Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wa iya wa'azi da fadar gaskiya?tab di..Sam shikam bazai iya zama anai masa wannan raini da tsantsar cin fuska ba,..

Yana daga tsayen ya juyo a raunane
Ya dubesu
Yace"..shikenan mama..zanje din,
Nasan dai ko baki Furta ba ansan Ni Da mai yin biyayya ne agareki komin rintsi,tunda ke da bakinki yau kika koreni kika zabi danki zaidu shikenan na barki dashi,ke kuma hadiza saiki zauna anan shi zaidun ya aureki ya hadaki da Matarsa,can dama ba son zama a gidana kikeyi ba burinki ne kiga bayana,Kin hada Kai da yarki Kin rabani da albarkan mahaifiyata Allah ya isa min hadiza

A zafafe cikin bacin rai ya nuna rufaida tsaban ransa a bace yake baima iya maganan ba Sanda yaci minti biyu ya nunata da yar yatsa
Cikin Wani irin yanayi rufaidar ma ta narka masa kwayar idanunta da suke mugun jefarsa da nannauyan kalamai Masu rauni dake boye aciki wanda tuni ya karanto su kuma ya fahimce irin kunci da takaicin datakeji aranta game da shi
Duk da haka bai fasa ba yace
"Kije...na barki da su
Tunda akanki xanga tijara arayuwata.. rufaida Allah ya..cikin sauri yaa sheik ya rufe mai baki ya hanasa Furta koma miye zai Furta akan rufaida a mugun fusace ya bangaje hannun sa
Masifa ya shiga masa ya juyo a hatsale ya yo kansa tamkar zai bugesa
"Wai shin ni sa'arka ne zaidu?..inai ma yata magana meye hadina dakai da zaka toshe min baki?..ruwa xaka saka akasa kasha anxabeka a matsayin da nikuma ance canzani akai...
Amma fa Kusani haryau nine da Iko akan rufaida sabida nine na haifeta sannan bazan taba tsine mata ba,.
Niba kamar mahaifiyarka bace datake sallama yayanta ga duniya

Da sauri Yaa sheikk ya kallesa hjy mama ta miqe tsaye,'..tace eh aje ahaka, Dan ka zageni Wani abune?
Rufaida yarka ce Babu wanda ya isa ya canja Hakan shiyasa ma ka samu damar muzanta rayuwarta aida ni uwace agareka da ko auren ma ba'ayi ba.
Amma yarinya bata so bataso sanda akayi, bukar ashe bakama San mawanda ka lika wa yarka ba?Kai a naka tunanin wannan abunda ka aikata wa rayuwar yarka adalci ne?
In adalci ne ka fayyace min yanzu inji...Sabida ni ban gane salon jahilcin dake yawo akan ka ba,wannan ai mugunta ne da rashin sanin darajar Dan adam.
Toh alhamdullhi rufaida da bakinta tace ta yafe maka Amma nidai hasiya bazan sake daukar rashin hanklin ku ba,rayuwar jikata yafimin dukan abunda kake tunani.
Kuma Daga yau zan soma daukan mataki,karka Kuma saka aranka cewa akwai kalamin da zaisa na janye fushi na akanka bukar.
Araunane ta juya ta kalle umma tace
"Ke kuma ai saiki bishi ku barmin gidana,kije can kita masa bauta..karki karban ma yayanki yanci..Daga yau nidai bazan dau nauyin kowa ba duniyar ta ishi kowa riga da wando
,hadixa na bar ki da yar ki rufaida,..kije kisata agaba ki kashe ta kema...inkin ga dama karki tsaya mata har abada, nagaji da ke da jahilin mijin ki.
Duk ku futa kubarmin gidana
Cikin wata hargitsiyar bacin rai ta Kara sake musu tsawar da sukaji shi har tsakar ka tace
Kufita Nace muku ko saina tsine muku albarka ne ? Cikin
Mutuwar jiki da xuciya ya sheik ya gurfana agaban ta,
Tun kan ya fara rokon ta ta hankade sa cikin masifa
"Zaidu ka kiyayeni ko in kaima in faffalaka maka Mari...idan na Kara Jin bakinka akan zancen rufaida Allah ya isa ban yafe maka...tana Kaiwa nan ta fashe da matsancin kuka
Tace kabarsu suje da Ita su kashe ta.
Aiba Kai ka haifa masa yarba,tunda ya tsaneta baya kaunarta saiya tafi da Ita can gidansa ya kashe ta yasha Romo,ke kuma kije can kizauna kita masa kuka bakin cikin mutuwarta ya kashe ki..
"Ni ku futamin a gidana bana son ganin ku,na sallameku arayuwata duniya kaf su zageni,Aje afada Duk abunda za'ace akaina, eh din nazabe Dana xaidu na yafeka ka bukar,Nafada na Kara fada Dan ba tsoronka nakeji ba

A xuciye yaa malam
Yake kallon hjya mama wcce take maganan ta a xuciye Dan ta dade bata tsincin kanta cikin wannan yanayin fushi da bacin rai ba..

Jiki a sanyaye yaa sheik ya sunkuyar da kansa cikin rasa abunda yake masa dadi,yaa malam kuwa kada kansa kawai yayi cikin tsananin fushi ya saka Kansa agaba yay waje baikoyi yunkurin bata hakuri ba..
Da zazzafar fushin hakan ta miqe tsaye cikin masifa ta fatattaki umma hadiza waje datake famar kuka,"..
Haka ta rufe idanun ta tace rufaida maza tabi uwarta suje can..Rufaida batace uffan ba yanayinta ya balain nuna halin karayar da xuciyarta yakeciki,a sadade ta juya a hankli ta bi bayan umman tana takawa a dangale tana goge ruwan hawayenta,Suna fita a falon Hajiya mama tayi sauri ta haura sama ayayin
Da yaa sheik yabi bayan rufaidar da sauri kuka kawai takeyi,ya janyota baya ya Dan rarrasheta yana cewa zaizo har gidan gobe dakansa ya duba lpyarta ya mammata nasiha akan ta kwantar da hanklinta ya Kuma tunashar da Ita adduoin daya kokkoya mata acikin kwanakin Nan,hannu ya saka a aljihun sa ya debo kudin da baisan ma nawa bane ya damka mata yace tayi sauri ta iske ummanta da already ta isa bakin gate ta tsaya Agefe haka tana famar kukan takaici

Yaa mallam kam ko ajikin sa,Koda ya tsare adedeta ce mata yayi karta sake ta biyosa kota shigo masa gidan sa tare da rufaida

Yace mata ai dama tundacan ya fada musu cewa Duk wacce ta kashe auranta bazai Kara daukar nauyinta ba,bare ma rufaida data rabashi da albarkan mahaifiyar sa,yace ma umma ta zaba ko auren ta ko rufaida...

Umma batace mai uffan ba harya gama bambamin sa, ganin har rufaida ta fito tana tsaye tana jin Duk abunda yake cewa yasata dauke kanta daga kanshi ta shiga kallon yartan cikin sauke wata nannauyan Ajiyan xuciya batayi wata wata ba ta sakai ta isa gabanta direct ta rungume ta ajikinta suka tsaya suna ta Kallon sa

Kallon minti biyu ya musu sannan yaja wata arniyar tsaki aransa yana jin tsananin baqin ciki wato hadiza ta zabi rufaida akansa kenan ko,?Wani tsakin ya dada ja yanacema mai keken ya kaisa gida
Babu bata lokaci ya tafi ya barsu a wajen a tsaye...

Ko ajikin umma ta jawo hannun yarta suka fara takawa ganin kamar rufaida bazata iya jure tafiyar ba yasa ta sabata a bayanta har suka isa bakin titi sannan ta sauke ta,da kyar suka samu abun hawa dake dare ne,rufaida ta Ciro kudin take ta miqawa ummanta kudin da kawunta ya damka mata wanda a Ido dai zasu iya finn dubu ashirin sabbin yan dubu dubu,basu tsaya a ko ina ba sai chan anguwar maguzawa inda yakumbo take,dubu daya ta baiwa mai keken ganin dare yay ya tafi yanata godiya,still ta Kuma saba yarta abaya suka nufo cikin gidan Kai tsaye wani Lumshe Ido rufaida tayi abayan uwartan tayi luumui tana sauke numfashi batare da saninta bama har suka iske Wani daki dake shikadai ne ma a cikin gidan
Suna isa daf bakin kofar ta sauketa a hankli,waje rufaida ta nemi ta zauna ta jingine kanta da bango Jin yadda zazzabi yake ciccinta ata ciki Sam bata jin dadin yanayin ta.
Umma hadiza dake tsaye batayi wata wata ba ta shiga buga kofar tanayi tana juyowa tana lura da rufaida hankalin ta gaba daya yanaga Kan yartan da Dan qarfi take cewa
"Salamu alaikum yakumbo?Dan Allah yakumbo ki taho da sauri ki budemin kofa da ni da rufaida ce kuma batajin dadi...yakumbo
yakumbo...yakum..
Yakumbo dake tsakar da bacci ta somajin maganan kamar a mafarki can dai ta farka da bude idanunta a firgice Jin kamar muryan hadixa ne awaje ana kiran sunanta mamaki ya sata diro kasa Cikin sauri tana famar lalubar dankwaln ta daya salube wajen bacci Batama iya rufe cinyayyen farin kantan da kyau ba ta iso bakin kofar a agaggauce harta saka hannu zata bude kofar sai kuma ta soma tunani kode aljanu ne suka zo mata?inba Hakan ba yo mezai kawo hadiza cikin dare abunda bai taba afkuwa ba,hakan ya sa ta Kara Jin tsoro da dar dat aranta ta Dan dakata kadan na minti daya cikin Kara kasa kunnenta waje,Wani irin ciwo cikin rufaida ya hauyi ta riqe cikin dam cikin sarkafaffen numfashi can da ya murdota ta sake yar Kara tace wayyo Allah ciki na umma
A hanzarce umma hadiza tayo kanta
Tare da tallabota jikintane ya soma bata Hala yunwa ne yake damun rufaida,sake kallon kofar tayi da dan karfi ta nude muryanta tace "yakumbo,yakumbo kirufamin asiri ki bude min kofa Kar yata ta mutu..tun kan ta Kara Furta Wani kalamin sai butt sukaji dorowar mutum a gaban su kamar wanda aka jefota cikin tsananin razanar Jin muryan rufaidar datayi harta hankodo kofar tayi waje batare da saninta ba,a gigice cikin yanayin mamaki ta tsaya akansu tana tafa hannun ta da qarfin shauki mai cike da mamaki tace
...salawatu sanyi kalau....yau Menake Gani haka?"Menake gani haka hadixa!a Ina kika samo yarki Rufaida?Sai kuma ta fashe da Wani adadannnen kuka Laluben fuskar rufaidar ta hauyi Duk dama acikin duhu suke bai hanata kamota jikinta ba,cikin barkakken kuka mai tafe da rikicewar tsufa da mamaki tace"Rufaida?Allah sarki rufaida,har Ina kika shigane kika bace mana munta nemanki rufaida hankalin Kowa saida ya tashi akanki,oh ni yasu na dauka ma an gudu dake ne rufaida
...ashe da rabon kara saka ki a idona,..Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun
Allah yau mun gode maka,ta karashe Hakan cikin kuka sosai,a lokacin rufaidar ma kuka takeyi sabida ciwon datakeji ajikinta ya fara tsanantawa kanta da cikin ta Duk sun hadu sunai mata zugi ga Wani uban Nauyin da Zuciyarta yake mata,..lura da yanayinta yasa suka danne zuciyoyin su daga mararin tausayin ta da sukeji suka tallafota suka shiga daki da Ita tare,ba su sauke ta a koina sai Kan gadon yakumbo rufaida ta kwanta a ringingine ta damko cikinta tana Dan murkususu tana sauke Hawaye
,acikin matikar yanayin damuwa umma hadiza ta juya ta kalle yakumbo tace "yakumbo cikin ta ne yake mata ciwo ko akwai abunda zata sha taji Dan sauki? Ga dare ya rufa Duk an kulle shaguna aida sainaje kasuwa in siyo mata magani
..yakumbo bata tsaya Jin ta ba ta juya ta shiga jajjan tsohon ajiyanta na karkashin gado ta hau binciko mata magani,gaba daya umma hadiza ta kasa samun nitsuwa da sukuni sai juyowa take tana kallon yarta tanajin inama ta karbe wannan zafin ciwon da kuncin ta dorawa kanta Koda yarta data huta,can yakumbo ta dago tare da Wani kullin maganin gargajiya a hannunta tace yi sauri kijika mata Tasha insha Allah zai mata magani,hannu umma tasa ta karba Amma badon San ranta ba, fita waje tayi ta debo ruwa a randa kusan rabi dan tsaftaciyar mudansa ta jika maganin sannan ta miqawa rufaida ta umarceta da sha,a hnkli take hadiyar maganin tana yamutsa fuskanta warin maganin gaba daya ya hau mata Kai,shanta keda wuya ta rinka kwaxa musu amai,tamkar hanjinta zata amayar haka taketa aman gaba dayansu saida hanklin su ya tashi suka yo kanta,sai can aman ya lafa yakumbo ta jawota ta fitar da ita ta shiga tsaftace ta umma hadiza Kuma ta shiga tattara wajen datayi aman acikin dakin,zama sukayi a yar dakalin dake waje da dan fitilansu a gefen yakumbo na rike da rufaidar a jikinta ta rungumeta tsam tana shafa mata bayanta a hankli
Lafewa tayi sosai ajikin yakumbon ta Dora kanta akan kirjinta ta lumshe idanunta tsam Dan alokacin Babu abunda takeyi sai sauke gajiyayyun Ajiyan xuciya..

Sunfi minti 10 a haka Maganan da yaa malam ya gaya ma umma shiyake dawo mata yana ta damun zuciyarta
gaba daya saita rasa ita din wacce irin baqar mujiyace duba da yadda sanadiyarta ta jawo yau uwa da danta sukayi rabuwar Babu dadi,yan uwan juna suka raunana suka gaya ma juna baqaqen magana,ga mahaifiyata ta jefa kanta a cikin barazanan rasa aurenta sabida ita..
Ta rasa ita wacce irin halitta ce da bata da albarka Sam,mutane basa samun sauki ko sassauci atare da ita saidai ayita samun matsala dominta...

Dada runtse idanunta tayi tsammm cikin tsumayin baqincikin kanta datakeji Ita kanta Kukan daya kufce mata bata San ta Ina ya fito ba
Kawai jitayi yakumbo tana lallashinta da Muryan ta dayake fitowa da mugun tausayi

Itama kukan ta shigayi tana shashhafa fuskarta Koda zata samu ta nitsu Amma Ina abun yakasa dena cizon Zuciyarta,tana mugun mugun jin zafin abunda suke faruwa sabida ita,she just can't hold it anymore,it feels as asif she is just a badluck to anyone's life,a curse to those who loved her,gani take kamar baqin jinintan ne ma yasa baban ta ya kasa Jin tausayin ta,cikin matsanancin kukan da bata shirya masa ba tace..Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, Allah na tuba kayafemin Duk Wani laifin Dana aikata maka wanda nasani da wanda ban sani ba,Allah ka daidaita tsakanin yaa malam da mahaifyarshi da Dan uwansa Allah karka bari auren mahaifiyata ya mutu sanadiyata Allah na tuba kayafeni..sosai take kukan wanda yake fitowa da dukan qarfinsa daga can kuma kasar xuciyarta dayake mata zugi,jikinta ne ya hau rawa cikin tashin hankli da kidima ta rasa yadda zata aje kanta taji sanyi, Jin haka yasa umma barin Duk abunda takeyi ta taho har gabansu ta durkusa a sanyaye tace "yata rufaida me kike fada ne haka?Wani nakasashen Murmushi mai tafe da Hawayene ya kufce mata tanayi tana kallon fuskarta tana kuma share mata hawayen,cikin tsantsar dauriya da jarumtar iya danne ciwo irinta uwa ta cigaba da lallashinta tana cewa"Haba rufaidata,yar autata Kar ki Kara jefa kanki acikin damuwa kiyi shiru abunki kinji?nasan na aikata Babban kuskure Dana kasa tsaya maki akan burikanki,nayu sakaci wajen Kare ki yata,kiyafe ni,nai miki alkwari baxan Kara maimaita wancan kuskuren danayi ba har Abada.

..dada lumshe ido rufaida tayi ba'a cikin hayyacinta ba ta shiga girgiza kanta sideways cikin tsananin shehshekar kuka Muryan ta a Sarkafe tace...."Umma Dan Allah ki koma wajen baba tunda nice kawai bayason Gani,umma mezan cewa Allah innai sanadiyar mutuwar aurenki?hjy mama ta Sallame shi taci mutunci sa sabida ni wallhy nasan yana Jin haushi na akan haka,Kuma bazai taba yafemin ba Inna rabashi dake kema.
Umma kirufamin asiri ki koma wajen sa Koda Wani abu mai kyau zai faru Dani arayuwata umma rayuwata ta lalace sabida kinbin umarnin sa tun farko..dagaskiyar baba dayace nice banda gaskiya
Dan Allah karki bari na Kara shiga Wani damuwar a dalilin mutuwar aurenki
..wallah mutuwa zanyi umma, da sauri umma ta rufe mata baki hawayen da bata so ta sauke su suka shiga bulbulowa da qarfi wani Yuuuu suke zubowa daga cikin kwayar idanunta tamkar wacce dama ta boye sune awani waje..."yakumbo ta sunkuyar da kanta kasa bata iya Furta uffan ba tsaban tausayin su,Babu bata lokaci umma ta shiga goge hawayen ta a Duk sanda ta kallo rufaida agaban ta wani sabuwar Murmushin Jin dadin hakan zaka Gani yana haskata
Sanda ta Dan nitsu sannan a hankli ta juyo ta kalleta tace
"Rufaida ki kara hakuri kinji?".insha Allahu zaki cinye jarabawar rayuwar ki,nikaina
Nasan abunda kike tunani,Amma nakasa iya Jin shauqin aikata komi sabida nayi kewarki yata,ayau bana da wata bukata face inga na kula da ke, inaso matukar so in kasance a kusa dake har washe garin gobe,Kuma Koda banason komawa ga mahaifinki ni mai iya aikata Hakan ne saboda ke yata.,kisani
Duk Wani abunda zaisaki farinciki ko Aina yake zanje in Nemo miki shi
,Amma yanzu Ina rokonki da ki kwantar da hanklinki kinji?zanso ace kinci abinci kinyi bacci ki dan huta"..ta shiga shafo kanta cikin yanayina tausayawa tace tun da kika dawo baki ko huta bafa rufaida?..
Karki damu kanki ni nasan menakeyi Kuma insha Allah bazan sake yin kuskuren jefa rayuwarki acikin wata damuwa ba.

Da Hakan suka dinke maganan rufaida taji Dan sauki sauki aranta dake ma maganin da yakumbon ta bata asalin mai kyaune sai tuni taji dama Dama saidai bata iya cin komi ba har bacci mai mugun Nauyi da gajiya ya dauketa.

Rungume a kirjin mahaifiyarta take baccin Inda umma hadiza ta kasa runtsawa Sam ita kadai sai juye juye take tsabagen tunanin dayake yawo a kwakwalnta

Ko kadan bata so ace rufaida ta nemi alfarman ta koma wa yaa malam ba,Dan aranta tagama qudirawa akan zata tsaya ma rayuwar yarta ne komin rintsi komin wuya,saidai fa alkwari ta dauka nacewa Duk abunda rufaida take so shizatai mata musamman in ya shafe farinciki da samun nitsuwarta to koyaya yake tasa aranta kawai shi zatayi..

Can kusan asubahi yakumbo ta farka still taganta azaune ta rafka Wani uban tagumin ta Kure jikon bango da idanu,a lokacin harta Dan shimfede rufaida akan cinyarta tana Kuma lura da Duk Wani saukar numfashinra sai aikin shafo kanta takeyi tana sauke Ajiyan zuciya mai Nauyi wanda tamkar shekaru dari tayi bata kalle yartan ba.
Dan lumshe ido yakumbo tayi ta Kuma budewa Dan gaba daya tausayi hadiza take bata duba da yadda ta nitse cikin zurfin tunani aganin ta baidace ta kyale ta tana Tara ciwo da takaicin da namiji acikin zuciyarta ba Hakan yasa ta daure ta fincike Dik wani baccin dake cikin idanunta ta miqe ta zauna ta shiga yi mata nasiha masu shiga jiki tana tambayarta labarin yadda sukayi suka samo yarta rufaida?..Duk bazuwar labarin kama yaa malama da akayi yakumbo bata sani ba dake talauci yariga yay mata yawa Kullum yawon jeji take tana neman abinci da abunda zata Dan sayar ta rufa makanta asiri.

Babu Wani boye boye umma hadiza ta zage ta shiga zayyana ma yakumbo Duk abunda ya afku da rufaida da asalin abunda suke ciki ayanzu da mijinta dayace saidai ta zaba tsakanin auren ta da rufaida,wanda za'a iya cewa ko kukan datayi a farko baikai wanda takeyi ayanzu ba sabida sosai abun ya shigeta ya raunana mata ruhi, zuciya, da gangan jiki tanajin zafin abun aranta matuka bana wasa ba.

Ita kanta tasan dan dauriyar datake yi tana tsayuwa da kafafunta ayau Duk sabida rufaidarta ne,Dan ayanzu Sam bata da bukatar Kara mata Wani damuwa

Jikin yakumbo sosai yayi sanyi Dan taci kuka ta gode ma Allah har sanda muryanta ya dauke gaba daya, duk dama aranta taji matukar dadin irin hukuncin da Hajiya mama ta yanke akansu,saidai sabanin ita hajya mama datake ganin kamar lefin umma ne data kasa tsaya ma yayanta,ita kuwa yakumbo Gani take komi lefinta ne.

Aganinta Da can bata nemi maganin jeji awajen bukar ba da babu abunda zaisa ta bashi yar rikon ta hadiza bare har irin wannan mummunan abu ya afku.....surayyahms






*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


Part1:chapter 24


Bangaren yaa malam kuwa ana sauke shi a kofar gidan sa baiyi wata wata ba ya nufi cikin gidansan ayanayin bacin rai da tsananin fushi wanda tsaban munin sa aransa yasa hatta kwayar idanunsa sanda suka sauya kala sukayi jaajaxur kamar anhura garwashin wuta,tafiya yakeyi gaf gaf gaf kamar wani Doki,yana haki yana huci yana kuma sauri tamkar wanda zai kifu akasa ya ci da bakin sa haka yake jefa kafafun sa,idon sa a rufe take,bai biya dakinsa ba ya wuce direct zauren rubuce rubucen sa na lakanin qur'ani daya sabayi,yana hankade kofar zauren ya fada karkashin gado ya soma fidda wasu Alluna,ruwan tawada na musammn da Wani jimmamen buzu..

Kara lekawa karkashin gadon yayi ya fidda wani abu a lullube da farin kyalle Duk kura da datti ya hau kanta,baidamu ba ya shiga kakkabewa sanda kuran ya ragu sannan ya ajiyeta agabansa,cike da nitsuwa ya yaye kyallen,wata yar madaidaiciyar akwatin gongoro ne ta bayyana agaban sa wanda aka rufe ta kirif da makullin tokos silver colour,key dinta ya dauko ya budeta atake Daga Nan Bai bata lokaci ba ya shiga barbaje abubuwan dake ciki Wani irin qur'ani ne wanda yake brownish_red in colour,anjerasu a falle falle daga Ganin sa kasan jimammen ajiyane wanda bada fasalin hafs akayi rubutun sa ba,an zayyana ayoyin ne da asalin fasalin rubutun warash,Asalin irin rubutun nan na ta da can can wayanda suka matikar kwarewa..

Daukar qur'anin yayi ya ajeshi a gefe sannan ya Kara jefa hannun sa cikin akwatin yana lalube Jim kadan ya fidda Wani sihirtaccen turare,turaren baida wani yawa Dan kwata kwata bazaifi yayi cikin kwalban fiya fiya ba,budewar sa keda wuya Wani azaban qamshi mai ratsa jini da jijiya ruhi da kwakwalwa ta mamaye wajen hartana neman bugar dashi,a kusa da qur'anin ya ajiye turaren ya Kara lalubar akwatin ya fito da Wani ferarren alkalami mai Dan uban kaifi da tsini,gefe yay dasu duka sannan ya rufe akwatin.

Acikin allunan daya fitar yasaka hannu ya dauki na karfen cikinsu wanda yake tamkar takobi,sau daya ma ya taba amfani da Ita arayuwarsa tsaban qarfin sirrinta da muhibbanta a idanun sa, itakanta tawadar ma saida ya zaba daga nan bai bata lokaci ba ya hadata da ruwan Wani magani ya Kuma jefa wancan alkalamin aciki Nan danan ta jike aciki sosai

Miqewa yay ya nufi can sashensa ya bude kofar dakinsa ya shiga ya dauko kwarya da sauran abubuwan bukata kamar ruwa da buta da wasu lakani wanda bansan su ba...
Bai dawo zauren ba sanda ya shiga bayi ya doro sabuwar alwala yanayi yana wasu irin maganganu tamkar zararre da alaman har yanzu wutar dake cin zuciyarsa bata matso kusa da mutuwa ba

Shigarsa zauren keda wuya ya shimfida wata farar buzu ya haukai ya zaune kafafunsa a dungulme,sann ya dauki qur'anin ya shiga bubbudewa daidai Inda yakeso ya jera su falle falle, shafukan da zasuyi mai amfani kaf ya ajiyesu agaban sa
Zaman dirshan yay akan buzun Nan tare da nade hannun garensa yana wasu irin tofin da bansan kansu ba daga Nan Bai kara bata lokaci ba ya dau allon karfen nan da tawadar ya dorata akan cinyarsa ya hau rubuce rubuce Wanda Ako Wani iyakar rubutun dayakeyi saiya shaka dafin tawadar ta numfashinsa wanda yake tayashi jefa sirrin lakanin sa aciki,yanayi yanai ma wasu ayoyin wasali wasu kuma baya saka musu wasali,wasu yakan daure wasu yakan jaaa,ahakn sanda yaci kusan awa hudu yana abu daya.

Kafin ya gama Gabadaya jikin sa yayi tsami ga gajiya ga azaban yunwa ga tsananin fushi da bacin rai daya wuni da shi saidai dukkan wayannan basu hanasa aikata komi ba...

Ana daf za'a kira fajr ya miqe cikin sauri ya Kara komawa bayan gidan sa alwala ya Dora sann ya dawo,rubutun dayayi a allon ya shiga wankewa yana tsilalo ruwan a Dan madaidaicin kwarya,kusan cika kwaryan yay da ruwan rubutu sannan ya ajiyeta Agefe ya nade buzun sa tsaf ya dauko dayan jimammen buxun mai brownish red colour ya shimfida ta ya haura Kai ya tsaya a tsaye kyam kamar tsohon soja tare da kwaryan a hannun sa,daf setin bakin sa ya kawo kwaryan tamkar wanda yake shirin tofa Bismillah sai ya shaisha,,lumshe idanunsa yay ya shiga ambatar wasu irin tawaludun sumbatun karatu wanda ba agane komi sai sunan zaidu daya ke tofawa harda numfashin sa acikin kwarya....

Yana gama tofen tofen sa ya shanye rabin ruwan,sauran ya ajiye acan waje daf setin inda hasken rana zai billo ya dau turaren Nan ya zuba kadan aciki yabarsa awajen,komawa dakin yay ya tattara komi nasa ya maidasu one by one wajen ajiyarsu tamkar da ba ama taba su ba.

Lokacin daya fito ana famar kiraye kirayen sallahn fajr wasu masallatan harma sun shiga Dan haka yay sauri shima ya fita yaje ya kira nashi sallah yana mai jan almajiransa, daga nan bayan sun kammala suka bingire da bitan karatu.

Kowa sai mamakin
Ganin yaa malam yakeyi,cos last Thy know was polisawa sunzo sun daukesa sun tafi dashi Amma Daga Nan ba a Kara Jin sauran zancen ba..

Wato tsabar yadda axaban gulma da makirci da mugun iya saka ido yayi danko yayi kuma katutu a xuciyoyin Yan anguwar acikin Yan kwanakin Nan har comitee suka hada akaje har Gaban dpo domin aji Kan labari saidai basuci nasara ba..

All this while Babu abunda ake yayin gulman sa a anguwar face matsalar gidan yaa malam wanda tun daga auren rufaida basu gane kan komi ba.

Tun ranar da aka kama yaa malam aketa zirya a kofar gidan sun babba da yaro tsoho da tsofuwa,ahaka ma banda makwafta da Yan nesa wayanda sukayi degree a gulma,Kai hatta matar mai anguwar su saida tayi sawu goma shabbiyar a kofar gidan yaa malam Wai Koda ma zataci Karo da umma hadiza taji Kan labari.

Karshenta Acikin duhu suka zauna kowa da yanayin harsashen sa Duk

Please Login or Register in order to submit comment