Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanda baki tunani amma ta kafe bazata haqura ba. One of my greatest achievement and also the Hospital's own At six month aka yiwa Ni'ima CS aka cire little Hamdah. 'My Incubated Baby' a inji ta qarasa rayuwarta, har takai wata tara sannan aka cireta. Cikin ikon Allah da taimakon Dr Al-mustapha (Master) Little Hamdah ta rayu that was Ni'ima's and my whole family greatest joy.

Nayi murna kwarai kuma na fara son yarinyar tun tana wata shida da aka dakkomi ita. Kaman Toy, da kadan tafi qirman kadangare tundaga lokacin ta shiga raina kaman yanda kika shiga that was why i named her after you dukda sunan Mamanta naso na mayar mata but you over ruled it.

Bayan haihuwar Little da shekara daya muka sake barin London zuwa Germany saboda ciwon Ni'ima da ya sake tashi. She was subjected to bone marrow transplant. Akan Ni'ima na qara yarda da miqa lamurana ga Allah. Na kuma yarda nothing is in possible in life. Bayan aikin da akayi mata six months in between zuciyarta ta gaza. Mun shiga tashin hankali mara misaltuwa. Daga lokacin mu ka fara cire rai da ita saboda duk wasu dabarun likitoci sun qare akanta shawara daya ta rage itace ayi mata dashen zuciya. A ina zamu samu zuciya da har za'a saka ma Ni'ima? Idan an saka how sure are we zata tashi? Dashen zuciyan roba was the last option and its only warrant for a year.

Bada sona ba saboda anfi qarfina Mahaifinta shi yasa hannu da yardarta aka yi mata aikin ranar da Kika rasa mijinki Abdulmalik. I had some feelings that life was going to change a lokacin. Hankali kwance na ringa jinyar Ni'ima saboda nasan katangar dake tsakanina dake ta rushe. Na rigada na sakawa raina na same ki so banida sauran damuwa bansan cewa da saurana ba. Shekarun da muka debo basu qare ba.

Bayan shekara shida Na sake dawowa Nigeria a karon farko tun bayan da nayi mata tawaye da cikakken yaqinin samunki. Hamdah Ahmad Ammani, nayi zaton kin biyu, kin chanza daga Hamdah dana bari six years me shegen tsiwa da bata taba zuwa qasa ashe kina nan yanda kike. Ban karaya ba na sakawa zuciyata na sameki na gama se na tarar da wannan baqin bayahuden ya rigada yamin shigar sauri. Dukda haka bantaba yarda da cewa zaki kuma zabar wani akaina ba se ranar da aka sake daura miki aure a karo na biyu dukda irin jan kunnen da na miki amma abinda na yarda Rabo kona girki ne kaman yanda Hausawa suke cewa se kinje kinyi amma nasan zaki dawo, nasan Abdurrahman ba sa'an auran ki bane.

Se bayan da kikayi Bari Nayarda rabo ne yai Ajalin Abdulmalik nima dana matsa da kilan sedai wani bani ba da yanzu banyi wannan aikin ba" yayi maganar yana shafa cikinta. Tayi luf tana sauraronshi maganganun na mata yawo kaman almara. Wai ashe ba qarya yake koya musu a class ba, a gaske ana Irin wadannan transplant din. Yanzu ita Ni'ima ma zuciyar roba aka saka mata iko se lillahi.

"We are done for today" ya fada yana gyara mata kwanciya, ta gaji da wannan jan ran sekace cin kwan makauniya seta yaye bargon tareda janyoshi tace "Wallahi ka tashi, ka qarasamin kawai"

"Me kike so kuma ki sani?"

"Ya akai kasan yan gidan mu har kake zuwa?? How do you even know that I'm in London"

"Dan Allah ki kyakeni ki bari se gobe" seta saka masa kuka cike da zallar shagwaba, ta sani akwai wani abu. Jikinta yana bata akwai abinda kowa yake boye mata, meyasa Anty Islaha bata damu data ganta da ciki ba? Ya akai har Babansa ya aiko mata da wadannan saqon? And Mumcy irin gugar zanan da take mata ya isa dolensa ya fito yau ya gaya mata koma menen ta gaji da taraddadi tana so tasan Matsayin Dan cikinta.

"Idan kika tono abinda yafi qarfinki fa? Kika jiyo opposite din abinda kike so kiji??" Zuciyarta ta tambayeta. A fili ta furta "God Forbid bad things" se ya kyakkyale da dariya dan bata san a fili take dukka tunanin ba.










🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 5⃣0⃣


"Prof Ahmad Ammani's, my second Family. They gave me life after i was shattered, they brought my happiness back to me when i loose hope in getting it again, Ammani's means alot to me, they mean everything to me Hamdah". Murmushi ne me kyau akan fuskarsa, yanda yake maganar kadai ya isa ya nuna mata gaskiyar abinda yake zuciyarsa. Hannayensa biyu ya saqala a wuyanta tareda sakar mata kiss akan lips dinta data turo gaba,

"You want to know how i get to know Ammani's ko, ok i will tell you right now".

CIGABAN LABARI

Inzaki tuna ranar dana zo gurinki i think 2 or 3 days to auranki bayan kin tafi kin barni then your brother came, Muhammad Ahmad Ammani. Baffa was my childhood friend, tare mukayi primary school dashi a Cairo shida Abubakar dukda ban taba zaton ke kanwarsu bace banma san a kano suke ba dan mun dade da rabuwa almost 20 years back. A lokacin mukayi exchanging contact dukda i lied to him cewa watace ta bani wrong address seda nazo naga ba gidan bane. The following day Ni'ima fall sick wanda har aka daura auranki ban sani ba ina asibiti tareda ita.

Sati daya bayan Ni'ima ta samu sauqi muka koma UK, Kishin da nake dashi akanki ya qara ninkuwa musamman idan na tuna wa kika aura. Koda ace kin fito daga gidan Abdurrahman ya rigada ya shiga gonata. I was having a strong feeling zamanku bame dorewa bane sedai har akayi six months banji wani labari ba sena fara surrender. A bakin Baffa naji abinda ya sameki saboda yazo London lokacin muna tare aka masa waya akan baki da lafiya har an kwantar dake a asibiti, dukda bansan ainihin abinda ya faru ba amma nayi farinciki kuma nasan hasashena ya kusa zama gaskiya.

Ban iya zama ba dole na biyo shi saboda ayi komai a kan idona a cikin jirgi yake bani labarin Bari kikayi kuma Mijinki ne sanadi and bazasu yadda ba dole su bi miki haqqinki saboda rayuwarki ya nema. Allah kadai yasan irin murna da farin cikin da nayi a lokacin, bamu rabu da Baffa ba seda na tabbatar na dorashi yanda babu wani lallami da zesa ya haqura kici gaba da zama da Abdurrahman koda kuwa buqatar hakan ta taso.

Hamdah nayi sallah, nayi azumi na bada sadaka da roqon Allah ya dawomin dake cikin rayuwata. I believe it was my last chance, in har ban sameki ba a wannan lokacin to qilan bani da rabo a duniya ne. Ranar da Abdurrahman ya baki takadda seda na yanka shanu Goma na rabar sadaka na godewa Allah saboda nasan na riga na sameki tunda babu iddar sa akanki. Na samu Baba da maganar ina so a nemamin aure amma kinsan meya faru? Wai Baba yace nawa nake da har zan hada mata biyu. Yaushe ma na zauna na nutsu bare na yi tunanin yin wani auran. Hankalina yayi matuqar tashi, kamar sabon kamu na samu Ammi amma se itama ta rikida ta gayamin the same abu da Baba ya fada. Ta manta da alkawarin da tayimin na nema min duk matar da nace ina so.

Ganin suna neman sumin sakiyar da babu ruwa yasa na taka da qafata na samu Abbanku dakaina naje neman auranki. Ranar Baffa yasan tsakanina dake, na zayyanewa Abbah komai da yanda nake sonki, bansan me suka shirya min ba a lokacin wai Abbah yace min na tafi Iddah kike kuma in ma haka ne iyayena ya kamata na tura su nemamin auranki bani da kaina ba. Hamdah kamar mace haka naringawa Abbah kuka, nace zan tafi amma yamin alqawarin baze kuma bawa kowa ke ba, kinsan me yace? Wai ai yanzu bashida ikon zabar miki miji, in bari nan da 3 months na dawo, idan kin zabeni bashida matsala da wannan.

Hamdah nasan baki da Iddah amma ya zanyi tunda sun fada, haka na zauna ina jiran da lissafin lokaci duk yanda zuciyata take azalzalata nazo gurinki amma na haqura wai duk dan karna bata neman aurena nayi nema a cikin Iddah. Wata uku daidai na sake komawa Baba da maganar nema min auranki amma se Baba ya qara zuwamin da wata wala wala, na ma rasa gane me yake nufi.

Haka nayita pushing hardaga qarshe ya yarda mukaje, amma se Abbah yace wai ya sake bawa ni ke, wani ya rigani. Ranar nayi baran bara mata a gaban surukina nayi rashin kunya. Na kuma tabbatar musu sena aureki, ina ta shirmena ban masan baki Nigeria ba a lokacin kin taho London. Se bayan da Abbah ya dauramin aure dake sannan suka zo suna tsokanata. Believe me Hamdah ni dan gata ne. Kinsan mutum nawa suka nemin auranki??

Ammina, Baba, Uncle Mustafa baban Ni'ima, Baffa, Fahad, Mumcy, da Abbanki dakansa. Dukkansu sunga dacewata dake. Bansani ba, ashe tuni suka yanke ranar auranmu, sunyi min haka ne wai saboda aikin jikinki. Sun san bazan iya haqura dake ba musamman dana furta sena miki ciki sannan zasu sake ganinki a gabansu which is risky to your health a lokacin shi yasa sukata garani kaman kwallo.

Hamdah you are married to me, an daura mana aure on one fateful Friday a cikin gidanku palour Abbah. Duk wanda ya kamata ya shaida auranmu dake, duniya kaf tasan ke mata tace ta sunna kuma cikin jikinki halattacce ne, kinyi amfani da kudin dana baki ranar dazan tafi Nigeria?" Seta dago kanta daya gama jiqewa a duniyar shock ta kalleshi da idanunta dake zubda hawaye,
"Kinyi amfani da kudi na tambayeki ba kuka ba" seta daga masa kai tana qoqarin danne kukan dake taho mata

"Kin dubasu gaba daya bakiga Nairas a ciki ba?" Nan ma kai ta daga masa alamar Eh.

"100k i guess, that was your dowry, sakin ki ne da aka rasa ta yanda za'a baki kuma kin karba yarinya kin zama Mrs Abdul'ahad Galadima" ya qarasa maganar cikin sigar dariya tareda rungumeta, kuka takeyi sosai a jikinsa yana bubbuga bayanta alaman rarrashi, shi kansa da zeyi kukan da ba haka ba. Ji yake kamar wanda aka zarewa qaya a maqoshi ya sauke nauyin daya dame shi bashida wani sauran fargaba.

"Why did you hide it from me, kabarni ina aibata cikina da kaina, and i was rude to you......"

"Shiii Don't say that ok, ya wuce and you never been rude to me just that matata matsiwaciya ce and every body knows that, she could do worst ma" seta kai masa duka a qirji ya riqe hannayenta yana dariya ita kuma tana kuka.

"To ni da izinin wa aka dauramin aurene ma fisabilillah gaskiya bazan yarda ba" se ya saki hannayenta ya riqe kunnensa dukka biyu yace

"Na tuba na biki Hamdah ki rufamin asiri dan Allah karkice baki yarda ba" yanda yayi da fuska se ya bata dariya, fuskanta shabe shabe da hawaye seta shiga qoqarin miqewa ita a dole tayi fushi, toilet ta shiga ta bugo masa kofar tana ji yana kiranta. Seta dafe sink ta saki kukan dake cinta a rai. Kuka ne na zallar murna da farin ciki, to idan bata godewa Allah ba ita kam me zatayi? Finally Allah ya bata Abdul'ahad a matsayin miji mafarkinta ya zama gaskiya. Seta dafa cikinta dake ta wuntsilawa a fili take magana.

"Kaima kana farin ciki ko? Tukunna ma seka zo duniya kaga baiwar da Allah yayi maka ta uba na gari". Seda tayi me isanta sannan ta wanke fuskarta da bakinta ta fito, ko qarfe nawa dai yanzu tasan dare ya tsala. Yana zaune ya riqe kansa da hannaye biyu ya rasa tunanin me zeyi, kodai tawayen zata masa kaman yanda yake ta taraddadi? Sautin dariyarta ce tasa ya dago da sauri

"Look at you, so kake nace Abdul'ahad banyarda ba nidai seka sakeni a wane dalili zaka aureni without my consent ko? To lie lie aure kam ya dauru amma da sauranka se mun sake sabon Dating, kayi proposing nayi accepting sannan" batasan sanda ya qaraso ba sejinta tayi cikin jikinsa gaba daya, kiss yake sakar mata a fuskarta ta ko ina

"Wai ban gama ba kuma dai bakayimin lefe ba" cafkan da yaiwa bakinta yasa tayi shiru, "we will date, i will propose and i will shop the entire clothes in Dubai for you alone my queen".

Daren ranar was the most memorable a cikin rayuwarsu. Darene daya kafa tarihi da suka aiwatar dashi a matsayin Mr and Mrs Abdul'ahad. Ashe duk baya ba komai bane se yanzu ne tasan ainihin Abdul'ahad Abdullahi Galadima. Wani tattali da kulawa yake bata kamar kwai nan ta samu guri tana zuba masa sangarta son ranta.

Tundaga wanka, saka kaya bada abinci dukka shi ya mata safiyar ranar tana kwance wai ita ta gaji. Shikam ko a kwalarsa, duk wani motsi nata burgeshi yake da qara sonta. Ko kadan beyi zaton faruwar abubuwa haka da sauqi ba, yayi tunanin se sun kai ruwa rana tukunna kafin ta yarda. Bayan la'asar suna zaune tayi pillow da cinyarsa yana oiling mata gashinta. Sabuwar wayar daya siyo mata dazu ta maida layinta ta hau qara. Sunan Anty Zahra ta gani yana yawo akan wayar seta kasa dagawa dan ita a duniya yanzu kunuar yan Nigeria kaf takeji, to ba dole ba ina zata kai wannan al'amari ita anya zata qara iya hada ido dasu kuwa.

"Ki answer mana se ta katse" ya fada yana qoqarin daga mata kiran, seta riqe hannunsa ta marairaice tace "dan Allah karka daga yanzu me zance mata ma dukfa kallon wawa sukemin ashe ni ina nan" seya saka dariya tareda daga wayar ya saka a speaker qasa qasa yace "kijira muji me zata ce".

"Anty Hamdah tuba muke irin wannan sharemu haka gaba daya ko duk dadin UK dinne yasa?" Muryar Anty zahra ta karade gurin, seta rufe fuska kamar tana kallonta tace "Wallahi Anty ba haka bane waya nane ta lalace se yau aka siyomin wata ya gida yasu Amrah I miss you wallahi"

"Kedai kawai nazata ai laifi mukayi har muna shirin yin kudi kudi mu turo wakili a duba mana ko lafiya" gaisawa suka shigayi nan take mata zancen Sa ranar Hamidah ta qarasa da cewa "yaushe zaki dawo ne ya kamata mu fara shirya abinda zamuyi ko naji Abbah yace wai shida Mumcy kadai zasuzo miki Grad har na tambayi Abban Ayman wallahi yabarni" .
Seta fara kame kame, Abbah da Mumcy suzo su ganta da ciki ta kade har ganyenta. Dakyar suka gama maganar ta kashe wayar tana kallonsa da idanunta da suka cicciko da hawaye.

"Kagani ko dan Allah yanzu a ganni da ciki a cemin me"

"Ace miki sannu kinyi abin kirki mana".

"Amma fisabilillah daga yimin aure banma sani ba se su ganni da wani ciki nidai wallahi tun wuri ma kasan yanda zaka dakatar dasu kar suzo" cikeda shaqiyanci yake mata dariya sannan yace

"Yaushe ne ma Convocation din?"

"23rd of next month" ta bashi amsa tana tura baki. "six weeks ma kenan, ok don't worry zance musu ni kadai ma na isa nayi representing kowa da kowa in banda abunki ma to menene shidai cikin nan kowa yasan da ubansa kece a duhu to kema kin fito haske". Qunquni ta shigayi tareda pouting bakinta gaba ya kama kuwa, seda yai kissing nata son ransa sanna yace

"You pout i kiss these lips ban damu ba ko a gaban waye" sake turo bakin tayi se kuma tayi saurin mayar dashi tana hararar shi yana dariya.

Six weeks leap

Tunda garin Allah ya waye tayi wanka take tsaye a gaban wardrobe ta fito da kaya sunfi set 20 amma ta rasa na saka wa a ciki. Abdul'ahad dake nade cikin bargo yana bacci ta kalla tareda zabga masa harara kamar yana ganinta tayi qwafa taci gaba da binciko kayan. Mugun ashe ba Abbah da Mumcy kadai ne zasu zo ba Harda Ammi da Baba, da Fahad Abokinsa ta gama sakankancewa bazasu zo ba shiyasa bata ma yi tunanin kayan sakawa ba. Gaba daya duk kayan data saka se cikin ya fito musamman yanzu daya ke wata na 6 kadan ya rage yayi 7 kibar datayi da ta sace se cikin ya fito sosai ya mata kyau. Dariyar datajiyo yana mata tasa ta juya a fusace kuwa ta wulla masa doguwar rigar shadda data dakko kafin ta saka kuka.

"Dole kayi dariya mana tunda bakai zakaji kunya ba ni na fasa zuwa ma Allah" ganin da gaske take ya saka shi meqewa ya qarasa inda take kafin ya dagata cak yakaita kan gadon "Relax babe wasa fa nke miki kawai, kalla kiga na siyo miki kayan da zaki saka fa" yai maganar yana janyo wata jaka da tun jiya ya shigo da ita bata duba content din ciki ba se yanzu. Kayan ya zazzage mata akan gadon. Pallazo trouser ne dark peach se white chiffon top da aka ma wata irin tattara a jikinta ta tsaya sosai yanda ko a saka a jiki bazata kwanta ba. As he expect kayan sun bala'in mata kyau haka rigar tayi yanda ake so sedai duk me hankali in ya kalla yasan dole akwai abinda ya qara tokare rigar. Tana zaune tana shan Tea shi kuma yana wanka wayarta ta shiga ringing.

"Hajia Hamdah munyi bacci mun tashi lafiya to da kika qi zuwa mu gaisa" muryar Mumcy ta doki kunnenta, seta fara dariya Dan bata san me zata ce mata ba. Jiya da yamma suka iso babu yanda beyi da ita ba akan suje su gaishesu amma taqi wai sa Hadu yau din. Ita tana fi jin kunyar Ammin sa da basu taba haduwa ba se a waya suke gaisawa. Tsaf ya shirya cikin wata Suit up white yar ubansu yayi kyau da bazaka iya masa kallo daya ka dauke idonka ba.

"Wow Abdul'ahad kayi kyau sosai" ta fada tana qoqarin fixing Dark peach veil din da tayi rolling dashi, seya janyota jikinsa ta yayi brushing lips dinsa akan nata yace "really har na kaiki kyau Kuwa" yai maganar yana dage mata gira daya, seta saqala hannayenta dukka biyu a wuyansa tareda yin dage tayi masa kiss a both sides na cheeks dinsa kafin tace "Allah sa na haifa Boy me kama dakai"

"No baby girl me kama dake da irin voice dinki".

"No Baby Boy"

"No Baby girl". Bubbuga kafa tashigayi ita bata yarda ba, yasan in suka fara wannan drama bata qarewa haka last week suka tara ma kansu yan kallo sunje shopping. Komai ya gani pink ya dauka ita ta dauki blue, seda aka zo gurin biyan kudi ta kafe baza'a hada da wadanda ya dakko ba shima yace baze biya nata ba. Sunka ringa jayayya qarshe se wata mata ce ta sasantasu tace suyi haquri su dauki komai white it will suit both girl or boy sannan fa suka haqura aka taho gida kowa na hararan daya.

"Its ok lets snap some pics and go its almost time" hotuna ya shiga daukansu dasukayi kyau sosai sannan yayi snapping nata ita kadai. A hanya suna tafe tana musu musu videos a snap har suka qarasa gurin already dukka convocants sun shiga Hall din. Gown dinta ta dora tana tayata aka rurrufe ciki tayi maza ta shige hall din har tsinin takalmin ta yana gurdewa se dariya yake mata. 12pm aka gama awarding nasu. Zo kaga bakin Dr Mrs Hamdah Ahmad Ammani kaman gonar auduga. She could help it but to burst in to tears lokacin data ga yan gidansu. Shekara daya da kusan 2 months kenan rabonta dasu. Mantawa tayi da batun ciki ta ruga da gudu Abdul'ahad daya zabura jin kamar shi yai gudun ze bita Fahad ya riqeshi tareda zabga masa harara irin are you ok dinnan, rungume Abbah tayi tareda sakin kuka tace "Abbah i made it, I'm now Dr Hamdah Prof Ahmad. Abbah you are proud of me right?"

Seya shiga goge mata hawayen tareda janyeta kadan saboda cikinta daya tokareshi ya rungumeta ta gefe yana cewa "to Mamana kukan na menene kuma keda baki girma jeki fara gaida Babanki tukunna". Seta waiwaya inda yake nuna mata, Yarima Abdullahi ne taganeshi saboda tana ganin hotonsa a Tv da news papers. Se yanzu taga kaman da sukeyi da Abdul'ahad. Kallonta yake da zallar kauna kamar yarsa haka yake jinta.

Kanta a qasa ta je gabanshi tana qoqarin durqusawa ya dagota yana cewa "Haba dai tashi karki bata jikinki Dr" se suka saka dariya gaba daya ta shiga gaisheshi yana amsa mata da kulawa. Ammi couldn't stand kawai ta janye hannunta daga na Baba tana cewa "Ya isa haka bari na gaisa da yata da aketamana rowarta" rungumeta tayi a jikinta sosai farin cikinta ya kasa boyuwa. Hamdah dai se sussunkuyawa akeyi wai karsuyi feeling cikin amma ina wai bonono rufe qofa da barawo. Mumcy was the last person, jikinta ta fada gaba daya wannan karan Abdul'ahad fincike hannunsa yayi ya riqota jikinsa tareda dunguremata kai. A kunne ya rada mata "So kike ki guntulewa Babyna hanci ko kike fadawa kan mutane haka" seta hada rai tana harararsa ta maqale Mumcy, "I missed you so much Mumcy na" ta fada tareda sakar mata peck a kumatu. Ita kunya ma ta bata se ta shiga tureta tana cewa "mutum dai baya girma".

Bayan gaishe gaishe suka dauka pictures kafin suka wuce 'YARIMA COMPLEX' Inda Baba ya shirya mata yar walima. Ba karamin mamaki tayi ba ganin kusan dukka friends din da tayi a London hatta da Zulaiha da batasan sanda ta dawo ba tazo, taro ya tashi lafiya ta ware sosai cikin Family dama Handah bame baqunta bace. Ganin babu wanda ya mata magana akan cikinta yasa ta ware ta shiga hidimominta, nan suka wuni se dare suka musu sallama suka tafi dan suma washe gari asubanci zasuyi.

Bayan tafiyarsu Ammi keyiwa Mumcy hirar "wai in banda abun yaro Dr Maryam mu Hamdah zata boyewa ciki koda yake shima daya santolon dana tambaueshi cemin yayi haba shi bema sani ba kiji shakiyi".

Dariya Mumcy tayi tace "kya gaji da gani indai wannan ce gani take tafi kowa wayo cikin da ko makaho ya shafa yasan da akawai shi zanga yanda zasuyi ranar da dan ko yar yazo duniya se muga qarshen iya shege" hira suka ci gaba dayi akan Hamdah da Abdul'ahad din har bacci ya daukesu..








🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 5⃣0⃣


"Ooch yarinyar nan kinyi nauyi gaskiya na dena daukanki" Abdul'ahad ya fada daidai sanda ya direta a qasa. Tsabar tabara taqi fitowa daga mota wai ta gaji sedai ya dauketa. Bubbuga qafa ta shigayi tana cewa "Allah aa ni banyi nauyi ba" seta tsaya tareda buga tsalle kaman yarinya kafin tace
"Yes i fooled them babu wanda ya gane inada ciki" seta hau rawa.

Kallonta kawai yake yana jinjina yarinta irin ta Hamdah, takalmin kafarsa ya cire tareda kwanciya akan kujera ya miqe dogayen qafafunsa yana kallonta with adoration. "You see na gaya maka i will out smart them kuma gashinan har Dr Mumcy couldn't find it thay I'm Pregnant" ta fada bayan ta zauna akan qafarsa ta zagaye hannayenta biyu a wuyansa, seya ja dogon hancinta daya fara budewa kawai tareda yin murmushi dan besan me ze ce mata ba.

"You how old are you?" Ya tambayeta,

"I will be 27 soon" seta buga qara da har seda ya toshe kunnensa. "I got my Doctoring degree a year behind you wooo". Iya gaskiyarta take murna, seya tallafe haba kawai yana kallonta. Her first answer shekarunta ya tuna masa da wata rana a office dinsa lokacin daya taba tambayarta, she was 18 then, and now wai ta zama doctor a year behind him shi yayi at 27 ita 26. Gajiya yayi da ihunta ta dagata cak ya ajiye a gefe seta riqo rigarsa.

"No miss Hamdah i need rest" yayi maganar kaman qaramin yaro, se miqe ita ma ta bishi tana cewa "I and your baby also need a rest". Tare suka shiga dakin, ya fara rage kayan jikinsa tana tayashi. Kallon fuskarta yake tana zuba masa uban surutu kaman wadda ta hadiyi aku.

"Wai dama haka kike da surutu Hamdah?" Seta murguda masa baki tareda juya ido. Ita kanta batasan me ya shigeta haka ba kawai taji tana so tayita masa

Please Login or Register in order to submit comment