Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kansa cikin kananan kaya yana zaune a babban palon yana kallon tv,Nan da nan ya tashi cikin sauri cikin yanayinsa mai saurin bayyana tsantsar farincikin sa, yana fitowa kuwa suka hade ido da imad,da Wani irin shauki Suka harxuko suka rungume juna tsam tsam suka dunkule kansu tamkar wanda zasu balla kafadun juna,a sadade malak taja gefe gudun karsu tureta tanata binsu da kallon mamaki.

Tun kan su wanye hug din saiga Yan cikin gidan bisa layi daya na bin daya Duk anyi rubibi an fito ruututu harda su hjy Adada da hjy saddika, dake hjya saddikan ta kasa hakura tajira shi a kano itama Ajiya jiyan tazo abuja musamman Dan ta tarbeshi dakanta...

Kan kace Wani abu hjy jasmine da su hjya saddika sun kewayeshi da Ihu da hamdala jinsu yasa har ya kasa iya danne ruwan hawayen sa wanda already sun nuna cikowarsu tam a kwayar idanun sa Duk dama basu sauko kasa ba tukuna,..

Daga bakin kofar nazli da shukra ne suka Dan rakube sai rawan dari suke jikin su na rawa rawa kamar masu Jin fitsari,wani ji suke kamar zasu fige kansu sama su tashi sann su sauko akan uncle dinsu tsaban murna saidai gaba daya ganin mufrad Agefen sa ya hanasu matsowa cikin ribibi,..sai uwar surutayya ake ana kyakyata dariya keeyan ya riko hannunsa dam Dam Suna ta surutu da mutanen gida
..wayar mufrad ne yay kara yaja jikinsa ya koma can gefe yana amsawa,Wani daka tsalle nazli da shukra sukayi atare tamkar anjefosu kamar wani walkiya haka suka diro jikin imad wanda ji yay kamar an watsu masa su ne daga can can nesa,wani kankame sa sukayi subiyun atare suka manne ajikinsa kamar super glue,sautin kiran sunan sa "uncle mad",uncle mad, kawai kakeji coming in different voices with different sort of emotion.

"I really miss u...nazli ta fada da uban karfi kamar zata fashe tsabar murnan da zuciyarta yake ciki har Wani kasa tsayuwa akan kafarta takeyi..

Gaba daya jikinshi saiya mutu,sai kallonsu yakeyi da ruwan dake cike a idanunsa,gaba daya ya rasa yadda zaiyi da axaban kaunar su dake mamayar ransa,sai bin kowannen su yake da ido bakinsa ya kasa rufuwa,Wani irin strong feeling yakeji aransa irin wanda Bai tabajin irinsa ba,he Neva tot abun zai shigesa haka,missing dinsun dayake yawan dannewa aransa baiyi tsammanin cikin sauki zata iya fitowa filli ba,kasa iya furta magana yy,saidai duk abunda Sukace ko suka tambayesa saidai kaga yana gyada kansa yana dariya Dan ji yake kamar inya budi baki zai sauke musu hawayen tsananin missing dinsu da yayi da kalar dadin dake dawainiya da zuciyar sa ayanzu daya tsinci kansa acikinsu,..alokacin kusa kowa na rike dashi,wasu hannu wasu kafada wasu sun tamke rigar sa,barinma shukra da har yanzu bata freeing dinsa da warm hug dinta ba..

Aikuwa yana janyewa suka hade ido da mahaifiyarsa dake tsaye ita kadai tana kkrin janye hannun sa ajikinsu sai yaji kamar gwiwonsa ake sassarewa Wani muguwar axaban kewarta dayayita dannewa tuni ya shiga rikita masa yanayi

A shagwabe ya Dan susuce fusknsa kalar shagwaba yanata kallon fuskarta dayayi missing tsawon shekaru yana murmushi ya ce mata "mama"..
Mama na dawo nigeria shikenan hanklinki ya kwanta?Hawayen ta data sauke ya sokalo masa nasa,da Dan shaukinta ta taho ta rungume sa tsammm ajikin ta tana shafa kansa cikin tsantsar bayyana tsananin Soyayyar datake masa a zuciyarta da kwakwalta,shima manne ta yay sosai har sanda suka so su ba mutanen wajen tausayi,cikin haka mufrad ya karaso kallo daya ya bibbisu da shi yaja karamar tsaki fuskan San Nan a mugun daure Babu ko alaman rahma bare sauki, Ganin mahaifiyar sa agefe tana goge kwalla ya sa ya Kara jan tsaki aransa yana shan mamakin su shi aganin sa baiga abun yamadidin kuka anan ba..

As usual ganin sa yasa aka soma raguwa kowa ya nufi cikin gidan da sauri badai ayadda yaso ba,hjy adada da hjy saddika ne suka shigo tare da imad din,ita kuma hjya jasmine suna baya tare da Anty meera da malak Suna shan dariyar masu oyoyo dake hjy jasmine da Anty meerah dama kawayene, tun a secondary school suka hadu suka San juna,to tunda ma sukazo suka aure majazen su Wanda suka kasance aminan juna sai aka dawo ana zumunci kamar Wani Yan uwan jini.
.


Fannin su ai'nau kuwa ba'acewa komi Dan tun dawowar su abuja Zarah take mugun bata mamaki,
,musamman ma wajen matsata datakeyi akan abubuwa,gaba daya tabi ta maida ta jakar gulma,tamkar wasu magajiyoyin gidan haka suka dawo,Banda aikin shishhigi da neman gindin zama awajen mutanen gidan Babu abunda sukeyi su biyun.

Haka zarah tasa ai'nau agaba saida taki Sam ta tare gidan mijinta dake can anguwar asokoro,suma zaman daram sukayi a mansion din ana damawa dasu Ako Wani harka,daga yau suyi Nan sai gobe suyi can hasalima sune agaba wajen hidiman shirye shiryen bikin dawowa sabon gida da akayi, da duk Wani hidiman murnan dawowar imad Nigeria da ake kanyi..

Halayen Zarah masu ban tsoro da mamaki wanda ko Ainaun bata San dasu ba su suka firfito mata a fili, sosai Zara ta Kure mata tunaninta,dan da alamun zarah tayi nisa bata Jin kira a fannin makirci da munafurci da kuma karya wanda ya riga yay ma rayuwarta dabaibayi ya zame mata tamkar rigar ado..

Tun dawowar su gidan zarah take famar fadi tashi wajen shishhigewa manyan matan gidan da salonta na makirtattun mata wanda sukayi course a munafurci yau itace aikin dafe dafe,yau itace kimtsa faloka har Yan goge goge saita tsaya akan masu aiki tana gyara musu,ga Wani dan uban parkaging din karyan ladabi da biyayya data Ara tana musu mai ban mamaki wanda ba lallai bane mai karamin kwakwalwa ya dago salonta cikin sauki,wanda ko gaisuwa zatayi saita langwasa murya ta zube kasa tana Jan aji tana sauke musu makirtaccen fadanci tana riritasu ,in abunma ya cicciyota takan zagene tayi abunda ainaun ma bata taba tunanin aikata musu a matsayinta na surkuwan gidan ba,tun zuwan Zarah gidan komi nasu ya sauya gidan ya zamo so busy and energetic gaba daya sanda ta nemi ta sauya musu tsarin rayuwarsu da biri biri da rawankai da rawan jiki,a
Komi in za'ayi itane Kan gaba yau aje Nan mall din gobe aje Nan chops din,nuna musu take ita gogaggiyace tasan harkan kashe kudi ta Kuma waye Dan harga Allah batason harkan raini,within few days ta shiga juya musu tunani Dan hatta hjy goggo saida ta soma fadawa acikin trap din makircin Zarah saidai daga baya datazo taga tafara xakewa dayawa sai ta dan ja jiki ta dena kulasu..

Hjy adada da hjy saddika kam tuni nasu ya dinke suka hade Kansu kamar dama can sunsan juna Dan kusan halayyar su ma Babu wani bambamci
Cikin Yan kwanakin Nan Babu abunda Zara batayi musu na kyautatawa da biyayya ba,Wani bin har gulman Aina'un suke suna camparing din halayyar ta da zarahn wacce bata da aiki sai zulman da zuciyoyin su musamman ma in ana zaune a dinning haka, aka sako hirar su imad,xarah bata tabayin sanya wajen kkrinta na dasa musu boyayyen manufarta na son kasancewa dashi datakeyi ba altho bata iya fallasa furucin na ta a fili cikin manakisa da makirci take buga musu kai da salon game dinta,har wani sabon salon kunya da respect take bawa hjy saddika fulani abun harna so ya basu mamaki aransu

Dake ma gidan yana da girma sosai sashen sama can Inda Aina'u ta tare itama take kwana.

Daga sun kebe su biyun zasu haura ma juna da zagi gau gau Suna fadace fadace sabida bakasafai ainaun take Jin dadin salon zakewar da Zara takeyi agidan ba,abun haushi yake bata,wani yarfa Kan da Zarah takeyi in d name of neman suna yana balain konata..

Itama zarar haka take zagewa ta dage ta duddura ma ainaun ashar tayi ta mata gorin cewa dabiunta na jan aji da rashin iya bida mutane shiyake kasheta a gidan mijinta,haka zasuyi ta hargagi ma juna da tsiya da bala'i sanda ta rinka cusa ma ainau damuwa aranta, ta kuma sata agaba wuta wuta akan shan maganin mata,within dis short time Aina'u har tashha kusan rabin magungunan mata da zarahn ta sissiyo mata,dake bata saba ba sai takejin Babu dadi ajikinta kullum sai anyi dagske .


Tun jiya da akace imad ya sauka a nigeria Zara ta haukace da kimtse kimtse,suka hau shiri,not just normal shiri,babban shagali suka bude a dakin ainau tamkar wanda zasu tarbi shugaban ksa koma ace mahaifinsu daya riga ya bar duniya,yestades make up da aka biya zunzurtun kudi har dubu sabain haka ya tafi a banza,bata daddara ba tun asuba ta sa aka kara Nemo mata make up artist Cynthia oge wanda ta shahara sosai a fannin iya kwalliya a maitama.
Kusan same amount ta Kara bata ta tsantsara mata make up bamai nauyi ba sabida ita salon nata makircin da brain take yinshi.

Wani bin zakaga kamar tanaso tana Kaiwa kasuwa ne, but still she is nothing like her sister Aina'u who is extremely strict nd Nonsensical bata son yarfa kanta at all cost.

Ko ayanzu ma abunda ya hanata bin zugar oyoyo kenan,cikin ranta Sam babu dadi bazataje araina ta,beside who is imad inba marar imanin guy dib dayake sauri dauke hanklin mijinta akanta ba,ita tun Tuni ana murnan dawowarsan nan Amma harga Allah aranta baqinciki takeji,she secretly hate him sabida kimanta shi da mufrad yakeyi arayuwarsa,many times arabta saitana ganin kamar mufrad yafi daraja bukatun imad akan nata ita datake Matarshi,
infact a duniya bayn aikin sa data tsana imad ne yabiyo baya,she just can't hide d fact,bata son kayan Reni kuma bata son harkan karanta, ko jiya jiya ma sai da ta shaqi maganan banzan da nazli ta yabawa Zarah acikin wasa datace mata"..Omo local gang awon busy body"..she was like..akan imad din ne har za'a ce musu busy body?nazli tana da Wani salon rainin hanklin da kokadan bata so,shiyasa ma atarayyarsu basu cika dinkewa ba.

Ga shukra data lura kamar tana bibiyar su tana kallon Duk abunda sukeyi,she is sure yaran nan sukanyi gulman su abayan idanunsu,by now tariga tasan halayyar shukra na mugun iya saka Ido da dora kahun zuka akan rayuwar wasu,tasan abunda zasuce akan Zarah na batanci Hala kunne ma bazaijuyu ba..

ficewa tayi daga dakin zaran ta wuce nata dakin direct, gaban mirror ta nufa tadau marykay oil control powdern ta wanda yake da haske dayake colour 1 take shafawa,nan ta Dan Kara gogawa sama sama akan fusktarta,ta dada gyara brow line,ta kikkimtsa Dan ta Kara fito da kyallin kwalliyar datayi ma mijinta Dan da shi kawai takeji azuciyarta take Kuma gani sabida Duk sauran Yan gidan ba damuwar ta bane..

Ita Harga Allah ma ta tsane su kawai dai yanayin rayuwace data zabar makanta wanda yakasance mata dole sai ta zauna dasu tabisu a hankli

Miqewa tsaye tayi agaban Mirrorn tana Dan juyi ciki dada gyara ma wata arniyar fitted gown dinta na atampa lace zama,dark purple colour with touch of gold saiya fidda farin kalar fatarta ya mata mugun kyau,juyowa tayi cikin sauri kamar zata fice tana bude kofar kuwa ta soma jin muryan zarah daga can kitchen Wani wahallalen tsaki ne ya kufce mata feeling d litle litle noise dake tashi a kasa,she despretely want to end all this games da Zarah ta bude agidan nan,ta kosa takoma gidan mijinta,inda tasan ita kadai ne dashi Koda ma zata dan huta da hayaniyar wayannan rubabbun mutanen...





*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


Part1:chapter 28


Daga kitchen zarah ne kace kace a tsaye agaban su uwani ta Dora hannunta a kugu cikin wani mayyar suturarta dayayi mata mugun kyau ya zauna akan dirin shape din jikinta ya mata cas cas,riga da siket ne fitted ta wani deep blue colour voile lace mai Dan karan tsada,infact komi data sanya ajikinta yau mai uban tsada ne,she was standing tall on an Italian cage pump heels dakema ba Wani tsayi take dashi ba takalmin ne ya temaka ya Kara mata tsaho,Bakinta yaci uwar sa da matte redish brown lippo..

Everything on her face is on fleek nd carefully calculated har Wani sauya kamanni yau tayi..

Masu aiki suyi Nan suyi can sai zagin su takeyi tana hantarar su
"Ke da Allah kiyi Abu da jikinki,ta juya ta kalle uwani ke kuma kiyi sauri ki dauko dump waiter ku sassaka abincin Nan afarayin kasa dasu..mschewww "waiya kuke wani Abune kamar dabbobi?I don't want you to waste anymore time,c'mon girls,wani maiyyar nishi ta sauke, cak ta dakata daga Furta Wani magana tana Wani irin kallon su kamar taga kashi,Wani kyamataccen numfashi ta ja sannan ta lumshe idanunta at same time ta budeshi tana wani sissine idanunta, tsaban rigima eye brows dinta har wani shaking sukeyi Suna gil gil Suna rawa rawa kamar zasu tsinke daga idon su fado kasa
Cikin wata rigimmmaiyar tune wanda ya fito da kasalliyar sautin muryanta tace,"oh my gosh..my honey is already here,ta Wani Lumshe idanunta tayi tana sauke kakkarfan Ajiyan zuciya like yo she is feeling it,a rigime ta dafe goshin ta,wani hade rai ta karayin tana jinkanta kamar wata hamshakiyar matar gida,tanajin zuciyarta a harzuke daya kasance su uwani basu kammala komi akan lokaci ba,bata ma lura da Shigowar ainau ba tana famar sauke mugun kallonta akan su uwanin wanda iya bare baren da jikinsu keyi kadai ya isa kasan Suna cikin Wani yanayin Jin takaicin ta,biri biri kawai sukeyi sukansu sun kasa tabuka komi duk tabi ta ruda su da tsawa da tsiwa summa rasa Wani oderta zasu soma kulawa

Wani uban tsawa ta daka musu ainau ta karaso ciki cikin sauri fuskarta a Dan dore,a hnkli cikin muryanta mai cike da aji tace pls Enough Zarah please let d girls be"..ta dada matsowa kusa daf da kunnenta tace haba Dan Allah sai kace kece matar gidan?nifa bansan kayan Reni Nikam Muje daki,wats wrong with you..Ta karashe mgn cikin sauri tare da watsa musu uwani kaskantaccen kallo she care less Inba basu Gama akan lokaci ba ita Ina ruwanta?..ba yabo babu fallasa tace "Bunch of useless things,tun daxu ace kuna abu daya?da Allah ni Kuyi sauri ku barnan ppl are already starving..,a hnkli uwani tace Ayi hqri hjya yanzu za'a sauko da sauran abincin,Bata kara kallon su bama bare ta kulasu,cikin sauri ta janye hannun Zarah suka haura can sama dayan dakin tan

"Let go off me'
Zarah ta fauce kafadunta data riko a hatsale da alamun ranta ya mugun baci, Adan zafafe tace wai Meye hakane Aina'u?inai musu magana kin Wani zo kin dakatar Dani mtsew Nidai Karki Kara min haka,ya zaki jawo har masu aikin gidan nan su renani?

Wani juyi Aina'u tayi Tare da sake yangataccen Rolling eyes ta juyo tana kallon ta..
"Zarah Raini ya wuce anjima kadan kijisu Suna gulman ki Suna zaginki? A hujajan Zarah ta juyo zatayi magana Aina'u tayi saurin daga mata hannu fuskarta a matukar daure tace"Hey hey Ki dakata min please,I hope ure not forgetting yestade nazli call u local with her full chest tana refring rawan jikinki da Omo busy body
Zarah waime sa hakane?mesa baki son rike mutuncin kanki ne?..how can I make u understand?

'Zarah dake Jin Wani zafi aranta cikin bacin rai a hnkli ta furta I don't know Kuma ki kyaleni,daga Nan ta dauke kanta tamayar gefe muryanta a matukar shaqe ta shiga tambyarta ciki ciki..."Wai mu yaushe zamuje ne..pls let's go down now,I'm eager to see him..dama abun da ya kawo kenan right? So let me do nd leave dis goddam place abeg,ta karashe da jan tsaki a zuciyar ain tace ai gara ki tafin Dan ji take kamar ta shaketa cikin dauke Kai itama tace Indai a shirye kike let's go..zarah batace mata uffan ba ta wuce fuuu gaban mirror Inda ta aje jakarta ta dauka ta bude ta dauko Wani mayyar sihirtaccen turarenta mai qamshi irin na turaren prince hamdan of Dubai wanda zee zee ne ta bata data karbo musu awajen malami,Dan kadan ta afa ta gogga a jikinta ta mayar ta ajiye sannan suka sauko Suna tafiyar su ta catwalk kowa da abunda yake sakawa aransa

Wani irin takun aji da kakalo girma suke wanda sautinsa yake a hankli Suna Wani irin kamewa cikin bayyana tsarin ajinsu, Nan ma saida ain ta rinka bin Zara da kallon gefe tsabar mamaki ganin yadda lokaci guda zarahn ta Wani dauke wuta ta kuma binne rawan jikinta ta fuske tana Jin kanta tamkar ba itace All desperate ayanzu ba...

Saidai Duk baza takun nan da sukeyi har suka sauko daga steps Babu wanda ya daga Ido ya kallesu,Banda hayaniya da tsaban karfin surutu da aka bude shafinsa a main palon Babu abunda kakeji Duk ahalin gidan sun mamaye shi.

Uhm uhmm Zarah tayi Wani yangataccen gyaran murya wnda ya fito da Wani Dan uban sautin rigima da Dan karfi tace
"Assalamu alaikum.

Wani Shiru sukayi gabadaya batare da kowanensu yayi yunkurin furta wani Abu ba duka suka juyo suka kare mu su kallo,yaken dole ne ya kufce a fuskar ain ta riko hannun zaran suka karaso ciki da sauri suka hau gaisuwa,wani irin numfashi da ajiyar zuciya Zarah ta dinga saukewa a hakli ganin yadda imad ya dan bata lokacin sa ya kalle su..aransa kallon baisan su ba yake Dan shi harya soma mantawa da kamannin Aina'u dake jinin su bai Wani hadu ba..

Zarah kuwa sai sunkuyar da Kai kasa take tana Wani sake mayyar Murmushi kamar wata amaryan Doki daga ta Dan dago ta kalle fuskar imad shikenan sai ta Lula duniyar gajimare,
Aranta ta dauka Duk haduwarta da ladabin Kule a buhunta ne ya tafi dashi har ya dan kallesu.

Su hjya kuwa tambayar su suke abunda ya tsayar dasu Aina'u take musu bayanin wai sun tsaya kulawa da abinci ne shiyasa basu sauko da wuri ba,a lokacin Aina'un ne kawai take magana dan kwata kwata Zarah ta susuce ta rasa nitsuwarta batama San mezata ce ba sai Wani kirsa take cikin sanyin makirci Tamkar wata budurwan kauye gata da zakewa ahaka sanda tayi jikin kowa ya shiga bashi cewa Duk wa imad take wannan uban murmushin da sadda saddan Kai din.

Aina'u batacewa mufrad komi ba ta dauke kanta akanshi shima haka yy kamar bai ganta ba dakema hanklin sa nakan wayarsa ne tuntuni yanata kallon Wani video da aka turomai daga can America da wireless earpiece a kunnen sa

Zarah ta dube imad direct tuno da idanunta akwai kwallin sihiri data shafa saita hau murmushi ta daddage ta sinne murya ta kakalo mai zaki da dadin
Tace mai ya hanya?

A hnkli imad ya juyo Jin yadda malak ta dan tsakureshi a boye,Hakan yasa yaki bada hanklin sa akan Zarah suna hade ido da malak ta sauke kanta kasa tana turo mai bakinta a shagwabe
Daga Nan kuma Shikenan ta dauke hanklin sa daga kan su Zarah gida Kuma ya dauka da tsokanar su"..imad na dariya yake cema mahaifiyar sa ai ya samu matar aure anata musu dariya,ahakn saida Zarah taji Wani balain kishi acikin zuciyarta,Duk dama tasan wasa akeyi amma atake atake taji ta tsane malak har makoshi..

Wanda Ko acikin wasan ma Hjy goggo ce kawai take bayansa tace sun dace da malak,tace ai tunda malak takai 15years aita isa aure,hjy adada da hjy jasmine da Anty meera sunata musun cewa batakai ba,hjya saddika kam batacewa komi sai yawan Murmushi Dan ganin fuskar danta ma kawai ya isheta Jin Duk Wani nishadi

Mufrad ne ya tashi ya haura sama da alamn kira zai amsa a hnkli ainau tabi bayansa da kallo tanajin tsananin kewarsa aranta,ji take kamar tayi xcusing dinsu tabi bayansa Amma kuma Ina she can't risk leaving Zara anan wajen bata San Wani irin abun wawanci da zubda mutunci da zata aikata mata ba.

Mufrad yana bacewa nazli ta yunkuro cikin saka baki a maganan tace "uncle mad kwanan nan fa zakayi aure har yaushe babe din Nan ta girma..kawai kace bakaso muyi asoebi...ta karashe tana langwabar mai da wuya..

Shukra ta shiga washe baki sabida aranta tana mugun son tayi kawance da malak but she can't show it yet sabida Ji take kamar tafi karfin sauke kanta ma wani,a tunaninta malak ce yakamata ta soma mata magana and for the fact dat malak is so gentle,charming educated and classy,yasa take tunanin nasu tafiyar zaizo daya,saidai da kamar wuya dataga malak din bamai son surutu kamar ta bace..ita Kuma bazata taba yadda a raina mata kurwa ba..she love to hate and suspect any one..

Imad ya Dan sake Murmushi was nazli yace.."I wil wait for malak"...hjya jas tace sai mubari ka cuce yarinya ai lokacin ka tsufe Anty meera tana dariya tace..gwarama kanemi wacce ta dace da Kai dai..
...zai budi baki yay magana Aina'u tayi saurin dakatar dashi tana yaken da baije har kasan wuyarta ba tace Kamar irin sa'ar nazli haka,ta dafo kafadun zaran cikin Kara drawing attention dinsu kanta,tace Zarah I think u're age mates da nazli ko?..Dan dariya akai,nazli ta Kau da kanta slowly cikin jan wata arniyar tsaki,Dan aranta ta Gama raina ajin zarahn ita Sam bata fiye son mutumin da baida class ba,tanajin hjy adada da kininbinta tana ta bayanin cewa ai yafi dacewa da irinsu zarahn
..komi dai acikin wasa akayi shi,Inda Zara ta shiga Jin dadi aranta musammn ma da hjy saddika tazo ta tsoma baki da aka kawo hirar dacewar su akan imad tana ce masa son irinsu nazli sune dai dai Kai ba yar yarinya ba..she knew they were just saying it Amma sosai Hakan yay tasiri aranta tasomajin kamar ma bata shi akayi mai gaba daya..

Hjy jasmine tace shukra jeki kirawo yayanki,I want everyone on d table now,Bari na duba su uwani...Butt Zarah ta miqe tsaye cikin Wani makirtacen salo tana Murmushi tace no maa,kiyi zamanki kawai bari inje in dubosu ..hjy jasmine dake dan Murmushi tace thank you yar albarka..da Wani irin salon tafiyar rigima ta wuce ta haura sama cikin sauri,dai dai lokacin idon nazli da shukra suka ci Karo Wani dariyar raini suka tuntsire dashi
"Wats wrong with u guys?..Aina'u ta hade ranta sabida ta shaqi da waye sukeyi,.bakinsu a hade Sukace nothing...shukra ta miqe da rawan jiki ta haura sama dantaje tayi gulma sannan taga yadda za'a kaya da Zarah da masu aiki a can kitchen..

Wayar hjy goggo ne yay kara aka miko mata ta Kara a kunnen ta suka hau gaisawa da Hajiya mama"..imad ya matsa sai anbashi wayar shima Dan sosai hanklin sa ya koma kano saidai bazaka fahimce Hakan ayanayin sa ba..haka kuwa sukaki su barshi ya amsa wayar kowa na cemasa Babu Inda zaije har sai yaa sheik ya dawo..

daga kitchen kuwa haka shukra tayi cirko cirko daga bakin kofar tana ta kallon su Zarah altho har an riga an kammala komi,Abu dayane kawai ya kwafsa ma Zarah ganin bazata iya musu ihu da ikon data sabayi agaban shukra,itadai har Yau neman gindin zama take bacin bata san shukra ta Gama fahimtar ta tsaf ba.

Tare da masu aiki zarah ta sauko aka hau karasa jera abinci Banda saka Ido irina shukra gaba daya hanklin Zarah baiyya jikinta
Ganin yadda imad da malak suketa hira.

Cikin sauri tasa aka kammala shirya table ta dawo tace musu angama anata yabonta Aina'u kam ko ajikinta duka suka wuce Kan dinning aka zazzauna,ana gama zama saiga mufrad yana saukowa cikin tafiyar sa mai cike da nitsuwa da daukar hankli harya sauya suturar jikin sa zuwa wata
Hadaddiyar Italian white t-shirt ta kamfanin renato balestra hade da lallusan wandonsa Wanda yanayinsa yake kamar sport wear shima fari dogo,kafarsa yay kyau matuka acikin wata convertible loafer sai takunsa yake a kasaitance tamkar halin da ake ciki agidan na zumudi da murna Bai darashi ba

Harya karaso ya zauna kallon sa akeyi,wasu a sace wasu a fili as usual kusa da IMAD ya zauna mahaifyar sa hjiya jasmine tana daga dayan gefen sa kafin Nan ainau da nazli,ata dayan bangaren kuwa zarace daidai setin kujeran dayake kallon na imad tare da sauran mutanen gidan kowa da kalar expression dinsa awajen,hjy jasmine ta miqe tsaye zatayi serving still Zara ta miqe ciki kadadi ta karba Wanda Hakan ya tursasa Ainau mikewa danta tayata har wani Allah Allah take ita tasawa imad din bacin hanklin sa baima wajen tunani dayawa su riga sun cikke masa kwakwalwa

Please Login or Register in order to submit comment