Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

anyi kamu lafiya cikin farin ciki sun sha rawa dan dama HAMDAH ba baya bace a wannan fagen Liqi kuwa samari sun mata shi kaman basu san ciwon kudinsu ba ko ita kadai ce mace a gurin. Koda aka tashi daga Kamun sam taki shiga motar Guru seda Maryam ta nuna bacin ranta sannan ta bisu suka tafi. A hanya ko sunga cuna baki in abin ya ciyota tayi tsaki tareda murguda baki duk ita kadai har suka dawo gidannasu daya ke nan suke zaman kawance.
Kokarin bude motar takeyi Amma ta kasa saboda lock din daya saka Dan tuni su Maryam suka fice ita da angonta, kallonta kawai yakeyi harta gama kiciniya da kofar sannan taja ta zauna "toh ai se a bude wa mutane kofa su fita koh" Be kulata in banda ma Kwantar da kansa da yayi a jikin kujera yana binta da kallo, Shi dai tasa Qaddarar kenan, Allah ya jarabce shi da son wannan yarinyar. Jiyakeyi kaman ya shekara 100 beganta ba, ta masa kyau musamman dabe taba ganinta da make up ba se yai. samun kansa kawai yayi da janyota gaba daya zuwa jikinsa ya mata wani tight hug Kaman wani ze kwace masa ita. Pecking goshinta yayi lokaci daya ya saketa tareda danna lock din yace "ki kwana lafiya Allah ya huta gajiya and make sure kinyi mafarkina". Murfin kawai ta bude Daidai lokacin Yusuf din yadawo Da alama har sun gama sallama da Amaryar tasa, fuskar Yusuf data kalla ce tasata murmushin dole, stain din Jambakin Amarya dambarere a kan kumatun Yusuf din, Seda safe tayi masa sannan ta nufi cikin gidan.
Sam bata biyewa surutun yammatan ba ta kammala duk abinda zata yi na kwanciya ta haye gado,wayar minti 5 sukayi da Abdulmalik yana gaya mata kilan gobe ze zo kano ya gaji yana missing dinta sosai. Badan tana jin baccin ba haka ta takurackanta yinsa dan bata so tabawa kwakwalwarta damar yin tunanin abinda ya faru yau tsakaninta da Guru.

Washe garin ranar Akayi dinner sedai tayi kokarin ganin ta toshe duk wata hanya dazata hadata da Guru, yanda ta tsare gida dole ya saurara mata amma hakan be hana shi liqe mata bomper to bumper ba data dauke kafarya daya ajiye tasa ko kunyar dalibansa da suke a gurin beji ba. Gurin cin abinci ma Serve ur self akayi, shiya zubo musu abincin a plate daya batareda nuna damuwa ba ta saka cokalinta ta fara ci hankalinta kwance abinda ta sani daga ranar ba qara ganinta zeyi ba bare ya takura mata. Ranar Saturday aka daura auren Maryam da angonta Yusuf da daddare suka kaita gidanta dake Rijiyar zaki akan washe gari zasuyi Sword crossing.
Bayanda batayi da Maryam ba akan ta kyaleta tabi su Afiya amma taki bata da zabi illah ta zauna Addu'arta Allah yasa banda Guru za'a zo rakiyar Ango. Ko yau a gidan daurin aure taji haushin abinda ya mata. Kamar hadin baki suka saka kaya kala daya shi shadda light Ash ita kuma Lace. Tunda suka shigo yake nunawa Abokansu wai ga Amaryarsa "kungani ban gayabmata kalan Kayan da zan saka ba amma saboda zuciyarmu daya munsaka iri daya" abokan da suka fishi rashin hankali se cheering dinsa suke wai ya iya zabe har wani yana cewa ya masa shigen layi shi yaso ya kafa gomnatinsa amma Guru ya riga. With full confidence yake cewa "Ai wannan shinge nane babu wanda ya isa ya ratsa" haka suka ringa daukarsu pictures kamar ita ce amaryar.
Se 9:30 yan rakiyar ango Suka qaraso. sedai Addu'ar ta bata karbu ba Dan Sallamarsa ce a gaba. Bayan yan gaishe gaishe da wasa sukayi musu nasiha sannan sukai wa Amarya sallama suka Fara fita daddaya. Sabon kuka Maryam ta saka wanda dole ita ma Hamdah ta tayata. Akace sabo tirken wawa shikenan yanzu Maryam tayi aure ta barta dakyar Yusuf ya lallashi Maryam din suka hau sama ita kuma ta fita waje.
Mota daya ta rage a parking lot din gidan da alama itaYusuf yake nufi za'a kaita gida. Tana share guntun hawaye ta qarasa jikin motar jin yana mata Horn. Seda ta zauna sosai sannan ta gane motar waye ta shiga ba abin ta fita ba dan har ya fara tafiya. To in ta fitan waze kaita gida ga unguwar tsit babu ma alamar masu adaidaita sahu. Bata da zabi Se kawai ta daure fuska karma ya samu damarta.
"Naga se wani kuka kikeyi in kin shirya kema se a miki auran kiyi me dalili". In ta amsa shi ku da kuke karantawa kun amsa, abinka da me saurin fushi kawai se shima ya shareta dan yaga alama in ba'ayi soyayya ba to raini ze shiga tsakani. Se kawai ya kunna waka ya qure volume din, yana dauke hannunsa ta mayar da nata ta rage karar kidan tana mita "kawai se a kunnawa mitane wata waqa ko dadi babu kaman sunce suna so". Be kulata ba ya qaro volume din ta kuma ragewa a na uku ya dago a fusace dan takai shi bango "if you dare touch anything here again sena baki mamaki wallahi".
Kallonsa kawai tayi dan ta ji tsoro. Sak ya dawo mata Dr Guru data sani Na BUK dan haka salin alin ta kama kanta. Tana jinsa yana tsaki shi kadai karshe ma ya kashe waqar ya kashe AC ya sauke windowa din motar dukka ita dai a ranta tace kaji dashi. A kofar gidansu ya, tana shirin fita daga motar ya tsaida ita ta hanyar cewa "ji mana"
Komawa tayi ta zauna Ta hade girar sama da kasa, se yaga tayi masa kwarjini yakasa fadan abinda yayi niyya. Haushi yabata Ya kirata kuma ya mata shiru "shikenan seda safe" ya fada bayan ya bude murfin motar ya fito, bude mata motar ta fita. Seda ta tabbatar ta fita daga motar sannan ta kalleshi "Malam ka dena wani abu kaman an saka ka ni dinnan da kake gani nagama gane take takenka so you better know I'm already taken. Kallonta kawai yakeyi ya kasa ce mata komai, motar sa yai wa key ya bar wurin zuciyarsa na wata irin suya. kuka ta fashe dashi haka kawai taji Kamar bata kyauta ba. Da zata iya da ta bishi tabashi hakuri meyasa bata tsaya taji abinda ze fada ba fincikar da aka mata ce tasata maido da hankalinta, Abdulmalik ne fuskarsa tayi Ja tamkar wanda yaci yaji jijiyoyin kansa duk sun tashi. Kamar mazari haka jikinsa yake rawa, motar yabi da kallo kafin yadawo kanta cikin shaqaqqiyar murya yace mata "Yau kuma daga ina ya dakkoki?" wannan kuma se meya faru iye nace uban me ya hadaku da har Ya dauke ki".
Hotonsu da guru Wanda takusa faduwa a gurin kamun Maryam yake nuna mata. Tsawa ya buga mata cike da hargagi yace "Dama baki da abin fada tun ganina dashi na farko ban yarda dashi ba kwata kwata kallon dayake yi miki ba kallo bane irin na Malami da Daliba kallone irinna masoya masoyinma wanda zaka iya yin komai akansa......"
2⃣0⃣2⃣0⃣


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*By Maryamah* 💞💞
©2020

PAGE 0⃣7⃣

"Enough Abdulmalik" ta katse Har lokacin hawaye basu dena zuba daga idonta ba. "Bakaso kaga wani ya rabe ni ko bakason ganina tareda Ko wanne namiji ba toh ka Aureni, na amince Abdul katuro iyayen ka ko gobe a daura mana aure Indai haka ze sa ka yarda da soyayyar da nakeyi maka" Tana kaiwa nan ta shige gida tana kukan da bata san dalilin yinsa ba.
Wani Gumi ne Ya shiga keto masa nan take cikinsa ya shiga hautsinawa har yana jin amai na yaso masa Alamar ya kai qololuwa cikin tashin hankali. Naushi ya kaiwa ginin dake bayansa tareda Kifa kansa a jikin bangon shidai Malam Sa'idu me gadi kallon ikon Allah kawai yakeyi. Wannan shine goma da ashirin, ta yaya zata dakko maganar aure a wannan lokacin bayan ita ta kawo tsarin seta gama school wanda yana ganin shima kafin lokacin abubuwa sun daidaita a nasa bangaren? To waima tun farko meya hanashi gabatar da ita a gida ne yasan da komai ze zo masa da sauki amma yanzu kam abubuwa sun rincabe. Haka yai ta sambatu a hanya shi kadai sedai ya qudiri aniyar koma me ze faru baze bari ta subuce masaba Koda hakan yana nufin batawa da kowa, he don't care kome za'ayi sedai ya faru Amma dole ze tunkari Alhaji da Maganar nan.

A bangaren Hamdah Da kuka ta shiga gidan, Dankwalin kanta da mayafin dukka a hannu dama tuni ta cire takalminta a waje. gaba suna zaune a Main palour suka bita da kallo. Ikon Allah kawai Abbah ya fada ya ci gaba da duba Jaridar Hannunsa aransa dai yana mamakin hali irin nata katuwar budurwa ki shigo gida kina kuka kamar wadda aka daka, da ace Abubakar ko Baffa na gidan ne ma se ya ce daya daga cikinsu ne ya maketa.
"Anya kuwa Mumcy Anty Hamdah bata da Iskokai Dan dai abinnata ya fara wuce na Islama" Hamida ce tayi tambayar tana bin hanyar da Yayartata tabi da kallo. "Bata da wasu Iskokai se Iskanci" cewar Farouk dake zaune a gefe. Seda Mumcy ta sauke numfashi sannan tace "Nima dai Hamidah lamarin yar uwarki yana daure min kai kwana biyunnan na fuskanci tana cikin damuwa Duk yanda take dokin bikin Maryam amma kwata kwata bata da walwala ga yawan koke koke data samu Kamar Matar Mamaci ina ga ko dai ita da Abdulmalik ne ko?" ta qarasa maganar cikin sigar tambaya.
"Na Fa gaya muku Ba abinda ke damunta se iskanci inba haka ba kawai ta shigowa mutane gida ba ko sallama ita ga Yar So Ai Abbah ya dawo Abinda take so kenan dama ku tada hankalinku to thank God Bema ko kalleta ba " "kaidai Yaya Farouk baka san me aka mata ba kawai zaka fara cewa haka" hamida ta fada bayan tamike ta bi bayanta, tasan Yayarta sarai bata kukan banza dole akwai abinda yake damunta. Shiru palour yayi kowa da abinda yake saqawa Daganan kowa ya fara watsewa saboda dama dare yayi.

Duk irin hakurin da Hamida ke bata seya zama kamar qara tunzura ta takeyi. Kuka takeyi sosai Wanda in zaka kasheta A lokacin bata san namene neba. Fushin Abdumalik ne ko Kuma Sir Guru ne ita ma bata sani ba. Abu daya dae tasan tana son Abdulmalik, so na hakika haka nan babu ko digon son Guru aranta to meya ke faruwa haka?? Ahaka ta raba dare tana kukan rashin sanin madafa abinda ya haifar mata da ciwon kai me tsanani Kafin safiya zazzabi me zafi ya rufeta. Washe gari har 1pm tana kwance a dakin, dakyar tayi sallar asuba ta qara kwanciya gashi tun da dare ta kori Hamida dan ta isheta da tambayar meke damunta. Wayarta bata san inda take ba kuma har lokacin babu wanda ya leqota. A bangaren yan gidan kuwa Sanin halinta na in tana fushi bata so kowa ya shiga sabgarta yasa suka kyaleta a zuwan in ta sakko da kanta ta fito. Koda Mama Uwani ta gama girki dan tun 6am Mumcy ta fita aiki Farouk cewa yayi karya kai mata in taji yunwa zata fito dan kanta. Se 3pm Mumcy ta shiga gidan tana tambayarsu ina Hamdah kowa ya bata amsa da be ganta ba tana bambamin fada ta shiga dakin hankali tashe tayi kanta ganin yanda ta kudundune cikin bargo tana rawar sanyi, dagota tayi ta rungumeta a jikinta "Hamdahna lafiya Meya sameki?" Gaba daya ta rikice jin numfashinta na neman daukewa ne yasata shiga Kwalawa Farouk kira.


A tare yaran nata suka shiga dakin jin Yanda take kiransa babu qaqqautawa sun san babu ba Lafiya ba. Hankalinsu dukka ya tashi da ganin halin da take ciki dan lokaci daya ta fita hayyacinta seka zata ta yi sati tana jinya, bata da nutsuwar bata wani emergency dan haka suka nufi asibiti kawai da ita.
*************************
Abdulmalik kuwa bayan barinsa wurin Hamdah straight gidansu dake unguwar Sharada NNDC ya nufa. Tun daga yanayin parking dinsa me gadin yasan ba lafiya. Da Gudu gudu yanufi part din Mahaifiyarsa da suke kira da Hajja. Hamshakiyar Kyakykyawar mace Fara tasKallo daya zaka mata ka hango tsantsar kamar su da Abdulmalik din, Tana zaune cikin hadadden palournta daya gaji da haduwa tamkar fadar wata sarauniya tsabar yanda aka tsarashi kai dagani kasan Naira tayi kuka a gurin.
Sanye take da wani hadadden Lace Wanda ko ba'a fada ba Ya lashi daruruwan Nairori daga siyanshi har zuwa dinkin Bubu irin na manyan Mata da suka ci suka tada kai da akayi masa. Kyalkyalin da wuyanta da hannayenta sukeyi ya isa (nidai nace idan aka sace Hajja wannan barawo ya gama yin kudi). Kwalliyarta sak irinta isassun matan SHUWA. Hajiya FATTU kenan Uwar gidan ALH KAMALU DALA.
Hajia fattu ko muce Hajja Itace Mace ta Farko cikin jerin matan auransa Alhaji Kamalu guda hudu kuma mahaifiyar Abdulmalik. Macece mai matukar izzah, takama, Da Isa. Tana da son kanta Hakanan bata hada komai da soyayyar Yayan ta ba. Takan bata da mutum duk yanda suke Indai har ze taba mata Yaya dan kwata kwata bata ganin lefin yayan ta. Tsabar Bala'inta yasa shikanshi Alh Kamal din yake shakkarta Wanda har wasu suke gani Kaman asirine sedai ko daya wannan ba halinta bane Dan tace ba wani Malamin karya dazata bawa kudinta yai mata abinda bata yiwa kanta ba. Hajja Fattu kenan.

Kallonsa tayi yanda ya shigo kamar wanda ake bi gaba daya ya hargitse, seta maida kallonta kan masu aikin dake ta karakaina cikin palour Dan su basu guri. Ido ta zuba masa dan Hajja bata tambaya kallonta kadai ya isa ka gane abinda take nufi. Ganin bashi da niyyar magana dan da alama ma hankalinsa baya tare dashi, murya a shaqe kamar an mata dole tace "Daga Ina kake?" Seda ya nemi gurin zama yana Sunkuyar da kansa ganin yanda ta kafeshi da ido sannan yace
"Daga gidansu Hamdah nake Hajja".
"Wace ce Hamdah" ta tambayeshi da kallon rainin hankali a fuskarta. Yasan bata son kwana kwana dan haka kaitsaye yace "Yarinyar da nake nema da aure". Shiru tayi na dan wasu seconds kafin tace "Da izinin wa, kuma ita din yar waye a kasar nan?" se ya daga kansa ya kalleta, be gane da izinin wa ba, dama namiji yana buqatar izini kafin ya nemi aure dama ai gurin iyayen yarinya yakama ta yane ma kafin ya fara tsayawa da ita to sun bashi dama...... Tunaninsa ne ya katse
"Nace maka yar waye a kasar nan?" ta qara jefo masa tambayar
"Hajja Yar gidan Prof Ammani ne". Cike da bala'i tace "Yar gidan wa kace Prof menene me na sama yaci bare ya bawa na kasa? Ni kake tunanin zaka dakkowa ahalin yahudawa A matsayin suruka me suke dashi in ba tarin takaddun banza da bazasu amfanesu duniya da lahira ba" fada takeyi haiqan dan dama ba baya bace a wannan fannin. Hajja masifaffiya ce ta misali musamman abu ya tarar da dalili. "Amma Hajja ai ita nake so kuma in kika ga yarinyar seta burgeki. Hajja tana da kyau Kuma ....." "Kyan Uwarka" ta katse shi sannan taci gaba "Nace kyan uwarka me za'ayi da kyau wanne ne ban gani ba? Yaya nawa aka baka masu kyan kaqi ashe kana can kana jajibo mana irin matsiyata to wallahi Ahir dinka kar ma ka kuskura Alhaji yaji wannan maganar dan kasan rankane ze baci a banza shashasha kawai kai ko kishin irin da Yan Ubanka suka auro bakayi se kao Guda daya da Allah ya bani zaka tozarta ni a gaban kishiyoyi ka auro min wata yar Professor da likita to Jami'a da Asibiti ma sunci uwarsu da ubansu Tashi ka bani guri kafin na bata maka rai .
"Dama Hajja tace ne inna shirya in tura Iyayena ayi magana to shine nake so kiyiwa Alhaji magana". Baki kawai ta bude tana kallonsa. Waiwayawa tayi gefen ta babu komai se tumbler na karfe ta dauka ta jefeshi dashi cikin zafin nama ya goce ya fice daga palour da sauri, Abinda yake gudu kenan tun tuni amma baze iya jure rashinta ba, dole yasan yanda zeyi ya janyo hankalinsu suyarda da auransu. Dakinsa ya shiga, zarya yake tayi daga bango zuwa bango ya rasa tunanin daya kamata yayi a lokacin. Ada yana ganin har gara Hajja zata iya karbar abun to Alhaji fa daya fita tsanani in aka zo batun auran Jari? Bashida mafita dan haka ya dauro Alwala kawai ya tada sallar da shi Kansa besan abinda yake karantawa ba.

****************************************

Seda Hamdah Ta kwana uku a asibiti sannan ta warware, a kwana na biyunne Abdulmalik ya kirata, Hamidah ce ta dauki wayar Ta gaya masa Cewa anyi admitting dinta a asibiti kwana biyu kenan. Hankali tashe ya nufi asibitin, Allah sarki Shi ya zata tana sane ta shareshi kwana biyu bata nemeshi ba shima ya shareta ashe bata da Lafiya ne duk ya tashi hankalinsa gani yakeyi Kaman shine silar ciwon nata.
Bayanda ba ayi da ita ba akan tafadi abinda ke damunta Amma taki Dan Dr ya tabbatar musu dacewa damuwa ce tayi mata yawa harta haifar mata da zazzabi. Haka dai aka sallameta da sharadin tayi kokarin cire komai a ranta in ba haka ba jininta ze iya hawa. Wani sabon tattali da kulawa Abdulmalik yake bata dan dakyar ya koma Lagos amma kullum suna manne a waya. Wata sabuwar shaquwa ce ta shiga tsakaninsu, so da kauna kullum qara hauhawa yake a zukatansu fatansu Allah ya mallaka Musu junansu. A haka har aka koma hutun makaranta.

Ranar Wata Monday Suka koma hutu, kowa ka kalla cikin tsananin farinciki yake dan sunyi missing school ba kadanba. Shirye shiryen Presentation da zasuyi akan special project sukeyi ko wanne dalili ya zabi abinda zeyi inda wasu kuma Supervisors dinsu ne suka zabar musu. Hamdah tana cikin wadanda aka supervisors dinsu suka zabarwa. Kusan kwana hudu kenan yau tana zuwa office din Dr Guru kuma as usual a rufe, juyawa tayi ta kalli Maryam Amarya datayi wani kyau na musamman da gani kasan Tana jin dadin auranta. kamar zatayi kuka tace "Maryam kin gani ko this is the fourth time I'm coming to this office bayanan Kuma ranar friday ne Defence dinnan kinga yau tuesday wallahi Zanje nayi duk abinda naga dama nayi presenting tunda dukka sauran yan group dinmu sunce sun kirashi ya basu topic".
"Aa Hamdah badai abinda kika ga dama ba why not kema ki kirashi kuyi magana a waya yanzu kikayi gaban kanki ya hanaki presenting wa aka cuta" setayi shiru Dan zancen gaskiya ya basu time tun last week friday yace suzo su sameshi kuma tana sane taqi zuwa maganar Maryam nakan gaskiya amma dukda haka batajin zata iya kiransa dan ita tuni ma tayi blocking numbersa. Dakyar Maryam tayi convincing dinta ta yarda amma akan sedai ta kira mata shi a tata wayar haka kuwa akayi Maryam ta kirashi.

Yana zaune a madaidaicin palour sa, exam scripts ne na postgraduates a gabansa yana marking wayar ta shigo. Mrs Yusuf daya gani ya saka shi dagawa yana mamakin dalilin daya sa matar yusuf ta kira shi, seda ya kalli Agogo karfe 9:30am sannan ya kai wayar kunnensa. Bayan sun gaisa take cewa "Sir dama munzo office dinka ne da Hamdah so wayarta babu charge ta mutu shine tace na kira mata kai" "wace ce Hamdah?" ya tambayeta. Seda tayi jum sannan tace "Hamdah Ahmad Ammani IT student dinka ce Sir"
"Ok kice ta jirani i will be there in 60 minutes Insha Allah" ya katse wayar. Handah data gamajin komai dan a handsfree wayar take tace "Tab se yaga wanda ze jirasa har 1hr wato ga mara aikin yi ko"
"kedai kin fiya matsala wallahi meye to muzauna muna hira haryazo mana" haka suka zauna kofar office din kusan minti 40 sega Yusuf ya kira Maryam wai yazo ganinta, dole tawa hamdah sallama ta tafi.

Tsaki tayi yafi cikin kwando dan ya qara kusan 10mins akan qhr din dayace. Kamshin turarensa ne ya sanar mata da zuwansa lokaci daya taji zuciyarta na bala'in son ganinsa. Wata irin kewarsa ce ta taso mata Lokaci daya. Yayi kyau matuqa cikin Jean and T shirt daya saka all black haka ma takalmin kafarsa. shidai Komai yana masa kyau ta fada aranta tana kallonsa har bata san sanda ya qaraso inda take ba.
"Malama dena kallona haka karki cinyewa budurwata ni" ya fada a saitin kunnenta. Ai ji tayi ina kasa ta tsage ta shige ciki tsabar kunya dan tabbas bazata musa ba kallonsa takeyi. Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta ringa jan kafa har tashiga office din daya bar Mata a bude sannan ta rufe kofar zuciyarta na bugawa irin yanda ta saba..

2⃣0⃣2⃣0⃣
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*By Maryamah* 💞💞
©2020

PAGE 0⃣8⃣

"Bam" aka fada daidai kunnenta. Bakaramin tsorata tayi ba dan bata san yana bayanta ba. Dariya yake haikan se kawai ta saka masa kuka. "me kuma ya faru" ya fada yana kokarin tsaida dariyarsa
"Ba kaine ka tsorata ni ba sannan kuma kake min dariya". Se ya qara fashewa da dariya, the look on her face got him wani kyau na musamman takeyi idan tana kuka. Seya riko hannunta ya jata kan kujerar dake gefen office din, tsugunnawa yayi a gabanta still hannunta na cikin nasa yana dariya ita kuma tana kuka. Ganin abin nata bana qare bane kawai ya dauki wayarsa ya fara mata video ai kuwa ta qara volume din kukan harda bubbuga kafa a kasa kamar yarinya. Seda ta gaji dan kanta yana zaune kamar ya samu TV haka yaringa kallonta, ganin ta gama kukan ya sa ya tsiyaya mata ruwa me sanyi ya mika mata sannan ya ciro hanky me kyau se kamshi yake daga aljihunsa ya shiga goge mata fuskarta "Oya fato hancin" kamar yarinya ya goge mata majinan hancinta.
Mayafin kanta ya kama da niyyar cire mata setayi saurin rikewa "relax naga kina zufa ne shine zan cire miki kisha Iska" ya fada yana ci gaba da sauke mayafin kafin ta rike har ya saukeahi kan kafadarta, gashin kanta data kama dakyar dan ribbon din ya masa kadan kuma tana sauri Dama mayafinne ya taimaka mata ya tsaya ya samu nasarar zubowa har gadon bayanta bakikkirin tayi dying karshensa da Golden colour.
Kamar me tsoron gashin haka yakai hannunsa Ya shiga tattara mata, laushi da kamshin da gashin yakeyi really got him, Yana son gashi, yana daga qualities din da yake so a jikin mace gashi Hamdah tana dashi morethan his expection. Har ya daure mata gashin ya daura mata Mayafin kamar dankwaki Akanta bata dago ba seda taji ya ajiye mata abu akan cinyarta, Laptop ce. Tuni ya kame akan kujerarsa yana jujjuyawa yace "Ki duba zakiga folder with your reg number go through the content". Da kai ta amsa masa ta shiga yin abinda yace. To her surprise Mini project din da take ta qoqarin hadawa ne ta kasa, mamaki take a ina ya samu notes dinsu na Asibiti da har ya hada mata komai? Hatta da Power point din presentation din yayi mata she couldn't Help it but to smile lallai Sir Guru yana da kirki in yaga dama. Dago kanta tayi with so much Joy tace "Sir...." seta kasa qarasawa ganin irin kallon dayake binta dashi. Waske wa yayi ya

Please Login or Register in order to submit comment