe ita take yaudarar kanta da cewa yana sonta" se kawai ta fashe da kuka, ture daurin kanta dayai bala'in yin kyau tayi ta kwanta akan gado tana kuka me ban tausayi. "Allah na tuba ka yafemin da yanzu na cutar da bawan Allah me sona dagaske, yanzun dana rabudashi na kama bilhu kenan? Abinda take saqawa aranta kenan ya qara sakata kuka. Ba irin rarrashin da ba suyi mata ba Amma taki shiru abin har ya bawa su Aysha haushi " Se kace akanki aka fara aure kome yau ko auran dole akai miki ai iya kacin abinda zakiyi kenan Hamdah tunda aka fara auren nan kawai kin bi kin dagawa bawan Allah hankali Kaman ba ango duk a rikice yake, sekiyi dagaske Allah ya bada sa'a tunda ke baki jin magana". Mumcy ce ta ke mata fada bayan da itama tayi aikin rarrashin ta gaji haka suka kyaleta kowa ya fice daga dakin ya barta.

Ango Abdilmalik ya shiga gidan da zugar abokanshi. Masha Allah yayi kyau sosai cikin Sky blue Babbar rigar daya saka bakinnan kaman ze yage tsabar dariya. Haka suka ringa ratsa mutane ana gaggaisawa se wulla ido yake yana neman ta dan bashi da burin daya wuce ya rungumeta a jikinsa a lokacin ya kirata da "Zauji". Wa cousin dinta ce ta lura dashi, yana durqushe gaban Goggo dake masa tsiyar ita ce amaryar ba wacceb babyn robar ba tace " Goggo ki kyaleshi an riga an rudeshi da farar fata da dogon gashi tashi in kaika inda Amaryarka take ka rabu da wannan tsohuwar" kamar wanda yake a kan qaya haka ya mike ba ko kunya yabi bayanta mutanen palour na ta masu tsiya, shidai be tanka ba dan a lokacin bashida wani burin daya wuce yaga Hamdah. Kukan ya tarar da ita tanayi abinda baze taba iya jurewa ba yaga hawayenta yana zuba, tuni ya aje duk wata surukuta a gefe, babbar rigar jikinsa ya cire da hula sannan ya haye kan Gadon ya dagota gaba daya ya rungumeta a jikinsa
"To ya isa haka haba duk kin bi kin gogemin kwalliya tun ban biya kudinta ba" ya fada yana kallon tsakiyar idonta. Hanky yasa yana goge mata hawayen Kaman wadda yasawa stop haka tai shiru tana kallonsa a zuciyarta tana tunanin da yanzu ta rasa shi, da yanzu ta rasa wannan masoyin ita kam wace irin sagegesuwa ta kusa tayiwa kanta? Ya mata kyau matuka dan tunda aka fara bikin beyi kyau irin na yau ba kayan sun matuqar amsarsa. Setaga kamar har wani haske ya qara amma kuma ya rame a sanin da tayi masa.
"Hey stop looking at me like this kar kisa nayi abin kunya a dakin surukata". Dukda mood din datake ciki seda ta harareshi sannan tace " In naqi fa me zakayi?"
"Let me show you" ya fada yana qoqarin juyata qasa setai tsalle ta tashi daga gadon tana dariya tace "Look at you bako kunya". Mikewa yayi daga kan gadon ya nufi gaban mirrow yana murmushi, at least he made her laugh, alkawari yawa kansa baze qara barinta ta zubda hawaye ba. Powder ya dauka ya qarasa gurinta har lokacin tana tsaye, shafa mata ya shiga yi tsaf ya gyara mata fuskarta harda qara mata lip gloss ya kama hannunta yana cewa "Ina dankwalin ki da veil muje ana jiranmu kar wadancan su ganemin gashin mata". Murmushi kawai takeyi ta nuna masa inda ta wullar da dankwalin se veil a kan bedside drower, gaba daya ji tayi damuwarta ta yaye wani irin sanyi yana shiganta sai ajiyar zuciya data ringa saki a hankali.

"Nidai na kasa Amma bari inyi miki irin Wanda naga kinyi ranar nan" ya fada bayan ya gama kiciniyar daura mata dankwalu ya kasa. Sosai taringa dariya kai bakace itace tagama shan kuka dazu dazu ba. Daurin ture kaga tsiya yai mata ya tsaya a gaba goshi kamar me tafiya dambe ya yi mata kyau sosai. "Haba Jaan yanzu se na fita da wannan daurin a yau" ta fada kalmomin a rarrabe. Seya bude idonsa yana kallonta, baze iya tuna rabon data kirashi da Jaan ba lallai ta fara komawa Hamdahnsa ta baya. Mayafin ya yafa mata har kai sannan yace "Eh mana duk Wanda yai magana kice masa Angon ki ne yai miki haka yake so ya ganki" dahaka ya riko hannunta suka sauko kasan.
Masha Allah kowa yake fada bayan sun gama hotunan ne angwayen suka wuce gurin reception. A daki kannen Mumcy da kawayen ta suka sakata kowa da kalar tata nasihar kafin yar Sudan ta shiga aikin shirya Amarya Dan da wuri za'a kaita saboda gidan su Ango sun shirya Dinner da daddare.
***************************
Durkushe take a gaban Abbah, wani farin lace ne a jikinta dinkin riga da skirt dayai matukar karbarta ya fito mata da shape sosai. Tsaf aka lullubeta cikin wata hadaddiyar laffaya fara me adon duwatsu golden fuskarta babu ko digon kwalliya hakan ya qara fito mata da ainihin kyanta kana kallonta sak Amaryar me cikakken gata. kafatanin yayyenta na zaune sun a falon shiru bakajin komai se shashshekar kukanta. Abbah ne ya katse shirun ta hanyar cewa "Akwai me sauran magana ne?" Gaba daya suka amsa masa da "Aa".
" Masha Allah Zahra zo ki kama yar uwar ki kuje gurin Mommynku Nidai nagama nawa Allah ya sa Gidan zaman ki kenan Ina mai karayi miki nasiha da hakuri, karki gaza kiyi hakuri akan dukka lamuranki insha Allahu bazaki tabe ba".
A gefen gado suka tarar da Mumcy Haj zainab Aminiyarta da Anty Amna sun sakata a tsakiya suna magana Wanda shigowarsu ta saka su yin shiru. Hannunta Haj zainab ta kamo tana cewa
"Ai Zahra dama kun wuce kawai baki dawo da ita ba".
"Mama Abbah ne yace a kawo ta suyi sallama Ai" cewar Zahra.
Zaunar da ita tayi a kasa daidai kafar mumcy da taki koda dago kai ta kallesu tace "Toh Maryam ga yarki tazo miki sallama". Wani bangaren daban ta kalla dan ji take kaman kukan datake dannewa ze fito tace sannan tace "Ai nagama gaya mata duk abinda zan fada aje ayi Hakuri Hamdah Banda kai kara ko gayawa kawaye sirri bani ba ba Zahra ba kar inji maganar mijinki a gun kowa Allah yayi miki Albarka ni dai na yafe miki duniya da lahira....."kuka ne ya kufce mata tai saurin mikeqa ta fada toilet. Ai nan sabon daru ya barke Dan Hamdah ta dage Idan Momynta bata fito ba bazata tafiba da kyar Abbah da yaya Abubakar suka fita da ita tana kuka kamar wadda zasu kai kabari, fasa saka ta A motar daukar Amaryar yayi ya ce "Saddiqu dauko mukullin mota ta kawai da kaina zan kaita". Tana jikin Yah Abubakar tana kuka har suka dauki hanya, tana jin lokacin da Abbah ya kirshi akan ya jirasu a gidan gaahi nan zuwa.
Sun isa gidan nata dake kusan hade da gidan su Abdulmalik din duk cikin unguwar ta sharada NNDC. Har kan katafaren gadonta Abbah ya zaunar da ita sannan ya kalli Abdulmalik da kamar anyi masa bushara da Aljanna yace "Abdulmalik ga Amanata nan basai nagaya maka matsayinta a gurina ba ina fatan zaka rike min ita dakyau kaman yanda nayi tunani daga gareka".
"Insha Allah Abbah zan kula da ita sama da yanda zan kula da kaina". Cewar Abdul din yana sosa kai. Gajeriyar nasiha ya qara yi musu gaba daya duk akan hakuri sannan yai musu sallama suka tafi abokan ango se yaba dattako suke irinna sirikin abokinnasu.
Se bayan tafiyarsu yan rakiyar Amarya suka karaso kowa nata santin gida. Su Haj zainab ne da wata yar Abbah suka shiga da ita cikin main house din dan dama abinda suka so yi kenan badan da kansa ya kawota ba, sun samu kyakyawar tarba daga dukka matan gidan da dama suna jiran zuwansu daga nan suka mayarda ita gidannata. Se Bayan da suka idar da sallar magriba tasake wanka me kwalliyar da aka dakko ta shiga zayyana duk wata fasaha da Allah yai mata akan fuskar Hamdan daga nan kowa ya fara shirin Dinner Ango kansa yana can yana tsatso nasa kyawun dan yace baze yarda kullum ta fishi kyau ba.
Dinner ce aka shirya ta manyan mutane ba kadan ba Guri ya tumbatsa domin an shiryata ta ta shiryu, Hajja Fattu tayi matukar kokari gurin ganin

Please Login or Register in order to submit comment