Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musu girke girke,itace tayi wancan tayi wannan girki kusan kala hudu tayi lafiyayyu,tuwo,shinkafa,pper soups da sauran su tamkar basu taba zuwa gidan ba..rufaida na zaune a falo ita kadai Ko motsawa daga inda suka barta batayi ba.
Jim kadan sai gasu nan sun sauko anty fareesa da malak suka wuce da kulolin abincin dinning hajya ce agaba cikin sauri da murna zatayi wajen rufaida data hngi azaune idanunta har suna kkrin fidda ruwan hawaye

A tsaye rufaida ta mike cikin fixga ta mugun hade ranta ta kawar da kanta gefe tanamai kallon kofar fita wajje kamar wata mai aljanu,wani turus hjy ta tsaya ta a kallon yanayinta" jiki a mugun sanyaye ta matso kusa ahnkli tace..Rufai?Rufai kece wannan?
Alhamdullahi,Alhamdullah...tuni kukan datake dannewa ya fito sarari,da jikin tsufar ta fado jikin yar jikarta ta kankame ta tana surutai,saidai tamkar tanayi wa gunki kuka haka rufaida ta tsime taki kulata,Kuma takiyin koda motsi bare ajega hawaye,saima kiciyar kwace kanta data shigayi cikin haushi da fada fada.
Saketa hjy mama tay da fuskar tausayi tayi narai narai da ido tana lura da yanayinta
"Rufaida mai nayi maki kike jin haushi na ko bakiji ddin ganina bane?Ta roko hannunta cikin hatsalar da bata san daga ina ya zo mata ba ta wafce hannunta ta dau jakarta muryanta na rawa sosai tace
"ni tafiya gida zanyi...kamar malak zatay magana anty ta kwabe ta da ido akan ta kyalesu
Muryan antyn ne ya dan dakatar da rufaida tanacewa malak akan ta debi abinci suje dayan falon tare da su jawad su fara ci

Batare da tayi musu ba ta debo abincin ta janye yaran kaf suka bar wajen aka kyalesu su uku,
Wani shiru ne ya gifta hjy mama ta juyo gwanin ban tausayi ta kalli anty faresa.."Fareesatu kode ba rufaida bace...yanxu haka yarinyar nan ta dawo wata masifaffiya dubeta fa kamar zata shararamin duka?
Cikin share shirmen ta anty faresa tace "rufaida meya faru ne?..ina zakije kuma!A hnkli ta soma magana muryanta kasa kasa cikin..in..inna tace Anty daman daman ni gida kawai zan tafi dan banga amfanin zuwa na nan gidan Ba,Caraf hjy mama ta cafke maganar"Kinci gidanku rufai..Nan ba gida bane ?Ta juyo ranta a bace tana murguda baki tace "oho..ni bansani ba..ni kawai zan tafi

To ki tafi mana kifi ma ruwa gudu

,..tasan a wasa ta furta mata hakan amma sosai maganan yay mata daci a cikin zuciya."

"Zan tafi,kuma bakya kara gani na a inda kike...Ai Dama can kece kika kore mu,dani da su baba..ni me ma zanyi a gidan ki..Allah ya kiyaye min..hawaye ta fara saukarwa tun daga cikin zuciyarta,wni kuka mai ciwo da radadi shiya kufce mata ya fito sarari atake ta karya musu gabobin jiki sukayi tsamo tsamo suna sauraronta cikin ynyin rasa abun yi..tunkan waninsu ya motsa rufaida ta fixge jikinta azafafe ta kama hanya zatayi waje da gudu hjy mama ta riko hannunta taja ta da karfi ta jawo ta cikin falon ta dangwalar da ita akan gujera tayi zaman dole,kuka tahau yi da karfi snn ta hade kanta da gwiwa dan sam bazata iya kallon kwayar idanun su a wannan lokacin ba.

Har gabanta hjy mama ta rusuna tana matse kwalla
Cikin raki da masifar karfin hali as usual ta dinka zuba ma rufaida bayanan abubuwan da suke faruwa,da kalar nadamar da tayi akan korar su datayi,saidai kamar ba shiganta maganganun sukeyi ba,dan wani irin taurin kai take nuna mata a yanayinta tana jan shessheka tana dada daure fuskarta.

Da kika koramu babu abinda ya xanca.. baba ya tsane ni,baya barin mama tazo inda nake,nasha wahala sosai da tsangamar mutane har gida ake zuwa a zazzageni,sau daya baki taba nema na ba,sai yaune da nazo gidanki zakina min wani bayani? Nide bana bukatar wann karyan,kuma nasan matsayi a wajenki,..kamar yar yarinya hjy mama ta kara fashewa da kuka rufaida ki yafe ni,rufaida kuwa sai tamfatsan masifa takeyi..bana cire tsammanin kece ma kika hana kawu zaidu zuwa dubani sabida ki nuna min bambamci,ai da sauran jikokinki ne da bazakyi musu haka ba..to dakikyi dana sanin mesa baki nemi baban kin lallabeshi ya yafe ni ba?ni me namiki,shine zaki kara harzuka shi kika saka a ka dauko ni?.

Hannu aka hjy mama ta dora tana jin balain zafin maganan da rufaida take furtawa, tsabar taga fitina yau tsirartar da ragwabben muryanta gwanin ban dariya tana hawaye sosai tace wohoho na shigga uku ni hasiya uwata ta mutu uwata ta dawo,dama can ninace maki bazan nemi bukar bane?wai mesa baki da haquri ne,shegiya da shegen tsaurin ido..Faressatu kina kallo yarinya ta sakoni agaba tana zagina ta wani cije tana min ihu kamar xata buge ni baza kiyi wani abu akai ba?sama anty ta daga hannu alaman babu ruwanta acikin fadan sun abun dariya abun kuka

tun dataga bamai bin bayanta haka ta rinka zuba tana amsar laifinta tana kuma baiwa rufaida haqri lallabarta ta dingayi cikin lallashi da wayo tana mata alkwarin zata shiryo kansu yaa malam harda yin mata alkwarin zataje har gida shima ta lallaba shi.

Aikomai ya wuce tunda kin ware dubeki waras masha Allahu tubarkallhu rufai kamar bake ba?Allahu akbar Allah shi ma fareesatu albarka..Allah yasa ku gama da iyayenku lpya .

Tun rufaida bata ra'ayin saukowa harta sauko tayi haquri,dayake da dan qarfi hjyy mama take nata maganan tun tuni malak ta dan soma fahimtar asalin kan matsalar tasu.

Batace komi ba sanda suka hadu duka akaci abinci akayi hira sosai ana ta barkwanci ana dariya,hjy mama kamar zata fige dan murna daga yanayin muryanta zaka fahimci tana cikin matukar farincikin kasancewa tare da jikarta rufaida.
Yau ko iyakar Kawancen rufaida da malak data gani ya isa ya jefa mata jin dadi aranta sosai

Dan haka godiya ta musamman ta shirya aranta zata yi ma fareesatu da mijinta da suka bata wannan kyakkwan shawarar..
Sai can da yamma bayan kowa ya huta ana daf zasu koma gida ta jawo anty suka haura sama dansu tattauna dan sosai abunda rufaidan tayi mata dazu ya dame zcyarta

Malak da rufaida suna zaune a falo tare da yara an kunna musu mbc3 sun kafa kai sunata kallo...
Tashi malak tayi ta kawo musu tea suka koma gefe suna hirar komawar ta abuja..sabuwar kankanin lokci amma harji suke kamar bazasu iya rabuwa da junansu ba,bayn sun gama hirar irin rayuwar da zasuyi tare ta yan gayu can dukkan su sukayi shiru harna tsawon lkci,a hnkli malak cikin sauke ajiyan zuciya ta soma magana muryanta kasa kasa cikin yanayin fargaba...tace hey babe..can i ask u sumting?take kirjin rufaida ya tsaya cak,amma ta daure tayi nodding head kamar ba komi aranta..ajiyar zuciya malak ta sauke tayi hummm sann tace

"Am sorry to ask,daxu naga kunata rikici da hjy mama but what really happen to you?whats going on pls..and why dont you wanna talk about him?(imad)..?

Pls Karkice inayi miki shishhigi, im just confused abt it, naga ranar dan na kira sunan sa kawai ki kyi kuka kuma sai baki kara Kula ni ba,dazun kuma danayi magana da baba na,u acted weird,shima haka.
bankira masa sunanki ba but is like he already knws you..kuma uncl mad really talks to me about you alot, amma ke naga kamr ma baki son kiyi maganan sa Dani, why?

Gyara zama rufaida
Tayi a karkace kirjinta na balain bugawa ta ciki tay gyaran muryan ehm em..tace."I ...i am..shiru tayi jin ta kasa iyayin wani maganan ma
Runtse idonta kawaii tayi kadan sanda ta ja lokci tana jan numfashi tana dan fetsarwa waje kafun ta dawo daidai.

"U said what happen?..

a sanyaye malak ta riko hannayenta suna kallon idanun juna tace yess ..whats going on?meya faru.

Wani humm rufaida ta sauke ajiyar zuciya ahnkli ta zame hannunta daga nata ta sunkuyar da kanta can kasa cikin jin tsananin bugun zciya
..muryanta na rawa rawa tace what im about to tell u is my secret,nd by Allah i leave it with u..
Gyada mata kai malak tayi a nitse tana mai sauraronta

Gyara zamanta tayi cikin yanayin sakewar jiki sann tace kinga nayi taurin kaine wa mahaifina,i want school, not marriage
And then,I was forcedly married to the wrong person.
Sai ta danyi shiru,
A Take jikinta ya karayin sanyi..a dan raunane ta cigaba da maganan
Tana fitar dashi a bakinta kamar ana kwaco kalaman a dole ta dubi malak tace"my ex.husband is...i dont knw,but He is a very...ver..y dangerous man, he almost killed me in cold blood amma shine ya mutun daga karshe..
Toh Anan ne na hadu da shi barista,(imad)da kuma mahaifinki..barister
I..ma..d,imad was my lawyer. and ur dad a doc,he treats me while i was going thru serious mental instability.
Da mamaki sosai Malak tace so you knw my dad?gyada mata kai rufaida tayi tace yes..,so"What kind of mental instability did u have?U mean ur ex husband shiya jefaki a halin da kika shiga ciki kenan?..Well uncle mad has told me abt sumting dat u were sick nd very depressed

Ajiyr xcya Rufaida ta sauke Bata wani so taja maganan ba A hnkli tace It's true i was depress,saidai tawa Depression din is more than" oh I'm sad , oh I was bullied , and other random thoughts.

Da gefe mayafinta ta share wani maqudan hawaye
Tace malak'Have u ever felt numb like totally numb Where you are alive but dead? You can't even feel any pain.You try so hard... to inflict yourself with pain so you could feel something but cant.

"Imagine having crazy flashbacks of deadly events..
Sumone eating flesh of human beigns tourting u, imagine living with a survival guilt,muryanta na rawa sosai cikin wata karamar kuka tace "malak, That's just one quarter of what my depression looks like.

Kukan data sake sakamakon tuno wasu abu daga cikin halin da tashiga cikin alokcn mai matukar tsuma shiya gama rikirkita yanayin malak yasata tayi sanyi, ta mike tsaye batare da ta sani ba, jikinta na tsananin rawa taji kamar ta soma fahimtar zafin abun a zcyarta,itama kukan ta saka ahnkki tana zubda ruwan hawaye sosai.

Mikewa tsaye rufaida tayi tana ta kukan data kasa dannewa duk dama burinta kenan ta iya controlling dinshi, da kyar muryanta ke fitowa fili a hnkli cikin sanyin murya "tace,did he actually tell u my story?pls what did you knw about me malak
..A dan rikice malak ta shiga kkrin controlling dinta danta mata bayanin cewa bata san komi har can can ba, sai taga ta kauce da jikinta tayi baya can tana jan zuciya sosai..a raunane ta runtse ido tana jan zazzafr ajiyan zuciya.."Dats my secrets, he shudnt have..ni na tafi,Allah yakaiki gida lpya kawata..sai wata rana..

Tana kammala fadin haka ta wuce sama Da gudu ta bar malak awajen tana kuka sosai

ji tay kamar kowa ya tsane ta a duniya.ta rasa Meyasa, toh meyasa zai gaya ma wata labarinta?
How many more will hear it,gashi tazo ta bude zucyrta ma yarinyar nan har sun fara kawancen su mai dadi,saiyau take fahimtar kamar da alaman cewa yarinyar ta san dikan labarinta ko dayawa daga ciki tunda dai tasan she was depressed and once married..

Dukan su basu ji dadin yadda abun ya kare tsakanin su yau ba,zucyoin su a take ta dau nauyi da radadi,amma basu kwatanta nuna alamar hakan agaban su anty ba normal sukayi bankwana da junan su ana daf gabanin mgrib su rufaida suka bar gidan

Kowacce acikin su bata da wani cikken nitsuwa zcyrsu gaba daya tana dame,haka malak tayi ziriya cikin zullumi da fargaban rasa kawancenta da rufaida,rufaida ma hakan ne,duk a tunanin ta imad ya kan bawa mutane labarinta ne shiyasa taji ta damu sosai, Bayan kwana biyu
Tunanin imad da malak su suka sakota agaba har suna barazanar hanata samun nitsuwar runtsawa.

Iya bakin kkri malak tayi wajen kirar anty koda za'a hadasu ta waya da rufaida suyi maganan, amma koda sunyi wayar basu gane ma junan su sosai.

A fannin rufaida gani take kamar rabuwa da tsabgar malak shizai fiye mata kwancyar hnkli ayanzu dun muddin suna tare a wann yanayin to tabbas bazata sake sosai da itaba.

Ita kuwa malak aranta sam ba haka bane,lokaci kawai ta bawa kawartan dan ta samu nitsuwa, aganinta sabanin fahimta ne kawai ya gifta tsakanin su kuma zai warware wata rana..

Kwananta uku a gidan hjy mama ta bar kano ta koma abuja,a fannin rufaida kuwa kusan abu mai sauki ne danne damuwarta dan haka tay kkrinh share tashar malak ta cigaba da kulawa da kanta...babban burinta ynzu baifi taga ta koma makaranta ba.


Book 2,Page 3

*Shade of rufaida part 2 is not free lovely sisters pls dont read it if u dint pay,to subcribe, ku biya Naira dari uku "300" ta wannan acct 0152983148 mohd sule surayya Gtb or MTN pin ta wannan layin 08060712446 saiku turo shedar biya a same phone number.*

I Dedicated this part daga farkonsa har karshen sa ma lovely sisters dina
Maman mubeena da maman bappa Allah ya Albarkace rayuwarku my sisters Ameen.





5️⃣4️⃣


*Shorfda is not free lovely sisters pls dont read it if u dint pay,to subcribe, ku biya Naira dari uku "300" ta wannan acct 0152983148 mohd sule surayya Gtb or MTN pin ta wannan layin 08060712446 saiku turo shedar biya a same phone number.*


Abuja.
5.30am

Cikin wata nitsuwa daya samu ta sanadin sakarma kanshi ruwan sanyi dayay yake tahowa ahnkli cikin dakinta hannun sa dauke da wata lallausar Sallaya bai tsaya kwankwasa kofar dakinba kai tsaye ya bude ya shigo,da kallo daya yabi kan gadon kusan a yadda ya barta haka ya dawo ya sameta kwance cikin bargo ta lullube jikinta daga kafa har kai tana kan tikan bacci harda minshari.

kansa ya girgiza sannan ya dauke hanklinsa daga wajen,sai daya fara shimfida abin sallar sannan ya karaso gareta yana mai dofanuwa abakin gadon daf da ita.

Ajiyar xucya ya sauke,Bacin wani kasalallen kallon daya karema jikinta Gefen fiskarta ya shafa da tafin hannun sa mai tsananin laushi a hnkli,bai kula da kin motsin datayi dagangan ba yace "babe kinyi sallah kuwa?Wani mika tayi,ta sake juyi tana shirin juyamai baya,da sauri ya tarota ta jingine ta fado akan faffadan kirjnshi"Get up my friend..ki tashi muyi sallah,ya fada yana mika mata hannu, a hankli ta bude idanunta ta wani kalleshi sai kuma ta fuske, amaimakon ta bashi hannun kamar yadda ya bukata sai tay kkrin miqewa tsaye a gajiye,bai damu ba ya tallafo ta da jikinshin ya tsadaita sosai suka tsaya sannan ya mata nuni da abun sallah,kamar zata fashe mai da kuka haka tadinga ji aranta dan ta tsani abunda zaina katse mata bacci, da kyar ta shiga bathrum tayi alwala ta fito aksale,can jikin kofa taja ta tsaya lura da kamar na jam'i yake son suyi,tsaye tayi tana kallonsa,.har ya bude wardrob ya dauko wata farar jallabiyar sa fara kal tasha guga ya saka ajikinshi da yar karamar hula wacce ke tsayawa a tsakiyar kai ya feshe jikinshi da turaren ck mai dan uban qamshi sann ya shiga gaba tana biye dashi ya tayar musu da sallah.
,raka'a biyu sukayi rak amma yadda kasan akan kaya haka take yamutse yamutsen fuska da motsi da jiki,shikan ya riga ya saba a kowani sallan fajr dinsa baya gajerta surorin da zai karanto,yau da baije masjid yay ba sai taji wani daban,muryan sa mai dadi yana ratsata amma bashi ya hanata jin ta matsu a idda sallan ba,gaba daya a wuya take,suna kai raka'a na karshe bata jira sallama bama ta daga ido ta kalle agogo tana kiyasce lokaci,a raka'a biyu ne za'ayi almost 8mint?,ana sallama ta tabe baki,tab bazata ma iya tuna when last tayi minti 2 a sallar safiya ba,besides suratul qulhuwa da suratul qulhuwa kawai tasan take yawan karantawa a sallolin ta shidai muffy dan wahala ne,kkrin tashi tsaye takeyi sai suka hade ido dashi da sauri ta dakata tana kaucar da nata idon cikin sauri saboda yadda ya kafeta da kwayar idanun sa dake mata kaifi da nauyi
,kai ya girgiza mata alaman bai aminta ta bar wajen ba tukun,haka ta koma badon taso ba ta gyara tayi zaman dole agaban shi ya bude qur'ani ya hau karantawa da muryansa mai tsananin dadi tana jinsa tayi jim cikin ynyin yin shiru,gaba daya kunnenta da jikinta nauyi ma yakeyi mata,she cant just tolerate this she knows,lura da yanayintan yasa shi sakin wata tokarreiyar murmushi Cikin wata saukakkiyar murya mai taushi
Ya Bata umarnin cewa tahau gado ta kwanta ta huta basar da shi tayi kamar batajishi ba,miqewa tsaye yay batare daya kulata ba yahau tattare sallayarshi
Abazata taji ya saka karfi ya wawuso ta jikinshi ya dagata cak yana mai rabata da kasa,ita kuwa gaba daya idanunta naga kan murdaden damtsen hannunsa ne da suka wani tattaso, zaratan jijiyoyinsa take kalla masu daukar hnkli sun wani bashi wata sabuwar salo na azaban kwarjini sunyi darara gwanin ban shaawa,a hnkli ya taka ya isa da ita har bakin gadon sannan ya shinfideta gently a saman gadon ya kwantar da ita yana dan nishi nishi cikin yanayin barkwanci yace."..hey Ashe dan banzan nauyi dake?
murmushi kawai tayi, Idanunta ta juya cikin yin rau rau dasu tana kkrin sake mai miskilalan jiji dakantan danta san batada sauran abun fada mashi ayanzu,lumshe idanunta kawai ta dingayi a hankli harta rufesu sannan ya miqe ya fice daga dakin.

Yau da kansa ya dauki mota ya fita neman masu abunda zasu karya dashi, kwana biyu he has been trying to convince her sosai waiko za ta sauko ta rika mashi breakfst sunayi tare amma fir haka taki ta kuma shahsantar da zancen gaba daya,ita dai saidai suci na gida general,inya damu lallai sai sunci tare kuma saidai shi ya fita sassafe ya siyo.

Haka yauma ya fita ya dinga tuki a titin anguwarsun a kasalance ya rage glass din window sanyin iskar safiya wadda ke gauraye dana Ac na ratsa shi,sanda ya gama shawagin sa sannan yay parking cikin wata mayyar hotel ya siya musu lafiyayyen abinci yabi yay oder harda na dare dan yasan daga ya taba ainau kadan duk saita wani langabwe tace ta gaji,har ya koma gidan bata farka a bacci ba,karshe haka ya zauna yaci nasa abincin ya zauna yana kallonta tare da ipad a hannun shi yana duba ingantattun labarai dake yawo a base dinsu don ya samu cikkaken information akan ayyukan dake matsowa gaban sa


10:30am
General Shagari luxury complex Abuja.

Babban gini ce irinta masu fada aji yan siyasa da masu kudin gaske.

Wani kyafaffen Gidan sama ce wanda akayi ginin ta da strongest steel walls,da kuma benen glass mai hawa hawa har hawa goma sha takwas, ko wani kofar shige da fice acike take da security barinma yau daya kasance ana biki budirin taron bude wajen.

Wayayyu, hadaddu gawuttaccu da kuma isasshun mata masu aji da arziki ne kaca kaca a awajen ana famar nuna bajinta da isa, kowacce mace da kalar abunda take tinkaho dashi.

Ai'nau ce zaune a office dinta tana kallon event din life daga tv tana kare musu kallo filla filla daga kasar takalmi har tsakar ka tana sipping sassanyar orange juice dinta dake aje gefe,tuni taji ta kasa zanne ta kasa tsaye,
hanklinta sosai ya tashi ganin kaf matan wajen basufi sa'anninta ba
Barin ma dataga kawayenta guda biyu aciki wanda tun bayan bikin auren ta ta watsar da kashin su bata kara neman inda suke ba..wato maryam da hasina..
Da alama suma gaggan mata ne awajen dantaga ana damawa dasu kaca kaca,shigowar su wajen ne yaso ya mugun zautar da ita,a kaf matan wajen haka su biyun suka fasa taro cikin wata shegiyar motar lamboghini kirar URUS irin sabuwar motar yayi da kamfanin lambo tayi saidai shi ba sport car bace JEEP ce dunkulalliya.

Last she knws a wajen mijinta kawai ta taba ganin irin motar a nigeria shima da alamar god fathern shi ne ya aiko masa dashi kyauta tun daga kasar waje dan tasan muffy bai cika siye siyen motocin yayi ba

Wani irin zafi da tsananin kishi ta rinkaji aranta data gan irin wann motar a hannun kawayenta data gama rainama ajin su wayau,babu abunda yafi daga mata hankli face auren dan minister dataji ance maryam tayi,ita kuwa hasina itace ma ceon shagari luxury complex mai gaba daya,tasan yanzu kam sunyi kudi suna cikin daula,su biyunsu suka balain haske taron suna wani jiji dakai wa mutane suna balain baxa takun salon rigima da kyaffiyar motar su wanda bakowa yake da ita ba,..

Ainau sam bata da ra'ayin yin wani business, but for sure yau sai dataji tsuminta ya balain tashi,ita dai kawai taganta cikin wayannan matayen ana gwagwarmayan competiton da ita.
Ai itama ta isa kuma ajinta sosai yakai nan wajen dan haka dolene ta dawo dasu hasina cikin clique dinta su cigaba da kawance

Atake ta saka aka tura musu wani hadadden congratulation cards da complimentary flowers mai aji da sanda akayi kusan kure garin abuja ana nema,bata saka sunan ta ba tace ace daga offishinta ne...tasan duk yadda akayi zasu neme sanin wanda ya aiko musu.

Kwana biyu kuwa saiga maryam ta turo mata da katin gayyata ta xuwa wajen shahararriyar opening dinner party da za'ayi na wajen,ainau ta rasa me yake mata dadi
Ba abun ta tambaye mufrad aron mota ba ajinta ya wuce nayin karya ma kawaye,kuma tasan is imporsible ta tunkareshi tace ya siya mata irinshi kafin ranar dinner.

Sosai ta daga hanklin ta,abun da zai boosting egonta sam batayin wasa dashi,bata zanne bata tsaye a gidan kullum acikin waya take da brand supliers tana tsare tsaren yadda itama zata fasa taro ta kuma kure adakar ta aranar dinner dan kar arainata.

Tun mufrad baisan metake ciki ba harya zo ya fahimta.

Kwana uku da faruwan haka da wani yamma ci yana zaune a falo shikadai yanadai zaune ne kawai amma sam bayajin dadin zaman wanda shikansa bazaice ga dalili ba lokaci zuwa lokaci yakan dubi kofar shiga yana tsammanin ganin shigowar ainau,tun ranar data soma yin dare awaje saiyaji gaba daya hanklin sa bai kwanta ba,bai tsawwala bane saboda baison ya fiya shiga rayuwarta kamar da can harya zamana akwai takura aciki

Karar wayarsa ce ta katse shi ya dauka yana sauke ajiyan zuciya"..hajya mama ce,ya san kiciniya kawai ta kira ta sauke masa mikewa tsaye yy sannan ya fara gaisheta ta dakatar dashi"ni ba gaisawa na kiraka muyi ba
Nace ina son ganinka amma kayi kunnen uwar shegu dani ko..wai shin ni saarka ne ko yaya aka soma..?dan
murmushi yay sannan ya datsi numfashinta 'toh yanzu kuma tsalle tsallen kauna muka soma?in zan taho saidai nazo miki da matata,in mukazo kuma kece ta farko da zaki saka mana ido ki hana ruwa gudu...doguwar salatin data ja ya sashi yin dariya irin wadda ya dade baiyi irintasa ba,ya naji kinyi shiru?baki a bude tace iyyeee kaga marar kunya..toh gafara banga sabada ba tunda dai ba acikke ma zaidu gida da jikoki ba,da cewa nayi kazo na ajiye ma yar shila daidai dakai kar abinne ni a rami in mutu banga jikokin zaidu masu muni masu kama da kai ba"kana ji na ko? Toh wallh ina nan ina jiranka da magana..a hnkli yace dama kinyi shiru ne?,ai kuwa kamar ya kunnata ta hau surutai tana barbade akan maganan dawowar kannen sa da karatun su nigeria dan har yau tana kan bakanta na dawowarsu nigeria bata fasa ba,cewa kawai yay yaji....snn ya katse wayar yana tuna ta shikadansa yy yar dariya sai yaji ransa kuma tayi fess...Kamar ance daga kai ya hangeta bakin kofa mayafinta a hannu har wani layi take tsabar gajiya,gyaran murya yay da dan qarfi ta juyo a dan firgit,suna hade ido ta dauke kanta yayn da ya sassauto da murmushin dake fuskansa"..sai yanzu kika dawo!
Saita karaso tace yes,ya ce hmm to zauna nan,tana zama ya dubeta yace har kinci abinci?da hannu ta bashi amsar eh sannan tace,what about u?a hnlki ya kafeta da shanyayyun idanunshi yana maganan cikin wata narkkiyar salo mai daukar hankli
"Idan nace banci ba zaki dafa min ne yanzu? Da sauri ta daga kai ta dubeshi sannan ta saki harara mai zafi "no"..im tired,ni wallh wanka ma kawai nake son amin ..take narke ta wani langwame shi wuyarta sosai baby?..ya sake guntun smirk bai kara cewa komi ba.


Washe gari da sassafe ta shirya tsaf tana cin abincinta a hankli tana taunawa a kasaitance yayin da ya lafe jikin kujera kamar mai kallon wani abu saidai ita yake satar kallo time to time Yana wani tunani,..

Mikewa tsaye yay ya wuce ya bar dakin tabi bayanshi da kallo,jim kadan sai gashinan ya dawo dakin rike da wani box a hannun sa.

Kirjinta ta ne ya buga cos duk inda surprise yake sai kajishi daban dama can Da akwai motar data

Please Login or Register in order to submit comment