Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dukka sun dawo dashi. Ranar Monday sukaje gidan harda Hajja da wasu daga cikin kannensa se Amininsa guda daya bayan sun gaisane Alhajin ya fara yiwa Abba magana akan abinda ya kawosu dan Harda lauyan Abdul din suka taho. Hamidah aka aika ta kirawota suna zaune Anty Bilkisu mayar Yaya Baffa ta tasa ta a gaba akan dole yau se ta danyi kwalliya ko yayane tunda ta gama takaba tuntuni. Bakar Abaya tasaka data kara haska farar fatarta dama ta kara kodewa, batayi kwalliyar ba se lip balm kawai ta saka dole ta baka tausayi Dan gaba daya ta susuce ta fita hayyacinta dakyar take tafiya har ta karasa falon Abbah.
Kanta a kasa ta gaida su "Hamdah ya karin hakurinmu?" Hajjah ta tambayeta zuciyarta na Mata kuna gefe daya tana share kwallar data zubo mata na tuno da irin abubuwan data shuka "Alhamdulillah Hajjah" ta amsa mata cikin rawar murya. Shiru sukayi kafin Alh Mansur kanin baban su Abdulmalik ya katse shirun da cewa
"Wato abinda ya kawo mu dai bai wuce maganar rabon gado ba domin zartarda umarnin Allah dakuma saukewa Mamaci nauyi Alhamdulillah a tsahon wannan lokaci kuma ya kasance an samu tsautsayin rasa cikin da kike dauke dashi wanda be riga da ya zama Da ba dan haka bashida Gado, kuma mun gama tattara komai mun kuma samu babu wanda yake binsa bashi haka nan duk wadan da yake bi sun dawo dashi. Sannan mun samu wasika rubutacciya acikin aljihunsa wadda ya rubuta da kansa akan cewa Akwai gidansa da yake gimawa a cikin Nasarawa kyautace ke yake ginawa haka motarki dakike hawa da duk wani abu da ya kasance kina amfani dashi nasa to baya cikin kasafin gado kyauta ce yayi miki" daga nan Lawyer ya dora kan yanda rabon ya kasance.

Allah sarki dukda kasancewar Abdulmalik yaro matashi saidai ya kasance mai zuciya domin ya mallaki abubuwa da dama nasa na kansa, a ciki ta samu gidaje biyu Banda Wanda ya mata kyauta da fili guda hudu se motocin hawa biyu harda favourite car dinsa sai kudi kimanin Naira Million 9.7 Har suka gama magana kanta yana kasa in banda hawaye babu abinda takeyi ayau ta kara tabbatarwa ta rasa Mijinta Har abada rayuwa kenan abinda bata taba koda a tunani ba yau gashi Abdul yabarta. cikin kuka ta kallesu sannan tace "Abbah na yafe bana bukatar komai Mijina kawai nake so kuma yabarni". "Hakuri zakiyi Hamdah Allah ya fimu sanshi bayanda zamuyi" itama Hajjah kukan take sai gashi mutuwa na neman ta dawo musu sabuwa. Da haka taron ya watse bayan ta danqa komai data samu a hannun Abba shi kuma ya bawa Yaya Baffa.


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 2⃣6⃣


Addu'ar data dage dayi ta taimaka mata sosai wurin raguwar damuwarta segashi A hankali har ta fara sabawa da rashinsa. Su Malam Hadiza ne suka dameta akan ta koma bakin aikita hakan ze kara sa ta sake da mutane Amma Mumcy tace ta bari se wannan ramar tata ta ragu tukunna. Akace babu abinda ya gagari addu'a sai gashi a hankali al'amuran Hamdah sun fara daidaita ta fara samun nutsuwa a zuciyarta Dan har tana fita waje. Addu'a dai ba fashi kullum cikin yiwa Abdulmalik ta keyi aikin ma ta ajiye acewarta karatu zata koma yanzu ko zata cigaba da aikin bayanzu ba Dan haka Abbah da kansa ya nema mata gurbin karatu a Abu zaria ta fara Masters dinta, saboda yanayin karatun yasa ta komawa Kaduna gidan Anty zahra da zama dan ta sami sauqin zirga zirgar Kano to Zaria hakan kuwa ba karamin taimaka mata yayi ba Dan Hayaniyar yaranma bata barinta yin wani dogon tunani se karatunta data saka a gaba. Shekara kwana tuni ana lissafin wata takwas da rasuwar Abdulmalik. A cikin kudin gadonta ta ware wasu kaso ta gina masa Boreholes, sannan ta cire fili daya daga ciki tayi Foundation ta taimakawa Marayu da fatan ladan ya jewa Abdul din.

Ana haka watan azumi ya riskesu dan haka Abbah ya shirya musu tafiya zuwa umara ita da Anty Zahra, Hamidah, Mumcy, Junior se Yaya Abubakar da Matarsa. Sunyi ibadah sosai, rabin addu'ar Hamdah ya tafi gurin nemawa Abdulmalik gafara a gurin ubangiji sai kuma fatan Allah yai mata jagora a rayuwarta ya bata dangana dan ita ko kusa ko alama bata tunanin zata qara sha'awar yin wani auran, acewarta zata zauna ta jira cikar nata lokacin. A duk lokacin da tayi irin wannan maganar se Mumcy tayi murmushi kawai tace "wasa kike yarinya masu Yaya ma suna dan gana suyi auransu bare ke da kike ke kadai" ita sedai ta zumburi baki kawai amma ta sakawa ranta babu wani aure da zata sakeyi. Bayan Sallah da kwana uku ranar wata Alhamis suka dawo Nigeria, a Abuja jirginsu ya sauka kafin suka karaso kano. Tun a cikin jirgi take lura da irin kallon da wani mutumi yake mata da kuma murmushi a duk lokacin da suka hada ido, ko bayan sun sauka a Abuja tana kallon yanda ya ringa binau har seda sukayi magana da Yaya Abubakar batasan dai me sukace ba yai masa sallama alamar shi a nan ze tsaya. A take taji kawai ta tsaneshi duk da bata san shi din ko waye ba, mutum kamar maye se wani kallon mutane yakeyi.. Haka tayi ta mita ita kadai har suka sauka a Kano.

Sati daya da dawowarsu misalin karfe 8pm suna zaune a falo suna hira khalifa ya shigo "Ke kije kinyi bako a waje" ya fada yana kallon saitin da Hamdah take zaune. Banza ta masa dan ta tsani abinda ake mata, shikenan saboda mijinta ya mutu se akace musu zata saurari kowa ne? Tsabar rashin sanin ya kamata acewarta kenan har wasu daga cikin Abokanan sa ne sukazo wai neman auranta kamar dama jira suke ya mutu su ce suna sonta. Duk ranar da akayi sallama da ita kwana take tana kuka gani take kamar taci amanar soyayyar Abdul in har ta saurari wani namiji bayan shi, taya ma zata yarda wani ya keta Gonar Abdulmalik?

"Ba dake ake magana bane Hamdah" muryar Mumcy ta katse mata tunani, seta daga kanta ta kalleshi tareda maka masa uwar Harara kamar idonta ze fado. "Madam ya da Harara daga fadar saqo ai bani na turo shi ba shigowa zanyi na ganshi a compound kin san kuwa yana da matsayi tunda har aka shigo dashi cikin gida ba irin zawarawanki da suke layi bane kike saka Sa'idu yana Fafararsu bane".
Kalamansa sun mata daci, wai zawarawanta yanzu fa itama ta shiga sahun zawarawa kenan ko sunan da ta tsana a rayuwarta, nan da nan idonta ya kawo kwalla, seta kalleshi sannan tace "Lallai Khaleefa ka rainani ni zaka kalla kace wai zawarawa suna min layi ina sakawa ana korarsu koda yake ba laifin ka bane, da ace mijina be mutu ba da babu wanda ya isa yai sallama dani" kawai ta saka musu kuka. Duk se sukayi jugum suna kallonta, to shi meya fada da yayi zafi haka har zatayi kuka? Se ya matsa kusa da ita ya zauna sannan ya fara magana
"Kiyi hakuri Yaya Hamdah ba abinda kike tunani bane wallahi ni wasa kawai nake miki amma kiyi hakuri bari naje nace masa ya tafi baki nan" ya mike ya da nufin fita daga palourn. Yaya Baffa da shigowarsa kenan ya tsaida shi dan shi ya aiko shi ya kirata. "Hamdah bakiji wani yana jiranki a waje bane kika zauna kinawa mutane kuka kega matar Mamaci ko, to tun wuri ki koma sensea dinki dan babu wanda ze zauna yana kallonki da qananun shekarunki kice bazakiyi aure ba tun wuri ki tashi ki fita tun kafin na saba miki". Tasan halinsa sarai bashida wasa seta mike tana ci gaba da kukan tana kallon Mumcy da taqi cewa komai.
" A haka zaki fita kanki ko dankwali babu" ya katseta, seta juya dakinta kawai aranta tana ayya na irin wulaqancin da zatayiwa koma wanene. Kayan jikinta ta cire ta canza da baqar Abaya wadda babu ko dingon wata kalar a jiki duk a son ta quntata wa baqon nata, abinda bata sani ba a duk kalolin duniya babu wadda takai baqi yi mata kyau kasan cewarta fara, hula ta saka sannan ta yafa mayafin rigar fuskarta jeme jeme ta fita tana qissima abinda zatayi masa.

Yana zaune a rumfar da suke zama ita da Abdulmalik a lokacin Yammatancinta, tsabar samun guri kujerar da Abdul dinta yake zama wacce take kallon Main entrance din gidan anan ya zauna qafa daya kan daya yana kada Key a hannu sa. Baqi ne Amma ba mai duhu sosai ba haka yana da kyan fuska da kallo daya zaka masa ka gane hakan. Kaftan ne a jikinsa light blue dinkin zamani kansa babu hula hakan ne ya kara fito da zallar Quruciyarsa in ba ma tsaurin ido ba ina ita ina wannan "Kedin nawa kike just 25 fa" zuciyarta ta raya mata. Tana kallon yanda yake yaqe mata baki daya hangota, se mike tsaye yana cewa "Barka da fitowa sarauniyar mata". Wani kallon rainin hankali tayi masa kafin ta tsaya kerere akan sa dan maganar sa haushi ta bata dama zuciya a kusa se kawai ta saka masa kuka.

"Subhanallahi Hajia Hamdah me kuma ya faru ko sarauniyar dana fada ne ya bata miki rai". A maimakon ta kulashi se ma qara volume din kukanta data yi kara har seda tayi me isarta sannan tayi shiru, kallonsa tayi taga yanda yayi tagumi ya zuba mata ido kawai Kaman ya samu Tv. "Kar ka kara zuwa gidan nan inma kuma kazo to ka tabbata gurin wani daban badai ni ba saboda ni nagama kula kowanne da namiji a rayuwata in ma baka sani ba to Bazawara ce ni na taba aure kuma mijina ya mutu ya tafi da dukkan wata soyayyaya ta tun wuri kasan inda dare ya maka ka samawa kanka lafiya ka ka rabu dani" tana gama fada tayi gaba abinta ba tare da ta jira jin ta bakinsa ba.
Se kawai ya bita da kallo kalmar bazawara data fada tana masa yawo akai dan shi ko kadan be zaci ba budurwa bace ba, koma dai yaya take ya riga da ya fara sonta kuma sonta dada fizgarsa yake musamman ma yanzu daya ganta gata gashi, Kansa ya shafa yana murmushi, a fili ya furta "Dole na same ki yammata Dan ban taba neman wani abu na rasa ba Hamdah" sannan yaja kafafuwansa ya fita yana ta faman doka murmushi kamar sabon wawa.

A tsakiyar palour ta zauna kamar karamar yarinya tana kuka tamkar yau Abdulmalik din ya rasu, ido kawai suka sa suna kallonta gefe daya kuma dukka ta basu tausayi Dan ko ba'a fada ba sunsan kukan me takeyi, haka ta kusan raba daren ranar tana yi mutuwa kenan mai tonon asiri badan ita ba me ze hada ta da wani har ya biyota gida wai da sunan soyayyah da haka bacci ya dauketa, Hutun da bata karasa ba kenan ta tattara ta koma Kaduna sedai a banza Dan yanda kasan an budewa samari bama masu mata ba kofar zuwa gurinta haka suke ta tururuwar zuwa gurinta ita kuma tace kuka Salamu alaikum. Sau dari namiji ze mata magana sau adadin haka zatayi kuka a rana duk nacin mutum kuwa haka ze hakura dan bata ko kulasu sedai ka gaji da naci ka tafi in taga mutunchinka sosai nema zata tanka ka harta ce maka tana da Matar aure ce ita.

Sun gama lectures se research work kawai ya rage mata hakan yasa kullum tana gida in dai ba wani muhimmin fita ba to zaka sameta a gida tana bacci ko tana karatu. Wata yammacin juma'a suna zaune Yaya Nazir (Mijin Anty Zahra) ya shigo tare da bako, kallo daya tayi masa ta ganeshi wannan mutumin da yaje gurinta a Kano ne me bala'in nacin masifa se a yanzu ta tuna inda ta taba ganinsa ma shine dai wannan mayen me kallon tsiyar da suka hau jirgi daya da Azumu. Yanda suka gaisa da yayar tata ya tabbatar mata Akwai sanayya sosai a tsakaninsu Haka Su Amrah sun sake dashi sosai se murnar tsarabar daya kawo musu sukeyi. A bakin Arif taji sunansa wai Uncle Abdurrahman ga mamakinta ko kadan be nuna wata sanayya a tsaka nin su ba yanda ta basar dashi haka shima ya shareta harya tafi.

Bayan da Yaya Nazi ya dawo daga rakashi cikin murna yake gayawa Zahra wai fa Abdurrahman din ya gaya Hamdah kuma yana son ta da Aure bada wasa ba. Cikin jimami tace "Tab Amma dai Daddy kamanta wace ce Hajara ko da har kake tunanin yin jagora ayi mata kishiya koma ba haka ba bana tunanin ma Hamdah zata saurareshi dan kana dai ganin irin tata burzar da ake da ita ta kafe akan ra'ayin bazata sake aure ba".
"Ai kinga halin naku tun daga gurinki ma an fara samun matsala yanzu Ina ruwanmu da wata Hajara ita ke iko dashi ko yaya, sannan in ma kina wani tunani duk fada ce ta mutane da ake cewa tafi qarfinsa Amma ba ruwan ta akan fitar da Matan sa sukeyi haline kawai beyi dace ba har yanzu kuma ko zabi aka baki kinsani Hamdah ita ce daidai da tsari da halayyan Abdurrahman". Seda ta danyi Jum saboda kwata kwata ita abin be kwanta mata a rai ba to amma bazaka ja da lamarin Allah na dab basu san meya shirya ba se kawai tace "To Allah ya tabbatar da alkairi Amma nidai ba ruwana karma ka lissafoni a cikin sha'aninku can in sun daidaita falillahi Hamdan".
"Yawwa Maman Arif ko kefa Amma da zaki sake mana gwuiwa ko kinawa Aminina bakin ciki samun irin ni'imar da nake ciki ne" pillow ta cilla masa tana cewa "Nidai babu ruwana".

Kwana biyu a tsakani Abdurrahman ya kuma dawo bayan doguwar magiya da lallashi aka samu ta fita gurinsa sedai Kaman wancan lokacin yau ma kuka ta tasa shi agaba ta ringa rusawa abin har ya fara bashi tsoro kodai aljanu ne da yarinyar? Haka ya tattara kafarsa ya tafi aransa ko ya kudurce ko kukar bulukiya ce akan ta baze rabu da ita ba. Tun daga ranar ya mayar da gidan wurin zuwansa duk da bata kulashi wataran ma ko fitowa bata yi haka ze gama zamansa ya tafi karshema data gaji ba Wanda ta gayawa se ganin ta sukayi da jaka wai kano zata tafi sanin magiya bazata sakata ta zauna ba yasa suka kyaleta ta tafi. A kanon ma bata sauya zaniba Dan Duk sati yana kan hanya dukda ba fuska yake samu ba Amma bai gajiyawa.
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 2⃣7⃣

3 weeks later.
Tana kwance daki Dan wunin ranar gaba daya a ciki tayishi, Annur yaron Yaya Abubakar ya shiga da bindigar wasa a hannunsa, kan gadon yayi tsalle ya hau yana mata dariyar sa irin ta yara sannan yace " Mami granny is calling you". Gaba daya Niece da Nephews dinta Mami suke kiranta dan tace bata son Anty Hamdah. Doguwar riga ce me hannun spaghetti a jikinta se ta dora dogon hijabin sallarta har qasa akai ta kama hannun Annur suka fito daga daki. A downstairs ta tarar Mumcy se Ahmad tsohon Aminin Abdulmalik da yazo, cikin girmamawa suka gaisa yanda suka saba a shekarun baya dayake abokin mijinta tana tambayarsa Ummi matar sa da kuma yaransa Shuhuda da Shahida. Yanayin yanda ya kasa sakewa se ya sa Mumcy ta tashi dan ta basu gurin bata san meya kawo shi ba a lokacin, gaba daya sukayi shiru bakajin komai a falon se karar Tv da Ac dasuke aiki ita tana jiransa yayi magana shi kuma ya rasa ta ina ze fara mata maganar.

"Haj Hamdah ashe kinzo gari seda jiya naje gaida Hajjah Kausar take gayamin sunzo gaisheki jiya wai Kina Kano". Dan murmushi tayi sannan tace "Eh wallahi ai na ma kwana biyu da zuwan". Wani shirun suka sakeyi, agogo ta kalla sannan tace masa " Yaya dai in babu wani abu ina so in koma akwai dan aikin da nake qarasa a ciki". Seda ya tattaro dukka jarumtarsa sannan ya fara magana cikin qarfin Hali "Am nasan zakiyi mamakin ganina da kuma jin abinda nazo miki dashi sedai ba wani abu bane inkika yi laakari da alakata da marigayi..." sai kuma yayi shiru yana tunanin ta yanda ze sanar da ita abinda ke zuciyarsa.
"Ya kayi shiru kuma Ina jinka" ta fada tana tsareshi da ido, sai kuma ta sakeyi masa kwarjini nan da nan ya duburburce ya fara in ina "Toh dama dai na samu Hajjah munyi magana inji ko cikin yan uwan shi marigayi Akwai Wanda zai nema to ta tabbatar min da babu kuma ta nuna goyon bayanta sosai Dan itace ma tace inzo Dan kuma kar a samu sabani "tun kafin ya dire maganar fuskarta ta fara chanzawa zuwa matsanan cin fushi da bacin rai jikinta har rawa yake tace "sai akai yaya kuma" seda ya hadiyi wani yawu sannan yace "Dama inaso ne idan zaki amincemin in maye miki gurbin Aminina tunda dama ance ko Dan uwa ko Amini ma......" "kai dallah Malam dakata" ta katse shi ciki tsawa sannan ta miqe tsaye tana nuna masa qofa.
"Tashi ka fita kuma kar na qara ganin kafarka a gidan nan, yanzu kai ko kunya baka jiba ka kalleni kake gayamin wadannan maganganun wai zaka maye gurbin abokinsa kai bame tayashi kishi da kare mutuncina koda wani kaga yana kokarin hakan bazaka hanashi sai kai da kanka zaka debo wasu munafukan ledojinka to bari kaje wadanda kake kawo wa ma shekara daya ban taba ko da duba abinda suke ciki ba dan ni koda Mijina ya Mutu be barni da tsiya ba yabar min komai najin dadin rayuwa ka kuma san da haka shine zakace kana sona wato dama jira kake ya mutu kenan ka aureni" ta karasa tana mai fashewa da kuka, se ya mike a kidime yana cewa
"Subhanallahi Hamdah me yayi zafi wace irin magana kikeyi haka s ganina wannan ai shine kadai abinda zanyi masa na aureki na riqe masa ke amana".
"Tashi Malam tunda ka gama abinda ya kawo ka, ka tabbatar kuma kafarka karta kara tako gidannan in ba haka ba you will regrate my action" bashida sauran bakin magana a dole ya tashi jiki a sabule, Mumcy data gama jin duk abinda suke fada ta fito da sauri tace "Dan Allah Ahmad kayi hakuri kaji kar abinda taimaka ya bata maka rai kasan yanda al'amarin nan ya kasance har yanzu bawai tagama komawa daidai bane" se yayi saurin tareta da cewa "A'a wallahi Hajiya ai babu komai nine ma ya kamata in bada hakuri gashi daga zuwana na sakata kuka, sai anjima Allah qara hakuri" ya juya ya fice daga palour.

Fada sosai tashiga yi mata "Fisabilillahi Hamdah sai kace akanki a ka fara mutuwar miji da zakibi ki tsangwami rayuwarki daga an miki magana ki hau kuka ke ga Matar Mamaci ko, nida na rasa uwata da ubana ma da babu madadinsu amma nayi hakuri se ke da mijinki ya mutu idan baki saurare kowa ba taya zaki samu wanda hankalinki ze kwanta dashi ko kuwa haka zakiyi ta zama muna kallonki."
"Ni Mummy bazan iya cin Amanar Abdul zan jira nima har mutuwa ta daukeni inje na tarar dashi muci gaba da rayuwar mu yanda muka fara ta". Se kawai ta buda baki tana kallonta da mamaki, lallai abin nata yayi nisa bata ko jin kira tasan ko me zata fada bazata ji ba ayanzu dan haka kawai ta gyada kai tana ayyana abinda zata mata a ranta a fili kuwa se tace "toh Allah ya sawwaqa yanzu tashi ki dora mana Abincin dare dan Yau Abbanku ze dawo duk da nasan ba da wuri ze shigo ba", kitchen din ta shiga har lokacin bata dena share hawaye ba, zaman shekara daya ace har an gaji da ita a gidan ita da ba sabgar kowa take shiga ba dole ta nemawa kanta mafita, zaman nan baze kaita ba dole ta nemi abinyi taga alama harda shiru shirun da takeyi yasa aka fara rainata dan haka ta daura aniyar komawa Ainihin Hamdan ta. Tun daga wannan rana ta sake sabon babi, ta koma Hamdah Ammanin ta matsiwaciya da bata barin ko ta kwana. Ya zuwa yanzu ta rage damuwa sosai tayi kiba abinta duk wannan ramar ta cike, dole ta birge ka yanda ta qara zama wata classy Babe, dama ya lafiya kura bare yanzu da take juya kudin kanta gayu se wanda ya qaru abinda yake qara rudar maza akanta kenan kwalliyarta. Idan kaganta bazaka taba mata kallon wadda ta taba aure ba a shekaru ko a yanayin jiki dan ta qara zama wata yarinya danya in suka jera da Hamida ma seka dauka ita ce qarama dan Hamida tafita tsahl da girman jiki in ba ka kalli idonsu ba ko kuma a magana, sosai take Fafatawa yanzu Har su Maryam na tsokanarta wai zawarcin ma me lasisi takeyi se dai kawai tayi murmushi dan qarfin hali kawai takeyi ba wai har zuciyarta ba. Taga alamar in ba ta sake da walwala ba baza'a dena takura mata ba.
Acikin maneman nata Abdurrahman Dan anace ne ya kafe Dan shi wulakanci datake masa baya damunsa seya ce wai ba'a samun abu me daraja da sauqi, ya kwallafa rai akanta ya kuma tabbata seya sameta dan se a yanzu ya gane ita ce irin macen dayake so. Shi jin ta taba auranma wani qaunar ta ya qara masa be dauki hakan a matsayin wata matsala ba ko kadan dan haka ya liqe har seda ya fara samu karbuwa a gurin mutanen gidansu ta silar Nazir mijin Zahra. Su Malam Ahmad dai tun tijarar da tayi masa be kara dawowa ba duk da ada yaso auran Hamdah saboda mace ce ta kwarai da kowanne namiji zeyi fatan samunta ko ba komai yana so ya kwatanta bata kyakykyawar rayuwar da Amininsa kullum yake fatan samar mata. A lokacin yana raye bashida wani burin da ya wuce na Hamdah taji dadi Hamdah tayi walwala yana so ko bata fi kowacce mace sa'a ba to a sakata a layin farko se gashi beyi dadewar da ze cika mata dukka burikanta ba.

A kace mahaqurci mawadaci se gashi a hankali juriya da naci irin na Abdurrahman sun fara masa amfani dan har ya fara samun galaba akan ta, ba laifi yanzu tana amsa wayarsa dukda gaisuwa ce kawai komai ze fada bazata tankashiba se yaci Sa'a zata bishi da Eh ko Aa haka ko gida yazo wani lokacin tana fita kuma ta dena kukan da takeyi Amma fa hakan bawai yana nufin zata aure shi bane Aa sedan Fadan da ake mata kullum akan wulaqanci babu kyau. Ita dai ta qudure a zuciyarta fa ta gama aure.
****************************
Yau da wuri ta kwanta saboda Mararta data dameta da ciwo. Cikin baccin ne tayi mafarki dashi da shi karo na farko tun bayan rabuwarsu.Tafiya takeyi cikin wani katon fili fetal da bata iya hango karshensa lokaci daya tsoro ya rufeta ganin ita kadai ce a gurin babu kowa Kamar daga sama taji an kira sunanta sannan wani hannu me laushi ya riqeta ta baya seta juya a tsorace, Abdulmalik ne cikin kyakykyawar shiga ta fararan kaya fuskarsa na fitar da wani irin kyalli da haske yana yi mata murmushi daya sace mata zuciya dashi. Cikin tsananin farin ciki ta kankameshi tareda fashewa da kuka da kuka se shima ya rungumeta a jikinsa yana buga bayanta alamar rarrashi har lokacin beyi magana ba, seda ta tsagaita kukan nata sannan cikin muryarsa da bazata taba mantawa ba yace "Hamdah ta Nagode Nagode kwari tabbas kin cika masoyiya ta Hakika a kullum kyawawan addu'oin ki suna tarar dani ga lada dana ke ta samu duk ta sanadiyyarki Amma me yasa kullum kike kuka bana so". Seta share hawayenta sanna tace masa " Abdulmalik na kasa sabawa da rashinka, kullum bani da burin daya wuce in sake ganinka nayi jiran wani yazo yace min da wasa ake min baka mutu ba zaka dawo amma ban samu ba, bani da wanda ze rarrasheni a lokacin da nake kuka amma kaqi ko a mafarkina ban taba ganinka ba" ta

Please Login or Register in order to submit comment