Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda ya shiga dakinshi yaci gaba da aikinshi sai kuma sallahn fjr daya tadashi,jiya bai kwanta ba sai after 12, yana kwanciya bacci ya kwashe shi, washegari 6 ya tashi bayan yayi sallah asuba yayi wanka sannan ya biya kowani sashe yay sallama da kowa, jeans blue ya saka da farar rigar cashmere marar nauyi sannan ya daura blue Tuxedo ta giorgio Armani daga saman rigar, kafarshi kuma ya sakala mata pure white sneekers ta kamfanin balenciaga itama fara kalce babu surkin komi, kayan ba k'aramin kyau suka mishi ba kasancewan shi dan dogo mai kyaun siffar kafafu agogon new police golden wine colour ya mak'ala a hannunshi sannan ya fesa turaren hermes 24 fauborg da vesace eros

k'arfe bakwai daidai ya gama shirinshi ya fita suman kanshi tasha gyara tana wani kyalli.

DBX golden colour ya bude ya shiga ya fita daga gidan, office din yaa sheik ya wuce, a nan yaci gaba da aiki har sai da aka yi mishi waya suka tafi sighting wani international prjct legistlation affairs dayake kulawa dashi, shi ya bada shawaran contractors in da ya kamata ayi aiki dasu sanda ya kammala dasu sannan ya wuce airpot by 12:00 yana son yakai report letter wajen sabowar aikinsa a kano,jirginshi na sauka yaga k'iranta da number ta asali gaba daya ma ya manta da yace zai nemeta,dan tun jiya ta turamai sakon cewa in yau dawo din ita da kawarta zata zo har aiport su daukosa, tsaki yadan ja kamin yayi recieving call, kamin yayi magana ta riga shi da murna tayi mishi magana "Hello Baby ka dawo ko,i was informed dat you just landed, yanxu ma kai nake jira ina waiting area. sai da ta gama yace "olryt gani nan zuwa", yana fita yayi hanyan wajen, side din international arrivals yabi, waya ya dauko zai k'irata kenan yaji an sa ihu daga bayanshi "Babyna am here" ko bai juyo ba yasan itace, da gudu ta taho ta rungumeshi kamar za a kwace mata shi,"i missed you soo so much baby" peck tayi mishi a kumatu sannan ta dan sassauta rik'on da ta mishi ta dan kwanta a kafadan shi shi mamakin halinta ne ya hanashi magana

duk mutanen dake wajen har workers sunata kallonta amma babu ruwanta haka tazo ta mak'aleshi, janyeta yayi daga jikinshi yayi mata magana a hankali baki ganin akwai jama'a a nan zumb'uro baki tayi tace "ai dama nasan bakayi missing dina ba, komai nayi is not right to you, wata daya we didnt meet saiyau, i was just super happy to see you kuma su Mutanen ai sun san ina sonka ne" bai sake ce mata komai ba dan yasan she wont understand him

k'arasawa yayi inda kawartan take tsaye, gaisawa sukayi ya juya ya kalli mutumin dake doso su,agogon hannun shi ya kalla
Yace toh yan mata angama tarban ko? Wani Bata fuska tayi shrin Zatay korafi ya tsareta da yatsan hannun shi yana magana kasa kasa "As u can see My PA is here so pls kuje gida da friend dinki inna gama abunda nakeyi i wll call u bk,a dak'ile ta amsa mishi da okay,PAn kuwa na karasowa bai kara duban inda suke ba ya kada kanshi ya barsu awajen,wani tsaki kawartan taja ta wuce gaba, itama ganin ko darajar bye bye basu samu ba bare rage hanya yasata taja tsakin tabi bayanta.


Direct wajen sighting aikin ya nufa tare da wannan mutumin daya zomai wanda tun zamarsu a motan yaketa bashi bayanai akan tsarin abubuwan su anan kano gyada kai yakey kamar yana jinshi amma tuni hanklinshi yay nisa, tunani yake aransa gaba daya yarasa da ta ina zai fara inya juyo,dan baiki ace masa yau din nan da fuskar rufaidarsa zai fara gamuwa ba..
Salsakar nunfashi ya fetsar ta ramin bakinshi,it wont be long yasan zai sameta tunda dai yaci nasaran isowa garin datake,but when where and how?dan murmushi ya sake da yaji zucyrsa ta basa amsar cewa yaje gidan hajiya mama
Ko bai ganta anan ba dolene yaji labarinta da na halin da ake ciki..wata nannuyar ajiyar zcyce ta kufce masa game da lumshe ido feeling soo relive da wannan idean.

Around 2 hajya mama ta gama rarrashin malak tayi shiru harta danyi bacci daga farkawanta wani wankar ta karayi ta canza kayanta zuwa simple fitted gown na material lace aranta tanajin babu wani dadi sosai,ga wayarta a hannunta ta amma rasa waye zata kira ta dan ji dadi kewar iyayenta sosai yake tabata nd she though of Imad many times tunda ya dawo shiru kakeji ga babanta yace mata karta dameshi da kira tunda yau shima din zaizo,ta rasa meyasa rufaidarta batada waya mtsw komi ma haushi yake bata aynzu,tunowa da she needs to take passpot yasa ta sauko ta same hajiya mama itakadai a falo tana kallon tv,kusa da ita ta nemi waje ta zauna hjy ta kalleta cikin harshen yare tace"..malama har kin farka?.gyada kai kawai malak tayi can tace mata tanada bukatar daukr sabbin passport din da zata je schll dashi gobe dan tay submitting files dinta a department dinsu,ba musu hajy ta hadata da driver akan suje yanzu sudawo sabida ta samu ta kikkimtsa kayayyakinta a sabon dakinta.


Can da yamma anty fareesatu ta dawo kenan daga office its around 5pm na yamma gidan yay wani shiru bakajin motsin kowa alaman su jawad ma basu dawo daga sabuwar islamiyar da aka sakasu ba,sama kawai tayi refreshing kanta ta saka simple english wears,red skirt da white t shirt da dan guntun white hijabi ta dawo babban falon ta bude computerta tana latsawa,jim kadan saiga rufaida ta fito
Anty ta daga kai tabita da kallo har kasa ta durkusa ta gaisheta tana tambayarta kota kawo abinci".Anty tace a'a,can ta karacewa .malam liman ya duba yaran nan kuwa? Its almost time yakamata aje adaukosu,mikewa tsaye rufaida tayi toh bari inje in masa magana,mayafin kanta ta warware ta yafa gyalen doguwar rigan datasa akanta tayi lillibi sannan ta wuce bakin gate ta same shi yana zaune da redio a hannu"yana kallonta ya sasaauta da sautin rediyonsa labarai aketayi akan yan ta'adda da suka shishhigo,"asalam ina yini malam liman...yace wasalam alaiki karamar hajy anfito lpya ."anty ne tace ingaya maka lokacin daukar su jawad yay..yace to to bari in dauko motar,daf zai juya ta tsaresa malam liman pls bari naje na dawo mutafi tare yace ba matsala da wuri ta wuce ciki ta same anty tana zaume a inda tabarta,"har kasa ta rusuna a hnkli tace Anty inbishi dauko su jawad din?dan Dakatwa anty tay tana kallonta she looks bored kullum ita kadai a gida can tace mata "off couse dear kuje mana"..da murmushi a fuskanta tace nagode toh anty sai mun dawo anty tace adawo lpya rufaida ka a tsaya akoina fa, tace ok..snn ta fice ta samu har malam liman ya juyo da kan mota

Gidan gaba ta bude ta shige ciki ta zauna tare da maida dubanta jikin window tanata kallon motocin dake wucewa dan batada waya ko wani abun latsawa dazai na debe mata kewa..

Suna isa kofar makaranta yay parking ta sauka ta shiga har ciki,dumbin yaran masu hannu da shuni ne kawai awajen sai daidaiku middle class acan dungu ta gano su suna makale da juna suna hade ido iman ta kwaso da gudu tayo wajenta tana murnan ganinta dan bakaramin kuka takeyi a islamiyar ba itadai sam batason zuwa islamiya,jawad ne babu ruwan shi tuni ya karaso wajenta suka koma mota.
Suna zama aka fara cike motan da surutu kowa nason taji nashi labarin,
Anty rufaida anty rufaida gobema zakizo ki daukomu ko?iman ce tay tambayar rufaida tana murmushi taja hancinta tace eh amma saikin dena kuka a makaranta.
Wannan hirar suketayi har sanda suka iso anguwarsu
Wanda Isowarsu tayi daidai da isowar wani dan adaidaita sahu

Mal liman na kkrin danna horn a bakin gate,yaa malam ya sauko daga keken sanye da wata katon garensa wanda ya nade hannunsa daya ata ciki,kirjinta ne ya buga atake ta juyo tana kara kallonsa cikin mitsike idanunta dayake' neman mata gizo
A hnkli kuma cikin firgita tace "baba?
Duka yaran harda malam liman suka juya suna kallonta
Cikin sauri ta bude kofar jeep din ta sauko alokcin bata san wani tsoro da fargaba ba itadai kawai tasan taga mahaifinta ne data dade bata sakashi a idanuwanta ba,tana dira ta nufoshi zucyana na bugu kamar zai ballo ya fito daga kirjinta
Baba.. baba..
Ya sako kansa agaba baima ganeta akan lokaci ba saida ya shako sautin muryanta,
A Kasa ta zube yadda suka saba gaishe sa kamar wani sarki"..Sannu da zuwa baba ..dan nitsawa yay cikin tsananin mamakin ganin yadda ta dawo wata fesssssss kamar a mafalki."keeee rufaida meya kawoki nan?..tsawar daya daka a tsakar kunnenta yasata dawo cikin hayyacinta agaggauce

Dik Jikinta da Muryanta na rawa tace "naz..na..nazo..
Nazo wajen anty faresatu ne..wani wawan marin daya sauke mata afuska sanda ta kife a kasa ta fadi agigice,"a guje malam liman da yaran suka yo wajen
Allahshi gafarta Malam lpya?iman ta fashe da kuka zatayo jikin rufaida tsawar daya kara dakawa ya gigitar da ita"Wani ubankin ne kikeyi anan wajen?wato bakiji ko rufaida?malam liman na kkrin ya kara saka baki kawai sukaga ya zaro wata zukekeyr dorina dagata cikin garensa"..a gigice rufaida ta mike tayi cikin gidan da uban hudu tana ihu wayyo Allah ma baba kayahakuri
Binta cikin gidan yayi da mugun sauri
Aka bar Malam liman rungume da Yaran anty sunata kuka sabida razanar da sukayi.




MJ COLLECTIONS shagon siyar da kayan Ado na mata muna siyar da Dogayen riguna na kasar Turkey, dubai da saudi.ready KALA-KALA, muna da Turaruka na jiki,na kaya dana kamshin daki,Sarka,Dan'kunne awarwaro da Agwogwo.muna dinka kayan Amare,tel No 08082238202/WhatsApp No 09076198408.Bulama House Sabon gari market kano.


5️⃣8️⃣





Anty fareesatu tana kkrin rufe laptop dinta kenan saiga karar tahowar rufaida da wata irin salon gigitacciyar gudu ta banko cikin falon tayi kanta ta fada agigice babu abunda takeyi sai haki,a mugun tsorace anty tace lpya?bakin kofa kawai taga rufaida ta kafe idanunta akai,anty tana kkrin mikewa tsaye taga meyene caraf saiga mutum ya shigo burum har cikin falon da wata iriyar zukekiyar dorina yana zare jajyen idanunshi yanacewa "ina Rufaidan take? Sosai gaban anty fareesa ya fadi dataga shine,baya sosai ta ja a razane dan daga ita har rufaidan data manne a bayanta ta kankameta bari suke yi kar kar kamar anjona musu shocking

Cikin i..i na anty ta tattaro jarumtar magana tace baba,baba dan Allah kayi hakuri mubi abun ahankli..pls listen to me,ganin baima san tanayi ba ta juyo tace..Rufaida wani abun kikayi masa?rufaida dake kuka daga bayanta tace anty wallhy banma sa komi ba,nifa a kofar gate na sameshi shine.. shine..basuyi aune ba sai shafffff shaff sukaji saukan dorina ajikinsu wanda da alaman wayarsa kawai ya kaiwa dukan saita samesu duka Wani irin ihu dukansu sukayi atare sabida tsananin zafi,irin dorinan nan ce ta buzaye wanda aka yita da fatar rakumi aka kuma jikata ta kwana cikin tandun mangyada,tuni rufaida ta zube kasa tace Wayyo Allah baba kaya hakuri
...baba natuba bazan karaba,tsawa kawai yake daka mata shi a dole an zalunce shi an rainasa "shahshar yarinya kawai ki wuce ki bar nan gidan kafin inzo in tattaki,marar hankli marar mutunci,inke bakida mutunci to ni inadashi ke baki isa ki toxarta ni ba dan uwataki Maza Zoki wuce kibar musu gidansu kije duk inda zakije inyaso kina kwana a titi amma nikam bazakuci mutunci na ba,"alkcin rufaida bamajinshi takeyi ba ta damke jikin anty gam gam tana ta kuka,cikin dauriya anty fareesa ta soma bashi hakuri muryanta na rawa haryana fidda sheshhkar kuka,kin mata magana ma yay saboda aganin shi ba girmansa bane yay zance da yar yarinya yar cikun zaidu ai Saidai yy da ubanta dan shine kadai saar yinsa

arakube suke tsaye da juna duk ya gigita su da zage zage,ahnkli rufaida ta soma karaya murya can kasa tahau rokon anty, tace Anty kice masa yy hqri zan tafi amma dan Allah karki barshi ya bugeni..,"..girgixa mata kai anty tay cikin yanayin turjiya da alaman a'a babu inda xata barta ta je suna cikin wannan muhawwarar sukaji saukar dorina ta kota ina akansu yanabin kan uwa da maibi kaff dinsu ya hada cikin harzuka yana kaiwa dorina haka ya musu ciki da bai jikinsu yay rada rada da shatin zana dukansu saida sukayi kuka da idanunsu suka fidda hawaye,ganin abun ya faskara rufaida ta biktice musu ta hau kokowa da anty,"anty please kibarni intafi,i cant stand this anymore,
anty kuma ta rikota dam dam taki sam tasake ta ,har sanda tayi miqa ta sulale kanta da karfin balai daga jikin antyn dan ji takeyi kamar zuciyarta zai fashe yay feshin wuta data ga haikan ya hada harda antynta ya buga ata dalilinta,anty tana kkrin janta da karfi ta ficceke kanta da banzan gudu ta bangaje shi ta fita waje da mugun gudu tana kuka sann ya juya ya biyo bayanta,sosai yaran anty fareesa suke kuka dan basu taba ganin tashin hankli irinta yau ba.

Da kyar Anty ta iya tattara saukar nunfashinta dake shirin daukewa, fitowa waje tay taga ashe harsun bar tsakar gidan sunyi waje, duk sai taji koinanta tayi sanyi idanunta suka hau fidda sabbin ruwan hawaye sosai,jiki a matukar sanyaye ta janye yaranta duka suka shiga cikin gida dakinsu takaisu direct ta kullesu sann ta fito

Wayarta ta laluma bata jira an dauka bama ta fashe da matsanancin kuka
Hajiya mama tana sakawa a kunnenta tunda ta shako sautin kuka ta mike tsaye innalillahi wa inna ilaihi rajiun
Fareeesatu? Meya sameki fareesatu
Tana shirin barkewa da kuka anty fareesatu ta rigata da ihu da masifan da bata ma san daga ina yake fitowa ba"..furucinta na farko a zafafe tayi shi, cikin tsananin bacin rai da kunan zcya,bacin rai abune ne mai wuya kaganta tanayinshi arayuwanta yau saigashi,tace Hajya wallhy In rufaida ta mutu laifinki ne,kinyi sake dayawa..kin sake ma kawu abbakar dayawa yanayin duk abunda yaga dama akan rufaida..in kashe ta zaiyi basai ya kasheta ba?ni bangane abunda yake so ba,wallh in wani abu ya faru da rufaida dake da baba sai Allah ya tambayeku...matsanancin kuka ta fashe dashi tana mai datse wayar ta jefar saboda ba acikin hayyacinta tayi maganan ba.

Jikin doguwar kujeran dake falonta ta koma ta sulale a hankli ta kwanta tare da kife kanta
Nannuayr ajiyar zuciya tahau saukewa tare da sake zazzafar hawayen dake malala daga cikin kwayar idanunta zuwaga kan fuskanta ahnkl tana maida nunfashin dawowa cikin hayyacinta.

Tunda ta jefarda Wayar agefe wayar take ringing babu kakkautawa wanda
Ko ba agaya mata ba tasan waye me kirar,..shiru tay cikin rasa meyasa ma bata gaya mata asalin meya faru ba.
Itade tana zaune ne tana jin karar wayar amma batayi kuma yunkurin dagawa ba.


Hajya mama kuwa ta kasa tsaye ta kasa zanne har tsakar gidan ta fito a gigice da waya a hannunta cikin rikicewa rabonta dataji kukan fareesatu aibazata ma iya tunawa arayuwanta ba.
Saikiran wayar take amma ba a dagawa,
Ta rasa meyake mata dadi,sai maimaita kalaman data gaya mata takeyi aranta,gashi yamma yayi sosai har ana neman 6 da rabi saura,ta duba gabar da yamma bataji motsin kowa ba,malak ma tana hanya tare da driver waisunje siyar ice cream basu dawo ba,a kasa ta zube
Na shiga uku ni hasiya faresatu taki ta dauki wayar,ko meyake faruwa ne?
Karde bukar ne ya sace yarsa rufaida?
Ko guduma ya gwada mata akai?tunani kala kala hardana banza babu wanda batayi ba,tanayi tana matse hawaye...

Around 6.30pm akayi horn abakin gate ta mike tsaye cikin sauri ta koma cikin falon tayi zaune cikin matsanacin damuwa tana shahshare idanunta atunaninta ko malak ce ta dawo kar ta tsince ta tana kuka ta daga mata hankli,cigaba da kirar layin antyn tayi sai can bayan kamar kira ta biyu taji an dauka.

Da wata nannauyar ajiyar zuciya ta amsa wayar taname karawa a kunnenta "ahnkli da muryan lallashi tace salamu alaikum fareesatu?faresatu meya faru meyasa meki,cikin yanayin shehsheka anty faresa tace zan kira ki a video call ki dauka,..daga nan bata jira cewarta ba ta datse wayar aftr 2 min sai ta kira da wuri hjya mamn ta dauki kirar cikin sauri,"video photage yanayin clear taga Anty faressatu zaune ita kadai akan gadonta kanta sunkuye akasa alamu duk sun nuna cewa tana cikin bacin rai da tashin hankli Jiki a tsananin muce hjya tace faresatu Lpya kuwa?.Dago kai anty take shirinyi kawai taga shatin bulala ratata a hannunta abunka da farar fata take wajen yay wani jajur yayi layi layi kamar an dandana masa wuta.
Kare ma jikintan kallo tayi sannan ta mike tsaye da wayar a hannu
"Innalillhi wa inna ilaihi rajiun,a mugun rude ta sake wayar akasa tabi ta dauka cikin sauri tana cewa faresatu meye wannan ajikinKi kamar shatin duka?Hawaye Anty fareesa ta sauke
A hnkli tace Kawu Abbakar ne ya zo nan har gida ya zanemu dani da rufaida..cike da razana da kaduwa hj ta doki kirji tace bukar din ne yazo har gidan Ya zane ku?ina ita rufaidar take?..nan anty ta nitsa tahau bata labarin duk abunda ya afku tanayi tana kuka tana blaming dinsu Tana cewa ita karankanta zata dau tsattsauran mataki akan rufaida insu bazasuyi komi akaiba.

Sun kai minti sha biyar suna magana batare da hajya ma ta iya cewa komi ba
Dan kamar wata kungi haka ta rike wayar tana sauraran jikarta farisatu da take magana araunane tana zubda mata da hawaye. Aranta tay tunanin duniyan nan sai can ta fahimce cewa ashe ga asalin abunda ya faru ranan dataje gidan bukar dan tasan babu yadda za'ayi ace ba aranar ne yaji kan zancensu ba,kuma Dama da shauran mamakin saukin kansa ta ranar ta taho gida ashe da walakin goro a miya


Gaba daya sun lume cikin wani yanayi na shagala da zancen anty faresa tanata kawo mata zancen kwacewa rufaida yanci ita kuma tanata lissafin yadda aka soma samun barakar wann mtasalar harma bukar yasan inda rufaida take ya biyota...Yo inma jinsu yayi toh meyasa baizo tun ranar ba?Meyasa kuma hadiza bata sanar da ita cewa yajiyo zancensu ba
Acikin wannan tunanin tay zurfi
Ta ma mance da horn din da taji tun tuni abakin gate

Imad kuwa tunda mai gadi ya bude masa ba ya shigo yay parking motarsa a harabar gidan,dan tun barinsa wajen aiki yakeji ajikinshi kamar bazai iya karasawa gidansu ba face ya ratsa ta nan gidan hjy ko don yaji wani abu game da labarin rufaidarsa,in beyi haka ba yasan baida wani nutsuwa shikansa yasan daren ne zai masa tsayi, saidai bai iya karasowa ciki ba jin sunan rufaida da aketa ambata tun daga cikin falo,a bakin kofar shiga ya tsaya ya rakube da labule yana jin abunda anty fareesa take fada tun dazu

Suman Kanshi yahau shafawa dagaske yana jan numfashi,a hnkli ya lumshe idanuwansa saboda ya samar makanshi cikayyar nitsuwar karasowa ciki..

Hajiya mama tana katse wayar taji gyaran muryan balagaggen Namiji daga bakin kofar

A matukar tsorace ta miqe tsaye tabi kofar da wata razannen kallo
Dama an dade anay mata bakin cewa bukar danta shine zaiyi ajalinta
Koma shine yazo zai kasheta?

Wani cak ta tsaya awajen tana raya hakan acikin zucyarta "imad ya karayin gyaran murya sannan ya budi muryansa yace salama alaikum hajiya in shigo..?

Wani nannuayr Ajiyar zciya ta sauke jin murya nadaban hakan yasata jin dama dama aranta tace
Wayene kam shigo ciki mana,buuut taganshi a tsakiyar falon kamar an jefoshi..."shi baizo da niyyar dariya ba amma yanayin yadda tayo da fuska data ganshi sanda yaji wani bangare a zxyrsa tayi sanyi
Ihu acikin kuka ta saka tana mikamai hannu akan yazo ta rungumesa tana cewa.."Zo nan dan albarka,imad?...ohni hasiya jikar malamin yau ana wata ga wata ...au nace sai yau kaga damar zuwa min bayan ka gama bulayinka agari?
Kasa kawai ya tsuguna daf da kafarta cikin sanyin murya ya hau gaisheta tana amsawa tana tare hawayen murnan ganinshi datayi amma shi sam hanklin shin ma baiya wajen,"
Tana zama tace tun yaushe ka iso,ya mike tsaye yace na dade anan wajen inajikii "waida waye kike ta waya ne,kallonshi tayi a razane saikuma ta dauke idanunta daga ta inda yake ,Shiru tadan yi, kamar an tsakureta ta kama kada kanta, sai yakara masowa
"Bazaki fadamin ba.
Toh shikenan aina ji ma,cikkn gwalo ido waje tace d'an nan kaji mene?..jakar sa ya ajiye aksa yace hajiya wai meye haka nakeji?tsaye ta mike da jikin tsufa
Tace "dakata Kai,.yaushe ka dawo da zaka fara tarar wata magana
A dan fusace yaja da baya yanacewa
I dont bloody care
Kuna zaune anan Ina ita rufaidar take?kunyi tunanin inda zataje acikin daren nan ko miye zai mata a hanya?..
A gajiye ta yarfa hannu"toh Ni ya kakeso nayi ba yarsa bace?aisai ya kasheta,idonshi ya gwalo wake yana hararta Yacee what?,yaga ta juya mai baya tana share guntun hawaye tsaki yaja aransa ya mugun hade rai "Well im not letting this happen, ni zanje in nemota a duk inda take,a fixge ya juya zai doshi bakin kofar,saidai yana saka kafarsa daya akasa itama ta zube akasan ta kamo kafafunsan ta damkesu dam dam,"imad ka rufa mini asiri kar yaje ya maka lahani in shigga uku,runtse idonsa yay yace ni ki sakemin kafana tace...anki...toh acikin daren nan ne zaka fita? ina zaka same rufai?..taji baice uffan ba tace
imad kanajina kuwa,kafarsa kawai yaketa kkrin janyewa a hankli dan Kawai dan ita tsohuwa ce xai barta dan da wani ne da tuni ya hankadesa yay gaba.Banbami yahau yi yana cewa
" bazaki sakeni ba?..Ure not serious kuna zaune zai kasheta ita faresa hauka takeyi da bazata kaisa ga hukuma ba?,shi waye dazai zo har gida ya bige matar aure.Dan rufaida yarsa ce bashi zaisa ta zama batada yancin kanta ba...ni kibarni inje in nemota.

Ganin kamar dagasken gaske fa yakey yasata mikewa tsaye tahau lallashin sa da dukkan kalami masu taushi tana cewa "ka tsaya banda gaggawa wallhy nasan inda rufaida take.Inkarya namaka daga gobe zaka gani rufaida tana tareda mahaifyrta batada wajen xuwa saican...kuma nasan bukar bazai taba kyale maganan nan ba.Kayi hkri dama Gobe ne nake so inyi tattaki inje har anguwar gangare in samesu agidan gwara ayita gwa da gwa tunda anyi na sirrin amma abun baiyi ba

Anan ma ta kwashe duka labarin sauran abunda ya afku tsaf ta gaya masa harda xancen plan dinta data shirya akan sauran yayun rufaidar..

So nake mubi abun a sannu, kaga yaje har gida ya dake yar zaidu har gidan mjinta Yanzu zaidu shima inyaga dama saikaga ya dau abun nan da zafi,kuma akan yarnan zai huce fushinsa yace ai bamu gaya masa mun dauko rufaida tun farko ba.

Yo Kodan sabida fareesatu bazakay hakuri ba?nide ka rufamin asiri kar ka tareshi da fada cikin daren nan gobe inyaso da sasaafe ka fito nidakaina zanma jagora muje gidan bukar tunda gani gaka zamu iya mukawto rufaida,ai koni sai in rama musu dukan su,da kyar da maklyata imad ya sauko ya fahimce shirmenta ta dan ya zuciya Sosai,shi inda za'a kyaleshi da cikin daren nan saiya san idan ya nemosu.

Bai wani zauna agidan ba yace mata shi zaije gida goben da sassafe zai fito,abincin data dafa haka ta tarkata ta hadashi a cooler ya fita dashi na dole,ko minti biyu da barin gidan baiyi ba saigasu malak sun dawo,tunda ta bata labarin yazo tahau kumbura fuska tace toh meyasa baijirani mun gaisa ba,hjy batace mata komi ba harta tagama bambaminta ta wuce sama can dakinta ,shikuwa Tunda ya isa gidan su baqin ciki da damuwa ta yanke masa cak sabida tsananin yanayin murnan ganinsa da mahaifyrsa take ciki

Yau Da kyar ma ya samu yay alwala yay salla,tunda suka zauna yana dan hutawa tahau kawo masa hira,yau komi mishi takeyi abinci abaki A masa tausa kusan duk sanda suke tare sai ta tuna da babanshi late xcellency khalid matori,da yay gvnorship agarin, haryau sunan gidansu yana da babban daraja da kima a idon jama'ar gari saboda tsabar muhimmancin reputation din mahaifiinsu alokcin dayay mulki.

Kowa yasoshi kuma anji dadin mulkin san sosai shisa ayanzu ma take son ma imad siyasar tasan hala farinjini da kimar mahaifinsa zai iya shafarsa.

Abu mai matukar wuyane awajensa ya aje tunanin halin da rufaida take ciki amma sabida mahifyrshi ce yasa har zakaga yana dariya yana nishadi tamkar ma ya mance da kowa.
Tanajin dadin ganinsa yana farinciki Saidai wani abu na damunta haryau game dashi ko dayazo dinma ta lura suna tare ne ana hira amma intay maganan aurenshi sai taga

Please Login or Register in order to submit comment