Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba inba tare da Berbie Dady ba"

"Haka ne ku barta kawai, kiyiwa ita Habiban bayani ai zata fahimata idan da rai wata rana da kanta zataje musu yanzu kam bata san kanta bama bare tasan wani rashin uwa" magana suka cigaba dayai akan little Hamdah.

*************

Ya kalli agogo yakai sau saba'in tun bayan saukarsu birnin London, Baba daya gaji da miqa masa wata qaramar jaka yayi tsaki kafin ya saketa akan cinyarsa har seda yadan tsoraya yace "Malam tashi ka tafi and make sure you see me tomorrow by 10am before i take off ka gaidar min da surukata ga shinan ka kai mata injini" ai jiyai kaman ya goya Baba tsabar murna, seyamiqe yan sunkuyar da kai yace "A tashi lafiya Baba mun gode" ya juya
"Kuka gode kai da wa, ita na bawa ai bakai ba"

"Baba nida ita ai daya ne" ya fada bayan ya fara tafiya yana yar dariya. Already kayansa na cikin motar, tun da suka sauka yake Allah Allah Baba ya sake shi amma yaqi. Dole ya halaci meeting din da Baban yayi da ma'akatan kamfaninsa na samar da gas na girki wanda ya kasance shine kamfani mafi girma a birnin London duk da mutane da yawa basu san mallakin Dan Nigeria bane.

Wata Hamdala ya saki daidai sanda Mr Richard yayi parking kofar gidan. Wata iska yake shaqa da take cakude da kamshin turaren wuta daya tabbatar ita ta kunna. A kofar plat dinta aka sauke masa kayan sa sannan Richard ya masa sallama ya koma can guest In din Baba inda ainihin gidan Abdul'ahad yake amma neman magana ya sakashi kama gida a estate din dalibai. Password dinsa ya shigar jikin kofar da mamallakiyar gidan bata taba lura da ba ainihin kofarta bace. Komai da komai sak iri daya ne da kofar data sani amma wannan programmed ce. Ita ko tunanin ta inda yake shiga ma batare da muqulli ba bata taba yi ba haka bata taba sa ido taga ya yake bude kofar ba indai zata zura key ta bude mata ita ba ruwa ta.

Gidan tsaf marbles din se daukar ido suke kamar ka zuba ruwa ka lashe haka ya ringa jefa dogayen qafafunsa yana shaqar kamshin da yake me dadi tamakar ana saka masa sabon rai. Babu ko wa a palour se karar Jambox dayake jiyo wa an kunna karatun alqur'ani mai girma da alama daga dakin sane seya dire kayan hannunsa a hankali ya tura kofar dakin.

Sanyin idaniyarsa, nutsuwar zuciyarsa, tana kwance idanunta a rufe zarazaran eye lashes dinta baqaqe sidik sun kwanta kamar an qara jansu. Kallonta yake tun daga ka ta da babu dankwali, wasu qananan gashi sun kwanta luf a goshinta, zuwa kan dogon hancinta dayake kamar ita ta zabarwa kanta kwance kan kyakykywawar fuskarta idonsa ya sauka kan Lips dinta light pink kamar na balaraben jariri. Ta janye rigar jikinta zuwa kirjinta abinda ya bashi damar hango cikinta daya turo gaba, da sassarfa ya qara sa gabanta kaman wanda aka ja da igiya hannunsa har rawa yake amma ya kasa tabata. Kallon cikin yake kamar wanda aka cewa abinda yake ciki ze leqo ya ganshi kafin ya daga hannayensa dake rawa lokaci daya wasu hawayen da yake da tabbacin na farin ciki ne suka shiga zubo masa.

"My child, result of my own hard work" ya fada kamar wani dolo sanda ya dora dukka hannayensa akan cikin yana kallon fuskarta. Sanyi da taushin hannunsa suka sakata rumtae ido dan kamar a mafarki taji abin, seya rungumo cikin gaba daya ya dora kansa akai ya shiga kissing nasa tareda lasar fatar cikin yana sambatu kaman wani sabon hauka.

A hankali ta bude idanunta, da farko tsoro taji amma kamshinsa da hannunsa dake akan jikinta suka tabbatar mata Abdul'ahad ne. Rashin mutunchi ta shirya masa sunfi girman London gaba daya amma ganinsa durqushe a gabanta yana kuka se kawai ya sare mata guiwa. Motsin da tayi ne ya tabbatar masa ta farka se ya miqe tareda dagata gaba dayanta ya rabata da qasa ya shiga juyi da ita a dakin har lokacin hawaye basu bar idanunsa ba yana cewa

"Nagode Hamdah na gode Allah yayi miki albarka ya saka miki da mafificin alkhairi, this child means the world to me thank you for keeping him or her safe for me. Me kike so ki gayamin in baki Tukuicin wannan kyautar". Seta bata fuska dan tuni ta fara jin Amai yana neman taso mata ga juwa saboda juyin da yakeyi da ita amma seta dake tace

"Ni banason komai kawai ka saukeni ka kuma fita ban son turarenka tayar min da zuciya sukeyi" Allah sarki seya direta da sauri yana cewa "an gama just give me five minutes in dai wannan kamshin ne bazaki kuma jin saba" ya juya da sauri, seta saka kuka. Hannaye biyu ya dora aka yace "Abdul'ahad ka kade har ganyenka ka fada komar da bazaka iya fita ba" a fili kuma seya nufota yana cewa me e ne kuma Maman Baby" hannu ta daga masa wai ya tsaya a inda yake kafin tace

"Its kicking me......." Ai bata qarasa ba ta ganshi a gabanta ya yaye rigarta data saki tareda dora kunnensa akan cikin ya shiga shafawa da hannunsa yana cewa "ta inane dan Allah nuna min when did it star kicking. Bravo my baby is very strong har ya fara kicking" tausayi, da takaici suka rufeta lokaci daya, seta tureshi tareda yin baya tace

"Ni I'm hungry that's why the baby is kicking" seya miqe da sauri

"Me zaki ci?"

"Inada tuwo a Freezer da Anty Islaha ta kawomin jiya shi zaka warming min na ci but first get rid of this scent bana son su"

"Yes Ma'am" ya fada yana rusunawa kaman yanda ma'akatan hotel sukeyi, seta saki murmushi har seda dimples dinta suka lotsa sannan ta zauna a hankali tana shanshana jikinta da kamshinsa ya kama.

"God I missed him thank God he is here again i don't know what life could be without him".

"Sannu wato daga ganinsa har kin sake fallen ko karki tunkari abinda yake a gabanki" zuciyarta ta gargadeta. Hannu takai ta shafa cikinta da har ya shiga wata na biyar, a yanzu bata jin ko duniya zata taru zasu iya rabata da abinda yake cikin ta. Wata irin so da qaunar sa take kamar su dawwama tare bama seya fito doron duniya ya hadu da cin zarafi da tsangwamar da take jiran sa ba, nan da nan hawaye suka taru a idonta

"Inama dan Halal ne kai, ina ma kana da yanci irin na kowanne Da, but Still momma loves you so much and she is willing to sacrifice anything for you baby. Be thankful you have two loving parents i can see it from ur Daddy's eyes i know he loves you too"

Wani irin so da tausayinta ne suka rufeshi lokaci daya, seya ajiye tuwon akan bedside drawer shima ya dora hannunsa akan nata dake kan cikin, a hankali ya kai lips dinsa yayi pecking daidai kasan cikinta inda yaga wani baqin layi da be taba lura dashi ba setayi saurin runtse idonta dan saqon yaje mata har cikin kwakwalwarta.

"We love you both Champ, and we will take care of you all together, get no worries boy, Your Momma and Papa have you"......




















🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 4⃣7⃣


Kallonsa take kaman wawuya yana surutai, "Oya tashi ki wanke bakinki kizo kici tuwon rigimammiyar kawai nidai i beg you karki haifar min yaro ko yarinya me kukan Banza please" ya hade hannayensa biyu alamar roqo, seta zubo fararen kafafunta qasa tana hade rai while can kasan zuciyarta farinciki ne da murna fal, ina ma aure sukayi da Abdul'ahad yake bata irin wannan kulawar! Kafin ta fito ya shimfida mata table mat saman lallausan rug din sannan ya ajiye mata filo da zata zauna akai harda wanda zata tokare bayanta wai. Duk ya rasa me ma zeyi basabanba wai mata nada ciki.

Dariya ta kyalkyale da ita sanda ta fito taga ubannin pillows din daya jera, se yai saurin qarasawa inda take ya dagata gaba dayanta sama yana cewa "As from now you won't step on your legs again ni zan daukeki duk inda zakije just make sure you and my baby are fine". Seda ya zaunar da ita tayi saurin janye pillow daya dorata akai tana cewa "wai kai meye haka, haka ka gani anayi a garinku idan mace nada ciki ne ko matar ka haka ta ringayi?" Se yayi tsam yana kallonta, ya rasa me yasa take son mentioning matarsa ako da yaushe, "kishi" zuciyarsa ta raya masa.

"Mata ta bata raini ciki ba" ya fada a zuciyarsa amma a fili se ya kalleta kawai yayi murmushi, abincin ya shiga bata a baki ta kuwa zage tana ci dan tun da ta samu wannan cikin ta zama se a hankali, ci take kamar gara bata ragawa kwano setaga babu komai a ciki. Seda ta cinye tuwom tas ya bata ruwa tasha ta godewa Allah sannan ta miqe tsaye tareda riqe qugu.

Alhamdulillah tunda yanzu naci na qoshi ina da qarfin yin magana" se ya kalleta shi dariya ma ta bashi, dama ya yake ganinta kamar tea mug a gabansa in ta tsaya bare yanzu da ciki yasa ta haye ta zama yar lukuta se ta zama kaman wata cup cake 🤣🤣🤣 tsaf ze sa kujera ya zauna still ya dora abinci akanta yaci kuji sharri, seya shiga tattara kwanukan yan cewa "ina zuwa hajjaju bari na kai wannan kitchen se nazo naji ya akayi".

Seda ya dauraye kwanukan dan tun ba yau ba ya lura bata tara wanke wanke. Da taci abinci take wanke kwano dole shima ya koya dan ko dirty spoon ya aje mata ta ringa mita kenan se ya gaji ya wanke. Tana tsaye inda ya barta se kumbura baki takeyi ya nemi gefen gadon yayi tsalle ya haye kamar yaro yana jin wani nishadi.
"Anty Hamdah gani to meya faru?" Yai cupping fuskarsa da hannu biyu yana qarewa chest dinta da suka qara cika kallo.

"Ka maimaita cewa ni kadai na shiga uku banda kai".

"Ina wayarki" ya tambayeta ba tareda ya kula tambayarta ba. Seta harareshi sannan tace "Ban sani ba".

Taku daya yayi kafin ta an kara ya fizgota ta taho jikinsa gaba daya ta bude baki zata masa ihu dama abinda yake jira kenan ya shiga kissing nata passionately. Duk yanda taso hana kanta amma zuciyarta taqi bata hadin kai dole ta sakar masa kanta gaba daya dan ita kanta tayi missing nasa ba kadan ba. Mantawa yayi da cikin jikinta ya shiga juyata son ransa sun fi awa uku cikin Duniyar Abdul'ahad sannan ya kyaleta dakyar shima badan ya gajiba sedan Cikinta da yaji ta ambata ya maqalqaleta a jikinsa yana shafa gashin kanta da kissing goshinta a hankali tana sana'ar tata wato kuka.

"Gaskiya gulmarki tafi qarfinki yarinyar nan, se kin gama enjoying zaki zo kina wa mutane kukan munafunci, wai tsaya ma dan Allah me ya faru gaba daya kin chanza kin fi da sau saba'in da......" Duka ta tai masa ya goce ya shiga kyalkyala dariya, har zuciyarsa ba wasa yake ba gaba daya ta kuma chanza masa, ganin kukan na shirin zama na gaske ya saka shi gyara mata kwanciya sosai a jikinsa ya zamana tana gabansa ya zagaye bayanta da hannayensa yana hura mata iska a kunne Dif kuwa tayi shiru, kafin wani lokaci bacci yayi awon gaba da ita. A gogo ya kalla saboda curtains din dakin duka a sauke suke windows a rufe dan an fara sanyi tuni, karfe 8 harda minti 10 ba Magriba kadai ba har anyi sallar Isha. Seya miqe da sauri bayan yaja mata bargo ya fada toilet. Seda ya yi sallolin duka sannan ya koma kan gadon ya dago kanta zuwa cinyarsa ya saka hannayensa biyu cikin gashin kanta yana mata tafiyar tsutsa ai kuwa tayi saurin bude idanunta da sukayi Ja alamar baccin na kanta.

"Tashi kiyi wanka kiyi sallah se a koma bacci Kasa" seta bata fuska cike da shagwaba tace "Yunwa".

"Ki rufamin asiri kar ki haifomin Dan dambe wannan cin abinci ba kuwa sena siyi share a food companies ba" bata kula shi ba dan da gaske yunwar takeji, Tea ya hado mata da Cake yana kawowa tace ya koma a cikin cabinate a kwai wani Mug a ciki ze hado mata. Buda baki kawai yayi yana kallon Mug din, duk cinsa be isa ya shanye Tea cikin wannan ba bare Hamdah daya sani. Lallai dole a tausayawa mata in ba ciki ba me ze sata wannan cin? Haka ya ciko mata shi dam da shayi tunda ta kafa kai kuwa bata sauke ba seda ta shanye tas yana tsaye yana kallon ikon Allah.

"A qaro" ya tambayeta
"Tunda ga me cikin zani ko"
"Na sani to ke wai tsaya da bana nan wa yake miki wannan hidimar ne"

"Shafa kaji" ta bashi amsa daidai sanda ta bude kofar bathroom din ta shige. Sedata gasa jikinta sosai da ruwan daya hada mata sannan tayo wanka ta fito lokacin baya dakin, a palour ta wuceshi ta shiga nata dakin dan ta sa kaya ya bita da wani kallo na tsantsar so da burgewa. Shi kam bashida sauran buri yau ga Hamdah na yawo da cikinsa. Wata baggy shirt ta saka bayan ta idar da sallar ta kame gashinta data busar guri daya sannan ta fito yana zaune yana kallon kwallo gefensa kuma wayarsa ce ya kunna waqa.

"Se ka zabi daya kallon ko waqa ka cikama mutane kunne kaman wani gidanka"

"Allah baki haquri me gida" ya fada yana offing both Tv da waqar daya kunna, seta zauna a qasa ta miqe qafafunta sosai, ba wani girman kirki cikin yayi ba amma tsabar son jiki irin na Hamdah jinsa take kamar duniya. Sakkowa yayi yana matsa mata kafar yace "yadai suna miki ciwo ne" yana duddubasu amma bega alamar kumburi ko wani abu ba. Dagowa yayi jin tayi shiru suka hada ido gana daya hankalin ta yana kansa shi take kallo. Se yanzu ta lura da uban ramar da yayi se dogon hanci ga gashi buzu buzu a fuskarsa

"Let me help you shave" ta fada tana kai hannunta fuskarsa, seya riqe hannun tareda kissing tsakiyar tafin hannunta yace "thank you gobe zanje amin aski ma gaba daya".shiru ne ya ratsa palour,
"Akwai abinda kike so ne dare ya farayi na nemo miki" ya fada dan ya kawar da shirun, ya lura yau itama miskilanci take ji seta girgiza masa kai sannan tace "i almost have everything ban son komai had i know yau zaka dawo da ka tahomin da tsami gaye da alawar dinya"

"Whats that?" Ya tambayeta, seta tura baki gaba ba tareda ta bashi amsa ba. Jakar da Baba ya bashi ce ta fado masa a rai, se yamiqe ya shiga dakin ya dakkota. "Gashi in ji Baba yace akawo miki"

"Wane Baba?"

"My Dad" ya bata amsa. Seta karba tareda cewa "Nagode Allah saka da alkairi"

"Bude muga mene ne a ciki". Zip din ta zuge, wasu fararen jarkoki ne guda uku da farin ruwa a ciki da bata san ko mene ne ba an nadesu da seal tape se takadda daga gefensu ta dauka ta ware ta anyi rubutu layi biyu "ki juye su a babban mazubi ki qara ruwa ya zama shine ruwan shanki" se kuma zuma roba daya itama ta ringa sha babban cokali daya safe da yamma se kuma dabinon ajwa. Tarkacen kayan kwalamar irin na Nigeria da take missing. Tsami gaye, carbin malam, magarya, kurna, dan tama tsitsi, garin budidis, charbin malam da duk sauran tarkace harda farar qasa.

"Allah ya saka ma Baba da alkhairi ya biyashi da aljanna" ta fada cike da murna. Yaji dadin addu'ar kwarai tsabar tsokana se ya shiga tattara kayan with irritating face yace "dama wannan abun Baba ya sako a fancy jakar nan har ina zaton wani abun kirki ne to bazaki ci kisamin yaro yaxo da kalolin wadannan shirmen ba". Seta Galla masa harara tareda fizge kayanta takwashe su tana cewa "Ji ko kunya Cikin Shegen akewa wannan rawar qafa....." Tsawar daya daka mata ba shiri ta saki kayan tayi gefe jiki na rawa, kafin kace meye wannan fuskarsa ta chanza zuwa tsantsar bacin rai da tashin hankali.

"Cikin nawa kike kira shege?" Ya tambayeta yana nuna cikin da hannunsa

Duk yanda jikinta yake rawa da tsoratar da tayi bata fasa furta "In ba shege ba menene? Ya sunan dan da aka haifa babu aure?" Seya miqe ya durfafeta ta kuwa tattara zata kwasa da gudu dan ta tabbatar in ya zo bazasu kwashe kalau ba amma ko taku biyu batayi ba ya cimmata ya dagata cak kamar kaza"

"Ka sauke ni Abdul'ahad zanyi maka ihu ka sauke ni" a banza wai an mintsini kakkausa sema tafiya daya ci gaba dayi da ita.

"Wayyo Allah cikina" ta fada dukda ba abinda ya samu cikin neman hanyar tsira kawai take, seya direta akan gadon yana cewa "meya faru meya samu cikin kin gani ko in banda shirme ya za'ayi kiyi gudu". Ita dai data samu ta mirgina can qarshen gado tace "anyi jikinka ko nawa"

"Ok naji amma ki sani bazan dauki ganganci da shirme ba dole ki kula da kanki ki kula da cikin nan wallahi in ba haka ba nida kene" seta saka kuka

"Tsabar mugunta wai ni baiwarka ka mayar dani kome, ka haikemin duk sanda kaga dama kamin ciki sannan kasamin doka dole na kular maka da cikin to wallahi ka cire abunka ni bana so ka kaishi inda za'a kula maka dashi" seya saki murmushi ya dora kafarsa daya akan gadon yana kallonta,

"Karki damu, kinga little, a inji na reneta gata na tana yawo ko ina shima wannan ki barmin shi kawai yayi 7 month a jikinki zan cire abuna na qarasa renonsa...." Allah ya sawwaqa kasa min Da a inji itama bata san ciwon kanta bane shi yasa ta yarda" seya bushe da dariya

"Au Dan shegen?"
"Don't you dare call him like that again"
"Or else? Ba ke naji kina cewa Shege ba bayan nasan dan da bai da ubane wannan shi kuwa wannan ga uwarsa da ubansa a tare amma ki ringa sheganta mana Da ke matsala ta dake kauyanci wallahi malama Love child ake kiran irinsu"

Kallonsa kawai take, lallai barikin Abdul'ahad me lasisi ce wato love child. Seta hadiye kukanta ta miqe tsaye saboda fitsarin da take ji, "ina zaki"
"Fitsari zanyi"
"Ok" sanda ta fito yana kwance ya kunna system dinsa, hoton Ni'ima ne akai ya hade hannayensa biyu yana kallon ta. He is missing her beyi aune ba sejin wasu siraran hawaye yayi sun biyo fuskarsa yayi saurin dauke su jin motsin kofa amma he was late dan ta gani. Kallon abinda yake kalla tayi sannan ta zauna a hankali a gefensa kishi na nuqurqusarta

"Hamdah pray for her please she is no more" ya fada yana kama hannunta dukka biyi, seta fizge cikin firgici "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Ni'ima ta rasu yaushe?"

"Kwana biyu bayan komawana, ranar da kika kirani qarshe kwananta daya da rasuwa" se kawai ta fashe da kuka tareda fadawa jikinsa tana fadin "I'm sorry Abdul'ahad ban sani ba kayi haquri for all tje troubles i have caused meya sameta dama bata da lafiya?"

Issa long story kiyi shiru ba kuka zakiyi ba ki mata addu'a". Duk yanda taso tsaida hawayen ta kasa a fili ta ringa jero mata addu'oi yana amsawa, Allah sarki Ni'ima haduwarsu ta farko a gidan Maryam data qarshe ana i gobe daurin auran ta da Abdurrahman ta tuna, mace me sanyin hali da fara'a Allah ya gafarta miki. Lallai Abdul'ahad is really strong, ashe matarsa ce ta rasu dalilin wannan ramar da yayi kenan, seta tuna kanta lokacin data rasa Abdulmalik irin tashin hankalin data shiga da damuwa se kukan ya zamar mata biyu. Rarrashinta ya shigayi ganin yanda take kukan da iya gaskiyarta dakyar ya samu tayi shiru sannan tace

"Little fa tana ina" tayi maganar tana jan majina.

"Tana gidanku gurin Mumcy, tunda na kaita taga picture dinki shikenan tace bazata qara komawa gurin Ammi ba har se Aunt Berbie ta dawo, opps na manta ance na gaya miki an saka ranar auran Hamidah six months masu zuwa tunda kinyiwa kowa tawaye kin kashe wayarki". Seta daga kai tana kallonsa, "gidan mu? Dama kana zuwa gidan mu me ya kaika yama akayi ka saba da yan gidan mu har ka kai Little can ya akayi kasan zancen auran Hamidah" yanda ta tsatstsareshi da idanun nan nata masu saka shi ya manta komai ya sa ya daga hannayensa dukka biyu sama yace "Allah baki haquri ranki ya dade wacce tambayar zan amsa daga ciki"

"Dukka" ta fada ba wasa. Qarshen tika tika tik, yasan dole azo nan and he is glad, ya gaji yana so su fara zama irin na sauran ma'aurata. Seya janyota jikinsa tareda tura kansa cikin rigarta yace "its late now 12am tayi sleep i promise gobe zan gaya miki duk abinda kike so kiji nasan you have so many questions regarding my self yanda rayuwata ta kasan ce bayan mun rabu, aurena da Ni'ima, Samuwar Little da dawowana rayuwanki a yanzu i promise i will tell you everything but dan Allah yanzu kiyi bacci kinji" seta rufe idanunta kawai, tana jin yanda yake yawo da Hannayensa a dukka sassan jikinta yana qarasa zare duk wata laka da tayi saura a tare da ita.

"That's my babe, kiyi bacci ba abinda zan miki" sama sama take jinsa daga nan bacci me shegen dadi ya kwasheta wanda rabon da tayi makamanci sa harta manta.

Asuba ta gari Mr and Mr Galadima 😊😊😊













🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 4⃣8⃣



Yana kwance akan three sitter kunnensa saqale da Airpod yana amsa waya. Magana yake amma shi kansa baze ce ga abinda yake fada ba saboda yanda hankalinsa gaba daya ya raja'a akanta duk wani motsinta yana kan idonsa. Yau abun kirki take ji, tunda suka tashi da safe ya mata shara tareda mopping ita kuma ta shiga hada musu breakfast yana ta tsokanarta wai Amai ya tsaya ashe duk wannan Aman data ringayi some months back tace masa menstrual pain ne qarya ne ita dai bata tanka masa ba se murmushi da takeyi. Allah Allah take ta gama ya bata labari yace se sunci abinci.

A baki ya ringa feeding nata se ta kwace fork din wai he is too slow ta hau ci dakanta, seda yaga tana nema ta tashi da dukka chips da egg din data soya musu su biyu sannan ya janye plate din yana cewa "Iko se lillahi Hamdah nifa bana Noma ki rufamin asiri dan Allah ki rage ci". Baki ta turo ita a dole ta ji haushi ta shiga hada shayi a Family size mug dinta dan bilhaqqi bataje geji ba, yana ci yana kallonta yanda take kwankwadar shayin tausayinta na ratsashi. Matar da ada se anyi dagaske take cin abinci amma yanzu ji yanda ta zama. Shi ya kwashe komai tana nade akan carpet tana sauke numfashi sabida Aman da tayi, se mita take wai daga zuwansa ya dawo mata da Amai ita rabon datayi har ta manta ya wuceta ya shiga dakin.

Wanka ya sakeyi ya shirya tsaf cikin Suit Blue da farar Inner se qamshin sabon turaren data tilasta masa amfani dashi yake ya fito ya tsaya akanta se zuba gyangyadi take a zaune kaman dole.

"Zanje meeting amma ba dadewa zamuyi ba just 2hours i will be done" seta shiga goge idonta tana kallonsa kafin ta tabe baki kamar yarinya qarama ta fara magana. "Allah banyarda ba nidai babu inda zakaje kai nake jira fa tun dazun ka sani" se shima ya kwaikwayi muryarta ya fara magana yana cewa "To ya kike so ayi, nima fa yanzu aka kirani muna da meeting idan banje ba a ina kike so na nemo kudin siya miki abinci to?" Rigima ta shiga masa yana biye mata seda wayarsa tayi qara alamar kira sannan ya dagata cak suka shiga daki, Abaya baqa ya dakko mata da mayafinta tana tsaye ya zura mata yace suje. Seda ta zauna a motar ya rufe mata qofa sannan ya zagaya nasa sit din ya shiga.

Tafiya kadan sukayi suka isa Wani hadadden building da bata san ko ina bane taga sun shiga. Kanta akan kafadarsa suna tafiya a hankali a haka

Please Login or Register in order to submit comment