Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

timae. Agogon dake dakin ne ya buga karfe biyar daidai, se ya miqe cikin mutuwar jiki tunawa da ko sallar azahar beyiba a jirgi ta sameshi. Sanda ya fito se ya kasa kallonsu musamman Umman Ni'ima da yake ganin kaman be kyauta mata ba. Ta dauki yarta ta bashi dukda ba'ason ransa ba amma ai shi yayi alqawarin kulawa da ita. Masallaci ya tafi yayi Alwala ya rama sallolin kansa be koyi tunanin neman abinci ba dukda yanda yunwar take sakadarsa. Seda akayi Magriba sannan ya fito lokacin duk sun tafi se Ammi kawai da Umman Ni'ima da Aminullah daya kawo musu abinci da yake su suke kwana da ita.

"Baka tambayi yar rigima ba" Ammi ta masa magana duk ason kore masa damuwar dataga ya shiga. Shi sam ya manta da wata Little ma se yanzu, zama yayi Umma ta zuba masa Tuwan farar shinkafa da miyar Agusi data gaji da haduwa se kamshi take tace
"Yar rigima kam ai ni naga tsiya jiya kina gani fa qememe taqi sakin Dr Maryam wai zata gudu ta barta ja'ira" nan suka shiga hira akan Little shidai bece musu qala ba harya fara cin abincinsa. Ganin da Ammi tayi baze tanka ba ta kuma san halinsa sarai yasa tace
"Tana gidansu Takwararta fa, tun ranar da sukaje fa Hafsa taga hoton Hamdah shikenan se kayanta na aika mata dasu wai tana jiran Berbie din Daddy ta dawo araina nace Barbie nacan gurin Daddy ai sun miki wayo" ta qarasa maganar cikin yar dariya.

Seya dafe kansa da hannu daya, lallai akace wata damuwar me kore wata. Shi wallahi Sam ya manta daya baro wata Mata a London kuma yanzu Ni'ima da larurarta kawai ce a gabansa. Allah sarki ashe haka ya manta da Ni'iman lokacin da giyar Hamdah ke kwasarsa lallai da akace adalci tsakanin mata akwai wahala, a haka wasu suke iya aje hudu harma da side chicks a waje?? Se ya miqe yana goge hannunsa da handkee bayan ya wanke yace
"Am bari naje gida nayi wanka se na dawo" yana kallon agogon hannunsa lokacin karfe 8 harta gota.
"Ai kayi zamanka kawai Babana ka huce gajiyar hanya in Allah yakaimu gobe se ka dawo" Umma ta fada cike da kulawa. Seya girgiza kai Alamar Aa yana cewa
"No Umma zanje na dawo ku ya kamata ku tafi gida, its my responsibility to take care of her dan haka daga yau na karbi ragamar kula da Ni'ima, zan nema mata lafiya da karfina da kudina at any cost, ina tunanin chanza mata asibiti nema dan gaba daya wannan Isan besan me yakeyi ba naga alama idan Idris ya dawo dani se ku tafi ku hada kayanku kawai" yayi gaba abinsa. A motar da Aminullahi yazo suka tafi dan Fahad ya dade da tafiya, se alokacin ya zaro wayarsa daga aljihun rigarsa ya kunnata. Tunaninta fal a zuciyarsa ya take me takeyi yanzu? Tama ci abinci kuwa dan ya lura kwana biyu tana wasa da cin abinci se ya shiga kiran layinta bayan ya chanza sim dinsa zuwa na Nigeria sedai har wayar ta qaraci ringing dinta ta katse ba'a amsa ba. Haka yacigaba da kira seda ya mata kusan 10 missed calls amma ba'a daga ba dole ya haqura ya dena kira.

A gidan ma wanka kawai yayi ya chanza kayansa tareda daukar duk abinda yasan ze buqata ya koma Asibitin, gardama ce ta sarqe tsakanin Ammi da Umma akan wa ze zauna da ita dukda yace musu duk su tafi shi kadai ya isa amma su ka qi a dole wai se daya ta zauna. Dakyar ya lallabasu akan su ringayin kwana daidai sannan aka samu Umma ta tafi dakyar dan tafi Ammi jigata kuma ita kanta ba isashshiyar lafiyar ce da ita ba qarfin hali kawai takeyi. Haka suka kwana cikinsu babu wanda ya runtsa daga shi har Ammi, kewar Hamdah yake yanda be taba tsammanin zeyi ba. A cikin wata ukun nan basu taba raba shimfida ba da tsiya da bala'i a gado daya suke kwana gashi yaj bama gida daya ba qasa daban daban zasu kwana. Sallah suka ringa jetawa shida Ammi da addu'ar nemawa Ni'ima sauqi ga zuciyarsa data karkata da son sanin halin da Hamdah take ciki amma ba dama, haka ya haqura badan ya so ba da niyyar da safe ze nemi hanyar samunta be sani ba ko wata sabuwar hanyar ta bullo da ita ta yanke communication tsakaninsu. Da wannan tunanin ya samu bacci ya daukeshi dakyar bayan yayi sallar Asuba dukda ko kusa bana dadi bane ba.

LONDON

Tun bayan data sheqa duniyar bacci ba ita ta farka ba se qarfe 1 harda rabi na rana, as usual kamar yarinyar goye haka ta tashi da kuka ga uban yunwar datakeji kaman an mata sata a ciki. Tafi minti goma tana kukan wanda se daga baya zuciyar ta tuna mata da wanda zatayi wa shagwabar bayanan dole ta shafawa kanta lafiya ta miqe dakyar saboda yanda jiri ke neman kada ita tana dafa bango ta shiga kitchen din. Ruwa ta jona a heater sannan ta zuba madara da milo a Mug tana jira ruwan ya tafasa seta Jingina da freezer tana maida numfashi, kamshin tafasar ruwan ne ya fara tashi shaf ta manta da Abdul'ahad ya zuba kayan kamshin Tea a ciki jiya da daddare da ze dafa Tea nan da nan cikinta ya shiga hautsinawa kafin kace kwabo ta fara sheqa Amai. Babu komai a cikinta se ruwan data sha haka ta Amayar dashi tsaf a galabaice ta zauna kan dandanyar marbles din kitchen din tana mayar da numfashi kaman wadda tayi tsere. Ji tayi yunwar ta qaru, se yanzu ta gane ashe wargima guri yake samu da ace yana nan da yanzu ta langwabe tana masa tabara komai sedai ya mata yanzu kuwa ko mutuwa zatayi sedai in ta rube aji wari azo a fitar da gawarta, seta miqe dakyar kanta na wani irin sarawa ta tara mug din a famfo kamar tsohuwar mayunwaciya haka ta kwankwade Tea din da ruwan sanyi, be mata ba seda ta hara Mug uku sannan taji dan dama dama shima bawai ta qoshi bane. Kunun tsamiya ne kawai a ranta amma ina zata same shi? Dakinta ta shiga tayi Alwala ta gabatar da sallar Azahar a daddafe saboda zazzabin da taji yana neman rufeta wanda take tunanin yunwa ce ta ja mata shi. Dolenta ta daure ta soya chips dataji tana dan son ci dukda kafin ta gama tayi Amai sau biyu sannan ta yi warming ragowan kazar jiya ta hada tas kuwa ta cinyesu ta kora da Lemo me dan karan sanyi sega zufa na keto mata ta ko ina.

Wanka tayi gaba daya se takejin gidan ya mata girma da babu shi, ta kalli agogo yafi sau nawa tana jiran lokacin dawowarsa wata zuciyar tace mata "Nigeria fa ya tafi gurin matarsa, kilan ma ke ya gama da babin rayuwarki ya miki wayo kedashi kuma se ranar hisabi" se kawai ta saka kuka, kukan Kishi zallah yanzu yana can tareda matarsa ta sunna kila ya manta ya taba sanin wata Hamdah a rayuwa. Haka ta wuni tana aikin kuka har seda zazzabi ya kwanatar da ita sannan ta sararawa kanta. Tana yin Sallar ta bingire a gurin ta shiga sabuwar sana'ar data yankarwa tikiti wato bacci. Duk kiran daya ringa yi mata tana can duniyar bacci me cike da mafarkan sa masu dan karan dadi bata san yana yi ba.

Akace sabo turken wawa, wannan daren daga shi har ita babu wanda yai baccin dadi musamman Hamdah da jikin Abdul'ahad ya riga ya zamar mata katifa taimakonta daya baccin daya sameta me dan karan nauyi shi ya taimaka mata gurin janye mata duk wata kewa da tunaninsa. Asubar fari ta farka da Yunwa kaman ta shekara bata ci ba, babu zancen zabe abinda ta fara cin karo dashi a kitchen shi taci, bread zalla babu batun kayan hadi ta ringa qasuma kota rufawa kanta asiri jin yunwa na neman ajalinta. Seda taci guda biyu ta kwankwade ruwa kaduwar gora me sanyi sannan taji dama dama. Mamakin kanta ne ya kamata, wannan uban cin abincin da take bana lafiya ba ita da ada abinci ma be wani dameta ba amma yanzu ci take kaman Gara data ci data farajin yunwa, kafadunta biyu ta daga alamar oho koma dai mene lafiya ce ta kawo hakan dan in bata da lafiya bazata ci ba. Tsaki tayi lokacin data shiga wanka ta kalli kanta, tayi qiba, bata buqatar wani ya gaya mata ba qibar ce abar damuwarta ba Tumbin dataga kaman ta farayi shine matsalar. Ta tsani tumbi sam dole ta fara watching cin abincinta "bari dana tashi daga school yau Asibiti zani a prescribing mun maganin de worming dan da alama worms sun taru a cikina su suke tayani cin abincin nan" da wannan tunanin tayi wanka ta shirya dakyar ta samu kayan daya mata daidai dan ita dinkuna daidai jikinta ake mata, yanzu kuma gashi ta fara fin qarfinsu dan haka ta zura abaya plain black me laushi tayi rolling da mayafinta, lokacin data kalli kanta a mirror ita kanta seda ta qara bude ido sosai tana kallon kanta. Wani mugun Haske taga tayi kamar Albino seta hau shafa fuskarta wai ko wani abun ta goga bata sani ba. Ganin zata bata ma kanta lokaci yasa ta haqura ta fita, mukullin motarsa daya bar mata ta dauka tana tafiya gaba daya take jin jikinta so empty dakyar ma take tuqin motar harta qarasa school.

Da Umm-Ashrab ta fara cin karo ai kuwa ta shiga tsokanarta wai "Amarya Amarya kodai sun kusa samun Baby ne" kunya kamar ta nutse tun ba yanda course mates dinta suka shiga congratulating nata ba wasu na qorafin meyasa bata gaya musu zatayi aure ba. Ko a class bata barta ta huta ba, Aliya itama course dinsu daya kuma yar Nigeria ce aiki yakai Mijinta London suke zaune acan, suna shiri sosai da Hamdah saboda tana da kirki sosai tace

"Wallahi Anty Hamdah nidai shiru nayi tunda baki fadamin kinyi aure ba amma tun kwanaki na fara suspecting ciki ne dake in ma baki sani ba to ki fara lissafi kawai dan wlh kin zama Mummy" se Grape juice din da take sha ya maqale mata a maqoshi ya kwareta tsabar kidima nan ta shiga tari baji ba gani.





🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 4⃣5⃣



Ruwa Aliya ta miqa mata suka shiga yi mata sannu, seda tarin ya lafa sannan ta dago fuskarta da kallo daya zaka mata ka hango tsoro a cikinta tana kallon Aliya data dage tana zayyano mata changes din data gani a tattare da ita.
"Ke ko daga wannan dashewar da kikayi ai kyayi zargin wani abu na lura Anty Hamdah kema u are careless about ur health, ai ni ko qurji na gani a fuskata sena je an dubamin na menene bare har in samu ciki in kasa gane wa in baki yarda ba in mun fita mu biya pharmacy din can na siya miki Pt strip kije gida ki gwada zaki bani good news". Wasu miyau ta hadiye dakyar, ta na gyadawa Aliya kai Alamar ta yarda. Lecture ranar kaf ba abinda ta tsinta dan a zaryar toilet ta cinye lokacin ta saboda Kamshin turaren mutane dayawa daya cakude a class din gaba daya ya hana mata sukuni. Karfe biyu suka fito, yunwa take ji sosai dan haka suka fara tsayawa Cafeteria zata ci abinci. Kanta akan table din ta rasa me yake mata dadi a duniyar gaba daya, tunda aka ajiye mata pepper soup din kayan cikin da tayi order ta kasa koda kallon sa bare taci.

"Ko akwai wani abu da kike so ne se muje gida na girka miki" cewar Aliya da take kallonta da tausayi, ta fuskanci laulayin nata me zafi ne dukda Hamdah ta qi admitting cewa cikin ne da ita, Danwake ne ya fado mata a rai seta daga kai dakyar tace mata
"Kina da kayan yin Danwake?"

"Abu ya tabbata muje ina dashi duk wanda kike so na flour ko garin rogo duk an aikomin dasu" Aliya tayi maganar cikin tsokana. Gidanta bashida nisa daga makarantar ita se suka shiga motar Hamdah suka qarasa. Tana kwance ta gama hada mata danwaken daya sha yajin tafarnuwa da Vegetables, ta kuwa sake sosai taci harda qari qarshema ta juye mata ragowar ta tafi dashi gida. A hanya ta tsaya ta siyi PT strip din zuciyarta nata taraddadin me zata tarar, seta kasa komawa gidan ma dan gurin ya mata shiru da yawa daga ita se halinta kaman mayya haka taringa yawo a gari har seda akayi magriba sannan ta shiga gidan.

Wanka ta farayi tayi sallah sannan ta qara cin danwakenta ta kora da Banana Juice me shegen sanyi, bata haqura ba seda ta sha yoghurt roba guda sannan tajita dam, robar strip din ta dakko daga jakarta ta zari guda daya ta shiga toilet, fitsari tayi, da Bismillah ta saka abin gwajin ta nemi gefen bath ta zauna tana karanto duk addu'ar data zo bakinta.

Tafi minti goma sha biyar a zaune ta kasa koda kallon in da abin yake tsabar tsoron me zata gani har wasu yan hawaye takeyi, ganin babu madogara ya sakata rufe ido tareda Bismillah ta daga strip din kafin ta fara bude idanunta a hankali tana kwararo addu'a a cikin zuciyarta.

A farko ta zata gizo idonta ya mata saboda ba sosai take gani ba seta ga layin ya rabu gida uku, qarasa bude idonta tayi gaba daya dan ta tabbatar gizon ne kodai daya ne ya rabu uku ai ba shiri ta cillar da abin cikin matuqar kidima ta dafe qirji ta ma rasa abinda zatayi. Se kawai ta fice daga toilet din hankali tashe ta dakko robar gaba daya ta koma cikin toilet din.

Ta gwada sunyi guda goma amma abu daya take gani, seta sulale a qasan tiles din lokaci daya ta fashe da wani irin kuka,

"Na shiga uku ni Hamdah, CIKI, cikin ma na SHEGE shikenan na banu na lalace" kuka take tamkar ranta ze fita. Tunda take a duniya bata taba shiga tashin hankali irin na yau ba kai ko lokacin data ga gawar Abdulmalik albarka. Tausayin kanta dana dan cikin takeyi ita yanzu ya zatayi? Ya cuceta ya kuma kaita ya baro yanzu ya za'ayi ma ya karbi cikin nan ai tasan ko giyar wake tasha ma bazata liqa masa ba dan tasan ba karba zeyi ba.

"Allah ya isa tsakanina dakai Abdul'ahad ka cuceni kaci amanar qauna wallahi bazan taba yafe maka ba har kuwa a gaban Allah" magana take cikin fitar hankali, seta miqe tsam kamar wadda aka cikara, wayarta ta shiga nema a cikin dakin Allah ya taimaka ta hangota kan mirror ta kuwa yi saurin rarumarta. Number sa take nema akan wayar tana gunjin kuka bata ko ganin contacts din sosai, tsabar yanda ta rude bata ko lura da ubannin missed calls din dake akan wayar ba sedai sama ko qasa ta rasa Number Abdul'ahad ta Nigeria, cilli tayi da wayar ta zauna ta ci gaba da rera kukan da bata da me lallashinta tana qara jera masa Allah ya isa da duk baqin fatan daya zo bakinta batayi shiru ba har seda bacci barawo ya saceta akan Dandaryar Tiles tukunna tayi shiru.

NIGERIA

Dr Abdul'ahad ya farka cike da damuwar da suka taru suka hanashi sukuni, na farko jikin Niida ba wani ci gaba har yanzu ga kuma Anty Hamdah da ya kasa samun wayarta har yanzu, daya daga cikin securities din estate din su ya kira ya kuma tabbatar masa da ta fita da safe sannan ya dan samu relief ya tabbatar lafiyar ta qalau hali ne kawai ya motsa. A Asibitin ya wuni se bayan magrib ya koma gida yayi wanka saboda yana so yaje ya gaida Mumiya kuma gano little. Karfe 8pm tayi masa kofar gidan Prof Ammani. Yayi kyau har ya gaji cikin yadin filtex daya saka me kalan Maroon da akayiwa dinki me gajeran hannu ya murza hularsa ta zauna daram akansa. Kafafunsa sanye da baqin takalmi daya rufe dukka qafarsa se agogon danyar azurfa daure a hannunsa na hagu.

Kallon gidan yake da wani irin expression akan fuskarsa bayan daya parker motar sa a bakin gate saboda Sa'idu daya tarar yana Sallah a kofar gidan. "They give me life" ya fada a hankali yanda shi kadai yaji me yace, kofar gidan nada tarihi da yawa a rayuwarsa tundaga shekaru 6 da suka wuce zuwa watanni biyar baya da gidan ya kafa babban tarihi a rayuwarsa. Ranar da Dubban Jama'a suka shaida Daurin auransa shi Abdul'ahad da Hamdah Ammani. Wannan rana tana da girman da bazata taba shafewa a babin rayuwarsa ba. Yana fatan ko a lahira yanemi alfarmar a qara haska masa wannan rana ya ganta sosai yaga irin murnar nar da take akan fuskarsa a lokacin. Wanda ya gani a video da pictures bata isheshi ba yana so ya qara gani sosai cikin camerar data fi kowacce kyan dauka.

"Barka da zuwa Dr" muryar Sa'idu ta katse masa tunani, se ya daga kai yana murmushi. Sa'idun na daga cikin mutanen da suka taka rawa gurin samar masa farin cikin a rayuwa shi yasa yake matuqar ganin kimarsa. Hannu ya miqa masa lokacin da yake qoqarin durqusawa ya gaishe shi yace
"Sau nawa zan gaya maka ka dena bana son wannan abun musabaha zamuyi tafi kowacce gaisuwa da zakamin"
"Tuba nake yallabai" Sa'idu ya fada a ransa yana jinjina sauqin kai irin na Abdul'ahad. Seya dora da cewa

"Bari na bude maka gate ka shiga da motar"

"Aa ka barshi kawai ai ba jimawa zanyi ba, Abba yana ciki kuwa?"

"Eh yana nan ai yau ma ya dawo daga Abuja dukkan su ma yan gidan kowa yana nan har Antu Zahra tazo mutuniyar ce kawai ka boye mana ita a qasar turai kasan gobe za'a kawo kudin auran Hamida da sa rana" ya bashi amsa, se ya gyada masa kai kawai tareda miqa masa key din mota yace ya kwaso kayan da suke a boot shi kuma ya shiga ciki.

Da Farouk suka fara cin karo da yake kunna mota alamar fita zeyi ya dakata tareda bashi hannu suka gaisa, shi ya masa iso cikin gidan Har palour Abba na sama dan yana can shida Yah Abubakar da Yah Baffa se Uncle Sani qaninsa suna Magana. Tamkar Da da Uba haka suka gaisa yana tambayarsa me jiki haka sauran ma duk suka gaisa sosai. Baffa ne yadan zungureshi kasa kasa yace
"Mutumin se ka qaro sadaki dama mena gaya maka qanwata pro ce wallahi yanzu ka tabbatar kenan" ya qarasa yana masa dariyar shaqiyanci, shi dai kasa cewa komai yayi saboda Abba da Uncle Sani da suke gurin. Ganin da Abba yayi sun gama maganar da suke yasa yayi excusing nasu shida Uncle Sani suka fita nan kuwa Baffa ya tasa shi gaba ya zage shima sosai yana ramawa harda cewa badan Yah Abubakar surukinsa bane da yanzu ya baro masa aiki tunda yaga shi babban kwabo ne. Yah Abubakar da keta dariya yace
"Wani ba ruwana, kuyi abunku nisa ta masa shi yasa yake mata dan biki amma bari kayi maganinsa kawai bari zakayi se liqin ya balle ku raba rigimar kawai duk randa ta diro gidannan akwai kallo kuma wallahi kawai kace Baffa ne ya baka ita sadaka ka koma gefe kasha kallon ikon Allah".

"Kai amma Yaya bansan fulatanci na yawo a jikinka ba se yanzu wannan yar dabar zaka hado ni da ita ai na kade har ganyena wallahi" . Dariya suka saka gaba dayansu, sallamar Hamida ce ta katse su data kawo masa try cikeda kayan motsa baki dangin snacks da Dambun Nama. Sannu ya mata da godiya bayan sun gaisa yana tsokanarta wai Amaryar Pilot tana sunkuyar dakai.

"Daddyyyyyyy, Amya, Afya come and see my Daddy he is here" kafin yayi wani yunquri tuni tayi tsalle ta dane shi har tana tunkude cup din daya cika da lemu ze sha, se ya rungumeta wata qauna da tausayinta suna ratsa shi lokaci daya. Little tayi kyau ta qara qirma da wayo kamar ba yar shekara uku ba, tayi kyau sosai cikin doguwar rigar da aka mata dinkin yan kanti amma da atamfa iri daya data jikin Amrah da Afra da suka tsaya suna ta masa murmushi. Se ya miqa musu hannu dukka su biyun suka shiga jikinsa ya rungumesu a zuciyarsa yana cewa "Allah kasa nima Hamdah ta haifar min twins mata masu kama da ita haka. Gayya Little ta ringayo masa ta yaran da suke gidan su zo suga Dadynta, seda Yah Baffa ya musu jan ido sannan suka rabu dashi shi kam babu ruwanshi nishadi yake dan Allah ya dora masa son yara dayawa.

Kayan daya zo dasu dama duk tarkacen yara ne na ci dana wasa se turaruka ya bawa Hamida yace takaiwa Mumcy in taso ko daya ne ta bata. Ya dade sosai a gidan har besan lokaci ya tafi ba seda ya kalli agogo yaga shadaya harta gota.

"Subhanallah amma ashe dare yayi haka ban sani ba" ya fada yana miqewa,
"Ai na zata kwana zakayi har nasa an share maka tsohon dakin matarka ka kwanta acan" cewar Baffa yana miqewa shima dan tafiya gida tuni dama Yah Abubakar ya tafi saboda shi gidan sa nada dan nisa daga nan din. Tare suka sakko a babban palour suka hadu da Mumcy da shigowarta kenan daga asibiti kana kallonta kasan ta gaji, har qasa ya durqusa yana gaida ita, yana matuqar kunyarta da ganin girmanta, ta zamar masa uwa, ta bashi mata, ta riqe masa Ya sannan ta tsaya akan rashin lafiyar matarsa. Sallama ya mata tana tsokanarsa wai baze tafi da Little ba yace Aa ai tayi sababbin yan uwa tunda Baffa ya koresu dazu be qara ko jin duriyarta ba da haka sukayi sallama.

Yana tafe a motarsa yan qara gwada numberta amma taqi shiga, tsaki yayi abun nata kuma ya fara zama da rainin hankali kenan daga a kira bazata daga ba se ta kashe waya? Haka ya cigaba da tuqi duk zuciyarsa babu dadi har ya qarasa asibitin nan ya tararda abinda ya mugun daga masa hankali. Ni'ima ta farka ba a lokacin da ake so ta farka dinba. Sanda ya isa likitoci hudu ne akanta saboda yanda jikinta yake rawa kamar wadda aka jonawa shocking ga kuma jiki dake zuba daga guraren da ta fizge alluran jikinta. Ammi kuka Ummanta kuka haka ya tarar dasu babu me rarrashin wani, dakyar aka mata allurar bacci itama seda ta dauki lokaci kafin tayi tasiri akanta. Seda Nurses suka gyara mata jikinta sannan suka barshi ya shiga, unlike dazu daya fita yanzu ta kumbura kaman wadda aka hurawa iska fatarta har qyalli takeyi, sekawai ya zauna yai tagumi da hannaye biyu yana sauraron Dr Isah dake karanta masa shirme a cewarsa.

"Abdul'ahad duk wata dabarar mu ta qare akan matarka inaga zamu chanza mata daki mu maidata Amenity kawai kaga nan ba koda yaushe ake barin mutane shiga ba can kuwa za'a zauna tareda ita a jira yanda Allah zeyi"

"Are you done?" Ya tambayi Isah ba tare da ya dago kansa ba,
"Eh amma...."
"Get out kaje ka shirya mana takaddun sallama"

"Amma Abdul'ahad a yanda take babu Asibitin da zasu karbe ku in ma qasar kace zaka bari da ita zata qara wahala ne kawai" Dr Isah yayi maganar cikin yanayin tausayin Abdul'ahad din. Yasani sarai Ni'ima bazata tashi ba amma yaqi bari zuciyarsa ta yarda da hakan

"Babu ruwanka just do as i say" ya bashi amsa cikin isa da iko.

"An gama amma bani kadai ke handling case nata ba, Dr Gadanya ke kula da Kidney case dinta, na kuma Heart problem din akwai Dr Muhsina ita ce in charge of Cancer case din kuma bata nan, abinda yayi delaying chemotherapy din kenan ma so dole se dukkan su sun bata sallama tukunna".

"Idan kuma na dauketa na tafi se naga uban da ze cemin dan me, malam in zakaje kayi abinda nace maka kawai kayi Matar tawa kaza ce da zaa ringa jagwalgwalata haka ko yay har wasu likitoci hudu ne akanta ita kadai to Allah tsinewa duk wanda be bata sallama ba" yanda yake maganar

Please Login or Register in order to submit comment