Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wai kanta ne ta dawo yana ciwo shine tasha magani ta kwanta.
"Kodai har kin fara missing gida ne" Hamida ta tsokane ta, harararta tayi ta ci gaba da kurbar shayinta lokaci daya wayarta ta shiga ringing.
Kware wa tayi da shayin sakamakon sunan data gani yana yawo akan screen din wayar, dama bata goge wannan number ba? Sannu suka ringa mata Hamida ta miqa mata ruwa dan tasha lokacin har wayar ta katse, Mumcy ce ta shiga yiwa Khaleefa fada da shigarsa kenan ya fara tsokanar Hamdan a tunaninta magana zata masa yasa ta kware. Plate din chips dinta ta dauka da sauran shayin ta fita daga kitchen din jikinta har rawa yake yi ta shiga dakinta ta zauna a qasa daidai lokacin da wayar ta dauki sabon ringing still shi dinne seta daga dan taji abinda ze gaya mata.

"Aeesh" ya fada cikin wani irin murya data saka ta farajin sanyi kamar wadda aka watsawa ruwa.
"Aeesh kina jina ko bacci kikeyi" ya qara maimaitawa.
"Uhm" kadai ta iya fada dan gaba daya ji tayi kamar an datse mata harshe.
"Oh Aeesh kina jina dama kikayi shiru ko to ina kwana tunda bazaki gaisheni ba ya gajiyan jiya" wannan karon cikin sigar shagwaba yayi maganar dan har seda ta jingina sosai da gadon dan jitayi Juwa Juwa na dibarta a zaune.
"Dama na kira ki ne naji ya kike and please da daddare zanzo na ganki kinji ina so muyi magana ne amma banda rashin kunya kinji" seta zumbura baki wato ita cema mara kunyar dan haka tace masa
"Rashin kunya ai sabon karatun dana koyo kenan ko ka manta" ta qarasa tana murguda baki kamar yana gabanta. Murmushi me sauti yayi kafin yace "karki damu yarinya, se nayi maganinki bari dai nagama da wannan lusarin da kike shirin aure a matsayin miji"
Hohoho ina wuta Hamdah ta jefa shi wai Abdurrahman ne lusari sedai kafin ta bashi amsa ya datse kiran kuma data kirashi back wayar taqi shiga, kwafa tayi aranta tace "zaka zo seka maimaita abinda ka fada yanzun".

Abdul'ahad ko bayan ya kashe wayar murmushi yaringayi yana juya wayar a hannunsa, dan qaramin towel din daya maqala a wuyansa ya jawo ya goge zufar kan fuskarsa sakamon motsa jikin da yayi. Motsin dayaji a bayansa ya sakashi waiwaya wa, Ni'ima ce dauke da tray data doro masa coffee se tururi yakeyi se yaji wani iri Allah yasa bata ji wayar a yake yi ba. Try din ya karba daga hannunta ya kai kofin bakinsa ya kurba idonsa akanta, tayi masa kyau cikin doguwar rigar Atamfar data saka amma bata ko kama kafar Hamdan sa ba, imaging ya fara yi ace ita ce cikin wannan shigar irin kyan da zatayi
" Yah Abdul ga Little can tana jiranka a palour ni na hanata shigowa nasan damunka zatayi tayi wankan tafiya gurin namesake" ta fada tana murmushi dason share abinda yake damunta a zuciya, taji wayar da yakeyi sarai daga farkonta har qarshenta amma ya zatayi in ma tace zata ji haushi kanta kawai zata kwara ba wani ba.

Dafe kansa yayi sannan yace
"Oh Allah kinsan yarinyar nan tun Asuba dana shiga gurinsu ta tashi wai se Fadila tayi mata wanka zamu tafi unguwa dakyar fa na lallabata na gudu shine yanzu zata biyoni" se yayi gaba yana ci gaba da kurban Coppee dinsa.
"Daddy" Little Hamdah ta kwalla kiransa kafin tayi tsalle ya cafeta, juyi suka shigayi yanda suka saba yana ci gaba da cillata sama yana chafewa seda suka gaji sannan ya zauna akan kujerar Dining ya dorata akan cinyarsa. Data bude baki zatayi magana seya zira mata abincin da Ni'ima ta zuba masa haka yaita dura mata har seda ta gaji tace "Daddy I'm full lets go please its getting late" sauketa yayi a kasa sannan yace
"To bari nima naci abinci" kallonsa tayi cikin rashin fahimtar abinda ya fada sannan ta kalli Momyn ta
"Eh kinji me yace ai kika tsareni da idonki kamar na mage" seta tabe baki kamar zatayi kuka dan bilhaqqi ita fa bata jin Hausa shiyasa taqi yarda da kowa indai ba turanci kayi mata ba wai tana tsoro kar a sace ta wai wadannan mutanen masu speaking foreign language. Tsiya sosai Ammi take mata taci zata ci gidansu zata ga foreign language bayan Hausar ita ce yaren uwarta da ubanta amma take gudunta "Rainon Inji akw gayamiki Ammi ta ina ta hadu da hausa dama wannan kina ganin kalarta ma duk tafi mu haske da alama Yaya kun manta baku saka mata Melanin ba" cewar Amina ranar dasuka zo musu sannu da zuwa kememe taqi yarda ta tabata wai saboda she is black.
Seda yaci ya qoshi dan baya wasa da cikinsa sannan ya shiga wanka duk tana zaune tana jiransa a palour, wayo ya mata suka koma part din Ammi dan yau babu inda zeje anan suka wuni duk yana lura da duk wani motsin Ni'ima. Besan me take shiryawa amma yana suapecting kamar bata da gaskiya,har wayarta ya dauka ya duba dayaga tana ta waya amma bega komai ba se number mamanta data sister ta sukayi waya dan gobe a gidansu zata wuni abinda be sani ba ta goge Number Hamda ta haddaceta akanta dan tasanshi da bincike bataso ya samu wani clue da ze zargeta. Dan haka take taka tsantsan sosai akansa fatanta Allah yasa ta samu nasarar abinda take shirinyi.


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 3⃣1⃣

Bayan sallar magriba ya shirya tsaf cikin Shadda cream dinkin riga iya gwuiwa, hularsa ya kafa ta zaunu sannan ya feshe jikinsa tsaf da turaruka masu kamshi da ka ganshi kaga me zuwa zance. Ni'ima na kwance akan gadon tana binsa da kallo kishi na nuqurqusar zuciyarta dan wannan kwalliyar da alama akwai dalilin yinta amma seta dtace

"Yah Abdul kayi kyau wai ina zakaje ne"

"Allah ko zance zani gurin kanwarki" ya bata amsa yana gyara zaman hularsa. Se da ta danne abinda ya taso mata sannan tace

"Kai amma naji dadi kam ai daka gayamin ma dana tayaka shirya wa da gayun yafi haka dukda yanzun ma na san bazata iya resisting wannan kyan naka ba" ta karasa maganar tana dan haki saboda wani daci da zuciyarta taji tanayi a alama kishine, se ya aje comb din dayake taje gemunsa ya nufeta

"Baki jin magana Ni'ima kiyita magana bayan kinsan it is not good for your health at all". Kwata kwata bama tajin maganar dayake fada se lips dinsa datake kallo yanda suke motsawa.

"Do you want some" ya tambayeta bayan ya lura da irin kallon da take masa, kai kawai ta daga masa nan ya shiga kissing nata passionately, ko minti biyu ba ayiba yaji bugun zuciyarta ya qaru se yai saurin pulling out ya dora kanta a shoulder dinsa yana dan bubbuga bayanta a hankali yana jin yanda take jan numfashi a wahale kafin wani lokaci bacci yayi awon gaba da ita. A hankali ya shimfideta badan fitar ta zamar masa dole ba da babu inda zeje, wayarsa ya dauka ya kira Farida akan tazo ta zauna da ita ze fita karta farka babu kowa a gurin ko zata buqaci wani abun tunda Bangaren Faridan ne itace dama me kula da ita ko can a UK.

Yana tafe a hadaddiyar Benz dinsa duk inda ya wuce se an kalleshi, tuqi kawai yake amma hankalinsa ya kasu gida biyu, daya yana kan Ni'ima daya bari a gida daya kuma yana kan Hamdah da besan dame zata tare shi ba. Cikin girmamawa Sa'idu ya gaishe shi yana tambayarsa bayan rabuwa shekaru da yawa basu hadu ba, kudi masu yawan gaske ya bashi yakuwa zube yana masa godiya kafin ya shiga cikin gidan ya kira masa ita.

Yanda ta fito tayi bala'in tafiya da Imaninsa, Atamfa ce a jikinta dinkin skirt and blouse da suka dan kamata kadan sabida kibar data danyi kwana biyu. Dinkin ya amshe ta sosai bata daura dankwali ba mayafi data yafa har kanta kalar Atamfar hakan ya bashi damar hango tulin gashin kanta data daure da ribbon daya ta cukwuikuyeshi dan wai Da Kitso wata Goggonsu zata mata aka fasa. Hannunta riqe da lemon Cocacola guda daya se glass cup ta zauna akan kujerar datake fuskantarsa fuskar ta dai babu yabo babu Fallasa.

Lemon ta tsiyaya ta mika masa dan tasan shine favourite dinsa a da bata san yanzu ko ya dena sha ba se ya karba yana ci gaba da binta da kallo fuskarsa dauke da murmushi. Kallo sa ita ma tayi, yayi kyau sedai Hassada amma a fili seta tabe baki sannan tace
"Next time ka ringa saka perfume kadan please wannan yayi yawa har ya fara hawamin kai karshe ma yasaka mutane mura". Seda ya ajiye kofin hannunsa sannan yace " Don't worry inada wani a cikin mota bari sena dakko miki dama naji kin cewa Maryam kina so" seta harareshi bata dai ce masa komai ba.

Shiru ne ya ratsa tsakaninsu, ita ta sunkuyar da kanta tana wasa da zoben hannunta tanajin yanda idanuwansa suke yawo akanta gaba daya sr takejinta uncomfortable amma ta dake kawai.

"Hamdah Gani Abdul'ahad na qara dawowa a karo na biyu neman auranki ina fatan zaki amincemin a yanzu". A bazata taji maganar tasa, seta saga kanta dan ta tabbatar shi dinne ko wani daban. Yanda ta ga fuskarsa ya tabbatar mata that he mean what he said nan da nan zuciyarta ta shiga tsere har yayan cikin ta suna hautsinawa. Ina ma yazo a lokacin daya dace, ina ma yazo sati biyu kafin wannan ranar da babu abinda ze hanata karbarsa da zata yarda ta aureshi kodan ta samar wa zuciyarta abinda take so amma yanzu its too late. Bazata rushe abinda ta faro ba kai bama ze yuwuba.

"Hamdah ke nake sauraro kinyi shiru" ya sake fada yana kallonta. Seta dago idanunta da suke burgeshi, irin kallon nan dayake so takeyi masa, kallo ne daya nuna tsantsar kaunar da takeyi masa wanda ita kanta bata san tana hakan ba seta fara magana A hankali
"Sir...."
"No call me by my name, call me Abdul'ahad i prefer that mothan anything ban taba jin sunana a bakinki ba dan Allah ki fada na tabbata se kinfi kowa iya fadin sunan".
Murmushi kawai tayi a ranta tana cewa " kaman yanda kafi kowa iya fadan sunana ba" a fili kuma seta ce

"Abu Hamdah dafarko zan fara da gode maka akan son da kace kana yimin, i know you have loved me from the beginning sedai kamar Destiny have other plans for us. A wancan lokacin kazo a lokacin da muka rigada mukayi alkawarin aure da wani, duk da da ace kai din ka nuna dagaske kake da abubuwa zasu iya canzawa kilan da yanzu.." Se tayi shiru. Gaba daya ya tattara nutsuwarsa akanta jin tayi shirun ya saka shi gyara zamansa sannan yace
"Da yanzu me ina jinki" seda ta danyi shiru na wani lokaci sannan tace
"Kilan da yanzun ni na haifa Little Hamdah" ta qarasa maganar in a low tune. Se yayi murmushi sannan shima kasa kasa kamar yadda tayi tata maganar yace
"They were so many complications in Hamdah's existence ni ma i wish you were the one nasan da banyi undergoing all that i went through ba, nasan da dakanki zaki haifarmin Hamdah kaman yanda ake haifan kowanne Da a duniya".
Kallon rashin fahimta take yi masa, ta fuskanci ya qara birkicewa gaba daya yanzu se ya ringa wasu irin maganganu da ake kasa ganewa amma koma yaya wannan ba shine matsalarta a yanzu ba, yana zata fahimtar dashi akan basu da sauran chance kawai shine a yanzu.

" Hamdah nasan zaki so kiji abubuwan da suka faru dani a cikin wadannan shekarun, bana buqatar sanin naki dan dukkanain wani motsinki tamkar a gaba kikeyins. Kiyi hakuri Banyi miki gaisuwar Rasuwar mijinki ba naji duk abinda ya faru kuma nayi masa Addu'a insha Allah ya dace da rahamar Allah dan ko ba komai ya kula dake, ya kyautata miki kwatankwacin abinda nima zanyi miki amma bazan boye miki ba Naji dadin yankewar zamanku, na kuma yi farin cikin barewar cikin jikinki dan nasan wannan ze iya maida ki a ahalin gidansu. Nasan zasuyi amfani da abinda zaki haifa daya daga cikinsu ya aureki dukda nasan ke baki san manufarsu akanki ba. Bayan faruwr wadannan al'amuran Nayarda ubangiji ne ya dubeni ya kuma amsamin roqona ya dawo dake cikin duniyata, nasan zakice meya hanani dawowa tun lokacin da kika gama iddah, Uzurine babba.
Matata Ni'ima tana cikin wani hali da bazan iya tsallaketa a wannan lokacin ba saboda tana matuqar buqata ta a kusa da ita. Na zauna da yaqinin zaki jirani tunda katangar dake tsakanin mu ta rushe amma kawai sena samu labarin shigowar wani daban cikin rayuwarki da har kin bashi damar zamowa miji a gareki. Hamdah Abdurrahman be dace dake ba kwakwata bakuma dan inasonki bane yasa nake fada miki hakan karkiyi tunanin kamar ina so in batashi ne a gurinki ko daya nasanshi tun ba yau ba. Tare mukayi karatu dashi a UK. Nasan Abdutrahman baya Shan giya bakuma ya neman Mata amma yana da aqidojin da suka fi wannan muni, boko ta ratsashi yanda baki tunani badan qarfin addu'ar iyaye ba ina Tabbatar miki za'a iya wayar gari ma yace ya bar duk wata ibadah saboda tsabar yanda Yahudawa suka shiga jikinsa. Base na tsaya miki wasu dogon baya nai ba Kije kiyi tunani akan abinda na gaya miki ki kuma dubawa kanki abinda yafi, karki maimaita kuskuran da kikayi a baya".

Doguwar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta janye tagumin da tayi, mutum biyu kenan, Anty Zahra ma bata son auran nan dukda ita tunaninta Matarsa ne bawai shidinne yake da matsala ba amma mene gaskiyar abinda Guru yake gaya mata a yanzu? Ita dai a sanin da tayiwa Abdurrahman bataga wasu dabi'un yahudawa daya fada ba yanzu. Ita har mamaki ma takeyi kamar yanda yace yayi rayuwa ne cikin turawa tsahon 15 years amma babu wani abu dayake nuna hakanc a cikin halayyarsa. Se kawai zuciyarta ta raya mata yana gyara tasa kasuwar ne kawai bawai dan haka abin yake ba dan haka ta dago ta kalleshi sannan tace

"Nagode kwarai ina ma ace ina da yanda zanyi sedai ka makara ko nace mun makara, maganar da mukeyi yanzu Jibi ne daurin aurena da Abdurrahaman taya kake tunanin zance na fasa..." Seya dakatar da ita ta hanyar cewa
"Aa Hamdah karki aikata abinda zakizo kina dana sani daga baya karki maimaita the same kuskure da kikayi dan a yanzu sedai a kirashi da ganganci". Mikewa tsaye tayi dan tasan inta ci gaba da zama tabbas zeyi galaba akanta, in har taci gaba da jin muryarsa to kuwa ze rusa duk wata dauriya tata a yanzu se ta shiga girgiza masa kai tana cewa

" Ba kuskute nayi ba na auri Abdulmalik saboda ina sonsa shima yana so na, rabuwar mu daga Allah ce wa'adin zamanmu ya rigada yaje qarshe ban ta ba daukar tsangwamar da ahalinsa sukamin a matsayin wani abu ba, na dauketa kawai a qalubale da kowacce mace take samu a zaman auranta. Idan kuma na Auri Abdurrahman kwatankwacin haka ta sake faruwa dani" seta dakata tana kallon yanda ya birkice lokaci daya shima ya tashi tsaye. Kallonta yakeyi yana haddace duk wata kalma da take fada se yace
"In hakan ta sake faruwa me za'ayi?"

"Zan dauki hakan a Matsayin _RUBUTACCIYAR QADARAH_ ta da ban isa na kauce mata ba zan kuma rungumeta hannu bibbiyu na biyata akan yadda aka rubutata ta". Cikin tsananin tashin hankali yace
" Aa Aysha karkice haka dan Allah ni kuma fa menene makoma ta a wane matsayi nake a gurinki".
Seda ta mayar da hawayen da yake shirin zubo mata sannan tace
"Ka jirani, inaji a jikina qaddarar mu daya zamu rayu qarqashin inuwa daya wata rana komai zahon lokaci indai muna raye" tana kaiwa nan ta shige gida ta barshi a tsaye kamat bishiyar da aka shuka. Kwakwalwarsa ma taqi yadda da abinda ta fada taqi bashi damar yin tunani akai, se ya zame hular kansa ya shiga fifita da ita saboda zafin da yake ji. Beji sallamar da Yaya Baffa yake tayi masa ba seda ya taba shi tukunna.

"Abdul'ahad Galadima is this you? dama kana nan or wait me ma kakeyi a gidanmu" Yaya Baffa ya jero masa tambayoyin, Abdul'ahad was his childhood friend tare sukayi Nursery da primary school a Cairo. Karfin hali kawai yayi suka gaisa da Baffa amma ya kasa amsa masa tambayar meya kawoshi gidan se kawai yace masa wata yarinya ya gani ta bashi wrong address seda yazo yaga ba a gidan take ba, sallama ya masa bayan sunyi exchanging contact ya tafi yana shiga motarsa wasu hawaye masu zafi suka fara zubo masa.

Meyasa bashida sa'a a rayuwarsa? Meya sa haryau ya kasa mallakar zuciyarta kenan yanzu ma ze qara rasata a karo na biyu? Yana ji yana gani wani ze mallaki abinda yake nasa. Ikon Alla ne kawai ya kaishi gida. Kamar mace haka ya saka Ammi a gaba yana mata kuka

"Ammi bata sona, she rejected me for the second time Ammi me na ragu dashi da bazata soni ba? Ammi meyasa bazata gane itace cikon rayuwata ba? Ta kuma zabar wani da be kaini ba a karo na biyu" haka yaringa sambatu Ammi na tausarsa. Ta rasa wannan wace irin jarabawa bace yake fuskanta akan wannan yarinyar. A da tayi zaton ze manta a ita tsahon wadan nan shekarun amma setaga abin kamar Tishi, kodan yanayin dayake ciki ne da Matarsa? Tasani Su Fatima sunyi gaskiya Abdul'ahad ba yaro bane yanzu, ko beyi wa kansa wannan tunaninba ya kamata ita tayi masa. Yana da buqatar macen da zata kula da shi ta bashi farinciki irin wanda ko wanne lafiyayyen Namiji yake so, to Amma wannan auran ma da yaya akayi shi? In ta tuna gumurzun da aka sha kafin ya yarda da auran Ni'ima bazataso a maimaita irinsa ba. Ita dai bata da sauran wani abu Addu'a kadai zata ci gaba dayi masa tasan ita yafi buqata sama da komai.

Akan cinyar Ammi yayi bacci, haka ta zauna tsahon dare tana gadinsa kamar jariri cikin zuciyarya tana saqa abinda take gani kamar shine mafita kawai, zata nema masa auran wannan Yarinyar da kanta duk da yace bayason hakan, bayaso wani ya shiga cikin maganarsu yafiso ya samu soyayya da amincewarta da kansa amma bazata biye masa ba dole tasan abinyi.









🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 3⃣2⃣

Karfe 4 na yammacin ranar Alhamis tayiwa Ni'ima a gidansu Hamdah kamar yanda sukayi alkawari. Halinda mijinta kuma yayanta ya shiga a jiya shi ya qara qarfafa mata gwuiwa akan abinda take da niyyar yi. Ita da kanwarta Safeena sukaje wadda batasan menene sukaje yi ba ta dai ce kawai tazo ta rakata gidansu wata friend dinta suka bar little Hamdah acan gidan nasu.

Tana zaune ana mata baqin Lalle bayan tacire Ja dayayi bala'in yiwa Fatarta kyau a daya daga cikin dakunan BQ saboda cikin gidan ya fara cika da Jama'a yan biki kamar ba bikin bazawara ba. wayarta ce ta dauki qara, me lallen ce ta daga tareda saka mata wayar a speaker. Bayan sun gaisa ne take shaida mata gata a gate dan haka ta tura Amrah ta shigo da ita.

Ko kadan batayi tsammanin ita bace har fuskarta ta kasa boye mamakin, guri suka samu suka zauna Safeena da bata da baqunta tashi ga zuzutun lallen da ake mata
"Kai amma yayi kyau sosai se kace Amarya" ita dai Hamdah Murmushi kawai tayi a zuciyarta tana tunanin meya kawo wannan matar kuma. Dambun naman da akayi na gara da soft drinks ta saka aka kawo musu har lokacin Ni'ima batayi magana ba saboda ganin me lallen da kuma Inteesar Matar Yaya Baffa da ita ma aka saka mata lallen.

"Kiyi hakuri kinzo kuma ina dan uzuri i thought i will finish before the time i gave you but unfortunately kuma na zarta". Murmushi Ni'ima ta mayar mata kafin tace
"Ba komai zan iya jira dukda ina dan sauri nabar yarinya a gida".

" Ba matsala we can talk here ai" hamdah ta fada ganin Ni'ima na kalle kalle. Dukda abin be mata ba, she wanted them to have some privacy suyi magana ta fahimtar Juna amma tasan in tace seta jira har an gama zata bata lokaci. Little zata iyayin kuka and shi kansa ze iya kiranta at any time ta dawo gida dan haka tacewa Safeena ta fita waje dan bata so taji maganar da zatayi, tasan ta da surutu zata iya zuwa ta gayawa Mamansu da sauran Sisters dinta, tana qunquni tana komi ta fita dan ita lallen ma taso ayi mata.

Bayan Safeena ta fita ne ta koma kusada Hamdah ta zauna suna fuskantar juna, kallon inda Inteesar take ta sakeyi dan batajin ta me lallen sosai kilan yayarta ce dayar ko kuma ita ce Amaryar da ake bikin.
"Karki damu feel free to talk we are all family" Hamdah ta fada tana mata murmushin karin qarfin guiwa. Seda ta yi shiru for some moment sannan ta fara magana

"Hamdah nasan zakiyi mamakin ganina and you will ask your self on what is so important that i want to discuss with you" se ta danyi shiru kadan. Hamdah data tattara hankalinta gaba daya akanta tace
"Yes ina jinki"
"To cut it short Hamdah mijina nazo nemawa auranki". Ba Hamdah ba hatta me lalle seda ta saki kwarkwaronta tsabar mamaki karma Inteesar taji labari abinka da Yar jarida seta yi saurin qarasa sabule lallen da takeyi ta matso kusa sosai kodai kunnenta ne bejiyo mata daidai ba. In between dariya Hamdah tace

"You must be kidding wane mijin naki kika zo nemawa auran wa?"
Seta gyara zamanta cikin son nuna mata da Gaske ta keyi tace
"You know who I'm talking about, amma tunda ta haka kika biyo muje a baki sanshi ba Ni Ni'ima nazo Nemawa Mijina Abdul'ahad auranki ke Hamdah".
Seta dakata kadan tana kallonta sosai, lallai matar nan ta samu matsala in ba haka ba ita zata zo nema ma mijin nata ma aure? se kawai ta daure fuska dan abin ma yafi kama da rainin hankali, dakatar da me lallen da mamaki ya hanata ci gaba tayi ta gyara zamanta sosai sannan tace

" Shine ya aiko ki?" Ta tambayeta cikin tsare gida alamar babu wasa. Seta girgiza kanta
"Ba shi ya aiko ni ba nina aiko kaina sabida naga hakan....."

"Dakata malama, be it shi ya aiko ki ko ke kika aiko kanki ki koma I'm not interested in your Goddam Husband inda nasan ke ce da tun farko ban answer wayarki ba" Hamdah tayi maganar cikin dacin rai wanda a qarqashin zuciyarta wata wutar kishi ce take ci. Tun asalin Hamdah me zafin kishi ce bare a yanzu kuma akan abinda take so.

"Ki tsaya mu fahimci juna Hamdah dan Allah, Yaya Abdul'ahad loves you so much. Dukkan shekarunnan hankalinsa da tunaninsa yana kanki, Hamdah aure kawai nake amma bansan menene soyayyar miji ba, mijina ke yake so ke kadai yake kallo a matsayin mace". Shiru ne ya ratsa palour, ita Ni'ima tayi shiru ne sakamakon wani abu da taji yana taso mata me daci irin yanda takeji duk lokacin da ta tuna mutumin data fi so akan komai da kowa wata yake so daban, ita kuwa Hamdah jikinta ne yayi sanyi qalau da kalaman Ni'iman. Me lalle da Inteesar kuwa sunzama hoto kowa ta bude baki tana sauraron ikon Allah to da alama wannan matar bata san meyake faruwa ba.

"Hamdah ki taimaki ne ki auri mijina muna buqatar ki a cikin rayuwarmu auransa ne kadai zesa nima nasamu farin ciki kamar kowacce yantacciyar Mace. Hamdah hatta Yata tafi so da dokin ganinki sama da kowa a duniyar nan, kinsan meyasa? Saboda da sunanki ta fara koyon magana. Hotonki yazamar mata kamar ibadah a kullum shi take fara kallo har ta fahimci shi kadai ne abinda yake saka Babanta farin ciki. Hamdah kinga irin murnar da tayi ranar data ganki as small as she is 3years amma ta iya gane abinda take gani a hoto tun daga ranar kullum kukanta a kawita gurin Namesake bata a sauran magana se taki ko dan ita bazaki taimaka ki aureshi ba".
Tuni hawaye sun gama wanke mata fuska. Duk wata kalma da take fada jinta take kamar tana tsirawa

Please Login or Register in order to submit comment