Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa ta ci gaba da wayar ta, shima se nemi guri ya zauna yana kallon kayan data zube. Da daddaya yaringa dagasu kome yake dubawa oho haka cosmetics din data ajiye qarshe ma seyai snapping nasu da wayarsa. Gefen data ajiye Underwears ya daga Kunya kamar ta nutse lokacin daya daga daya daga cikin Bra din kome yake nema kuma oho se tayi saurin katse wayar ta iso inda yake ta re da fizgeta daga hannunsa.

"Wai meye haka malam zakazo kana min bincike a kamar ka bani ajiya". Be kulata ba shima ya fige yaci gaba da neman abinda yake nema din sannan ya danyi rubutu a waya da alama text ne kowa ya turawa oho.
"Ina zaki kike hada kaya" ya tambayeta hankalinsa akan wayarsa. Sedata hararaeshi sannan tace
"Inda ka aikeni".
Seya dago ya kalleta kadan kafin yayi kwafa ya maida kansa kan wayar, badan wani abu ba daya koyawa yarinyar nan hankali yanzu base anjima ba yanda ko ce mata akayi ta qara gaya masa maganar banza bazata iya ba. Se ya mike da kwalbar turarenta daya a hannunsa yace
"Get me some food I'm hungry please"

"Baza'a dafa ba" ta fada a tsiwace

"I said please" ya maimaita yana mata wani irin kallo. Se kuma ta danji kunya, ko ba komai yau rokonta yayi. Ita se alokacin ma ta lura kaman ya dan rame ga hancinsa nan ya qara tsaho, to ko bashida lafiya ta tambayi kanta. Kitchen din ta shiga, simple jellop rice ta masa da vegetables already tana da kaza a oven data gasa bata ma ci ba da safe seta qara te-heating masa ita ta hado da Coca-Cola me sanyi da ruwa da dora masa akan Dining har lokacin be dawo gidan ba dan haka tashiga shirya kayan. Seda ta gama tsaf ta zuge jakar sannan ya shigo ya chanza kayansa bana dazu bane da alama wanka yayi hannunsa riqe da ledoji guda biyu.

A kujerar Dining din ya zauna ya jingina kansa dayake matuqar sara masa idonsa a rufe yace
"Can you please serve me?" Seta kalleshi, salon nan nasa fa ya fara takurata. Baki a gaba ta isa gurin ta fara zuba masa abincin yana binta da kallo duk motsinta har ta gama ta tura masa gabansa bayan ta tsiyaya masa ruwa da lemo dukka.
"Ke bazaki ci ba" ya tambayeta yana kai lomar farko bakinsa, seta daga masa kai Alamar Eh. Shiru sukayi duka yana cin abincinsa lokaci lokaci yana kallonta ita kuma tana yan danne danne a laptop dinta.

"Take this" ya fada yana nuna mata daya daga cikin ledojin daya shigo dasu, seta taso kawai ita ma yanzu bata fiya son yawan maganar kuma ba takai hannu zata dauka wadda take kusa da ita yace
"Not this one the other one" yana pointing dayar ledar. Sanyin data ji ya tabbatar mata da mene a ciki seta ja kujera ta zauna har dimples dinta na lotsawa saboda murmushi ta bude Ice cream din ne kuwa favourite flavor dinta. Seta kalleshi lokacin da take kai spoon bakinta tace
"Thank you". He only smiled saboda yanda yake jin sa duk se a hankali. Ice cream din take sha har wani rufe ido take tsabar dadi shi dai kallonta kawia yakeyi dan ya gama cin abincinsa. Magunguna ya ballo a dayar ledar yace ta bashi ruwa mara sanyi abin kirki ba musu ta tashi ta dakko masa har tana tambayarsa meyake damunsa se ya nuna mata kansa kawai yana dan kwanciya akan kujerar idanunsa akanta. Seda ta shanye rubar gabanta tas sannan ta dauki dayar takai fridge ta ajiye, har lokacin yana zaune idanunsa a rufe se kuma ta danji dausayinsa. Tasan lafiya qalau baze zauna haka ba kila da yanzu tayi kuka.

"Ko na kira maka Dr" ta fada tana tsaye akansa fuskarta da alamar damuwa. Haka take akwaita da tausayi sosai idan taga mutum bashida lafiya.
"No i will be fine" ya fada yana qoqarin miqewa saboda mararsa dayaji ta wani murda masa kamar zeyi ihu, a daddafe ya nufi kofar seya tsaya saboda wani amai dayaji yana taso masa lokaci daya ba shiri ta isa inda yake jin yana kakarin aman tana zuwa kuwa ya wanke musu jiki tas daga ita har shi. Sannu ta ringa jera masa har ya gama dukka jikinsa yayi laushi. Zaman dirshan yayi a gurin jin wata juwa na neman kadashi ciwon da yakeji yana lafa masa.

Duk seta tsure tana tunanin meya sameshi haka. "Help me remove my shirt please" seta tsaya tana kallinsa, ita ta ina zata iya tabashi harta cire masa riga. Wai kodai yana manta dokokin musulunchi ne?
"Taimako ko a addini Halal ne _Ayush_" ta tsinkayi muryarsa. _Ayush_ din daya fada ne ya kashe mata jiki tareda sakata wani shauqi, seta tsugunna ta kama buttons din a hankali ta hau cirwa yana bin fararen yatsunta da kallo yanda suke trembling kaman me taba maciji. Seda ta ballesu dukka ya dan dago ta zare rigar gaba daya tsikar jikinta se tashi take da ganin kwantattun gashin dake hannayensa taqi ko yarda ta daga kai ta kalleshi.

"Aush" ya fada yana dafe kijinsa da cikin rashin sani ta karceshi da farcenta setayi saurin daga ido ta kalle shi tareda kai hannunta gurin tana shafawa tace laushin jikinsa na ratsata.
"Yi hakuri ba'a sanina bane".
Kallon dayake mata ne cikin ido ya fargar da ita abinda take aikata wa, seta miqe cikeda kunya ta fara kame kame tana cewa
"In zaka iya tashe kaje kayi wanka sena gyara gurin" cikin kwaikwayon muryarta shima yace
"Bazan iya tashiba ki dagani". Setasa hannayenta ta rufe fuskarta dasu tana cewa "ka bari bana so". Nan ya samu abin tsokanarta, moment din seya tuna masa sanda take Hamdah yake Abdul'ahad a zamanin rayuwarsu a BUK. Kamar bashi ya gama Amai yanzu ba ya mike tsaye yana cewa
"Let me go and fresh up ki bari na dawo sena gyara wurin" ya fice dagashi se dogon wando da singlet dukda karfin hali kawai yakeyi.

Bayan ta fita tsaf ta gyara gurin hatta da rigarsa seda ta wanke sannan ta shiga wanka ita ma. Batasan ya ya qare ba dan har dare bata kuma jin duriyarsa ba kamar ta leqa apartment dinsa amma ta fasa haka tayi bacci dan da wuri zasu tafi washe garin.

Jiki ba kwari ta ringa abu da safen dan har mafarkinsa tayi dan haka tana tashi saboda shi ta dora breakfast. Bayan ta gama tayi wanka ta shirya tsaf cikin baqar Abaya mara Adon komai haka fuskarta fayau turare kawai ta fesa. Seda ta fita da trolly dinta kafin ta dakko basket din data saka masa abinci ta nufi gidan kirjinta na bugawa ta danna door bell din jiran minti daya ya bude.

A kallo daya ta hango ramar dayayi ga kuma Cannular data gani a hannun sa seta bude bakinta a hankali tace
"Ya jiki?" Cike da mamakin ganinta ya amsa da "Alhamdulillah" dan ko kusa be kawo ita din ce ba, ya zata Benjamin yaronsa daya kirane ya iso, se ya matsa tareda bata hanya yace "Bismillah".
Gaba tayi yana binta a baya karon Farko data fara shiga gidan. Tsarin iri daya ne da nata se banbamcin furnitures nasa komai fari ne qala palour daga painting har kayan ciki. Sosai gurin ya mata kyau yanda yake a tsaftace kaman ba gidan namiji ba seta dire basket din tana kallon Agogo tace
"I will be gone for some assignments, ten days zamuyi" setayi shiru tana kallon yanda ya zuba mata ido da wani expression da ta kasa ganewa.

"Allah ya dawo daku lafiya take care, and Thanks for the Food". Mikewa tayi yana take mata baya har suka fito waje, dan kallon surrounding din yagi yaga babu kowa se kawai ya janyota ya mata wani irin tight Hug har seda ta dan tsorata, a cikin kunnenta ya rada mata "Thanks for the Food Baby Girl" ya saketa a loaci daya, seta juya ta fara tafiya har tana hardewa tsabar yanda jikinta ya amshi saqonsa. Motar da zata kaisu school tuni ta iso dan haka ta shiga ta zauna tana mayar da numfashi. Tanajin yanda idanunsa suke yawo akanta ta tababate be tafi ba yana tsaye har sanda Umm Ashrab ta fito suka gaisa sannan ta shiga motar suka tafi se a sannan ta daga ido ta kalleshi, murmushi ya mata bata san ya akai ba itama se kawai ta mayar masa wai seda suka fita sannan ta fara jin haushin kanta. Yanzu seya zata ma tana son abinda yake mata ne, ita kadai ta ringa cika tana batsewa da bata san dalilinta ba.

Koda suka hadu da Nurain baya baya yayi da ita dan ko a tafiyar be yarda ya hada Bus daya da ita ba dan shi kadai yasan me yaji ba iya wadda ya masa a school bane takanas ya bishi har gida ya kafa masa strong warning akan ko kallonta ya qarayi se yayi maganinsa dole ya shafawa kansa lafiya. Cikin kwana tara suka gama abinda ya kaisu a na goma ta dawo cike da kewar data rasa kota waye sedai Motarsa kawai data gani ta yaye kashi 60 cikin abinda yake damunta. Tunda suka tafi bata da wata nutsuwa sosai ance sabo turken wawa tariga ta saba da scent da kuma warmness na jikinsa harzuwa taste of his lips tayi missing. Da Azahar suka iso, shara ta hauyi dan gidan ya danyi qura dan an fara sanyi dukda beyi nisa ba har bayan la'asar sannan ta gama. Seda tayi magriba sannan ta salla wanka tayi sallar isha sannan taci abincin da Zulaiha ta girka musu kafin tabi lafiyar Gado ta kwanta baccin gajia.

Cikin dare qarar wayarta ta tada ita, cikeda magagi ta daga wayar ta kara a kunnenta batareda tayi magana ba
"Ki tashi kiyi sallah" kadai taji kamar an fada kafin a kashe wayar qit. Seta miqe idanunta har rufewa suke yi tsabar bacci tana mamakin saurin da Asuba tayi. Wanka tayo ko baccin ze saketa amma a banza haka ta tada sallah. Har ta idar da sallah tana qunquni tana zaune akan sallayar tana lazumi tajiyo motsin mutum a palour se kawai ta saka kuka dama abu a kusa. Wannan wace irin jaraba ce daga dawowarya, ita yau ko gidan Karuwai take zaune ai tana da Yanci tunda zaman kanta take baza'a ringa fado mata gida Any how ba sannan ita dai ta duba keys dinta dukka sunanan babu wanda ya bata to ta ina ya samu mabudin gidan?
Tana cikin share hawaye ya shigo dakin jikinsa sanye da Farar jallabiyya kal kansa ya gyara gashin kansa daya tara kadan kaman wani under 30. Kamshin mayen turarensa ta faraji kafin tajiyo sallamarsa ciki ciki. Gefen gadon ya samu ya zauna yana kallonta a ransa yana mamakin hali irin na Hamdah se kace matar Mamaci kullum kuka
"Ka manta ita dince ai" zuciyarsa ta tuna masa. Se yayi tsaki me sauti cikin qufula yace
"Malam tashi ki bani abinci ni yunwa nake ji kuma da wuri nake so na fita" seta tsaida kukan tsaf ta miqe tareda riqe qugu tana so yau kam suyita ta qare ne ta gaji, seta fara magana kamar haka

"Daka biya nawa kudin sadakina ehe nace a nawa ko kuma Baiwa nidin aka ce an kawo maka da zakazo da gadara asubar Allah karinga bani command kaman wani ubana wai na baka abinci to wallahi ka dade baka ci ba ka kuma tashi kafitar min daga gida kafin na tara maka Jama'a".
Kallon yanda take maganar cikin tsallar fitsara da rashin kunya yake har wani girgiza jiki takeyi ita ga mara kunya, seya gyara kwanciyarsa sosai akan gadon yace

"Banason yawan magana ki wuce kiyi abinda kawai na sakaki kinji ko" ai kafin ya rufe baki tayi kansa, kafafuwansa ta fara ja tana masifa
"Wallahi tashi ka fita na gaji da irin wannan tozarcin da wulaqanci ai ni ba Karuwa bace da zaka ringa shigarmin daki da mutunchina da darajata har kasa Mutane sun fara zargina da aikata sabon Allah kuma wallahi bazan dafa ba tunfa ba ajiyeni kayi ba kuna ban yafe batamin sunan da kayi ba se Allah ya saka......" Be bata dama ba saboda wata irin damqa dayai mata ya birkitota kan gadon gaba daya ya zamana tana qasa yana samanta. Gaba daya ya birkice mata kaman wani tsohon zaki duk yanda taso ta daure amma seta kasa ba shiri ta saka kuka ganin abin nasa na neman wuce gona da iri. Cikin kuka ta fara magana

"Kayi hakuri Abdul'ahad karka keta min haddi na roqeka ka tausayamin dan girman Allah ban taba zina ba kuma kaima nasan ba mazinaci bane na tuba ka yi hakuri ka kyaleni".
Kaman an dauke ruwa haka ya tsaya, kalmar Mazinaci data ambata ce ta katse masa duk wani hanzari. Seya mirgina gefenta ya dafe kansa da dukka hannayensa biyu saboda yanda yake sara masa yana ambaton suna Allah a ransa. Bargon dake kan gadon taja ta rufe jikinta saboda tuni yayi fatali da Hijab da kuna rigar baccin dake jikinta. Kuka take bana wasa ba tana jin wata irin quna har cikin ranta.

Ita kuma tata qaddarar kenan daga aure se kuma fadawa tarkon Namiji wannan shine ta fito daga rana ta fada wuta. Kukan da takeyi da ciwon da kansa da Mararsa suke masa lokaci daya suka hadu suka qara dagula masa lissafi seya kai hannu da niyyar rarrashinta. Baya taja da sauri tana qara wa kukanta qaimi tana cewa
"Nidai ka tashi ka fita dan Allah" ta rufe idanunta se hawaye dayake zubowa kawai.

Dakyar ya miqe yana layi ya zura jallabiyyarsa, bazata ce ga abinda yayi ba ita dai tajito qarar rufe kofofi dukda idonta a rufe yake bata kasa gane qaruwar duhu a dakin ba da alama an kashe fitila an kuma rufe labulaye saboda garin har lokacin beyi haske ba. The next thing sejin numfashin mutum tayi a kusada kunnenta yana qoqarin hade fuskarta da tashi lokaci daya ta dena kukan jikinta ya dauki rawa jin wani baqon Al'amari da bata tsammata ba.

Wani irin kiss me tafiya da sauran hankali yakeyi mata dayai nasarar sakata yin shiru, sauran abubuwan da suka biyo baya bazata iya fasaltasu ba. Abu daya data sani sun shiga wata duniya ita da _ABDUL'AHAD GALADIMA_ me ban al'ajabi. Abubuwan sun ringa faruwa ne kamar a mafarki wai ita da Abdul'ahad? "Innalillahi wa'inna ilahi raji'un" ta furta da qarfi tareda fashewa da kuka daidai lokacin data qarasa dawowa cikin hayyacinta.

"Abdul'ahad mun sabi Allah mun aikata babban laifi Abdul'ahad Zina da Aure mun shiga uku" ta fada tana sake rushe da kuka da qoqarin janye jikinta daga mugun riqon dayayi mata kusan minti goma da suka wuce. Tanajin yanda wani zafi ke fita daga jikinsa yana ratsata amma bata damu ba burinta a yanzu be wuce ya saketa ba, ta ina zata fara roqon yafiyar ubangiji? Wannan yafi kama da ganganci ba kuskure ba me ma ya kaita bada kai har bori ya hau? Seta qara kecewa da Kuka tana jifansa da duk kalmar data zo bakinta.





🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 4⃣1⃣

"Ka cuceni ka yaudareni ka kuma ci Amanar yarda wallahi se Allah ya sakamin wannan itace soyayyar da kake iqirarin kana min dama abinda kake muradi kenan meyasa tun farko baka bayya na manufarka akaina ba". Shiru yayi mata saboda Ubangiji ne kadai yasan yanayin da yake ciki a lokacin, wata duniya yaje ya dawo da be taba sanin wanzuwarta a doron qasa ba. Lallai hausawa sunyi gaskiya da sukace wai garin dadi na nesa, amma abun ya so ya daure masa hankali kadan.

Dukda besan mace ba a rayuwarsa be taba kusantar wata mace ba se yau amma a karance yasan komai game da mata. Hamadah tayi aure har sau biyu amma a yanda ya sameta idan badan ya sani ba he can swear with his own life that she is Virgin. Takai ta zarce duk wani hange da tunaninsa, her inner beauty is far beyond his imagination. Ubangiji ya mata baiwar daya tabbatar ba kowacce mave ba dan idan duk matan haka suke da babu wawan da ze yarda yai asarar Mace kamarta. Kukan da take yi yana neman ya hanasbi tunanin da yake me matuqar dadi da qawata zuciya. Beqi su dawwama a wancan yanayin ba har qarshen numfashinsa. Nutsuwa da kwanciyar hankalin daya samu da ita ta zarce misali, se kawai ya birkito ta gaba daya ta dawo saman jijinsa dukda irin zazzabin dayaji yana bi masa qashi da tsoka kaman ana gasa shi a Oven.

"Allah yai miki albarka AYSHATU Ubangiji ya baki abinda kike so duniya da lahira yanda kika farantamin kema Allah ya miki sama da haka". A cikin kunnenta dukka yayi wannan maganar, dukda irin kukan da take amma seda ta dan tsagaita na wani lokacin dan kalamansa sun mata Dadi. Sun tuna mata da daren farkon ta da Habibinta Marigayi Abdulmalik yanda yaringa rawar jiki yana sa mata albarka. Abdurrahman bazata dorar da komai akansa ba dan sambatune mara sa kai ya keyi shi amma Abdul'ahad fa? Idan ta tariyo maganganun daya ringa gaya mata dazu kwakwalwarta ai bazata iya dauka ba shiyasa ma bata bada muhimmanci gurin riqesu ba.

Seta saki sabon kuka lokacin dataji yana qoqarin sake maidasu ruwa. Se a sannan hankalinta da tunaninta suka dawo daidai ta tuna da danyan aikin da suka aikata. Fuskarsa ta riqe da hannayensa dayake aika mata saqonni dasu kafin ta mirgina da sauri ta sauka daga gadon se kuma ta kwalla qara tareda durqushe wa a gurin tunawa da babu komai a jikinta.

"Wane dare ne kuma jemage be gani ba Ammata, dan Allah tashi na kalleki sosai na qara godewa Allah bisa irin ni'imar da yayimin" magana yake cike da qarfin hali saboda zazzabin daya fara cin qarfinsa har jijinsa ya fara rawa. Yana kwance yana kallon yanda ta hada kai da gadon tana kuka abin tausayi taqi tashi ta kuma qi magana dukda irin roqonta daya ringayi. Abu daya take maimaitawa "ya cuceta ya bata mata rayuwa bazata yafe masa ba se Allah ya musu hisabi ita dashi tunda fin qarfinta yayi ba a son ranta ba" har muryarta ta dashe tsabar kuka ga ciwon kai da zazzabin ita ma yana neman kamata.

Babu daya a maganganunta da suke masa dadi, amma shi ta ina ze farawa wannan yarinyar me shegen kafiya bayani? Zama ta yarda ta saurareshi ne a yanda ta hau dokin zuciyar nan shedan na qara buga mata ganga? Kukanta ya ishe shi, se kawia ya mike tsaye da niyar zuwa inda take ya rarrasheta ko ze samu tayi shiru cikin tsautsayi jiri ya debe shi ya tafi gaba dayansa ze fadi da azama ta tareshi suka koma a tare suka kwanta kansa a qirjinta yana fitar da numfashin wahala me azabar zafi. Ba shiri kuka ya tsaya cak dan jin zafin jikinsa na barazanar qona mata fata ta shiga tattaba kansa zuwa wuyansa tana cewa

"Meya sake ka baka da lafiya jikinka yayi zafi Abdul'ahad sosai". Yanda ta rude se kuma ta bashi tausayi. Yasan Hamdah tana sonsa koda bekai yanda take sonsa ba, se kawia ya qara narkewa a jkinta yana yanda fatarsu ta manne guri daya ya masa dadi ji yake kaman ya rabe biyu ta shige ya sake hadewa, dakyar ya bude baki yace
"Bake ce kika kika lasamin zuma ba ni kuma na kasa jurewa gashi har kin kusa kasheni". Setayi saurin rufe fuskarta da hannayenta tsabar yanda maganar ta bata kunya. Kansa ta shiga turewa daga jikinta tana cewa
"Ni ka dagani ai bani na gayyato kaba kai ne ka kawo kanka da kanka"

"Ni Aa muyi ta zama a haka kinji" ya fada yana gyara kwanciyarsa sosai dukda qarfin hali kawai yakeyi. Drama suka shigayi tana tureshi yana sake manne mata kamar ma ta manta da abinda ya faru yanzun, "Idan kinaso na tashi to ki bari na qarayi sau daya shikenan sena dagaki amma in ba haka ba ba inda zani".

Ai ba shiri ta hambarar dashi daga jikinta har kansa dake ciwo ya bugi gefen gado. Toilet ta afka ta shiga rera sabon kuka da iya qarfinta, da hannu biyu ya dafe kansa kafin ya samu dakyar ya maida rigarsa yana bin bango ya qarasa jikin kofar toilet din cikin sanyin murya ya fara magana

"Hamdah ki bude i will explain everything to you, i have never for once had the intention of hurting you koda kuwa a mafarki ban yaudareki ba ban kuma yimiki wani abu da sunan cuta ba amma ki fito I promise zan gaya miki komai...." Setayi saurin katse shi da cewa
'ka gayamin me, me yai saura badai ka kawar da Sha'awar shekaru shida akaina ba to kaje Allah ze saka min ka kuma fitar min daga gida tunda ka gama abinda ya kawoka". Ba karamin bata masa rai maganar ta tayi ba, shi zata cewa ya kawar da Sha'awar shekara shida akanta? A zatonta dan wannan abin yake sonta inda shine da tuni ya dade da goge shafinta da tuni ya amshe abinda take tutiya dashi din da bebarta takai gidan wani ba. Se ya bude baki cikin daga muryar dake nuna bacin rai yace

"Na rantse da Allah idan baki tsaida kukan nan kinyi wanka a minti biyar kin fito ba sena baki mamaki, kinsan ba fin qarfina kikayi ba, I will rape you in barmiki tabon da har ki mutu baze goge daga zuciyarki ba"

Ai tun kafin ya gama ta kunna shower ta shiga ruwan na sauka a jiki ta tana kuka. Ta sani idan batayin ba seta raina kanta a hannunsa. A haka a hankali yabi da ita amma ita kadai tasan me ta jiyo to inaga yana maganar Rape ai gara yasa bindiga ya harbeta kawai ta huta da baqin cikin rayuwa. Yana zaune dirshan a kofar toilet din ta fito gashinta na zubda ruwa alama tayi wankan Tsarki. Kallo daya ta masa ta dauke kai idanunta da fuskarta sun kumbura ba kadan ba abin tausayi. Gefen gadon ta samu ta zauna tana satar kallonsa ganin yanda yake cije baki hannunsa riqeda kansa dayan akan cikinsa seta tabe baki a ranta tace "baka ga komai ba sema Allah ya isata ta fara kamaka

"Hamdah zan mutu" ya fada kalaman a rarrabe. Ai bata san sanda ta saki man data dauka da niyar shafawa ba bayan data gama kunkuninta tayi kansa cikin matuqar tashin hankali tana kai hannu jikinsa ta janye saboda yanda taji yayi zafi rau. "Get my phone zakiga Master please ki kiranin shi be Sharp".

Saboda rikicewa seta dauki tata wayar ta shiga neman number, a gefen bed side ta ga wata wayar tayi cilli data hannunta ta dauketa tana kallon yanda yake struggling da numfashinsa kaman wanda ake zarewa rai abinda ya qara tsorata ta kenan, ita yanzu ya mutu a gidanta tacewa mutane me? Me yazoyi har mutuwar ta riskeshi anan? Password ne akan wayar se kawai ta saki kuka tana koma wa inda yake a zaune "da password akan wayan kuma ni bansan yanda zan bude ba" tayi maganar kaman wata qaramar yarinya har seda ta saka shi dan murmushi.

"Ki kai screen din face dinki zata bude" ya fada kaman bayason maganar setayi saurin kai wayar fuskarta nan take kuwa ta bude, tana shirin dialing number master kiransa ya shigo seta daga cikeda zumudin
"Galadima kana ina ne gani by ur door i come to drop ur medicine kanin gwauro....."
"He is in plat A30-3 kazo we need ur assistance" ta yi saurin katse master. Kallonta Abdul'ahad yake with adoration, shi meya masa saura bayan alfarmar da Allah ya masa ta mallaka masa wannan? Ai a duniya dai ya gama dace sedai fatan samun dacewa a lahira kuma. Dakyar ya iya bude baki yace "ki saka Hijab ki bude masa kofar and please ki rufe fuskarki banso yaga wannan kumburin" ta "To" ta amsa kafin ta bude wardrobe ta dakko zumbulelen Hijab me fuskata saka lokacin har ya fara knocking, tana bude kofar ta juya tayi shigewarta dayan dakin ta bar Master da baki a bude cike da Mamaki, sedai ya girgiza kai dan besan wacece ba a iya saninsa kuma Galadima baya harkar Mata kuma wannan Fara ce bare yace Ni'ima ce.

Kofar dakin daya gani a bude

Please Login or Register in order to submit comment