Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta koma daya hannun ta hau mota sanin qasa ce me doka da tsari ba kamar inda ta baro ba yasa cikin kwanciyar hankali ta fara taka titin bayan da danger ta tsayar da dukka masu ababen hawa ta kuma bawa masu tafiyar qafa damar tsallakawa sedai yanda ya shararo mota kamar ze bi takanta ne ya matukar bata tsoro har bata san sanda ta watsar da kayan hannunta gaba daya ba tsabar diricewa seta tsugunna akan titin. Wani abin haushi abin takaici kwata kwata ashema ba akan hannun sa take bane a daya tsallaken motar take, seta bi bayan motar data wuce kamar walqiya da kallo kunya da takaici suka cikata ganin yanda aka baibayeta ana mata sannu da tambayar bata dai ji ciwo ba ko, ita dai tunda ta samu aka hade mata kayanta suka tare mata Taxi ta shige tayi gaba tana kara Allah wadai da Halin koma waye daya tsorata ta da gani wannan duk inda ya fito Dan Nigeria ne dan su kadai suka saba da irin wannan bala'in gudu babu gurin zuwa din haka tayi ta mita har me Taxi ya sauketa a kofar Estate dinsu ta bashi kudinsa sannan ta kwashi kayan ta shiga ciki.

Tana qoqarin bude kofar plat dinta idanunta suka sauka akan motar dazu cikin parking lot dinsu kamar yanda komai na Estate din yake a tsare gidaje hudu ne a kowanne rukuni haka kowanne mutum an tanadar masa gurin ajiye mota guda daya yanda kowanne gida yake da Number Haka parking lot din ma yake kowa da nasa.
A 'No 506' a kayi parking motar ma'ana ta maocinta ce da akace yafi shekara biyu be zoba seta tabe baki kawai aranta tace "Kowa da halinsa ze zauna" ta kwashe kayanta tsaf ta shiga dasu.
Wanka ta farayi dan ta gaji sosai sannan tayi Sallar Azahar ganin lokaci yayi, tana dab da dora girki ne Zulaihat ta shigo hannunta dauke da Coler abinci se kuma Leda qarama da batasan ko menene a ciki ba. Da murmushi ta tareta ta hutar da ita girki, haka suke duk wadda tayi abinci tana bawa kowa a cikin su ukun tun tana baya baya dasu harta haqura ta saki jiki dan Su biyu kusan shekararsu Hudu a tare ita ce zuwan kwanan nan, zama zulaiha tayi tana mata sannu bayan ta mika mata abincin tayi mata godiya ta fara ci tana wa Zulaiha tsiyar girkinta Yaji gashinan har ta koyawa Umm Ashrab kaman yanda suke kiran Darussalam ita ma tana cika yaji a abinci.

Ledar data shigo da ita ta mika mata tana cewa "Gashi Neighbor dinki ne ya dawo dazu ya kawo mana tsaraba nasan besan akwai new tenant ba shi yasa na raba nawa biyu na kawo miki kene me son Perfumes sosai" . da murnarta ta karbi ledar me tambarin Alharamain ta shiga fito da turarukan ciki, guda ukune kwalabe yan mitsi mitsi amma duk wanda yasan darajar turare yagansu yasan masu daraja ne. Dagowa tayi ta kalli Zulaiha kafin tace
"Amma dai wannan neighbor da kirki yake na kuma gode sosai kuma wallahi kaman kinsan na dade ina neman wannan turaren" tayi maganar tana shanshana kwalbar hannunta, sedai ta kasa tantance turaren ciki ne yake qanshin ko kuma ledar da aka sako su ce. Ita dai ko a lahira tana tunanin zata shaida wannan Kamshin dan a gurin mutum daya take jinsa amma yau gashi a wani guri daban, seta mayar dasu ciki ta qarasa cin abincinta sannan ta zura dogon Hijabi akan Armless gown din jikinta suka fita tareda Zulaiha dan su je plat din Mum Ashrab su qarasa shirin birthday celebration din da za'ayi da daddare.
****************************
Kamar kidan ganga haka zuciyarta ta shiga bugawa ga hannunta daya gagara tsayawa guri daya tsabar rawar da yake har seda Zulaiha ta lura ta karbi key din data kasa rufe kofar dashi ta rufe. Duk kalma daya dayake fada a zuciyarta da kwakwalwarta take sauka tana qoqarin qaryata kanta akan cewa bashi bane ba dan haka ta dauke kanta dan ma karta kalli me maganar ko ba komai bata so tsohon mikin data kwantar ya qara taso mata. Ta gefensa suka wuce, dogon mutum me cikakkiyar sura ta mazantaka ya juya baya dan haka bata ga fuskarsa ba tayi saurin fadawa gidan Umm Ashrab kamar wadda aka biyo tana mayar da Numfashi.





🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 3⃣8⃣


Kallonta Zulaiha da Umm Ashrab suka shigayi tareda tambayarta abinda ya faru, bata amsa musu ba se ma gefen kujera data samu ta ta zauna tareda Lumshe idanunta tana kokarin saita bugun zuciyarta. Ta kusan minti biyar a haka mamaki da tsoro duk ya cika su to meya sameta haka? Bude idanunta tayi ta kalli yanda suka tsatstsaya akanat se tayi dan murmushi tana gyara zamanta tace

"Hey relax its nothing serious i was just a little bit panic ne but I'm good now". A kusan tare Umm Ashrab da Zulaiha suka sauke ajiyar zuciya kafin kowacce ta nemi guri ita ma ta zauna. Tsare tsaren party suka shigayi dukda rabin hankalin Hamdah yana kan wanacan mutumin na waje lokaci lokaci tana kallon kofa kamar ance mata ze shigo gidan harseda Umm Asharb ta lura ta tambayeta ko tana expecting zuwan wani ne, kai ta girgiza mata alamar Aa, suna gamawa ta mike jiki ba kwari tace kanta na dan yi mata ciwo zataje ta kwanta kafin Magrib seta dawo.

Lokacin data fito shima ya fito kenan daga plat dinsa, ba kaman dazun da yake sanye da Three quarter da Armless shirt ba yanzu Suit ce a jikinsa me kalan Blue se Inner daya saka fara qal ya riqe jacket din a hannunsa be saka ba, waya ce a hannunsa yake daddannawa da alaman wani ze kira ko wani abu yake nema. Babu gashi sosai a fuskarsa yanzu hatta da gemun da yake ajiyewa ya rageshi sosai se kadan hakan ya qarawa fuskarsa wani kyau da Haske na musamman. Ta kasa hana kanta kallonsa, wani irin shauqi ke dibanta zuwa gareshi, qamshin turarensa da bazata manta ba abinda ya fara ribatar zuciyarta zuwa gareshi ya cika gaba daya atmosphere din ya hade da daddadar iskar dake kadawa a gurin suka bada wani yanayi me dadi.

Batasan iyakar Lokacin data dauka a tsaye tana kallonsa ba kuma har lokacin kansa yana kan wayar be dago ba balle yasan da tsayuwarta a gun.
"I'm on my way" sautin muryarsa ta doki kunnenta a karo na biyu, tabbas ba Kama bace wannan _ABDUL'AHAD ALIYU GALADIMA_ kamar wata yarinya haka ta kwasa da gudu ta isa kofarta har key din na faduwa saboda saurin da takeyi ta bude se a lokacin ya daga kansa ya kalli Direction din data bi, da karamin murmushi ya rakata kafin ya qarasa ya bude motarsa ya kunna yana ci gaba da kallon yanda take kiciniyar bude kofar, kamar dazun a tsiyace ya figi motar ya fice tayi saurin waiwayawa tana kallonsa a ranta tana mamakin sautawar dabi'un nasa, to kodai be gane ta bane ko kuma dai wani ne daban kaman yanda zuciyarta tafi yarda bashi din bane.

Duk yanda taso tayi baccin kasawa tayi haka har magribar tana kwance tana juyi akan gado. Seda aka kira sallah sannan ta tashi dan gyare gyare ta shigayi saboda tana fashin sallah dukda babu abinda gidan yayi, two bedroom plat ne se toilet da bathroom se kuma kitchen section da yake gefe a cikin palour hade sa qaramin Dining dinta. Daki taya ta saka gado dayan kuma ta barshi matsayin study room tunda ita kadai take rayuwarta daki daya ya isheta. Duk wani abun buqata tana dashi a cikin gidan ta qawatashi to her taste saboda yanzun ta koma asalin Hamdah ta yar kwalisa shiyasa dole gidan ya birgek idan ka shiga.

Wanka tayi bayan data gama yan ayyukan ta shirya cikin wata black simple gown babu adon komai a jikinta se colar da ayi mata se hannun da ya dan matse daga qarshensa. Loko da saqo na jikinta tabi ta feshe da turaruka sannan ta yafa baqin Veil mara nauyi akanta ta zula slippers a kafafunta sannan ta dauki wayarta da gift din Asharba da tayi rapping a babban rapping sheet ta fita daga gidan.

Sannu sannu take tafiya kamar me tausayin kasa tana jin kamar iskar da ake danyi zata dauketa saboda yanda takejin jikinta babu nauyi sam, cikin tsautsayi iska ta dauke mata dan mayafin data rufe kanta tabarta tsurarta se tulin uban gashinta data tattare a tsakiyar kai.

Bin Mayafin dake yawo a iska tayi da kallo kaman zata saka kuka waima ta ina zata fara kamo shi se kawai gani tayi ya sauka akan fuskar mutumin da bataga tahowarsa ba se kawai ganinsa tayi a kusa da ita.

_Abdul'ahad_ Pov
Tunda ya faka motarsa yake zaune a cikinta, ya gaji liqis saboda conference din dayaje akan wani case study da zasu fara anan Imperial Collage akan wata sabuwar cuta datake shirin bullowa. Yana kallon lokacin data fito daga cikin gidanta, shigarta da yanayin tafiyarta yana qara mutar dashi a cikin soyayyarta. Tunda yake a rayuwarsa be taba samun nutsuwa irin ta wannan karonba, ya godewa Allah ya kuma gode masa. Yayi Sallah yayi Azumi ya kuma bada sadakoki duk akan irin wannan baiwar da Allah yayi masa. Tabbas ya yarda da maganar da akace ba'a yanke qauna da rahmar Allah kuma hanyoyin Allah yawa ne dasu haka nan bawa besan lokacin da ake karbar addu'arsa ba. Yana kallon sanda mayafin nata ya yaye yayi saurin fitowa daga motar saboda gurin tarwai yake kamar rana. Duplex din gefensu kusan duka mazane baya fatan wani ya fito idonsa ya kai kan gashinta har ya kalleta sema ya farajin haushin meyasa bata daka koda qaramin Hijab bane yanda iska bazata cire ba?

Mayafin ya riqe da hannunsa lokacin daya sauka a fuskarsa yana shaqar daddadan qamshin dayake fitarwa, sannu a hankali ya qarasa inda take tsaye kamar wadda ta taka Glue Gum ta maqale. Idan beyi qarya ba seyaci yaji yanda zuciyarya take bugawa kamar ana kidan mandiri har abin ma yaso bashi dariya seya gimtse ya shiga Zagaya mata mayafin akanta ya zauna sosai akaman yanda yaga tanayi a shekarun baya da kuma yanda yake taya Ni'ima a yawancin lokuta idanunsa akan farar fuskarta da babu dugon kwalliya ko kasan a kai se dogon hancinta da wadannan lips din masu juya masa tunani.

_Hamdah_
Kamar mazari haka zuciyarta da jikinta suka ringa rawa lokacin daya kusantota sema taji kaman numfashinta ze dauke saboa yanda kamshinsa ya cika mata hanci ga numfashinsa da takeji yana sauka har akan fuskarta. Yana gama daure mata Veil din tayi gaba kamar iska har bata san sanda agogonta da be gama dauruwa ba ya fadi tayi saurin fadawa plat din Umm Ashrab dayake kofar a bude take saboda baqin da suka gayyato.

Palour ya cika da friends din Asharb da parents dinsu da suka kawo su se few of their course mates da Darussalam din ta gayyato nan da nan ta ware suka shiga gaisawa da mutane duk a qoqarin cire tunaninsa daga zuciyarta. Party yayi party yara sun cashe sosai haka Hamdah ta shiga tsakiyarsu suka dinga tiqar rawa dama ita ba baya bace a wannan bangaren karma taji sabgar yara shiga ciki takeyi suyi kamar sa'arsu se gurin 11pm aka fara watsewa suka shiga tattara tulin gifts din da Ashrab din ya samu basu fita daga gidan ba se after 12am.
Ita da zulaiha suka fito suna yar hira, ta ninke veil din ta daurashi akanta kamar dankwali tsabar gajiya takalmin ma a hannu ta riqosu dukda slippers ne.

Yana zaune a kofar plat dinsa kan resting chair ya mike dogayen kafafunsa gefe ya ajiye dan karamin stool da system akai, hannunsa biyu a hade a karkashin habarsa ya zubawa kofar Umm Ashrab ido tundazu mutanen da suke fitowa akan idonsa suke yana jira yaga sanda zata fito. Saurin dauke idonsa yayi tare da gyara Zama lokacin daya hangosu, se yaga ta qara masa wani kyau na musamman and she looks younger.

Gaisawa suka shigayi da Zulaiha sanda suka zo gifta shi Hamdah kam tura baki tayi gaba bayan data harareshi ta gefen ido duk akan idonsa se kawai yayi murmushin da iyakansa lips sukayi sallama da Zulaiha suka wuce. Tattara kayansa ya shigayi dan dama abinda ya zaunar dashi kenan ya shige gida sedai ko kadan ya gagara bacci. Wani irin abu yakeji da bai taba jin irinsa ba, urges na sexual desire suka taso masa lokaci daya mararsa ta shiga wani irin ciwo. Dakyar ya sakko daga kan gadonsa zufa na keto masa ta ko ina ya shiga neman wayarsa, Master ya kira shine suke kusa kusa kuma kasancewarsa likita murya a shaqe ya masa bayanin yanda yakeji sannan ya ajiye wayar ya rufe idanunsa yana cije lips dinsa kaman ze fasa su.
Minti 10 a tsakani Master ya qaraso, yana da spare key din gidan shi yake lurar masa dashi lokacin da baya nan dan haka ya bude ya shiga kai tsaye.

Da sauri ya qarasa cikin dakin yana masa sannu nan da nan ya shiga bashi duk wasu taimako da suka kamata zuwa wani lokaci bacci ya daukeshi saboda Allurar dayayi masa, be bar gidanba har seda ya tabbatar da komai normal koda ace Abdul'ahad ze farka baze tashi da ciwon komai ba.
Mita yake tayi a zuciyarsa kan halin da Abdul din yake nema ya jefa kansa, ya rasa wace irin zuciya Allah ya halittoshi da ita dan tabbas da a zamanin mutanen farko Abdul'ahad yazo irinsu ne aka sha wahala dasu kafin su biyu in ba haka ba da ransa da damarsa ya zauna yana azabtar da kansa akan wani abu mara tushe, yanzu yana tunanin in ya mutu sanadin haka me ze ce wa Allah bayan ya bashi duk wasu qarfi da ikon saukewa kansa nauyin? Ture wannan yana zaton idan har wata nakasa ta same shi ta wannan dalilin ita wadda yake dominta zata haqura ta zauna dashine?
Haka yaita mita a ransa har ya ja masa kofar ya fita tareda rufe babbar kofar gaba daya.

Hajia Hamdah kuwa tana shiga gida kiran Mumcy ya shigo wayarta, agogo ta kalla tana mamakin meya faru take kiranta at this hour sedai ta daga wayar da taraddadin me zataji.
Muryar Mumcy fes suka gaisa tana tambayarta karatu, yar hira sukayi har lokacin tana jira taji ko wani abu ya faru ne.
"Yawwa Islaha tazo Nigeria kin sani ko" mumcy ta tambayeta.
"Eh na kirata jiya ban sameta ba se whatsapp mukayi magana take cemin yayar Abban su Maisar ce ta rasu ko"
"Eh wlh ai cikin week dinnan zasu dawo zan bata saqo ta kawo miki idan kuma akwai abinda kikeda buqata se ki fada ta taho miki dashi".
"Babu Mumcy mota kawai nake so na gaji da hawan motar hayan nan so stressful in emergency fita ya kamaka seka ta jiran wani taxi"
"To bari zan qullo miki motar a jaka seta kawo miki" mumcy ta fada cikin sigar gatse. Seta saka dariya tana cewa
"Oh Hajia Mumcy ikoj Allah nifa ba haka nake nufi wai dama ki tunaww Yah Baffa shi yace ze siyamin mota"

"Sannu taru ke naki kudin bana ci bane ko to baze siya ba ki fitarda kudinki gobe ki se mota kinga ni se anjima bacci nakeji gobe morning nake dashi nadai kusa Retire na huta da wannan aikin ki tabbatar duk abinda ta kawo miki kinyi amfani dashi dan da kudi na siya duk abinda baki gane ba ki kirani" da haka sukayi sallama.

Abdul'ahad be farka ba se karfe 8 harda yan mintina na safe. Da salati a bakinsa ya mike ganin yanda dakin yai tarwai da hasken rana ba shiri ya shige toilet sauri sauri yai wanka sannan ya dauro Alwala ya fito, farar jallabiyya ya saka ya tada sallah bayan ya idar kitchen ya nufa saboda yunwar dayaji ta fara damunsa. Dama can shi ba mutum bane me wasa da abinci shi yasa ma ya koyi yanda ake girki karma mace ta horashi da wannan. Coffee ya hada ya fara sha kafin ya dumama wata kaza daya siyo daren jiya be samu damar cin ta ba. Duk seyake jinsa wani iri, tunda ya dawo London siyan abinci yake dama ko a China idan Ni'ima bazata iya girki ba suna da Cook. Jiyai yana son magana da iyalinsa dukda yasan lokacin dare ne su acan amma haka ya kira wayar Ni'iman ringing biyu aka daga.

"Daddy" muryar little ta cika masa kunne, se ya gyara zama sosai akan couch yana sipping coopee dinsa nan ta shiga masa surutu ba kama kafan yaro. Allah yayiwa little dan banzan wayo da kaifin basira shiyasa take qara shiga zuciyarsa. Sunfi minti goma suna magana dukda wasu abin ba ganewa yake ba turancin nata ya hadu da tsamin bakin da take sedai yayita binta da Yes da No wani lokacin ita kuma ta dage seya gane abinda take fada har gara idan a fili ne yafi fahimtar gwarancin nata. Gajiya yayi da surutun nata yace ta bawa Momy se tace masa wai tana bacci dazu Aunt Farida tayi mata Allura.

Seya samu kansa da rashin jin dadi meya sameta kuma da be sani ba. Seyaga kaman ya tauye mata hakki da yawa ko ba komai Ni'ima matarsa ce tana da buqatar cikakkiyar kulawa daga gareshi amma ta yaya ze iya hakan bayan shi kansa bashida cikakkiyar nutsuwar zuciya?
"Nigeria kawai zan tafi" ya raya a zuciyarsa.
"Gurin wa zaka a Nugeria bayan gatanan a kusa da kai" zuciyarsa ta tambayeshi. Dafe kansa yayi da hannu biyu yana tuno irin tarin rigima da kishin daya hango a cikin kwayar idanunta.

Yasan Hamdah ba sanin yau ba baqaramar drama zasu kwasa da ita ba wannan kishin nata akan abinda take so yana nan be canzaba. A nasa bangaren ya sauke komai ya kuma yadda qaddara ta riga fata ubangiji ya rigada ya rubuta wasu mazan a rayuwarta kafin shi amma ita a gurinsa ita ce farko kuma ita ce qarshe baze qara maimaita kuskuren da yayi ba, ya gwada yakice ta daga zuciyarsa bejibda dadi ba tunda ya rigada yayi kuskuren yiwa kansa register da ita yasan har numfashinsa na qarshe baze dena son Hamdah ba no matter how no matter what. Se yai saurin miqewa kamar wanda aka tsikara ya fita wajr, jikinsa ne ya bashi ta fito karaf kuwa suka hada ido lokacin da take dauke goran ruwa daga bakinta.

Sanye take da track suit dark blue wandon me rubber a karshensa saboda yar zufar da takeyi sakamakon exercise din datayi ta cire jacket din ta daure a qugu se Armless shirt data bi fatarta sosai. Hular kanta ta zame daga gaba yana kallon yanda baqin gashinta ya kwanta luf kaman na yar baby be san ya akayi ba kawai ya ganshi a tsaye a gabanta kaman zasu hade. Nemo kalman da zeyi magana ya shigayi amma ya kasa se kawai ya bige da kwance mata rigar wai ze saka mata.

Hannunsa tayi saurin bigewa daga jikinta tana ja da baya cikin tsiwa tace" malam lafiya ka sannine ko yaya daga ganin mutane zaka zo kana tabasu".
Yanda take maganar tana turo masa baki yai bala'in qara kunnashi, kaman wawa ya riqita lokacin datake qoqarin juyawa ya hade Gap din dake tsakaninsu yavmata wani irin tight hug tamkar ze karya mata qasusuwa within seconds ko me kuma ya tuna yayi saurin sakinta ya juya ba tareda ya sake koda kallonta ba.
Kafafuwanta da sukayi sanyi ta ja ta shige gidanta kafin ta samu gefen kujera ta zauna kaman mara laka. Wani irin tasiri rungumar tayi a jikinta, ya taso mata da tsohon mikin sonsa a ranta da abubuwan da suka faru a baya. Rayuwar Yammatanci, makaranta da rabuwarsu har zuwa dawowarsa rayuwarta a yanzu.

Haka ta wuni ko kayan jikinta ta kasa cirewa saboda mayen turarensa daya kamasu da bataso ta dena shaqa, tun usul take son kamshin Abdul'ahad wata nutsuwa ta musamman yake sakamata. Sa'arta daya ranar daga Zulaiha har Mum Asharb basa Estate din kowa ta fita uzurinta dan haka ta wuni tana malelekuwarta daga kan gado ta koma kujera har akayi Sallar Isha sannan ta samu karfin yin wanka ta shirya cikin Riga da Skirt na Atamfa data matukar karbarta.
Ice cream take sha'awar sha kuma bata dashi dole se ta fita ta siyo. Karamar jakarta ta dauka ta reda rataya veil a shoulder dinta tana qoqarin rufe qofa shima ya fito.

"Sak ranar dana fara ganinta" ya fada aransa. Irin haka ta saka Atamfa riga da skirt tayi wannan daurin ture kaga tsiya mayafinta a kafada tana kokarin rufe kofar motarta, se yaci gaba da takowa a hankali har ya qaraso bayanta ba tareda ta sani ba tana gamawa ta waiwayo cikin rashin sa'a kafarta ta goce ta tafi gaba daya zata fadi. Ta gama saddaqarwa seta sha qasa lokacin dataji ta fada a jikin mutum, kamshinsa ya isa yasa tasan ko waye a maimakon ya saketa sema qara gyara mata zama da yayi a qirjinsa ya shiga tafiya da ita a haka. Ta shiga wata duniya ta daban har bata san sun isa motarsa ba se qarar rufe wa kawai taji kafin tayi wani yunquri har ya zagaya shina ya shiga ya tada motar suka fara tafiya seta bude baki da niyyar magana amma kallon daya mata ya sakata saurin yin shiru. Gani tayi ya dawo sak Dr Abdul'ahad Galadima na BUK, ya hade fuskar nan tsaf haka sukayi ta tafiya har suka isa wani guri da batasan ko ina bane. A mota ya fita ya barta, tun tana irga lokaci har bacci yayi nasarar awon gaba.






🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 3⃣9⃣


Firgigit ta farka tana zare ido jin an bude motar ga bacci a idonta har bata iya gabe waye sekawai ta kware baki da niyyar fasa masa iyu amma yaqi bata damar hakan, tuni ya rufe mata baki da nasa ya shiga kissing nata kamar babu gobe ko kuma ance in ya bari mutuwa zeyi. Sunyi kusan minti biyar a haka kafin ta samu nasarar kwatar kanta tareda fashe wa da kuka. Kansa ya jinginar a jikin kujera yana kallonta, ji yake kaman tana watsa masa ruwan zafi duk digon hwayenta. Ganin da gaske takeyi ya sakashi jayota gaba daya ta ya maidata kan jikinsa kamar wata yarinya yace

"To ya isa cry cry baby, ke baki da aikinyi kullum se kuka akan dan abinda bekai ya kawo ba dan ma kin samu nayi kissing dinki in kuma be ishe ki bane ba kuka zakiyi fa bude baki zaki ki magana kinji ammata amma fa sedai ki biya na baki bonus" seta saki baki tana kallinsa, takaici mamaki duk suka kamata lokaci daya. Yaushe Guru ya koyi surutu haka sannan taga alama shi rashin kunyar tasa ma qara gaba tayi, se ta fara qoqarin sauka daga jikinsa amaimakon ya kyaleta sema qara matseta da yayi yana qoqrin sake kissing nata dan ji yayi kaman ta tada masa da kwadayi. Ganin babu sarki se Allah yasa ta saka masa kukan Gaske, cikin kukan take magana
"Abdul'ahad meye haka, mena maka da kake min irin wannan abun kasan dai ni ba muharramar ka bace koma haka ne wannan abun haramun ne a tsakaninmu ka sani amma ka take kodan ka ganni a wata qasa da bani da kowa kake so kayi taking advantage tage dina?" Ta qarasa tana masa kallon tuhuma. Ko daya daga maganganunta be saurara ba shi sunansa kawai data ambata yafi masa komai. Be taba sanin sunan nada dadi har haka ba seyau dayaji shi a bakin Hamdah se kawai ya saka qarfinsa ya kwantar da ita ajikinsa zuciyarsa na wani irin bugu kaman ana daka a turmin qarfe. Akace fadan daya fi qarfinka seka maidashi wasa, haka ta kwanta tana jan majina sabida kukan dayaqi tsaya mata na takaici. Waima ya akai yasan inda take, a ina ma yasan auranta ya mutu dan dai da auran wani ba yanda zaayi yaringa tabata haka ita da tasan shine ma wancan dayan tenant din da bata kama gida a unguwar ba gaba daya ma da bata zo London karatu ba.

Gyarata yayi sosai a jikinsa ya tura kujerar baya tareda miqe dogayen kafafunsa ya kunna motar "Ina zakije ma wai da kika yafo wannan tayani gantalin yarinyar nan kina so ki gama

Please Login or Register in order to submit comment