Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rayuwa mai kyau wa yayanki a Duk Inda suke,Addua yana sauya qaddara daga mummuna ya dawo kyakkyawa ina miki fatan samun sauki umma,sannan kisa aranki ni ina tare dake,insha Allahu Allah bazai barsu rufaida a hannun wani mugu ba
..Nakasahiyar Murmushin ta mai tafe da hawaye ta sauke tana kallon fareesan"..tace toh shikenan fareesa na ji shawararki..Allah ya miki albarka Allah ya saka muku da alheri dake da iyayenki nasan kunyi iya bakin kokarin ku akaina da Yaya na.Yanzu dai ki zauna kihuta,jikina da Dan sauki bari inshiga ciki in samo miki ruwa..da sauri antumy reesan ta rikota tace A'a umma kibarshi kawai,saita mata karya tace inama azumin litinin da alhamis,kedai zauna kici abincin Dana kawo miki

Murmushi kawai tayi Dan rabonta dataji sha'awar cin Wani abinci tun satin daya wuce Amma sabida damuwar datagani a idanun faresatun yasa tace zata ci "..
Miqewa Anty fareesa tayi ta shiga ciki Jim kadan ta dawo da plates har guda biyu da serving spoon Dana cin abinci,ajewa tayi sannan ta koma ta debo kofuna ta kawosu, ledojin data shigo dasu ta bubbude ta fidda Dan madaidaicin cooler abinci da sauran abubuwan ciye ciye data kawo

Gyara zama umma tayi tanata kallon yadda ta ke saka mata abincin,komin ta a nitse yake tamkar yarta rufaida,fried chicken stew ne da spagehti,adan roba haka kuma tayi couslou mai kyau ta hada mata dashi da fruit salad da ruwan gora mai sanyi
Tana kammalawa Mika mata tayi tana Dan murmushi umma ta amshi abincin badon ranta yaso ba,a hanklli ta shiga ci sai dai Duk hanklinta naga kan yayanta ne musamman ma rufaida..koma Suna samun abincin suci ko Yaya ma take ciki?shin lpyarta kalau? Duk dai bata sani ba,kuma ta maidashi abun damuwarta.

Tana kan ci anty fareesa ta shiga yayyanka mata fruits daga cikin wayanda ta kawo abarba ne da apple da kuma lemo sai kankana da ayaba.

Umma zan aje miki wannan a fridge in anjima saiki sha.
Yanzu kam nafiso inga kinci abincin nan sosai sabida jikinki babu kwari,karamin Ajiyar zuciya umma ta sauke tace Toh faresatu Allah dai yy miki albarka. .tace Ameen,"can umma tace "uhm dama zan samu wanda zai tayani ci ne Dan bana jin dadin cin abinci ni kadai, babu tantama
Anty fareesa ta bar Duk abunda takeyi tawanke hannunta ta taho suka hau ci tare,mamaki sosai ta bawa umman saidai batace mata uffan ba dake ta fahimce meyasa da can din tace mata tana azumin
'babu laifi sosai Anty reesa ta ja umma ta cika cikinta da abincin tam,sosai take nuna mata kulawa da tausayi Duk dama ata Wani fannin Hakan kusan umarnin mahaifiyarta ne da kuma kakarta hjya mama Dan ako yaushe basada abokiyar tada damuwarsu sai ita

She is not planning tama gaya musu cewa tazo din,Dan tasan inhar ta fada to tabbas Hajiya mama zata iya barbada maganan awaje har yaje kunnen yaa malam da ko kadan bata son yaji cewa tana zuwa bare a kara saka umma acikin Wani matsalar..

Sosai umma ta samu relieve da kasancewar anty fareesa atare da Ita yau,wacce bata bar gidan ba saida ta gama mata aikin komi ta tsaftace mata gida.

Bayan kwana biyu haka ta kara dawowa each time taxo saita nemi taji damuwarta badon komi ba danta tayata rage abubuwan datake dannewa a zuciyarta tana fama da azaban nauyinsu itakadai..

Barister fareesa tayi iya kokarinta a satin har saida umma ta soma dawowa hayyacin ta..Wani bin inta mata hira harka ga tana dariya sosai

To aranar da yaa malam zai dawo ne sukayi ban kwana kuma aranan ne faressan take hadasu awaya da su hjya jasmine wacce ta gaya mata cewa sun yi tafiya da mijinta Yaa sheik suna can Abuja..

Fatan alheri tayi musu sannan tayi godiya,she was bit ok yanzu kam data samu wayanda suka Dan kwantar mata hankli wajen gaggaya mata maganganu masu sauki wanda suka kara mata jib karfin gwiwar fuskantar rayuwa..

Abu daya kawai tasaka aranta yanzu kuma shine Allah
..dukkan lamarinta da na yayan ta gaba daya ta mikka masa
Ta kuma saka aranta cewa zai Kare mata yayanta a Duk Inda suke a Duk halin da suke ciki..

*Bayan kwana biyu*


Agogon _Mariano de veio_ din dake manne jikin bango ne yayi ticking dot 6:30am dai dai na safiya tare da yin sautin alarm mai karar morning scent wanda tuni ya gauraye wajen da kara mai cikka kunne.

Tashi yayi tare da mikewa daga kan lallausan katafaren gadon da yake kwance akai,yana mai karanto adduar tashi daga bacci i.e Alhamdulillahillazi ahyana ba'a dama amatana wa illaihin nnushur sannan ya kara dayiwa Annabi (SAW) salati

Dagowa yayi sann ya juya ya kalli agogon da ya farkar dashi daga bacci yaga har 6:35am tayi,da sauri ya diro kasa daga nan baijira ba ya fada toilet din dake cikin dakinshi

cikin hanzari ya saka toothpaste acikin brush dinsa wanda yake fari kal brand din bojaler senteler,da sauri sauri yayi brushing teeth dinsa ya kunna shower yay wanka sannan ya fito daga toilet din daure da hadadden white body towel da kuma wani dan karamin towel din a hannunshi yana famar goge fuskarshi da ita har ya karaso gaban wani babban mirror da mutum kan iya kallon kanshi gaba daya tun daga kai har kafa yana kare makansa kallo,..

yana cikin karasa goge kanshin kenan zai shafa mai yaji karar wayarshi na ringing,Dan daga girarsa sama yy da har yayi kaman bazai dauka ba sai kuma ya juya ya karasa inda wayar take yana ganin mai kiran da sauri yayi maza ya dauka tare da neman wajen zama cikin risina kai mai nuna alamar tsantsar girmamawa tamkar mai Kiran na gabanshi zama yayi kamin ya kara wayar a kunnanshi tare da cewa Hello mummy kin tashi lpya?Daga daya bangaren aka amsa da cewa lpya Alhamdulillah sannan aka sake ce mishi harka shirya ka fita ne yace à ah mumy Amma saura kadan yanzu zan shirya in fita

tace ok,uhm yawwa Dama munyi magana da Aina'u ne tace ta kikkiraka baka dagawa ko lafiya?

Take walwalar fuskan sa ta dauke tuno da abunda ya afku jiya, Dan shiru yayi sannan yace lpya kalau mumy bacci nayi dawuri or..or maybe I wasn't aware..

Tace toh saika nemeta pls..it's asif she is tensed ni bangane mata ba,ko Hala bata San zaka dawo nigeria Ajiyan bane oho?I dint know that she is not back yet Ni tun ranar da tace min zasuje kadunar ma bamu kara magana awaya ba,but yestade she told me dat you ain't picking up..nikuma bana gidan ma bare ince a kiraka ka amsa.

Adan gaggauce Yace "No..Karki damu mama,I will call her..bye.

Yana fadan Hakan ya katse wayar sa batare daya jira Wani furucinta ba,da alamar ranshi ya lalace.

Closet din kayanshi ya bude sannan ya dauko wani sky blue din getzner mai laushi da tsada ya saka ajikinshi,ya bude wata madaidaicyr transparent visconte safe ya dauko cuff links dinshi masu azaban kyau na kamfanin Mandarina duck sannan ya sanya su a hannayen rigartasa tare da dauko hularsa ta Zanna bukar shima sky blue mai ratsin brownish_black da dot din red ya seta Dede a kanshi kamar da kan akayi hular ta zauna d'as das,agogon shi na rolex oyster ya makala a hannunshi na dama sannan ya dauki Turaren paco rabane da Calvin Klein dake gaban mirror dinshin yafesasu a jikinshi
Duk Inda ya juya kansa qamshin ne ke binshi
... kamin ya koma gaban wata small coffee table,hannu ya Mika ya dauki car key din motarsa dake ajiye akai da kuma wayarsa daya jefata acikin aljihu sannan ya jawo takalminshi baqi half cover ya fito daga dakin yana saukowa yana dan kallon agogon hannun shi yaga wai har bakwai da rabi tayi


Saukowa yake daga kan benen cikin kwanciyar hankali da natsuwa har ya karasa sauka ya isa katafaren parlourn su, karasowa yayi cikin parlourn ya isa wajen wani dattijon mutum mai dan haske yana sanye da manyan kaya na alfarma , sanye yake da farin glasshi à idonshi hannunshi kuma riqe yake da Wani katoton littafin sharia at same time ya saka tashar Iqra yana jin yadda yaran musulmai ke nuna farin ciki ga ubangijinsu wajen saukar da karatun qur'anin sa mai girma da sukayi.

gabanshi kuma glass table ne dauke da hadadden royal flask din tea an zuba Kadan a dan karamin transparent kofi na shayi,Nan ya karasa gaban sa tare da zama dab da kafan dattijon tare da Ce mishi "fatan ka tashi lpya Abbu?Barka da dawowa,
Sauke lttafin dattijon yay daga idanun sa yadan kallesa kadan yace barka dai mufrad ka tashi lafiya? yace Alhamdulillah abbu sannan yace mishi Jiya na tura Adamu da aika wajen ka an sanar maka?yace min ka rufe kofa kuma wayoyinka ma duk a kashe

A hankli yace ehh Abbu na gajine jiyan shiyasa na shiga da wuri na kwanta,Amma kauyukan da kace aje kai zakka an gayamin wai hanyoyinsu babu kyau amma keeyan ya kirani ya fadamin
Komi ya tafi daidai

Atakaice dattijon Yace ehh tun jiya ya kirani,daga Nan shima yace okay bari in shiga inga Hajiya mama dan tun safe ta aika a kirani ban San meye matsalarta ba

murmushinsu na manya kawai alhj zayd yy yace ai Hajiya tun karfe biyar ta tashi bata koma ba sai da tashi kowa har masu aikin gidan nan,kaga tun sassafe aketa hidiman dafe dafe.hmmmn

Dan murmushi yay yace ai Hajiya akwai kokari,ya karashe maganan sa Tare da miqewa tsaye,"na barka lpya Abbu..
gyada kai kawai yay ya Dan kallon sa harya sauka daga kan matakala da basu fi taku sha biyar ba yabi wata hanya har ya isa bangaren kakarsu tare da yar sallama a bakin kofar Wani Text ne ya shigo wayarsa adaidai lokacin da yay knocking kofar palorn sai ya tsaya karantawa,daga ciki kuwa nazli ce a zaune akan dinning table tana shan corflakes wanda ta tula masa rabin kwalin madarar dano da dan water flask haka agabanta dake bata ma iya shan shi da ruwan sanyi ba.

Daga cikin palon kuma Wani hadadden matashin saurayi ne wanda kwata kwata bazai wuce 25 years ba ya nitsu sosai ya maida hankalin sa agaban wani babban tv screen wanda already ya jona da wayarsa ta iphone yana kan buga video game dinsa mai suna Assassin's creed da alaman dukka hanklin sa nakai

Daga ta dayan bangaren kuma shukra ce akan cinyar yar tsofuwar sun babu abunda take sai rabza mata shagwaba,tayi nasha nasha akan cinyarta da system akan cikinta Suna jin wata waqa tare..
Jin an kara yin sallamar yasa ta harare su duka tace
"To wa zaije ya bude muku kofar..

Cikin su kowa ya turo baki,da alaman keeyan kam ko jinsu bayayi,"da gefen ido shukra ta bibbisu da kallon kasan Ido sannan ta dada gyara kwanciyarta tana tabe baki..Nide bazanje ba wallahy
Ai nagaya maki tun jiya na fadi ciwo ma fa kafa na yakeyi
Hjy tace I min shiru waye baisan halinki ba shukra?dagowa ta karayi tana dubanta ..to ke kitashi kije mana ai Nan falon ki ne,baki bude hjy mama tace
In tashi inje ko?toh saukar min da wannan gingrimin kan naki a jikina ki tafi can dashi,ai ba kurguwa uwata ta haifeni ba kune dai
Kuka lakawa kanku sakalci,narkewa ajikinta shukra ta karayi,hjy Dan Allah Kar ki je ni gaskiya bana son in mike zaune,"..a hankli take kallon yayun nata tace baga su Nan zaune ba?su din me sukeyi,hjy taja kunnen ta,cikin biye mata itama kasa kasa ta furta maganan ta tace eh lallai kam to bari dai sujiyoki keeyan kadai ya ishe ki anan, sannan ta juyo ta kalle nazli dake shan cornflake dinta hankli kwance
"Bokan turai ai Kya tashi ki bude mana kofar ko?ko kema kin karya kafan ne inje dakaina,nazli batace uffan ba ta miqe ta nufi kofar ta bude,gaban ta ne yy mummunan faduwa ganin yaa muffy ne a tsaye da uban sauri ta bashi hanya ya wuce tana binshi da gaisuwa,"..good morning yaa muffy".
Muryan ta na Dan rawa ta ce hakan kallon 2 scnds ya mata sannan yace
Morning,me kikeyi a gida?tace hutu aka bamu..shi ne hjya tace wai nadawo Nigeria,shekaran jiya na dawo..
Wani irin kallon ya wtsa mata ya tabe bakin sa sannan ya furta".Good for you
Now..excuse me.
Matsawa tayi can gefe da shi har ya karaso ciki dawuri ta koma kan dinning din ta zauna ta cigaba da shan cornflakes dinta

Shima wajen zaman ya samar makan sa kusa daf da su hjiya ganin yadda dukan su suka sha jinin jikinsu yasa shi hade rai yy tamkar bai ma gansu ba

"Keeyan ne ya juyo ya fara gaishe sa ya amsa masa normally ,baima jira ba ya katse kallon game din San kawai yay waje,a hankli shukra ta janye jikinta zata miqe saura kiris ta fadi
"Get out of here ya daka mata tsawa sanda ta kara tsorata,hjy ta riko ta"a'a ya haka yarinya ta tashi xata gaishe ka zaka Wani hantare ta?.
Kuma fa kafarta ya karye...baima kula mgn da kyau ba ya furta"to meya hanata zuwa asibiti?ita yarinyace da sai angaya mata..ya furta hakan a hankli yana mai relaxing kansa akan cushion din,cike da barin Murya shkra tace..ai Hjya ce..yay saurin dakatar da ita da idanun sa
."Shut ur mouth..ba dake nake magana ba..meit ta nade bakin taja tayi shiru tayi tsuru tsuru ta rasa meyasa yaa muff baya saurara mata arayuwa,
Hjya ma batace musu uffan ba nazli ta gama ta tattara cups din takai kitchen daga Nan bata kara saukowa ba,shukra ta zame tabi bayanta a sudade..

"Ke bazaki saka Ido akansu ba.
Islamiyar da kika ce za' ana koya musu fa..one is busy eating rubbish kinbi kin sakalta wann wawaiyar ta girma bata San ta girma ba,gwara ma maska(keeyan) atleast hutawa yakeyi..

Ai dole zaka ce haka kabi bayan Dan uwanka namiji dake buga game din banza a wofi sabida sukam zunubi kaga suke aikatawa ko?

Dan tsaki ya sake kasar wuyar sa
Why did u call me
Meye?ya dage qirar sa sama yana dubanta a tsime.

Ajiyan zuciya ta sauke ta danyi shiruuu kai kace ba ita ta gama masifa ba"..can ta juyo ta kalle shi ganin ya dauko bootle water yana shirin bude murfin da alaman zaisha,yasa ta kyale sa harya saida ya gama sha yy hamdala..gyara zamanta tayi
Uhmm magaji?ganin ya shareta yasa ta saka fuskar kuliya tace dama wata magana ne ke tafe dani,Idanunshi ya wara akanta da alaman yanaji..Dan shiru tayi sannan ta sauke Wani sasanyar Ajiyan zuciya"...Akan kawun ka ne?
Nace ko zaka iyayin anfani da mutanen ka ka binciko min
Shi Ina son insan halinda jikoki na suke ciki dan Allah magaji kataimaka min bana bacci inna tuno su..Nan da nan muryan ta ya sauya kalar kuka yace hmm,"tou meyasame su su kuma,ta fashe da kuka ai dama baka damu ma dasu ba ta ina zaka San damuwarsu?yan uwanka ne fa mufrad?hr ace baka san halinda yayan kawunka suke ciki ba,kukan ta karawa sauti kamar wanda aka bugeta,yy shiru yana kallon ta sannan ya dauke kansa akanta

Har saida ta sasaauta kukan sannan ya juyo,
"Ki fadamin meyene? ni bazama nake ba bare in sani..Sanin kanki ne abhu yace Kar muje gidan kawu Wani hidima Arne fa yake ce masa

Tace eh Amma ai yan uwan juna ne kuma ni na haifesu duka...hannunka bazai rube kayanke kayar ba tunda shi yace babu ruwanaa ai kai saika na kulawa da rayuwarsu ko?

Hmm kawai yace bayan wasu mintina yace toh ni me kike so nayi musu naga dai dukkan su matan aure ne kowa tana gidan mijinta

Eh nasan da Hakan Amma ai auren bada son ransu bane,yafa hana kowa yaje musu kuma ya hanasu kawo ziyara gida...

Dan Tsaki ya sake yace"..Kuma suka yarda masa ahakan?it's thy choice den..
Dan daure fuskarta tayi ta shiga mita kasar wuyarta tana ta fade fade kusan anan yaji Duk abunda ya afko daya baya Nan

Ganin abuntan bana karewa bane yasa shi ya amsa ta amma badon yaso ba,miqewa tsaye yayi da alamn ficewa zaiyi yace insha Allah Zan sa a duba miki halin da ake ciki,Amma saina nemi izini daga wajen abbu
Dan share fuskarta tayi da bakin mayafinta tana mai washe baki tace toh shikenan,Dan Allah dai ataimaka musu magaji,Duk Inda naka yake au naka ne,ya gyada kansa,dan
Murmushi tasakar masa hade da saka masa albarka
Daga Nan ya sakai ya fice a sashin.






*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


Part1:chapter 9
*Destiny At fault.*



_9.30am:ivy cottage U.S.A._



Hasken ranar da ya hudo windown dakintan ne ya sata bude idon ta a hankali..

ranan da ta gani ne ya sa ta wara yan madaidaitan idanuntan ta dubi karamin agogon dake kan bed side drawer taga har 9:30, da tsalle ta sauko daga kan gadon gashinta mai tsayi da cika da ya barbaje tana bacci ta kama ta hade su in a messy bun sannan ta sauko

toilet ta nufa ta kuskure bakinta da mouth wash tayi maza ta tube kayanta sannan ta kunna shower tana mai sake ma jikintan ruwan sanyi, can ta fito daga wankar bata tsaya yin wata wata ba ta maida kayan jikinta tsaf kamar yadda tasaba Dan dama sukadai ne gareta bata da Wani kaya.


Daga Nan fridge din dakin ta bude ta dauko ruwan sanyi ta sha kadan sai ta mayar da gorar shima ta ajiye,Wani nannauyan Ajiyan zuciya ne ya kufce mata mai alaman dawowa da Ita cikin hayyacinta,Dan juyowa tayi tana shirin komawa bakin gado caraf sai idanunta suka ci Karo da Wani faranti a lullube da farar wrap da alamar abincin ta Aka aje mata kamar dai yadda aka saba yi a kullum

Gaban abincin ta nufa ta bude wrap din a hankli tana kallon abunda ke ciki,normal chips tagani da omaletes saida wani abu kamar sandwiches a dukunkune Agefe
She is very hungry saidai gaba daya abun duniya ya dame zuciyarta sai taji kwata kwata ma kamar bata sha'awar cin komi,yau kwananta 7 kenan da zuwa Nan akoyaushe tana kirgawa Amma Koda sau daya ne ba'a barta tafito ba kuma shima mijin nata baizo mata ba...

Tunda wancan matar ta kawo mata abinci da toiletries a ranar farkon zuwarta daga Nan sai bata kara ganin Wani halitta da idanunta ba,ita dai zama kawai takeyi cikin rasa yadda zatayi da rayuwarta,gashi ita ba son magana takeyi barema tace zata tambayesu Inda Alhajin yake,but now dataji ta a matse she is really feeling ready nd eager to ask Dan zaman kadaicin Nan sosai yafara razanata,she is nearly depressed alone,babu waya babu tv,daga gado sai wardrobe da Dan fridge wanda batama sanin lokacin da ake kulawa dashi,most time saita farka daga bacci ma take ganin an sasaaka mata drinks da ruwa an jona mata Duk Wani abun datake bukata.

For the past 7 days bata San wayake kawo mata abinci ba,and she only get to eat food 2 times a day, da safe da kuma yamma,yanzu haka Da wuya in ba sanda takoma bacci bane aka shigo aka aje mata wannan abincin,Babu mijin nata babu waccan matar sannan bata ganin masu kawo mata abinci.

A Yadda tayi tsammanin gidan mijinta shine daga tazo zataga mata biyu da yara da kuma ango mai dokin amaryan sa
But none of this have happen yet

Abubuwan mamaki ne kawai yaketa faruwa da ita Dan Sam bata gane ina rayuwan ta ya dosa ba,is bcoming clear to her dat she is being treated like a hostage,kamar wacce aka Sato ta za'ayi Wani abu da Ita.

Dan daga tazauna tunani babu abunda take juyawa aranta sai yanayin rayuwarta anan din, komi sounds really odd and strange Abinci sau biyu arana,daki kullum a kulle and no one is visiting her bare ajega bata waya.
Ayanzu Komai mamaki da tsoro yake bata


Haka kuma rayuwanta ya kasance inta gaji da bacci tayi kuka inta gaji da kuka ta bude window tayita kallon waje,gashi da akamar anguwar babu kowa Dan takan fi awa uku tana kallon kasa ta waje Amma bata ganin wulgawar kowa Sai daidaikun motoci...

Idanunta is alwys wet,jikin ta Kullum a nannade yake da hannayenta kamar maijin sanyi,she look so pale and agitated tamkar wacce ciwon depression yake shirin kamawa..

A dan dolenta ta zauna ta Dan taba chips din batama wani ci dayawa ba ta miqe tsaye tayi bathrum ta wanke hannunta da bakinta sann ta fito.

Gadonta ta koma ta dukunkune kanta a gefe guda,addua babu wanda batayi Amma still ji take kamar ta kashe kanta tsaban batajin dadi rayuwa

She is sooo lonely frustrated and depressed at same time,Kullum takan runtse idanun ta tayi shiruuu na tsawon lokaci wai Koda zata danji nitsuwa saidai bata iya bude idon shikansa face zafafan hawaye masu azaban radadi da ciwo sun kassara shi

Babu irin kokarin da batayi danta cimma burinta na ganin mai kawo mata abinci,Wani bin haka zata hana kanta bacci tana gadi Amma Duk abnza so take lallai ta tambayesu shin ina mutanen gidan kuma meyasa ake kulleta Amma Ina haryau dai bata taba cin sa'ar su ba


Bayan kwana biyu da taga abun babu ci saita hakura kawai ta shiga maimaita bitan karatun qur'ani iya wanda tayi hadda ta maidashi daily routine sabida tana tsananin bukatar abunda zai daidaita mata tunani ya kuma kubutar da Ita daga haukacewar da kwakwalta yake so yayi.


Haka Rayuwanta ya kasance harna tsawon sati biyu babu Wani canji,ranar tana bacci kwasam saita somajin Wani irin motsi motsi da kara kara,cikin sauri ta farka tare da bude idanunta a mugun razane saidai bata kwatanta kunna wuta ba Jin kamar ba daga dakinta motsin yakeba saidai tabbas tasan motsin agidan Nan ne..


Wani lumshe idanunta tayi Jin yadda kirjinta yake tsanata bugu,Dada Kasa kunnuwanta tayi nadan wasu lokuta can ta soma juyo muryan mutane da kuka kuka abun dai gashi nan gaba daya bata gane meke faruwa ba,ta dade ahakan,cikin yanayin dauke numfashin ta cak,a hankli ta sauke kafafunta akasa cikin sanda ta iso daf da baqin kofa, tsaye tayi abakin kofar na Dan wasu mintina tanakan jiyo sautin ihun,sai can kafin tafarajin shiru daga Nan saita bata kara Jin motsin komi ba..


A haka ta kwana cikin tsananin tsoro da razana baccin ma gaba daya kasa yinshi tayi,washe gari ma haka ya sake faruwa,haka ta rinka Jin ihun da motsi,hakama next day,har sanda ta soma jin ihun da akeyi ya Dan matso kusa a daf daf da ita kuma tabbas tagane cewa ihun mace ce wanda take cikin tsananin bukatar taimako

Tunda take arayuwarta bata taba sanin cewa tsoro da razana kan iya saka mutum fadawa ciwo ba sai akanta,Dan tunda wannan ihun ihun ya farayin tsanani sai ta somajin kamar zazzafar zazzabi ne yake ta shiganta, aranta gani take kamar gidan yankan kai kawai aka kawota za a yankata ne sai ayi kudi da Ita.

Kukan datayi a satin nan Allah ne kawai yasan adadin sa
Addua da neman taimakon gaggawa babu wanda batayi shi ba,and each time she tried to open d door sai tajishi gam gam da alamn ta waje ma ake kulleta


After 2 days kwance take akan gadon tan ta dunkule jikinta a waje guda da alaman Wani azaban zazzabine mai tsananin zafi ya shigeta harya yake hanata iya miqewa..

Ga abincin yau da na jiya duk bata samu taci ba,she was soo weak harta sallame barin duniyar kawai Gani take kamar zata mutu,cikin wannn yanayi after like 2hrs ta fara bude idanunta da sukayi jaaa tsaban ruwan dake fita aciki,ji tayi kamar ana taba kofar da alaman motsin mutum cikin axama ta ware idanunta,Jim kadan matar Nan ta shigo wanda hakan yasa ta miqewa zaune batare da ta kula da yanayin zafin ciwon bama,Tun kan matar tayi mata magana Wani rusashiyar kuka ne ya kufce mata..kara fashewa tayi da Wani irin kuka mai tafe da tsantsar razana tace "malama Dan Allah ki fitar da ni daga nan,na hadaki da Allah ki cece ni,pls ni zan koma gidan iyaye na...kallonta matar ta cigaba dayi can ta basar tace "magani akace in kawo miki,"tace waye yasan banda lpya bayan babu nake gani yake shigo min?koke ce kike kawomin abinci?toh meyasa zakuna kulle ni,am scared...please..where I'm i? ihun me nake yawan ji da daddre?ina shi mai gidan Dan Allah,
ihun mace fa nake ji kamar ana yankata,pls who are u ppl...
Da sauri matar ta matso kusa daf da ita cikin toshe mata baki da alamar bataso ta kara furta

Please Login or Register in order to submit comment