Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tana jinsa ya na buga kofar amma tayi banza dashi dukda wata zuciyar tana ce mata "ki bude, idan har hasashenki gaskiya ne tun wuri kusan abinyi ai bake kadai ya shafa ba" har ya gaji ya rabu da ita Seta durqushe a gefen gadon ta fashe da wani irin kuka kaman Marainiya. Wace Qaddarar ce kuma haka ta ke neman tarar da ita?
"Ubangiji ka sa ta zomin da sauki ka bani abinda zan iya" ta fada cikin wani irin sauti me ban tausayin. Tarin nadama da dana sani suka lullubeta, tana ganin tafi kowa laifi dan ita ta bashi fuska kuma be taba mata dole ba, duk tsiya dai itama tana bada Hadin kai tunda ba daureta yakeyi ba. Soyayya batayi mata rana ba a wannan lokacin meyasa tun farko bata hango wannan illar ba? Ita yanzu ya zatayi? Batasan iya lokacin data dauka ba da abinda ya faru bayan nan qarshe kawai ta farka taganta cikin jikin Abdul'ahad.

Baza ta iya fadar ainihin abinda ya faru ba amma ta tabbatar wani al'amari ya kasance. Yanda yake sunkuyar dakai ya kasa koda kallonta seta mike kawai kuka na neman kwace mata ta fada cikin bathroom. Seda tayi me isarta sannan tayi wanka ta dauro Alwala lokacin karfe uku harda Rabi na dare ta fara jero nafiloli, Irin kukan da take yi me ya daga masa hankali dan ya banbanta dana ko yaushe. Yana kwance yana kallonta afarko ya zata sabon halin data koya ne se daya ci gaba ya gane akwai abinda yake damunta. Jira yayi ta sallame Raka'ar da take ya dagata cak ya aza kan gadon yabita ya kwanta a gefenta hannayensa biyu cikin gashin kanta yana ya mutsawa. Addu'oi ya ringa tofa mata a hankali ta fara tage kukan se Ajiyar zuciya datake saukewa ajere ajere har ta nutsu lokacin har an fara kiraye kirayen Sallar asuba.

"Hamdah ki dena yawaita kukan nan bashida kyau fa dan Allah" ya fada cikin sauti me rauni. A maimakon shirun da tayi seya dawo mata da abun sabo. "Waifa kilan akwai dan sa ko Yarsa a cikinta" tausayin kanta dana Abinda zata haifa din suka kamata seta sake fashewa da wani sabon kukan tana miqewa zaune daga jikinsa. Kaida Guiwa ta hade ta ringa kukan me ban tausayi shidai yana zaune ya kasa tabuka komai dan besan me kuma aka mata ba. Tambayar duniya taqi magana karshe tace in yana so tayi shiru ya fita yabar mata dakin. Allah sarki seya miqe shima duk ya sukurkuce lokaci daya. Idonta biyu akayi sallar Asuba, tana idarwa ta dora daga inda ta tsaya da kukan karshe se Bacci barawo ne yak nasarar saceta tana kukan.

Karfe 2pm har ta gota sanda ta farka. A maimakon kan sallaya data kwanta seta ganta akan Gado lullube da Duvet. Kallon dakin tayi sosai seta gane dakinsa ne saboda kamshinsa daya kama ko ina wanda ada take bala'in so Amma yanzu se taji yana neman tayar mata da zuciya. A sanyaye ta zubo fararen qafafunta qasa tana kallon ko ina na dikin, Fitsari datake ji ya sa ta miqe ba shiri ta shige toilet din seda tayi shi sannan ta samu nutsuwa, cikinta ne yayi wani kuka seta fita zuwa kitchen dan har wani jiri jiri take ji. Ta rasa me yasa kwana biyun nan in taji Yunwa duk seta firgice. Yoghurt ta samu 2L data daga se robar ta sauke ta nemi kujera ta zauna tana sauke numfashi minti biyu Amai ya taso mata seda ta Amayar da yoghurt din tas sannan ta kuskure bakinta da ruwa ta fita daga kitchen din tana jin kaman Aman ya tafi da duk wata kasala data tashi da ita. Sallah ta farayi dan lokaci ya tafi sannan ta shiga gyaran gidan da kuiya tasa kwana biyu bata yi ba. Seda ta gyara gidan tsaf ta bi duk wani lungu da sako ta saka turaren wuta masu azabar qamshi nan da nan gida ya dau harami kaman wani gidan Amaryar Kanuri. Kafin ta gama aikin har Magriba ta kawo kai.

Wanka ta shiga, jikin pant dinta taga digon jini kadan kadan lokaci daya ta saki wata irin wawuyar ajiyar zuciya tareda Hamdala a fili sannan ta shiga wankan hankali kwance bata da sauran tsoro kuma. Tsaf ta shirya cikin wasu pencil skirt baqi da peplum blouse pusher pink da suka matuqar yi mata kyau. Kayan daidai jikinta ne amma yau setaji sun dan takurata musamman rigar amma setayi tunanin kodan tana period ne a wasu lokutan boobs dinta na dan expanding. Baqar hula ta saka bayan ta tattare tuli gashinta ta feshe jikinta da wasu turare da Mumcy ta sako mata cikin wasu saqo da aka kawo mata baya bayan nan, ita lamarin Mumcy daga mamaki ya koma bata dariya kuma. Ubannin kudi take narkawa tana hado mata kayayyaki kamar wata me aure, da tayi magana se tace wai ai gara ta shirya jikinta batasan sanda auran zezo ba. Sa'a daya kusan duka kayan kwadayi ne dan haka tana ci iyakar karfin ta tunba yanzu data koyi dan banzan kwadayi ba. Kamar ka saceta ka gudu haka ta kame kan kujera tana shan Banana smoothie tana kallon wani comedy se dariya takeyi. Can kasan zuciyar ta tunani ne fal Ina ya tafi tun safe?
Motsin kofa da taji ya sakata juyawa da sauri suka hada ido daidai sanda yake shigowa. Ledoji ne manya manya a hannunsa ya ajiye a palour ya juya ya kuma fita. Seda ya shiga da kusan guda bakwai sannan ya kulle kofar ya jingina da ita yana qare mata kallo, duk wata gajia daya kwaso ji yayi ta ware lokaci daya, salon gayun Hamdah ze zautar dashi. Se ya bude mata hannayensa tareda langabar da kansa cikin sigar roqo.
Bata san meyasa bata iya tsallake tarkonsa ba, duk yanda taso ta dakatar da kanta amma ta kasa dan wani irin feeling takeji akansa. Tayi missing Hug dinsa ba kadan ba kaman ta shekara bata jita a jikinsa ba. Seta miqe tana tafiya kaman tarwada cikin salon da bata san illar dayake masa ba. Lalacewa yayi da kallonta har besan sanda ta qarasa ba seda yajita cikin jikinsa tukunna.

"Ya ilahi kabarmin yarinyar nan" ya fada daidai sanda ya dagata sama dan ya fita tsayi sosai yai mata wani mugun riqo da seda tayi yar qara "wash" seya sassauta yana qara rungumeta a jikinsa. Kamshinta yake shaqa lokaci daya ya fara neman birkita masa kai, seya sauketa tareda jinginata da bango ya mata rumfa lokaci daya ya shiga kissing nata. Bata hanashi ba dan itama ji tayi a lokacin tana so, seda ya gaji dan kansa sannan ya dagata cak suka qarasa cikin palour ya zauna tareda dorata akan cinyarsa yace
"Babe zaki kashe ni da gayu, kinyi kyau over" ya fada yana jan dogon hancinta, fari tayi da ido batareda tayi magana ba aransa yace
"She is damn beautiful Allah sa duka yarana suyi kama da ita" a fili kuma se yace
"Babe I'm hungry me kika ci" ya qarasa yana shafa cikinta da yake a lafe kamar bango. Seta dan yamutsa fuska dan ita ko sunan abinci ba wai tafiya son ji bane yanzun, barta da kayan kwadayi setace
"Yoghurt da rana kuma dana sha ma nayi amai se kuma yanzu wannan" ta qarasa tana nuna masa Cup din da take shan smoothie din. Rungumeta ya qarayi yana cewa "Sorry me ya saki Amai, kwana biyu naga kaman baki jin dadi Babe we need to go and see doctor ko" ya qarasa yana kwantar da kansa akan chest dinta. Se yaga kaman they are much more fuller yanzu kai kusan duka jikinta ma ya sauya Like her Hips sun qara fitowa skin dinta ya qara kyau abubuwa da yawa dai shi se yanzu ma yake noticing

"No ba se naga Dr ba may be kodan period en da nake ne" muryarta ta katse masa tunani. Lokaci daya jikinsa yayi sanyi, "so she isn't pregnant?" Ya tambayi kansa. Dagata yayi ya dora akan kujera sannan ya miqe duk yanda yaso ya boye damuwarsa amma ya kasa se kawai ya shiga tattara Ledojin daya shigo dasu yace ta taso ta taya shi. Suna kitchen din suna jera kayayyakin, shopping yayo mata babu ce kawai babu a ciki ga uban kayan kwalama tuli duk wanda ya gani seda ya siyo mata. Lura da yanayinsa daya chanza a ranta ta fara tunanin to meya same shi of sudden haka kodan tace masa tana period ne? Seta tabe baki kawai tace "Jarababbe ai nama godewa Allah da yazo din" a ranta, haka suka ci gaba da aikin har suka shirya komai a inda ya kamata. Noodles ta dora masa tunda yace yana jin Yunwa. Kamshin dafuwar daya fara tashi ya hautsina mata ciki ba shiri ta fara sheqa Amai dama tun dazun daurewa kawai takeyi.

In banda sannu babu abinda yake jera mata harta gama ta wanke bakinta ya kamata zuwa palour duk yabi ya rude. Ruwa ya bata mara sanyi tasha sannan tace masa wai zafi takeji, seya zuge mata zip din rigar gaba daya sannan ya qara masa sanyin Ac ya koma kitchen din ya juyo musu noodles din a zatonsa wai ko yunwa ce ta sakata Amai ai tun be qarasa inda take ba tana shaqar warin tamike da sauri ta fada toilet ta ringa sheqa wani Aman. Dama ya lafiyar kura bare tayi zawo nan danan ta daga masa hankali, kuka haiqan takeyi dukda ya fita da Noodles din ma gaba daya daga gidan seya tasata a gaba kawai yana kallo ya rasa abinyi ga yunwa ga kuma damuwarta. Seda ta qaraci kukan dan kanta ta sulale a gurin da take bacci ya kwasheta.
"Rigimammiyar kawai" ya fada daidai sanda ya dagata ya qarasa cire mata rigar ya kwanatar da ita akan gado yana qare mata kallo yanda jikinta ya qara cika masha Allah, se yai saurin jan Duvet ya lulluba mata gaba daya ma ta korar masa Yunwar dayake ji se kawai ya shiga wanka. Sallar Isha ya yi sannan ya fita daga gidan gaba daya yaje yaci abinci tareda qarasa hado abubuwan da yake buqata dan gobe jirgin 8am zebi zuwa Nigeria.

Sanda ya shigo ta farka tana zaune tana kuka akan gadon, seya dafe kansa da duka hannu biyun a ransa yace "Nikam naga abinda ya isheni yau" a fili kuma ya qasa tareda hawa kan gadon ya janyota jikinsa
"Me kuma ya faru yanzu?" Tuttureshi ta shigayi daga jikinta dan sam bata qaunar turarensa yanzu, ganin yana neman Lips dinta yasa ta hadiye kukan ta mike da sauri tana cewa "Babu komai Allah dama tashi nayi ban ganka ba shine naji tsoro".

"Lallai Yarinyar nan nidin da kullum akewa ihun kwarto shine yau harda kuka ba'a ganni ba to gani nazo me zaki bani" ya qarasa yana qoqarin riqota. Se tayi saurin yin hanyar toilet din tana cewa "Aa ba komai dan Allah yunwa ma nake ji get me something before i fresh up"

"Something like" ya tambayeta yana miqeqwa tsaye

"Anything creamy or spicy, and some Ice cream please"

"Yes Ma" ya fada yana ficewa daga dakin ita kuma ta shiga wanka. Wani dadi ya ringaji yau ta sake dashi sosai, motarsa ya dauka ya shiga gari nemo mata abinda zata cin.

Abin haushi abin takaici yanda ta saka pad din haka ta cireta, a ranta se tayi tunanin ko dan maganin datasha dazu da mararta na ciwo ne dama haka yake mata wani lokacin se ya dauke mata period din gaba daya. Wanka tayo da Alwala ganin dare yayi ta sallaci Magriba da Isha se zuga Hamma take dan wani bacci takeji bana wasa ba. A gurin ta dungure ta farayinsa ko cikakkiyar addu'a bata samu damar yi ba.

Minti 30 ya dawo gidan, kaza ya siyo mata dan ya lura kwana biyu ta qulla da nama, safe rana dare cinsa take, ranar nan tsakar dare ya kamata a kitchen tana cin sandararriyar kaza daga freezer se kuma Ice cream da Pizza duk ya hado mata. "Ikon Allah wani baccin ta koma kenan" ya fada sanda ya shiga dakin, seya ajiye kayan hannunsa ya dagata cak tareda zare mata Haijab din jikinta. Kamar wata yar maye haka ta ringa layi, ya sakata tsakanin cinyoyinsa yana bata Naman a baki dan ya lura gaba dayanta se a hankali kuma. Seda ya tabbatar da ta qoshi sannan ya dagata cak ya kaita Toilet ya wanke mata baki, ba maganar nighty kawai ya kwantar da ita akan gado ga jikinta daya ji kaman da dan zazzabi se ya rage mata gudun Ac ya tattara kayan ya fita dasu. Seda yayi wanka sannan ya kwanta yajata cikin jikinsa sosai yana jin yanda zafin jikinta yake ratsashi. A sonshi daren yau ya zama na musamman amma in yayi kaman be kyauta mata ba dan da Alama bata da lafiya se kawai ya rungumeta ya musu addu'a kafin shima bacci ya daukeshi.

Ko da Asuba seda yai dagaske sannan ta tashi da kuka kamar qaramar yarinya. Wanka ya sata ta farayi dan zazzabin ya sauka se kuma gumi dayaga tana tayi sannan sukayi sallah. A jikinsa ta jingina yana karanta musu Azkar tana maimaita wa dan yaga yau kam se godiyar Allah Sallar ma yinta kawai akayi, shirun dayaji ne ya sakashi leqa fuskarta ba shiri dariya ta kwace masa ashe ita bacci ma take shaqa abinta harda bude baki. Azkar dinsa ya qarasa sannan ya dagata ya maida ita kan gadon ya shiga wanka shima. Samun guri wai gada a kabari sega Guru nawa Hamdah wanka Dan yaga lamarin nata se an hada da du'ai kuma kamar wadda akaiwa Allurar bacci haka take ta fama. Shi ya shafa mata mai ya dauko mata wasu riga da skirt na Atamfa dan shigar na bala'in burgeshi a jikinta amma qememe skirt yaqi zuguwa. Ta gwada Atamfa sun kai biyar amma duk ba wanda ya mata daga Wanda riga tayi kadan se wanda skirt yayi kadan ya tasata a gaba kuwa yaringa tiqar dariya ita Kuma tana kuka wai tayi qiba abinda ta tsana shi kuma yace wai tafi kyau haka shi Allah sa ma tafi haka nan gaba, ganin yana shirin bata lokaci ne ya sakashi dauko mata Doguwar riga ta Atamfa yace ta saka kila kayan ne suka matse bawai ita ce tayi qiba ba sannan fa ya samu lafiya tayi shiru shima se riga Zip yaqi zuguwa saboda me Breast cup ce, Wannan karan dole ya hadiye dariyar sa dan dagaske take kukan yanzu. Abaya ya dauko mata kawai ta saka yace suje dan har 7 tayi shida ze tashi 8am. Seda suka fita palour taga jakunkuna sannan ta fara raba ido tana tambayarsa ina kuma zashi.
Hannayenta ya riqe cikin nasa yana murzawa in a way that yasan bazata iya tsallake masa ba ya fara magana

"Babe i will be going to Nigeria, Ni'ima bata da lafiya and she will really need my attention but i promise i won't stay long zandawo wurinki kinji Honey Bunch".
Yanda yake shafa hannunta da kuma tasirin idanunsa akanta suka hanata musa masa, se kawai ta gyada masa alamar toh amma can qasan zuciyar ta damuwa ce, kishi da tunanin kewarsa da zatayi. To wai ma ita a wa ta hanashi tafiya? Ni'ima fa matarsa ce ta sunna ita kuma fa? Hannunta daya matsane yasa ta dawo daga tunanin da ta tafi, "muje kiyi dropping dina a Airport seki dawo da motan but please babe ko coffee ne ki hadamin da Egg in ci abinda hannunki ya hada kafin na tafi" seta karyar da kai tace
"Abdul'ahad coffee kawai I can't fry egg zanyi amai". Seda yaja hancinta sannan cikin kwaikwayon maganarta yace
"Ok Hamdah coffee din ma ya isa". Sakin sa tayi ta shiga kitchen, 5 mins ta fito da Mug me dauke coffee se qamshi yake gaba daya fuskarta a hade saboda yanda kamshin ya addabeta,

"Barakallahu fik" ya fada sanda ya karbi mug din sannan ya zauna akan kujera tareda dorata akan qafarsa yana zuqar coffee din yana kallon fuskarta se wani cin magani take, Mug din ya kai mata baki tayi saurin kawar da kai tareda toshe hancinta. Seya saki baki yana kallonta, this days she is becoming strange. Haka dazu ta hanashi saka turare qarshe se Nata ta bashi ya fesa wai batason warin turaren sa da iya saninsa for this six years ba abinda take so kaman wannan kamshinsa. Haka ya qarasa suka jero abin sha'awa suna tafiya. Ita ke Driving har suka qarasa Airport din, seda ya gama komai sannan sukayi sallama.

Wani irin hug ya mata me tsayawa arai kafin yayi brushing lips dinsa akan nata, ya lura daurewa kawai take amma any moment zata iya saka masa kuka.
"I love you so much Babe ki kulamin da kanki" ya fada tareda kissing goshinta, ganin yanada kusan minti biyar kafin jirgin ya tashi ya sakashi rakota har cikin motar ta zauna. Envelope ya dora mata akan cinyarta cikin sigar tsokana yace "ga kudin cefane nan, in be isa ba a ranta min inna dawo sena biya and please a rage wannan baccin a kuma ringa zuwa makaranta" dukan wasa ta kai masa ya janye tareda rufe mata kofar yana dariya. Harta juya motar yana daga mata hannu ita ma haka ta juya tabar Airport cike da kewarsa. Ta rigada ta afkawa soyayya a karo na biyu wadda take da tabbacin tafi ta farko zafi. Haka ta koma gidan cike da kewarsa Allah ya taimaketa tana zama kan kujera baccin da take ta dannewa ya kwasheta.






🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 4⃣4⃣


Nigeria.
Karfe 2pm Jirgin British airways ya sauka a filin sauka da tashin jiragen Sama na Malam Aminu Kano dauke da Passengers ciki harda Dr Abdul'ahad Abdullahi Galadima. Tafiya yakeyi cike da kuzari yana ratsa Aiport din zuwa inda ya tabbatar da Fahad dayazo dauka sa yake jiransa. Cikin doki suka rungume junansu, Fahad daya bude ido sosai yana kallon Aminin nasa daya tasamma shekara ne ganshi ba yace
"Man wai dama kai Fari ne? Kai tsaya ma kana kallon kanka a Mirror kuwa" daidai lokacin da suka zauna acikin motar, murmushi kawai yayi dan yasan dole ze sha tsokana shi kansa yasan ya canza ba kadan ba.

"Aboki gaskiya Amaryar nan ta iya kiwo dan Allah in zaka koma zan bika nima naci girkinta ko zanyi kyau haka'. Duk wasa yakai masa yana dariya yace
"Tunda ance maka abinci kadai nake ci nayi kyau din ba to abinda yafi qarfinka me dan iska". Dariya sosai Fahad yayi harda dukan steering yana cewa "Ina yafi qarfin ubana ma balle ni ai sekai".

Seda suka hau titi sosai fuskarsa ta chanza da yanayin damuwa ya kalli Fahad dake tuqi yana murmushi shi kadai yace
"Fahad how is Ni'ima doing? Why on Earth ma da zaku boyemin ciwonta?" Kallonsa kawai Fahad yayi ganin lokaci daya fuskarsa ta chanza daga farin ciki zuwa damuwa yace
"Wallahi nikaina ban sani ba, i was out of town for some assignments seda na dawo Ammi take sanar dani but she warned me kar na gaya maka". Shiru yayi yana kallon window babu wanda ya qara magana har suka shiga cikin Asibitin AKTH. A kofar ICU inda yake da tabbacin an kwantar da Ni'iman ya tarar da Ammi, Khadija, Hafsa se Umma wato mahaifiyar Ni'ima da yayyenta Maza guda biyu da Amna qanwarta suna zazzaume akan qatuwar dardumar da suka shimfida. Sannu da zuwa suka shiga yi masa gaba daya yana amsa wa dakyar yanemi guri kusada Umar Yayan Ni'ima ya miqa masa hannu sukayi musabaha haka Naseer ma. Hibbatullah yarinyar Khadija ta dane cinyarsa tana masa surutu ya shafa kan yarinyar kawai ba tare da yace komai ba.

"Babana ya hanya ya Amarya? se kuma aka taso ka ba shiri ko seda nacewa Yaya ta barka kawai tunda dai wannan ciwo ne sedai kawai a nema mata rangwame da ga Allah babu ranar tashi" tayi maganar cikin lafazin da yake nuna rauninta. A cikin Yayanta Allah ya dora mata qaunar Ni'ima se kuma ya bata ita me tsananin larura da tun tana yarinya ake saka mata ranar mutuwa gata dai har yanzu se wahalar kawai ake sha.

"Aa Umma ko daya dama ina shirin zuwa dan na samu sauqin ayyukan da nakeyi kuma se wannan din ta kasance yanzu me Dr din yace akan condition dinta?"

"Likitan yana ciki yanzu ma tunda muka zo babu wani takamaiman bayani da suka bada in akayi magana se suce wai seka zo ko Umar sunqi magana dashi" tayi maganar cikin son kecewa da kukan tausayin yar tata. Se sukayi shiru gaba daya, Ammi dake kallonsa tundazu abu biyu na yawo a zuciyarta. Na farko jin dadin sauyin data gani a tattare dashi wanda ko makaho ya shafashi yasan an samu sauyi sosai a rayuwarsa se kuma tausayinshi akan halin da matarsa take ciki, fitowar likitance ta katse musu magana ya miqe da sauri ya qarasa inda yake ya bashi hannu.

"Mr Galadima muje office dina ina son magana dakai" binsa bayan Dr Isha yayi yana tafiya kamar mara laka a jiki, gaba dayansa yayi sanyi. Rashin lafiyar Ni'ima na matuqar daga masa hankali. Seda ya zauna sosai a kunerar dake kallon likitan sannan ya turo masa folder dake dauke da hotuna na scanning. Beyi magana ba yajasu ya fara dubawa a hankali cikin zuciyar sa inbanda salati da tasbihi babu abinda yake a zuciyarsa wata zufa tana keto masa. Hotuna ne kusan guda biyar wanda aka mata.

"Am Galadima I'm sorry to say but she just have a little chance of survival, ka duba pictures din nan sosai(ya miqa masa wasu copys daban) kayi comparing da scanning results dinta. Dayan kidney dinta ta harbu, and about her heart" se yayi shiru.
Abdul'ahad daya zuba masa idanunsa da suka chanza kala tsabar tashin hankali dukda Split din dake bada sanyi a office din amma zufa yake yace "Isah what happen to her heart?"

"Nasan tun bayan surgery din sun gaya muku she might only live for a year and cikin ikon Allah ta zarce hakan getting to two years now but I'm sorry Abdul'ahad" se ya dan dakata yana jin nauyin maganar daze fada sannan yaci gaba.

"Ni'ima is on life supporting machine, zuciyarta ta kumbura kaman yanda ka gani anan and bugun zuciyarta yana raguwa a duk minti. Already ta dena zuqar numfashi da kanta forgetting the Cancer issue..."

"Will shut the goddamn explanations and go straight to the point Isah" yai maganar cikin daga sauti tareda dukan table din da har seda Dr Isah ya miqe tsaye. Gaba daya jijiyoyin kansa sun miqe, wani irin tashin hankali da tsoro suka rufeshi lokaci daya. Dama haka akeji kana ji kana kallo ace maka zaka rasa wani naka? "Innalillahi wainnailaihi raji'un Allah kabarmin Ni'ima kar ka dauketa yanzu" abinda ya fada kenan tareda komawa ya zauna akan kukerar ya dafe kansa da Hannu bibbiyun jin yanda yake barazanar tabewa gida biyu. Beji ban hakuri da lallashin da Dr Isah ke masa ba, se ya mike kamar wani mayunwacin zaki ya fice daga office din baya ko ganin gabansa sosai. Duk irin maganar da suke masa babu wanda ya tanka har ya shige dakin da Ni'iman ke kwance cikin halin rai ko mutuwa.

Badan numfashinta dake kai kawo ta cikin computer ba babu yanda zaayi yace tana da rai a lokacin, se kawai ya zauna akan kujerar da aka ajiye jin kafafunsa kaman bazasu dauke shiba. Hannunta dake maqale da allura ya kama ahankali yana shafawa zuciyarsa na masa wani irin quna, be tabbatar yana son Ni'ima ba se yau dayake neman rasata. Kallonta yake yi a cikin watanni kusan hudu da be ganta ba ta chanza sosai. Fatarta da take chocolate me duhu yanzu gashi har tana neman finsa haske tsabar yanda ta dashe kai da gani kasan bata da isashshen jini. Seya kwantar dakansa gefenta yana qoqarin danne hawayen da suke neman zubo masa. Jiyakeyi daya na da iko da ya dauke mata ciwon jikinta amma baze iya ba. Tausayin kansa harda na Little ya kamashi, se ya shiga karanto addu'oin samun sauqi yana tofa mata.

Besan iya lokacin daya dauka ba yana zaune a gurin kasancewar ba'a barin mutane na shiga da yawa sedai one at a

Please Login or Register in order to submit comment