Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kodan a karbo mata rufaida,ga matsin su hajy Adada duk sunyi fushi dashi akan ya sharesu ne shiyasa yaki dawowa Abuja,Ita kanta hjya jasmine saida taji tazo har wuya da kalar rikicinsu,duk safiya intaje gaidasu sai sunta mita suna cika mata ciki da zamba da kananan maganganu,izuwa yanzu sosai ta fahimce su,boyayyr gaban da sukeyi da hajya mama sosai yake fitowa sarari ta lura jira kawai suke yaa sheik ya daqo dan komai na gidan ya dawo hannun su.

Shikansa yaa sheik baya samun kunnen jin sakat Allah Allah yake ya dawo cikin familyn sa sabida ya gama fahimta tamkar komi a tsaye yake cak shikawai ake jira a tada wani ruguntsimi

Hatta imad ma jiransa yakei batun komawa kan aikin sa,Anty fareesa ma daga ta kirasa awaya zata soma kawo masa korafi akan saken da akeyi acan gida da wayo,duk dama hjya maman ne take yawan tursasa ta..

Yaa sheik ya rasa ta inda zai fara dora tunanin sa,jiya da misalin karfe 10 ya kammala aikinsa amma bai iya jiran kowa ba by 4pm na yamma har ya tarkace komi nasa ya diro kasarsa nigeria,yana sauka a jirgi baiko isaga ofishinsa ba aka aiko mai sakon gaggayawa da cewar ana son ganinsaa babban jibiyar Aviation Administration na nigeria,ministern tsaro ta kasa dakansa yake bukatar ganinsa da gaggawa dan haka bai samu daman kirar kowa ba ya nufi federal ministry Cikin gaggawa ya isa sectery ne ya masa jagora har ciki inda ya same sa a zaune offishinsa tare da chief security of federation da manya manyan majors daga kafafe daban daban na military su biyu,sai shikansa ogansu mufrad din wato Admiral general na navyn gaba daya,ido suka zuba masa gaba daya saiyaji gaban sa ya fadi duk dama bai saka komi aransa ba,dama can dayaga kirar jikin shi yayita basa akwai wani abu,ransa ne yaketa gaya masa ba lafiya ba kuma dansa mufrad ne yaketa masa yawo akai ayanzu.

Waje aka samar masa ma musamman ya zauna suka gaggaisa da kowa a mutunce, babban ogan navy gaba daya, shi yahau masa bayanai batare da wani bata lokaci ba.Yace masa..ba wata matsala bane yasa suke nemasa ama Akwai wata lamarin datake kunnowa a kasa wanda za'a iya cema sa matsala ce kuma ba matsala ba..ta fuskar matsalar shine tsoron su gameda hatsarin datake cikin lamarin
Ata fuskar rashin mtsalar kuma shine dukan su sunada yaqinin cewa dansa mufrad ne kawai zai iya kaisu wannan babban matakin nasara a tarihin rayuwarsu dana aikisu gaba daya.

Dan haka suke mika kokon bararsu garesa daya basu cikakken yarda da goyon baya,bai wani fahimce su ba sabida sau tari sukanyi abubuwnsu da mufrad basai an shawarce shi ba,karshe dai saida minister tsaro daknsa ya kara masa da bayanai kafin ya gane inda aka dosa,bayani sosai ya masa akan last mission din da mufrad yayi dashi da team dinsa which was infact very succesful and clean.

Matukar Abun farinciki da Alfahari ne agaresa dayaji hakan,harda cewa matattarar tsaro na duniya da kungiyoyin kare haqqin dan adam sunji dadi kuma sun karrama jajircewan dan sa mufrad abun alfaharin sa.

Shi baima san mufrad yay underground mission akan lord hermain ba,the great jamaican cartel mutumin ya tsaya wa kowa a wuya dan tsaban muguntar sa,danwa mugayen kasashen da suke turnuke musulmai da innocent non muslims civilians kawai sukafi saidawa miyagun makamai da kwayoyi,tabbas da yasan za'ayi haka da wallhy bazai bar dansa ba,as an eminent judge and beurocrat, he knows it has a deadly life long consequences but Alhamdullhi tunda har anyi an kuma samu nasara ayanzu fargaban sa bai wuce nan Gaba ba,duk dama ba ya shakku yasan Allah zai kare masa dansa.

Ahaka sukayita convincing dinsa da maganganu,har saida suka sakashi ya biye musu akan wata sabuwar mission din da ake so mufrad din yay jagora nan Gaba da alama akwai hatsari aciki wanda ba a bayyana masa na menene ba..

Babu yadda ya iya musamman dayaga yadda suka nuna makurar yardan su akan dansa haka ya bada amincewar sa ya musu fatan alheri da samun nasara,ranar sai 10 na dare ya dawo gida.
fannin umma hadiza babu yadda batayi da yaa malam akan ya bar suhan ta dawo gida ba amma haka yaki mata firrrr kaf abunda take ciki na matsatsin takurawar yan unguwa yana sane amma ko ajikin sa.

sau tari anty faressar ce takanso taje har gidan yakumbo domin ta dauko rufaida dan sosai ta fahimce cewa yarinyar ta shiga wani halina damuwa dan sosai rufaida ta jeme ta rame ta fita a hayyacin ta

Duk iya dauriyar datake kkrinyi wani bin bata iyawa da tulin mugayen baki da baqaqen maganganun mutanen anguwa

izuwa yanzu kusan kowa ne ya tsangwameta a anguwar gangare an kuma hada harda tsanan da akeyi ma ummanta ana muzguna ma rayuwarta matuka.


Abu daya ne kawai yakan dakatar da Anty fareesa in ta tuna Fadan da Abbunta zaiyi inyaji anma sanar da ita labarin abunda ya afku,badon haka ba itakam ta riga ta yanke hukunci babu abunda zai hanata raba rufaida da cikin jahilcin mutanen nan,sumtimes she imagine her own self or even doughter in dat kind of situation gaba daya saitaji abun yana mugun mata ciwo har cikin kokon xuciyarta takejin tausayin rufaida,kusan zance ita da hjy mama bansan wayafi zakuwa wajen jiran dawowar yaa sheik dansu samar ma rufaida mafita arayuwarta ba.


Washe gari da sassafe yaa sheik ya farka daga bacci dauke da sallati abakinshi bayan ya kammala karanto adduar sa dayajima yanayi.."subhanAllah wal hamdullahi wallahu Akbar kafa goma,yau yayi addua mai dumbin yawa wa y'ayan shi da iyayen sa da dukkan sauran Ahalin sa musamman ma yayan shi yaa malam,ako wani adduarsa ta farkawa a bacci musamman ma irin wnan data kasance mustajaba baya iya mantawa da kowa.

Daddan Qamshin turaren humra daya tadasa a gajiyayyen baccin dayayi yasaka shi sakin wata kayatciyar murmushi,saukowa yayi a gadon yahau lekawa ta windown sanin cewa bazai wuce matar sa bace ta biyosa har kano har acikin ransa kewarta shima yakeyi sosai

Daga nan bayan yabar wajen ya nufa bathrum dinsa ya fada wanka within 40 minute har ya fito ya shirya kansa tsaf cikin wata lallausar yadi da ake kirar sa da Gorvenor wanda ko makaho ne ya ratsa ta gaban sa t tabbas yasan ansaka abu mai kyau da tsada,sky blue colour ne kalar kayan an masa dinkin manyan kaya da garershi ishahhiya gaban garen san sosai yasha adon kece raini na asalin zaren hannun baggara,ya dora da hular sa ta tandoran duk sanda yay dressing babu marabarsa da wani angon,sai sanyin nitsuwar dake tafiyar dashi,turaren sa ta creed by Ck ya shafa kadan qamshinta mai tsananin sanyi ta biye har jikinshi da numfashin sa inya shaka dantana da kama jiki sosai

Direct sashen hjya mama ya nufa dan jiya daya dawo late basu samun daman ganawa da ita sosai ba,da nitsataiyar sallamar sa ya kawo har bakin falon sau uku yana nanatawa baiji an amsa sa ba saiya dan leko kansa taciki,gani da yy babu kowa a falon ya sashi karasowa har ciki ya tsaya,karar sautin takunta yasaka shi saurin dagowa kai izuwa kan matkalar da ake takawa a kasaitance tuni kirjinshi ta buga yasan wnn yakun ta muradin zuciyarshi ce,daya hango ta dauke da tray din Abinci saida yaji wani mqudan sanyi hatta yunwar datake makale acikinshi ta hargitso,kanta ta sauke kasa tana dan murmushi tsabar farincikin ganin sa ne shimfide akan fuskar sa shikuwa sai kallonta yake bai dauke kwayar idanun sa aknta ba,maroon colour lafayar data saka ajikintan bakaramin dauke masa hankli yayi ba dan kalar bakaramar amsar kalar fatar jikkn yayi ba,har cikin falon ta karaso ta rasa meyasa yau takejin kunyar sa,kodan ta saka shi araine duk sanda yay tafiya mai nisa haka takanji duniyar gaba daya tayi mata zafi kamar yadda dawowar sa yakan saka taji sanyi da sauki,aranta bata da tantama tasan duk sanda mijinta yabar duniyar hala itama bazata iya daurewa ba zata bishi..

Wuce shi tayi ta wuce har gaban wata kayatacciyn dinning table shi kuwa Kallonta ya cigaba dayi yana bibiyar duk wani kyakkwar motsin ta dayake yawan rudashi haryau ita kominta a nitse takeyinshi tamkar wacce bata da wani damuwa, sanda ta kammala sauke manyan manyan warmers din akan table sannan ta dawo inda yake ta sameshi, acikin ladabtaciyar yanayi ta rusuna har kasa batare da ta kalle fuskarshi ba ta hau gaishe sa cikin sanyin murya daga tsayen idanunshi kurr akanta yana amsata cikin nitsuwa da jin sanyi ajikinshi mai ratsa gangan jiki,babban garen shi ya nade da dayan hannunsa sannan ya nemi waje akan 3 seater dake kusa ya zauna a kasaitance fuskar sa dauke da miskilallen murmushi yace
Ranki shi dade wai yaushe kika taho ne?murmushin itama ta saki acikin numfashi tadago ta dube sa."rankashi dade jiya na taho bayan na tashi a aiki saina biyo jirgi, private plane din mufrad ya kawoni around 11pm ma ina gidan nan, naga kanata bacci ne shiyasa ma ban dameka ba,zaman sa ya gyara yana saurarnta har sanda ta kmmala hajiya saikace wanda zaa sace miki ni bakya bari in dawo miki dakaina..tace"A'a,umarnin Hajiya mama nabi fa..yace ohh badon ni ba kenan akazo?tayi murmushi mai sanyi sosai,tun kan ta furta wani kalma ya tabe bakinsa yace nayi kewarki jasmine,wannan karon sai naji daban, hanklina gaba daya yana gida,mikewa tayi ta dawo kusa da shi ta zauna daf dashi tana dan kallon annurin fuskarshi dayake sanyaya mata zuciya
"..yaa sheik,kabi komi a hankli please..wallh,bana son kana dga hanklin ka evrything will be fine,da sauri ya riko hannunta ya hade danashi yana murxawa sabida yadda tayi maganan cikin lallami da rarrashi ya bala'in narkan dashi.yace "nagode gimbiyata,toh yaya zanyi ne? matsala goma da ashirin yana jirana hanklin bazai taba kwanciya ba,ina fatan su anty acan basu takura ki ba ko?wani ajiyan zuciyane ya kufce mata bazata,da sauri ta dauke kanta ta mayar gefe dan bataso su hade ido barema ya fahimce wani abu da sakin fuska tace,"wani irin takura kuma?even the kids are very much enjoying their company, kawai dai kasan yadda zakayi ka wanke kanka wajen su sai naga kamar hajiya goggo tana fushi dakai,kuma bazai wuce dan ka dade baka dawo gidan ba ne,ta karshe da cewa uhmm saikuma tayi shiru,kansa ya kada ya riko yatsun hannunta ya shiga murxawa anashi yana murmushi"Kekuma saiki kasa wanke mijinki ko? yar dariya ce ta kufce mata.."wallhi nayi iya bakin kokari kullum saitace laifin hajy mama nibansan mezance mata ba.. hmm kawai yace,sannan ya sauke kanshi akan kafadarta ya dan jingina da ita wanda yasaka dan dole itama ta mannu dashi sosai atare suka sauke wata ajiyar zuciya yace,"..insha Allah komi zai wuce i trust u..Tsintar kanta tayi a saman kirjinshi a hnkli ta furta Allah ya dafa mana Abbansu
kyakkwar sumba ya sauke mata a saman goshinta ita kuwa ta kara kakkameshi tanajin wani sabon kwanciyar hankli..

"Jasmina haryanzu baki gama jeren ba ko kamaki akayi wajen?ohh ni hasiya naga ikon Allah,da uban sauri hjy jasmine ta yakice jikinta anashi ta mike tsaye tama kasa furta wani kalma sabida tsallen da kirjinta yayi,ganin hjya mama dake kkrin isowa har kasa wajensu yasata jin nauyi da kunya,a hnkli take tahowada kyar da jikin tsufa,tayi kamar bata san dasu ba,Alhalin duk hirar da sukeyi a bakin kunnenta ya kare..yaa sheik ya zame a hankli ya koma kasa kan carpet ya sunkuyar da kansa can kasa,a sadade mahaifiyar shi ta dubeshi ta kuma duban hajiy jasmine din datake kauda idanun ta itama,kwafa tay ta kyabe baki "a'a kice abunda ya shanya ki kenan mana, wato kinga mijinki kin jibga min aiki a kitchen kin fito ko?..hjy jasmine tace yi hakuri mama yanzufa zan wuce saikuma ta wucen din da sauri ta nufi kitchen ta kulle kanta aciki
,tsohuwar ta kada kai aranta tace"hmm Lallai wai ita yar tsohuwar zuma,su wai basu girma ne? Ga yara gandama gandama agabansu anma jasmina tazo ta wani nanike ma dana tana matsemin shi?"A'a wallhy zaidu kam tuni ya gama aihuwarsa in ita bata gama ba saitaje can tayi wani sabon aure, tarbiyan wayannan jarabbun yaransan ma kadai sun ishe shi bare wata jarabar"..
"Ya dago kansa a nitse tamkar bai fahimce metake ciki ba,"mama na barka da fitowa,Da mamaki a muryanta tace ohh zaidu kaine anan?aina dauka baka ganni bane dakema yau matarka kawai kake kallo,adan dolen sa yay murmushi mai sauti,wnnan karon saiyaji ya kasa iya dago idanunsa sabida shi mutum ne mai alkunya sosai..yana dan murmushi yace
"Anan nayi sallama har sau uku baki fito ba,saiga ta ta fito shine muka dan zauna.."ita wadin?
Sai ya dan gyara zaman hularsa,
Wani dariya ta fashe da shi mai tattare da son ganin nashi daryar shima, tace ohni hasiya jikar malamai yau naga ikon Allah jasmine dinne yau ka mance da sunanta zaidu?Hmm Abun naku kamar dai na tababbu,shiru yy yaki yace mata komi danyasan ta da kakilar maganganu,aikuwa bata fasa ba tunda ta nemi waje ta zauna tahau masa tadin haihuwa,saiya yarasa mema zai furta sabida yasan dasu kawai take son ta kafa misali,
"Ka duba yayan faresatu yadda suka girma yanzu kaimafa ka dawo kaka,haka su nazali da keeyan zasu jajibo maka nasu shikuma mufrad dama ubanka dikko ya gado,oh allah sarki dikko allah yajikan maza shibaima cika samun lokacin haihuwar ba,dansa bai dauko halinsa ba aiga jikarsa nan ya gadoshi,anya mufrad yana ma samun lokacin wncan matarsan can kuwa"?uhmm can musu aiko a iya haka aka tsaya nabar baya.

...ni menawa aciki ma?,rabonsa fa da gidan nan tinda ya koma abuja dama bason kirana awaya yakeyi ba har gwara gwara ma imad yaron kirki toh gashi shima naga sai gantalin yke, ..yaa sheika baice mata uffan ba tasake kawo masa hirar su rufaida wanda haryau ta rasa fahimtar dalilin dayasa haryau Allah bai bawa sauran yayun rufaida haihuwa ba All of the sudden tanakan maganan then she became sudenly emotional fuskanta take ya dawo abar tausayi sosai..

Shigowar hjy jasmine da sauran tarkacen abincin ya katse musu hirarsu
Ta zuba mata ido ta gama lura jasmine ba sabawa tayi da aikacen aikacen gida ba harara ta wurga mata daga wajen"Tattaro abincin ki dawo dasu nan kasa, agaba na za kuci ni karku dattar min da waje,dama can farisatu da yayanta suke zuwa su goge min kinga ma yau basu lekoni ba,hjy jasmine tahau tattara kayan saman dinning data riga ta jera tana dawowa dasu kasa tana jerawa agaban su da saibi saibi duk saita janye hanklin mijinta dake zaune awajen,lura dasu yasa tshuwar mikewa tsaye tace bari inje in dawo ina zuwa.Tana barin wajen ya dan duka kasa ya shiga taya matarsa yin aikin yana mai ce mata sannu cikin lallabawa da lallashi,hannushi ta rike dam dam..yaa sheik kabari dan Allah bana so tazo ta kara ganinmu ahaka"baikula shagwabrtan ba har sanda ya aje two spoons a kan plate din dake agaban sa
Yace"hjy Tare dake zamuci abincin nan.
confidently ya furta wanda hakan yasata tayi lamo da fuska tana kallonsa
Cikin wata irin kasalliyar yanayi tace"Ya sheik agaban maman kuma?kabari dai sai mun koma gida acan zan maka duk yadda kake so kaji?girarsa na sama ya daga yace haramun ne in kula da matata anan ko?ni toh anan nakeso can ai duk yarane ko kinfiso muyi agaban su..batace uffan ba,saiga hjy ta sauko dada janye jikinta anashi tayi
Ta koma can gefe
Hjya da dan masifar ta da baiya karewa ta iso"ke Jasmina yada haka ya naga baki tattara wajen ba toh wallhy muna gamawa ki koma kitchen nide babu ruwana zuwanki dai gidan nan fesss yake ko yayan faresatu da suke zuwamin basamin ta'adi kamar nak.
Hjy jasmine ta dan turo bakinta gaba aranta tana dan kukkuni,shikam ma daria suke basa,haka ta gama serving dinsu yana shiru yanajin dramarsu.

Haka fir kuwa taki taci abincin dashi sukaci nata tare da hajya mama,a nitse sukecin abincin har suka kammala babu wanda yay wani kwakwarn magana..
Gudun mitar hjya maman yasa hjy jasmine mikewa cikin sauri ta hau tattare tattare ta wuce dasu in hnyar kitchen,tanajin mitar hjy kasa kasa"Zaki dawo kisame ni kuwa inbaki kimtsa min waje ba,haba da Allah jasmine ta gama lalacewa da saibin jiki kamar ba ita ba, kuma duk laifin kane zaidu
Ka sakalta matar ka abin baimaka ba ka dawo ka sakalta ya'yan ka,gashi duk saundau hanyar lalacewa, aynzu ma bana tsammanin nazli ta iya kwakran girki na abinci bare ajega ita shukra,kuma fa duk sun girma nan danan sai kaji sun kyalloro namiji sun turo mana shi ana zancen kwaba musu aure, oh ni hasiya ina zankai kaina da abun kunya gurbatacen tarbiyar ku ta zamanin nan shiyake famar tona mana asiri,to nide asiri na a rufe yake Allah dai yasani niba a haka na raineka ba,shima bukar ai bayinsa bane tayu a ruwan rubutun ubansa ya shayo baqin hali.


Dan haka itama jasmine din ta taho ayi maganar gaskiya da gaskiya tsakani da Allah,yaran nan Kaf adawo dasu kasar nan su kuyi tarbiyan mu na hausa,inma karatu ne ai akwai makaruntu,ga jamiar ahamadu bello gana tafawa balewa gana awowolo?inna kudi kake so ai akwai su birjiki aksar nan
Nide sam tarbiyan da kuka tsiro agidan ka baimin ba,idan bazaku sauya ba saina cigaba da zaman anan na tsame hannu na kaje can kaida matar ka aidama kanada sabbin iyaye acan,ace yara mata bazasuyi girki su kula da gida ba saidai suyita tsalle tsalle suna kwalliya irinta aljanu ana sakaltasu da kudi baza'a kuma kwabe su ba.
Dadai nasan Jasmine da shegen kkri amma yanzu duk tsoron bintun shehuri ya nakasata tana kallo suna gigita mata tabiyan yayanta tayi musu shiru matsoraciyar banza to wallh ni bana tsoron kowa a doron duniyar nan
In karya ne kaje ka tambaye bukar shi ai yasan halina,kaga shima din daya tafi bai kara waiwayata ba kuma ban damu ba ...

Adaidai nan ta fashe da wani rusashiyar kuka






*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


Part1:chapter 41


Juyowa yay ya zuba mata idanunsa da suka jima da sauya launi yanai mata kallon dabazai iya fassarashi ba dan har cikin kokon zuciyarshi yakejin ciwon kukan datakeyin,tambaya yay ma kansa a rude kode wani abu ya farune bayan tafiyarsa?yanzun suka gama wasa da dariya within next minute ace tsohuwa ta birkice haka?saidai abun bai wani fito masa a dunkule ba dan Sosai ya soma fahimtar inda ta dosa da maganganun tan duk akansu hajiya Adada ne, ya kuma yadda ya amince sunyi sakaci ata fannin tarbiyan cikin gida,saida bai wani yadda cewa laifin daga matarsa bane danko shi ya shaida iya bakin kkri tanayi akan tarbiyan yayan su saidai dan abunda baza'ara sa ba.

Tuni ya sauke muryanshi kasa kasa yahau rarrashin ta da dukkan imanin sa
Yana kalallame ta ta kowani hanya amma duk abanza, Borin data barke masa dashi yajanyo hjya jasmine dake can sama saukowa cikin sauri tazo ta samesu,zama tayi tana tambayar su meyafaru bata samu wanda ya amsa mata ba, ganin yadda hjyr ta birkice tana ta rikirkito da manyan maganganun da basusan farawar sa da gamawarsa ba yasa tuni itama jikinta yay sanyi.

"Ni za'a mayardani mutumiyar banza?

"Ace Kaf dinku dana haifa bamai jin magana na,baku dauke ni komi sabida kunga bana da gata a duniya bani da kowa saiku sai Allah,bukar anan ya kada rigarsa yayi tafiyarsa yace min ya fita a harkata kaima Zaidu danake alfahari dakai kana neman watsamin kasa a ido,sam ban isa dakaiba saboda kana ikirarin kanada wasu iyayen atawani waje Toh insha Allah nima zakuga gata na, kuma rana na zuwa da zaku nemi ku rasa kaida dan uwanka bukar tunda banzame muku komi a duniya ba sai gwandon shara,tana ta surutai..yaa sheik yay wani irin shiru tuno mishi da xancen illegitimate doghter sa lailaa zayd matazu datayi yasajin asalin jin karayar zuciya ,hajiy jasmine ta fashe da kuka dan sosai take ganin harzuka a yanayin hajy mama "mama dan Allah kiyi hakuri in wani laifin mukayi miki kifada mana wallhy zamu gyara,mama dan Allah kiyi hakri,ko ajikin hjy mama dan so take yau din nan ta fitar da dukann abunda yake cikin ranta inyaso kowa yaji ita bazai dameta ba, danta gama lura saken da sukeyi suna kau da ido akan abubuwan dake faruwa dasu bazai taba ficcesu ba...
Cikin kukan tace
"Bukar yafi karfina ya lalata rayuwar sa harda na yayan sa,kaima kadau hanyar hakan zaidu..wayyo Allah na,ni menayi muku ne?ina zan saka kaina da wannan tijara ba gwamma na mutu da in zauna ina kallon tabarar nan ba ! Yaa sheik ya kasa iya dago idanunshi da suka sauya kala ya koma zallan ja,tunani masu nauyi ne suka cikke birnin fadar zuciyarshi,Kallo daya zakai masa kasan shi irin mutanen nan ne da suka tsane ganin fushin iyayen su musamman ma hawayen mahaifyar shi daya mugun tsana dayake gani ayanzu.

Sai ayanzu ya yadda ya amince da cewa tabbas akwai sabanin fahimta mai nauyi tsakanin iyayen nasa harda kakn kan sa hjya goggo

Tuno da yadda kowannen su yake behaving kwana biyu daya wuce inya kirasu a waya don yaji lpyar su,wani binma hjy goggo shareshi takeyi sam bata amsa masa gaisuwar sa saidai tayi ta jefa masa maganganu marasa dadi,suma acan cewa suke bayaji dasu sabida yabiye wa uwarsa,toh gashi anan ma uwartasa cewa take yabi hudubar wayancan ya kyaleta.

Gaba daya sai yaji ya rasa meyake masa dadi,aransa ya rasa menene mafarin matsalar su da basa cika samun fahimtar juna,ko da can ma yasan mahaifyrsa itace mai yawan kauda kai da ido waidon kawai azauna lpya,amma birkicewan ta ayau ya balain tsorata shi.Does dat mean dat she cannot tolerate anyone anymore?,ta yaya mahaifyarshi zata furta masa kalman cire hannunta akansa da familyn sa gatsau babu wani shakku ko tantama,tsoron hakan sosai ya nuna anayin sa har rawa rawa hannun sa da jikin sa yakeyi shikadai,tayaya shi zai iya jure irin wannan rayuwar, itakadaice hasken rayuwan sa,itace mabudin aljannar sa,Abun yanai masa ciwo aransa matuka.dama can bai taba yin tsammanin zata kyale yaa bukar ba,duba da yadda take matukar kaunarsa take kuma masa uzuri arayuwa,amma kuma saiyaga ta aikata komi kamar yadda ta furta musu,da alama soyayyarta agare su bazai taba yin tasiri wajen aikata abunda take so ko daukar wani tsatsauran hukunci akansa shima ba,shikuma harga Allah baijin akwai abunda zai rabasa da ita har abada,yaa bukar din ma dolene yau yaje duk inda yake ya samesa su sasanta kansu koda hakan bazai samu cikin sauki ,dan tun bayau ba yake cikin damuwar rabuwarsu baiyarda da zaman da sukeyi ahakan ba yasan nan gaba wannan zaman nasu bazai taba amfanar su ba .

Cikin zurfin tunanin sa yaje jiyo yadda hjy jasmine take faman aikin lallami da rarrashinta da magiya da komi harda jan shesheka wai koda hjy mama zata sauko amma ina abun sai gaba gaba yake,duk wani complain dinta game dasu saida ta amayar dashi.

Kama daga sake kan tarbiyan yayansu,Izuwa rashin girmama zumuncin da sukeyi a tsakanin su dayake so yay qarfi.

Hjya bata dena kafa musu sharuda da dokoki da wayo ba har saida suka jiyo sallamar Anty fareesa da yayan ta sa suka shigo musu bazata,nan ma dai kamar an kunnata ta cigaba da azarbaba zance tana kwakwalo magana akan lallai tana son akwaco mata rufaida ta zauna agaban ta.

Anan nema yaa sheik ya samu daman shiga zuciyarta,tuni ya kalallemeta da cewan yau din nan shi zaije har anguwar gangare dakansa ya samu yaa malam su tattauna kodan acika mata burinta na dauko rufaida

Haka ta rinka basar dashi,ta nuna bata damu da a sulhunta ta da bukar ba itawa rufaida kawai take kkri,while azahiri kowa ya fahimce ta abunda take matikar bukata kenan taga cikakken hadin kan atsakanin yayanta da jikokinta.

Bayan fitar yaa sheik awajen aka barsu su uku agidan suna shirye shiryen tafiya Abuja nan duka suka hau hirararrakin yadda abubuwan gidan zata kasance.
Sosai hjy mama ta rinka ingixa zuciyar hjy jasmine akan ta dage ta tsaya akan tarbiyansu na nazli tanata kafa mata misalai masu mugun kashe jiki.

Tace in aka koro yarki agidan miji akan bata iya girki ko kulawa da gida ba abun kunyar akanki zai kare ke kadai,su wayanda suka lalata miki su suka sangarta su suna can daga gefe

Please Login or Register in order to submit comment