Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka shiga cikin elevator sannan ya dago kanta yana kallon fuskarta, murmushi yayi ganin yanda ta hade rai yace "sorry Babe banaso kowa ya kallan mun beautiful face dinki shi yasa". Baki ta tura gaba har elevator ya tsaya suka fita.

Bude baki tayi tana kallon haduwar office din daya bude mata se kace na wani shugaban qasa tsabar haduwa ga mayan qamshinsa ya kama ko ina. Akan kujerar sa yai mata masauki kafin yayi gaba ya danna dan dan wani maballi se taga bango daya ya bude, ga mamakinta dakine a gurin da gado da komi tsaf dashi. Fridge din dake gefe ya nuna mata yana murmushi yace "gashi nan akwai komi da zaki nema a ciki in kuma kinason wani abu daban call me zan shiga meeting I'm already late" seta bata fuska kadan, bata so ya tafi. Seya zagaya bayan kujeran da take zaune ya warware mayafin data yafa kafin ya dora kansa a wuyanta numfashinsa na ratsata har cikin jininta, daidai bayan kunnenta ya sakar mata kiss me qara kafin ya rada mata "Don't miss me you hear" ya saurin ficewa.

Ita kadai taringa sakin murmushi tana shafa inda ya mata kiss din, Abdul'ahad is just too good. Miqewa tayi kafafunta sun mata sanyi ta bude fridge din, ta bakin nasa akwai kusan komi a ciki. Katuwar robar Yoghurt ta dauka ta nemi guri ta kwankwadeta sannan ta shiga dakin, seda ta cire Abayan jikinta sannan ta kwanta akan gadon tareda rungume pillow idanunta a rufe tana tunaninsa. Abdul'ahad ya riga ya gama kankame duk wani lungu da saqo na zuciyarta. Sonsa yabi jini da bargonta tana jinsa har cikin numfashinta abinda bata taba ji akan wani dan Adam ba. Hannayenta ta dora akan cikinta tana shafawa, yanzu ta yarda harda son uban cikin yasa take qara qaunar yaron a zuciyarta. Tanajin zata iya fuskantar kowa da komai akan sa bata da sauran tsoro yanzu as far as Abdul'ahad is by her side. Bata san tsahon lokacin data dauka tana juyi ba kafin bacci ya dauketa.

Se a lokacin hankalinsa ya kwanta ya rufe system din gabansa da yake kallon duk abinda takeyi, saboda makarar da yayi meeting din seda ya dauke kusan awa uku sannan suka gama. Fita yayi yaje ya siyo mata abinci dan yasan zata nema ilai kuwa yana shiga ta farka tana sana'ar tata kukan yunwa. Shi ya wanke mata baki ya bata abincin sannan sukayi sallah dan lokaci ya rigada yayi.

"Abdul'ahad kagama meeting din ka gayamin yanzu" seya dagata sama bayan ya cire Suit din jikinsa suka kwanta akan gadon yana cewa "yarinyar nan daga cewa ina so ki ringa kiran sunana shikenan kuma kin samu babu ko Bismillah ki ringa kiran Abdul'ahad ko" seta turo masa baki, yayi saurin dora lips dinsa akan nata ya shiga kissing nata deeply, seda yayi ya gaji sannan ya saketa idanunsa sun fara chanza kala ya kalleta nata idanun a rufe ta cije lips dinta na qasa, "she looks so hot" ya fada a ransa se yaji baze iya kyaleta ba dukda baya so ya fiya takura mata kodan saboda condition dinta na yanzu, birkitota yayi ya hade fuskarsu yatsunsa cikin nata

"Abdul'ahad bab....."
"Shii" ya katseta daga nan labari ya chanza.
It was a memorable moment for both of them, yayi mamaki matuqa yanda ta sake dashi ta bashi hadin kai sosai se kuma ta shiga sussunkuyar da kai taqi yarda su hada ido. "wato yau kuma kunya ta ake ji wo ni lallai yarinya tafara daukan karatu". Ita dai bata kulashi ba se shirinta takeyi har tagama yafa mayafinta yana kwance.

"Ka tashi mu tafi" ta fada tana zama akan dan stool dake ajiye a gefe, seya miqe har seda ya tsoratata ya shige toilet, wasu kaya daban ya fito dasu a jikinsa fuskarsa a dan hade yace "muje" yayi gaba tana binsa a baya se gulmarsa take wai me ya chanza shi daga shiga toilet. A mota ma shiru suka ringa tafiya har suka je gidan, be shiga ba yace ta sauka zeje ya dawo ta fita daga motar tana kallonsa yaja ya fita da gudun tsiya. Seta tabe baki kawai ta qarasa ta bude kofarta a ranta tace kaji dashi.

Se bayan sallar magrib ya shigo yana yan waqe waqensa harda wani yin gaba yayi baya duniya ta masa dadi lokacin ta yi wanka tana tsaye da kaskon turaren wuta a hannunta. Ciki ciki ta amsa masa sallamar da yayi ta masa kallo daya ta dauke kai taci gaba da tafiya, se yai saurin riqota ta bata tareda dora kansa akan kafadarta yana dariya ciki ciki yasan kwanan zance,

"Mutum ya dawo gida babu ko sannu da zuwa kinyimin wani kallon tara saura kwata zaki wuce haba Mammy". Seta shiga qoqarin cire kansa daga jikinta tana cewa "ni ka dagani ba korana kayi daga motanka ba kayi tafiyanka ai nima baka yi min sallama ba kafin ka tafi". Seya juyo da ita tareda karbar kaskon ya ajiye a qasa sannan ya rungumeta sosai yana cewa "I'm sorry Babe aski nake so naje and i know you in na biye miki bazan kuma fita ba". Zama yayi ya dorata akan qafarsa yana murmushi kaman idiot ya shafa cikinta.

"I think cikin nan ya isa scanning ko ya kamata musan Gender din baby before we start to shop" seta bata fuska
"Baki so?" Ya tambayeta
"Bana so gara mu jira kawai kome Allah ya bamu ko kana da choice?"
"Kome na samu ina so amma kinsan ko da za'a bani baby girl me kama dake i will be much more grateful but still koma wane iri ne as far as its from u ina so". Se tayi shiru wani abu na taba zuciyarta,

"Astagfirullah Allah ka yafe mana" ta fada a cikin zuciyarta hawaye na kawo wa a idonta, seta miqe daga jikinsa ta shige dakin saboda kukan da ta kasa tarewa. Bin bayanta yayi tana kife akan gadon tana kuka ya dafa kanta. "Hamdah menene kuma yanzu shikenan saboda nace ina son baby girl to na fasa ki haifa Boy koma twins, triplets, quadruplets duka ina so ki cikamin gida da Gang of Boys i will love them all", maimakon tayi shirun seta fada jikinsa taci gaba.

"Abdul'ahad Don't you have any regret after doing this, I mean in ka kalla cikin nan bakajin komai dama ace bamuyi sauri ba munbi dukka necessary formalities??" Murmushi me kama da dariya ya saki ya dago kanta, qaramin hannunsa ya saka yana zagaya lips dinta yace "I have no any regret upon seeing this Hamdah, infant i feel like I'm the most happiest person living on Earth seeing Hamdah carrying my baby around. I just can't wait randa zan ganki kina breastfeeding Baby na Hamdah ban san irin farin cikin da zanyi ba, you have no idea on how much i love you kina ganin komai kawai kaman wani wasa ko??"

Seta miqe daga jikinsa "Allah sarki So ya haukatar dakai Abdul'ahad har baka hango abunda yake jiranka a gaba..."
"Majnoon A so na zamo me hauka, sauqin se an bani ke munyi aure". Se kawai ta bishi da kallo a ranta tace ubangiji ya shiga lamarinka. Riga ta saka sannan ta koma kitchen ta dama Custard a qaton bowl ta dawo palour yana zaune bayan ya chanza kayansa zuwa white shorts and Vest se ya nuna mata cinyarsa akan tazo ta zauna, tasan halinsa sarai dole ta je ta ajiye bowl din a gaban ta tana shan custard din shi kuma ya zame ribbon din kanta ya shiga hargitsa mata gashi. Tana jinsa ta masa banza,

"Are you ready for the story now??" Ya tambayeta, tsabar sauri har batasan sanda ta ture bowl dinba yai saurin tarewa
"Yes I'm ready ai kana sane kake ta wani jamin rai dan kasan inaso"
"Oya shanye maza se na gaya miki" ai gaba daya ta kafa kai ta kwalkwale Custard din da gudunta ta wanke kwanon ta dakko musu Pringles da ruwa me sanyi. Fitilun palour ta kashe gaba daya ya rage saura hasken Tv kawai sannan ta zauna a gabansa sosai suna fuskantar juna kaman wadda ze koyawa karatu, janyota yayi ya kwantar da ita akan carpet ya zura hannayensa biyu yana shafa cikin ta

"Abdul'ahad ka....."

"Shii labarin zefi dadi".

"Hamdah kin tuna ranar dana sauke ki a gida kika gayamin kina da wanda kike so zaki aura kar nayi wasa da hankalinki ko?"

Kai ta gyada masa alamar eh sannan ya ci gaba

**********************

Six years ago

Bayan dana bar wurinki bansan me nake tunani ba, na gwada duk wata dabara tawa amma ta kasa bullewa. Fahad Aminina shi kadai yasan halin da nake ciki se Ammi amma ita kanta bata San ainihin abunda ya faru ba kawai na ce mata kince baki sona. Da taimakon Yusuf mijin Maryam qawarki na samu contact din Abdulmalik tsohon mijinki. Hamdah a rayuwa ban taba zuwa gurin wani neman alfarma ba amma a karon farko nayi, ni Abdul'ahad na durqusa a gaban Abdulmalik na roqeshi yabarmin ke amma a lokacin ya nuna min ya fini buqatarki.

Hamdah nayi amfani da kudi da iko amma duk a banza ban same ki ba. Na ringa turawa Alhaji Kamal Dala kudi akan ya bijire ya kuma hana Dansa auranki amma saboda Allah ya fimu sanin me ya tsara da kuma abinda ze faru se Hajja Fattu ta rinjayemu, ikon ta yafi namu tasiri. Duk da haka ban karaya ba nabar Nigeria na dawo Nan London da yaqinin cin nasara sedai lokaci ya rigada ya quremin se labarin daurin auranki na tsinta ana saura kwana biyu. Duk wata dabara tawa ta qare a lokaci, haka na taho kamar mahaukaci nazo na tarar da abinda nayiwa laqabi da baqin al'amari. Furuci mafi muni a kunnuwana. Ina tsaye aka shada dauruwar auranki da Abdulmalik Kamalu Dala, daga lokacin na fitar da rai da duk wani farincikin rayuwa.

Nayarda Allah ya bani kudi da mulki amma ya tauyeni da samun cikon farincikina. A lokacin na tabka kuskure da sabo da nikaina se daga bata nayi realizing na ringa neman yafiyar ubangiji which I'm very sure InshaAllahu ya yafemin domin nayi su a fitar hayyaci.

Tun bayan da nabar Nigeria a karo na biyu ban sake waiwayarta ba haka na yanke alaqa da duk wanda ze kiramin koda sunan qasata ne ciki harda iyayena. A lokacin na koma Ukraine da zama banida kowa se Allah haka babu wanda ya sanni na nemi aiki a daya daga cikin jami'oin kasar na cigaba da koyarwa. Kinsan meya sameni?? Ashe na samu tabin kwakwalwa ban sani ba. HOD department dina ya nemeni akan wani aiki da nayi yace nayi publishing da sunan makarntarsu, Na duqufa ina ta harhada ayyukan Hamdah bansan ashe shirme nakeyi ba. Se ranar conference nazo zan gabatar da proposal na aikin. Hamdah a gaban duk wani mutum daya jiqu a duniyar Genetis kowa yana Jiran Abdul'ahad ya gabatar da aikin da HOD ya gama zuzutawa duniya kinsan me nayi?? I ended up giving them your story. Duk aikin danayi ashe akanki nake ta rubutu.

I wrote about you and our love story, komai akanmu Hamdah i even included our pictures, daga lokacin aka dakatar dani. Sukace ina da buqatar hutu wai na samu mental disorder. Qarshe na koma abun tsokana da sunanki ake kirana. Daga lokacin yammatan da suke sona suka chanza sabon salo, suka ringa zuwarmin da sunan Hamdah. Wasu har chanza kalar fatarsu suka ringayi wai ko abinda ya rudeni kenan. Da akwai wata yarinya Helen baturiya ce yar Asalin qasar Switzerland tare muke aiki da ita. Could you believe har plastic surgery tayi ta koma irinki sak. Amma abinda bata sani ba shine i love the inner you. I was captured by urs pure soul bawai wani materialistic thing ba.

To cut the story short dan na ci gaba miki da labarin wahalar dana sha a Ukraine se kinyi min kuka. Dakyar na shekara daya nabarta saboda sun mayar dani mahaukaci har asibiti abokanan da nayi a gurin aiki suka kaini wai aringa duba kwakwalwata likita yace banida matsalar komai, damuwa ce kawai tayi min yawa.

Daga Ukraine na koma Spain, life wasn't also easy there sauqinta kawai acan akwai mutanen da suke debemin kewa. Al-mustapha friend dina da Isma'il were also in Spain then. Wasa wasa seda na shekara biyu cif ban waiwayi kowa nawa ba. Nayi zuciya dasu dukda basu da laifi ko kadan. What i Don't know Baba yana sane da duk where abouts dina. Ya zubamin ido ne kawai yaga iya gudun ruwana. Shiya sa akamin transfer dole na qara dawowa London. Yazo dakansa ya saitani ta hanyar yimin buji buji har seda na kalli rayuwa a yanda take. Na gane na rasa ki dole na dauki haquri. Through secret spy dina nake samun duk labarin yanda zamanki yake a gidan auranki duk wasu abu da kike undergoing.

I'm sorry to say amma nayi matuqar jin dadi lokacin da na samu labarin zaman da kukeyi. Se nake ganin kaman lokaci yayi da zaki dawo gurina. Na zafafa addu'a Allah ya kawo qarshen auran ku ya bani ke ban damu ke din alkhairi na bace ko Aa i just believe samunki shine alkhairin............

Shiru yayi, seta dago idanunta da suka cika da kwalla tana kallinsa
"Ya kayi shiru?" Fuskarta ya shafa sega hawayen sun fito.
"Shikenan kija se gobe zamu ci gaba tunda kika yi kuka"
"Na dena dan Allah" a gogo ya nuna mata karfe daya harda mintina. Seya dagata cak dukda magiyar da take masa akan ya ci gaba ita bata jin bacci amma be saurareta ba

"Sleep Esha we still have tomorrow inshallah"
Seta lumshe idanunta nan da nan bacci ya dauketa.










🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 4⃣9⃣



"Abdul'ahad issa story time" Hamdah dake tsaya akansa ta fada.
"Wayyo Allah yarinyar nan baki da tausayi, ji nan yanda hannuna duk yayi ja ya kumbura saboda wahalan kama gashinki sannan ko hutawa banyi ba kice min wani story time go on Television ki kalli labarai mana". Kallonsa tayi ta dan harareshi ta gefen ido kafin tayi gaba tana cewa

"Ji kaman wani dayayi abin kirki kitson da duk sun gama warewa ma"

"Haba dan Allah" ya fada yana tashi zaune kitson da ya shafe awa biyar yanayi shi ne za'a ce ya ware. Seta zame hular kanta gashin data tattare ya zubo har kan mazaunanta baqi sidik se walwali yake, babu alamar anyi kitso se farkon kawai inda be qarasa warewa ba.

"Allah ke kika kunceshi seda nace a saka sabulu kika qi yanzu gashi nayi wahalan banza dama kinsan kanki baze kitsu ba kika saka mutane wahala".
"Ko kuma kaidai daga gani akan wasu kace se anyi ai gobe in aka ce kayi bazayi ba" ta fara masa gwalo. Kiran sallar da wayarsa yayi ne ya katse masa amsar daya so ya bata, se ya miqe yana cewa "kiyi alwala muyi jam'i" ya shige toilet. Dayan dakin taje tayo alwalar ta shimfida musu sallaya kafin ta saka dogon hijab dinta ta zauna tana shan ruwa har lokacin be fito ba. Ruwan da taji an watsa mata a fuskaka yasa ta kalleshi, ashe wanka ya yi. Farar jallabiyya ya saka ya fesa turare sannan ya jasu sallar. Bayan sun idar hijab din kawai ta cire ta miqe kafa daidai akan sallayar tana cewa

"Abdul'ahad yunwa nake ji kuma ni dan wake nake so naci da yajin tafarnuwa da tomatoes da onion, boiled egg...."
"Ai seki tashi ki dafa kuwa, wannan uban lissafin ni an ce miki nasan ingredients din hada wani dan wake ne" yai saurin katseta. Seta bata fuska harda buga kafa kamar wata yarinya tace

"Zan nuna maka fa dan Allah in nayi da kaina bazan iya ci ba, in ba haka ba to ka kaini gidan Aliya sena kirata tayi mun"

"Wace ce Aliya?"
"Course mate dina ce"
"Babu inda zakije get up muje kitchen din ki nunamin yanda akeyi". Seta miqe da sauri kuwa ya tareta dan ya tsorata da yanda ta miqe din, "Hamdah meye haka what if you hurt your self or the baby you know i won't takr it lightly with you ko?" Seta saki murmushi, kulawan da yake bata ta daba ce. Abdul'ahad qarshe ne gurin iya soyayya da tattalin mace. Hannunsa cikin nata suka isa kitchen din ya ja mata kujera ta zauna tana bashi command.

Kamar me girka abincin biki haka yayi kacakaca da kitchen din, taimakonta daya danwaken ya hade saboda ita ta zuba masa kuka da quantity din kanwar da ze kwaba dashi. Haka ya damula mata kitchen kamar anyi dambe yace kuma baze gyara ba tunda yayi girki ita tayi wanke wanke. With irritating face yake kallon dan waken data zage tana ci, dan dai kawai Ammi tace yaringa barinta tana cin duk abinda take so shi yasa. Seda tayi nak ta sha ruwa sannan ta shiga gyaran kitchen din yana zaune yana kallon ta dan ya rantse bazeyi ba se tura baki take tana riqe baya a dole ta gaji.

Wunin ranar haka suka yishi se wani shan qamshi yake itama ta debi iskar data kwaso shi ta watsar.

"Anty Hamdah fushi kuma akayi da Abdul'ahad" ya fada daidai sanda ya tsaya akanta tana qoqarin cire dan kunnenta dan ta fara jin bacci, ta gaji da jiran labarin yana sane kuma yai mata shiru. Seta zagayeshi ta haye gadon tana qunquni "dan ma mutum yaga an damu da labarin shine ze wani shanya mutane, to kasa maida yaji ka cinye shi". Seya saka dariya dan yajita, rigar jikinsa ya cire sannan ya kashe haske shima ya hau gadon.

"Malam ka tashi ka tafi can dakin, koma ka tafi apartment dinka mana ana dole ne" Hamdah tayi maganar cikeda tsiwa ganin yana qoqarin shiga jikinta. Seya miqe zaune shima tareda kunna bed side lamp yana kallon fuskarta, "wai duk saboda labarin ne to yi haquri zo kiji" fitilar ya sake kashe wa kafin ya janyota cikin jikinsa kansa akan kafadarta ya fara magana.

CIGABAN LABARI

Shekarata daya a Spain Ammi tazo da kanta da wani sabon al'amari. Idan zaki iya tuna wata yarinya da kike yawan tambayana wa cece ita da nake ajiye da pictures dinta a cikin system dina. Ni'ima yar qanwar Ammi ce Antu Habiba da take binta. Allah ya dorawa Ni'ima sona tun tana yar qanqanuwarta duk da nima ina ji da ita ina kuma shiga sabgoginta sama da duk wata yarinya mace a fadin Familyn 'GALADIMA ABDUL'AHAD MUSA'. Yes Ammina itace Babbar yar Galadima Abdul'ahad mace idan baki sani ba kuma sunansa naci dalilin Galadiman da kike gani a qarshen sunana kenan duk da wasu na tambayana me yasa bana amfani da YARIMA sunan mahaifina.

"Are you Yarima Abdullahi's Son?" Ta dakatar dashi. Dukda a cikin duhu suke amma be kasa gane expression din kan fuskarta ba, seya matsa hannunta kadan yace "Yes, I'm Yarima Abdullahi's Only Son, Abdul'ahad Abdullahi".

Gaba daya se tausayin kanta ya kamata, su dai sun shiga uku kawai. Wannan wane irin bacin suna suka jawa iyayensu haka. Yanzu ace anyiwa Yarima Abdullahi da Prof Ahmad Ammani jika da dan shege me yafi wannan tashin hankali???

"Inason Ni'ima irin son da nakewa su Khadija da Amina kannena. Ban kuma taba mata kallo koda sau daya na soyayya ba saboda kwatakwata bata kai standard dina ba. Ina tausayinta ne kawai saboda irin halittarta. Ni'ima sickler ce ta kuma hadu da ibtila'in ciwuka a rayuwa. Tunda aka haifeta dama tazo da ciwon zuciya wanda ya hanata girma ya kuma dakatar mata da abubuwa da yawa na rayuwarta. Bata fita daga wannan tashin hankalin ba tazo ta hadu da blood cancer still qodarta daya tun tana shekara 10 aka cire mata ita" seta dora hannu aka kawai ta saka kuka tana kiran "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah mun tuba duk wannan bala'in ita kadai??"

"Ko kiyi shiru ko in bar labarin haka" ya fada da kwantaccen sauti. Shi kansa ji yake kaman yanzu abubuwan suke faruwa, hotonta yake gani a idonsa lokacin da take cikin ciwo tayita juyi tana kuka "Yah Abdul komai ciwo yake min wai ni me nayi aka hada ni da wadannan larurorin" kalamanta ada wanda seda yayi da gaske ya fitar dasu daga bakinta. Yayi qoqarin gaske wurin nuna mata baiwace shi ciwo kankarar zunubi ne ta godewa Allah daya jarabceta tun a duniya tayi qoqari kuma ta cinyesu.

Kukan dayaji ta rage ya bashi damar ci gaba da magana yana cewa.

"Saboda wadan nan ciwukan yasa nake janta a ciki ban sani ba ashe ita sona take. Haka nan ta tasarwa da iyayenta rigimar ita aure take so a mata bata so ta mutu ba tareda tayi aure ba kuma ni Abdul'ahad Take so. Ammina dakanta ta taso har Spain ta sameni akan na taimaka Ni'ima zata mutu idan ban aureta ba, a lokacin kin san me nace? Ta mutun kawai shi yafi mata sauqi taya za'ayi na auri matar da bazata amfaneni da komai ba? Matar da wanka da sallah kadai take iyayi da kanta suma wani lokacin in ta kakake ba iyawa take ba taya zata dauki lalurata a matsayin matar aurena??

Na shafawa idona toka a gaban Ammi nace bazan bana son Ni'ima ba kuma zan aureta ba. Idan ma auran ake so nayi a nemomin mace mana na aura se wata ragowan ciwo da na tabbata kyakykyawan riqo na mata seta mutu. Ranar na ga tashin hankalin da ban taba gani ba a rayuwata. Ammi ta durqusa tana zubda hawaye da roqona na auri Ni'ima, tayi min alqawari indai tana numfashi in har ta samu dama zata aura min ke a duk lokacin yuwuwar hakan ta samu. Hamdah ni waye? Ni da nake neman gamawa da duniya lafiya. Ni din da addu'arta ce ta sa na samu duk wasu daukaka da nake taqama dasu a rayuwa sannan har uwata ta durqusa ta roqeni a take na amince Ammi bata bar Spain ba seda aka daura aurena da Ni'ima aka kuma kawota nan.

Farin cikin da Ammi tayi na tabbatar da ya wnake bacin ranta akaina se a lokacin na samu nutsuwa a zuciyata. Daga ranar na tabbata ni kuma nayi sallama da nawa farin cikin. Na rusa duk wani tsari da nayiwa kaina, wata tariga ki zama Mrs ABDUL'AHAD.

Zama na da Ni'ima zama ne na kowa yana cin gashin kansa. Dukda gida daya muke zaune amma ina iyayin sati biyu ban ganta ba bata ganni ba saboda na aje mata duk abinda zata buqata Nurses biyu na ajiye masu kula da ita a gida da likitan da kullum yake zuwa ya duba lafiyarta. Nayi qoqarin ganin rayuwata ta koma normal, na samu sabon aiki sannan naci gaba da karatu saboda ina so na kai qarshen boko kaman yanda kika taba gayamin bazan birgeki ba se nazama Emaratus professor at the age of 40 na dauka wannan aniyar.

Watan mu shida da aure Ni'ima ta taso da wata sabuwar rigimar wai tana so ta haihu at any cost koda kuwa hakan yana nufin rasa ranta ne. Ta samu goyon bayan Ammina. Hamdah bana son wani abu da ze qara saka Ammi tayi fushi dani, dole na nemar mana mafitar dagani har ita. A farko na yanke shawarar bata haqqin ta na aure a matsayinta na mata ta amma se na kasa. Na yarda zuciyata da jikina were only for you Hamdah. I ended practicing my Knowledge on her, I'm sure you are familiar with ARTIFICIAL INSIMINATION??

Seta daga kanta ta kalleshi baki bude, tana jin ana labarin artificial Insimination ta kuma karanta amma bata taba yarda ana yinsa da gaske kuma Yaran suna rayuwa ba. Seya katse mata tunani ta hanyar cewa

"We did artificial Insimination, i lied to everyone cewa Ni'ima bazata iya conceiving ba sedai ayi mata dashe dukda Baba was against the plan at all. Yace beyarda ba mu haqura da haihuwar gaba daya saboda yanayinta. We are not even sure zamu haifi lafiyayyen da batare da ya dakko ko daya daga cikin ciwukanta ba amma Ammi da Umma suka fi qarfinsa. Acewarsu tunda har ita ta nema a barta kilan ta haihu itama ta bar baya a duniya.

The transplant was successful, and Ni'ima was admitted since from day one under intensive care har cikinta yakai wata shida, i couldn't bear to see how she was suffering. Tasha baqar wahala

Please Login or Register in order to submit comment