Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba da kashedin daya mata akan tsokana dakuma motar da ta dauko ta ajiye Dan haka tanajin Hamidah tazo kiranta tace "Yah Hamdah kizo inji Big bro kikarbi tsarabarki" ta karasa tana dariya kasa kasa. Harararta tayi Dan tasan sarai bawai kiran Allah da annabi bane Akwai wata akasa Dan haka ba bata lokaci ta fita kiran nashi.

Yana zaune a dakinsa ya tasa computer a gaba yana aiki ta shiga, gefe guda ta rabe ita bata shiga ba bakuma bata fito wajeba adduarta Allah ya kawo abinda ze fitar dashi yanzu. Seda ya gama abinda yake sannan ya daga kai ya kalleta "Wato kin rainani ko Hamdah?" Girgiza kanta tayi alaman A'a
"Will you open ur mouth and talk or not kinamin nodding Kaman wani abokin wasanki" ya fada on top of his voice. Tuni jikinta ya dauki rawa "what did I told you the last time?" Wanna karan ma shiru tayi bakuwa tayi auneba taji saukan bulala a bayanta aikuwa ta daka uban tsalle tareda ihu tai hanyar kofa sedai yarigata tuni yarufe kofar tareda cilla key din aljihunsa.
"Ba magana nakeyi miki ba" babu baki magana, shiru tayi masa in banda gunjin kuka da takeyi hakan kuwa ya tunzura shi yashiga dukanta babu ji ba gani ita kuwa in banda ihu ba abinda takeyi. Gaba dayansu suna tsaye kofar dakin yayan nasu tausayinta fal ya cikasu sunsan halinsa bashida dadi in ransa ya baci bare ita da ya dade yana kafawa warning. Baffa ne ya fara bugun kofar tareda rokon yayan nasu akan ya bude Amma yai banza dashi Hamdah kuwa zuwa yanzu tayi laushi Banda Kukan wahala ba abinda takeyi.
Mumcy da shigowarta kenan tajiyo kukan yar gaban goshinta ko parking bata karasa ta nufi part din da sauri, bata bi takan suba tanufi kofar tana bugawa "Abubakar ka bude kofar nan kashemin ita zaka yi ko yaya nace ka bude".
Jin muryar Mumcy tasata kara dagewa tana kwala ihu cikin kukan nata ne tayi subutar bakin yi masa Allah ya isa harda tukwuicin Azzalumi ai nan yafara tamola da ita tamkar ya samu Dan uwansa namiji Mumcy ganin babu sarki se Allah yasata fashewa da kuka tana kiran sunan Abubakar din abinda yasashi dakatawa kenan ya bude kofar ya hankado musu ita. Jikin Mumcy ta fada tare da sakin kuka, abinka da farar fata gaba daya fuskar nan tayi ja ga kwanciyar jini aduk inda ya doketa. Dakinta ta jata Hamidah tasa ta kawo mata ruwan zafi da towel tashiga daddanna mata jikin sannan ta bata pain killer tasha se fa sannan suka samu saukin kukan sakamakon baccin daya dauketa.
Ba karamin Fada ya sha ba kamar shima zata dokeshi, Abba kansa seda ya kira shi a waya ya masa fada sosai akan abinda yayi shikansa se a lokacin yayi dana sanin dukanta yarinyar ce bata ji, zuwa yanzu yaci ace ta dena abubuwa da yawa da takeyi amma kullum qara gaba haukarta takeyi. Haka ta ringa jinya da fin rabinta sharri me kawai duk tabi ta dagawa kowa hankali a gidan, Allah sarki Abdulmalik haka ya koma kamar wani bawa duk bayan kwana biyu seya zo kano dubata har ta gaji ta warke.
Sosai ta matsawa Abdulmalik lamba dan yanzu ya dawo kano da aiki dakyar bayan yarda da sharadin da Alhaji ya kafa masa. Ya yarda ne kawai a irin nasa wayon kafin ya samu mafita. Dan haka ya Dawo kano da Full hope din samun muradin ransa haka ya cigaba da aikinsa hankali kwance.
A wannan lokacinma zaune yake gaban Alhajinsu dayai shiru yana kallonsa. "Wato Abdulmalik ni kamaida karamin mutum ko in ce maka kaje kaga yarinya jiya ashe baka jeba naga alamar so kake kanunamin iyakata ko sau nawa kakeso nayi Maka tuni akan aure?" Shiru yayi yana sauraron yanda mahaifin nasa ke ta sababi seda ya gaji Dan kansa yai shiru sannan yace masa "Alhaji wallahi mantawa nayi kuma na zata zuwan nawa ba wai wani me muhimmanci bane"...." Me muhimmancin uwarka ba ce maka nayi kaje kaga yar gidan Excellency ba ku fahimci juna" Alhaji Kamalu ya katseshi cike da masifa. Se ya daga kai ya kalli Alhajin, cike da in'ina yace Amma dai Alhaji ka mantawa kayi Ai nayi maka magana nasamu wacce muka daidaita".
Wani kallon you are not normal ya watsa masa sannan yace "Au to haka akayi ai ban sani ba to wacece ma I mean waye ubanta a garinnan?"
"Alhaji Sunanta Hamdah kuma yar gidan Prof Ahmad Muhammad Ammani ce"
"Prof Ammani dae Wanda nasani" ya tambayeshi yana gyara zama.
"Eh Alhaji shi na nan Tudun-yola" ya fada cike da murna a tunaninsa ya yarda ne.
"To ban amince ba". Tamkar saukar aradu haka yaji maganar begama recovering daga shock dinba ya kara masa da cewa
"Wato tsabar rainin hankali dama akan wannan yar tsohon bayahuden kake neman tozartani kaki yar Aminina ko? me wani professor ya tara bare har mu amfana dashi iye.
Yara nawa aka kawo maka yayan hamshakan masu kudin da duk inda ka zaga a Nigeria ansan dasu amma kaqi ina nan uwarka yar dan takarar Governor take nema maka kaqi....." "Alhaji ai shima din a duniya ma duka ansan dashi saboda iliminsa" yai saurin katse Alhajin.
"Ilimin ubanka mezan karu dashi a ilimin nasa to tun wuri inma zaka chanza tunani kayi kazaba cikin biyu Ko yarinyar nan Aisha yar gurin Matawalle ko kuma Firdausi Yar Alh Sanin Naira Dan kasan ni akomai Ina lissafin samu ba faduwa ba"yana kaiwa nan ya mike ya barshi a gurin.
"Aikuwa babu ko daya daza ayi a ciki Dan tuni mungama tsara komai da Aminiyata zamu hadasu aure da yar gurinta" Hajja ta katse musu zancen. Fasa tafiya Alhaji yayi ya juyo yana kallonta sannan yace "Zancen Aminiyarki ai bogi ne tunda baki da tabbas din zasu ci zabe ko Aa, ga zahiri wayake lissafi da abinda babu shi". Kallo isa ta masa sannan tace " Ina dai Da nane ko ta abinda na yanke masa kenan kuma babu wanda ya isa ya chanza". "Toh ai ga fili ga maidoki se mugani wa yafi iko akan Dan "cewar Alhajin, nan fa gardama ta kaure tsakaninsu kowa yana fadar raayinsa za'abi shidai sunsum yafice aransa yana takaicin hali irinna Iyayensa da suka bawa kudi muhimmanci a rayuwarsy, qiriqiri sun mayarsa yayansu hannun Jari. Gashi Abin ya tsallake mata ya zo har kansu Mazan Allah dai ya sauwaka.

************************
Shiryen shiga Camp takeyi dan befi saura kwana uku su shiga ba. Zuwa yanzu ta jingine maganar Abdulmalik a gefe ta zubawa sarautar Allah kawai ido. Abubuwa ne suke ta faruwa rashin dadi sosai rigima ta tashi aka maganar auran Hamdah da Abdulmalik din. Har gida Alhajinsu ya taka wai yazo jawa Abbah kunne akan yarsa ta rabu da dansa dan shi yayi masa mata. Shidai abin dariya yabashi Dan haka yace masa "Bakomai Alhaji zan ja mata kunne karta kara zuwa zance gurinsa haka kiran waya na soke insha Allah bazata qara ba". "yauwa Ko naji idan ba haka ba duk abinda yafaru ita taja" cewar Alhaji Kamalu.
"Babu abinda ze faru se alkairi Insha Allah". Da Haka sukayi sallama Wanda se bayan ya tafi yagane ashe Magana ce Prof Ammani ya fada masa, wato dansa ne yake zuwa zance Dan Haka Shi za'a yiwa magana. Basu gayawa Mata abinda ya faru ba har se bayan tayi sati uku sun fito daga Camp tukunna.
Da Nasiha Mumcy tasame akan ta hakura dashi Amma sekawai ta saka mata kuka. Ta rabu dashi ta kamawa? Zuciyarta ta turata ta kori Abdul'ad yanzu last option din zasuce ta bari? Seta kalleta hawaye na zuba a idonta tace "Aa karkimin haka Mum addu'a kawai zaki tayani da ita bani da kowa sai shi, bazan iya rayuwa babu Abdulmalik ba soyayyarsa tabi duk wani bangare na jikina Mumcy cire shi lokaci daya abune me wahala..."

2⃣0⃣2⃣0⃣


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 1⃣0⃣
Sosai tausayin Hamdah a kama Dr Maryam, lokaci daya duk ta zabge tayi wata irin rama. Ta tabbatar dole ta damu ba abune me sauki a rabaka da masoyinka ba. Tausarta ta shigayi da qoqarin nuna mata da ta fawwalawa Allah komai, babu wanda ya isa ya canza *_RUBUTACCIYAR QADDARAR SA_*. Dan Haka ko da Abbah ya mata Maganar ce masa tayi "Abban yara mubarwa Allah komai, Damu da su babu wanda ya isa ya hana faruwar wannan al'amari in Allah ya nufi haduwarsa haka duk soyayyarmu da ayi in babu Rabon se dai mu hakura". Seda yayi dogon nazari sannan yace "Hakane Dr Allah to ya zaba mata mafi alkairi" ta amsa masa da Amin.
Daurewa kawai takeyi harta fara zuwa gurin aikinta, cikin polytechnic take serving ba qaramin qoqari take ba wurin ganin ta cire damuwar komai a Zuciyarta. Kamar kullum tana zaune a compound wayarta abokiyar hirarta a hnnunta. Da tunanin Abdul'ahad ta tashi, wata irin kewarsa take ji kamar me tundazu take gwada kiransa se ta kasa ganin babu sarki se Allah ya sakata yin qundumbalar kiransa kawai sedai as usual wayar a kashe take. Dafa kanta tayi tanajin kaman tayi kuka, ita yanzu a ina zata nemo sa? Maryam ce ta fado mata a rai kota kirata tasan Yusuf baze rasa sanin inda yake ba dan haka kawai ta shiga dialing number Maryam.

Ringing biyu ta daga "Nikam nayi fushi yaushe rabonki da ki tuna wata Maryam ma" abinda Maryam ta fada kenan bayan sun gaisa. "Wallahi ba haka bane Bestie kinasan service dinnan se a hankali in kika fara zaki fada kema" ta bata amsa.
"Haka ne kuma ai dai wallahi ba'a kyautamin ba yanzu duk se kun rigani gamawa ina Afiya mutanen Ondo?"
"To bestie in banda abinki ai lafiya tafi komai in ba so kike ki qara mana Asarar Baby ba ki bari ki haife cikinnan in yaso daga baya sekiyi koma mene". Hira suka ci gaba dayi maryam din na mata complain akan irin complications din datake samu da ciki, Karo na uku kenan data samu ciki tun bayan aurenta amma biyun duk basu zauna ba acewar likitan wai saboda zarryar da takeyi ne kuma mahaifarta is not strong enough to carry a baby, dole yanzu suka bata total bed rest Wannan dalilin yasa Yusuf ya hanata fara Service yace ta jira next year. Wannan hirar ce ta dauke mata hankali harta manta dalilin kiran data mata, sun dade sosai kafin sukayi sallama. Ta hakura yanzu, bata da wani aiki illah na kaiwa Allah kukanta Dan shikadai ne ze iya mata maganin damuwarta.

**********************

Da ga bangaren Abdulmalik din kuwa dagaske sukeyi akan maganar, kaf yabi Yayyensa Maza da Mata akan maganar ko zasu taimaka masa as he expected Yan dakinsu dukka a against the matter dan gaba daya halayyar su daya, They are all capitalist. Duk da wasu daga cikin yayunsa maza suna goyon bayansa to Amma abanza tunda wadanda ke da say a maganar sunce Aa a yanzu bashida sauran kwanciyar hankali ko nutsuwa, ya kafe yavkuma qudurcewa zuciyarsa komai wuya komai rintsi baze hakura da ita ba. Babban abinda yake damunsa yanta take nuna masa halin ko in kula, yanzu in bashi ya kirata ba bazata taba daukar waya ta kirashi ba haka in zeyi wata beje wurinta ba bazata ce masa dan me ba sedai haka ko dar be saka masa ba, he believes tana sonshi kuma babu abinda ze chanza hakan kai ko ta dena sonsa shifa se ya aureta wallahi dan shi aka halittota.
Kwanaki nata tafiya babu kuma wani chanji a bangarori biyun, zuwa yanzu Hamdah ta gama saduda akan lamarin Abdul'ahad domin in bata bata lissafi ba yau wata shida kenan cif rabonda taji ko labarinsa bare ta ganshi, hatta Yusuf data tambaya ce mata yai yayi tafiya amma babu wanda ya san kasar daya tafi hatta kuwa Hajiarsa be fadawa ba. To me ya same shi haka? Me aka masa da yayi fushi ya rabu da kowa? Tunanin haduwarsu ta qarshe tayi ranar daya dawo da ita gida bayan wancan Incident din, zata fita daga motar yarike hannunta yana kallon cikin idonta "Hamdah i'm asking you one more time, will you please marry me?"
Bata san meya shiga kanta ba a lokacin, alredy tanajin haushin abinda ya mata earlier dan haka itama seta rama, seta saka shi yaji haushi. Zamanta ta gyara bayan ta bude murfin motar ta murguda masa baki sannan tace "Hey Mr Man, dama tuni na gama gane take takenka and who do you think will marry you ni Hamdah? Allah ya rufamin asiri kadai nema daidai da kai a gaba nimakam I'm already taken". Lokaci daya ya saki hannunta yawa motar key, badan ta yi saurin fita ba babu abinda ze hata faduwa kilan ma yabi ta kanta. Yanda ya fizgi motar kana gani kasan a fusace yake hakan kuwa ya mata dadi koba komai ta rama tai shigewarta gida ranta fes.

Lokaci daya ta fashe da kuka, wato ya yarda da abinda ta fada masa kenan shi yasa yai fushi ya bar mata qasar. Me yasa be tsaya ya kara nemanta ta gaya masa wasa takeyi na? Tun farko ma meyasa suka shaqu har haka ita yanzu gata bata ga tsuntsu bata ga tarko, kukan Nadama da dana sanin wautarta ta ringayi. Wannan shine abinda Aysha da Afeeya suke gaya mata ashe akan kartayi wasa da damarta. Baka sakin abinda yake hannunka ba tare da ka kama wani ba, gashi yanzu babu Abdul'ahad Babu Abdulmalik din. Haka taringa kuka har seda ta gaji dan kanta tayi shiru, gaba daya ta chanza baka taba cewa itace wannan me neman rigima da tsokanar, tayi wani irin sanyi ko magana yanzu wahala takeyi mata.
Tun chanzawarta yanawa yan gidan dadi acewarsu sun huta da rabon fada har ya zamana su dakansu suke Neman tayi maganar. Mumcy tayi iyayinta ta hakura tasan dai damuwar nada nasaba da guguwar rikicin maganar auranta. Lokacin data sameta akan tayiwa shi dayan Abdul din magana tunda wannan babu shi kuka kawai ta saka mata, take gaya mata ya tafi babu wanda ma yasan inda yake a yanzu, addu'a kawai Mumcy tai mata akan Allah ya fito mata da wanda ya fisu alkhairi.

Abdulmalik ne kwance cikin dakinsa, kallo daya zakayi masa katabbatar yana jin jiki dan yau kwanan sa biyar kenan a dakin bayan Yajin daya dakawa yan gidan gaba daya A cewarsa baze kara fita waje ba harse Alhaji da Hajja sun yajanye kudirinsu nayi Masa Auran dole. Abdullah kaninsa ne yashiga dakin dan jin shirun yayi yawa abu har kusan Kwana biyar a nan ya tararda mummunan yanayin da yayan nasa yake ciki. Da gudu yakoma cikin gidan ya shaida musu nan fa hankalinsu ya tashi gaba daya, babu shiri sukai asibiti dashi shidai Alhaji ko a jikinsa Dan lokacin da aka gaya masa ma waya yakeyi da Amininsa akan yanda lamarin biki ze kasance.
Asibitin Yayansa aka kaishi. Amenity ward suka kwantar dashi bayan dogon bincike Dr suka saka masa ruwa sannan ya nemi su barshi ya huta dan yana matuqar buqatar hutu a wannan yanayin. Jininsa yayi mugun hawa ga kuma zuciyarsa na barazanar Harbuwa mafita a bashi abinda yake so in dai ba auna so su rasa shi ba. Ba qaramin tashi hankalin Hajja yayi ba dan a duniya bata hada kowa da Abdulmalik na, shi kadai Allah ya bata Da Namiji dan haka bazatayi wasan da zesa ta rasa shi ba. Masifa ta hauyi tanaji tana gani baza'a kashe mata Da ba bashiri ta shiga kiran Alhajin. Duk abinsa yana tsoron Masifarta dan Hajja bata da sauqi in dai akan fada ne. Kamar dan data haifa haka ta ringa balbala masa masifa shi kuma nutsu yana sauraronta gaba da gabanta. Dan indai bala'i ne to Fattu ta dameshi ta shanye duk cikin matansa babu wacce yake shakka irinta Dan haka a dole ya tashi ya tafi asibitin sedai fa ya kudurcewa zuciyarsa wannan karan ze nuna mazantakarsa Dan baza a maidashi kara min mutumba a cewarsa ya gama yanke magana da Matawalle babu me tada wannan zancen.
Sedai shi da kanshi yanayin dayaga Abdulmalik din ya bashi tsoro yana kwance bambancinsa da gawa numfashi gaba daya ya zama wani qashi da rai. Amma ya dake har yana cewa inma mutuwa zeyi sedai ya mutu Amma aure ba fashi.
"Eh ai dole kace haka tunda baka da asara kana da wasu Yaya mazan to wlh kaji da kunnanka bazan zuba ido Ina kallo inrasa Dana ba Dan haka yau base gobeba zakaga abinda zanyi".
"Ai sekiyi muzuba mugani nida ke wazeyi nasara "fuuu ya ja rigarsa ya fice daga asibitin. Dama a hanya yake akwai Important meeting da ze tafi Abuja washe gari amma saboda bata masa ran datayi a ranar ya tafi.
Kaman yanda hajiyan tayi alkawari kuwa kwana biyu ta hada Kanin Alhaji Kamalu guda daya Baba Salisu da Amininsa tun na yarinta Alhaji sabo se babban Dansa Namiji da me bi Masa Alhaji Nura da Dr Ibrahim ta kirga kudi 200k ta basu suka kai kudin gaisuwa dan tun a ranar da aka kwantar dashi da kanta ta kira Mumcy akan ta shaidawa Abbah zasu turo. Da farko yaso yayi gardama Amma da Mumcy ta nuna masa akan yayi hakuri basu san sirrin da Allah ya boye a auran ba tunda masu adawarma sun hakura to su bari kawai.
Haka suka karbi kudin ba tareda tunanin komai ba suka kai tunda sunsan Tsakanin Alhajin da Hajian ba'a shiga. Sun samu kyakykyawar tarba, harkar girma aka musu suka baro gidan suna yabon dattako irin na Prof da yan uwansa. Labari me dadi suka dawowa Abdulmalik dashi an saka ranar auransa Sati biyar masu zuwa. Tuni ya warke tunda ya samu maganin ciwonsa.
Masifa bala'i har ma da tsinuwa sun shata alokacin da Alhajin yasamu labarin abinda tayi masa Amma bashida yanda zeyi Dan ita ma ta nuna masa jan wuya dole ya hakura amma tabbas Fattu ta ja masa asara, kwangilar daya karba ma ta hannun Matawalle yake ji sedai cikin ikon Allah koda ya gaya masa rashin lafiyar Abdulmalik din da kuma hukuncin da da Hajja ta yake Matawallen yace ba komai ai aure rabone hakan kuma baze shafi zumunchinsu ba.
Sosai ake shiri ta kowane bangare Hajja dakanta ta tafi Dubai ta hadowa Dan nata kayan lefe Dan yanzu ba laifi tanayi da Amaryar tun bayan daya kawo mata ita suka gaisa, yanayinta da nutsuwarta ya birgeta sannan ta tabbata kaf surukan gidan babu kyakykyawa kamarta dama ita damuwarta kar ace an fi danta Dan haka da gaske take shirin koba komai babu me kushe zabin Dan nata dan duk cikin kawaye da kishiyoyi babu wacce takeda zukekiyar suruka irinta.
Aminiyar Haj Hauwa ta kira ta akan rade radin da takeji na wai an saka wa Abdulmalik rana to ina Zancen nasu Hadin ya tsaya kai tsaye ta gaya mata cewa "yaro baya so Dan haka baza tayi masa dole ba" bakinta taja kawai tayi shiru dukda yanda yar tata take damunta akan abin Amma tasan muddin tafadi wani abu yanzu suna iyayin baran baran sedai tayi alkarin bazasu barshi haka ba dole ta dau mataki akan al'amarin.

2⃣0⃣2⃣0⃣










🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 1⃣1⃣

Biki nata matsowa shiri akeyi ta kowanne bangare, tuni ango ya murmure haka ma Amarya kashi 70 na ramar da tayi ya tafi sedai fa har a sannan bata da nutsuwa. A koda yauahe yaushe tunaninta ya na wani guri daban Wanda su suke gani Kaman Jimamin barin gida ne sedai agurinta ba haka bane.
Bakuwa wani abu take tunani ba illah GURU Wanda har yanzu bata san duniyar daya ke ba. A kullum ta kwanta seta yi mafarki dashi sedai ko a mafarkin bata samun damar yin magana dashi. Kuka kam ya aureta dan in batayi da yawa ba tayi na awa 3 a rana ita kadai tasan me take ji a ranta. Ina ma zata qara ganinsa ko sau daya ne ta fada masa abinda yake ranta, ina ma zata samu damar bayyana ma sa asirin zuciyarta, sedai lokaci ya qure mata a yanzu. Magana ake ta saura sati biyu daurin auranta da mutumin dayafi kowa sonta, Allah ya sani tana son Abdulmalik amma kuma shiya jarabceta da son Abdul'ahad.
"Me yasa ka shigo rayuwata kuma ka fita a lokacin da nake buqatar ka, ina ka tafi ? A ina zan ganka bamu da isashshen lokaci ka dawo Abdul'ahad ina sonka zan aureka". Kalaman da take ta fada kenan kamar zautacciya tana riqe da waya, ta gwada numbers ya fi sau 50 amma dai amsar daya ce a kashe. Kuka ta keyi tamkar wadda iyayenta suka mutu tana fadar maganganun da suka cunkushe mata zuciya seda tayi me isarta sannan ta wanke fuskarta a fampo ta tashi daga gurin kanta na bala'in sara mata. Cikin gidan ta nufa zuwa lokacin jama'ar da suka taru dazu sun ragu sosai se yan uwa najiki da kawayen Mumcy suka rage. Akwatunan da aka jere a gefe masu azabar kyau guda 24 ta kalla se daukan ido sukeyi. Inda a lokacin bayane tabbas data shiga cikin masu kallon kayan anyi da ita saboda sunyi mata irin designer data gaya masa tana so ne latest design amma a yanzu da me kayan, da wadanda suka kawo da masu kallon dukka ta tsani ganinsu. Ji take da za'a barta tsaf zata iya cinna musu wuta su qone kowa ya huta.
Da sauri ta nufi staircase jin wata kanwar Abbah tana cewa " Lah ga Amarya zo nan ki kalli abin arziqi yarinya lallai baki farin banza ba wallahi Abdulmalik ya biya Lefe yayi saura Sadaki" a maimakon ta tsaya seta qara wa tafiyarta sauri karshe ma ta hada da dan gudu dan jin wani kukan na neman kufce mata. Kan gadonta ta fada tareda fashewa da Kukan, ita kam ta shiga uku wannan wace irin masifa ce? "Allah ka kawo min agaji, Allah ka kawomin dauki" shi kadaine abinda take maimaitawa. Haka taci kukanta ta godewa Allah har zuwa lokacin da me mata gyaran jiki ta shiga dakin, kamar yanda ta saba haka ta mata anayi tana kuka se lallashinta take a tunaninta ko irin kukan da amare sukeyi ne sedai abinda bata sani ba ita nata ya banbanta dana sauran.

A kan gadonta ta tarar da envelope bayan ta fito daga wanka, dauka tayi ta bude tana bin content din ciki da kallo. Pre-wedding pics din da sukayi shekaran jiyane sunyi kyau sosai Masha Allah. Tsura masa ido tayi tana kallonsa, shin menene laifin Abdulmalik? Ta tambayi kanta. "Bashi da laifin komai" zuciyarta ta bata amsa, jiki a sabule ta shiga shiryawa har an kira sallar magrib dan haka tana gamawa ta tada Sallah, ba ta bar kan abin sallar ba har seda tayi Isha tukunna ta miqe saka makon kiran Da Abba yayi mata.
A Palour ta same su kusan dukkan yaran gidan Harda Anty zahra data zo tun jiya, wasu set din akwati ta gani a gefe daban da wadan da ta gani a matsayin na lefenta. "Hamdah ga kaya nan ki bude ki gani idan akwai abinda beyi miki ba se ki fada a kara ko a canza miki". Badan Abbah bane yai magana ba abinda ze sakata duba kayan dan duk abinda ya shafi shirin auran nan bata maraba dashi. Akwatunan suka shiga budewa ita da Hamida kayane nasu kyau da tsada kuma choice dinta, tasan aikin Anty zahra ne dan already tasan irin attire din

Please Login or Register in order to submit comment