Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lafiya?". Bata amsaba swma gefen gado data samu ta zauna zuciyarta na ci gaba da bugawa kamar wadda tayi tsere. Wani irin tsoro ne yake shigarta tareda fargaba Wanda bata taba jin irinsu ba, meya ke shirin faruwa da ita ne? Wai dama haka mata sukeji idan mazajensu zasu qara aure lallai kishi babban abu ne, seta shiga share hawayen daya fara zubo mata zuciyarta na mata quna. Kusa da ita ya koma ya riko hannunta cikin nasa sannan yace "Babe please menene?" Duk yanda taso ta daure seta kasa kawai ta fada jikinsa ta ida sakin kukan me sauti tana cewa "Maleek dan Allah karka juyamin baya kar giyar Amarci tasa ka wulaqantani ban san ya zanyi da raina ba". Bubbuga bayanta ya shigayi yana dan murmushi kafin ya dago fuskarta yace " Babe kishi, keda kika ce mayi hudu ma ina ruwanki shine har kin karaya a guda daya". Boye fuskarta tayi a jikinsa taba sauke ajiyar zuciya shi kuma yana ci gaba da tsokanarta har seda tayi dariya sannan ya taahi da ita a jikinsa. Dakinta ya kaita ya ajiyeta akan Stool shi kuma ya koma kan gado ya kwanta idonsa akan duk wani motsinta. Murmushin Yake kawai takeyi duk sanda suka hada ido. Se tace masa " katashi kayi wanka dan Allah kaga kowa laifina yake gani banaso yau a samu matsala Dan bakaga irin abinda sukayimin ba jiya saboda bakaje gurin dinner din nan ba" se tayi rau rau da ido tana shirin fashe masa da sabon kuka. Murmushin gefen baki yayi yana kada kansa, se ya mike ya isa inda take ya mata peck akan lips dinta sannan ya fice daga dakin. Nasa dakin ya koma ya shiga wankan.

A sanyayae take komai har ta gama shiryawa cikin wata hadaddiyar atamfa shareton Pink datai bala'in yi mata kyau dinkin riga da Skirt. Dakin da su Hamida suke ta shiga har sun gama hada breakfast sunyi wanka suna zaune suna hira, fita tayi daga dakin bayan sun gaisa ta koma nasa ta zauna a gefen gadon tana wasa da zoban hannunta har ya fito daga wankan.Ita ta taimaka masa ya shirya in banda kallonta ba abinda yakeyi dan kwalliyar tata ta birgeshi sosai batai auneba se ji tayi ya janyota sun fada kan gadon gaba daya.
"Jaan 9:30am fa tayi....."
"Shiiiii..." ya katse ta yana ture daurin Dan kwalin dake kanta.
Wata irin soyayya yake gwada mata wadda zata iya cewa a zaman auransu shekaru Hudu bai taba kwatanta mata ko kusan irin taba. yanayin surutai da maganganun da yake se suka fara bata tsoro sun wuce ace na shauqi ne. Sun dade cikin wannan halin kafin ya rabu da ita sai ajiyar zuciya da yake saukewa wata na bin wata ya dauki kusan minti goma sannan ya Mike tareda daukanta tamkar yar baby suka shiga toilet din, shi yai mata wanka sannan shima yayi haka shiryawa dakansa ya shiryata tsaf cikin wani hadadden Lace maroon da akaiwa kwalliya da zare golden dinkin riga da skirt. Sosai tayi kyau saboda yawancin lokaci tare sukeyin komai yasa duk wata kwalliyar mata ya iya. Tana zaune tana kallonsa da alokacin bata da karfin tsinana komai se kallo da ido har ya saka Farar shadda kar dinkin babbar riga da tayi bala'in karbarsa, setaga ya qara mata kyau na musamman ga wani kyalli da annuri da fuskarsa take futarwa. Daure duk wani kishi tayi ta karbi hular dayake qoqarin saka wa ta saka masa sannan ta daura masa Agogo. durqusawa tayi ta saka masa baqaqen takalmi sau cikin daya dakko sannan tashiga fesheshi da turare.Wani abun mamaki ko kadan yau seta nemi kishi tarasa gaba daya zuciyarta ta juye inbanda wani azababben tsoro da fargaba da suka cikata (kishin kenan Lol), rungumar dayai mata ce ta dawo da hankalinta sannan ya janyo wayarsa kirar IPhone 11pro max ya shiga daukansu pictures dasukayi bala'in kyau kai kace yaune daurin auransu. Suna tafe yana uploading pics din akan Instagram dinsa da whatsapp tuni mutane suka fara commenting Dan dole su bigeka. Hoton da ya dauketa ita kadai bayan ya sakata yafa mayafi ya uploading tareda yin rubutu akasanshi

*_You are my dream come true. I have loved you ever since the day I first met you. Forgive me for days when I fail to make you feel appreciated. Thank you for making me feel like the luckiest man in the world every single day. You never cease to surprise me with all that you can do and all that you can achieve. Thank you for making our married life all that I dreamed it would be. Thank you for filling our home with love and happiness_* *_I love you with all my heart matata yar Aljannah_* 😘😘😘💗💗💗💗💗😍😍😍 *_Ubangiji yayi miki albarka Aishatu Allah ya faranta miki yanda kika Faranta min a duniya da lahira. See you again"_*.

A babban falon suka tarar da Ahmad da wasu abokansa guda uku cikin shigar daurin aure nan suka shiga tsokanarta wai uwar gida ran gida ta basu ango haka karsu makara it dai murmushi take tayi suka fita. Har ta juya taji ya riko hannunta wata irin runguma yai mata ya shiga sakar mata hot kisses a kowanne bangare na fuskarta batareda kalmar I LOVE YOU ta bar bakinsa ba. Lamarin nasa yafi kama da na zautacce seta shiga janye shi daga jikinta tayi saurin barin gurin Dan alokacin ji tayi tamkar zuciyar ta zata fado tsabar fargaba ga wani kuka daya taho mata. Bata san tsiyar da suka tafka a bangaren Hajja ba ita dai zata tuna lokacin da taji fitar motarsa cikin wani matsanan cin gudu abinda yake nuna yana cikin matukar bacin rai kenan lokacin suna waya da Mumcy take gaya mata yanayin da takeji a jikinta, murmushi Mumcy tayi sannan tace "Ho Hamdahna wannan ai shine kishin Amma naji dadi da kika iya dannewa kici gaba kinji Allah yana tareda masu hakuri Insha Allah zaki ga ribar hakan a gaba Allah yai muku albarka Allah ya hada kanku ya baku zaman lafiya."Haka tayi ta jero masu addu'oi fitar motar tasa ce ta sakata katse wayar daga nan ta koma dakinta ta kwanta Dan huta gajiyar daya saukar mata aranta tana fadin "O ko ya zaman mu ze kasance oho Allah dai ya bani ikon cinye wannan jarabta" da haka bacci yai awon gaba da ita.

Wurin 12pm Su Anty Zahra da matansu Yaya Abubakar da sauran danginta suka karasa gidan. Gaba ki daya layin a dinke yake da jama'a kai kace anan gidan ake daurin auran ko hanyar da zaka ratsa da kafa ma se kayi da gaske. Lokacin da suka isa daidai gate din gidan su Abdulmalik din abun ya daure musu saboda kuka da kururuwar mata dasuke jiyowa daga ciki ga wasu maza da yawa. Se tunaninsu ya basu ko wa rigimarce dai bata kareba tunda halinsu ne masifa da bala'i Dan haka Humaira yar kanwar Abba taa tabe baki tace "Me za'ayi da wannan jarababbun mutane ni wallahi in nice Yaya Hamdah nagama auran haba mutane Kaman dangin shedan" harararta Anty zahra tayi dan haka tayi shiru suka qarasa cikin gidan.
Abangaren Hamdah kuwa a gigice ta farka daga baccin data fara saboda wani mummunan mafarki datayi. bugun zuciyarta ne ya kara tsanan ta har tana jin tamkar zata bar kirjinta bashiri ta diro daga gadon ta shiga kiran wayarsa sedai harta tsinke be daga ba, kita taci gaba dayi tana cigaba da maimaita Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a wannan halin suka tarar da ita. Tana ganinsu ta saka kuka, Anty Amna ce ta riqeta tana cewa "Ya kuma kuka Hamdah ki bari dan Allah". Seta rungumeta tana ci gaba da kukan, " Anty ku kiramin Abdul dan Allah na kirashi baya dagawa ni shi kadai nake so na gani yanzu". Lallashinta suka ci gaba dayi har tayi shiru daga baya. Suna zaune jugum babu me cewa komai Alhaji Kabiru babban yayan su Abdulmaleek yayi sallama tareda wasu manya daga cikin Familyn, bayan sun basu izinin shiga ne ya kalli Hamdah da harta fada lokaci daya yace "Am in ba damuwa kuzo cikin gida muna son magana dake" suka juya kowa da irin abinda yake cikin zuciyarsa. Dankwalin kanta ta zame sannan ta zura dogon hijabinta har kasa suka nufi cikin gidan.

Tundaga kofar data raba parts din suka san ba lafiya ba, kururuwar mata da iface iface ne ke tashi daga cikin gidan se tashin kabbarar da Mazan suke tayi a haka har suka karasa cikin Babban Falon da taraddadin abinda zasu tarar. A tsatstsaye suka taddasu, Munubiya na tsaye akan Hajja tana kuka tana cewa "Hajjah kingani ko kinga abinda nake fada miki kika biyewa Su Hajia Hauwa gashi yanzu sun kaimu sun baro" ta karasa tana jijjiga Hajjah dake zaune kaman an ajiye gunki. Kallonsu taringayi daddaya kusan babu wanda baya gurin cikin yayan gidan mata da Mazansu dayawansu kuka sukeyi se masu qarfin zuciyane kadai suma kallo daya zaka musu ka karanto zallar tashin hankalin da suke ciki mutum biyu ne babu a ciki Abdulmalik se Aliyu dayake karatu abroad.
Cikeda karfin gwuiwa tareda son qaryata zuciyrta ta karasa tsakiyar falon idonta akan mutumin dake kwance lullube da zanin gado tayi saurin dauke kanta tana so ta goge duk wani mugun tunanin dayake gaya mata Abdulmalik ne Aa kilan Aliyu ne Amma anya kuwa ai kuma Hajia Shuwa ya kamata ta gani cikin irin Halin da Hajja take ciki da haka ta qarasa tayi zaman dirshen gaban gawar da takejin kamar tana janta da mayan karfe.

"Abdulmalik" ta furta a hankali dason tabbatar da abinda idonta ya gani, seta maida mayafin ta rufe tana mayar da numfashi kamar wadda tayi tsere. Qara budewa tayi a karo na biyu ta yi saurin juyar da fuskarta tareda runtse idonta, Inama wani ya tasheta ya gaya mata cikin bacci take wannan mugun Mafarkin. Abdulmalik dinta ne kwance fuskarsa fes tamkar ka kirashi ya amsa, farar shaddar daya saka ta dade da rinewa zuwa jar kala sakamakon jinin dake zuba daga jikinsa Wanda har zuwa yanzu be tsaya ba. Allah sarki Hamdah, sai gashi itama tabi sahun Hajjah, gefe ta samu ta makure bata qara cewa kowa kalaba.

11:30am
Adaidai lokacin da fadar gomnati ta cika makil da mutane masu jiran zuwan ango a daura aure tuni wasu suka fara tafiya dan suna da uzuri. Duk irin kiran da Alhaji da yayyensa suka ringa yi yana kwance a hotel room din da ya kama be daga ba. Ahmad da bakinsa kamar ze qara tsaho saboda magana yana tsaye akansa ya rasa ya yake ao yayi, kiran wayar Hajja ne ya shigo wayar Ahmad ba shiri ya daga tareda sakata a Handsfree "Ahmad ka gaya wa Abdulmalik ban yafe Nono na daya shaba in har be saki waccan tsinanniyar mayyar data lashe mas zuciya ba sannan kagaya masa koya tashi ya tafi daurin auran nan ko na tsine masa" kit ta kashe. Be saurari Ahmad ba ya fice daga dakin ya dauki motarsa ya fita daga Hotel din cikin tsautayi da qarar kwana daidai ya hau wata Gada ya rasa control din motar ya gangaro haka ta ringa juyi dashi kafin ta kife acan gefen titi kafin mutane sukai masa wani taimako har rai yayi halinsa. Kiran wayar Ahmad da ya shiga wayar wani mutum ya daga, shi ya sahida masa abinda ya faru tsabar rudu rasa me zeyi ma yayi seda ya tattaro yayyen Abdul din sannan suka qarasa inda abin ya faru kafin suje har Yan sanda sun kai gawar asibiti acan suka karbeshi suka wuce da Gawar gida.















🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 2⃣5⃣

Tunda ta zauna ta sunkuyar da kanta bata qara bari sun hada ido da kowa ba. Taqi yarda da abinda ta gani, har a lokacin jira take taji ta farka akan gado alamar mafarki ne, a maimako sema iface iface da suka cika mata kunne. Ko da yangidansu suka iso kallo daya Mumcy tayi mata ta dauke kanta ta samu guri itama ta zauna dan zuciyarta tarigada ta karaya. Tunda taji sakon mutuwar hankalinta yai matukar tashi ba kadan ba. Tausayi da jimamin halin da diyar tata zata shiga kawai takeyi. "Allah sarki Abdulmalik ashe rayuwar ba me tsaho bace anyi gwagwar maya ubangiji Ya karbeka baquncinka, Allah yasa annabi yasan da zuwanka Abdulmalik Allah yasa can din tafi nan" Abinda Abba ya fada kenan yana juya kansa cikin matuqar kidima. Mutuwar ta gigitashi kamar Dan cikinsa ya rasa maganganunsu na qarshe a jiya da daddare dajaje gaisheshi kamar yadda ya saba duk Juma'a, sun dade sosai suna magana akan wani project dayake so yayi akan Manfetur, "Idan Allah ya tabbatar da abin nan to ina gaya maka nan da shekara biyu sedai kaga sunanka cikin Top 10 richest Men in Africa" Abban ya fada masa cikin sigar tsokana se yayi dariya sannan yace "Abba to waya sani ko zamu ga gobe ma bare wata shekarar" da wannan sukayi sallama ya tafi.

Wani palour daban aka ajiye gawar bayan an gama shiryashi. Umar ne yashiga inda matan suke yace suzo inji Alhaji Babba suyi wa Abdulmalik sallama za'a fita dashi inda dubban Jama'a ke dakon yi masa Sallah. Nan fa sabon kuka ya fara seda Wani Kawunsu ya tsawatar musu sannan suka ringa zuwa sunayi masa Addu'a. Hamdah dake zaune bata da niyyar tashi har kusan kowa ya gama se Goggo Habiba ta kama hannunta tace "Daurewa zakiyi Hamdah Allah kadai yasan yaya kikeji daure kije kiyiwa mijinki addu'a ita yafi buqata a yanzu sama da komai itace babbar soyayyar da zaki nuna masa" bata mata musu ba ta mike duk suka bita da kallon tausayi. Har kan gawar ta kaita sannan ta saki hannunta.
Durqusawa tayi a gefensa ta dora hannunta na dama akan qirjinsa, karon farko tun bayan data samu baqin labarin tayi magana "Dana sani ban tayarda hankalina ba, dana sani na qarbi kaddarar data zo mana nasan da kaima kayi hakuri ka karbeta amma babu wanda ze kankare _Rubutacciyar qaddararsa_. Mutuwa dole ce amma Abdul tayi sauri ta dauke ka a lokacin dana fi buqatar rayuwa dakai" se ta dakata ta share siraran hawayen da suka zubo mata, jarumta ta aro ta sakawa kanta ta shiga karanto masa Addu'ar da Annabi ya koya mana da muyiwa mamaci, ta dade tana masa addu'a da roqa masa rahamar ubangiji da saukin tsananin kabari. "Ya Ubangiji Abdulmalik bawanka ne me yawan ibadah, me yawan azumi, me haquri, me kyakykyawar mu'amala. Abdul ya kasance me biyayya ga iyaye ya sauke haqqin aure, ya ubangiji kayi masa sakayya da mafificin lada ka bashi aljanna madaukakiya badan ayyukansa ba sedan ka kasance me rahma. Ya ubangiji ka kyautata makwancinsa ka tarbeshi kana farin ciki da dawowarsa gareka ka haskaka masa kabarinsa da haskenka, ka shayar dashi iska daga ni'imarka ni kuma ka bani haquri da juriyar rashinsa...." Seta kakare saboda numfashinta da taji yana barazanar barin jikinta kawai seta sulale ta kwanta ajikin sa. Da Amin su ringa amsa mata babu wanda bata birge ba a gurin. Fauziyya ce ta qarasa ta dagata daga jikinnasa tana kuka tamkar ranta ze fita se gashi wai Hamdan ce take basu hakuri akan su dena kukan.

Lokacin da aka fara kokarin fita dashi domin yi masa sallah sai a sannan Hajjah tafasa wata kara tareda riko gawar tana cewa "Na shiga uku na kashe Dana dakaina, Abdulmalin kayafemin, kakance me tsananin biyayya a gareni amma na biyewa son zuciyata akan naka muradin dama ka fada min amma na toshe kunnena naki jinka yau gashi son zuciyar ya kaini ya baroni na hanaka zaman lafiya da Matar ka na uzzurawa rayuwarku yau gashi is tafi kabarni da tarin nadama da dana sani ina zan kai haqqinka gashi baka raye bare na nemi yafiyarka nasan kana jina dan girman Allah na tuba kayafemin kayafemin Abdul..." Haka taringa surutai dai marasa kan gado da kyar aka janyeta ana fita dashi kuwa ta sulale a gurin sumammiya.

Allahu akbar rayuwa kenan. Aka ce ana bikin duniya ake na qiyama se gashi mutanen da suka taru domin murnar daurin aure sun juye zuwa zaman makoki. A wannan rana ta Asabat dubban mutane ne suka raka Abdulmalik Kamalu Dala zuwa gidansa na gaskiya cike da alhini rabuwa dashi kasancewarsa mutum na mutane, a tsahon rayuwarsa babu Wanda zaice ga abokin fadansa domin shi mutum ne mai yawan yafiya. Da akwai wata hira da aka tabayi dashi a gidan wata Tv reporter yake tambayeshi menene makamin nasarar sa a rayuwa se yace masa Haquri da yafiya, bai taba kwana da baqin cikin wani a zuciyarsa ba komai girman laifin da yayi masa kuwa, sannan ya riqe dare, qiyamullaili itace abar debe masa kewa, ya kuma riqi azumin Litinin da Alhamis, ya bi iyayensa sannan ya kyautatawa matarsa wadannan abubuwa kadai na riqe sune makamina. Abdulmalik nada barkwanci ga tausayi ga na kasa dashi, ya samu shaida ta gari daga yawancin mutane wadda ko wanne mamaci yake fatan samu sai muce Allah yasa kyawawan halinsa su bishi.

A bangaren gidan su Amarya Haula kuwa Sai gashi gidan biki ya koma na mutuwa, Hauka ne kadai batayiba a lokacin data samu labarin rasuwar Angon nata. Hajia Hauwa ko lokaci daya Wani tsoro ya shigeta tareda Nadama. A lokacin da Al-amin yayan Haula yashiga gidan da rigarsa da hula a hannu tana tsaye a dakinta tana waya da Bokan da yake mata aiki akan Maganar auran tana shaida masa ance haryanzu Ango beje gurin daurin ba gashi har mutanenn da aka tara sun fara tafiya. Ce mata yayi duk abinda take ta bari tazo akwai abin da ze bata sunansa qare aiki tana haramar fita Al'amin din ya kwaza musu maganar mutuwar seta nemi guri ta zauna zuciyarta na bugawa. Rayuwar kenan ashe duk hauka sukeyi tana shirin tafiya karbo qare aiki aahe shi tasa rayuwar ma ta kare gaba daya. Haka suka tattaro suka dunguma gidansu Abdul din anan ta tarar da Halin da Aminiyar tata take ciki wanda ita ce sula. Ta suma yafi cikin kwando da an samu ta farfado minti kadan zata koma se ihu da fizgefizge take ita a barta ta dakko danta be mutu ba, seda aka jona mata ruwa da alluran bacci sannan aka sami sa'ida.

Lamarin Hamdah kuwa ya ya zama se addu'a kawai domin har zuwa yau kwana biyu da rasuwar babu Wanda zece yaji maganarta, tana zaune sedai ta tashi tayi sallah ta koma same spot datake zaune ko gaisuwa aka zo mata sedai ta amsa musu da kai kawa. Ba yanda basuyi da ita ba akan tayi kuka Amma taki tadai zama kamar wata wacce tayi loosing memory bata uhm bata umum sedai duk abinda akace tayi zatayi ko abinci aka kawo mata zata karba ta ajiye dan baze iya wucewa ta makoshinta ba Mama Shuwa ce take dama mata kunu ba laifi tana dan samu tasha ko rabin kofi a lokaci ammafa bazakaji muryarta ba. Sau tari Mumcy zata sakata agaba tayita kuka ganin yanda lokaci daya rayuwarta ta chanza daga farin ciki zuwa akasinsa, ta rame ta fige tamkar wacce ta shekara tana ciwo se uban Haske data qara. Hajjah dai akwanakin ta suma yafi sau dubu Allurar ma ta dena daukarta ga jininta yayi mugun hawa.
Aranar kwana uku Khaleefa ya dawo kasar cikin tashin hankali a Instagram yaga labarin mutuwar yana ta trading a farko besan waye ba seda yaga hoton sannan ya shiga dimuwa haka yaita neman Ticket har se yau kwana uku sannan ya dawo yana kuka ya isa gidan yayar tashi nan ya tarar da halin da take ciki abinda ya kara tayar masa da hankali kenan. Anyi sadakar bakwai zaman karbar gaisuwa ya watse, Abbah ya nemi da sursu su tafi da ita gida tayi takaba a acan ganin yanayin da take ciki, Alhaji kamalu da duniya tayiwa karatun Kurma ya yarda cewa babu tabbataccen abu ne ya nemi alfarmar suma da abarta a dakinta zasu kula da ita insha Allahu, har lokacin akwai sauran darajar Abdul a idonsu dukda qasa ta rufe masa ido dole suka barta anan gidan suka bar mata Hamidah da wata kanwar Mumcy da suke cewa Adda Maimu itama mijinta ya rasu ta dan manyanta amma bata taba haihuwa ba su tayata zama. Se a ranar ta koma gidan ta dan Tun bayan Rasuwar anan bangaren take kwana.

Dakinsa tashiga, gadon yana nan yanda suka barshi tun waccen ranar haka Daurin dankwalinta daya cire mata batareda ya warware ba yana nan a ajiye akan Bed side drower. Idon tane ya sauka kan brown din hularsa dake ajiye akan mirrow take abinda ya faru a lokacin ya fara dawo mata, lokacin da tacire masa hular tana cewa "Haba Jaan wannan hula ai bata hau ba kwata kwata kalli fa aikin kayanka da kalan takalmin ka koda yake dama naga gayun ya fara sakinka duk ma ka fara tsufa" ta cire sannan ta saka masa Black kalar aikin rigarsa, muryarsa takeji akunnenta lokacin daya ce "Bakomai dama ai ke nakewa gayun nasan kuma kodashi ko babu shi kina sona a haka to bani da wata damuwa ni kam". Seta zauna a gefen gadon a hankali ta rungume hular a kirjinta, A yau ta tabbatar ta rasa mijinta me matukar Sonta da kaunarta, ta yarda Abdulmalik ya Barta bari na har abada se kuma a Darussalam ita dashi, wani kuka ta saki me cin rai da ban tausayi Wanda bata samu damar yinsa ba sai yau. Dole tayi kuka tasan ta rasa jigo a rayuwarta, ta rasa Abdulmalik shekaru hudu da kwana goma da auransu.

Lokacin mutuwar ta dawo mata sabuwa. Kukan da batayiba yanzu ta take yinsa. Tafi wata uku cikin wannan halin, damuwa da yawan kukan data keyi ga rashin cin abinci suka haddasa mata ciwo mai tsanani da yai sanadiyyar barin cikin wata uku da batasan tana dashi ba alokacin saura kwana biyar ta fita daga takaba. Sabon tashin hankali wannan karon Hajja seda ta kusan samun paralyse, surutai ta ringayi tana cewa " Allah na tuba, meyasa baka bar mana cikin nan mun samu magajin Abdulmalik ba, Allaj ko baka yarda da nadamar danayi bane kake qara hukuntani haka wayyo Allah na likita kasan abinyi dan Allah" fita da ita sukayi daga asibitin ba shiri ganin tana neman tara musu Jama'a ga sabon da take qoqarin tafkawa. Hamdah kanta tayi kuka data san tana da cikin nan da batayi wasan da zata rasa shi ba, shikenan bata da komai na Abdul se hotonsa kawai. Haka akayi ta bata hakuri qarshe ta dangana dama ba rabon ze taka qasa bane. Kwananta uku aka sallameta bayan dogon jan kunne da gargadin da likita yayi mata akan yawan damuwa, gida Mumcy ta tafi da ita tace sakacine ya jawo har cikin ya zube basu san dashi inda a gabanta take ai da bata barta cikin damuwa ba ko ba komai zata ringa ganin yan uwanta suna rage mata damuwa.

Kwananta uku a gida Afeeya tazo mata gaisuwa dayake mijinta ya samu chanjin aiki zuwa kasar America can suke zama yanzu mutuwar kuwa ta dakeshi bana wasa ba, koda suka zo kasa hada ido da ita yai haka ya ringa share hawaye kamar mace. A Maryam da Aysha ma sukaje, haka suka wuni suna aikin kuka babu mai rarrashin wani har dare sannan kowacce ta tafi gidanta Abdulmalik dai ya shude sedai a bishi da fatan samun rahamar Allah.
A yanzu bata da wani aiki daya wuce na zaman daki in ba Sallah ba to tana jan carbi ko ka sameta ta rabka tagumi tana tunani Wanda ya zame mata jiki sai anyi dagaske take fitowa cikin mutane saukinta tana Dan cin abinci haka takan danyi magana da su Amrah da Afrah da aka kawo mata hutu ko sa ringa debe mata kewa. Kusan ko yaushe yan gidan su Abdulmalik nakan hanyar zuwa dubata harda Alhaji kamalu da yayiwa kansa karatun ta nutsu da sauran kishiyoyin Hajjah dan mutuwar ta zamar masu ishara.

Cikin week end Alh Kamalu ya samu Abba akan maganar rabon gado, be musa masa ba saboda sauke nauyine sun gama tattara komai na Abdul din dan babu me binsa bashi wadanda yake bi ma

Please Login or Register in order to submit comment