Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuce har cikin dakin mahaifnsa Jin ko ina shiru sai glsses dinsa dayake kan mirror..zama yay akan kujera a gefe haka yana jiran fitowar sa da alama toilet ya shiga,yana Nan zaune sai gashi nan ya fito da towel a hannun sa yana goge ruwan da suka manne ma jikinshi da baqin gemunsa dayake sheki,sallama sukayi ma juna saida ya zauna tukuna ya rusuna ya fara gaidasa yace mufrad yaa baka fada min kana zuwa ba ba dazun Nan mukayi waya ba?,.yace eh Abbu dama naga kamar Hakan zaifi ne naji kanacewa dukanku baku da lokaci shine nace since am free bari nazo na karbeku..
Dan Kyabe baki yaa sheik yay yace"...I'm glad..dama andameni da kira a chamber then u take over gida yayi kyau ko?..kara duban dakin yay da gefen idanunsa sann ya gyada kai yana murmumushi yace eh yayi..
So when are we all coming back?
Yakai sati? Batare daya dubesa yace "zaima iya fi..sabida akwai yan uwana da zasu zo suma zasu zauna tare damu nadan Wani lokaci
Da sauri muffy ya dago kai yace suwaye kenan?yace daga wajen ta bangaren mahaifina ne,kanwar mahaifina ne Anty adada da kuma mahaifiyar sa Hajiya Goggo kasan itama ai tana raye saidai tun kuna kanana rabonku dasu shiyasa ma bazaka wayesu sosai ba,muff Yace ohh tou ..Allah ya kawo su lpya..yaa sheik ya cigaba da shirin sa baice mai uffan ba sai Can ya juyo yace kana da lokaci sosai ne?kanshi ya Dan shafo not so sure ya amsa yace I think so..Ajiyan zuciya yaa sheik ya sauke sannan yace "mahaifiyarka bata kusa saboda ayyuka sun dan mata yawa,dama itace da take lura da komi game da karashen ginin gidan nan,toh yanzu dai angama komi bansan ya zaka yi ka tsara wa kowa sashen sa ba..
Kai kam ai zakayi hakuri yanzu ka koma can gidanka a maitama tunda duka mundawo nan abujan inaga ai babu wata matsala ko?
Gyada kansa yyi a sanyaye Yace eh Abbu Hakan ma yay sannan ya mike tsaye toh Barinje inga mai zan iyayi,yace ok Allah ya taimaka yace Ameen daga Nan ya saka Kai ya fice a dakin.

Fitarsa keda wuya ya bazama cikin gidan yana zagayawa tare da maaikatan ganin gidan mai girma ne sosai harma ya zarce gidansu na kano,Anan Kusan sashuna shida aka tsara da alaman wanna Karon kowa zaman kansa zaiyi,Yana cikin tantance girman kowani sashi saiga fitowar mahaifinshi wanda yayi matukar kyau acikin suturar sa ta manyan kaya dark brown shadda mai tsada da uban garen ta wanda tasha adon zare mai aji da burgewa..
Waya ne a kunnen sa Dan haka mufrad yay shiru baice masa komi ba tukun harya kammala yana katse wayar ya juyo da Dan Murmushi akan fuskar sa ya dube mufrad din
Yace DR MEHRA ne fa ya kirani akan zancen dawowar IMAD Nigeria, so ni zan wuce office.

Dan dariya muffy yyi yace har yanzu imad baison ya dawo ko?nidai Allah karya hadamu dashi dan wallhy saiya dawo Dan dolenshi,he is not serious yaza ai mutum yaki zama a countrynshi ya manne ma na mutane? yaa sheik yace hmm IMAD problem be,nadai barshi da Dr Mehra zaijo dashi sunfi kusa ai uhmmmm Yawwwa thanks for reminding kaga wancan side din?...yace eh yabi inda hannun yaa sheik din ke nunawa tacan gefen dama ne Inda aka dire wata shimfidadfiyar 4 bedroom flat duplex,yace
Nan ne bangaren IMAD...Amma bazai shiga yanzu ba saiya kawomin matar aure, daga anyi aurensan anan zai zauna..
Dariyar mufrad ne ta fadada yace "what?Abbu shine ni zaa fitar Dani waje sai akawo mai katon kan Nan cikin gida ko?..hmm mai katon kan ai kawun ka ne,kodan kaga ya maida ka abokinsa toh kwaji dashi I'm in a hurry saina dawo yace ok safe dad..daga haka suka rabu yanata kallon ficwwar motar mahaifinsa har aka rufe kofar gate din gidan sannn ya maida hanklinsa kan abunda yakeyi ya cigaba..


_The Old vincarage hilltop ht34. United state of America_ .


Wani kyakkwar saurayi ne ya fito daga wajen shan iska cikin sauri yana tafiyar sa mai cike da aji ayayin da body gurds dinsa guda biyu suke binsa abaya,da sauri dayan body gurd din ya karasa ya bude mai motar
Sannan ya shiga
wani dan wahalallen tsaki yaja ya gyara zama ya rungume hannayenshi,wajen 20min drive sukayi sukai parking agaban wani hadadden gida bachelor's reserve da sauri qurds din suka fita kafin ma subude mai kofa har ya bude da kanshi ya watsa musu harara ya wuce yay cikin gida yabude door dinsa yashiga.

Babu kowa a hadadden palorn San dayaji adon black and white chairs kominshi is black and white,da alaman kalan dayafi so kenan musamman sabida profession dinsa na law, dan shi international law ya karanta sannan Allah ya bashi ilimi da daukaka ya zamto one of the toughest barister wayanda Sam basa failing client dinsu most espicially incase mai zafi ne, stairs yahau da sauri yana atishawa har ya bude wani hadadden daki da komi na ciki yakenan white color, zama yayi kan Royal bed dinshi yanajin sanyi sanyi har cikin kashin shi hannun shi ya mika zaidau remote din AC dake kusa da pillow atake wayarshi ya hau ringing daukan remote din yayi ya kashe ACn mai gaba daya kafin yaciro wayan daga aljihunnsa daure fuska yayi ganin sunan Hajiya jasmine kamar zaiyi kuka ya kara akunne baima jira mai zatace ba yace "ADDA JAS..I'm on it wallhy yanzu zan kirashi sabida shi fa nabar wajen shan iska na dawo gida

Daga dayan bangaren hjy jasmine tace "Do that now Imad..Kar ka maida mutane yan iska..call him now..yace ok
Katse wayar yy yana takune fuska Saiga kiran dr Mehra ya shigo kaman wanda akace dole yay picking call din ganin wayar na neman katsewa ya kai kunnen shi yay shiru batare dayace komiba cikin kwantar da murya mutumin yace "yanzu fushi kake da kowa ko barrister?" shiru yayi baice komi ba ahankali mutumin yace "haba gusar yaki Duk wanda ya fara dakai bazai Kare lpya ba, yaro dan maman shi toh maza tashi kadau rigan sanyi kasaka kaji Mr rashinji, dan murmushi yayi dan yasan cikeda tsokana yafadi hakan. Ya dade harde hannun sa cikin shwagaba kamar yaro mai fushi.doc Mehra ya kara maimita mai "tashi kasaka right now my friend Ina sane da cewa kaje ka shiga ruwan pool a sanyin ure insane aren't u?!..da sauri imad yace" enough enough doc naji" yafadi yana sauka daga kan gadon yakarasa gaban wani vintage wardrobe dake manne da bangon dakin yana kallon kanshi ata mirror jikin har Wani jajir hancinshi yay sabida sanyi wani burton ya danna kofar wardrobe din yabude mai gaba daya ya ijiye wayan akan gadon yaciro wata dark grey sweater mai shegen kauri da kyau yasaka tamai mugun kyau yakara fito da hasken fatarshi, daukan wayar yayi yamaida kunenshi doc Mehra baima barsa yaha nunfashi ba yace "kasaka sweater?" gyadamai kai yayi yace "eh" yace yauwa ko kaifa kaga yanzu sanyin zai ragu ai,and pls stop acting stubborn kaji ko?I know you kuma nasan bakason iska dayawa abu kadan mura mura, you need to be taking care of yourself okay..
"kaga saisa ma yaa Sheik ya ke son lallai kadawo Nigeria kawai hankalinsa zai fi kwanciya"

Imad kaman zaiyi kuka yace "yaa sheik yace in dawo nigeria ko?Doctor... saurin tsare sa yyi yace "common Imad ,don't Doctor me my friend" why don't y just listen?

cikin muryanshi mai bala'in dadi da taushi yace
"Nigeria weather is super harsh nime zanzo inyi muku a Nigeria?gaskiya I don't wanna come back...eva,..please nika kyaleni"
Doc Mehra baice mai uffan ba ya cigaba da kukkuni
"Haba doc Dan Allah Ka shawo kan yaa sheik mana, Kai fa babban amininsa ne Kuma yana jin shawararka,pls tell him I don't wanna move over there . cikin Dan kakkausar murya doc yace "anki a gaya masa kuma bazamu kkyaleka ba saikuma yay shiru kafin yadan sassautar da murya yace "haba sarkin yaqi,mai sunan Abba na kafa gama Duk Wani cases dinka kagama komi thy ve missed you badly baka tunanin Amma?(hjy sadiqa), kadawo gida let her see you koda itama zataji dadi aranta,
I know well dat jasmine tana da nata familyn she is doing alot kaine ya kamata kazo kusa kana kulawa da mahaifyarku hjya saddiqa,just lemme arrange everything idan akwai any available flight gobe gobe kabiyo kadawo gida,I assure I akwai manyan cases a inda cibiyarka take, kuma kana dawowa kaga saimu nema maka mata kai aure abinka ko ijiye?"

kwanciya yayi akan gadon yaja bargo ya lulluba kansa tareda lumshe idanun sa tsammmm sann ya gyara wayan akan kunnenshi yace "nifa kadena min maganan aure, banaso,wallh idan shizakamin bazan ma dawoba,meye kuma aure?I'm sure wannan hadin baki ne,hajiya mama ita ta kawo maganan Nan ko?kafada mata nifa ban shirya aure ba,ni ina zankai wata mace?women dat are soo fake nd lousy, I just want to focus on my career bana son arika squexing min kwakwalata da shirme....Murmushi kawai doc Mehra yy Jin shirmen San
Oho Amma dai koba dade ko ba jima za'ayi ko?dukanmu muna mararin muga aurenka imad zama haka Nan babu dadi,ka dubi mufrad yanzu don't u rhink he has become more responsible daya aje mata?
Ko kaima baka so arika kimanta ka ne

Wani Shiru yay alaman maganan ma ta ishe sa...
Doc yace kadai dawo goben pls
Yace a'a
Zan dawo Amma ba a gobe ba
Yace to jibi.
Yace a'a kuban Nan da kwana uku...
Yace to shknan Allah ya kaimu

Part 1 IS FREE,TUKUICI NE GAREKU MASOYA NA U CAN READ IT HAR ZUWA INDA ZAMU TSAYA,SAIDAI CIGABAN SHI NA KUDI NE,PLS SHOW SOME LOVE AND SUBCRIBE.

the ACCESS FEE IS 300 NAIRA ONLY
VIA 0152983148
MOH'D SULE SURAYYA GTB.
OR katin MTN vtu tran via 08060712446

Screenshot ur evidence to SURAYYAHMS 08060712446

OR MAMAN MUBENA
08036651119.






*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


Part1:chapter 12
*A Moment in hell.*



_Ivy cottage U.S.A_
_Morning 10:30am_

Cikin mugun firgici rufaida ta farka jin ta kafe waje guda ko musulmin motsi ta kasayi,Wani dishi dishi take gani a idanunta ayayin da kanta yake juyawa cikin Wani matsanancin zafi da ciwo ga uwa uba yunwa daya gama nakasata,ganin Inda taken wanda baiyi kama da Inda aka ajiyeta daxu ba yasa ta tashi zaune a firgice tana kallon wajen,tamkar bayan gida hake yake babu gado babu kujeru sannan da katako kawai aka zagayeshi,dafe bangon katakon take Koda zata iya lekawa ta waje

Ɗigowar wani abu a saman goshinta kamar ruwa yasa taɗanyi ƙarfin halin aza dan'yatsan'ta guda asaman goshin ta dan lakato abun Sai cin karo tayi da wani irin jiniii da sauri ta ja da baya inda santalelen hannun mutum ya sulalo kasa ya fado ajikinta,Wani irin kara ne ya sufce mata cikin tsananin razana duban gefe da zatayi kenan taga fatima kwance nashe-nashe a cikin jini,babu kafa da hannayenta,an jingene ta a saman katakon har an mata yankan rago

Yankar jiki tayi ta fado kasa Cikin matsanancin tashin hankali ta buga wata irin kafurar kara mai hade da ihu nan take ta zame ta tafadi kasa kwance sumammiya..
Minti biyar mai kyau batayi ba taji ana janta waje da qarfi acikin sauri,da kyar ma ta iya finciko kanta daga suman ta bude idanununta Jin maganganun su takeyi a sama sama da yadda suke ta kwashewa da mahaukciyar dariya suna famar bidiri
Alhaj baturen ne agaba yana Jan rufaidar da kansa yana fadawa thugs dinsa yadda ya kashe Fatima sabida taci amanar sa,bakin sa harna Tara yawun Kwadayi yace yau miyan taushe za'ayi masa da naman cinyoynta Wani irin sheke dariyar su kawai sukeyi tamkar ba mutane ba.

Dayan yace boss
Meyasa ba a cire kanta ba?
Ko anfasa dantsawa ne..
Yace a'a,tare da sake wata muguwar Murmushi ya juyo yana kallon rufaida "tukuna,Muje backyard zakuga yadda za'ayi da shi we need to teach her some lesson
Wani Ihu suka kaure dashi Suna ce mai sai oga,by then rfaida ta dawo cikin hanklinta sosai Dan dariya da ihun nasu ma kawai ya isa ya jefa ka cikin Wani mummunan hali

Har gaban Wani old dumb dake bayan gidan suka jata isar su keda wuya ya jefata kasa yabi ya kwaso ta ya damke Gashin kanta tana layi ya gurfanar da Ita a rusune.

Hawaye ne kawai suke saukowa daga cikin idanunta dan hatta karfin yin Ihu ko magana ta kasa samun shi atattare da ita,addua kawai take Allah yay gaggawan daukar ranta in Hakan shiyafi mata alheri.
Dan kuwa tabbas ta cire rai ga rayuwa.

Wasu manya manyan fatanyoyi da axes taga katten mazajen sun dauko
Kirjinta kamar zai tarwatse da matsanancin tsoro ta gama bari cewa lokacin ta me itama yaxo Hala tunda ya kashe Fatima itama Hakan za'ayi mata
Wani kukan ta kara barkewa dashi tana jujjuya kayinta cikin baqar dimauta mai nuna tsantsar rikicewar yanayin da zuciyarta ke ciki

Banda Allah babu abunda zuciyarta yake kira,gaba daya tarasa Inda zata aje kanta Wani irin matsanacin rawa jikinta yakeyi,kawai tana gurfane ne Amma ita kanta bata San Wani kalar nau'in gushewa hankalinta yayi ba..

Wani irin gaafffff aka sauke dukan guduma agabanta sanda ta razana tayi tumbul taja da baya,kara fincikota yayi ya tursasa agaba tana kallon abunda sukeyi da alama Rami suke hakawa agabanta
Dan karamin ditch haka wanda tabbas kasan binne abu za'ayi,saide bata San me za'a binne ba shin sauran dead body fatima ne ko ita?cikin wannan tunanin ta kara zautar da kanta..

Da Dan fadi suka haka ramin dake basuyi shi yy zurfi sosai ba,Suna kammalawa aljai bature ya juyo ya kalleta yace
"Ki kalla Wannan shine makomar wanda yaci amana ta" Kaiwa nan ya juya yana mai nuni da gangar jikin fatima..Kinsan wannan matar?
Rufaida dake cikin tsananin dimauta gyada kanta kawai tayi Dan bazata iyama Furta kalma ko daya ba,"..Wani dariya ya fashe da shi,"..yace..tun tana yar shekara 5 na samo ta,iyayenta ne suka ban ita da hannun su a kyauta Dan inbasu kudi nikuma nayi mata adalci namaidata yata shine ita kuma yau zata saka min da cin amana.

U made killed my doughter..
Azaba mai tsanani zan maki sannan in fanshi ladan aurena
Kafin in jefaki a rayuwar datafi dacewa dake.

Wani kakkarfan numfashi ne ya kufce mata a hnkli tana hawaye tace' Dan Allah kayahakuri kaji tsoron Allah ka kyaleni

Baima kulata ba ya juya kansa sabida tabbas yanayinta akwai ban tausayi
She look too sick,too weak and too scared gaba ki dayanta arikice take babuma alaman hankli atattare da ita

Ya kallo thugs dinsa fuskan sa a daure yace..."Bring d traitor foward..

Nan da nan suka dauko gawar Fatima wanda take nan daga kafada sai Kai da jiki babu hannu da kafa jininta ne ako ina
Ya barbaju

Hannunshi yy stretching aka miko masa katoton guduman dake hannun thug dinsa
Ayayin da saura biyun suka je dauko akwatin gawa daya umarce su dauko

Juyowa yy ya kalleta ganin kanta a sunkuye tana ta kuka,irin kukan Nan na na shiga uku kukan sallamewa da rashin samun mafita.
sawa yy aka baje masa kan Fatima sannan ya dga Rodin sama ya buga guduman akan nata sanda kan ya faffashe,atake atake rufaida ta yanke jikinta ta fadi Dan ko mutum mai sauran hankli bazai iya jumre kallon abunda take Gani ba,debarta sukayi suka cusa ta a
Cikin akwatin gawan,daga Nan ya urmarce su da cewa su barta anan har saiyaje ya gama sauran deals din sa ya dawo

Musamman yau ya ware ranan ma rufaida ita kadai

Yaune Ranan da zai
Walakanta ta,yayi yadda yake so da jikinta sannan yayi mata azaban da har agaban Allah saita ji shakka da tsoron nunasa.

Da yayi niyyar kasheta ne Amma saiya fasa ganin yarinyar zata iya jawo masa kasuwa saboda ya lura tana da zurfin ciki da wayo,ahakan ma bakaramin buri ya dora akanta ba..
Dan haka daga wannan satin shikadai zaina yin sex da Ita idan yaga ta bude sosai yadda zata iya daukar kowani namiji zai bada ma'aikatan sa su dad'd'ana ta,in harta rayu daga nan saiya jefata cikin kasuwancin sa.


Kano state, nigeria.
9:am Saturday morning Zayd matazu residence..


Da misalin 9 na safe Wasu manyan manyan SUV jeep guda biyu bakake kiriin masu fidda wata uban sheki suka shigo harabar gidan sukayi parking ayayin da driver yay saurin saukowa kasa ya bubbude musu kofofin su Yana mai rusuna kansa akasa cikin yanayina tsantsar girmama wa

Wata dattijiwar mata ce wacce bazata wuce 62yrs ba ta sauko kasa cikin shigarta na alfarma Tasha baqar leshinta exclusive hole lace daba atula mai tarukucen design ajiki ba,style dinta style din wata arniyar dogon riga ce ta bubu daya mugun amsar hadadden dirin jikinta na manyan mata wayayyu masu iko da kansu wanda babu wani alaman rama ko alaman talauci atattare da su,ko inanta a murmure yake fatar jikinta acike tam da tsoka ga Wani irin sheqin da fatar jikintan yakeyi tsaban yaji wanka da tsantsar hutu babban mayafin ta na Dubai asalin babba tadada gyara wa zama akafadunta ayayin da Wuya da hannunta suke fidda wani uban walkiya sanadiyar hadaddun gwalgwalan saudi gold data kawata su dashi,driver su wanda suke cewa malam liman ya Taho da gudu ya amshi jakarta da wayoyin ta ya rike mata su yana binta su abaya

Cikin tafiyarta na kasaita ta karaso har Gaban dayan motan wanda har yanzu mutum ne aciki Amma bai sauko ba,tana karasowa gaban murfin motar taja ta tsaya tana kallonta

Wata tsohuwar mata ce fara sol da ita aciki wanda akalla zata haura shekaru tamanin da takwas zuwa casa'in Dan kuwa ta tsufa sosai bana wasa ba,kafafunta da hannunta Duk sunyi nauyi idanunta sunyi ciki ciki saboda tsabar tsufa Wani dankareren medicated glass ne ta toshe kwayar idanun nata dashi
Itama leshin ne ajikinta nata yellow an mata dinkin buba da zani kafarta cikin wata flat shoe mai kama da Dunlop slippers da kyar ta motsa jikinta sabida tana da Dan kauri dayan matar ne ta riko hannunta domin ta taimaka mata zuwa kasa,kan kace Wani abu kusan rabin ma'akatan gidan sun kewaye su da gaisuwa

"Barkan ku da zuwa Hajiya Goggo"
Allah yasa anzo a lpya...kusan kowani ma'aikaci yana Miko gaisuwarsa cikin yanayin girmamawa da nuna farincikin sa da ganin su

"Sannunku dai"
Sannunku...Ta fada da kyar sabida tsufar dayake shake mata murya tana yi tana Dan waving dinsu da hannu,
dayan matar data riko su tace An sameku lpya?duka Sukace lpya lau ranki shi dade hjiya Adada..Nan ta juya tana kallon driver su
"Mallam liman sai ka babbasu na shan ruwa bari na shigar da mama ciki.
Da sauri Ya rusuna kai yace toh hajiya Allah kare ki angode,Duka sauran ma'aikatan dake washe baki suma suka bibbita da addua,ya bude jakar ya fidda sabbin bunches din dari biyar biyar ya shiga rarrabamusu 5k a hannun su tuni wajen ya kaure da godiya da yabo kowa na washe baki

Itakam Bata kara ma kallonsu ba ta riko mahaifiyarta suka nufi ciki A hankli suke tafiya sabida yanayin jikin tsohuwar sai an bita a hankli musamman ma da bata fiye son zaman waje daya ba,jirgi suka biyo suka zo kano daga katsina amma still saida jikinta yayi tsami da kyar take Jan kafarta take takawarta a hankli


Suna daf da bude kofar gidan sukaci Karo dashi yafito fuskarsa dauke da kyakwan murmushi kallo daya zakamai kasan yana tsananin murna da isowarsun,da sauri sauri ya karaso da alamn an riga an sanar dashi labarin isowarsun ne Wata iriyar shigace a jikinsa shiga mai ƙara daraja da kamala farin yadin chairman ne a jikinsa wanda a ƙalla zaikai Darrikan kudi,ya ɗaura baƙar khufya akansa da wata muguwar al'kebbarsa baƙa mai faɗi,Hakan yasa Fuskarshi nan ta fito ras sajenshi da gemunsa mai tsananin kyau yayi lib a fuskarshi sai sheƙi yakeyi..Wajen tsohuwar ya nufa ya rikota ajikinshi ya rungumeta tsam wacce already tana
Hade idanun ta da nashi ta fara sauke wasu maqudan hawaye, cikin muryanta na tsufa da bai fitowa sosai"tace'..zaidu?"Wani shafa kansa tayi a lalume tace "Alhamdullahi,saita juya ta kalli yartan dake famar Murmushi tace Alhamdull Adada yau gani a gidan zaidu..yaa sheik dake Murmushi yace "Ina matukar farincikin samun isowar ku
Ta juyo cikin muryan kuka"Ohh zaidu,toh Ina yayan naka ya baka fitomin da suba ?nima inga jikokin Dana,Ohh Allah yajikan mahaifin ka dikko, Allah yasa dikko yana cikin inuwar Rahman ubangiji Allah yay ma albarka kaji Dan jikana,da sauri Ya dago kakar tashi ta cikin tsantsar tausayinta da kaunarta dake mamaya aransa yace "Allah ya kara miki tsawon rai hajya,in Ina ganinki tamkar Ina ganin Abba na ne,Allah ya masa rahma matsanancin kukan ta kara fashewa da shi Tace uhmm uhmm karka tunamin,dama can saida yace min mama insha Allah zan barki da wanda zaina kulawa Dake,sai ga Nan an haifoka, zaidu Allah ya sa maka albarka Allah ya kau da idon maqiya akanka ko ayau na bar duniya ai naga baya...cikin kukan take fadan haka tanayi tana share hawayentan da gefen mayafinta.

Kara rungumeta ajikin sa yayi
Da Murmushi akan fuskar sa suka gaisa da Kanwar mahaifinsan wato Hajiya Adada wanda tuni idanunta ya cikko da ruwa itama Dan sosai suke kallon yaa sheik da sigar mahaifinsa alhaji dikko sabida shi ya yakasance mutum ne mai mugun shiga rai da son kyautatawa nakasa dashi.

Cikin gidan ya musu jagora tareda da yar tsohuwar ajikin shi,ayayin da Ita Aunty adadan ta juyo da baya ta amshe jakarta da wayoyinta ta kuma umarce malam liman daya sa ma'aikatan gida sutayashi shigo da kayan su da sauran abubuwan tsaraba da sukaxo dashi

Daga cikin gidan kuwa kusan kowa shiri yake Dan yaga ya hallaro cikin babban katafaren falon sun on time,yau babu wanda bai haska yay kyau a shigarsa ba musamman ma hjya jasmine data sha Wani haddiyar malaysian lafaya dark red in colour wanda ya amsheta kwarai dagske,cikin wata golden atampa wax nazli da shukra suka sha dinkin su kowa da kalar nasa style din,shikuma keeyan ya saka light brown shadda da dark coffee cap,Dan musamman yaa sheik yasa su nazli da keeyan din suka bar schl suka taho Nigeria da niyyar suyi kwana biyar ma auntyn san sukuma samu lokacin sanin juna da mahaifiyar mahaifinsa wato hjiya goggo


Hjiya Goggo itace mahaifiyar Alhaji dikko,wanda shine mahaifin alhj zayd mataxu wanda asalin sunanta shine hajiya Ameena husaini daura.

Itama yar katsinan ce Dan anan aka haifeta ta taso tayi karatu,tayi aure,anan ta samu yayanta biyu dikko da kanwarsa mai suna fatima bintu wanda ake cewa hjya adada ko aunty adada..

Dake danta Alhaj dikko matazu shine babban da namiji hkn yasa sa shiya rike arxikin mahaifin sa ya kuma gaje shi akan harkokin sa daya bari kafin shima yazo ya barma nasa Dan wato alhj zaidu.

Ita kuma kanwarsa hjy Adada da tun tuni aka mata aure agidan sarauta ta auri Wani Dan kabilar kanuri acan jahar maiduguri sunan sa prince Shehuri bajama,,shi mutum ne mai kyau da kima a idanun jama'ar sa,so ita a maidugurin tayi rayuwarta mai gaba daya,haihuwar ta bakwai da mijinta Shehuri Amma duka yayan basa yin rai sanadiyar Allah da ya daya jefata a taskon wata muguwar kishiya wanda akecewa "yar buxuwa"
bakaramin azaban wahala hjy adada Tasha a hanun buzuwarnan ba,ita juya ce amma Ko kadan bata son hjy Adada ta haihu,daga tayi ciki sai ace Dan ya mutu,ga Wani irin sibbace sibbace da jifan aljanu da salon mugunta kala kala masu wahalar fahimta,hatta hauka saida tasa hjy Adada tayi,ta rabata da gidan mijinta kusan shekaru hudu,daga karshe da Allah yazo ya takaita muguntan tan saiya toni asirin ta alokcin da batayi tsammanin ba har Shehuri ya rubuta mata shika uku aka koreta daga masarautar batare da taci darajar samun ko asi daga arxikinsa ba,da addua da rokon Allah sai a sannan hjya Adada ta dawo cikin hayyacinta ta dawo cigaba da rayuwarta da mijinta Shehuri harta haifi yan biyunta duka mata aka samu su suna Hawwa da khadija Ana ce musu hassana da husaina,Duk da haka buzuwa bata daddara ba saida tayi sanadiyyar raba hjya Adada da yaran Nan nata wanda haryau ba aji cikakken labarin su ba duk dama antaba tabbatar musu cewa hassanan su ta riga ta mutu Amma ba akarajin labarin husainar ba.

Daga Nan hjy adada ta shiga cikin Wani mummunan hali na tunani,daga bisani bayan an shafe shekaru sai Allah ya axurta ta da Yaya maza Abuturab Shehuri wanda ayanzu aka Fi sani da uncle Shakiri da

Please Login or Register in order to submit comment