Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qarasa tana sakin wani qaramin kukan. Murmushin ya kuma yi mata sanna yace "Hamdah kin taba ganin wanda ya mutu ya dawo? To kiyi hakuri na tafi na barki har abada a zahiri amma zan dawwama cikin zuciyarki har zuwa lokacin da Allah ze qara hadamu amma kin san mene" seta girgiza masa kai alamar A'a. Se ya cigaba "Banji dadin yanda kika qiyin aure ba akwai wani abu daya wuce kasan cewarki cikin gidan aure"
"Abdul bazan iya cin amanar ka ba bazan iya zama da wani ba kaiba"
Hannayenta biyu ya riqe sannan yace mata "In dai Dan ni ne kiyi aurenki kinji shine cikar mutuncinki bazanso ki tarar dani a haka ba Hamdah kamar yanda na Mutu Ina Mai aure haka kema nakeso ki samu wannan rabon kinji in ba haka ba zanyi fushi dake ba zan kuma kara zuwa ba". Cikin zubar da hawaye tace masa "Kar kayi fushi dani zanyi Insha Allah". Hawayen ya shiga goge mata sannan yace "Yawwa yar albarka Kaman yanda kika zamarmin jari a duniya kema Allah ya baki Wanda ze yi miki Hakan a bayan ranki kalli can ki gani" wani guri ya nuna mata dan nesa dasu, wani mutum ta gani a zaune ya juya musu baya bata iya ganin fuskarsa, juyo da ita yayi sannan yace "Kin ganshi shine madadina a gurinki, shikadai ne mutumin dana yarda yana miki irin son da nake miki amma kin san me" "Aa" ta bashi amsa. Se ya ci gaba

"Wai fushi yake dakowa akanki, ya rabuda kowa da komai nasa saboda ke, kiyi min alqawari zaki nemeshi ki dawo masa da Farin cikinsa daya rasa ta sanadiyarki". Qanqame hannayensa tayi tana hawaye tace " Bazan i...." Se ya katseta "Alfarma zakiyi min ko akwai abinda zan rokeki ki kasa yinsa shikenan ni na tafi" ya juya kamar ze bar gurin, setayi saurin riqo shi tace "Na maka alqawarin zan nemoshi a duk duniyar da yake, zan bashi duk wani farin ciki dayake nema iyakar abinda Allah ya horemin". Se ya saki wani murmushi me kyau sannan ya kama hannunta suka qarasa har gaban mutumin da har lokacin bata ga fuskarsa ba. Hannunsa ya kama ya hada da nata yace " Ga Amanata nan kariqemin ita dakyau" sannan ya kalleta ita ma yace" ki gaidamin da Hajjah ki gaya mata na yafe mata dama ni ban taba kullatar ta a raina ba nasan ko mai ya faru muqaddarine na barki lafiya" daga haka ya bace mata.

Kokarin kwacewa daga hannun mutumin ta farayi se a lokacin ya dago fuskarsa, "Sir Abdul'ahad" ta faa cikin son tabbatar da abinda idonta ya gani, be kulata ba ya fara jan hannunta dan subar wurin suddenly sega wannan nataccen ya fado kamar an jefoshi ya fizge hannunta daga na Abdul'ahad yana cewa "Bazan barki ki bi wani ba ke tawa ce". Kallon Abdul'ahad daya tsaya ba tareda yace komai ba tayi se yayi dan guntun murmushi sannan yace "Let it be, kuje kawai" ya juya ya barsu a tsaye shima. Seta fara ihu tana fadin "Abdulmalik ka dawo Dan Allah karka tafi kazo ka rabani da wadannan mutanen basu cancance ni ba" abinda take maimaitawa kenan acikin baccinta har maganar tata ta fito fili bata sani ba. Mumcy da ihunta yafarkar da ita ta shiga dakin babu shiri ta shiga tada ita da alama bata cikin hayyacinta. Kuka sosai takeyi tana gaya mata yanda sukayi da Abdul din A ciki mafarkinta, seta rungumeta cikin lallashi tace "Ki dauka hakan nasiha ce aka miki, kiyi hakuri Hamdah ki mikawa Allah lamuranki ki nemi zabi sa sekiga kin samu fiye da abinda kika rasa kinji" haka tayita lallashinta har ta samu tayi shiru, tunaninsa fal a zuciyarta se kuma ganin Sir Guru daya makale mata a zuciya, rabon data tuna dashi har ta manta, dama motarsa ce take gani ta tuna shi to tun bayan da akayi musu gyare gyare a gidan aka dauke ta aka boye a garage dan Abba yace ayi ta ajiyarta har ranar da me ita ze waiwayi abarsa tunda tace bata san ina yake ba. To ta ina zata fara neman sa ma ita yanzu? Abu daya tayarda idan har Allah ya hukunta wani al'amari a tsakaninsu komai tsahon lokaci ze dawo duk ma inda ya tafi, da wannan ta samu ta yakice tunaninsa a zuciyarta.

Kwana uku ta jera tana salatul istikara sannan ta dage da addu'a akan neman zabin Allah, a ranar data cika ta ukun ne tana zaune Abdurrahman wanda sun fi sati basuyi waya ba ya kirata. Tayi qoqari sosai suka danyi hira abinda bata tabayi ba ko ba komai yanzu kashi 70 na nauyin da takeji a zuciyarta ya ragu. Se a yanzu take ganin wautarta at 25 years har take tunanin ta gama aure, kwadayin haihuwa da son yiwa Abdulmalik takwara su suka kara saka mata azamar son tayi auran, cikin maganar ne yake gaya mata ai yana kano se tace masa yazo in ya samu lokaci tana son magana dashi.

Kamar me jira da yamma se gashi yazo, tana zaune ya kirata akan gashi a waje lokacin Mumcy bata nan tana asibiti daga ita se Mama Asabe da Annur da aka kawo dazu, bata shafa komai ba ta zura dogon hijabinta dark purple ta fita. Tun daga nesa yake kare mata kallo a Gaskiya in ya rasa yarinyar nan bai san yanda zeyiba. Dukda fuskarta babu kwalliya Amma ta masa kyau musamman yanzu da ta qara cikowa fatarta har wani kyalli takeyi. Kallon qurillar dayake mata ya sakata harararsa qasa qasa dan ta tsani kallo shi kuma gashi kamar maye yayi ta wani kallonta yana wage baki kamar Wanda akayiwa wata kyauta.
Ba yabo ba fallasa suka suka gaisa sannan ta fara magana "Na kiraka ne badan komai ba se mu fahimci juna tunda kasan nidin ba yarinya bace da zamu tsaya bata wani lokaci Dan haka Ina so insan kai waye". Se ta bashi dariya wai ita ba yarinya bace in banda abinta har nawa take yasan dai ko Zahra matar Nazir bazatafi 30 years bare ita kanwarta ta biyu, se yayi dan murmushi sannan yace " Dan Allah wai ni shekarar ki nawane" seta qara hade fuska a dole bata son raini sannan tace "25 meya faru"
"Aa ba komai" ya faa yana danne dariyar sa ashirin da biyar shine Amma take kiran kanta babba bayan ko shekarun wasu Yammatan ma bata kai ba se kawai yace "To ba matsala Malama nima ba wasa ne ya kawo ni ba maganar aure ce kuma Kaman yanda kika tambayeni Suna na Abdurrahman Ibrahim Khalil. Mahaifina Ibrahim dan Asalin Kankara ne Mahaifiya ta Maimuna kuma yar katsina amma duk a Katsina suke. Babana Dan siyasa ne nasan bazaki rasa sani Barr Ibrahim Khalil ba tsohon Governor Katsina state kuma Senator me ci a yanzu. Bazan iya gaya miki wasu abubuwa da yawa ba akan Katsina saboda ni a Kaduna aka haifemu acan mahaifiyar mu take zama dayar abokiyar zamanta kuma tana Katsina, sannan tun a kananun shekaruna aka kaini kasar England a hannun Yayan mahaifina na tashi acan nayi secondary school dina har na gama karatuna na Jami'a nidin Psychiatrist ne wato Likitan Masu lalurar kwakwalwa" se yayi shiru yana kallonta. Ita ma shi take kallo jin yayi shiru yasa tace "ci gaba ina jinka" gaba dayanmu mu goma sha biyu ne yaran gidanmu maza biyar mata bakwai kuma ni ne na shida Inada yayye Biyar Maza biyu Mata uku gaba daya duk sunyi aure se autanmu Isma'l kadai ya rage. Shekaruna 38 kuma Ina da Mata guda daya Hajara duk da na auri wasu bayan ita Amma dai yanzu dai ita kadai ce wannan shine Abdurrahman Khalil a taqaice".
Kallon mamaki take masa jin wai He is 38 mutumin da take ganin kaman baze wuce 29 ba yayi wuta yaje irin 32 dinnan, se kawai ta gyada kanta sannan tace masa "To Allah ya wuce mana gaba" ta mike tsaye. "Yadai ranki ya dade shikenan dama"
"Eh" ta bashi amsa tana shirin barin wurin, Annur daya fito ya kira yana dan yi masa wasa sannan yasa hannu a aljihu ya jiro bundle na yan 1k ya bashi yace "Ungo ka kaiwa Anty ta siya muku chocolate kusha" se yaron ya karba da murna jin an kira chocolate yabi bayanta dan lokacin har taje kofar daki, Sa'idu ya kira ya kwashe uban siyayyar daya yo mata ta kayan kwalliya, turaruka da sauran tarkacen mata sannan shima yayi masa alkhairi ya tafi. Kallo daya tayi musu ta dauke kai karshema tace bata so Hamida da Maman Annur se wata cousin dinsu data zo su dauka su raba, kudin ma karshe Khaleefa ne ya karba bayan ya cirar wa yaron kudin Alawa ya jefa su a aljihu yana cewa "Allah yaci gaba da hankado masu rabon shan wahala ni kayan nan ma da bani kukayi na fara tarin lefe wlh nasan ajikin Zawarawan Hajia Hamdah tsaf zanyi akwati 12" dariya suka saka gaba daya banda Hamdah data debi pillows ta fara jifansa dasu yana cigaba da mata tsiya.









🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 2⃣8⃣

Cikin satin daya Magana ta fara yin qarfi a tsakaninsu dan Har Abdurrahman din ya turo neman izini kamar yanda yake a shari'ar musulunci. Sai ayanzu ta yarda da abinda Maryam take fada mata akan seta bawa mutum dama sannan zata ga abinda ze iya Dan Abdurrahman din ya bata mamaki karshene a soyayya da iya tattali, sau tari in ta tuna wasu abubuwan da ringayi masa setaji kunya dan kamar yanda yai mata alkawari se ya goge kowa da komai daga zuciyarta to yana shirin tabbatar mata da hakan dan in har suna waya sata yakeyi ta manta da kowa da komai din se shi kadai take tunawa.
Kamar yanda suka tsara cikin sati biyu Yan uwan sa suka kawo kudin aure da gaisuwar iyaye 500k se kudin sa rana 100k aka kuma tsayar da magana akan sati hudu kacal acewar Abbah ba abinda za'a jira tunda dai anyi bincike bashi da wani hali mara kyau. A Cikin abinda bai wuce sati biyu ba Amarya tayi fes ga wani kamshi na daban da take yi wannan karon Hajjah da kanta take mata wannan gyaran dan a yanzu ta dauketa ne kamar yar cikinta nidai nace duk a banza tunda bana Allah da Annabi bane. Biki ya rage saura kwana goma suka kawo lefe na gani na fada Dan har yafi lefenta na auran fari, kayane iya ganinka tun suna irgawa har suka gaji wasu abubuwan ma dai gasunan kawai kamar ba'asan darajar kudi ba, a ranar Hamdah tayi kuka, kuka bana wasa ba. Se ta ringa tuna ranar da aka kaqo lefenta na auran Abdulmalik da ko kallon arziqi basu samu a gurinta ba dan a lokacin zuciyarta tayi fukafiki tana ta yawo a sama.

"Abdulmalik ban sani ba ko wannan shine zabinka, shi ya fado hanyata a lokacin danake tsaka da addu'ar zabin Allah dan haka na rungumeshi na dauki auransa yana cikin jerin _RUBUTACCIYAR QADDARAH_ ta. Zan yi aure zan zauna lafiya insha Allahu zanyi duk yanda kace" kalaman da take ta fada kenan tana rungume da hoton Abdulmalik dayayi kyau sosai kamar ka kirashi ya amsa. Sallamar Aysha ce ta katseta, seda ta share Hawayen fuskarta sannan ta dauki Miima Yarinyar da Aysha take goyo da take ta faman mika mata hannu alamar ta dauketa.
"Amarya kinsha kamshi ashe kina daki ko duk Amarcin ne ya fara boyeki" Aysha ta fada tana zama akan stool din gaban mirror. Murmushin yaqe Hamdah tayi taba ci gaba da yiwa Miima wasa dan bata so ta dago kanta Ayshan ta fahimci halin da take ciki. Juyawa Aysha tayi idonta ya sauka akan hoton Abdul din data ajiye a gefe take jikinta yayi sanyi itama se ta kasa cigaba dayi mata magana. Zaman kurame suka cigaba dayi har seda Parrot Afeeya ta shiga dakin da Jaririnta Asad dan wata uku me dan banzan kukan tsiya lokacin ma kukan yakeyi, dungurar dashi tayi kusa da Hamdah tana cewa "kai Jama'a nifa dan nan ya isheni ayi yaro se shegiyar rigima ba sakat wani ya daukeshi se kuka"
"Ikon Allah abinda ka haifa ne kuma ze dameka Afeeya ga jarabar son yaya amma bazaki iya kula dasu ba" Aysha ta fada tana daga Asad dake ta chanyara kuka. Kayan jikinsa ta rage masa nan da nan kuwa se gashi yayi shiru seta ce "Bawan Allah ashe zafi ne ya dameshi wai halan mantawa kike a Nigeria kuke da kike sinqeshi da uban kaya tsabar mugunta kisa masa riguna har uku".
" Ki kyale wannan yaron wlh haka yake da shegen rigima so nake ya saba da kaya masu nauyi dan mun kusa komawa kuma lokacin sanyi za'a shiga" cewar Afeeya, haka suka ci gaba da tattaunawa dukka dai akan yara ita dai Hamdah ta tafasa bata ce musu ba har Maryam da Anisa kanwar Mijinta suka shigo.
"Amarya nafa manto saqonnan se dai in kin samu lokaci gobe ko jibi ki shigo dan inna koma yau gaskiya bana jin zan kuma iya fitowa" Maryam ta fada tana zama dakyar a gefen gadon saboda jikinta da yayi mata nauyi sosai qarfin hali kawai takeyi, da kallon tausati ta bita, gaba daya ta sauya saboda tsohon cikin da take dashi, na uku kenan bayan Ruqayya ta kuma haifar Aliyu se yanzu kuma wannan cikin, har tsiya suke mata wai tayi sauri se tace gara ta maida abinda ta zubar. Basu wani dade ba kowacce ta tafi gidanta tunda dama duk da motocinsu suka zo.
Da daddare Abdurrahman yazo wai akan yaji tsarinta me dame zatayi na biki, kallonsa kawai ta ringayi gani take ma ya raina mata hankali se kace wata yarinya har ma yake tambayarta me zatayi da biki ko kuwa ance masa wani son auran takeyi, se kawai tace masa "Abubuwa da yawa inaga sati zan yi ma ina shagali se inda kudina ya tsaya" ta fada cikin sigar gatse shi kuwa gogan a tunaninsa da gaske ta ke se kuwa cewa yai
"Kai amma naji dadi da i was thinking se Thursday zamuzo kano Friday daurin aure kice na taho tun Monday kawai".
Seta ce masa " Eh koma tun next week kai kayi zamanka ma kawai daga yau se an daura se mu tafi tare kawai". Se a sannan ya gane inda ta dosa, dan murmushi yayi yana shafa kansa sannan yace "Allah baki hakuri amma please tell me how much you will need for the wedding ko ke bazakiyi komai ba. i'm sure Mum will do". Kafewa tayi akan bazata karbi ko sisi ba har abin ya bata masa rai, shifa har yanzu ya gane bafa wani masauki ya samu sosai a zuciyarta ba, àmma ba komai wuyarta daya dai a daura yasan Seta biyu ta yanda yake so dan haka se ya mike ya qarasa cikin motarsa ya dakko wata babbar Envelope da ya taho da ita kamar yasan zasuyi haka, miqa mata yayi yana cewa " Gashinan manage this in da buqatar qari se ki gayamin and get ready there will be a grand dinner at Kaduna bayan an kaiki"
"Bazan iya halarta ba" ta katseshi, se ya daga kafaar sa dukka yace "Fine, gobe da safe zan tafi kilan se Thursday koma Friday morning din feel free to call me if you need anything" ya juya yai tafiyarsa.

Juya Envelope din hannunta take dan ta mata nauyi, seta juya kawai ta koma cikin gidan. A parlour ta tarar da Su Zahra da Anty Amna se Mumcy da Maman su Maryam da wata abokiyar aikinta Dr Ramla da sukazo tare da Maman su Maryam din, tana shiga sukayi musu sallama suka tafi suna ta tsokanarta wai Amarya. Anty Amna ta miqawa envelope din
"Wannan kuma na mene ne" ta fada taba qoqarin yage bakin takardar, hannu ta watsa alamr oho ta zauna tare da miqe kafarta tana chanza channel. Zaro ido Anty Amna tayi ganin uban kudaden da suke cikin katuwar envelope din,

"Anty Maryam kallu ki gani 5M ne cif" ta fada bakinta na rawa kamar bata taba ganin kudi masu yawansu ba, kallon kudin Mumcy da Zahra sukayi sannan suka maida hankalinsu kan Hamdah tata qurawa Tv ido suna neman qarin bayani.
"Wannan kudin daga ina" mumcy ta tambayeta, batare da ta juyo ba ta bata amsa da "Abdurrahman ne ya kawo wai na hidimar biki in basu isa ba a gaya masa".
"Basu isa me ba, wato da aka ce karya saka komai na furnitures din shine ze baki kudi har Million 5 kiyi me dasu ko ke kika ce masa kina buqata" Mumcy ta qara tambayarta, seta juyo ta kalleta sannan ta mayar da kanta batare da tace komai ba

"Mumcy wannan fa ba komai bane akan irin abunda Abdurrahman yakewa mata in zeyi aure, shifa kamar besan darajar kudi ba haka yake akan mace nidai tsorona yanda auransa basa zuwa ko ina amma dai kunce kun amince kuma Abban su Amrah ma yace ba matsala to Allah yasa hakan" Zahra ta fada bayan data sauke tagumin da tayi, ita dai har ga Allah auran be kwanta mata arai ba. Tasan matarsa farin sani kishiyoyi biyar ta kora duk ciki wadda ta dade itace tayi wata shida qarqarin dadewarsu wata biyu uku ne suke fita dan ta qarshen ma daya saka satinta uku ta fita Duk da wasu sunce wai matan dan kudin daya ke kashe musu suke auransa sabida in ze auri mace bata zuwa da ko tsinke sannan duk wadda ya saka seta tattara komai daya siya mata ta tafi dashi to wai auran neman jari sukeyi.
****************************
Ranar Tuesday ya rage saura kwana uku daurin auranta ta shirya zuwa gidan Maryam karbar wasu kaya data siya a hannunta dan tana so ta gama hada kayayyakinta a daren ranar washe gari za'a kaisu Kaduna. Gaba daya satin dauriya takeyi bata jin dadi kwata kwata ga faduwar gaba data ke yawanyi har Mumcy tayuwa complain tace ta dage da addu'a insha Allahu ba abinda ze sameta se alkhairi to yau tunda ta tashi abin yafi na ko yaushe. Wanka tayi ta saka doguwar riga Chiffon Abaya me adon stones masu kyau, kalan Dark blue ce dan haka ta mata kyau ta qara haska yaluwar fararta da gyara yasa taqara kyau. Abin kirki yau jarda su Eye liner da Mascara ta sakawa zara zaran eye lashes dinta sannan ta shafa chapet akan lips dinta. Turare kadan ta saka dan jikinta kamshi ya gama kamashi sannan dukka kayanta kafin ma agoge seta turarasu da turaren wuta na kaya asalin me kyau da Hajja take bata duk sanda taje gaisheta. Sabuwar motarta data siya Last month da kudinta bata taba hawanta ba se yau ta dauka ta hau titi tanajin ta gata nan kawai. Seda ta biya wasu guraren sannan ta dauki hanyar gidan Maryam din zuciyarta na qara tsananta bugu adadin kusancinta da gidan, koda ta isa kofar gida kasa shiga tayi saboda ji tayi jikinta ya dauki rawa gashi tana ta kiran number wayar Maryam din tana ta ringing bata picking haka ma ta Yusuf data tabbatar yana gari. Dukda Me gadin ya bude mata gate amma ta gwammace ta bar motar a waje, se ta fito ta dauki ledar datayowa Ruqayya da Aliyu tsaraba sannan ta dauki handa bag dinta ta nufi cikin gidan, a gate suka gaisa da Sulaiman me gadinsu take tambayarsa Ko Maryam tana ciki tana ta kiranta bata dauka ba

"Tana nan Hajia baqi tayi inga shi yasa basu daga wayar ba da kinshiga da motar ciki naga sabuwa ce kar yara su karta miki, mota fa tayi kyau Allah ya sanya alkahiri" da Amin ta amsa sannan tace masa ba dadewa zatayi ba bari ta shiga ta fito, yasan me take nufi nan da nan ya hau murna dan a duk baqin da suke zuwa gidan yafi maraba da ita se kuma wani Abokin Alhaji da shima baya gajia da kyauta.
Wata hadaddiyar mota ta gani a parking space din baqa se daukar ido takeyi, motar ta burgeta kwarai a ranta tace "Oh su Yusuf yan gayu mota aka sake kenan burin Maryam ya cika seya bar mata tasa" tana wannan tunanin tayi sallama tareda tura qofar palour da ba'a gama rufewa ba.

Wasu turare ta shaqa masu matuqar dadi da sanyaya zuciya nan take taji duk wata gajiya data dakko ta rabu da ita. "Masha Allah Bestie fito ki dakko min wannan turaren koma wanne irine ina so kamshinsa yayi min wallahi" ta fada tana kada bude kofofin hancinta dan ta shaqi turaren da kyau bangare daya kuma tana jin kamar tasan kamshin a wani gurin amma ta manta, kilan a gurin Abdulmalik shine meson turare kala kala. Kan daya daga cikin kujerun palour tayiwa kanta masauki tana fadin "wash Allahna Aliyu, Rukky kuna ine wai naji gidan shiru haka" idonta a rufe duk take maganar dan haka batasan da mutane a cikin palour ba. Bude idonta tayi tana dan tsaki kadan tace "Kilan tana can tana baccin nan nata shiyasa ma bata daukan wayar ba" ta fada sannan ta dauki kofin lemon data gani an rufe da dan murfin glaas ta kafa kai ta fara sha, Sauran lemon neya maqale mata a makoshi lokacin da idonta ya sauka akan mutumin dayake zaune kan kujerar da take facing dinta, ji tayi kamar ansa kwado an datse mata jijiyar datakai iska cikin kirjinta ba shiri ta fara tari kaman zata shide ga wasu zufa da suka fara keto mata babu ji babu gani, seta zame mayafin kanta da ribbon din data daure gaahinta dashi har lokacin tarin be tsaya mata ba, ji takeyi tamkar ta cire rigar ita ma ko zata samu sauqi. Kamar me cutar Asthma haka ta shiga fizgar numfashi da qarfin gaske dan taga yana barazanar yanke mata gaba daya.

Wata mata chocolate kyakykyawa mara jiki da take zaune a gefen kujerar da Hamdah take ce ta taso ta riqeta Maryam ta miqa mata ruwa a cikin kofi ta kafa mata a baki take ta shanye shi tas, "A qaro" matar ta tambayeta, kai da daga mata alamar Eh haka ta kuma tsiyayawa ta bata se a sannan ta fara jin iska na shigarta. Sannu take jera mata wata nabin wata ita dai ta jinginar da kanta a jikin kujerar ta rufe idanunta tana son ta yarda cewa mafarki ne ko Gizo ya mata bawai a zahiri ta ganshi ba. Yusuf da Maryam na tsaye akanta cikin damuwar abinda ya sakata irin wannan kidimewar haka, seda suka tabbatar ta samu nutsuwa sannan Maryam tace mata "Sannu Bestie tashi muje daki ki kwanta ko zaki qara samun nutsuwa kinji" bayan ta yafa mata mayafin ya rufe mata dogon gashinta.

Idanuwanta ta qara budewa a karo na biyu, ba mafarki take ba dan gashinan a zaune dungurgur akan kujerar ba abinda ya dameshi sema lemon da yake kurba yana danna wayarsa kamar besan budirin da sukeyi a cikin palour ba. Wata Yarinya ce Fara tas da kallo daya zaka mata ka gano tsantsar kamar da yakeyi da ita ta shigo palour da dan gudunta ta fada jikinsa cikin yar siririyar muryarta da bata wani gama iya magana ba tace "Dady hide me Ayiyu will beat me". Se ya dire kofin ya dagata sama yana dariya kamar yanda ita ma yarinyar takeyi tana qoqarin buya a jikinsa Aliyu kuma ya dage seya janyota daga jikin Dadyn nata.
"Lah Dady our Berbie" tafada tana zamowa daga jikinsa ta nufi Hamdah da gudu ta haye jikinta tana taba fuskarta. "Look Dady she is blinking her eyes yeeeee she is our real Berbie Ayiyu come look at her". Tsalle take tana murna a dole taga Berbien Dady yau ita kuwa Hamdah ta zauna kamar wadda aka dasa seta kalleshi ta kalli yarinyar data dage tana jagwalgwala mata fuska da gashi. Matar ce ta shiga janyeta tana cewa " Stop that *_Hamdah_* this is Aunt not Berbie stop it or else she will not take you to Your name sake" nan da nan ta bari yar karamar fuskarta me kyau ta chanza zuwa kalan tausayi tace "Please Aunt take me to my namesake i really want to

Please Login or Register in order to submit comment