Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

see her, my Daddy is always telling me about her please" ta qarasa tana hade hannunta alamar roqo. Seta qaqalo murmushi ta dora akan fuskarta sannan tace "Ok Jawel i will take you to ur namesake, whats Your name again"?
"My name is *_AYSHA HAMDAH ABDUL'AHAD GALADIMA_*" Yarinyar ta fada cikin murnar za'a kaita gurin namesake dinta.

Bata buqatar sauran qarin bayani tabbasa wannan SIR GURU ne, kuma wannan Matarsa ce sannan HAMDAH yarsa ce, se kawai taji wasu hawaye sun shiga sakko mata da bata san na menene ba tana fara kukan ya mike tareda daukan wayarsa, idonsa akan matarsa yace "Zanje na dawo take good care of Hamdah ok" ya juya yayi tafiyarsa.



🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 2⃣9⃣

Da kallo ta ringa bin Ni'ima dake ta faman doka mata murmushi, at last yau taga Hamdah, Hamdan data hanawa mijinta walwala. Matar da tayi awon gaba da dukkan farin cikin Mijinta. A tsahon zaman auransu tasan Gangar jikinsa kawai ta aura amma zuciyarsa tana tare da wata duk da hakan ba wani damunta yake sosai ba saboda ita take sonsa, ta sani tausayine yasa ya aureta ba wai dan Soyayyaba kuma har zuwa yanzu bata da yaqinin ya karbeta a matsayin masoyiyarsa.
"Ina ta jin labarinki a bakin Dadyn Hamdah dama nace duk randa muka zo Nigeria sena nemeki se gashi bani da rabon shan wahala na ganki ma a free" Ni'ima ta fada tana qarewa Hamdah kallo cikin yaba kyau da kyawun surar da Allah ya mata. Tabbas ta isa a sota, ta isa ta dauke hankalin ko wanne namijin da ya isa da kansa, ayanda take ganinta a hoto se taga har tafi kyau a fili dan tuni ta haddace kamannin Hamdah tsaf saboda yawan hotunanta a cikin gidansu. Tabbas da ace ta kasance cikin mata masu tsananin kishi da batasan yanda zata kaya musu a wannan haduwar ba, kilan da se ta kasheta duk hukuncin da za'a mata sedai ayi mata shi. Tana matsayin matar Abdul'ahad ne kawai kuma uwar yarsa bayan wannan bata da sauran wani matsayi a gurinsa ta sani. Kallon yanda Hamdah Karama taketa liqewa Hamdan take wani tunani ya darsu a zuciyarta, irga kwanakin da take ganin su suka rage mata tayi a zuciyarta ko ba komai rabin burinta ya cika taga Other Half din Abdul'ahad, abu na qarshe shine ta sake hadasu, su zauna a karkashin inuwa daya ma'ana a matsayin ma'aurata.
"Zaki iya hada miji da ita, zaki iya jure kallon Abdul'ahad yana nuna mata irin soyayyar da kikayi kwadayin samu a gurinsa" zuciyarta ta shiga tambayarta, setaji hawaye na neman kawo mata dan haka ta miqe tana tambayar Maryam Toilet, Bedroom dinta ta kaita sannan ta dawo gurin Hamdah data zauna a zahiri hankalinta yana kan Little Hamdah dake ta faman zuba mata surutu a badini kuwa ta kusan zuwa China a tunani, tunanin da takamaimai bata san name takeyi ba.

"Hamdah nasan zaki ga laifina wallahi nima bansan....." Seta katse wa Maryam din magana tace
"Baki laifin komai ba Maryam, kilan keda mijinki baku san kasancewar mu tare. Amma meya sa baku gayamin yayi aure har ya haifi ya ba? Meyasa duk lokacin dana tambayeki ko Yusuf se kucemin baku san inda yake ba? Maryam cewa fa kikayi rabonki dashi tun muna makaranta meye ribar boyemin da kukayi" se ta dakata saboda fitowar da Ni'ima tayi, Hawayen da suka fara sakko mata ta shiga gogewa Little Hamdah na tayata dukda bata gane komai, Zaman mayafin kanta ta gyara sannan ta dauki jakarta da key din motarta ta nufi kofar tana cewa "Na tafi zan aiko Hamidah anjima ta karbarmin kayan kawai" bata saurari magiyar da take mata ba ta sa kanta waje a zuciyarta tana tunanin if Maryam is truly her Bestfriend. Cikin motar ta shiga ta zauna amma ta kasa kunnata se kawai ta kifa kanta akan stirring ta saki kuka me ciwo, tsohor Soyayya ce taso mata akansa, da kadan da kadan take tuna wancan lokacin, kalamansa daidai da suke da mugun tasiri a zuciyarta da bata taba mantawa dasu ko sau daya ba, ashe ita take shirmenta, ita take tunanin akwai wata *RUBUTACCIYAR QADDARAH* a tsakaninsu. Ita take ganin kamar wata rana zasu zama abu daya, Ashe duk shirme takeyi tuni yayi aure ya manta da babinta a rayuwarsa. Kila ma ko ganin daya mata yanzu be gane ta ba shi yasa ma yayi tafiyarsa.
Haka taci gaba da kukan da babu me rarrashinta.

****************************************

Tacikin Mudubin motarsa yake kallonta saboda glass dinta masu haskene bata rigada tayi musu Tint ba. Duk saukar hawayenta daya yana jinsa kamar digon Dalma akan zuciyarsa ne amma yaya zeyi? Ya rigada yayi wa kansa alkawarin cireta daga zuciyarsa tunda dai bashi da Sa'a, a koda yaushe baya taba zuwa a daidan lokaci se wani ya rigashi Fara gini tukunna. Be manta da Hamdah ba, abubuwa da yawa sun faru dashi bayan rabuwarsu wanda sedaga baya yake ganin duk laifinsa ne. Shi yayi saurin Cire tsammani yaja da baya a filin daga, ya sani da ace ya saurareta a wancan lokacin da kilan abubuwa basu tafi akan yanda suke yanzu ba amma yaya zeyi? Qaddarar Auran Ni'ima da Haihuwar Little Hamdah ce ta saka shi wannan fushin zuciyar ya tafi akan abinda befi ya dauke shi a matsayin wasa ba.
Ji yake baze iya jure kukan nata ba, har yakai hannu ya bude motar da niyar zuwa ya rarrasheta sedai ko me ya tuna se kawai ya maida kofar ya rufe. Ganinta a yanzu ya qara hura wutar soyayyrta a zuciyarsa da wani bala'in kishinta. A duk lokacin daya tuna ta taba aure ji yakeyi kamar ya kashe kansa tsabar kishi. Harga Allah yaji dadin Mutuwar Abdulmalik, abinda ya hanashi dawowa rayuwarta a lokacin uzurine babba wato Matarsa.

Ni'ima Amana ce a hannunsa, tana cikin wani yanayi da baze iya tsallaketa ya tafi gurin wata mace ba amma hankalinsa da tunaninsa akoda yau she suna Kan Hamdah, dalilin daya saka wa Tilon Yarsa sunanta kenan saboda yaringa tunawa da ita duk sanda aka kira sunan yarinyar. Lokacin da Yusuf ya sanar dashi shirinta na sake aure ya shiga yanayin dayafi na baya muni, a kullum yana jiran ta kirashi, tace ya dawo, tana sonsa za kuma ta aureshi amma yau tsahon shekaru biyar kenan wannan saqon be isar masa ba gashi wai yau saura Kwana uku ta daura aure a karo na biyu da mutumin da be cancanceta ba, mutumin da kyau da surarta ne kadai suka rudeshi bawai dan yana son ta ainihin ita din ba dole yasan abinyi, dole ya dakatar da wannan auran baze yarda ya qara rasata a karo na biyu ba, se ya balle murfin motar ya fita cikin zafin nama irin nasa ya qara sa jikin motarta ya bude

"Fito ki koma can" ya fada cikin sigar umarni. Seta dago idanta da suka canza kala ta kalleshi tana so ta tabbatar da shi yayi maganar ko yaya.
"Zaki fito ko na fiddoki da kaina" ya qara fada yana dage mata gira daya. Se kawai ta mayar a kanta ciki ciki take magana
"Idan Motarka ce ai seka zo ka fito dani mutum se isa da iko kamar ya haifi mutane" ta manta da kaifin Ji irin na Guru se kawai ji tayi ya sunkuya ya tattaro kafafuwanta gaba daya yayo waje da ita daga cikin motar
"Kina yi min ihu ina maimaita abinda ya faru 5 years ago". Dole ta ja bakinta tayi shiru har ya zaunar da ita akan kujerar me zaman banza sannan ya zagaya yashiga motar
"Da alama kin manta ba'a daring dina Yammata, waima me kike ci kikayi nauyi haka ji yanda duk kika sa hannuna suka sage" ya fada hankalinsa akan tuqin dayake kai bakace ma da ita yake magana ba.
Harararsa tayi qasa qasa sannan tayi qaramin tsakin ai kuwa ya dalle mata baki da hannunsa yana cewa "Naga alama ke auran ma rashin kunya ya qara koya miki harda yimin tsaki senayi maganin wannan bakin naki naga alama tunda bashi da control". Bata kulasa ba se shafa inda ya bigeta da take tana masa Allah ya isa a zuciyarta har ya wuce Gadar Kabuga taga yana shirin daukar wata hanyar daban.

" Malam ina zaka kaini nifa gida zanje" ta fada cikin zafin rai, seya kalleta yayi murmushinsa da iyakacinsa gefen baki ba tareda ya bata amsa ba yaci gaba da tuqi abinsa zuciyarsa fes kamar an wanketa da Hypo, ganinta zaune a kusa da shi yafi komai dan haka yaringa yawo dasu a gari kamar sun rasa abinyi, shiru tayi masa dan tayi alqawarin bazatayi masa magana ba in yaga dama su kwana suna garari a titi be dameta ba. Wayarsa ce ta shiga ringing, 'Wife' ta gani akan screen din seta dauke kai lokacin da shima ya juyo ya kalli wayar, murmushi yayi dan yaganta sarai yanda ta wani harari wayar kamar matar tasa ce a gabanta se ya daga tareda saka wayar a speaker
"Hello Yaya Abdul ina ka tafi ne muna ta jiranka gashi har Hamdah ta fara rigimar namanka and wai Aunt Berbie din ta tafi" Ni'ima ta fada cikin murya me nuna tsananin rauninta ko kuma wani yanayi na rashin lafiya.
"Bana hanaki doguwar magana ba" ya fada batare da ya amsa mata tambayarta ta farko ba.
"I'm sorry Sir" ta fada tana murmushi, se yace "Bawa Angel wayar". Miqawa Hamdah wayar tayi ta kuwa karba da saurinta
" Daddy where are you come back please lets go and find Aunt Berbie she left Uncle Yusuf's place" cikin siririyar muryarta me dadi take magana cike da shagwaba. Kwaikwayon muryarta yayi shima yace
"Don't worry Angel Daddy will bring Aunt Berbie home soon and she will forever stay with us you hear?"
Tsalle ta farayi tana murna ta shiga gayawa Mamanta Daddy yace ze kawo musu Aunt Berbie da ita zasu koma UK, murmushin karfin hali kawai Ni'ima keyi sukayi sallama ta kashe wayar. Duk yanda taso taja Maryam da hira ta tambayeta wani abu akan Hamdan qi tayi daga qarshema excusing dinta tayi ta tafi dakinta ta kwanta tunda basu saba bama, yau ita ma ta fara ganinta.

A bangaren su Hamdah kuwa seda aka kira sallar magrib suka dauki hanyar gida lokacin kamar zata fashe zabar fushi. Wani rainin hankali ya kwace mata wayoyi ya kashe ya zuba su a aljihunsa. Duk yanda yaso ya jata da magana banza ta masa har abin ya bashi haushi shima ya shareta, seda suka zo kofar gidansu ta kalleshi ganin ya samu gefe yayi parking yana jira ta fita seya tuna mata da haduwarsu ta qarshe ranar daya dawo da ita daga school da magriba kamar irin lokacin,
"Ka fita ka hau Napep zan shiga da motan ciki". Seya kalleta yana jin sonta yana fizgarsa adukkan daqiqa, ji yakeyi kamar ya janyota jikinsa ko hakan ze rage masa radadin missing dinta dayakeyi, kujerar ya gyarawa zama sosai ya kwanta yana cigaba da mata irin kallon dayake ladabtar da ita a shekarun baya, akwai abubuwa dayawa daya kamata su tattauna akai amma bayanzu ba har se yayi nasarar dakatar da wannan auran da take shirin daurawa amma ta yaya? Dole ya nemi lokaci su zauna da ita to amma besan kwanaki nawa ya rage auran nata ba dan haka se yace mata
" Saura kwana nawa ne ki qara daura auran Bazawara".
Tunda ake gaya mata kalmar bata taba mata muni irin na yau ba, ita Abdul'ahad ze kalla ya kira da bazawara lallai wato ya goge shafinta kenan tunda har tayi aure, se kawai ta saka masa kukan da take ta dannewa.
"Ya haka kuma daga magana se kuka kamar Matar Mamaci, ops namanta ashe ita ce to kiyi shiru dan Allah inkin shiga ciki se ki ci gaba karki saka min ciwon kai". Ai seta qarawa kukanta volume dama neman yinsa take yanzu kuwa ta samu dalili, " Bazata girma ba halinta yana nan" ya fada cikin zuciyarsa yana dan murmushi, hannunta ya kamo yana murzawa a hankali wani irin electrification na shigarsu dukka biyu
"Nifa wasa nake miki magana shine zaki fara kuka ni mantawa nayi da halinki naje na sakawa yarinyata sunanki gashinan itama ta zama fitinanniya irinki bata da aiki se gagara". Harararsa tayi tana murguda masa baki batayi dai magana ba, peck yai mata akan lips dinta dasuke matuqar birgeshi sannan yaja da baya yana cewa "Tashi ki fita please nasan Matata tana can tana jirana nasan ta fara missing dina" ji tayi kamar ya caka mata mashi akan zuciyarta, wato matar sa tana jiransa dan haka cikin zafin rai tace "Ai ba daure ka nayi ba bakuma nace ka biyo ni ba, se ka tashi ka fita ka bani motata".

" Yi hakuri Hajjaju ba guduwa zanyi ba ina zuwa gida zan bayar a dawo miki da ita kin san ni ba dan fashin mota bane da in na dauka bana dawowa da ita" ya qarasa yana kashe mata ido daya. Wata bala'in kunyarsa ce ta kamata, ashe be manta da motar sa ba, cikin son nade tabarmar kunya tace "Nima ai ba Sata nayi ba kuma all this while motan ka tana nan a ajiye yanzu ma jira a dakko maka ka tafi da ita" se ya katseta yana cewa "Aa ai ni kuma bana maimaita aji, innayi gaba na tafi kenan ki riqe ki qarawa wannan baqin mijin da zaki aura tunda naga ke baya kika ci gara ma wancan ya kai ki nunashi a matsayin miji wannan kuwa sedai ki ringa boye shima har na tausayawa yaran da zaki haifa I'm sure se sun ringa questioning naki akan meyasa kika aure shi wai ma saura kwana nawane" yanda yake maganar ze nuna maka zallar kishin da yake cinsa.

Rainin hankalin nasa ya fara yawa, mijin nata zece wa baqi se kace shidin farine ne dan haka taja jakarta da wayoyinta daya dora mata akan cinya ta bude motar sannan tace "Seka aika a tambayo maka ai kuma koyafi Coal baqi a haka nake sonshi yafi min kai sau dubu" ta fice daga motar.

Lokaci daya idonsa yayi Ja, jijiyoyin kansa suka tashi rudu rudu. Wace irin kiyayya yarinyar nan take masa ne haka, wacan lokacin ma fa haka tace masa, meya ragu dashi, menene bashi da shi da bazata soshi ba fisabilillahi. Harya koma gidan Yusuf yana wannan tunanin a zuciyarsa, mamaki fal ya cika Ni'ima da Yusuf daya fito rakasu dayaga motar da Hamdah tazo da ita dazu, kallonsa kawai ta ringayi lokacin dayake bawa Yusuf saqon ya kaiwa Hamdah motar gobe sannan ya karbi little da tayi bacci daga hannunsa ya sakata a mota. Ko a hanya babu wanda yai magana a cikinsu, dukda tarin tambayoyin da take dasu amma babu fuska, tasan dole za'ayi haka dama yanzu kam dolenta ta nema masa mafita kilan hakan ya tabbatar masa da irin qaunar da takeyi masa, zatayi koma menene dan taga mijinta yasamu cikon farin cikinsa koda kuwa hakan yana nufin rasa nata. Number Hamdah data dauka a wayar Maryam batare da sani ba ta qara dubawa ta tabbatar tana nan yanda take sannan ta kalleshi tausayinsa na ratsata.
Tasan so, dan haka bata ganin laifinsa akan duk abinda yakeyi ita ma irin yanayin da take ciki akansa kenan, ita take sonsa, ta sani ya aureta ne kawai badan yana sonta ba sedan tausayi dan haka tayi alkawarin sadaukar masa da nata farin cikin ta nemo masa nasa ko ta halin yaya kuwa.











🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 3⃣0⃣

Tafi awa biyu da kwanciya amma ta kasa bacci, Wani irin ciwo takeji har cikin zuciyarta kamar ana hura mata wuta. kallon Abdul'ahad dayake ta faman aiki a cikin system dinsa tayi tausayin kanta na dada kamata, se kawai ta saka kuka abinda kadai tasan yana janyo mata gaba dayan hankalinsa kanta kenan, tariga ta gane lagonsa ta wannan bangaren aikuwa babu shiri ya ture system din ya isa inda take a kwance ya dagota
"Menene Ni'imatullah, wani gurin yana miki ciwo ne" ya fada yana duddubata dan ya tabbatar da lafiyarta. Seta tsagaita da kukan har lokacin be bar tambayarta ba dan haka tace
"Ba kaine ba tun dazu ka shareni bakayi min magana ba na tambayeka meyake damunka kace babu komai" seya ja da baya yana dungure mata kai.
"Amma yarinyar nan kin rainani shine zaki fara kuka salon ki daga min hankali ko to ki tabbata sena hukuntaki kuwa" ya fada yana tashi daga kan gadon. Hannunsa ta riqe tashiga bashi hakuri amma ya shareta sema system din sa daya janyo ya ci gaba da abinda yakeyi.
"Yaya Abdul" ta kira sunansa idanunta akansa, ita dai Allah yasani tana son Abdul'ahad tun bata san menene so ba, tayi rainon soyayyarsa a zuciyarsa tun tana yar mitsitsiyarta. Seda ya gama abinda yake tsaf sannan ya juyo gaba daya yana kallonta
"Yadai Yammata kike kallona haka" ya fada yana dage mata gira daya, setayi murmushi tareda janye tagumin da tayi sannan tace
"Yah Abdul yau naga Hamdah, tana da kyau kuma tana da kirki Yah Abdul naji dadi sosai da Allah ya dawo mana da ita cikin rayuwarmu Hamah nata damuna Gobe ka kaimu gidansu mu qara ganinta kaji Yah Abdul dan....." Hannunsa ya dora akan lips dinta alamar tayi shiru sannan ya muke ya isa jikin wata yar Cupboard inda yake ajiye First Aid box dinsa, wasu magunguna ya dakko tareda ruwa mara sanyi sannan ya dawo kan gadon. Da kansa ya balla mata sannan ya saka mata abaki ta kora da ruwa ita dai se binsa kawai da kallo takeyi, irin wannan kulawar tasa ce take da da hura wutar qaunarsa a zuciyarta
"Oya kwanta" ya fada yana bubbuga pillow daya gyara mata, kwanciya tayi tana ci gaba da kallonsa tasan tunda yayi shiru baze bata amsa ba bata hakura ba ta sake cewa "Yah Abdul magana fa nake maka kayimin shiru".

"Wai Ni'ima ban isa na hanaki abu ki hanu sau nawa zance miki bana son yawan magana ne naga alama ke baki san mahimmancin lafiyarki ba da zaki ringa daukar abinda be shafeki ba kina dorawa kanki, kinga Hamdah nima na ganta se me? Se aka miki alkawarin aljanna ko yaya da zaki damu mutane, ki kwanta kiyi bacci in ba haka ba narantse sena bata miki rai yanda baki tunani" ya fada a fusace yana mikewa daga kan gadon ya shige toilet. Wani irin bacin rai yakeji a duk lokacin daya tuna ta, maganar data gaya masa ta masa zafi ba kadan ba wai me zatayi dashi seyaji kamar ya kashe kansa ya huta kawai. Ruwa masu sanyi ya sakarwa kansa yana sake nymfashi kamar wanda yayi tsere seda yaji nutsuwa ta fara saukar masa sannan ya daura towel ya fito lokacin har Ni'ima tayi bacci dan ba qaramin tsorata tayi da yanayinsa ba. Seda ya gama dukkan al'adun daya saba kafin yayi bacci sannan ya kwanta a gefenta yana kallon filuskarta da hawaye suka bushe da alama tayi kuka kafin tayi baccin. Hannunsa yakai ya taba wuyan ta babu zafi sosai dan haka ya qara gyara mata duvet din data rufa kafin ya qara gudun Ac,
Kwata kwata bayajin bacci, wata irin kewar Hamdah ce take damunsa ba kadan ba, duk fushin da yake da ita still yana sonta, yasan babu wani abu daze qara so a rayuwarsa kamarta. Ita kadaice macen dayakeji kamar dan shi kadai aka halicceta amma wani ya masa shigar sauri, ganin baze iya baccin ba ya saka shi tashi kawai lokacin karfe biyu harda minti goma. Alwala yayi ya fara jera sallaloli harseda ya fara jin baccin sannan ya dakata ya kwanta zuciyarsa fal da tuninta.
*************************

A bangaren Amarya Hamdah ma kusan haka take, tunda ta shige dakinta bata qara fita ba duk da bali'in yunwar datake ji. Ta chanza direction din kwanciyarta yafi sau goma amma ta kasa mata dadi to wai ma meyasa take tunaninsa? Ya kamata zuwa yanzu ta cire tareda goge duk wani abu daya shafesa a rayuwarta. Waie mayasa take kasa aiwatar da abin da tayi niyya in tana tare da shi? Meya kai ta reacting yanda tayi dazun har ya bagarar da ita kamar ma be gane ta ba yanzu kila matarsa tana can tana murna ya ganta after so many years ya shareta, se kawau ta saka kuka kamar wata yarinya kishinsa ne yake cinta bana wasa ba. Kodai ma ya fahimci tana sonsa har haka shi yasa yake mata duk irin cin kashin daya ga dama, in ta tuna yanda ta wahala a soyayyarsa, yanda ya kankame zuciyarta ya hanata sukuni a shekarun baya setaji ta ina ma bata faru ba, ina ma bata barshi ya shaci fili me girma haka a cikin zuciyarta ba.
A duk lokacin da tayi yunqurin auna nauyin soyayyarsa data Abdulmalik setaga bazata aunu ba. Tana ganin kamar Harda shaquwa da tausayi sukayi galaba akan ta da Abdulmalik amma Guru fa? Ta sani akansa ta fara experiencing abinda ake kira love at first site. Tayarda tsanar datayi masa a farkon lokacin daya Zo musu a matsayin malami ba komai bace illah so, tana kishin yanda Yammata suke kallonshi ako da yaushe. Duk lokacin dataji mata na maganar sa setaji kamar ta shaqesu ta ringa masifa da bala'i kenan akan me zasu ringa zancensa zama su sa yaringa jin kansa kamar ya isa alhalin babu inda yaje. Bata manta farkon zuwansa tun kafin ya fara koyar dasu wata rana Aysha take ce mata taga wani sabon lecturer "zaku dace wallahi Hamdah dama yace yana sonki irin mijin da kike so ne gashi yaro". Haka ta fitittike ta wanke Aysha tas akan me zata hada ta da wannan ranar da ta fara ganinsa kenan wai yana wani yauqi kamar Karuwa magana ma se yayi yanga wayasani ma ko dan daudu ne, rashin mutunchi kala kala ta ringa masa karshe har suna tasa masa wai Kichimilli se gashi yanzu Allah ya kamata akansa.

Ringing din wayarta ne ya katse mata tunani, Abdurrahman ne setayi banza da wayar bayan ta duba lokaci biyu har ta gota. Ci gaba da kira yayi har seda ya mata 3 missed calls sannan ya hakura ya turo mata da text message akan ta kirashi early morning gobe please wai he missed her sweet voice yau gaba daya basuyi magana ba. Tsaki tayi ta goge text din bayan ta gama karantawa ta rufe idonta a dole bacci ya dauke ta.

Washe gari bata tashi da wuri ba saboda baccin da bata samu ba jiya, missed calls ta gani barkatai na mutane da yawa Maryam ta kirata se Malama Hadiza da kuma Abdurrahman da tailor dinta da take da appointment dashi a safiyar zata karbi dinkunanta bata samu zuwa ba se wata number da babu suna ta kirata kusan sau hudu. Abdurrahman din ta fara kira basu wani dade suna magana ba saboda yana duba wani patient ne yace sukayi sallama. Wanka ta fara yowa dukda yunwar da takeji kamar zata fadi, tana cikin shafa mai number dazu ta sake kiranta se ta dakata ta daga tareda saka wayar a speaker batare da tayi magana ba.
"Assalamu alaikum" aka fada daga daya bangaren seta amsa saboda muryar mace da taji. Gaisawa sukayi sama sama dan bata gane waya ke maganar ba.
"Am Hamdah dan Allah in ba damuwa ina son zamuyi magana dake ne ki bani lokacin da zan sameki" matar ta fada daga dayan bangaren. Setayi shiru tana nazarin maganarta to wace ce haka da har take son magana da ita dan haka se tace
"Ba damuwa zamu iya yin kowacce magana ce a waya base mun hadu ba".
" Aa da dai zaki daure maganar tana da matuqar muhimmanci please i will be glad if you give me some little time out of your tight schedules " matar ta qara insisting. Seda ta danyi tunani na wani lokaci sannan tace mata
"Ok ba damuwa gobe yayi miki"
"Sure yayi min sosai a ina zan sameki and time please"
"Home, by 4pm" ta bata amsa. Se matar ta danyi shiru na wani lokaci dan bata san gidan su ba amma wannan ba matsala bane dan haka tace
"Ok insha Allah zanzo na gode sosai se kin jini" daga haka sukayi sallama ta kashe.

Straight kitchen ta nufa saboda yunwar da takeji, suna ta tambayarta meya sameta jiya tuna ta shiga daki bata fito ba se tace

Please Login or Register in order to submit comment