Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiru sabida tasan tabbas yaukam dama bazasu kwashe ta dadi ba sakamakon tashin datayi kafin closing hours jiya.

But what can she do?she had to leave work early jiyan sabida mahaifiyarta ne bata da lpya kuma ga yaranta a makaranta,both of them needed her urgently .

Cike da magiya tasa fuskar tausayi
"madam pls kiyi hakuri dan Allah.. ta tsuguna kan gwiwar ta tana roko
.
tabbas naomi ta fi kowa jajircewa da hakuri wajen bi da clients duk dama wasun su are rude and arrogant to her in sunzo hooking app sam basu mata da dadi Ga Aina'u bata yi ma kowa uxuri arayuwa batama tsayawa ta saurare su itadai tasan is alwys their faults

Wani bin shiyasa in abun ya ishe ta sai ta yi zuciya ta tafi bata kuma kara dawowa sai ta huce kullum fadan su da Ayn din kenan.

tsaki taja kamar batama ji metake cewa ba kasar wuya tace.. feeling like the boss hun?wai don ana yaba ki kin iya aiki msww,naomi bata fasa ba tana kan kafarta tana kan bata hakuri

Bayan cin fuska da banzayen maganganun da kyar zarah tace pls ayn kibarta tace sis kiba ta last go kawai u may still manage her Tana dai sake maimtawa wa chan wajen masu wanke public toilet za'a maida ta aikin sai a huta,useless thing,.. c'mon get out ki bamu waje ta daka mata tsawa wanda har cikin zuciyan Naomi saida tajishi but abu ne wanda ka saba jin shi don daman tasan Ayn can't do witout her barazana ne kawai da,Dan Murmushi tayi Tace..."thank u jesus,Nagode madam,I promise not to repeat dat again,am very sorry ma..basu ma kulata ba Dan kanta tasha jinin jikinta a sum sum tayi waje da sauri ta basu waje.


"Oh my god
Ayn tayi furzan iska cikin sake wata nannauya sight realive tana defe kanta lightly
"oh my god im kinda pissed off arggghh nagaji da duniyan nan wallhy

Office ba za'a barka ba gida ma?Zarah tsohuwar nan is so annoying ta karashe maganan ta feeling so disgusted tana tuno da fuskar hajya mama data tsareta ta kuma koshe ta daxu

Cike da takune fuska da yatsine Zarah tace wata tsohuwa kuma?

Dan lumshe Ido Ayn tayi tace Hajiya hasiya mana kakan muffy..

"ohhhh..that!!..Zarah tafada tana rau da idanun ta slowly looking side ways cikin yanayin takaici
' Toh meye kuma naki na cewa kin gaji naga dai ba yau tasaba ba ke dai just live ur life and karki sake mata ta dame ki ke da mijin ki ta hana ki motsawa a gidan I know all these old hags da mugun son sakawa mutum Ido..

"Espicially in anga kana zaman lpya da mijinka ma..Ayn ta karashe mgn tana mai motsawa kadan akan kujerarta cikin yanayin tunani

Cikin ran zarah tace tab dijam uhmm mssw ban da ma lokacin ku duka
Sis mance da su kawai ta fada a bayyane...

sannan ta jawo cup din juice da aka kawo tayi sipping
Tare da aje cup din tana sauke Ajiyan zuciya

ta cigaba da cewa "yawwa sis kudi nazo kibani,I need like 450k, kin gani, yau fa za'a turo min sabbin collections danayi oder tun daga dubai just cant wait to see them...

Ayn ta yunkuro cikin mamakin jin kudin data ambta tace "nagani kayan toh" Nan da nan zarah ta miqa mata wayar dadai kan wasu tsinannun kaya da takalma sa jaka, daga nan Suka mayar ma juna smiles nan suka waske suka cigaba da hirar duniyan su



Ciki harda tadin rayuwan auren su da mijinta muffy wanda Cikin mintuna kadan ta gama zayyana ma kanwartan labarin yadda sukayi da shi jiya akan gado,banda uwar shewa da kyakyata dariyar mugunta bakajin komi anan
She tot wani abun burgewa ne datayi masa hakan,ayanzu har ta saba komai sai ta gaya ma sister ta Zarah kai harta labarin sex life dinsu da muffy bata boye mata musamman in sukayi harka to ranan ba'a magana

a kullum labarin wannan sex and romance din shi ya dade yana mugun jefa kanwarta shiga wani mummunan halin son taga itama tayi aure,she is damn hyper sexual,irin wanda ko tadin sex akeyi sai sunji yarrrr ajikinsu,ita tunda taji ance capt muffy Jan namiji ne akan gado ta soma jin mugun sha'awar shigowa familyn su...
Gasu da kudi gashi ance sex game 100% full option wow hala ajinin su yake....

Tun awajen bikin su Tayi ta kokarin ta shigewa kanin captain wato keeyan, he is nice kam,sai dai he is too unreliable shifa saidai mata suyita binshi suna kiransa awaya amma shi sam baitaba bin wata budurwa ko ya kirata awaya ba,inkinzo ohonki in kin kirasa ma is all ur call,zarah har tagaji tazo ma takafarajii girman kan yin soyayya da shi sanin age mate dinta ne, gani take inta aure sa kamar girmanta ma ya fadi.

Itama Da biyu take yawan zulma sister ta Aina'u dan kawai tana bata details din sauran dangin mijintan cos she's already day dreaming about being part of thy family kota halin qaqa..

Suna cikin hirar suka kara sake wata shewa suka tafa dai dai lokacin sukaji budewar kofan office din,capt Muffy ne ya shigo fuska babu yabo babu fallasa,duka suka juyo Suna kallonsa

"Wow look who is here..What a suprise? cewar Ayn data dauke dariyarta chak tana dada juyi comfortably akan rolling chair din ta tana binsa da ido cikin mamakin ganin san.

Tuni zarah ta sauke kanta jin yadda kirjinta ya buga da karfi musamman dataga yadda kwarjini ya mamaye yanayin cpt muffy gayen yayi mugun haduwa,da gefen ido ta sake kallan sa,ganin wata sassanyar murmushin data kufce akan fuskar sa ga daddadar Gamshin turaren sa dake buso ramin hancin ta kamar ta tashi ta bingire da hauka haka take ji.

She just love irin wayyan kasaitattun mazan har cikin ranta takejin captain MUFRAD spec dinta ne,shiyasa in yana waje ta rinka satar kallonsa kenan,kai she just can help it he is damnnnnnm.. aranta she was like GOD WHEN?Atlast She cant control the feeling,tana juyowa ta gaishe sa tace ina kwana "capt muffy?...kallo na biyu bai mata ba ya amsa ta da "lpya' atakaice,sann yace..u good? Ta gyada kai..daga nan sai kawai tace musu excuse me sai tayi waje ta basu waje...

karosawa daf da seat din Ayn din yayi ita kam kallon sa kawai takeyi tana so ta tashi taje jikinshi but no,she can't gaskiya,tana mugun jin tsoron fadawa tarkon walakncin daya mata a farkon auren su,so now gani take kamar wannan kama ajin datakeyi take basar dashi shine yasa yake shiga hanklin sa har yake bibiyarta

....kallon ta kawai yakeyi closely
Can Sai ya Dan sake wata dattijiwar Murmushi dat is sooo noughty,irin wanda bazaka iya sanin meke mind din mutum ba, hakn yasa ta shagala da kallon dimples dinsa dake lotsawa duka biyu duk da ma bai murmusan sosai ba..

She quiclky moved uncomfortably Dan Kar abun yayi affecting dinta,tasan shi sarai yau baqi ne gobe jaa,, zata kara matsawa baya da shi ya Dan dafata ta,ji kawai tayi harya riko habanta da tafin hannun sa,ya dago fuskart sama Suna facing juna,after like 1scnd ya bata wani hot french kiss mai dumi akan labbanta

Wani irin dadi da sanyi ne ya shiga mamaye ranta 2 minutes tana juya harshen sa cikin nata tana jin mugun dadin kiss din amma data tuno waye shi sai tayi saurin katsewa da cewa"ya isa haka ni ya ishe ni zaka goge min lips stick dina na....
Tureshi ajikinta tayi tana yi tana dada duban bakin ta akan screen din computer taga ko jan bakin ya tabu?

murmushi ya sake cikin sanyin Muryan sa mai dadi yace" Ayn ni zan tafi abuja daga nan zan wuce united states just tot u shud know, Hala bazan dawo da wuri ba.

Ta kalle sa take rahamr dake kan fuskanta ya dauke chak kamar bata taba dariya ba,kiss ya kara manna mata akan lips dinta regadless,In a low and sexy tone yace take care babygirl,u're d best babe.. still tayi Bata ko amsa shi ba,wani Takune fuska ma tayi kamar She was deeply not impressed da romantic scene din nasa datasan bata cika samu daga gare sa ba.
Da kyar ta daure batare data kalle idanun shi ba ta furta
"....Allah ya dawo da kai lpya
Dan murmushi yy yace ameen...
Any oda thing ya tambaye ta,don a ranshi yaso ace ta gaya masa wani abun da zaisa ya ji dadi amma sai tayi shiru ohh well dama bai saka ransa sosai ba,sai yaga ma ta dada daure fuska..

Tashi yy niyyan yi sai taga kamar zaii sake matsowa kusa ne da sauri taja kadan tace soul ka tafiyarka ni aiki nake yi,nan office ne fa c'mon...pls
just goooo ta fada cikin Wani nau'in rigima da shagwaba tana dan tura shi.

Zarah dake makale a waje ta kasa tafiya mannuwa tayi da jikin kofa tana jinsu don kaf maganan da sukeyi a kunnen ta akayi shi she just cant deny it capt shikan sa yana burgeta.

Kallon Matarsa yayi datake zaune kamar sarauniya aransa yace hmmmm not a even a good bye kiss?
...
Bata ma bari ya kare maganan ba a gurguje tace mashi...bye..tasa fake smiles bisa kan fuskanta tana binsa da ido har
Ya sa kai ya fice abunsa.
..
Tafi minti biyar tana bin rufaffen kofar da kallo,Wani Hummmmmm ta sauke wanda ya fito mata tare da nannuyan ajiyan zuciya..
tace ohh is dat all wat he cares about? toh Allah tura keya,tayi kwafa ta zauna ta cigaba da aikin ta hankali kwance.

*****
_Murtala Muhammad intenartional Airport_ .
6:00am Sunday morning.

Ita kadai ce a zaune akan waiting chair da alamar ta rasa yadda zatayi ne sai faman juye juye takeyi tana kallon mutanen dake shige da fice awajen.

Kallo daya zaka mata ga fahimce cewa sam bata cikin hayyacin ta,tamkar ba rufaida ba,sosai ta jeme tayi Wani fayau kamar wacce babu ruwa ko jini ajikinta,Wani Ajiyar zuciya mai Nauyi ne ya kufce mata ayayin data juyo tana mai maida kallonta kan kofar Dan ji take kamar ta tashi ta fice da mugun gudu tabar wajen koda zataji sanyi,ta dade a haka tanata faman sake sake a cikin ranta,cikin sanyin jiki can ta dauke kanta a hankli sannan ta sunkuyar dakantan kasa cikin yanayin tsantsar damuwa da tashin hankli,tun ranar da aka rabata da gidan iyayenta ta kasa samun sukuni arayuwarta,tun zuwarsu garin nan tamaida kanta tamkar wata kurma,bata tabayin magana da uban kowa ba,kuma sai anyi dagaske take ci tasha,bacci kuwa tuni tayi bankwana dashi don duk sanda ta runtsa ummanta kawai take gani a idanunta cikin Wani mummunan yanayi,sosai jikinta yake bata cewa kamar ummanta ne batada lpya,gashi an rabata da wayarta barema tace zata kira kowa, not for once taji sauki ko farinciki a zuciyarta,a Kullum bakomai zuciyartan yakeyi ba banda zugi da azaban zafi,a kowani safiyar Allah inta farka hanklinta ne ke dada tashi,ta dade tana planning na yadda za'ayi ta kufce ma wayannan mutanen Amma kuma sai bata iya aikata hakan ba
Dan Ayanzu ji take kamar ma ta dena jin tsoron Duk Wani hukunci da yaa malam zai dauka akanta Koda guduwar tayi,Shin Wani ubane ma zai sayar da kwanciyar hanklin yayan sa yyi musu auren dole,wai har suna rokonsa akan yy musu adalci Amma sai yayi banza dasu?aranta tuni ta ajiye cewa yaa malam ya tsaneta ne kawai,dama tun tashinta ta lura,musamman ma ita,kamar dama can ya tsangwameta ne aransa Dan kawai tafiye son tayi karatu..

Ayanzu Abu dayane kawai yake hanata yanke hukuncin guduwa daga nan,tsoro takeji sosai inta tuno da irin mummunan halinda ummanta zata shiga ciki,wannan shine madakatarta ga aikata abunda ta yanke arayuwarta na gudu da kufce wa wannan mugun auren Dan taje can Inda zata gudanar da rayuwarta a nitse,tagumi ta rafka da alaman gwiwarta da zuciyarta sun karaye gabadaya Duk ta rasa abunyi..

Cikin zurfin tunani taji an tabo kafadunta ta waigo cikin sauri wannan dattijiwar matar ta gani a tsaye tana famar mata murmushi

Sunanta LAURA itace matar da aka damka ta awajenta a lokacin da aka kawota gidan mijin nata.

Since then itace mai zama tare da Ita take mata komi da komi Dan haryau basuyi Ido hudu da mijin nata da aka aura mata ba.

Dan Murmushi ta sake mata itakuwa bata amsa mata ba ta kau dakanta gefe
Matar tace
"Amarya lokaci yayi
Ke kawai ake jira.."
Jin hakan ya sa gaban rufaida ya kara fadi adan takaice ta dago tana kallon matar sannan ta mike tsaye ta tsaya still batace komi ba..

Wucewa gaba matar tayi aftr like 2 scnds itama ta shiga biyota abaya nan da nan suka billo ta Inda jirgi suke tashi

Saidai Gani Tayu kamar basu da yawa awajen duka da mata da maza da yara kanana wanda basufi uku ba are so few on board,taga kuma karamin Airplane ne abun sai yaso ya bata mamaki Altho ita wanan ba damuwarta bane infact she don't care inma karshen duniya za'aikata a ajiyeta,itadai tasan bazata yi magana da kowa ba bare taso sanin ina za a kaita,Sam bata damu ba,aranta She can recall dat yaa malam yace wai mijin nata acan kasar waje yake aje familyn sa tasan probably nan kenan itama za akaita.

Seat dinta shine seat din farko
Laurar ce tayi mata jagora har kan gaban shigarta cikin jirgin,sannan tayi mata sallama ta juya ta tafi abunta

Barinta wajen keda wuya jirgin nasu ya lula sama basu ko tsayaba sai can da misalin asubahi dataji anouncement na cewa sun iso hearthrow international Airport U S A

The Flight was soo comfortable for her Dan haka babu alaman Wani gajiya ajikin ta Dan sosai ma tayi bacci,daga nan Wani kebabben waje akayi da Ita,In less than 20 minute taga wai har anzo daukar ta,wasu mutane ne su biyu daya bakin fata daya kuma fari,basu ce mata uffan ba itama batace musu ba,nan suka dauketa a mota like 40 min drive sai gasu sun sauka a gaban Wani hadadden gidan sama mai hawa hawa Inda taji Suna cewa wai gidan san ne

Itakam Ido kawai take fitarwa tanabin koina da kallo,tsaban shirun anguwar tamkar da babu kowa saisu haka ta dingaji ga Wani uban sanyin da akeyi mai mugun taba kwakwalwa

Mutumin ne ya bude mata kofa,suka shige ciki tare suka tsaya acikin wata yar falo wanda babu hayania acikinta

Haurawa can sama yayi yabarta a tsaye,
Dan dama daga ita sai ita bata da komi ma bare tace zata taho dashi..

She was deeply lost in thoughts
Akace mutumin nan nada mata har biyu toh itadai bataga alaman kowa anan ba,atleast ai za'ace ya haihu yanada yara ko?but why is evrywher quiet,and neatly arranged tamkar ba a ma taba zama anan ba
Haka kawai taji kirjinta na tsananta bugun shi Wani abu mai mugun kama da tsoro na turnuke ta.

Cikin haka saiga wata murdadiyar mata suna saukowa tare da mutumin daya kawotan
Wanda Tun daga sama tajiyo sautin muryanta tana cewa
"Wow..sannunki yan mata..

Dan dago kai Rufaida tayi tana ta kallonta har ta karaso gabanta batace mata uffan ba
Murmushi matar ta dadayi tace mata.."ure welcome home.."Kamal Ka tafi kace ma Alhaji yarinyar ta iso..cike da ladabi Mutumin ya amsa da yes ma'am sann ya sauka da sauri ya fice ya kyalesu su biyu anan.

"Muje ciki ko?
Da sauri rufaida ta dago kanta setin Inda maganar ya fito,tanajin yadda bakinta ya Budu kamar wacce zatace Wani abu saidai Suna hade ido da matar sai taji gaba daya ma ta kasa iya furta wani magana.

Riko hannunta matar tayi so calmly sannan suka fara takawa rufaida tana biye da Ita abaya,can Sam suka haura kan balcony,its 4 step down sai gasu a can can sama Inda babu kowa kuma babu motsin komi

Wasu dakuna ne a jere har guda biyar sai Wani hanyar databi kasa..
Matar ta kalle ta tace"Ki zauna anan" at same time tanamai bude mata cikin dakin tamkar bata damu da shirun nata ba
Kara hade ido sukayi rufaida tyi saurin kawar da nata gefe tace
"My dear pls Ki sake jikinki nan fa gidan ki ne,Duk abunda kike bukata za'a kawo miki Nan bada dadewa ba ma Alhajin zaizo..

Da kamar bazata ce mata uffan ba sai kuma ta gyada kanta a hankli tace
Nagode

Murmushi kawai matar tayi ta juya tayi waje abunta..
Surayyahms/08060712446







*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


Part1:chapter 8
*At d core of my pain.*

_Old maguzawa site:Anguwar bayan gari, kano state._ .


Kwance take akan tabarma bayanta jingine da Wani motsatssen matashin kai tana maida numfashinta a hankli,daidaikun matar makwabta ne a zagaye da ita ana famar jajantawa ana bata baki,Matar mai anguwar ne ta kara maimaita maganarta tana cewa"Lallai Sannu hadieza,Allah ya kara sauki, Allah yasa ciwon nakin nan kaffara ne.

Da kyar Umman take dago kanta inta dan Kare musu kallo sai tace Ameen sai ta kara maida kallon ta gefe batare da ta kara furta musu uffan ba

Daga ganinta kaga yanayin wacce kwata kwata batajin dadi aranta
,musammn ma yanayin taruwar matan nan agabanta,ita kanta tasan ba Wani abu bane yake kawo matan makwabta gidanta face gulma da son jin kwakwaf kowa dai nason yaji asalin labari game da Auren bazata da akayi ma yarta rufaida..

Duk Dama tasan tunanin rufaidar shine silar ragwabewar jikin ta amma tana matukar tsoron wanda zata sake ta tattauna damuwarta da shi
Ayanzu Bata da kowa na kusa da ita Dan haka ta qwammaci ta cigaba da danne abubuwan dake damunta masu Nauyi da kuntatawa acikin xuciya.

mijinta Yaa malam ya riga yahana yayansa Koda yin waya da ita inba Wani abu muhimmi bane ya taso musu,ko da ya tason ma yafison su kirashi direct amma ba ita ba,Dalilin sa na cewa ai ana zugasu ne Dan su bar gidan mazajensu suki zaman aure.

Tun da ya rabata da su rufaida take cikin tsananin bakin ciki da damuwa and She have no one to talk to Bare ma ta amayar da kuncin ta waje Kodama zataji dan sauki sauki a zuciyartan dake mata nauyi.

Ta gama lura cewa wayannan mutanen anguwar nasu kusan Duk jirgi daya ya debosu acikin su babu mai isashen karatun arabi bare na boko,su basu San komi ba sai azaban saka Ido da bibiyar rayuwar mutum in tayi tsami suyi ta tsegumi ana dariya intayi kyau sununa tsantsar bakin ciki da hassadarsu a fili.

Hasalima badon an shede rufaidar da tsananin kamun kaiba da tuni an karade gari da cewa cikin SHEGE tayi ko ko ace an kamata tana zina shiyasa akayi mata aure irin wannan babu hidima babu shela kawai agaggauce batare da sanin uban kowa ba.

As usual Tunda suka shigo gidan babu abunda sukeyi sai raha a tsakanin su da kwakwale kwakwalen magana
Kowa dai burin sa baifi ya fadi wata kalman da zaisa hadieza ta harxuka ta shiga bude musu duka sirrikanta ba,burinsu ne su baje kunnuwan su kwasa sirrinta cikin satin nan sai asamu abun bazawa,Ita kuwa hdiza Sam taki kulasu,Koda ma an tambaye ta silar ciwontan saidai tace ciwon zuciyarta ne ya motsa kuma ma yanzu tanajin saukin shi,su Sam ba Hakan suke gani atttre da ita ba,Dan shi magulmacin mutum kusan yafi
Kowani mahalukin Dan adam iya lura da yanayin mutum

aganin su tabbas akwai abunda yake tafiya game da Auren rufaida wanda su basu gane ba,kuma koma menene sun san tabbas babu dadinji Dan sun dade basuga hadiza acikin yanayin tashin hanklin irin wanda take ciki yanzu ba

Ana cikin wannan yanayi saiga sallama a kofar gidan sun,bayan kamar minti uku da ansa sallamar can saiga almajiri ya shigo Niki Niki da kayan makulashe ya shigo da su ayar babban leda,wata kyakkwar mata ce ke biye dashi fuskarta babu yabo babu fallasa,tun daga kasar zaninta har tsakar ka suke kallon ta babu kiftawa,"..sallama alaikum..umma hadieza tana ciki kuwa?,Duk yawansun Nan ba a samu wacce ta iya amsawa ba sanda umman ta mike da kyar ta amsa maganan fuskarta dauke da murmushin jin muryan Barister fareesa matazu a tsakar gidan

Lale marhaba fareesatu ce? Ahh sannu da zuwa...
Shigo mana,Umma ta fadi hakan ayayin data Dan mike zaune fuskarta dauke da murmushi

"Ina wunin ku?
Barister fareesa ta Dan rusuna kai ta gaishe su duka,sai ayanzu suka farga daga azaban kallon tan da sukeyi,.atare duka suka ce uhmmmm Lapya barkanki da shigowa,tace yawwa,Daf tana shirin zama kusa da umman knan sautin wani magana ya dakatar da ita, wata magulmaciyar ce data kasa hakura azauna,tace hadiza
Wannan kuma fa?

Take umma tayi Murmushi tace
Maman abdul kenan,ai Kya bari ta zauna ko?...wannan fa antyn su rufaida ce,Fareesatu ce babban yar gidan Yaa sheik..Atare Suka washe baki "Awooo Allah sarki,sannunki da zuwa fa? lale marhaban
..Nan da nan suka kara gaisheta kowa na tambada nasa kalar iyayin,daga bisani da sukaga batayi kalar wacce zata kula haukarsu ba da daddaya suka zame suka basu waje.

Sai a sannan umma ta juyo a nitse ta kalle Anty fareesan
Tace "yata kin baro gidan lpya?Yaya Hajiya jasmine da yaa zaidu?Hajiya mama fa?ina fatan yaranki ma Suna Nan kalau Murmushi mai sanyi anty faressan ta saki tana mai riko hannayen umman cikin tsananin tausaya ma yanayinta aranta tace"Kowa lpya umma..toh Yaya jikin naki?..kina samun sauki kuwa?Ni kaina na kasa samun sukuni tunda hjya ta gayamin halinda kike ciki,yau da naji ance yaa malam bayanan shine Nace to bari inzo inganki,Umma fatan kina samun sauki daiko?ko Hjya mama ma ta mugun daga hankalinta da tunanin ku Dan Allah ki kwantar da hanklin ki umma,ki gayamin damuwarki Inda Wani taimakon da zanyi miki sai inyi mikishi yanzu

A hankli umma ta zame hannun ta anata,ta kuma kau da kanta gefe gudun
Kar hawayen da suka ciko idanunta su gangaro.

Koda ta saurare fareesa sai taji kamar garin barkwano aka kara zuzzubawa akan ciwon dake ciccin zuciyarta,sai taji zuciyar nata na mata Wani irin quna da zafi,Tafi minti uku cikin Wani irin yanayin bakinciki da tunanin kuncinta mai azabtarwa kuma marar misaltuwa wannan murmushin dauriyar shikadai yaki kufcewa akan fuskarta

Dagowa tayi cikin tsananin dauriya ta kalle kwayar idanun fareesan bakinta na shirin buduwa tamkar wacce zata furta Wani abu sai dai wani maqudan hawayene suka sauko mata a bazata"muryanta na rawa rawa tace.."lapiya na kalau faressa..tafin hannun tasa ta goge hawayen nata,still basu dena gangarowa,it feels asif she want to control her self nd her emotions Amma Ina sai tagama takasa iyawa,hawayene masu rauni da daci ke gangarowa daga cikin kwarmin idanunta,ta daure iya dauriya anma daga ta budi baki bata iya furta komi sai tace.."lpyarta kalau...Dan riko hannun ta da Anty fareesan tayi ne yasata ta barke da Wani marayar kuka mai tsuma da shiga jiki,tanayi ahankli gwanin ban tausayi,Murya na rawa Anty faressa tace"..umma dan Allah kiyi hakuri kifadamin abunda yake damunki Koda bazan miki maganin yaa malam ba na tabbata zakiji sauki a zuciyarki..karki bari tunanin su rufaida ya cutar dake,in kika bar duniyar Nan wazai tsaya musu umma?anan itama sai ta sauke hawayen ta tanamai tsananin jin tausayin umman..Rungumar ta tayi tana kukan tace"..Umma dan Allah Kiyi haquri ki samu lpya dukkan tsanani yana tare da sauki,da kyar umma gyada kai cikin danne ciwon datakeji aranta ta dauke kukan chak snn da ta dago,Dan kallon ta shiga yi
Tace fareesatu bani da kowa fa a duniyan nan sai Y'aya na,gashi ya rabani da su dukan su,.shin Taya hanklin uwa zai kwanta bayan bata San halin da yayanta suke ciki da rayuwarsu ba? rufaida tana can wajen wanda bamu San shi bamu kuma San yanayin rayuwar sa ba.
Yau In Wani abu mummuna ma ya faru da Ita ina zan sani?ya hana su kira ya hanani neman su..ni Sam bansan me nakeyi da rayuwata ba..
Ashe haka maraya yake shan kuncin arayuwarsa?tunda na aure kawunku nake cikin halin kewar iyayena na tabbas na gwammaci na zauna da iyayen da suka yarda ni a bola da in zauna da mutum irin yaa malam,wanda Duk Wani farincikan ka sai ya tsinka shi ya yasar,...Nide Allah na Gani Duk Wani nau'in wahala da mugun halin da yayana zasu shiga bazan taba yafewa ba kuma Alhakinsu na wuyarsa..Wani zazzafar numfashi taja alaman takaicin furta maganan ya shigeta sosai..
Wani kalman zata furta kawai saiga hawaye rututu Suna saukowa daga idanun ta kamar an kunna su Atake Anty faressa ta share hawayen ta ta matso kusa daf da Ita cikin yanayin rarrashinta tana mai dan shafa mata bayanta a hankli,tace "umma babu abunda yafi karfin addua,kiyi fatan

Please Login or Register in order to submit comment