Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

why the sudden change?"
"Nothing kawai kaina ne naji ya fara ciwo".
"Ayyah najawo miki koh muje gida seki sha magani kuma ga wannan azazzala'un sekira takeyi" (tana nufin Afeeya). Ita dai da uhm ta bita dan gaba daya jitayi komai ya kwance mata. Ko gidansu Maryam din kin yarda tayi ta qarasa, a bakin titi ta ajiyeta da niyyar anjima in taji sauki zata je su qarasa abinda basu gama ba. Lokacin data shiga gida wanka kawai ta fada ko zata ji sanyi sanyi. Ta rasa meya cunkushe mata zuciya lokaci daya haka. Kwanciya tayi lamo kamar me bacci duk da yunwar data shigo da ita amma ta kasa fita taci abinci. Khaleefa dayaga shigowarta amma shiru bata fito ba ya tashi ya bita dakin, da ido ta bishi har ya kulle kofar fuskarsa dauke da murmushin tsokana yace "trouble seekern Mumcy yadai yau ko an musulunta ne an chanza hali". Kallo daya ta masa ta dauke kai tunda yaga haka yasan yau tsohon hali ne ya motsa. Dukda kasancewarta me Surutu amma tana da halin miskilanci wanda yawanci se wani abu na damunta, a qa'idarta bataso a dameta when she is alone. Tafiyarda da ta same ka on her own ta gaya maka damuwarta than kai ka tambayeta.
Haka ta ringa juyi akan gadon dan ko Abdulmalik daya kirata ce masa tayi they should talk later yanzu Bata cikin good mood sanin halin mutuniyar tasa ya saka shi ya kashe ya barta ta huta. Messaga ne yashigo wayarta Daidai lokacin datake kokarin ajiyewa kaman karta duba amma ganin number ba suna ya sakata budewa. "Warm greetings. I'm Dr AA Galadima I shall be in your training centre tomorrow for supervision.Thank you"
Shine abinda sakon ya kunsa. Kara gyara kwanciyarta tayi kawai aranta tana mitar waya turo mata wani Dr AA fisabilillahi haka ze zo ya tasa mutum a gaba da shegun tambayar ya aka haifeka, dole ta fito da duk wani jotting dinda takeyi ta fara karantawa inda bata gane ba tayi googling ko ba kumai bata so ya raina mata hankali.
***********************
Karfe tara a cikin Training lab Tayi mata, Casual Attaire dinta ta saka Arabian Chiffon gown maroon da kananan stones peach colour agabanta da tsakiyar bayan. Maroon veil din rigar ta rolling kanta dashi bayan ta kama tulin Baqin shinta da ribbon tayi parking a tsakiya irin Acucin nan. As usual babu ko powder a fuskarta, yanda ta dora well Ironed Lab coat dinta Se ka rantse wata Consultant ce. Shoe da bag dinta duka peach Sosai kwalliyarta tayi kyau.
Gaba daya bata da nutsuwa yau din, wani irin yanayi takeji ajikinta dan haka tayi shiru bata saka baki acikin hirar da sauran students din sukeyi. Kamar ance tadago karaf idonta ya sauka akan Dr GURU. A iya ganin datake yi masa a school bata taba ganinsa da wani kaya Wanda ba suit ba Gaba daya se ya sauya mata yau. Wata dakakkiyar shadda Hilton cream colour ce a jikinsa. Yanda ya kafa hula akansa tamkar wani sabon Ango. Sabanin da dayake barin Suma akansa yau taga yayi askin saisaye har fuskarsa ya qara gyara quarter million Sajensa. Tasan Guru yana da kyau he got the perfect skin tone kamar me wanka da Madara. A hankali take jan numfashi tana ajiyewa wanda ke cike da daddadan kamshin turarenshi lokaci daya taji tamkar an sauke mata wani dutse daga kan zuciyarta.
Kallon mutanen cikin Lab din takeyi majority dinsu Matane hankalinsu gaba daya yana gurin Harda mazan dan babu Hassada Yau kam Gayun Guru ya kai a kalleshi. A karo na uku Malam Garba ya maimaita HAMDAH AHMAD AMMANI wanda se alokacin tajishi shima saboda wata Halima data taba ta seta mike ta dauki jakarya da Log book dinta ta nufi inda taga sauran course mates dinta sun tsaya kaman an zare mata laka. kallonta yakeyi Amma seka rantse bemasan dazamanta a gurinba wata irin nutsuwa na saukar masa. Yau kadai ya yarda SO bala'ine dan acikin watanni uku haukacewa ne kawai beyi ba, Dole ta saka shi karbar supervision din kawai dan ya ganta suyi magana ba wai dan shi ya kamata yazo musu ba. Kamshin turarenta daya shaqa kadai ya masa maganin qishin ganinta daya addabeshi, he missed everything about this Damsel just 5month Amma jiyakeyi kaman ya shekara 10 beganta ba. Had it been he has the chance he would have hug her and feel her close to his heart ko ya rage zafin sonta dake neman zautashi.
Bakinta ya kalla That looks dry, nan take ya tuna da wancen incident din ya hadiye wani mugun yawu daya kusan sakashi ya kware dole Ya bude littafin gabansa koda kawar da tunin daga zuciyarsa ya fara abinda ya kawo shi. Daga yanda yake tambayarta tasan da gayya yake hakan Sosai yai bombarding dinta da questions dan kusan duk abinda ya tambayi wani seya nemi data yi masa karin bayani akai ita kuwa ta cuna baki Wanda hakan ba karamin kara rudashi takeyiba. Suna gamawa ya mika mata jakarsa akan ta kai masa mota to his surprise bata musaba ta karba tareda yin gaba kafin ya fito. Seda ya gama sallama da kowa sannan yafita tana tsaye kofar SS Wali tana jiransa Dan haka yayi gaba ta bishi a baya.
Daidai jikin motarsa suka tsaya irin kallon dayake jifanta dashi ne yasaka ta sauke kanta kasa ta shiga wasa da zoben hannunta dan bazata iya jure Eye contact dashiba. Wasu irin abu take ji suna fitowa daga idonsa suna shiga nata. Bata san meyasa she is restless around Dr Guru ba ta rasa wane irin Chemistry ne a tsakaninsu datakejin wani abu game dashi da ko Abdul dinta bata jinsa haka. Dukda bata kallonsa amma tanajin yanda Idonsa keda effect akan duk wata gaba ta jikinta. Tamkar scanner haka yake binta da kallo yanajin baze taba gajiya da kallon wannan halittar ba. Gudun zuciyarta ne ya qaru yayinda qafafuwanta suka fara rawa tamkar bazasu iya daukarta ba, ta gaji da tsayuwa dashi kamar wanda yake shirin tsafanceta gashi yaqi karbar jakarsa daga hannunta. Dakyar ya iya katse shirun dan be ki su kwana a haka ba cikin wata irin murya mekama data Wanda ya suma cikin mayen SO Kamar me koyon magana Haruffa a rarrabe Ya kira sunanta HA...M...DA...H!!!!
Lokaci daya tsigar jikinta suka tashi danjin sautin sunanta a bakinsa, be barta ta dawo daga shock din ba ya qara mata da "I missed you HAMDAH......."

2⃣0⃣2⃣0⃣








🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*By Maryamah* 💞💞
©2020


*PAGE* 0⃣5⃣


Dariya sosai ta bashi ganin yanda take zare ido tana kalle kallen gefe Kaman Me tsoron kar wani yaji abinda ya fada. He is totally lost Dan haka inma yace ze chanza zancensa kara fallasa asirin zuciyarsa zeyi. Hannayenta yariko yana kallonta straight in to her eyes sannan yace "yes I Miss you Miss Ammani, i missed your troubles, your voice, ur scent, infact I missed everything about you Hamdah". Ita dae inbanda kallonsa babu abinda takeyi, she couldn't believe it wai daga bakin Guru takejin wadannan maganganun, kalaman da a wurin Abdulmalik kadai take samun irinsu. Hure mata ido yayi tareda dage mata gira daya yace "yadai yammata kina admiring kyau nane ko, to kallon ya isa haka karki ragewa budurwata farashin saurayi".
Haka kawai seta Tsinci kanta tayi da jin haushin kalmarsa ta karshe "wai budurwarsa" se kawai ta dauke kanta gefe tareda turo baki sannan tace "Toh naga ai dai nawa saurayin ma yafika kyau Kuma shi Fari ne kawai irin wannan ne bashida shi" tayi pointing quarter million sajen sa.
Seda yayi karamar dariya yarintarta nadaga abinda yake Kara birgeshi da ita. ya lura duk maganarta is straight from her heart Dan haka yayi niyyar tsokanarta yace "Iye kice kina da saurayi oya gist me about him". Aikuwa Kamar me jira ya tambayeta nan tafara bashi labarin Abdulmalik da irin son da takeyi mishi.

At this point Bakaramin dauriya yayi ba gurin saita nutsuwarshi. wani masifaffen kishi ke cinsa, kallon ta yake yanda ta dage tana bashi labarin Abdulmalik din "bari ma nanuna maka picture dinsa" ta fada tana kokarin ciro wayarta daga jaka seyai saurin tareta "Aa you don't have to keda zaki kawomin shi har office ya gaidani" murmushi me kyau tayi "kuma fa haka ne sir zan kawo maka shi kaganshi sosai you will believe what I'm telling you". Gaba daya jiyai wata zufa na keto masa, in har tana son saurayinta haka toh shi a wanne matsayi? yake anya ma zata bashi damar gwada tashi sa'ar a matsayin masoyi kuwa? Gaba daya seyaji komai ya qulle masa, yanzunma shawarar Fahad ce akan yafara janta ajiki amatsayin Abota. Gashi daga farawa tana neman tarwatsa masa zuciya da kalaman daya kira da muggan kalami.

Hannunta dake cikin nashi ya matsa kadan tareda cewa "hey is ok lallai wannan guy din yayi sa'a daya samu irin wannan zukekiyar yarinyar". kunya taji Dan haka tayi saurin rufe fuskarta da hannunta da har lokacin yake cikin nashi tana murmushi. Wani irin shock yaji lokacin da hannunsa ya sauka akan fatar fuskarta, laushi da santsin dayaji baze misaltu ba se yai saurin zame hannunsa dan yaga alama tana so ta chanza masa layi. Kallon agogonsa yayi sannan yace "I get to go se mun kara haduwa Amma fa you didn't replay me"
Bude idonta tayi tana kallonsa sannan ta watsa hannu tace "What?"
Yana kallon Impression din kan fuskarta yace "I said I missed you bakice komai ba" yakarasa da muryar shagwaba Kaman me shirin yin kuka.
Ba shiri ta fara Dariyar yanda yayi kalan tausayi, "Oh dariya ma na baki ko?" ya fada yana rungume hannunsa a kirji har lokacin kallonta yakeyi. Seta tsayarda dariyar tata sannan tace "Ok what do you want me to say?"
"Tell me you missed me too mana" ya kara marairaicewa kaman me shirin kukan gaske. Wata Dariyar takeyi sosai Dan yanda yadage akan inbata fada ba zeyi kuka, dakyar ta daure tace
"Ok ok I missed you too shikenan".
"Are you sure" ya tambayeta
"Yes I'm very sure" ita dai she just say it dan dai kawai Bawai har zuciyarta hakan bane. Gaba daya bata da nutsuwa duk lokacin data ke a kusa dashi,
"Thank you dear take good care of your self you hear" Ya fada yana kissing fararen tiny fingers dinta daya rike a hannunsa. Setayi saurin zamewa dan abun nasa kuma ya fara bata haushi
Da "Ok sir" tabashi answer. Allah Allah take ya tafi. Motarsa yashiga Tareda yi mata key yana daga mata hannu. Samun kanta tayi da daga masa hannu Itama harya wuce. "Thank God" ta fada. Juyo wannan dazatayi sukayi 4 eyes da Abdilmalik daya kumbura kiris yake jira ya fashe, idanunsa sunyi ja tsabar kishi. Ba karamin tsorata Tayi da ganin yanayin saba dan tasan be iya fushi ba, yau Allah ne kadai ze kashe wannan rigimar gashi bata san iya abinda ya gani ba. Kila tun dazu yana tsaye Sir Guru ya riqe hannunta. Harta qarasa kusa dashi tana sake sake a zuciyarta da yake ita ma gwanace se kawai "Jaan yaushe kazo Ina nan narako sir guru shiya zo mana supervision bari na dauko bag dina mutafi" tayi gaba Kawai dan bata sa ran ze amsa ba kuma ko me ze fada baze mata dadi ba. Da kallo yabita kawai Har ta shige cikin building din yayi kwafa ya shiga cikin motar yana jiranta. Wato ita bata ma lura da bacin ransa ba ko kuma shareshi kawai tayi, zata dawo ta same shi seta gaya masa wane dan iska ne wannan data zo tana wangalewa baki suna dariya harda kama hannunta.
Yana wannan tunani tadawo se jin rufe kofan mota yayi. A masifance yajuyo yana kallonta, yama rasa ta ina ze fara. dakyar ya iya nemo kalmar "uban waye wannan na ganku tare kina washe masa bbaki har yana rike hannunki?"
Murmushi tayi kawai tana kallonsa.
"Oh dariya ma kikeyi wato ga dan iska yana magana ba" se kawai ta kwashe da dariya dan gaba daya fadan beyi masa kyau ba. Aikuwa Kamar ta tunzurashi nan ya dage ta inda yake shiga batanan yake fita ba. gajiya dajin fadan nasa tayi Dan haka tayi saurin saka hannunta ta sakalo wuyansa sannan tarufe masa baki da dayan hannun tayi pecking hannunta dake kan lips dinsa. Ta sani dole yayi shiru, kokarin cire hannunta dayai wa lips dinsu katanga yakeyi amma ta hanashi sema baya da tayi tana wani killer smile tace "not now dude". Seya koma jikin kujera ya kwanta kawai yana kallonta dan daga Dan Rainin hankali se Hamdah yarinyar dagama gane lagonsa.
"Easy mana haba se fada kake tayi haka kawai kasamin kanka yayi ciwo wai ma bana gaya maka lecturer dinmu ne fa. Sir Guru ne fa danake Baka labarinsa. Binta kawai yake da kallo yana jin yanda take tsarashi. Shi dai tasa jarabawar kenan Allah ya dora masa Son wannan yarinyar, tana da matukar tasiri akansa duk da yanda zuciyarsa ke masa kuna amma bayanda ya iya. Abu daya yasan yana maidata cikin hankalinta wato ya shareta dan haka ya janye hannunta Dagajikinsa ya tada motar suka bar asibitin hankalinsa kacokam ya maida kan tukinsa.
Yana jinta tana cewa Zata ci shawarma, seta suka zo kofar Down town ya ciro ATM car dinsa ya mika mata tunda tasan pin din. Seta tsaya tana kallonsa tabbas tasan ransa ya baci tunda har ze ce taje ta siyo abu da kanta. Abdulmalik din da saboda ita ya mayarda dukka motocinsa super tint karma a ringa ganinta. "Na koshi" ta fada a sanyaye . Ga mamakinta setaga ya maida ATM din inda ya dakko shi. Har sukaje kofar gidansu be qara ce mata komai ba. Yanayin parkingya cire lock din motar alamar ta fita kenan lalai abin nasa da gaske ne. Dole ta tattara duka nutsuwarta ta fuskance shi.
"Believe me I'm all yours Jaan, you have me. Wannan daka gani he is only my lecturer wallahi babu komai a tsakaninmu". Ya yarda amma yana so ya shigar da ita saiti sosai dan haka seya daga kafada tareda cewa "what ever". Se kawai ta saka kuka, mataki na qarshe kenan datasan dole baze shareta ba. Aikuwa tuni ya rikice yana bata hakuri. Yana son yarinyar to the extent baya iya daukan fushi me nisa da ita addu'ar sa kawai Allah ya mallaka masa ita Kuma yaga alama lokaci yayi da ya kama ta ta kasance agidansa tun kafin wasu su masa kwace. Kafin wani lokaci ya ware Dama kukan bana Allah bane suka shiga hirarsu Kaman basu taba samun wata matsala ba,juyawa sukayi siyo shawarma da Ice cream din bayan sun dawo ya ajiyeta ya wuce gida.

Kusan sati uku kenan da faruwar wancan incidence din, lokaci lokaci Dr Guru kan kirata wai su gaisa sannan har a whatapp sukan danyi magana lokaci lokaci Musamman in yayibposting wani abu that is related to Genetics field din dayake wanda itama anan take so tayi specializing to anan ne yake samun dama suyi magana sosai dukka inform of lecture. A hankali sabo ya shiga tsakaninsu, they are getting to know each other dan zuwa yanzu tasan abubuwa da yawa akansa. Gidansu, Kannenshi da Yayyenshi dukka tunda yana saka pictures dinsu. Ta fuskanci kaman shi Kadae Ne namiji a gidansu. Koda wasa bata bari Abdulmalik yasan alaqarta da Guru ba dan ma yanzu haduwarsu ba sosaiba . Ya fara aiki a wani Oil Refinery a Lagos, Duk da kaurin Albashin amma kwata kwata beyi murna da samun aikin ba, yaso ace wadanda yayi applying a NNPC na Kano ne suka fara fitowa amma yasan ko giyar wake yasha be isa yacewa Alhaji No akan wannan aikin ba.

Yasan Mahaifinsa mutum ne me alfahari, ya gina yayansa domin kaf dinsu babau me qaramin aiki. Hatta Me aikin Likita a gidansu Yana da asibitin kansa. A cewar Alhaji KAMAL DALA kudi sune maganin komai dan haka ze kashe ko nawa ne akan yayansa ya gina su su samu aiki me kyau yasan ze maida abinda ya kashe. Satinsa daya da relocating zuwa Lagos kullum suna manne a waya. Voice call, video call aikinsu kenan. Dama ita tuni ta dena zuwa wurin aikin dan haka tana gida kome yakeyi haka ze kirata suna hira yana aiki. A daddafe yai sati biyu yazo kano amma be doshi gidansu ba a hotel ya sauka yai kwana biyu ya koma dan yasan in yaje gida Se Alhaji yayi tsirensa in beyi wasa ba.

Bikin Maryam ya taso gadan gadan dan ma ankara wata daya akan original date din bikin saboda angon da yayi wata tafiya. Wannan satin ya kama bikin dan haka basuda zama, shiri sukeyi sosai Dan Ita ce zata fara aure a clique dinsu Burinta ya cika zata auri her dream Military Man. Yau za'ayi kamu, karfe 1am Dawowarsu kenan daga salon sun baje dakin Hamdah, dinkunansu suke dubawa da sukayi matukar kyau. Mumcy ce ta leka dakin tana cewa "yanzu ku yarannan baza ku tashi Kufara shiryawa ba bayan wannan kwalliyar aljanun kadai sekun bata lokaci".
Da daddaya suka ringa wanka inda make up artists din dasuka dauko suka fara tsantsara musu kwalliya. Amarya Maryam na dakin Mumcy Wai Hamdah ce zata mata make up tsautsayi inji Afeeya, matar da bata taba yiwa kanta ba wai itace zata yiwa Amarya lallai yau akwai kallo. Ita dai Maryam bata qi ba dan dukda bata taba ganin Hamdah tayi ba amma ta yarda da ita. Tasan bazata bata mata ranarta ta musammanba. Tun suna secondary Alkawari tayiwa Maryam din cewa ita zata mata Make up din bikinta A lokacin su Aysha nata dariya.
Tsaf tagama mata Make up din daya yi matukar kyau, ita kanta Maryam din seda ta kara kallon kanta dan batayi zaton ta iya make up har haka ba. Ita ta taimaka mata tashirya cikin hadadden din da aka kashe kudi gurin siyan shi kalan Dark brown Anyi mata Hadadden bridal skirt and and blouse. dauri tayi mata daya zaunu sosai Ya kuma dace da fuskarta sannan takarasa shiryawa. Silver jewerries din datayi anfani dasu ne suka kara kawata kwalliyar tata tayi kyau sosai.

"Wow bestie kiinganki kuwa ki zauna yanzu kafin nagama Nawa yakara blending " Hamdah ta Fada sannan tahau nata kwalliyar, within few minutes tagama dan ba wani me yawa tayi ba, girarta bata buqatar carving abinka da me kyau dama. Ashoebe da sukayi na Atamfa Peach ta saka ta daura dankwalita sannan suka rankayo zuwa kasan Inda sauran yammatan Amarya suke. Zokaga yanda ake ruwan flash Dan babu Wanda beyi Mamakin kwalliyar da Hamdan tayi Amarya ba. Tuni Harabar gidannasu tacika da Yammata wanda dayawa course mates dinsu ne ae secondary school mates dinsu se kuma few family da friends na Islamiyya da unguwa dan nan suka saka meeting point na Yammata sannan ga motoci nan jere A waje da Ango ya turo dan daukarsu zuwa wurin Kamun ba bata lokaci su ka fara tafiya gurin bikin, wata hadaddiyar GLK ce baka wuluk ta tsaya akofar gidan, ko ba'a fada ba sunsan Amarya akazo dauka Dan haka Malam Sa'idu ya budewa motar Gate ta shiga ciki dan dakko Amaryar. Ita da Hamdah suka fito ta riko hannunta har suka qarasa jikin motar ta bude mata baya ta shiga sannan ta juya da nufin bin su Afiya "Beatie ae tare zamu tafi" Maryam ta fada tana gyara zamanta. "Ok bari na karbo wayana hannun Afeeya" "No kibari ki karba in munje can". Dole ta bude Gaban motar tazauna.

Ko a bacci taji kanshin turaren Seta ganeshi ballantana ido biyu sedai kuma in hancinta ne yake mata gizo, hakan nema to meze kawo shi wannan Motar? Bata gama tunaninba muryar sa me sanyi ta kunnanta "toh Ango mu tafi ne ko baka gama santin kwalliyar Amaryar taka ba". Da sauri ta kalleshi Inda tajiyo muryar, Guru ne zaune ya hade cikin wata hadaddiyar Gezna fara sai maiko takeyi Ashe kallonta yake da wani irin expression akan fuskarsa data kasa tantancewa bata san lokacin da bakinta ya furta "ya salam".

2⃣0⃣2⃣0⃣


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE 0⃣6⃣
Gaba daya suka kalleta danjin yanda tafurta maganar da Dan daga murya. Maryam ce ta leko kanta tareda cewa"Yadai Bestie?" Seta girgiza mata kai kawai alamar babu komai dan batajin zata iya magana. Tuni zuciyarta ta fara irin bugun data keyi a duk lokacin da suke tare, kwata kwata bata da nutsuwa.
Murmushi yayi Wanda sautinsa ya sakata juyowa Shima ita yake kallo, tun dazun yake karantar yanayin ta. He likes it when she is retless yanayin da fuskarya ke nunawa yana masa kyau seta koma kaman wata yar baby dake shirin yin rigima. Key yai wa motar suka fita daga gidan, seda suka hau titi sosai sannan ya kalleta, "Kinyi kyau" ya fada seka rantse bashi yayi maganar ba dan ko data juyo hankalinsa nakan Titi. Tafiya sukeyi babu me Magana da Dan uwansa se Dan kuskus din Amarya da Ango da kake ji.A zuciyarta Mamaki takeyi meya kawo shi bikin Maryam? Da alama yana da matsayi a gurin angon ma tunda gashi shiya kawoshi. Se a lokacin take tuna yanda suke gaisawa da Maryam, afarko har zagin Maryam din takeyi akan tana shishshige masa ashe abokin saurayinta ne. Tsayuwar da motar tayi ne ya sakata kallon window har sun iso wurin bikin The Afficient. A jere a jere motocin suka ringa shiga gurin, Anty Fatima kanwar Mamansu Maryam dince ta karaso jikin motar cikin fada tace "wai wannan wane irin iskancine tun dazu kun shanya mutane Abin karfe uku gashi har biyar tayi anata jiranku".
Murmushi Hamdah tayi tana cewa "kiyi hakuri Anty kwalliya ce ta tsaida mu". "Kwaji dashi Kilan ma batayi kyau ba se ku shishshirya" tayi gaba abinta tana ci gaba da mita. Jeruwa yammata sukayi da abokan Ango bayan sun saka Amarya a tsakiya, Hamdah data gama shirya su tayi gaba abinta acewarta bazata bi yan rakiyar ba. Hannunta taji an riko ta baya "Hey yammata saurin me kikeyi Haj baki ganin yanda tsarin yake?"
Se ta harareshi bata da zabi yanda ya riqeta in ma tace zata qi karshe kanta zata jawa attention dole ta dawo suka jera. sune a kan gaba. Tafiya take amma gaba daya zuciyarta na can tunani na daban, ba tayi aune ba seji tayi tayi Tuntube da stairs din bakin kofar tana shirin faduwa.
Cikin zafin nama ya tarota ta fado jikinsa, yanda ya rude seka zata shine ya kusa faduwar, Dan har ya fita firgita "Be careful please waima tunanin me kikeyi zakije ki fadi kiyiwa mutane asara?" ya fada har Lokacin tana riqe a jikinsa. "Ai dai inna fadi ma kaina na fadarwa bakai ba ina ruwanka to" ta bash amsa cike da tsiwa. Se yai kaman ze turata Ba shiri ta qanqameshi dan duk ta tsorata "Mara kunyar banza" ya fada yana dungure mata kai kafin ya dagata suka ci gaba da tafiya "Kai agaskiya ku tafawa wadannan couples dan sun birgeni kunga inda ake tattali" muryan Mc Masanzie ta karade gurin. Se a lokacin suka lura da gaba daya kallo ya dawo kansu, har ansamu wasu nata daukan su pictures harda masu video. Dan sun burge mutane ba kadanba hadin ya hadu.
Da kyar ta daure suka karasa inda aka tanada domin zaman Babban Aboki da kuma Babbar kawa suka zauna. Duk se take jin ta a takure ido yagi mata yawa, gashi shima ya wani manne mata se cin magani yake kaman wanda aka bawa ajiyarta, yanda suke dab da juna har tana jiyo numfashinsa a gefen kunnenta ga kamshin turarensa da yabi ya addabeta. gaba daya a darare take, kusa da kunnanta ya matso yarada mata "kinga yanda Mutane suke daukan mu pics yakike tunani ranar namu bikin?"
Da sauri ta kalleshi irin kallon "kasan me kake cewa kuwa" . Gira daya ya daga mata seta dauke kanta kawai dan taga alama rainin hankalin nasa yafara yawa. wai me ya maida ita ne?
Kiran Kawayen Amarya da akayi ne Dan su yanke kudin kamu ya sata tashi. Bata qara yarda ta koma gurin ba cikin yammata ta shige suna ta having fun. Alhamdulillah

Please Login or Register in order to submit comment