Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shaqa. Alamar zazzabi daya ji yana son kamata ne ya saka shi bata pain killer tasha sannan ya lullubeta a bargo ya rage musu sanyin Ac nanda nan bacci ya dauketa a cikin jikinsa. Kanta dake kan qirjinsa yake shafa a hankali, nutsuwa yake samu ta daban a duk lokacin da yake tareda Hamdah, Goshinta yayi kissing yana kara gyara mata kwanciya yanajin yanda zafin jikinta yake ratsashi wani sabon tausayinta ya shigeshi. Yanda taringa masa kuka yake tunawa amma ko kadab be saurareta ba. A haka yaringa tuna moment dinsu da baze taba gogewa ba acikin tarihin rayuwarsa wannan dare yana da daraja, shikadai yake murmushi in ya tuna har bacci ya daukeshi.

Rayuwa suke gudanarwa cike da aminchi da yarda da juna kowannensu na tattalin Dan uwansa. A yanzu bata da wata matsala dan ta samu soyayyar mijinta abinda take buri kenan. A satin su biyu da aure bazata ce ga wani abu daya mata na rashin kyautawa ba tattalinta yakeyi kamar danayan kwai. Ko a bangaren yan uwan bata da damuwa dan sosai suke yi da ita musamman yammatan gidan kasan cewarta yar gayu ya kara kulla alaka tsakaninsu kullum suna part din sedai fa in Abdulmaleek ya musu jan ido se yace wai suna hana Shi sakewa da matarsa. Matsalarta dama Hafsa ce kuma tuni Ta tattara ta koma inda ta fito duk yanda kuwa taso ta zauna a gidan amma Hajja taqi.
Satinsu uku da aure in kaganta seka kara kallonta. Tayi kyau jikinta ya murje kamar me wanka da madara haka shima Ango ba a magana Dan har wata kiba yayi kana ganinsa kasan yana more amarci da tsibke. Ranar Monday kuma a ranar ne yake shirin komawa aiki bayan dogon lokacin da ya dauka yana hutu, tun da sukayi sallar Asuba takeyi mishi rigima akan wai ta shirya su tafi tare ya ajiyeta a gida in ya dawo seya dakkota ita bazata iya wuni ita kadai a gidan ba shi kuma yaki. Har suka fito zata rakashi bata hakura ba ta masa kwalliya sosai Abdulmalik ya hade cikin wata suit kalar Blue black yayi kyau ga wata kamala da cika daya qara. Itama sanye take da atamfa exclusive koriya dinkin doguwar riga bata daura dan kwaliba se gyale data yafa ta rufe jikinta gaba daya dashi se shagwaba take masa wai zatayi missing dinsa da yawa. Seda ta rakashi jikin motarsa tana jera masa addu'ar a dawo lafiya da list din kayan kwalamar da ze taho mata dasu shidai babu abinda yake in ba murmushi ba, jin kansa yake kamar wani sarki. Indai zata ci gaba masa da haka to shidai babu boka babu Malam ta gama dashi wallahi. Dakyar sukayi sallama Kaman karsu rabu dan ya kusa makara yaja motarsa ya bar gidan, haka suka wuni a waya Dan motsi kadan ze kirata yaji me takeyi yayi missing dinta haka itama.


5pm tagama komai tsaf ta gyara gidan ta fesa wanka cikin wani hadadden lace Orange gaba daya falon ya gauraye da daddadan turaren wuta ga kuma turarukan da tayi amfani dasu. Suna zaune da su Surayya da shigansu kenan yayi sallama. Jakar hannunsa ya ajiye tareda bude mata hannu alaman tazo, tamkar tarwada Haj take takun da ita kanta bata san ta iya irinsa ba har ta karasa ta shige jikinsa ya maida hannunsa ya rufe ji yake kamar ya kwana be ganta ba. seda ya shaki kamshinta sosai sannan ya furta "I missed you so badly my Jewel" yafada looking straight in to her eyes. Ita ma shi take kallo tace "I miss you more Jaan" tana juya idonta.
"you sure" ya tambayeta yana dage mata gira
"Yh I'm very sure" ta bashi amsa
"Oya na show me how much you miss me". Ya fada bayan daya saketa kadan, without given a second taught kawai ta hade bakinsa da nata what he wasn't expecting nan kuwa yashiga kissing nata hungrily as if his life depend on it. Su Sumayya da suka ga alaman an manta da zamansu sumsum suka fice tareda kullo musu falon. Seda ya gaji dan kansa sannan ya saketa suka shiga ciki, already ta hada masa ruwan wanka, bayan yayi wanka ne suka zauna cin abinci yana ta mata labarin office. Se yaga kaman walwalarta ta ragu dan shi yake ta hirar ita dai seta amsa masa da eh ko Aa. " Babe namanta naga me agwaluma kafin kuma na siya aka bamu hannu kuma a saman titi nake bare na tsaya na siya miki". Shirun daya ji tayi bata amasa bane ya saka shi kama hannunta ya riko cikin nasa ya murza a hankali. Idanunta masu haske ta dago ta kalleshi ganin irin kallon datake masane ya sakashi cewa "ya dai yammata ina ta magana kinyi shiru tunanin me kikeyi". To his suprise se ga hawaye Kaman ya bude famfo.
Hankali tashe ya fara tambayanta me ya sameta me aka mata ko wani gurin ne yake mata ciwo " Jewel talk please me nayi miki ko magana na ta bata miki rai kiyi hakuri yanzu ma bari naje na siyo miki in dai agwaluma ce" bata amsa shiba sema kara volume din kukanta da tayi cak ya dauketa suka dawo cikin palour ganin yanda ya rude ne yana shirin yi mata kukan ne shima yasa ta bude baki dakyar tace masa "Mumcy I want to see my Mom". Ta kuma rushewa da wani kuka.
Kanshi ya dafe tareda jan guntun tsaki a ransa yana mamakin wauta irin ta Hamdah, "Wallahi you scared the hell out me mene na kuka anan just to tell me you want to go home shikenan seki dasa min kuka kamar wadda nace zanwa kishiya, naga alama dai sena fara zaneki akan wannan shagwabar taki karkizo ki koyawa Baby na kuka tun tana ciki" ya fada yana dungure mata kai. Baki ta turo masa tana cigaba da tabe baki cike da shagwaba. "Oya tashi kishirya saura ki bata min lokaci nace na fasa" ai bata san lokacin data mike da gudu ba bayan tayi pecking nasa a cheeks ta shige dakinta Dan kintsawa.
Saboda azarbabi A falon ya tarar da ita ta chanza shiganta zuwa doguwar rigar shadda gezner dark blue da akayiwa dinki da jan zare Dan haka mayafinta da takalmi da bag duka Red ne.Tayi kyau kwarai har yaji kishin kar wani ya kalle masa ita. Se yai niyyar tsokanar ta yace "I'm sorry Babe yanzu Alhaji ya kirani zan kaishi gidan wani abokinsa and its urgent, ina ga mu bari se gobe" Da yake ruwa ruwa ce se hawaye tace "Dan Allah Jaan ko ka bani mota, Driver ne kasa ya kaini" hade rai yayi yace "wasa ma kike Driver zansa ya kaiki kinyi wannan kwalliyar yaji kamshinki to baze yuwu baki jira kawai inna dawo da wuri se muje in ba haka ba kuma gobe". Se ta fashe da kukan gaske tana" Ni wallahi ko ma Napep ne sena shiga Dan Allah karka hanani zuwa" janyota jikinsa yayi da sauri yace "Shish wasa nake miki kiyi shiru dan Allah" shi ya riqe mata jakarta ya bude mata motar ta zauna, har lokacin gani take kaman ze ce mata wasa yakeyi. A gate din gidansu ya tsaya yace su shiga su gaida Hajja yau basuje da safe ba, "Ai tamayi hakuri har 4 weeks bata fita ba amaren yanzu da ko sati basa rufawa suke fara garari a titi" cewar Hajja bayan daya gaya mata gida ze kaita sannan sukayi mata sallama suka tafi. Seda ya tsaya suka yi musu tsaraba sannan suka nufi gidan.
Sun hau titi sosai ya kalleta yace "Ni a wa in hana fitar nan nasan yau baccina ragaggene". Murmushi kawai ta masa hankalinta naka titi ji take inama tana da fukafiki ta tashi sama. Ko bari ya gama parking batayi ba ta fice daga motar da gudu tana kwalawa yan gidan nasu kira ko saurarensa bata yi ba taji kiran da yake mata ba dan ba karya tayi missing dinsu garama su Hamida sunje mata sau biyu amma mazan ba wanda ya je. Da khalifa ta fara cin karo daya bude mata kofar falon Baki sake yake kallonta dan suna cikin maganarta ne sukaji knocking din.
Tun kudeshi tayi ta shiga palour tana raba Idanu ta na neman inda zata ga mumcyn dan ta tabbatar tana gida lokacin chan ta hangota tana binta da kallon mamaki itama aiko da gudu ta fada jikinta " Mummy" se kuma ta saki kuka.
Gaba daya ta sanyayawa Mumcy jiki Dan haka ta shiga tambayarta "Hamdah lafiya daga Ina kike cikin daren nan ina Abdulmalik din". Ganin hankalinta ya tashine yasa ta tsagaita tace mata "Mumcy daga gida nake kuma tare ma muke da shi yana waje". Se a sannan hankalinta ya kwanta tace "To Shi kuma kukan na magani da menene ke da Baki kaunar a zauna lafiya".
"Bazaki gane ba Mumcy kawai na yi missing dinki ne dan Allah kema haka kikaji lokacin da kika auri Abbah". Rankwashin wasa Mumcy ta kai mata sannan tace "kedai kin fiya shirme wallahi harkinsa hankali na tashi to inbanda abinki kukan kuma maganin me zeyi bagaki kin ganniba?" "Oh su kuruf anzo kuma yau dama gobe nake tunanin inzo inga chakwakiyar da kike aikatawa naga an ja lokaci ba'a kawo kararki ba" cewar khalifa nan suka fara Dan dama an dade ba'a hadu ba. Sallamar yaya Baffa ce tareda Abdulmalik ta katse su.
"Amma dai kedai wannan anyi shashashar yarinya dama be tafi ba kika barshi a waje" Mumcy ta fada tana kokarin gyara zamanta. Baki ta zumbura gaba sannan tace "Nifa Mumcy nima bansan ya tsaya ba ai kona sani dan Allah Jaan?" Girgiza kai kawai Mumcy tayi tace "Kyaci gidanku ai wato baki dai chanza ba har Ina murna kin karo hankali ashe sema abinda yai gaba ko".
"Aa fa Mumcy da na ce mata zanje na dawone shiya sa" Abdulmaleek ne ya tarewa matarsa. "To ai shiikenan" cewar Mumcy suka shiga gaisawa bayan hamidah ta kawo masa kayan motsa baki. A gidan sukayi magriba da isha har gurin goma basu tafi ba Dan seda Abbah ya dawo ya ji dadi sosai yanda yaga Hamdan tasa sannan ya karayi musu nasiha sosai Mumcy ta kara bata wasu kayayyaki sannan sukayi sallama.
Zata shiga motar kenan idonta ya sauka kan BMW din Guruin da ke ajiye a gefe, lokaci daya komai daya faru ya dawo mata a kwakwalwa, ranar da ta dau kota har zuwa haduwar su ta karshe. "Ko yana wace duniyar kuma oho" ta raya a zuciyarta nan suka nufi gida ranta fal da kewar yan uwannata.


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 1⃣7⃣

Rayuwa da masoyi me dadi, Abubuwa dayawa sun faru cikin zaman Auran Hamdah da Abdulmalik. Tana wata na biyu da Aure Maryam ta haihu tasamu ya mace sun sha suna yarinya taci sunan kakarta Maman Yusuf din wato Ruqayyah suna kiranta Amal. Tuni ta koma aikinta da Sabuwar motar ta da Yah Abubakar ya Siya mata lokacin auranta Dan haka bata da matsalar transport.
Kamar yanda ta saba duk ranar juma'a takan raba wuni a cikin gidannasu Abdulmalik din saboda bata zuwa aiki ranar yau ma haka ta kasance, suna kicin tareda Anty Amarya kamar yanda suke kiran last wife din Alhaji Kamalu suna taya ta girki, A babban Dining me cin mutum 16 kamar wani conference table tana jera kayan abincinne ta jiyo sallama daga cikin palour. Yammata ne zakada zakada har su hudu se Babbar mace da akalla atayi sa'ar Hajja, kallo daya zakayi musu kasan jininta ne saboda kamar da sukeyi sosai. Gaba daya su ukun suka gaisar da Anty Amarya data fito daga kitchen din haka itama mahaifiyar tasu ta tsaya suka gaisa sama sama banda guda wadda kuma da alama itace babbarsu data dauke kanta gefe tana danna waya da taunar chewing gum. Part din Hajja suka nufa ita dai Hamdah tana tsaye tana kallon ikon su dan babu Wanda ma ya lura da ita cikinsu. A falon Hajja suka baje nan da nan aka cika musu gaba da kayan makulashe bayan sun Dan taba ne su ukun suka shiga dakinsu Khausar se dayar data kame a kujera tana ta muzurai. Kallonta Hajja tayi aranta tana kara karantar halin yarinyar.

Haula kenan uwar jiji da kai da takama ita tsabar nata isar ko gaisuwa ma se an roka inbanda son cimma wata manufa tata Ina Abdulmalik Ina wannan kodaddiyar yarinyar? Muryar Hajia Hauwa ce ta katse mata tunani tace "Bari na shiga bangaren Amare haryanzu fa banga surukar tamu ba". Haula dataji kaman mahaifiyar tata ta daba mata wuka tayi saurin jifanta da kallon wani kallo, inkiya tayi mata da ta nutsu sannan taci gaba " Ai naso inzo bikin wallahi hajia amma kinsan lokacin muna tsaka da campain ne ba dama se dai naga hotunan biki Amarya kam masha Allah". Murmushi hajja tayi dan tasan wannan magana ba har zuciyarta takeyinta ba se tace mata "Amarya ai tana nan cikin gidannan ma nazata ma kun ganta kafin ku shigo tana taya Halima girki". "Toh kila tunda kinsan ba saninta mukayiba Amma dai babu ma wata bakuwar fuska dana gani gaakiya sedai ko tana cikin kitchen ne". "Ok bari to a kira miki ita" cewar Hajja sannan ta shiga kwalawa Rufaida kira taje ta kirawo Matar Yayansu.

Tunda suka shiga palour Hajia Hauwa da yarta Haula suka zuba mata ido kowanne da abinda take kissimawa aranta. A bangaren Hajiya tsantsar kyau da gayu irin na Hamdah ne ya rudata, Ita kuwa Haula zuciyarta ce ta shiga tafarfasa wani irin bakin kishi yana taso mata, babu hadi Matar Abdulmaleek ta mata fintinkau nisan bana wasa ba. A she Momy cutarta tayi datake cewa wai farar fata kawai Gareta. Harta karaso ta zauna kusa da ita bata sani ba se kamshin turarenta da ya cika mata hanci. Faram faram suka gaisa da Hajiya Hauwa ta tambayarta ango da zaman kadaici acewarta, "Ai babu ma wani kadaici dan ita ma tana fita aiki dan zaman da take ita kadai bashi da yawa" cewar Hajja ita dai Hamdah murmushi kawai tayi. Juyawa tayi tayiwa Haula da kiris ya rage tayi bindiga inkiya da ido nata gaisheta, iya wuya ta shaqa dandai bata san manufar Momyn tata ba yasakata ce mata "Sannu dai yakike"." Yawwa sannunki" Hamdah amsa mata a ranta tana jin haushin irin kallon data kafeta dashi kamar wata mayya dan haka seta mike tareda kallon Hajja tace "Hajja bari na wuce zanyi girkin dare lokaci ya fara ja". "Toh ba damuwa kema dai ke kike biyewa rigimar Abdul in ba Haka ba ga abincin anan girkin me zakiyi". Murmushi tayi tana tafiya tace Aa Hajja kinsan shi daga girkin ki se nawa yake ci gara dai nayi masa".
"Haka nada kyau kuma shima ya ringa cin girkin matarsa Ai" cewar Hajia Hauwa da zuciyarta ke tafarfasa kaman zata fashe dan gani take kamar da gayya Hajja Fattu ke jan surukar tata a jiji ba, bata zaci cewar ta sake har haka da ita ba ganin irin kai ruwa ranan da akayi da ita kafin ta amince da auran, idan kuwa hakane ashe dole ta tashi a tsaye ta sake shiri Dan zama be gantaba, da ganin idanun wannan yarinyar ba karamar kissa zatayi ba amma ai in tasan wata bata san wata ba. Kwafa taja aranta tana ayyana abinda ya kamata tayi dan bazasu taba bari ya kufce musu ba, bokanta ya gaya mata shi din dai shine mijin Haula kuma aure ne irin wanda take so dan yaron yana da Nasibi a rayuwa sedai har yanzu ta kasa hango mummunan abin daya ce ze faru a gaba tunda har tayi sakaci Ya auri wannan yarinyar, koma dai menene tawa kanta alqawari seta raba auran nan ta maye gurbin sa Haula koda zata rasa komai data mallaka.
Sun jima suna tattaunawa da kawar tata sedai ko kadan taki bata fuskar da zasuyi magana akan hadin Abdulmalik da Haulan, suna shirin tafiya ya shiga gidan dawowarsa kenan daga aiki ya shiga ya bawa Hajja wasu saqo daya karbo mata a tasah. Kasan cewar Juma'a ce yayi kwalliya cikin wata shadda cream se daukar ido take. Cike da girmamawa yagaida Hajia Hauwan se qara daure fuska yake saboda wani kallo da Haula ta kafeshi dashi kamar zata hadiyeshi. Gani tayi ya qara mata kyau na musamman kodan ta dade bata ganshiba ga wani qasumba daya tara tasha gyara ji take kamar ta tashi ta rungumeahi. Kallo daya yai mata ya dauke kansa, yaganeta sarai Amma seyai biris da ita. ya tsani mace marar Aji se wani lanqwashe murya take wai tana gaishe shi, seda ta maimaita kusan sau goma sannan ya amsa mata da "lafiya" yayi wa Hajjan sallama yai waje. Zungurinta Hajia Hauwan akan ta bishi kamar dama tana jira cikin Hanzari ta cimmasa yana dab da barin main falon, jin alaman mutum na binsa a baya ya sakashi tsayawa sannan ya kalleta "yadai" ya fada fuska a daure".
"Ba komai dama rakoka nayi" ta fada tana gyara tsayuwarta. Se ya kalleta sama da kasa sannan yace "No bana bukata ba fita zanyiba gurin Matata zanje" yai gaba yabarta a tsaye kaman zata kurma ihu. Lallai ma ya raina mata hankali wato gurin matar sa ma zeje, kamar kazar da ruwa yawa duka haka ta juya cikin gidan, su Surayya dake zaune a falon sukace me zasuyi inba dariya ba. Ko takan Mahaifiyarta ta dake tambayarta abinda ya faru ba bata bi ba ta suri jakarta kawai tai ficewarta dan tanajin bazata iya qara koda minti daya cikin gidansu ba. Dole Hajia Hauwa tayi wa Hajja sallama suka tafi. Ko a mota inbanda kuka ba abinda take uwar nata rarrashinta Mansura kanwarta data gaji tai tsaki sannan tace "wai fisabilillahi ance daga Maleek dinnan babu wani namiji ne ko yaya da zaki bi ki tsangomi rayuwarki a kansa, mutum yace baya sonki to ki hakura mana ko ana dole Haba duk kin bi kin damu mutane wani yace kije inda yake ai Dama in ka nunawa namiji kana sonsa dole yama wulakanci bare ke ai dai ko bakida zuciya yakamata ki hakura haka... " "In naki kuma fa uwata Ina ruwanki koni sa'ar kice Dan ubanki" Haulan ta katse Mansura cikin masifa. "Allah ya taimaka" Sayyada karamar kanwarsu ta fada kasa kasa gudun kar fadan ya dawo kanta da haka suka karasa gida.

Bangaren su Hamdah kuwa a kitchen ya tarar da ita, miyar dake kan Gas take juya wa a hankali tana bin wakar data kunna harda Dan taka rawa. Sosai ta burgeshi, yanda take juya jikinta ya masa kyau se kawai ya ciro wayarsa ya shiga yi mata video. Aikinta take hankali kwance ita bata ma San da tsayuwar sa ba se kamshin turarensa dataji ya fara yawa a kitchen din, tunawa da tayi ta fesa kadan yasa bata kawo shi din bane. Duk lokacin datake missing dinsa se kawai ta fesa turarensa hakan na rage mata kewarsa sosai. Kaman ance ta juya taga mutum jingine da Freezer yana doka mata murmushi ba shiri ta saki ludayin dan Harga Allah taji tsoro ko kadan bataji shigowarsa ba. Saurin karasawa yayi ya rungumeta yana dungure mata kai "Matsoraciyar kawai, da in da zakije" bakinta taturo sannan tace "To ai kaine banji shigowarka bafa ko karar motarka banji ba se kawai naganka kana kallona". Gaban stove din suka karsa still tana jikinsa ya shiga bude tukwanen yace "Me kike dafawa ne haka tun daga office nake jiyo kamshi duk yawuna yagama tsinkewa". Steamer ya bude, burabuskon shinkafa ne fari kal se tashin kamshi take. Tana kallon yanda yake hadiye yawu Dan tasan yanda yake son abincin, janye jikinta tayi ta dakko warmer din data ajiye a gefe tashiga juye hadaddiyar miyar Irish potatoe data ji nama yankan kanana dakuma vegetables, shi ya kwashe Burabuskon bayan ta diba wani a Warmers daban da zata kai wa Alhaji dan Yau yake dawowa. A tare suka jera kayan akan dining sannan suka shiga wanka. Suna tsaka da cin abincin sukaji sallamar Khaleefa shida Amrah da Afrah yaran Anty zahra. Da murnar narta ta taresu suka dan gaisa kamin a fara halin da aka saba yana kwasar girki yana kushewa harda cewa Abdulmalik ya nemi Pligil dan dakyar in cikinsa baze baci ba wannan jagwalgwalon. Seda yai sallar isha sannan yai mata sallama tana ta mitar meyasa Anty zahra bata biyo suba dama Hamida tasab inda ta ajiyeta, rabon data je mata har ta manta. Dariya yayi yana cewa sunfi kusa ai ita kuma Anty Zahra dare ne yayi shi yasa bata zoba suma din sun takurane aka kawo su kwanar mata.
Washe gari a gidan Anty Zahra suka wuni se tsokanarta take wai kodai tare zasu juye irin wannan kiba da tayi haka (dayake itama tanada karamin ciki) dariya kawai tayi tana cewa "Haba Anty wallahi banida komai kawai dai hutune a haka ma fa Dan yanzu Ina fita aiki rana na dukana". Haka suka wuni suna hira sai bayan magriba suka tafi.

Rayuwa nata garawa kwanaki na shudewa se gashi wai har ana ba tun shekara da auranta, babu abinda ya chanza cikin kulawar da sukewa junansu sai daima abinda ya karu, zuwa yanzu tafara damuwa akan maganar samun ciki. Wata biyu da suka wuce da tayi missing period harta fara murna sedai watan gaba sega period dinta yazo abin tausayi har kuka tayi yaringa mata dariya kuwa. Tuni ta gama service se zaman shiru duka babu dadi abokan hirar ta ta duk sun tafi makaranta Khausar ce kawai Autar su Abdulmalik a gida ita kuma ba wani shirin kirki sukeyi da ita ba dan kusan shekarunsu daya dan haka ta rainata hakan yasa take kiyaye duk abinda ze hada su. Ita kam ta qagu dan har Mumcy ta kira wai ta mata prescribing maganin da Zata sha ta samu ciki se kawai tayi dariya tace mata wai saurin me take ta jira setayi goma ma.
Abinda ya qara mayar da hankalin ta akan tunanin tun wata ranar da Anty Amarya ke cewa Abdul din "Ni kuwa Abdul duk sa'annin auranku daga masu haihuwa se masu tsohon ciki mu kunki yo mana miji ko kishiya gashi dai Fatima ta haihu jiya da namiji naji ma wai sunanka za'a sakawa Dan" ta karasa cikin sigar dariya sedai tsaf yagane magana ce ta gaya musu shida Hamdan. Fatima Kanwarta ce datai mutuwar son Abdul din Amma yaki haka ta hakura sati dayane tsakanin auransa da nata shine yanzu ta haihu. Se yayi dan murmushi sannan yace "Haba dai Anty mudin nawa muke kuma auramma shekara daya kawai bari dai mudan kara hutawa tukunna kin babies din nan duk takura ce dasu suzo su hana mutum rawar gaban hantsi sudai Allah ya raya musu". Baki ta rike alamar mamaki ta daiyi shiru kawai, Mikewa shima yayi Dan dama tun fara maganar Hamdah ta shige gurin Mama Second wife din saboda suna shiri da ita babu laifi, ta fuskanci a fuska kadai Anty Halima ke nuna tana sonta amma a badini ta ringa yaba mata magana a fakaice kenan se yanzu ta gane dalilin saboda Be auri Kanwarta bane.
Da yamma ya shigo gidan, A dakinsa ya tarar da ita a kwance rubda ciki, bayanta ya hau ya zauna ba shiri tashiga tureshi tana "Wayyo Mumcy ya ballamin baya wayyo Abbah ya fasamin ciki kuzo ku ceceni". Birkitota yayi yana cewa "Muga cikin Ina ne ya fashe" ya shiga yi mata chakulkuli tana dariya. Seda komai ya lafa sannan yace mata "meya sa dazu kika gudo kika barni". Seta chanza fuskarta zuwa kalar tausayi sannan tace "Jaan maganar Anty fa gaskiya ce, ya kamata musan abinyi ko asibiti ma muje a duba mu". Hade rai shima yayi ya riko hannunta yace "Look Hamdah bana son shirme kema kin fara daukar irin tunaninsu kenan, ita kanta datake miki maganar kin san shekararta nawa a gidan nan kafin ta haihu?" Seta girgiza masa kai alamar Aa sannan ya

Please Login or Register in order to submit comment