Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dauke kansa tare da cewa "You were talking" murmushi tayi sannan tace "Yes i want to thank you nagode sosai now i just have to read through shikenan". Yanda take murna yasakashi jin dadi, for once ya faranta mata rai dan haka yace "Never mind kawai any time you need anything i will be there for you, you can leave now in da flash a hannunki kiyi copying in babu ki tafi da system din but make sure you return it dan ke ba'a baki aron abu ki dawo dashi".

Kasakasa ta harareshi sannan tace "Ai wancan ma ba ara nayi ba"
"Sata kikayi kenan" ya bata amsa. Bata tanka ba illah mayafinta data ware ta yafa ta suri Laptop din dan bata shigo da flash ba "Ji mana" ya tsaidata. "I like your Dress" kallon kanta tayi, doguwar riga ce Jallabiyya ta mata kirar Oman a jikinta me colar Neck da buttons a hannun kaman links na Maza, rigar ta boye komai na jikinta haka ma kafarta lofers ne Silver dan haka tafin hannunta da face dinta ne kawai a Bude, se kawai ta maida masa da "Thank you, you Look Good also". Ta juya ta fita. Kamar soko yaringa murmushi, he is seeing progress in the relationship Allah dai ya ida nufi. Gida ta wuce kai tsaye ta kwashe komai a System dinta, haka nan ta shiga ta ringa masa bincike pictures dinsa dana familynsa, Friends da dai sauran Hotuna. Babu hoton Single mace in banda na wadanda tasan kannensa ne se kuma wata yarinya daya dataga pics dinta da dan yawa. Ba laifi tana da kyau sedai ba fara bace, to ko ita ce budurwar tasa? To ma ina ruwana? Ta tambayi kanta. Seta koma kan videos, latest movies ta gani ta kwafi son ranta. Bata da abinyi a school ta san kuma ba da wuri ze tafi ba dan haka se karfe hudu ta koma makarantar.

A kofar office dinsa ta tarar dashi suna magana da wani Mr Bayero, bayan ta gaishe su ta nemi gefe ta tsaya ya hade rai tsaf yanda ya saba. "shi kuma haka yake, minti kadan yayi dariya minti Kadan Hada rai matarsa ta shiga uku" bata san a fili tayi maganar ba seda taji yace "Thank God kin sani seki shirya". Kallon gurin da yake tayi already Mr Bayero ya tafi dan haka ta bude front sit dinsa ta aje masa Laptop din. "Care for a Ride" ya fada dan yaga sanda me Napep ya ajiyeta. Ba gida tayi niyyar zuwa ba, daganan Hotoro zataje gidan wata kawar Anty Zahra zata karbo ma yaranta kayan da tayi order kuma yau kawai a Adaidaita take son yawo, seta ce "Aa ba gida zani ba ai na gode".
"Get in " yai commanding nata, dole ta shiga ya tada motar suka bar cikin Makarantar. Seda yaje Gate sannan ya kalleta "Ina zakije"
"Hotoro" ta bashi amsa.
"Wacce a ciki" ya qara tambayarta "Maiduguri road wurin Excel Collage". Har suka je dai dai inda ta kwatanta masa ba wanda yayi magana, time to time yakan kalleta ita ma haka. A kofar gidan ya tsaya ta shiga, bata jima ba ta fito da babbar Leda a hannunta. Yana zaune akan moyar yana waya ya hangota, sauka yayi ya karbi kayan ya saka a back seat sannan ya bude mata motar ta shiga suka dauki hanya "se ina kuma" ya qara tambayarta.
"Aminu Kano zaka ajiyeni, Hamida tana school bata dawo ba babu kowa a gida gara in je wurin Mumcy mu tafi tare". Dungure mata kai yayi yana murmushi yace "Sannu yar yaye wato gurin Mumcy to bazakije ba gida zan kaiki". Daga nan suka fara yar hira kadan, daidai Alpen store ya tsaya "Amm please Hamdah girlfriend dina ce zatayi birthday so ni gaskiya bansan duk girly girly abubuwan ku ba so i don't know if you can help me choose for her". Bata musa masa ba suka shiga gurin, "ki dibar mata duk abinda kike ganin ya dace dake she is just like you in terms of taste".
Kaya ta jida ba kadanba tunda yace Money is not a problem, tun daga kan cosmetics, perfumes, jewerries, chocolates, buscuits babu abinda ta manta. "Harkin gama" ya tambayeta "Aa ka tambayesu inda suke aje shoes da bags da Jallabiyya" murmushi yayi ya kira wani ma'aikacin gurin ya kaisu Sama inda kayan suke. Da "To da Ok" yake binta dan surutu take masa ba kadanba. Duk abinda ta dakko seta nuna masa tayi masa qarin bayani har suka gama. Data gama masa siyayyar yace ta dibar ma kanta taqi se Icecream kawae data dauka Babbar roba daya da Chewing gum Orbit. Trolleys sunyi hudu ta ciko da tarkace shidai ATM dinsa ya bada aka cire kudin aka Loda musu a bot suka tafi. Yana ajiyeta yai mata sallama ta shiga gida shi kuma ya juya dan Magriba ta kawo kai.

****************************************
03 March
At exactly 12 o'clock Message ya shigo wayarta "Happy birthday Hayatiii Allah ya mallakamin ke a karkashin inuwar Aure, banida sauran burin daya fi wannan. Enjoy your day have fun to the fullest". Shine abinda message din ya qunsa. Tasan ba Abdulmalik bane dan baya nan then who could it be? Ita shaf ta manta da yau birthday dinta m koma dai waye ta gode. Daga nan kira ya ci gaba da shigo mata dukka na well wishing, seda tayi sallar asuba sannan ta kwanta bacci.
Karfe tara take da Lecture Sir Guru, ranar kwalliya sosai tayi kodan its her special day. Bata makara ba course mates dinta nata wishing nata da tambayar ina cake dinsu a haka ya shiga ajin ya samesu. Ranar he seems happy. Class rep ya tambaya meya ke faruwa ya gaya masa that Hamdah Ammani ke birthday kuma bata siyo musu cake ba. Kallonta yayi sannan yace "Lallai kam we need to celebrate daga yau ma ya zama doka duk wanda ke birthday ajin nan ze zo ya kawo mana cake muci tunda bata yi ba i will take responsibility ina zuwa". Fita yayi about 20mins se gashi da katoton cake wani Baker yana binsa a baya harda stool, haka aka Dinga shigo da drinks da snacks kafin kace me class ya zama wani mini joint dan Harda Jam box a ka kunna kida a class din. Duk lecturer daya zo dan yayi magana dayaga Guru seya koma, masu irin halinsa suka joining aka ci gaba da sha'ani sosai. Anci ansha celebrant ta yanka cake da taimakon Sir Guru haka aka tashi taro lpy lecture da baayi ba kenan. Wannan abu yai publicizing relationship dinsu a cikin makaranta duk inda kabi gulmarsu akeyi, wasu suce sun dace yan hassada kuma su kushe.
Ranar Da murna ta koma gida to see another surprise waiting for her. Kayan da ta dibarwa Guru a matsayin budurwarsa zatayi birthday su ta gani a gidan wai wani ya kawo mata birthday gift. Tambaya kama ta shata gurin yan gidansu har ta rasa ta wanda zata amsa. Hamida ce tace "Lah yah Hamdah da alama an kusa ture Gomnatin dan Lele". Nan da nan hankalin ta ya tashi, she felt like tana cin Amanar Abdulmalik ne a lokacin tayi wa kanta alkawarin fita daga harkar Sir Guru amma ina washe gari data je office dinsa da niyyar taka masa birke se labari ya sha banban, muqus ya kashe mata jiki da irin kallon da yake mata, se rufe kofar tayi ta koma inda ta fito tana jin haushin kanta da kanta.
***************************
Satittika nata tafiya abubuwa da yawa suna ta faruwa, tuni suka fara project dinsu kuma luckly Dr AA ne supervisor dinta dan haka abubuwan sun zo mata da sauki. Shi ya zabar mata topic din on Genetics sannan ya bata duk abinda yasan ze taimaka mata a aikin nata wannan karon yace baze mata ba amma duk inda ya shige mata duhu ta zo ta same shi. A cikin hakan sabo ya shiga tsakaninsu bama Sabo ba dan takanji kaman she fall for his love. Dukda ba wai ta yarda bane tana ta'allaqa hakan da rashin Abdulmalik a kusa da ita dan sati biyu kenan yayi tafiya, ya tafi wani course ba 8 weeks a Morocco hatta wayar ma ba sosai suke samun yinta ba.
Ita da Sir Guru be taba furta mata kalmar So ba amma all his actions shows. Yanda yake kula da ita da kaffa kaffa da ita ya isa ya nuna maka nufinsa akanta. Duk wannan zafin kan ya ajiye a gefe duk da halin miskilancin yana nan amma dai da sauki yana sakarwa mutane fuska. Shirye shiryen Exam suke yi, sosai ta dage dan wannan karon tana so ta qarasa shiga first class ne and tasan zata iya. Ko a da dinnan bata so bane but yanzu with Guru's influence tana so tayi. Ya dage akan karatunta shiyake mata tutorials na kowanne course da bata gane ba, tuni Gulma ta fara yawa acikin School Saboda yawan zuwanta office dinshi. Wasu suce Ai soyayya sukeyi wasu ma sunce kawai Yaudararta yake yi yana rage lokaci da ita, a bangarenta ko sau daya bata taba damuwa ba tunda tasan duk rashin kunyar mutum be isa ya tareta ko shi ya fada musu ba sedai a bayan kunnensu.
Her First semester result was very successful Ta samu strong 4.89 CGPA dinta 4.75 tasan duk irin wasan da zatayi she will make it to her finals. Allah Allah takeyi ta turawa Abdulmalik dan yana mata bragging da first class ya fita daga university, yace ze gayawa yaransu that Momy ta Kasa Shiga first class ta maqale a 2.1 to dai se dai ya bada labarin wata ba ita ba. LOL

Daren ranar suna waya da Abdulmalik, kwana biyu ta rasa me yake damunsa bashida magana seta ta tayashi da addu'a Allah ya bashi ita. Ya ce mata wani lokacin yana ji a jikinsa kaman ze rasata seta ce masa "Haba Abdul kadai san ko mutuwa in tazo bazata dauke ka ta barni ba dan tasan halin da zan shiga na rashinka kama dena tunanin akwai wani abu fa ze raba mu a cikin duniya ko kana da kokwanto a cikin soyyar da nake maka ne?". Ya kan bata amsa da "Ko daya Hamdah na amince kina sona amma kiji tsoron *_RUBUTACCIYAR QADDARAH_* Ubangiji kadai ke iya sauyata. Ina sonki bana fatan Allah ya jarabceni na rasaki na tabbata daga ranar bazab qara moruwaba. Yanzu haka gangar jikina ce a Morocco amma ruhina yana tare dake Hamdah. Wallahi kece rayuwata" kukan Abdulmalik ne ya biyo bayan maganarsa. Ba shiri ta mike daga kwancen da take. Abdulmalik namiji ne me tsananin dauriya tasan ba karamin abu ne ze karya masa zuciya ba. To kodai yasan relationship din ta Sir Abdul'ahad ne? Aa inda wannan ne bazeyi shiru ba se ya mata magana tabbas akwai matsalar data ninka wannan.

Duk yanda zata tausheshi tayi karshe yayi shiru amma yaki gaya mata ainihin abinda yake Damunsa. Ce mata yai wai sonta ne ya masa yawa kuma ance in kanason mace da yawa baka aurenta, se tayi dariya "waya baka wannan philosophy din"
"Nima haka naji friends dina suna magana" dariya tayi sannan tace "to ba gaskiya bane koma haka ne Mu zamu karya wannan tarihin, ka gayawa kowa LAYLA DA MAJNOON din 21st century zasu karya tarihi zamuyi aure"
"Allah ya sa Hamdah na Allah yamallakamin ke bansan ya zanyi ba". Haka suka ci gaba da hirar su har tayi bacci.
2⃣0⃣2⃣0⃣

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*By Maryamah* 💞💞
©2020

PAGE 0⃣9⃣
"A ban garen Abdulmalik kuwa abubuwane suka cakude, bashida sauran hope a yanzu saboda ko a lokacin da ya tunkari Alhajinsu da maganar fata data yai masa. Nan take yace masa be amince ba, abinda yayi matukar tayar masa da hankali kenan Dan dama Hajja ta zana layin akan abun tuntuni tana da nata zabin datayi masa kuma tace indai be aure ta ba to sedai kowa ya rasa. Wadannan tunanin ne suka sashi gaba duk ya fige ya lalace ko karatun daya kaishi Moroccon be mayar da hankali akai ba. Kullum kirga kwanakin da suka rage masa Morocco da basufi 12 days ba. Allah Allah yake kawai ya dawo ayivme yuwuwa, a kwanakinnan yaga hankalinta ya fara karkata akan aure, be sani ba kodan sun kusa gama school ne. Tun dai waccan lokacin bata qara masa maganar ya turo ba so yanaso kafin ta waiwayeshi komai ya zama a kan tsari.
Two weeks after
Karfe 7pm tayi masa a gidannasu Hamdah. duk da rashin kirkin data shirya yi masa akan maganar turo iyayensa last week ya mata biris kamar ma besan ta fada ba. Ba qaramin tashi hankalinsa yayi ba ranar, yana zaune kawai ta kirashi wai Abbah yace ya turo, haka nan ya ce to ya kashe wayar jikinsa yayi sanyi dan be san wane bayani ze mata ba. Ya gaya mata me patents dinsa are against auransu daga nan ta tsaneshi ta fasa auransa ko kuwa wata qaryar zeyi mata? Tun daga ranar suke wasan buya data kirashi gaisuwa ce kawai ze taking excuae yace mata yana wani abun har ta fara Zargin akwai matsala. A nata bangaren kuwa hakan ne kadai take ganin ze mata katanga da Guru. Bata buqatar wani ya gaya mata ta tabbata ta afka cikin sonsa unconditionally amma bazata bari duniya tayi musu dariya ba. Bazata bari masu cewa Yaudarar Abdulmalik takeyi ba suyi galaba akanta, zata Auri Abdul insha Allah shiyasa take so tayiwa kanta tsakani da Guru by fire by force.
Jikinta ne yai matuqar yin sanyi da ganin yanayin sa. Abdulmalik din data sani Dan gayun Namiji meji da Ado shine ya rame yai Baqi ya lalace kamar wanda ya shekara yana ciwo. Fuskarsa ko arziqin gyara bata samu ba gashi buzu buzu da gani baya cikin hayyacinsa abinka da zuciyar da ta ginu akan soyayya nan da nan se ga Hamdah na kuka.
Sosai ya rungumeta ajikinsa yana jin wani kaso na damuwarsa yana raguwa, seda ta tsagaita da kukan nata sannan tafara magana "Meya sameka Jaan baka da lafiya dama shine baka fadamin ba, kaga yanda ka lalace kuwa kalla wuyanka kalla fa duk ka zama Baqi" ta qarasa tana shafa fuskarsa. Kiss ya kaiwa idonta masu kyau sannan yace "Dear I was all alone komai ya juyamin karatun dana tafi ma na kasa, Alhaji yaki yarda da maganar Auranmu haka ma Hajja please my love karki gujeni komai wahala kinji" yakarasa wasu siraran hawaye nabin kuncinsa.
Lokaci daya jikinta yai sanyi, seta kama Hannunsa ta riqe Sosai cikin nata sannan tace "Ur love is in my blood you know I can't live without you right? Put it at the back of ur mind Hamdah is yours and no one will change that fact expect Allah... zamu rayu tare kar wani abu ya qara daga maka hankali kaji Abdul dina". Kamar yaro haka yaringa daga mata kai dan yanzun kam har ta fishi dauriya. Wani bangare na zuciyarta ne yake gaya mata " kinga yanzu kin samu dama, babu me ganin laifinki ki rabu dashi kawai" dayar zuciyar ce ta kwabe ta da "Aa Hamdah karki zo ki aikata abinsa ze saka ki a dana sani, kiyi tunanin qaunar da kukewa junanku, wani hali kike ganin ze shiga?" Haka taita saqe saqe sedai tayi matuqar kokari wurin ganin ta saka shi farin ciki. Kalamai masu sanyaya zuciya suka ringa fadawa junansu tareda Alqawarurrukan zasu rayu da Juna for better for worse. Ya dade sosai dan har seda Abbah ya dawo da yake yana gari wurin shadaya na dare sannan ya mata sallama ya tafi. Ranar bacci qauracewa idonta yayi, tayi tayi ta yakice tunani daga ranta ta kasa.

Abubuwa sun chanza mata gaba daya basa tafiyar mata yanda take so. Duk yanda ta so data tsaida zuciyarta akan mutum daya ta kasa dan Zuciyarta ta kasu gida biyu equally akan kowannensu. Abun ya mata nauyi da har take gani bazata iya saukeshi ita kadai ba dole ta sanar da Mamanta kuma babbar kawarta. Wani yammaci Mumcy na zaune a dakinta bayan ta taso daga aiki, abinci take ci Hamdah ta shiga dakin dan haka ta nemi guri ta zauna tana jira ta gama. Tunda ta shiga dakin take kallonta ganin yanda tayi rama se dogon hanci da idonta da suka sake fitowa, se taga kamar har haske ta qara tabbas akwai abin da yake damun Yar tata ta dade da lura da hakan amma sanin halinta na zurfin ciki yasa bata tambayeta ba. Har tagama tana karantarta seda tasha ruwa tai hamdala sannan ta kalleta da murmushi tace "Farar mace Fitilar gida, farar mace Alkyabbar mata" irin kirarin da Abbah yake mata yau itama ta dana dole hamdah tayi murmushi sannan ta gyara zamanta sosai tana kallon Mumcy tace
"Mum wani abu ne yake damuna". Seta tattara dukk nutsuwarta tana kallonta tace " Inajinki daughter me ya faru?"
Tiryan tiryan ta bata labarin Guru da abinda yake tsakaninsu sannan ta gaya mata yanda suke ciki da Abdulmalik a yanzu sedai ta boye mata maganar kin amincewar iyayensa. Kallonta Mumcy takeyi har ta kai aya sannan ta sauke ajiyar zuciya tace "Hamdah kinsan tun farkon haduwarki da Abdulmalik kin tuna abinda na gaya miki? Nace miki karki tsananta soyayya kuma karki tsananta kiyayya, shi aure wani sirri ne da Allah ya barwa kansa sani. Duk yanda kakai da son wani da son ka aureshi idan Allah be rubuta hakan ba babu me aiwatar dashi ko?" Gyada mata kai Hamdah data nutsu tayi sannan taci gaba "To ki miqa lamarinki ga Allah ki jajirce da addu'ar neman zabin Allah. Kar kuma kiyi gaggawa domin daga shedan take. Aure wani abu ne na har abada in yayi dadi zaka dawwama cikin farin ciki haka in akayi rashin dace wanda ba'a fata haka rayuwa zata karewa mace a cikin qunci.

A matsayina na mahaifiyarki bazan ce miki ga wanda zaki zaba a cikinsu ba sedai zance ki barwa Allah zabi ki kuma bi abinda zuciyarki tafi karkata dashi, dukkansu Mazaje ne Hamdaj ko wanne kika aura a ciki nasan zaki ji dadin zama dashi amma a sanina kin fi son Abdulmalik haka nan shima yana sonki, na kuma yaba da nutsuwarsa amma ba wai ina Nufin shi Abdul'ahad din beyi ba A'a kinga ni ban ma sanshi sosai ba inga sau daya na taba ganinsa waccen ranar da muka gaisa ko? To kiyi addu'a ki kuma maida hankali kan karatunki karki bari wani abu ya dameki insha Allah zaki dace da miji na kwarai, zaki samu jindadi tamkar Yar uwarki Zahra. Kullum Addu'ata Allah ya aurar mun daku a inda zaku huta hankalina ya kwanta". Rungume Mumcy tayi haka kawai Hawaye ya shiga zubo mata.
"Ya kuka kuma se kace yau ne za'a miki auran da Allah dagani ke matsalarki sakarci wallahi Aidai Se Abdul koma waye yayi hakuri da halinki" dariya ta tashi tana yi ta nufi dakinsu, a zuciyarta tana tuna kalaman Mumcy. Sedai tana ganin kamar Mumcy tafi na'am da Abdulmalik kodan shi suka sani oho, fasa shiga dakin tayi ta fita compound, inda motar Guru ke ajiye ta kalla nan take maganar da sukayi ta fado masa. Ana saura kwana uku su gama final exam taje office dinsa kai mishi Samosa dayace mata yana so. Seda yakai guda daya bakinsa ya gutsira sannan ya miko mata wai taci, seta girgiza kanta tana murmushi ta zauna akan kujerar dake fuskantarsa yanda yake cin abincin abin sha'awa, abubuwansa da yawa irin na Abdulmalik dinta, yanda yake tauna abincin a yangance kamar ana masa dole.
"HAMDAH ki aureni" kalamar ta doki kunnenta, seta dago da sauri ta kalleshi. Yana zaune yanda yake akan kujerar still da Samosa guda daya a hannunsa yana ci. Ajiyewa yayi ya fuskanceta da kyau sannan yace "Hamdah Allah ya jarabce ni da qaunar ki a karon farko dana fara haduwa dake a rayuwata, ke kika zaunar dani a makarantar nan badan ke ba da tuni na barta. Nayi duk yanda zanyi na daure na kasa dan Allah ki amincemin wallahi ina sonki da gaske bada wasa ba". Kaman statue haka ta ringa kallonsa har bata san ya gama maganar ba, hannunta daya matsa ne ya sa ta dawo hayyacinta ta rasa me zata ce masa " Kin amince zaki aure ni?" Ya qara tambayarta seta janye hannunta da sauri zuciyarta na bugu kamar zata bula kirjinta ta fito. Jakarta ta dauka da wayarta dake kan table din zata fita cikin zafin nama ya isa gabanta ya riketa, kokawar kwacewa ta ringayi amma yaqi bata damar hakan dan haka ta bude baki da niyyar yi masa fitsara kana ya saketa ba zato ba tsammani sejin warm lips dinsa tayi akan nata without second thought ya shiga kissing nata as if his whole life depend on it.

Yanda ta bude baki cike da mamaki ne ya qara bashi full access to her mouth, kaman wanda aka tsikara lokaci daya hankalinta ya dawo jikinta hawayene ya shiga zubo mata kafafunta suka shiga rawa. Jin tana neman faduwa ne ya sakashi rabuwa da ita ya rungumeta tsam a kirjinsa ji yake inama yana da ikon Bude zuciyarsa ya sakata a ciki kawai ya huta. Kuka takeyi sosai ajikinsa da bata san na menene ba, haushin abinda ya mata ne ko wani dalilin na daban oho. Kamar yarinya haka yaringa bubbuga bayanta yana shafa kanta yakasa bude baki yai mata magana, ji yakeyi kamar numfashinsa ze dauke. Yasan be kyauta ba, abinda ya mata be kamata ba kwata kwata amma ya zeyi, kaunarta tayi masa yawa in har yana tare da bashi da burin daya wuce ya ganta a jikinsa. Ganin taqi yin shiru ne ya bude baki dakyar yace "you want me to do it again?" Setayi saurin tsaida kukan ta dago fuskarta ta kalleshi. Murmushi ya mata sannan yasa hannunsa ya fara goge mata hawayen fuskarta.
Duk inda warm hand dinsa ya taba a fuskarta setaji shock har qafarta ba shiri ta saka hannu ta goge hawayen dukka sannan ta nufi hanyar fita "Wait" ya tsaida ita, wayarsa ya dauka sannan yayi gaba tana binsa a baya. Gurin motar sa ya nufa bata da zabi dole ta bishi dan yanzu tsoronsa takeyi, har kofar gida ya ajiyeta be mata magana ba ya juya yai tafiyarsa. Tun daga wannan ranar be sake kiranta ko a waya ba sannan ko a cikin school bata kuma ganinsa ba har suka gama exams. Wannan karon ganin tana da lokaci kuma ba ta da wani abu a gabanta ya shirin tafiya Kaduna gidan Aunty Zahra (yayarta). Rabonta da ita an dade tun bayan da Zahra ta haihu tazo wanka gida. Basu dade da dawowa Kaduna da mijinta ba bayan sun je karo karatu ita dashi a Cyprus. Sosai takejin dadin zaman gidan kodan yanda Antyn da mijinta har ma da twins dinta Amrah da Afrah suke ji da ita.Tayi yawo Sosai samari kuwa ba'a magana duk inda ta shiga kamar zasu cinyeta Amma ita bata su take ba. Mutum biyu da suke rayuwarta ma sun isheta a yanzu, she got the best men ever se wanda ta zaba a ciki. Seda tayi sati hudu cif sannan ta fara shirin dawowa kano shima saboda Umarar da zasu tafi da Mumcy da Hamidah.
Dawowarta ta tarar da Yah Abubakar a gidan ya dawo daga doguwar tafiyar da yayi. Tsilli tsilli tayi tunkafin ya mata magana Dan bata manta rabuwarsu

Please Login or Register in order to submit comment