Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dama dayawan su cewa sukayi yaci kudin sata ne dama ansan sa handamamme mayen kudi,wasu Sukace sayar da yarsa rufaida yayi
Abun ya juya masu

Acikin anguwar kaf aka rasa samun wanda zai masa kyakywan zato shiyasa ayanzu da suka gansa kyam kyam yanai ma almajiransa karatu tamkar wanda Babu abunda ya faru dashi abun sai ya matukar Kara basu mamaki da tsoro.

Babu bata lokaci maganan dawowar sa ya fara karade kunnen mutanen anguwa,saidai komin gulman mutum zaka samu yana matukar Jin shakkar yaa malam danshi mutum ne mai tsananin son girma da daukaka bayason Wani ya dedeta kansa dashi ko yayi abota..

Ya dade yana kallon sa a matsayin Wani katon shehin malami mai kima da tsananin daraja Dan haka alamarin rayuwarsa baya sarara ma kowa.

Duk zumudin Yan anguwar haka suka binne zuciyoyin su Suna jiran karfe 7.30 na safe yay by then ansan ya Sallame almajiran sa

Bangaren su yaa sheik kuwa acikin su babu wanda ya kara samun wani nutsuwa acikin wannan daren,iya bakin kokarin sa yayi dan yaga ya sassaita hjy mama Amma haka takijin shi, takima ta bude masa kofa, haka tayi fafur ta hanasa tunkarar ta da wata magana data shafi yaa malam da su rufaida,while acikin ranta gaba daya hanklinta da tunaninta yana kan jikarta rufaida ne,Wani bin sai taga kamar batayi ma rufaida adalci ba data korata gida saidai tasan in batayi Hakan ba karshenta komi zaizo ya rikice musu ne daga karshe ..


Akan bakarta ta kwana Dan kokadan axuciyarta batajin zata ita sauya ra'ayin ta akansu,zaka kasha mamakin yadda ta raya daren tana Kai ma Allah kukan ta akan yayanta da ahalinta kamar ba tsofuwa ba...


Shikuwa Yaa sheik da taimakon Matarsa yadan samu nitsuwa don tunda ya rabu da hjy maman yakirata sukayi magana kusan rabam daren sukayi tare tana famar kwantar mai hankli da kalamanta masu taushi da tsananin sanyaya zuciya..

Sanadiyar haka yasa bai Wani samu isashen barci ba haka dai ya farka da safe Duk gabobinsa agajiye,ga kansa daketa masa Wani irin azaban ciwo Wanda tun acikin daren ya somajin sa saidai bai dauka zaiyi tsananin da zaina jinshi har yanzu ba..

Kusan da kyar yake iya daga Kan tsaban ciwon dayake masa,he tot he is just stressed,Dan haka kafin yay wanka sanda yaje sasshen motsa jiki Duk da haka baidena Jin komi ba saima jiri jiri dayake kokarin nakasa masa gabobin jiki Wani irin Dan uban kyuiwa da kasala ya rinka ji aransa abu kadan saiyaji ya gaji yananemam wajen lafewa abunda Sam bai saba dashi ba kenan arayuwar sa,Dan tabbas yasan kasala daga shedan take kuma arayuwarsa baya bukatar abunda zai danganta yanayin sa da shedan Dan haka ya ficceke kansa daga yanayin dayakejin ya fada bathrum ya doro wanka tare da alwala,...

Abu kamar wasa haka ya rinka bata lokacin sa a batrum abanza da wofi kwata kwata baisan saibin meyakeyi ba Kan ya hankara kawai ji yay anata sallan fajr a masallatai banda shi da sauri ya zura jallabiyar sa ya fita a gurguje, da kyar yau ya samu raka'ar farko..

A bangaren su rufaida kuwa tun da umma hadiza ta kammala ba ykmbo labari take cikin yanayn sanyin jiki da jimami sai can dai data samu yar nitsuwa sann ta sata agaba ta rinka yi mata nasiha akan yanayin rayuwa....

Sosai umma hadiza ta zubda hawaye anan gaban, Saidai wannan karon zafin kukan ta ba akan matsalar rayuwarta Dana yarta bane kawai,tsantsar tausayin yakumbo ne yake neman ya nakasa mata zuciya.
Tun tasowarta bata San kowa a rayuwarta ba sai yakumbon datace mata tsintar ta tayi a bola acan Wani gari,Kuma tun a lokacin yakumbo bata fiye bude mata labari akan komi ba,takan dai gaya mata gaskiya game da abunda ya shafi rayuwa,saidai gaskiyar dayau ta bude mata yaso yay ma zuciyarta illa da Nauyi Dan saiyau take ganin matukar takaici da tsansar halin damuwar da zuciyar yakumbo yakeciki akan rayuwarta,Wanda tuni ta laka makanta lefin duk wani digon wahalar da take sha danata rayuwan..

Yakumbo bata taba nuna ma umma cewa aranta tana matukar nadamar ganin irin wahalar datake sha a hannun yaa malam ba,yawanci ma saidai tayi bambami ta zageshi,Amma yau saita tsinci kanta cikin bayyana irin tsanar datakeyi masa,babu abunda ta boye ma umma hadiza game da Hakan Wanda yasa umma matukar Jin tausayin yakumbo a xuciyarta bana wasa ba..
Wani irin So,so irinna uwa shi ta bayyana ma umma hadiza a fili,sann ta nemi yafiyarta tana kuka mai ban tausayi,Wanda sanin cewa rufaida zata iya farkawa a ko Wani lokaci ne kadai yasa suka dakata suka Dan samu nitsuwa da kokrin neman kyakkwar mafita agaresu...
Amana umma tabar yarta rufaida a hannun yakumbo domin ta samu kulawa da kwanciyar hankli, ita Hakan ma a fiye mata,rufaida ta zauna anan din sabanin anguwar su data San dolene ayita cakubarsu da gulmace gulmace, Sallahn asubahi sukayi,batare da tsayawa bata lokaci ba ta shiga saka himman komawa dakin Mijinta Wanda har acikin ranta bata son yin hakan,Amma aynzu jitake zata iya aikata komi saboda samun kwanciyar hanklin yarta rufaida..

Sosai yakumbo ta Kara karfafa mata zuciya da nasihohi masu shiga jiki tace mata Allah yana kallon hakurin su kuma shikadai ne Kawai zai iya sassauta musu a lamarin su,tare da mata alkwarin Zata iya bakin kokarinta akan xancen kulawa da lpyar rufaida.

Acikin Kudin da yaa sheik ya basu ta Zara kusan dubu goma shabiyar ta danka ma yakumbo da cewar zata tafi da sauran duk abunda ake ciki zasuji shi ta sako...

Har bakin gadon ta isa ta zauna kusa da yarta data dunkule jikinta waje guda tana Kan bacci,ta dade awajen batare da ta aikata komi ba..
Wani irin kallon ta kawai takeyi da wannan shaukin azaban Nauyi da karayar xuciyar dayake sokiin ta har kashin bayanta
Wanda ya sata soma sauke wasu maraitattun hawaye masu tahowa da turirin dumbin Nauyi da kalaman data binne acikin zuciyarta,gyara mata kwanciyar kawai tayi tare da shafo gefen fuskarta a hankli ta rankwarfo ta sumbace goshinta sannan ta sauke Ajiyan zuciya tayi Sallama da yakumbo ta dau mayafinta ta nufi gida....

Isarta gidan keda wuya ta hange daidaikun almajirai a kofar zaure da alaman har angama karatun safiya,dauke kanta tayi cikin sauri batare da saurarar kowa ba ta shiga cikin gida,it was around 6:59am waje baima gama washewa da maraicen safiya na Dan haka duk Wani motsi da magana da akkeyi a gidan zaka iya jiyoshi....

Tsayuwar cak umma hadiza tayi Jin sautin sa dayaki yaki karewa,tabbas muryan yaa malam takeji kamar yana muzahara,Dan da Wani irin zuciya da karfi yake dukan kirjin sa yana kwada kansa da kwaryan,
atake jikinta ya hau rawa ta somajin tsananin bugun zuciya duk dama nawai fahimtar Abunda yake faruwa tayi ba,umarnin zuciyarta kawai tabi ta wuce sashen yaa malam din,cikin balain sauri take tafiyarta tamkar wanda ake kiranta da gaske,bata koyi Sallama ba sai gata a tsakar filin sashen Inda idanunta suka ci Karo da yaa malam a tube tumbir haihuwar uwarsa yana faman tsinewa rayuwar Dan uwansa zaidu yana cewa "zaidu bazai taba mutuwa ba har saiyayi jahilci ya toxarta mahaifiyar sa,duniya sai sun zagesa sun kirasa azzalumi,uwa uba sai hjy mama ta tsine ma zaidu da bakinta saita masa korar kare...idanun sa gaba daya ya rufe sai fadan Hakan yakeyi da tsananin axaban zakuwa da mugunta
Yana fada yana tofawa harda numfashin nishin sa acikin kwaryan,wanda ruwan already ya riga ya gamutsu da turaren ya dawo Wani irin kalar bakiii
Tamkar duhun dare haka ruwan rubutun nan ya dawo..

Kusan a daskare umma hadiza take tahowa kusa dashi Dan da alamn yayi nisa baima ji shigowartan ba..

Kallon sa da jinsa kawai takeyi sakaka tamkar wata tababbiyar mahaukaciya wanda ta rasa hanklinta,tsoro da mamaki ya riga ya dabaibayeta..

Yana ta tofe tsinuwar acikin kwaryan da alamn xai binne kwaryan ne da maganin a kasa a tsakar gidan Dan saida data matso take ganin ramin daya tuna da yar fatanya agaban sa,Cikin razana da dimauta da karfin balain ta finceko kanta daga kafewar datayi,Wani irin kururuwar axaba mai ratsa dodon kunne da dasa tsoro a zuciyar duk Wani mai sauraro shiya kufce mata,ta tuma a kasa ta wafto da uban gudu tayi kansa ba acikin hayyacin ta ba,ta bangaje kwaryan ya kifu akasa ta daka tsalle akai sanda ta farfasa shi kashi biyu,da ihu da tsawa da Firgita da gigita tace "malam?malam?kasan mekakeyi kuwa?Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun..
Malam kaji tsoron Allah,malam kasan zaka mutu kaje ka gamu da Allah
wa rayuwar Dan uwanka zakayi wa muqun Kulli?
Me yaya zaidu ya taba maka arayuwa?kafada min meya tsare maka?ko yaa zaidu ba Dan uwanka bane baicanci ka masa wannan Abun ba...kasani Allah zai iya tozarta ka kafin ka tozarta shi.. wa iya zubillah malam Allah ya kubutar damu,wayyyoo Allah na ,wayyo Allah na shigga uku wayyo Allah sai rigib ta fado kasa ta sulale a mugun dimauce tana birgima tana kururuwa tanata maganganu tana rabza uban kuka.

Yaa malam bai iyayin ko motsi na Dan shima A mugun razane yake,tunda ya bude idanun sa da suka firfito waje sukayi ja yana kallon ta bai motsa ba,a firgice ta damko kafafun sa tana ta tambayar sa me dam uwan sa yayi masa a duniya dazai saka masa da wannnan baqar muguntar? kururwan datayi ya isa ya sanar dakai takai koluluwar halin dimauta da rikita Dan sosai yaa malam ya bata mamaki yakuma kure mata tunani

Ganin ta rikita tana gagggaya masa maganganu masu tsananin nauyi da raunana zuciya yasa shima ya kakalo dauriya ma xuciyarsa ya soma zaginta yana daka mata tsawa yana cewa "itama bai barta ba,acewar sa yana gamawa da rayuwar zaidu zai komo Kan nata,saiya toxarta su ya muzantu su,suji zafin abunda yaji da suka saka mahaifiyarsa ta Sallame sa...ya rinka zaginta yana dirin masifa akan zubar mai maganin datayo wanda tabbas yaji matikar baqin cikin faruwar Hakan,Dan Koda ya sake Wani baizai to tasiri ba,Dan a shekara sau daya ake amfani da turaren tsabar karfin sirrinsa,kenan Babu halin ya kara daukar mataki cikin gaggawa dole saiya jira Wani shekarar ta zago,ji yake tamkar ya shake hadiza yakaita har lahira,a xuciye yake kallonta yana huci umma bata fasa ba tana ta jefo masa nannauyan kalamai wanda komin bushewar zuciyarsa sanda suka tsagashi suka shiga sunai masa zugi da ciwo,...karshen ta zama tayi dirshan akasa agaban sa tsabar ranta ya baci dan abunda take gudun shiya soma afkuwa dasu..
Ta soma fidda abubuwan dake zuciyarta game dashi,Tana bayyana masa cewa ta tsane zaman gidan sa tace masa saboda kwanciyar hankli da martaban rayuwan yayanta kawai take zama dashi bawai dan ya isa ba .
Tace ta gwammaci tayi karuwanci ta biyashi kudin bashin maganin dayake bin yakumbo akan zaman auren sa..
Ta rinka kuka da zuciyarta tana cewa tana nadama da baqin cikin kasancewar sa uba ga yayanta,tsantsar tsanan datakemai kawai take bayyana masa a furucin ta wanda Hakan ya dame xuciyarsa matika domin kuwa bazai taba iya rabuwa da hadiza ba,Dan kaf cikin matayen daya aura Babu wacce ta taba shiga ransa ta Sami matsiguni da daraja inba hadiza ba,aransa yana matukar kaunar hadixa,yana matukar matukar sonta irin sonda baima San ko so bane ko tabin hankli bane,shidai yasan ko mutuwa hadiza zatayi da tsanar sa saidai ta mutu a dakinsa Amma bazai taba iya rabuwa da hadiza arayuwarsa ba.

Shiyasa ma ayanzun dayake sauraran munana kalaman tsana datake fetsa masa aransa ya shiga jn kamar wuta ake watso waa gangan jikin sa ana qona sa.

Umma hadixa kuwa ba a ma cikin hayyacinta take ba sai magnganu kawai take yi
Tana ce masa gata ta dawo masa saiya kasheta,ya rabata da yayan ta,ya rabata da rufaida alokacin datake bukatar ta matuka
Tace malam ka cuci
Rufaida kamata auren dole ka Dora mata qaddarar kashe mijinta
Ka muzanta rayuwar ta
...malam tsakanina da Kai har mutuwa bazan yafe ba...
Allah ya isa min Allah saiya sakawa rufaida da sauran yayana...

Wani irin damko ta yay ya shakure mata wuya ya shiga dukanta yana kwallo da Ita har suka shiga daki yabi ya jefata akan gadonsa ya kulle kofar dakin da makulli..

Daga kofar gidan kuwa Yan gulma ne makil wayanda suka jiyo kururuwan ummma hadiza maza da mata sunkai su goma Duk an kasa kunne anajin abubuwan da suke fada...

Kan kiftawa da bisimilla har labari y karade anguwar kaf sanda akaji labarin cewa Rufaida yar gidan yaa malam
Ta kashe mijinta...
Wani irin hargitasen gurmi mai tada fence aka bude lungu da sako hirar da aka sunkuya yi kenan,saidai rufin asiri irinna ubangiji yasa iya maganan kisan kawai suketa riritawa ba'aje ga sauran abubuwan da sukajin ba,Dan aganinsu mace ta kashe mijinta ai bakarmin al'amari bane...

A safiyar ranar haka yaa malam ya sauke muguwar azabar jarabar sa datake ciccin sa ajikin umma,ya mata kaca kaca,ya shiga lungu da sako ajikinta yana mai huce haushin tsnar datace tanai masa,bbu gajiyawa sanda ya sauke Duk wata niyyarsa wanda tamkar yau ya soma tarawar aure da Ita,sosai yaci yaji dadi bai sauka akanta ba sanda yaga bata Wani kwakkwarn motsi,yana rikitowa kasa ya saka hannu ya jawo katon garen sa ya saba ya rufe tsaraicin sa yay dayan sashen da uban sauri Jin Wani azaban son hadiza dayake rikita masa tunani da zuciya

Duk da haka ma aransa cewa yake saiya ci uban hadiza saiya sata nadamar rainasa datayi yau..
Saiya raunana mata xuciya...

Da wannan rudaddiyar yanayin ya shiga bayi ya doro wanka,ya dade yana wankar saboda Wani sabuwar nitsuwar dayake dirar masa yanajin nitsuwa,tabbas hadixa mace ce Dan kuwa bai tabajin akwai macen dazatayi masa dadin da hadiza take masa ba har Abada Babu wacce take da baiwa irinta hadiza Dan ita ta musamman ce a duniyan mataye..

Yana kammala wankan sa bai jira uban kowa ba ya koma sashen Inda ya sameta har yanzu akwance cikin tsaraici tanata kuka,kallo daya ya mata ya dauke kansa da zafin hakan aransa Amma saiya basar ya cigaba da abunda yakeyi yana kammala shiryawa ya saka Kai yana Jan mata tsaki yayi fitarsa waje..

Umma dake Jin kamar ta hadiye ranta ta mutu haka ta daddage ta koma sashen ta ta nemi ruwan zafi ta shiga ciki,kafun kace Wani zagowar rabin sa'a harta soma jin daidai ajikinta,cike da dauriya da jarumta irinna mata ta warware cikin tunanin matakin da zata dauka arayuwarta Nan gaba...





*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


Part1:chapter 25



Daga ta bangaren su yaa sheik kuwa tunda ya idar da sallan fajr daga masallaci sai bai dawo cikin gidan ba ya tsaya a masjid din yanata karatun qur'ani wanda Duk da kasala da kwiuwa dayake neman shigarsa ya hanasa komi bai hanasa cigaba ba da aiwatar da karatun sa ba..

Sanda yay karatun sosai sannan yadan somajin dama dama Duk dama still kanshin bai dena masa nauyi sosai,anan ma baiyi kuskuren komawa cikin gidansan ba,jikin shi yanata basa cewa in har ya shiga ciki to tabbas kwanciya kawai zaiyi,da jallabiyar sa ajikin sa ya wuce direct sashen mahaifiyar sa..

Da kyakkwan sautin Sallamar sa mai cike da nutsuwa da Kamala ya kutso kansa ciki yanamai kalamshe idanuwan sa da mamakin abunda ya tarar da Ita tanayi..
Dan Murmushin gefen baki ya saki yana mai kada kansa wato haryau hjy bazata dena basa mamaki ba

Ita kuwa tunda ta daga Ido ta kalle sa bata kara kallon ko ina ba ta cigaba da abunda takeyi har ya karaso daf da Ita ya rusuna"..kin tashi lpya mama?..lpya kalau Alhamdullhi tace tana sauke wata nannauyan Ajiyan xuciya fuskarta tamkar Babu abunda yake damunta,Allon rubutun ta data gama wankewa ta daga tayi dashi can gefe ta jinginashi da kujera,tawadar da qur'aninta Duk ta Kau da su,u can tell dat ruwan rubutun ne acikin kwanon shan dake gabanta komai zatayi dashi oho yaa sheik dai binta da Ido yakeyi
Tana Dan tofe tofen ta,Yasan yanxu haka yana tsoma mata baki acikin lamarin xatace masa yay mata shiru Dan baisan komi ba,a Kullum acikin alfahari take da ahalinta,da kuma gidan da ta fito a matsayinta na yar gidan malamai,jikar malamai wanda kusan kaf zuriar mahaifinta da mahaifyarta malamai ne dan haka Babu Wani abun da bata iya ko ta sani gameda da malanta ba,duba da Ita kanta malamin zaure ta soma aura wanda zamanta a gidanshi kawao ya sata iya abubuwa Kuma tasan ta bambace gaskiya tsakanin malamai masuyi tsakanin su da Allah da masu saka son zuciya da asiri..
Shiyasa ma take ganin kamar a duniya babu wanda zai kaita sanin halin danta bukar dan kowa kwatankwacin halayyar sa kadan ne Babu acikin na mahaifinsa marigayi malam Amadu,.

Shiyasa tunda ya fita jiya cikin fushi ita sam hanklinta bai kwanta akansa ba,so bayan ta idda sallolintane ta fidda tsohon ajiya itama tayi yen rubuce rubucen ta da niyyar zata sha ta bawa danta zaidu yasha yauko yaki Allah saiya shi Dan yaa sheik bai yadda da irin abunsu na malantan Nan ba shidai yafi gane asibiti ko addua,Sam Sam baicika son shan Wani ruwan rubutu....

Bayan gaisawar su take cemai yakamata shima ya wuce can abuja yaga ya ake ciki dasu hajya goggo Kar suce ta ajiyeshi akan damuwar jikokinta,Murmushi kawai yay yace insha Allah zai je din,saita kafesa da Ido ganin yadda yake magana yana Dan yatsana fuska alamn kanshin har yanzu nadan damun sa yace mama ke yaushe kenan zaki taho?na dauka tare zamu wuce dake..
Tana lura dashi sosai tacce Ina zaidu,ai ku tafi can kawai inkaga nabar garin nan to komi ya daidata a rayuwar rufaida ne,Dan wayancan kam ban sansu ba..ji jikata ce damuwata...koya ma suke ciki oho?..tsaki taja cikin mita,tace awo ace mutum tsabar ya kashe xuciyarsa bazaima iya siyar Dan waya a hannun sa ana kiransa anajin abunda ke tafiya ba,zaidu ko kataba ganin hannun hadiza da wayar salula?nide ban taba Gani ba..
Kuma Duk wannan laifintane"abar bukar da jahilci amma ai shi ba matsiyaci bane..

Yaa sheik yace mama kamar tana da waya fa,cikin yar masifa ta juyo tace To daman kana sane kabarni inata kumfar baki,wayarta ta rarumo ta Mika masa tana miqewa sakamin lambarta anan,bai mata musu ba ya amsa lalubar aljihun jallabiyar sa yayi Jin ashe baifito da wayar bama yy fitar sauri gudun kar ya rasa salla atke ya maido mata wayar yanacewa mamma ki bari in nafito zan kawo miki kamar banfito da wayar ba,karban wayar tayi tana mita
O o nikam ma mairuwana da hadiza da ake min rowar lambarta
,badon jitakata rufaida bama Ina ruwana da wata hadiza,"..jingina Kai da yaa sheik yay a raunane yasata katse maganan cikin sauri tabishi da Ido Sam Sam bata fahimce yanayin sa bafa,sai tayi shiruuuu"can dai tace Kai zaidu?Wai meye haka kake narke min kamar Mai sabon ciki,ince dai ba sabon matsalar bukar ka dauko zaka yafamun ba?
Zaidu kafa kiyayeni
Kadauka ban fahimce ka bane
Anya zaidu kama runtsa jiya kuwa?
Wai Wai to ya naga idanunka sunyi Wani ciki ciki?
Ka dauko damuwar banza ka dorawa zuciyar ka..to kaima
Saika kashe kanka tunda bajina kakeyi ba,da sauri cikin dauriya yace a'a mama wallhy ba haka bane..
Tunda kince bakison maganan yaa bukar insha Allah bazan Kara kawo miki ba,ni damuwata rufaida ce,Wai naga ba lpya take dashi ba shine Nace toh ya za'ayi da Ita kenan?cike da yar hatsala Tace ohon musu,"..nide na hadata da uwarta,Kun dauka ko bansan abunda nakeyi bane?

Nayi Hakan ne Dan naga ko hadiza tana da sauran hankli,
Ni nana na haifi bukar,dukkan ku bazaku iya gayamin abunda bukar zai iya aikatawa,wato shi jahilin mutum yafi kowa gudun abun da zai rage masa kimarsa a idon mutane nasan bukar bazai taba yarda hadiza ta shiga masa gidansa tare da rufaida ba..

Nikuma burina kenan,nayi Hakan ne sabida hadiza ta shiga hanklinta ta zabi yarta rufaida ta rabu da bukar,zaidu Ina matukar tausaywa rayuwar yarnan hadiza,gashi bata da wani gata,banda azaba Babu abunda bukar yake gana mata a tarayyarsu,ita tsohuwar nata ma Duk talauci da ciwo ya nakasa ta bamai iya karban ma hadiza yancinta sai yarta rufaida..

Nayi musu Koran Kare ne sabida ta zuciya ta rabu dashi nahar abada itama ai tacanci taje ta kula da kanta....
Zaman gidansa zaman aljanna ne?
Inhar tayimin haka Nan ne zan iya kulawa da jikata rufaida acikin sauki batare da nama hadu da jarabar bukar ba..
Wallhy saida yaji anayi Wai kunu a Wani gida,Nan gaba in hadixa ta samu miji tayi aure nadan bazata hanani dauko rufaida gabana ba..yarinyar Nan tazo ta huta,dudu shekatun rufaidar nawa ne? Baifi acemin sha shidda ba fa,shukra anan saida aka haifeta kafin aka haife rufaida,kaga ai da sauranta,Duk karatun datake so inta dawo gabana saitayi shi,kamun ta Kara girma kadan sai in aurar da ita,insha Allah saina bawa bukar mamaki sai yayi nadamar abunda ya aikata min,...
Ajiyar xuciya Yaaa sheik dake kallo bakinta tuntuni ya sauke yace "Allah ya rufa asiri,Amma mama banso ace kinyi sanadiyar kashe auren yaa bukar ba,aure fa sunnan ma'aikin mu ne SAW,wanda a ranar karshe shida kansa zai kasance acikin alfahari da mu,bance shawarwarin ki basuyi kyau ba Amma nide Sam banji dadi daya jawo mutuwar aure ba,..
Mama kituna fa shaidan yakanyi matukar farinciki akan haka,nasan dai hadiz batajin dadin aurenta Amma ai qaddarar ta kenan,wanda inhar ta riqesa da Imani Sai kiga Allah ya dau mata mataki akansa dakansa..
Nide bazanso ace kece sanadiyar rasa auren hadiza ba.
Hjy mama dake harararsa tace eh ai dama nasan Hakan zakace shiyasa ma tun jiya nayi burus da qudiri ban saurareka ba..
Nima ai cewa nayi inason hakan ya afku bawai cemaka akayi har ya afkun ba,hmm zaidu?wato zaidu baka tashi yin wa'axinka sai akaina ko?yo ni meye nawa anan Dan Nace Ina neman wa rayuwar hadza sauki zaka wani fara lakamin tsiya kana hadani da shedan wai na kashe aure?..oh ni hasiya?karufamin asiri,basaima hadxar tayi wayau ba,kasanta fa saunace bana cire tsammanin bukar baiyi kwanan buzu akan yarnyar Nan ba ace mace Sam Sam ba zuciya?

Cikin sanyin Murya Yaa sheik yace insha Allah Duk zaa samu mafita..
Tace toh Ameen tana Satan kallon sa da gefen ido ganin yadda yake layi layin nan tasan bazai wuce yace mata zai koma can sashen sa ba
Caraf ta miqe tace jirani anan Ina zuwa
Bata jira mai zaice bama ta wuce sama cikin sauri tare da rubutun ta,kitchen ta nufa direct ta ajiye rubutun akan table,ta isa gaban Wani katoton microve ta dumama abincin dataci daxun yay saura Dan yau ko bacci bata samu tayi ba,so tuwon amala ne da miyan ewedu tana kammala xubawa a Dan plate ta debo hadadden miyar stew dinta dayaji barkwano qamshin atttarugun Duk ya buleta,dake kan gas yake haryanzu shima da zafinsa,nan ta yayyafa shi akan tuwon tare da namomin kaji daya cike ciki,ta dauko Wani katoton water flask da mug cup fari ta bude flask din ta juye rabin kunun daka dayakeci yana fidda uban qamshin kayan yaji,citta masoro,kajiji da sauran tarkace,ruwan rubutun ta ta dauko ta juye acikin kunun ta dama shi sosai yasan sake saida daga Gani zaka iya fahimtar Hakan sabida yadda kunun yaso yay tsololo.

Oho itadai bata damu badai aranta ta qudira cewa lallai zaidu saiyasha kunun na

Adan karamin tray tayi serving dinsa Kan kace kobo har ta sauko abu da bata taba ganinsa yayi ba takansa yanayi wato tagumi

Dan Kyabe bakinta tayi tana tahowa da mamakin yanayinsa aranta tana isowa gabansa ta aje tray din tace saika zauna kaci abinci ai tunda bakowa agidan daxai baka abunci Wayancan masu aikin naku dama ba iyawa sukai ba

Sanda Nace ma Jasmine ta tattarasu kaf suje can abuja Amma dake kunnen kashi ne da Ita sai ta kwashe su uwani da dayar mai dafa musu jagwlgwlen ta barni da maman Abdul,gyara zaman sa kawai yayi agabn abincin yanajin shirmentan danyasan bai isa yace mata bazaici ba,Alhalin ko kadan baijin sha'awar abincin Dan bakaramin ciwon Kai da bugun zuciya yake fama dashi ba..
Ayanzu Babu abunda yaketa bashi kamar kansa sanin komin kankanta ciwo yakan iya yin addua ya shafa awajen Amma yau saiyaga yakasa yin Hakan gaba daya,Wani irin muguwar axaban gajiya da kasala sun gama nakasa masa xuciyarsa taciki wanda kwata kwata baisan silarsu ba..
Arayuwa yakan going stress din daya ci uban na jiya shiyasa baiga dalilin da za'ace har jikinshi yana sacewa har haka ba,sosai yanayin sa yaso ya damesa aransa gudun ma kar ace masa Wani ciwo

Please Login or Register in order to submit comment