Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ci gaba "To rana Daya akayi auransu da Mami kinga Yaya Mansur ne Babban dan Mami yama girmeni da kusan 2 years, ita kuma Sharifa ce first daughter dinta inaga befi ta baki shekara daya ba. Koma ba haka ba kindai san baki kaini son ki haifarmin baby Girl me irin idon nan naki bako" ya karasa yana shafa saman idonta "To ki sauraramin da batun haihuwa yanzu, Allah daya bawa kowa ze bamu muma layi ne bezo kanmu ba kinji ko".
"Naji amma dai Jaan yakamata dai muje gurin Dr mudai tabbatar da lafiyar mu sannan se muci gaba da addu'a kawai". Banza ya mata ya shiga bathroom tasan ba amsata zeyiba Dan haka ta Mike itama tashiga jera masa kayan gugarsa da aka kawo a closet.


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 1⃣8⃣

A haka rayuwa ta cigaban musu baya taba biyewa shirmenta in ta fara akan maganar ciki. Yaga alama harda zaman banzan da takeyi yake qara sakata abinda takeyi dan haka ya shiga fafutukar nema mata aiki wanda a farko yace bazatayi ba. Da alfarmar Prof Ammani da kuma result dinta da yayi kyau ta samu lecturing a nan Polytechnic ta fara zuwa.
Hankalinta be tashi ba se ranar da Hajja ta tsareta da tambayar wai ta fa ji shiru haryanzu ba wani labari ita fa tana buqatar taga jikan danta Namiji, hankali tashe ta kira Mumcy tana kuka ta sanar mata abinda Hajja tace dakuma Abdul din dayaki daukan abun da muhimmaci. Rarrashinta taringayi tareda kwantar mata da hankali, misalai ta ringa bata akan bakowacce mace bace daga aure take haihuwa wasu ma sukan shekara biyar koma fiye da haka dakyar dai ta samu tayi shiru da alkawarin dakanta zata kira Abdulmalik tace suje asibiti.

Sauri take ta gama komai dan tasanshi dan oya oya ne baya son jira. Tana tsaye gaban mirrow tana gyara daurin dan kwalinta ya shigo dakin, yayi kyau sosai cikin shaddar daya saka Brown se kyalli takeyi. "Yanzu fisabilillahi baki gama ba minti nawa na qara miki amma har yanzu kina nan har karfe 12 tayi bayan kekika azazzaleni ke zaki gidan suna". Jakarta ta zara tayi waje tana cewa "Kai Jaan kafiya mita wlh Kaman me tsohon ciki muje toh". Gidan Nasir kanin Abdulmalik Dan Hajiya Shuwa zasuje matarsa ta haihu yau ake suna. A kofar gidan ya ajiyeta Dan yace taron matane baze shiga ba sun hadu da Nasir din da asuba gurin radin suna. Kudi ya bata da yawa akan ta bawa me jego dukda ledar dayaga ta ciko da kaya zata kai mata. Gidan ya cika makil duk yawancin Faccalolinta sunje sannan ga yayan gidan mata dukka nan aka shiga gaisawa suna ta mata tsiyar wai ba'a ganinsu daga ita har mijinta sun buya ba gidan wanda take zuw. Murmushi tayi take ce musu wallahi aiki ne ya hanata fita. Jaririn dayaci sunan Alhaji suna kiransa Na'im aka mika mata tasa hannu da bismillah ta karbeshi.
Zainab kanwa Abdulmalik da take binsa a dakinsu. Duk cikin yaran gidan ta fisu fitsara ita da Khausar, dukda bazata iya fadar ainihin matsayinta a gurin su ba ita dai tasan tun da aka aurota babu wadda zata ce tayi mata wani rashin kirki a bayyane in ba zainab da khausar ba. Suka daine suke shiga har gidan ta suyi mata rashin mutunci wanda tun bayan daya tsawatar masu basu sake ba. Dukda ba wani dogon shiri take da sauran ba amma dai kadaran kada han in an hadu a gaisa haka duk abinda akeyi tana kokarin ta ga taje ko dan gujewa kananan maganganu dan suna dasu musamman ita da aka aurota ba ra'ayin kowa ba. Taga alama kowa agidan akwai zabin daya so Abdul din ya aura. Dan haka tunda suka gaisa taja bakinta tayi shiru tana kallon Babyn hannunta me kyau.
Abinda bata sani ba tunda tashigo take kare mata kallo daga kan suturar dake jikinta tasan dai bazata yi mata gorin sutura ba dan har yau Allah besa ta taba ganinta da ko dan kunnen cikin lefen ta ba har tana cewa sun san me akayi kasuwa aka kai aka chanzo su ita dai bata taba tanka mata ko sau daya ba. Tayi niyyar seta tozarta ta dan haka ta mika Hannu daniyar karbar jaririn daya motsa ya Dan fara kananan kuka tana cewa "Mikoshi nan kiga yaro yana neman abinci yo wayaga ban saniba kinsan Wanda be ko taba daukar ciki ba Ina zesan abinda jariri yake bukata".

Ba Hamdah ba Hatta sauran faccalolin ta dake zaune a gurin seda zuciyarsu ta sosu dan sunsan habaicine ta take yaba mata da nufin wasa. Mejego Hanifa ce tai saurin cewa "Kai Zainab ai duk mace Ko bata haihuba tasan yanda zata kula da jariri tunda in bata haifa ba akwai kanne da yayan yan uwa .." Se tayi saurin ta reta da cewa "Ke na raba ki bar wasu matan dai da kissa da kisisina a kanainaye miji sedai aci a hau masai an kasa ajiye ko gutsire". Sumayya da abin ya batawa rai ce tace kuma dama ita ma yar uwar Zainab dince a fitsara tace "Amma dai Yaya Zainab naga Allah ne yake bada haihuwar nan dai da mutum ke bawa kansa kema da kin haihu". A fusace ta juyo kan Sumayya ta kwada mata mari " Dan uwarki ni sa'ar kice ko da ke nake ni zaki cewa da mutum ke bawa kanasa da nima na haihu shegiya kawai". Kuka Sumayya ta saka tana Allah ya isa, kuma yin kanta tayi mutanen gurin suka shiga rirriketa se kumfar baki take seta ci uban sumayyan. "Ku rabu da ita ke Sumayya rufe bakinki zata samu daidai da ita daze rama miki, in banda baki da Hankali Zainab harkinyi girman da zaki tasa matar Abdulmalik a gaba kina mata fitsara menene be miki a duniya ba, shi mijin da kike taqama dashi yana wahalta miki ne kamar yanda dan uwan naki yake miki dayake ke sallamammiya mara tarbiyya in banda bakida hankali kedin yaushe kika samu lafiya kika haihun da zakiyi wa wani gori" Kanwar Alhaji kamalu Goggo Habiba ta katse musu fadan.

Duk rashin mutunchinta taba shakkar Goggo Habiba dan yar bala'ice ita ma lamba daya, cikin kunkuni tace "Ai dole ki tare mata tunda kema Juyar ce kuma daza ace ban haihu ba Amma dai Nidai ai Ina bari kowa yasan ba Juya bace ni kuma badai uwata ba wallahi" Sabuwar Hayaniya sake tashi dan Goggo Habiba tajita nan ta shiga surfa mata ashar kwando kwando har da kai mata duka. Tsam Hamdah ta mike daga gurin maganganun Zainab na mata yawo a kai, wato ita ce juya? muryar Hajja tajiyo da Alama zuwansu kenan su uku Ita, Anty Halima se Hajia Sa'adatu haka sukeyi duk wadda ta haihu zasu shirya suje. Kallon su take daidaya har ta tsaya akan Zainab data sha maruka fuska tayi jawur "Wai meye haka kuke nema mu dagawa mutane hankali a gidan Taro tundaga waje ake jiyo hayaniyar ku". Zainab data sha mari a gurin Goggo Habiba ce ta shiga zayyanawa Hajja karya da gaskiyar abinda ya faru. "Wai Hajja daga wannan matar (ta nuna Hamdah) ta kusan kayar da Baby nayi mata magana nace batasan zafin Haihuwar bane shiyasa shikenan Sumayya tamin rashin kunya saboda na mareta ita kuma goggo ta shigar mata wai meyasa zan fadi Haka wai nace mata Juya".
Gaba dayansu suka saki baki jin wannan shimfidediyar karya da Zainab din ta zayyano, babu damar cewa ba haka ba dan sun san Halin Hajja kan lamarin kowa yayi shiru suna sauraron irin Hukuncin dazata yanke.

"Yo karya kikayi ko me daza'a tasamin ke a gaba saboda zalunci ana duka ke ko karya tamiki ke ba JUYAR bace" ta fada kallon inda Hamdah take tsaye. Tamkar kasa ta tsage tashiga ciki kawai bata taba ganin irin wannan cin mutunciba, bata da sauran abinyi a gidan dan haka taja Jakarta kawai tayi waje Matar Salim Fauziyya da Juwairiyya yayar Abdul din suka mara mata baya. Taso taqi shiga motar Fauziyya amma bazata iya wa Yaya Juwairiyya musu ba dan haka ta shiga tana zama ta saki kukan da take ta dannewa. Har suka isa gidan kuka takeyi, Fauziyya data gaji ta kira Abdul a waya ta sanar masa yazo gida babu lafiya. Mintina kadan ya shiga gidan Hankali tashe, tundaga falon yake jiyo kukanta. Be ko lura dasu Fauziyya ba ya rungumeta cikin matukar tashin hankali yake tambayarta "Babe meya faru me akayi miki please talk to me please" volume din kukanta kawai ta kara dan se yanzu take qara jin zafin abinda aka mata. Ganin bazata yi shiru ba yasashi Maida tambayarsa kan su nan Yaya Juwairiyya tashiga labarta masa abinda ya faru tiryan tiryan. "Yanzu Abdul abinda Hajja takeyi ya dace ace bazaka taba ganin laifin naka ba ko wani taga yayi makamancin haka ai kamata yayi ta masa fada bawai ta goyi baya a wulakanta mutum ba".
Ransa yayi bala'in baci jin wai Zainab ce ta fara abin dakuma irin hukuncin da Hajjan tayi akai, wato duk yanda ya ja mata kunne akan sabgar gidansa bata jiba kenan lallai kuwa se ya ci ubanta wallahi, seta gaya masa inshi sa'an wasanta ne bare matarsa. Sallama sukayi musu suka koma gidan sunan dan ita Juwairiyya tace badan yaranta da suke can ba babu abinda ze mayar da ita gida zata wuce abinta. Wannan hali na yan gidansu yana kona mata rai, da wuya suje taro a tashi lafiya se sun bar abin magana haka tayi ta mita har suka isa gidan. Bayan fitarsu kuwa rigima ce sosai ta tashi tsakanin Hajja da Goggo Habiba dakyar aka samu suka hakura kowa ta kama gabanta. Ita dai Hanifa ba abinda take inbanda tsine musu aranta dan Sun bata mata taro sunkuma bar mata abin kunya kowa yazo se ya tafi dasu a baki ina amfanin irin wannan dangin masifar.

Ba irin rarrashin da be mata ba Amma a banza, dafe kansa yayi tareda furzar da iska me zafi daga bakinsa. "Nidai ka kaini gurin Mummyna tunda kaki yin komai akai ai ita bazata juri ganin ana wulakantani ba" ta fada tana qara fashewa da wani sabon kukan. "Damn it" ya furta yana kaiwa gadon naushi. Waiima gaba daya auran nasu shekara nawa? wannan watan fa zasu shekara biyu shine har za'a fara saka mata pressure akan bata haihu ba, to wa zaa haifawa Dan badai shi bane? To baya so, Yace baya so se a kyalesu in kuma da wanda ze saka ta ta haihu dole se ya gani. Shidai yana son matarsa koda haihuwa ko babu Hamdah still remain his favourite. Shii kansa rashin samun cikinta ya fara damunsa Amma yaya zeyi? Damuwarsa ta isa tasa Allah ya basu ne? Ganin da gaske bazatayi hakuri ba ya sakashi sassauta murya ya dagota gaba daya zuwa jikinsa sannan yace "Ya isa toh kiyi hakuri gobe Insha Allah zamuje wurin Mommy koh". Se a sannan tarage kukan, jikinsa ta qara shige yana goge mata ragowan hawayen fuskarta ba abinda take yi se ajiyar zuciya. Kadan kadan yake kissing gashinta daya sha gyara aransa tunani ne fal "toh yanzu yacewa momcyn me in sunje? yakawo yarta ta dubata saboda bata samu ciki ko me? "abin ai seya zama kaman cin fuska ai. Wayarshi dake aljihu ce tafara ringing, ganin sunan me kiran yasakashi kwantar da Hamdah da bacci ya dauke ya yi waje ya Amsa kiran.

A falon ya iske Zainab da Munubiya, Khairiyya se kuma Aunty Khadija babbar yar Hajja. tattaunawa sukeyi akan abinda ya faru Munubiya da ko qarasawa gidan sunan batayi ba take nunawa Zainab din rashin dacewar abinda tayi dama ita babu ruwanta shiyasa suke takata yanda suka ga dama. Ciki ciki yayi sallama kana ganinsa kasan yana cikin bacin rai aransa Addu'a yake Allah ya hadashi da Zainab din Dan seya ci mutuncinta wallahi kome Hajja zatayi kuwa. Akanta idonsa ya fara sauka nan danan ya fara sauke mata duk abinda yai niyya "Wato Zainab raini tsakaninmu harya kai ki wulakanta matata a gaban jama'a ko, ba ita ya kamata kiyiwa ba ni zaki tara ki zaga senasan kin cika mara mutunchi mara tarbiyya yanzu ke har zaki iya tsayawa ma a inda za'a wulaqanta koda karen gidana bare matata? In baki ci, in baki sha in miki sutura, kudin magani duk wahalar ki ko akwai abinda Dan iskan mijin naki yake tsinana miki dashi". Gaba daya seta muzanta, bata zata abin ze kai har haka ba gasu Munubiya na zaune. A gidan Hajja ce kadai tasan da shi yake daukar Nauyinta domin kallon kitse sukayiwa rogo. Mijin data aura tun daga uban lefen da ya mata be qara dinka mata sutura ba yau kusan shekara 7 da aurenta, abinci kuwa tunda garar ta ta qare be kuma ajiye mata ko kwayar hatsi ba yace kudin daya kamata ya mata hidima su yake kashewa ubanta ga cin mutunchi har dukanta yake randa yaga dama.

"Ba dake nake ba kinajina kinyi shiru" ya daka mata tsawa da seda ta tsorata. "Toh ubanta ina kuwa zata jika seka daketa tukunna wato an saka ka a daki an karanta maka karya da gaskiya shine ka taho ka balbalemin ya da masifa har kana mata gori ko to baka isa ba wallahi karya tayi ko me? Idan ita matar taka taji haushi gobe muganta tana Amai". Da mugun mamaki ya kalli Hajja, sosai halinta akan lamarin daya shafi yayanta yake bashi mamaki. Shikenan ita nata baya badaidai a masa Fada ba? Ko kusa beyi tsammanin haka ba a irin yanda ta daukaki Hamdan wato shiyasa akace wanda yace baya sonka baya taba chanzawa dai. Bashida ta cewa kuma dan haka ya ja kafafunsa dasukayi sanyi yai waje yanajin yanda Hajjan ke surfa masa masifa kaman zata ari baki wai an shanyeshi.
Yanda yake tafiya kadai nuna maka tsantsar bacin da ransa yayi. dukk wanda yasan Abdulmalik yasan mutum ne me Sanyin hali da wasa da dariya. bashida hayaniya ko kadan dan Za'a iya cewa duk cikin yayan gidansu babu mai saukin hali irinsa Amma akace wai mai hakuri bai iya fushiba to hakance take faruwa aduk lokacin da ransa ya baci. Bashida dadi kwata kwata musamman akan abinda yake so. Irin so da kuma muhimmanci dayake bawa Hamdah akan komai nasa ya saka musu kishinta kodan kasancewarsa Namiji acikin yaya 8 da Allah ya bawa Hajja Fattu dan Haka suke ji dashi. Yana tafe yana Tunani yanda al'amuran gidan su suka fara wanda a labari ance duk laifin Hajja Fattu, ita ta fara watsa gidan ta saka musu muguwar Dabi'ar yan ubanci a tsakaninsu musamman yayanta akayi sa'a me gidan shima kan keke ne. Kwata kwata be damu da sanin wani abu da suke ciki ba idan ya fella ya tafi neman kudinsa se yayi wata uku yana yawon qasashe be waiwayi gida ba tun ma a wancan lokacin. A rayuwarsa Kudi kawai yasani kuma neman su ya saka a gaba.

Hajja Fattu itace macen auransa ta farko, Yayansu takwas da ita mata Bakwai namiji daya. Khadija ita ce babbar Yarta kuma Babba a mata a gaba daya gidan dan ya auri wata mata Hajia Laure wadda Allah be tsawaita zamansu ba ta rasu gurin haihuwa tabar Yara biyu dukka Maza. Bayan Khadija Hajja nada Ummu-Salma, Munubiya, Abdulmalik, Zainab, Hasina sai kuma autarta Khausar. Bayan rasuwar Hajia Laure ya auro Hajia Amina wadda akafi sani da Hajia Shuwa ko Mama inda itama ta Haifa masa Yaya Biyar Salim, Kabir, Abdallah, Husna da Hindu. Hajia Sa'adatu ita ce ta uku wadda suke kira da Mami ita kuma Yayanta Shida. Abubakar, Umar, Usman Da Aliyu sai Sumayya da Surayya. Sai kuma Anty Halima da keda Yaya shida itama wato Sharifa, Abdussamad, Muhsin, Zuhra da Fauziyya.
Babu wata jituwa tsakanin matan gidan sosai hakan ce ta shafi har yayansu musamman yan Dakin su Abdul din. Dukda a bangaren mazan da sauki basu fiya shiga alamuran Dake faruwa a gidanba haka wasu daga cikin matan...tunaninsa ne ya katse ganin kiran Hamdah a waya Dan Haka yayi saurin shiga gidan wai ta gaji da zaman shiru ita kadai. haka dai sukai wunin ranar ba dadi Sun kwanta da alkawarin gobe zasuje asibiti.
Asuba ta gari Mr nd Mr s Malik.



🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 1⃣9⃣

Zaune suke gaban Dr Nasir hannun Hamdah cikin na Abdulmalik din. Kusan minti biyar kenan da kiran da Dr yayi musu bayan check up din da aka musu yanzun ma result suka je karba. seda ya gama yan rubuce rubucensa sannan ya dago yana kallon su dauke da murmushi a fuskarsa, "Mr and Mrs Abdulmalik right?" Ya yi maganar yana kallon su duka. "Nasir go to the point please" ya fada dan yasan Halin Kanin nasa da was. Ya yarda da suzo gurin Nasir ne dan yasan koma wacce matsala ce ze rufe musu ita batare dackowa yaji a gidansu ba dan Hajja tace ya kawo mata result din in suka dawo yasan shi kadai ze iya masa alfarma ya chanza koda an samu matsala tunda Dan uwansa ne. Seda Nasir yayi yat dariya dan shima yana da yawan fara'a kamar Abdulmalik din sannan yace "Sakamakon bincikenmu ya nuna cewa you are all fine". Ajiyar zuciya suka sauke a lokaci daya kowanne yana godewa Allah a zuciyarsa, maganar Dr ce ta katse su inda yake cewa "Sedai ita madam dince take da yar matsala kadan from our investigation we found that she normally encounters serious pain when she is on her period and dama normally the drugs din da suke sha for relief sunada some side effect shine ya danyi affecting mahaifarta ta kasa saurin conceiving and wani abu ma is like ta samu cikin kusan two times so in yazo mata da ciwon mara se tasha wadannan same drugs din suyi flushing babyn out. Amma fa wannan ba wani serious issue bane magani kawa za'a bata insha Allah komai ze daidaita".

Tun da Nasir ya fara magana ta tabbatar da ita keda matsalar ta fara kuka, shikenan ashe itace bazata haihu ba tasan yanzu yan uwan Abdulmalik sun samu makamin yakarta dole ma su sakashi yayi aure kila yanzu seya auro wannan Me kama da Mayun, wannan tunanin da tsabar kishi suka qara tunzura mata zuciya. Lallashinta yakeyi har suka iso gida bayan Dr ya hadosu da magunguna da zata sha har na tsahon wata shida. Ranar yaga ta kansa, duk wata kalma ta rarrashi da dadin bakin dayasan yana tasiri akan ta yayi Amma abin kamar yana dada angizata. "Shikenan sekiyi tayi tunda bakisan kiyi abu kadanba ki hakura ba in kuma kukan ne zeyi mana maganin matsalar se naji hun?" Cikin fushi yayi maganar dan harga Allah ta fara bashi haushi.

Ya rasa da wanne take so yaji, da rashin lafiyar tata ko da kukan data tasa shi a gaba tanayi da yakeji kamar saukar ruwan zafi a jikinsa. Fada ya shiga yi mata ba kadan ba kamar ze doketa sedai ita kam ko a jikinta guri ta samu tayi zaman dirshan tana shaqar kuka shi kuma yana tsaye akanta yana surfa bala', Ganin da yayi babu sarki se Allah dan har cewa yayi in batayi shiru ba seya falla mata mari budar bakinta tace "Ai dama dole yace ze mareta yanzu tunda bata da wani sauran amfani a gurinsa". Ba shiri ya durqusa tareda janyota jikinsa gaba daya yayi hugging dinta yayi so tight at once yana shafa Gashin kanta da bayanta tare da hura mata iska a kunne. Kukan ta fara ragewa se ajiyar zuciya data ke saukewa wata na bin wata kamar Yarinyar goye. "Ya isa mana princess haba jiyanda duk kika hada gumi ga kanki har yayi zafi so kike se kin sa yayi ciwo ko" ya fada cikin wata kasalalliyar murya a ransa yana jin zafin furucinta. Yanzu har tana tunanin ciwo zesa ya qita ne? Yau ko HIV akace tana da ita a zatonta ze gujeta saboda hakan se akan abinda ma shine sula. Bayan shi ya ringa siya mata maganin da kudinsa tun ma a lokacin tana budurwa dukda hanata shansu da Mumcy takeyi se yace baze iya jure ganinta tana shan wahala ba alhalin akawai magani.

Jin tayi shiru ya sa ya ci gaba da cewa "Shifa Nasir ba fa cewa yayi bazaki haihu ba hasalima har magani kina gani gasu ya hadomu dasu just 2month treatment everything will be alright hakuri kawai zamuyi". cikin sanyi gaba da yi mata bayani bayanda ya fuskanci fadan baze sakata ta nutsuba. Gyara kwanciyarta tayi sosai a jikinsa ta qara lafewa sannan tace "Toh Jaan su Hajja fa nasan bazasu yarda da hakan ba ayanzu ma suna matsamin lamba inaga sunsan ga matsalata nasanma Aure kawai zasu yi maka kilan ma wannan me kama da aljanun (tana nufin Haula) ko wannan bulalar(Hafsa) zata aura maka" ta karasa maganar tana shirin fashewa da sabon kuka. Duk da damuwar dayake tareda ita maganarta bata hanashi yin dariya ba, se yanzu ya ganota ashe kishi ne ya sakata kukan, se ya shiga tsokanarta yana cewa "Yauwa Babe gara dai ki fadi gaskiya ashe kishine kawai yake damunki kinbi kin hargitsani to kwantar da hankalinki kima saka ranki a inuwa dan aure kam inda niyyar karawa baki sani ba jira kawai nake ki haihu kina tafiya wannan wankan gidan da kika ce sedai ki dawo ki tarar da Amarya a gidannan Allah ne yasoki baki da rabon yin kuka da wuri" ya karasa yana kashe Mata ido. Pillow ta dauka ta fara jifansa tana "wallahi Aa ai kace baza kamin kishi ba". In banda dariya ba abinda yakeyi yana cewa "Aa fa Babe banda sharri a yaushe kika ji na fadi hakan" nan suka shiga zagaya falon tana kai masa duka yana kaucewa. Seda ta gaji Dan kanta sannan ta kwanta tana mayarda numfashi. Akan cikinta ya dora kansa shima yana kallon fuskarta, yanda zuciyarta ke bugawa da sauri har a kunnensa, seya dora hannunsa saitin zuciyarta ya dan danna kadan yace "kwanta kwanta kishi ba yanzu zaka tashiba".

Mirginawa tayi ta ture kansa yai saurin rikota gaba daya yana dariya, locking lips dinsu yai for some minutes what he never get tired of sannan ya saketa yana kallon fuskarta. Magana yake so suyi amma ya rasa ta ina ze fara mata yasan yanzu sabon balli ze tashi amma baze jurumi ganin kukanta kullum ba, ya sani tana da zafin kishi amma dole yasan yanda Ze koya mata ta ringa daurewa, babu wanda akayiwa alkawarin gobe. Ko a mafarki be taba tunanin ze hada ta da wata mace ba amma hakan bayana nufin ya bata guarantee din daga ita ya rufe ba, ranar kuma da Allah ya jarabceshi se ya ce mata me?.

Hannuwanta dukka biyu ya kama yana kallonta with serioua face yace " Hamdah". Seta tattara nutsuwarta imduka ta maida kansa dan tasan ba kasafai ya fiya kiranta da Asalin sunanta ba dole abu me muhimmanci ze gaya mata. "Hamdah kisakawa zuciyarki hakuri komai dakika gani a rayuwar Dan Adam RUBUTACCE ne. kidauka cewa hakan _*RUBUTACCIYAR KADDARAH*_ cikin kundin rayuwar mu kinji, and abu daya karki taba yarda cewa ni Abdulmalik zan qi ki saboda lalura, lalurar ma wacce bake kika dorawa kanki ba. Hamdah ke nake so, komai naki yayi min daidai da tsarina. Zan zabe ki akan mata Dubu. ke nake so bawai wani abu nakiba haihuwa ko rashinta bazesa na rabu dake ba ko na wulakantaki ba. Kin manta ranar dana karbi auranki? Nayiwa Abbah alkawarin kulawa dake iya kar numfashina. Nayi alkawarin kulawa dake iya karfin iko na ko akwai ta inda na gaza?" Seta girgiza masa alamar Aa kanta jkinta yayi matukar sanyi, "To karki qara saka wa ranki zan saba wannan alkawarin, ko mata dubu na kawo gidannan kece shugabarsu dan kece zabina. Ke na fara aure, dan haka ko wata zata zo a bayanki take dukda ni banida tsarin mace sama da daya kin sani". Nan gurin take so yazo, setayi saurin damke hannunsa cikin sanyin murya tace "Jaan kishiya fa" kallon rashin fahimta ya mata Dan Haka ta kara cewa "Jaan promise me baza kayimin kishiya ba duk tsanani". Murmushi

Please Login or Register in order to submit comment