Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai ya tafi mata normal, biki take so tayi wanda babu kawarta data taba yin irinsa. Tayi matuqar qoqari kuwa tundaga kayan da Amarya ta saka, zuwa abincin da aka dafa a gurin na musamman ne,kusan kowa mai muhimmanci ya hallara a gurin dan haka aka fara gudanar da taro.

Zata iya cewa littafin qaddararta ya fara budewa ne a yau, yanda yammata suka ringa daukar hoto da Angon kadai ya bata mamaki, kowacce tazo daga cousin se yar kawar Hajja se family friensa. Abin be fara damunta ba har seda wata daga cikin yammatan tazo gurin da suke zaune, macece kamar an zana Alif ba wasali dukda irin dameta da lalatacciyar fitted gown din jikin ta tayi hakan be fito da komai ba fuskar nan tasha make up Kaman a bikin aljanu se wani karairaya da yauki takeyi tamkar zata karye. Bata gama nazarin yarinyar ba ta tsinkayi muryarta tana cewa
"Please Amaryarmu ko zaki Dan tashi Ina so muyi hoto da ango ne".
Seta kalleta galala wai ta tashi sannan ta ta kalli gogan dake faman Buda hakora Kaman gonar auduga yana cewa
"Aa Haj Suniya saukar yaushe aka ce baki zo ba". Seda tayi fari da ido duk dan son taja hankalimsa tana kada jiki sannan tace "ka bari kawai jiya fa na dawo ban ma shigo Kano ba se dazun da rana kaima dai kasan bayanda za'ayi na kasa halartar bikinka shiyasa na ajiye komai nawa na ta baro Paris kawai dan aaga wannan wace me sa'ar ce ta dauke Prince charming".

Magana take tana wani fari cikin tsantsar iya kissa da bariki shi kuwa dolon kara bude baki yayi a dole anyabe shi yana cewa "Ai kuwa kin kyauta gata nan kuwa yakika ganta?"
"Yah ba laifi Dan ta ma fi yanda nayi tunani". yanda tayi maganar kadai ze tabbatar maka daurewa kawai tayi Amma kishi ke nukurkusar zuciyarta.
Hamdah data saki baki tana kallon ikon Allah, ita kuma din wannan wa ce ce daga wace bolar take? bude baki tayi daniyar magana sedai zuwan Aysha ya katse ta janta tayi ta sauko da ita inda kawayen Hajja suka taru domin yiwa Amarya liki Dan tuntuni Mc ke ta kwala kiran Amarya ta sakko amma ina hankalinta nacan tana kallon sarautar Allah. Se karfe daya aka tashi biki yayi biki kowanne bangare sunyi bajinta. Taji dadi kwarai da Mumcy ta zo gurin setaji kaman gida zasu wuce in aka tashi sedai tuni idonta ya raina fata lokacin data gansu daga ita se shi a mota yanda suk zo sun dauke hanya daban da wacce yan gidan su suka bi.
Tun a mota ya ga chanji a tattare da ita, be kawo komai aransa ba dan tunaninsa ko gajiya ce dan haka be takura mata ba koda suka je gida dakansa ya hada mata ruwa masu zafi tayi wanka yalallabata tasha tea sannan tayi bacci. Ya dade yana kallonta yaso ya sameta a daren yau Amma ta gaji baze mata abinda bata soba. Wani irin farin ciki yakeji wai yau shine kwance tareda ita a matsayin matarsa ta sunna? Haka yaringa juyi yana waaikar jaki dakyar bacci barawo ya sace shi bayan ya rungumeta tsam a jikinsa tamkar wani ze kwaceta kafin safiya.
*_Asuba ta gari Mr and Mrs Dala_*.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 1⃣5⃣

A bangaren Abdul'ahad kuwa hankali tashe Yusuf ya wuce dashi asibiti sakamakon gani yana yin daya ke ciki. Sun isa asibitin aka karbeshi zuwa emargency bayanda Yusuf beyi dashi ba tun a hanya akan yakira Ammi ya sanar mata Amma yaki akan dolen shi ya hakura dan yasan muddun ya kirata bazasu kwashe kalau ba, ganin ya fara bacci ne bayan treatment din da aka bashi ya saka Yusuf tafiya gida dan ya dakko masa wasu kayan da kuma abinci kafin ya farka.
Se wurin magriba ya farka da fatan Allah yasa duk abinda ya faru ya zama mafarki ne sedai babu alama tunda gashi akwance kan gadon aaibitin da yai bacci. Sallolin da ake bimsa ya shiga ramawa bayan yayi wanka sannan ya diba abinci kadan ya fara ci, seda Yusuf yayi fama dashi sannan ya yarda aka kira masa Fahad ya kwana dashi, haduwa sukayi su biyun suka sakashi a gaba wai suna masa nasiha harda likitan shima in ya tankasu ku da kuke karatu kun saka baki, har 12am Yusuf na asibitin sannan yai musu sallama ya tafi gida koda yaje be fadawa Maryam ainihin inda yaje ba kawai yace mata wani abokinsa aka kwantar a asibiti da safe tayi girki da wuri ze kai musu da "To" ta amsa shi tana mamakin wannan wane abokinsa ne haka.

Gidan Amarya
Bacci sosai suka kwasa saboda gajia har seda suka makara sallar asuba. Ita tafara farkawa dakyar ta zare jikinta daga nashi saboda irin rikon dayai mata motsinta ya farkar dashi. Magana yake niyyar yi mata tayi saurin nuna masa katon agogon dake manne a jikin bango. Salati yayi ganin har 7:45am na safe Dan haka a gaggauce suka dauro alwala, yarigata fitowa daga toilet din se ya shimfida musu sallaya sannan ya dakko mata hijab cikin wardrobe ya zauna yana jiranta. Bayan ta fitone ya jasu jam'in sallar, kusan a tare suka idar da azkar Dan haka ta kalleshi cikin sanyin murya tace
"Ina kwana"
"Lafiya lau Amaryata ya kwanan bakunta?" Shiru tayi bata amsaba haka shima be kuma cewa komai ba se kallonta kawai da yakeyi yana nazarinta a zuciyarsa, gaba daya kamar a takure take. Gani ya keyi Hamdah ta chanza masa yanayin fuskarta da komai ya chanza, a da ya kanga zallar kauna da soyayyarsa a cikin idanunta Amma yanzu ba haka bane. Baya so ya gasgata abunda zuciyarsa take gaya masa, baya so ya yarda da cewa wani take so bashi ba. A zatonsa zata kasance cikin farin ciki da kasancewarta cikin gidansa Amma se gashi ba hakan bane yana kallonta yanzun ma hawaye take sharewa a hankali wai dan karya gani amma ta makaro dan ya riga da ya gani. Tun da aka fara bikin nan take kuka, be manta kukan da ta farka cikin dare tanayi ba wanda taki gaya masa dalili. Se yake ganin ko na Rabuwa da gida ne kawai, "Kwarai Sabo ne" zuciyarsa ta ayyana masa.
"Kaima kasan dole duk son da take maka zataji ba dadi na rabuwa da familynta" wani bangare na zuciyarsa ya kara tunatar dashi. "I hope so" ya fada a fili. Seta juyo ta kalleshi, murmushinsa me kyau yai mata tayi saurin saukar da kanta kasa dan yayi tasiri akanta. Mikewa tayi ta shiga ninke hijabin da tayi sallah dashi tace "Me ya faru".
"No nothing kawai zancen zuciya nakeyi" ya fada yana karasawa kusa da ita ya dora kansa a kan kafadarta, light kiss ya dora mata akan bear skin dinta. Wasu irin abu ne suka tafi tundaga wurin har tafin qafarta kamar electric shock wata kasala ta shiga sauko mata, saurin ture kansa tayi tana cewa "Ni Bacci". "Ok ok muje ki kwanta Amaryata".
Janta yayi ya kwantar da ita akan gadon yana patting bayanta Kaman yanda akewa baby in ana so yayi bacci. Likimo tayi tana jin yanda hannunsa ke yawo tsakanin gashin kanta da bayanta wanda tun tana jinsa har baccin gaske ya dauketa, jin ta dena mutsu mutsune yasashi leka fuskarta yaga baccin takeyi. Pecking goshinta yayi a ransa yana cewa Rigimamiyar kawai, a hankali ya zameta daga kan hannunsa ya shige toilet dan gaba daya bayajin baccin dukda kuwa gajiyar dayake tare da ita. Wanka yayo sannan yanufi dakinsa dan ya shirya, kayan sawarsa da ya barwa Abdallah ya jera masa tun a jiya da safe be gama ba ya shiga karasa shiryawa cikin wardrobe din a nutse ya kunna waka dan ta debe masa kewa. Yadauki kusan 1hour yana shirya kayan sannan ya gama. Ganin har lokcin bata tashi bane yasakashi fita palour ya zauna yana karewa komai kallo. " So unique" ya fada a zuciyarsa. Babu tarkace kwata kwata a palour daga set din hadaddun English Royal Gray color se daukan ido sukeyi sefa centre table, centre carpet dake shimfide a tsakiyar palour, Se fa Side Table a tsakanin kujerun. TV stand dinta da Tv kanta abin kallo ne, shimfidediya bango guda se wata flower guda daya a gefen. kowanne bango falon sunsha ado da wallpapers masu bala'in kyau kai ka rantse a gidan turawan asali kake.
Motsin daya jiyone ya sashi juyawa, Hamdah ce tafito tana yatsina fuska cike da shagwaba hannu ya bude mata alamar tazo. Cikin takunta me nutsuwa da daukan hankali harta karasa tashige jikinsa sannan tace "Shine kayimin wayo nayi bacci ka gudu ko?" Peck ya mata a goshi sannan yace "Sorry babe ba guduwa nayiba banaso na tashekine kinji" ya karasa yana kallon idonta masu kyau. Kasa jurewa kallon tayi ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi hakan yasashi dagota fuskar tata, "Look at me" ya fada in a low tune, tana dagowa ya hade bakinsu yafara aika mata da sakonnin daya dade yana ajiyewa, ya dade yana jiran wannan chance din yau gashi Halal ya samu, nan ya shiga kissing dinta like his whole life depend on it. A farko ta so tayi masa gardama amma ko me ta tuna kawai ta sakar masa kanta ya shiga sarrafata yanda yaga dama. Knocking din da akeyi da karfi ne ya katseshi, kallonta yayi ganin yanda ta takure a jijin kujera se kuma ta mike da gudu tayi daki, jiki a sanyaye ya mike shima yabude kofar a ransa yana mitar waye wannan ya katse masa jin dadi.

Sumayya da Surayya ne twins din Haj Sa'adatu step mom dinsa ko wacce dauke da basket dake cike da kayan abinci a hannunta. "Yaya Ina kwana" suka hada baki gurin fada. "Lafiya lau ya gajiyar biki" ya amsa musu fuska a dan hade dan sosai yaji haushinsu. "Lafiya Alhamdulillah dama Mami ce tace mukawo muku abinci" suka fada suna qoqarin shiga cikin palour, matsa musu yayi suka shiga ya maida kofar ya rufe sannan shina ya shiga. A Kan dining suka jere abincin sannan Sumyya tace
"Yaya Ina Anty Hamdah mugaisa" mintsininta Surayya tayi alaman tayi shiru duk akan idonsa. "Kwaji da gulmar ku tana wanka in zaku jira ta bismillah". "Aa yaya ma dawo anjima" suka hada baki gurin fada sannan suka fice. Dakin ya shiga bayan ya dudduba abincin, A gaban mirrow ya sameta tana fesa turare har tayi wanka. kallonta kawai ya tsaya yi Dan tayi masa kyau sosai. Atamfa ce jikinta java me kalar Red and Black hakan ya kara haska farar fatarta sosai, kara sawa yayi ya karbar turaren ya cigaba da fesa mata, murfinsa ya mayar sannan janyota jikinsa gaba daya har seda ta dan firgita yace "Kinyi kyau yammatana" ya fada yana zagaya hannunsa akan sarkar dake wuyanta.
Bayanta ta juya masa tace "Jaan please help me with the Zip". Seda ya gama tsokanarta sannan ya zuge mata. Ya fita yana mata dariya. Yanajinsa tana cewa itama zata rama ne ya tafi dakinsa. kayansa shima ya chanza harta fito palour dan haka suka zauna suka shiga cin abincinsu cikin kwanciyar hankali. Mayafinta yace ta dauko bayan sun gama sannan suka fita zuwa cikin gidansu su gaishe su, ta karamar kofar da yayi daga part dinsa zuwa can din suka shiga, A Babban falon suka tarar da yawancinsu ga kuma bakin da basu gama tafiya musamman yan uwan Alhajin nan aka shiga gaisawa kowa yana musu addu'a da fatan alkairi. Seda ya kaita ta gaida dukka matan gidan guda uku sannan suka karasa Bangaren Hajja, tana zaune ita da kannenta guda biyu Hajja Mairama da Anty yagana sai wasu yammata yayan yan uwanta da suka zo bikin suma se yawo suke a palour se kuma kannen Abdul din Guda biyu da suke ciki daya.
A kasa ta zauna tana gaishe su duk da yanda Yagana ke janta da ta koma kan kujera Amma taki. Da daddaya yammatan suka ringa gaisheta kowacce da salon tata gaisuwar da alama dole akai musu ita kuwa ko a jikinta dan dama ba damuwa tayi da a gaisheta ba. Wata figigiyar yarinya ce daban ta fito daga baya, ba wannan ta jiyan bace dan wannan har ta fi waccen qarewa kuma ita fara ce tas kamar zabiya amma fa na mai kilan ma harda allura ta hada. Tafiya takeyi tamkar zata karye har ta gota su ta dawo ganin Abdulmalik ta daka uban tsalle tareda daneshi tana cewa
"Wayyo sweety I missed u so much wallahi". kokarin rabata da jikinsa yake Amma ya gagara dan yanda take qara manne masa kawai se ya bige da cewa "Hafsa bakya girma". Anty Yagana da kunya ta isheta kamar me ganin Hamdah na zaune tace " Ina fa zata girma ai wannan jin kanta take kamar Nana (karamar yarta). "wai yaushe ma kika dawo ne kema haka" ya fada bayan daya samu nasarar sauketa daga jikinsa sedai bata sake shiba, hannunta cikin nasa still tace "Yesterday night na shigo very late dukda saurin da naringayi na halarci dinner kishiyata amma a banza". Tuni Hamdah ta fice ta basu guri, muqullin kofar na hannunsa dan haka kawai ta fita ta main gate ta zagaya gidanta me gadi nata mamakin yaushe ta fita.

Hira hafsa ta shiga jansa yana dan biye mata kadan kadan dan bala'in takura ce da ita. Ta zamar masa kamar wata kaska indai tazo duk inda ya sauke kafarsa tana bayansa ko da kuwa fita zeyi. Hafsa yar Anty yagana ce kanwar Hajja, tun tana yarinya take matuqar kaunar Abdulmalik amma shi yana kulata ne kawai a matsayinta na cousin dinsa bawai dan yana sonta ba. Seda takai ta kawo dakanta ta fito ta furta tana sonsa amma yai turning nata down da cewa shi yana da wacce yake so dukda a lokacin karya kawai ya mata bata yi masa bane kawai. " Sweety muje part dinku akwai labarin dazan baka" Hafsa ta fada tanayin gaba. Se a lokacin ya tuna da tare suke da Hamdah, wani miyau ya hadiye ganin bata gurin yasan fushi tayi ta tafi dan haka cikin sauri ya wuceta yana cewa "wait for me here sena tambayo izinin matata in ta yarda ki shigar mata gida" yayi gaba abinsa, ta kuwa shaqa iya wuya dan dama da biyu tace suje can din saboda ta qarasa batawa Hamdah rai, dole ta koma ta zauna Anty yagana dake jiran ya tashi ta shiga surfa mata masifa tana zaginta wai Mara zuciya, Allah yaso Hajja tunda suka gama gaisawa dama ta shiga daki an kirata a way.

Da Sauri sauri ya isa part din nasu saidai yai rashin sa'a ya tarar da su Anty zahra da Anty Amna se wasu cousins dinta guda biyu. Wani kallo ta watsa masa dashi kadai yasan ma'anarsa seya marairai ce fuska ya kama kunnensa guda biyu kamar yaro yai murmuring "please". Dauke kanta tayi se ya shiga gaidasu suka amsa masa cikin sakin fuska da barkwanci, dakinsa ya shiga dan ya basu guri dan besan me suka zo yi ba. Wani aiki ya shigayi a system dinsa har aka kira sallar azahar sannan ya tafi massallacin dake hade da gidansu. Bayan ya idar ne ya koma cikin gidan, bedroom dinsa ya qara shiga ya kwanta rigingine yana shakar daddadan kamshin turaren wutar da gidan yakeyi, Dukda ya saba da ire iren kamshin turaren wuta saboda Hajjar sa na amfani dasu sosai dan ko dakunansu in aka gyara musu se an kunna buner Amma se wannan ya zamar masa nadaban, baccin dake ta damuns ne ya samu nasarar daukarsa.

Sai bayan la'asar sannan su Antu Zahra suka tafi duk se taji babu dadi, wanka tayi sannan ta gabatar da sallar la'asar, kwalliya sosai ta tsala cikin wani skin tight blue se yar top me kalar red dan ta gaji da saka Natives tana buqatar shan iska. Yanda ta tufke kanta a tsakiya ta sakijelar tana reto a bayanta ya karawa kwalliyar tata kyau kamar wata babyn roba. Jinsa shiru yayi yawa kuma taga lokacin daya shiga dakinsa yasa kata lekawa dakin a karo na farko. Murmushi ne ya subuce mata ganin yana yin kwanciyar tasa a ranta tace "oh Maleek Kaman wani yaro" kafafuwansa daya bari a kasa ta shiga ja dan ta mayar masa kan gadon dai dai lokacin daya farka idonsa ya sauka akan ta. Yanayin gayunta ya tafi da imaninsa sosai se kawai ya saki baki kamar wani dolo yana kallo, iska ta hura masa a kan fuska tace "get up sleepy head har isha tayi kana bacci".
Saurin kallon agogon yayi 4:37pm. Tsalle tayi ta sauka daga kan gadon ganin yana neman rikota tana dariya tace "toh ae nasan in ba haka nayi maka ba bazaka tashiba yanzu ba" tayi waje tana cigaba dayi masa dariya.
Gaba daya Hankalinta nakan Tv batayi auneba seji tayi anyi sama da ita gaba daya, baki ta bude daniyar yin ihu dan bata ga ko waye ba cikin sauri ya rufeshi da nashi, within seconds ya fara barin layi, tafin da suka ji akansu ya sakashi saurin sakinta a dole. "Sannunku lover birds" cewar Hafsa tana mai gyara zama akan kujera. Idanunsa da suka chanza kala ya dago ya kalli Hamda data dukunkune tayi lamo a jikinsa sannan ya Maida kallonsa kan Hafse dake kokarin chanza channel.
Seda ya tattaro dukka karfinsa sannan dakyar ya iya cewa "Haka aka koya miki shigarwa mutane gida babu sallama?" "Sallamar dubu nawa nayi kuna chan wata duniya ina zaku jini" ta amsa masa with I don't care tune. Tsabar takaici kasa ce mata komai yayi dan jiyake kaman ya maketa. Takaici da bakin cikine yasa Hamdah mikewa tareda jan tsaki tayi cikin dakinta. Wannan wace irin rayuwa ce haka daga shigowarta ace zata fara da haka? Wai ma ita wannan mekama da bulalar daga Ina take dan dai tasan ba kanwarsa bace. Bataji shigowarsa ba illah tight hug din dayai mata, duk diban albarkar data so yi masa Amma be bata damar hakan ba seda ya tabbatar ya kore mata duk wani bacin rai da damuwa Sannan ya kyaleta.
Magana ya rada mata a kunne da banji me yace ba da sauri ta mike tana cewa "Nidai A'a wallahi"
"Ayya yarinya kin makaro" ya fada yana kwanciyarsa akan gadon, kukan shagwaba taringa yi masa ita dai A'a. Inbanda dariya ba abinda yakeyi mata, Zamansu sukayi a dakin har saida sukayi sallar magriba. Daga yanayin yanda yake Mata ne ya tabbatar mata yau bazata sha ba, tsoro fal ranta tagama shirin bacci ta rabe a gefen gado.
Danne Dariyar sa yaringayi amma ya kasa ganin yanda bilhakki take share hawaye, dariyar ce ta kwace masa nan ya qara tunzurota ta shiga dukan sa da pillow tana kukan dagaske ta samu dalili, ganin abin nata dagaskene ya sakashi rikota ya shiga rarrashi daga nan labari ya chanza ya canza salo.


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 1⃣6⃣

Asibiti
Kwanan Abdul'ahad hudu a asibiti yana jinyar zuciyarsa har lokacin babu wanda yasan ya dawo in ka dauke Yusuf sai kuma Amininsa Fahad. A cikin kwana na biyar din ne yanemin sallama dukda zaman aaibitin yafi masa dadi, alluran da sukeyi masa suna qara taimaka wurin mance damuwarsa in yana bacci. Be taba zatan akwai wata rana da zata zo shi Abdul'ahad ya so wata mace ba har ya kwanta ciwo saboda ita se gashi yau helplessly akan mace. Dama wannan shine So ruwan guba da ake faa tabbas kuwa ya kurba gashi dafinsa na dab da halakashi. Dr Muzammil likitan dake kula dashi ya gargadeshi akan ya cire damuwa itace ke neman zautashi Dan haka indai yana son lafiyarsa ta dore dole ya hakura da dukkan tunanin dake damunsa.
Yana cikin buttuning rigarsa Yusuf da Fahad suka shigo dakin, kallo daya ya musu ya dauke kansa danzu kam miskilanci se godiyar Allah. "Ah lallai mutumin Lafiya ta samu" cewar Fahad still be kula suba sema jakarsa da suka kawo masa kaya aciki daya jawo ya shiga zuba ragowar abubuwan da suke a waje, saida ya gama tsaf sannan ya juya yace musu "I'm going se Allah ya kuma hada mu thanks so much men Ana tare". Patting kafadarsu yayi ya shiga jan jakarsa ze fita haka suka bude baki suna kallonsa, ganin da gaske yakai kofa yasaka Fahad saurin shan gabansa yace "Going to where?"
"Inda na fito" ya bashi amsa yana qoqarin kauce masa dan ya fita abinsa. Se suka biyo shi a baya, Sulaiman Amintaccen yaronsa suka gani a harabar asibitin ya taso da sauri ya karbi jakarsa ya saka a mota sannan ya bude masa back sit ya shiga. Ta window ya sakar musu murmushinsa sannan motar ta tashi ya barsu a tsaye kamar bishiyoyin da aka dasa. Seda suka dena hangoshi sannan kowa ya kama motarsa ya tafi dan already yayi settling bill din asibitin.
Idonsa a rufe ya jingina kansa da kujerar har suka isa Airport da already Sulaiman ya masa booking flight da komai, Cikin awa daya yagama duk clearance dinsa ya zauna akan kujera jikin window a First class suite. Ta window yake kallon garinsa Kano lokacin da jirgin ya fara tafiya a sararin samaniya tun yana ganin gine gine har suka fara bace masa bayan da jirgin ya daidaita a sam, a fili ya furta "Se wata rana kano,se wata rana Nigeria". Amminsa da sisters dinsa ne suka fado masa a rai, lumshe idonsa kawai yayi Dan dole ze lallashi zuciyarsa Dan kuwa zaman Nigeria banasa bane ya sani muddin yacigaba da zama to dole wata rana se sun hadu abinda baya taba fata kenan ya hadu da ita tana matsayin matar wani ba tasa ba. Bayan tafiyar awanni da transits ya sauka qasar Japan lafiya, ya tarar da Abokansa daya baro da jimami na rashin sanin abinda ya sameshi. Ko da ya koma tambayar duniya su master sukai masa akan abinda yasa shi tafiyar da babu shiri Amma yai musu kunnan uwar shegu dole suka hakura sedai duk Wanda yasan shi inyaganshi ayanzu dole yasan yana cikin damuwa. Dama yaya lafiyar kura Dan haka yanzu miskilanci yaci uban na da aiki da neman kudi kawai yasaka a gaba ya ture duk wani batu na soyayya acewarsa ya gama, ita kadai tayi masa daya aura a matsayin mata, tunda ya rasata kuma shida aure se a aljannah.
*Fatan alkhairi ABDUL'AHAD ALIYU GALADIMAH Allah ya baka mafificin alkhairin Hamdah*.

*****************************
Da kyar Amarya Hamdah ta iya bude idonta tareda jawo bed sheet ta kara rufe jikinta, motsinta daya ji ya sakashi juyowa da sauri ya mikewa daga kan Sallayar da ya ke. "Sannu Zaujy Allah yayi miki albarka, Kaman yanda kika faranta min Allah ya miki sama da haka nagode Hamdah na gode Ubangiji Allah ya biya miki buqatunki na alkairi Allah ya faranta miki kema....."surutai kala kala ya ringa yi mata har ya sakata jin kunya se kace ba haqqinsa ba, hannunta tasa ta rufe masa baki tana cewa "Ya isa mana mene nayimin godiya nifa matar ka ce halalinka fa ko ka manta ne". "Haka ne na sani Hamdahta Amma dole na gode miki".
" Nidai ya isa lokacin sallah kuma yana qara qurewa" ta katse masa surutan da yakeyi. Shi ya taimaka mata tayi wanka kafinnan ya gyara dakin tsaf sannan suka gabatar da sallar asuba tare. Tea ya hada mata mai kauri ya ringa lalla bata tasha dan yasan dauriya kawai takeyi. Wata irin kimarta ce ta qaru a idonsa, son ta da tausayinta yana qara shigarsa aduk numfashin daya

Please Login or Register in order to submit comment