Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rufaida ta dabawa mijinta wuka aciki don kawai bata son sa.
Da gatse Yakumbo tace ehh sannan kuma mijinki ya arci na kare ya sakeku a walaknce baikara dawowa ba tsaban gaskiyar sa ba?,shin kin taba tambayar kanki meyasa mijinki yake wasan boye boye da hukuma,toh da walakin goro a miya..gwara ma ki nitsu kisan inda dare yay miki nikinga tafiyata cikin daka,da kallo suhan tabi yakumbo kirjinta na balain bugawa can anjima ta tashi itama tabi bayanta.

Bangaren rufaida kuwa bacci ta rinka shara musamman ma dataji ta acikin sanyi da qamshi.

Karfe 9:30 na safe Dot anty fareesa tayi horn agaban wani hadadden gida
Ginin zamani ne mai kyau modern scandanavian design komi na gidan Ash da light brown colour ga yelwataccen furanni masu dauke ofo da bishiyoyin umberalla da palm trees yn dagwal dagwal gwanin ban sha'awa..

Mai gadin su da ake cewa yaa liman da gudu yazo ya bude musu gate ta shigo ciki tayi parking motar ta a inuwa bata sauko ba harsanda ya kulle gate din gidan kirif,..barka da dawowa hajy, Anty fareesa tace yawwa malam liman please bayan likita na dazai shigo yanzu kada ka bari wani yashigo,duk wanda yaxo kace mai bana nan, strict oder.

Malam liman yace toh angama hjya..
Yana barin wajen ta bude kofar motar ganin har yanzu rufaida bacci take kanyi yasata sauke ajiyan zuciyaa a daddafe ta tallabota jikinta tana dan shafa fuskarta ahnkli harta dan farka saidai kallo daya zaka mata kasan ba a cikin hayyacinta take sosai ba,cikin wannan yanayin ta sauko kasa anty fareesa ta tarbota ajikinta suka wuce can cikin gidan tare.

Bata ajeta a koina ba sai dakinta dake can saman bene banda kalle kalle babu abunda rufaida takeyi a cikin nitsuwa ta shimfideta akan wani makeken italian bed wanda yagaji da haduwa an kawata shi da kwalliyar jan zanin gado,zama tayi abakin gadon tana kallon fuskarta da yay fayau,,a hnkli ta furta mata kalman sannu..sai sannan hawayen ta suka kara gangarowa ta gyada ma antyn kai

Tausayi sosai take bata shiyasa batajin aranta yadace ta takurata tun aynzu tayi wani magana dan gani take kamar itama zata iya barkewa da kukan tausayi agaban yarinyar alhalin alkwari sukayi da mijinta nacewa bazasu bari rufaida taji aranta ita abar tausayi bace awajen su

Jiya cikin dare suka yanke wannan hukuncin tsakanin su su uku itada mijinta da hajya mama,acewar hjy mama tunda ance musu yaa malam baya gari kawai fareesatu taje ta dauko mata rufaida ta riketa wajen ta nadan wani lokaci kafin suje abuja da yaa sheik su dawo,Alkwari sukayi dacewar babu wanda zaiji hakan atsakanin su harsai an sasanta komi.

Mijin anty fareesa ne ya kara karfafa ma hjy mama gwiwa akan haka,aganin sa Anata jan lokacine wajen neman sulhu kar kuma azo ayi dan dana sanin hukuncin da aka yanke akan ita yarinyar dan har yau babu wanda zaice ya san asalin metake ji a zuciyarta na damuwa.

Anty fareesa Tana zaune awajen tana ta tunanin yadda zasu taimakawa rufaida har likitan ta yazo,sunan shi doctor kabeer mathur Speacial physchologist ne dayayi karatunsa a kasar india ya balain kwarewa a fannin harkan psychology da social human neuro therapy,he can deal with trauma and stress at all levels akanyi aiki dashi har a asibitan dabbobi dana mahaukata infact he do work for security agency for intelligence jamian tsaro sukan daukesa in ana neman wani taimko akan gane yanayin mutum musammn inshi murdadde ne ko physcopth ko narcisst,nan da nan ya hau duba yanayin rufaida ya mata wasu allurai masu zafi wanda atake atake suka kashe mata jiki tahau wani sabon bacci nan ma ya ja jininta a syringe ya musu sallama dacewa sai can dare zai kara dawowa ya dubata.

Around 2pm rufaida ta farka,Zama tai ta dukunkume kanta cikin cinyoyinta kafafunta na rawa rawa ga wani irin zufa dake keto mata ta koina sabida azaban ciwon cikin dake murdata, tun tana zaune har saida takai kwance awajen tana juye juye,tsahon lokacin data dauka ahaka yasa ta jin kamar anyashe mata hanjin cikinta ne,tuni ta soma harsahen hala ba ciwon bane kadai harda yunwa dan rabonta da abincin kirki tun jiya da daddare,tashi tayi zaune a hankli tana waige waige ganin babu motsin kowa,gashi bata son shhiru yayi yawa ba waje yakan tuna mata wasu mugayen abubuwan data riga ta binne akasar zuciyarta

A hnkli ta koma ta kwanta ta rufe idanunta gam gam zuciyarta ta na kkrin karanto Addua, cikin ikon Allah kuwa saiga wani baccin mai mugun dadi ya kwasheta da alaman hakan nada nasaba ne da wahalar datake sha na rashin samun cikakken nitsuwa ta zuciya..

Fannin Ainau kuwa basa ko ga maciji da mufrad dan har wani tsanar sa matakeji aranta iyanzu,ganin tun ranar baibi takanta ba yake kara hatsala ta

Sosai idanunta suka rufe wajen son ta aje duk wani digon son sa dayake mata dabaibay aranta danta hukunta shi.

Duk dramar da akeyi agidan baiya kulawa,yauma daya kammala aikin dayakeyi ya sauko yaci abinci,bai wani ci dayawa ba ya tashi ya shiga toilet don dayake kasa yay alwala ya wuce masallacin farfajiyan gida,anan yakai har 4:30pm yana tashi awajen ya dawo gidan ya haura sama yacigaba da ayyukan shi bai neme kuwa sai kuma sallah dayake tadashi,haka yake rayuwar shi har dare after 12pm normally yake shutting eyes dinsa ya kwanta bacci,washe gari 6 zaka nemesa ka rasa agidan sai kuma inya dawo..

Ba Ainau ba hatta imad bai wani gane kansa kwana biyu nan ba,ga fitinar zarah data mugun makalake masa a wuya aynzu sam sam bata barinshi ya shaki iska a kullum tana nanike dashi kamar wata jela.

Fannin malak kuwa tunda mahaifyarta ta nuna rashin gamsuwarta da zuwa kano sai jikinta yay sanyi ta soma cire abun aranta kawai..
Yawan waya da sukeyi da imad ma tuni ta dan tsagaita duk dama haryau ta kasa iya furta masa asalin dalilinta.

Hjya mama dake shirin biyo yaa sheik Abuja wanna karon wani zazzafar zazzabi ne ya hanata,karshen ta shikadai din ya taho yazo ya tarar da gidan babu dadi dan sosai sukayi fushi dashi kusan kwana yay yana lallamin su
Yana musu bayani
Ahakan ba sonda suke masa ne kawai yasaka suka dan sassauto sukayi hakuri amma bawai har ransu suka yafe mashi ba...

Tun zuwarsa suke kayyado masa nasu dokokin daya saba na hjy mamah
,wanda akalla yasan bazai taba yuiwa ya dauki nasu ba sabida uwarsa ta wuce abun wasa.

Kawai amsa musu yakeyi,amma agefe tuni ya umarce matar sa akan ta soma nazarce nazarce da shirye shiryen dawowa da yaransu gaban sun kawai....

Haka suke ta abubuwan su a boye batare da sannin kowa a gidan ba,imad gaba daya ya daukewa yaa sheik hnkli kusan duk fitarsu tare sukeyi akan maganan kawa kan aikin sa.

Bayan kwana biyu.

Kamar kiftawar ido da bismilla Rayuwa ya fara sauyawa rufaida,kulawa na musamman ake bata ta kowani bangare,doc shima yana balain taimakwa wajen engaging dinta da deep converstion session irinasu na depressant professionals ahankli yanayi yana jin ra'ayoyinta tana kuma fitar da abubuwa da yawa wanda suke toshe mata tunani da jin dadi,ga wasu allurai da ake mata ajijiya suna da mugun zafi kam amma cikin kankanin lokaci ta somaji kamar kwacota kwaklta akeyi daga halin data shiga na tsananin damuwa, sosai ta soma fahimtar kanta ta soma jin sauki sosai a zuciyarta sabida samin nitsaten bacci da kwanciyar hankli,no one to scold or hurt her babu kadaici ko lokacin tunani yaran anty reesa ma kadai basa barinta da kalar suruntun su thy are alwys in her company,safe rana dare suna sakata dariya da magana dan dole,kuma sama docton cewa yay abashi sati guda da ita zai iya bakin kkrinsa wajen rage mata tunnani da damuwa sauran kuma su dasu dora daga nan...

Dan haka Anty reesa da mijinta suka hau shirya abubuwan da zasu na dorata akai
kamar kara rike addini ,karatu,girki Kallo da wasa da yara da duk wni abunda zai sauya mata yanayin ta zuwa normal mutum kamar kowa.

Burin su baifi suga rufaida ta dawo cikin hayyacin ta akan lokaci ba.
They all belive she have a better future ahead of her dan sosai hjy mama take so tacika mata burinta nayin zurfin karatu,haryau kokadan bata karaya da rayuwar rufaida ba

Ataikace dai zaman rufaida agidan anty fareesa kusan wani babban cigaba ne a rayuwarta,anan ne ta samu sukuni har take iya kawo tunanin wayanda suka soma taka muhimmiyar rawa a rayuwarta musamman lokacin datake matukar bukatr taimako
Hakan ya jefata cikin tuno da fuskar imad,koma ina yake oho?but wani abu can kasar xuciyrta yana gaya mata cewa a duk inda yke he wll remain special to her and she owe him alot,tabbas nan gaba zataso ta kara ganin shi da idanunta koba dan komi ba gayen yana daya daga cikin mutanen da har abada bazata taba iya mancewa dasu a duniyarta ba.



Thursday morning.
Karfe 10:30 aka danna door bell mai aiki ta taho ta bude kofar,imad ne ya shigo sanye da wata half jumfa yadin yoloyolo white colour data mugun amshar dirin jikinshi hannunshi dake kyallei yasha agongon dave martins dayan hannun sa sakaye da awarwaron maza germ d'ela parisà masu mugun kyau bakake kirin,turaren shi na guilty absolute sai binshi take da sanyin qamshi cikin salon takunshi mai tafe da aji da nitsuwa ya nemi waje ya zauna acikin kayattacen falon inda baiyi wani minti biyar bama saiga shi ya sauko Mikewa tsaye yay baima barsa ya karaso ba yace good mrgning pa doctor,..
doc mehra dayake kan kallonshi tundaga can nesa ya saki wata mischievious smile
Batare da ya sake fuskan sa sosai ba,Har gaban imad din ya karaso ya aje wani file akan table fuskn sa adan daure gyara tsayuwar sa yy tukun kafin yace
"Imad What is d meaning of this,wai na fara wasa dakai ne?Wani Shiru imad yy dan baisan me zai soma cewa He neva wanted it like this,duk shirun malak ce ya tunxirasa.

Doc yce Dakai nake magana are u daft?
Numfashin sa yaja har can sama snn ya dago idanunsa da sukayi mici mici
Kasar wuyar sa yace.."Doc please im sorry..nasan nayi maka shishhigi but just wanted to be der for malak as my litle sis fa shikenan,

Doc yace karka karayimin haka cos i dint ask u to take any additonal responsibility,infact inkayi wasa dani harkaima bazaka je kanon ba,da har yy shiru sai kuma ya dago kansa da alamun Zaiyi wata magana,cikin dakatrwa doc yace
"A'a Ban yarda da tsarin kan nan ba
Kuma aydda ka fara komi kai kadai haka zaka warware shi.

Masifa yahau masa "Ni nataba ce maka kayi wa malak registration?infact who d hell admited her in dat university batare da taje tayi screening ba?u havent even thoug of it..itama ai zata gamo da ni..im sure she is aware, u two are acomplices.

Ahnkli Imad yace
"No she is not..
Doc please..ya fada a marairace sosai.
Doc mehra ya kureshi da idanu, iska ya furxar ta bakinshi yadan shafe gashin kansa yace.."Okay i w tell u d actual truth,well is true nina fara kawowa malak tayin zuwa kano yin karatu but aganina hakan zaifi mata sauki tinda canma gida ne,and All of a sudden sai naga ta sauya ra'ayin ta wai tafasa zuwa karatun wai zatayi anan din kawai and i know malak,she neva wanted to give up on her dreams, saidafa na takurata sosai sannan nagane cewa ashe ma kune dai baku bata support ba...nd i wonder why wll you do that to her?soo unfair..
Shine Kawai dana samu oppurtunity jiya saina nema mata makarntar kawai..and

..da sauri doc yace and da permission din waye?

Nan ma shafa kansa yay ahnkli yace,babu, am sorry sir..kallonsa doc mehra yy har cikin kwayar ido,..taje ya susutar da fuska yahau bayani
"Doc malak is like my blood sister,i just wanted to fulfil her dreams inna mutu wata rana ai bazatace banmata kkari akan abunda take so ba ko,toni meyasa zaace banda iko akanta uve been more than evrything to me,a father a friend a mentor,my evrything ,i also wanna know how intense it feels to love and care for sumone dat ure not bloodly related to,dan Allah kabani damar kulawa da rayuwar malak kamar na yar kanwata da bani dashi,.Hararshi doc mehra yay cikin jan shaukin da yay maganan dashi wanda babu alamar wasa aciki sai tulin shagwaba,a hnkli yace toh ban amince ba,..imad yy shiru.Shima shirun yay sai can yace ka nemi waje kazauna toh sai nayi tunani na yanke shawara
Bai masa musu ba ya nemi waje ya zauna yana binsa da ido harya haura sama yakoma dagata ciki,jim kadan saigashi ya dawo da Anty meera da malak din dukan su atare.

Ita batama sanda cewa malak ta yanke hukuncin hakura da karatun ta a kano sabida ita ba,koda doc mehra yay mata bayani sosai taji dadi aranta kuma tasha mamkin da ya gaya mata cewa imad ya dauke musu nauyin komi da komi na karatun malak daga nan har karewarta unirvsaty duk na rubuce acikin file din.

Haka suka sauko suka kara sakosu gaba suna titsiye su da tambayoyi,anan ma malak ta kara tabbatar musu da cewa itamai hanklice,jin tace ra'ayi da farincikin iyayen ta na gaba mata da komii

Murmushi doc ya yi,
Wato yar tana son Babanta irin sosai-sosai ko?Murmushi tayi Kafin tace.Yes, Daddy sosai-sosai take matukar son dadynta yace toh shikenan tell me 10 good reasons why u want to study dat course "information tech,Yadda suke maganar tactically with nodding head sai da suka baiwa su imad dariya sosai karshe haka suka kyaleta Doc ya barsu a nan ya wuce upstairs yana dariya shima yana cewa kansa "i just cnt belive this dan shikansa baitaba tsammanin yarsa tana da nitsuwa har hakaba..





*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


Part1:chapter 43

Yau safiyar Asabar gidan yadau wani irinshiru sakamakon yan ziyarce ziyarce na sada zumunci da
hajiya Adada take jagorantar su suje wanda Already tamaida shi tamkar wani sabon al'ada agidan

Kowani ran asabar din karshen wata haka kowa zai shirya,yau ma tun karfe 9:30am na safe duka suka fito kowaccen su tasha kyau acikin dressing na mutunci kalar su makurar daukar hankli,komin su na Alfarma ne kama daga manyan kaya da mayafai na zamani da lafayoyi wuya da hannunsu yaci ubansa da tsadadun gwal na kece raini,kaf cikin gidan hajya goggo ne kawai bata yawan zuwa koina, akan barta ne a daki sabida jikin tsufa da kuma tana yawan rama bacci dake mata yawo akai kisan kullum, ciwo da tsufar jikintan sam baiya barinta tana samun cikakken nitsuwa bare barcin dare.

Ayau Zarah kamar zata mutu haka takeji dan murna dan yaune kawai A'inau ta yadda ta jawota cikin su har aka tafi tare da ita,wani irin hade kansu sukayi da yar uwanta akwana biyun nan bamai jin kansu,yau rawan kai wajen zarah wane wane,tunda Ainau ta sakata ta shirya bakinta yakasa rufuwa,yadda kasan itace ma hajya jasmine din hakata rinka azarbabi tana shishhigewa a duk inda akaje gaisuwa.
,gidan sarki, gidan gwamna,gidan manyan masu kudin garin Abuja duk anje dasu,tamkar wata zararriya haka zara ta dinga musu murmushi wani binma har bata iya boye zakewarta da kauyancita duk inda akaje saitasan yadda za'ayi a sanda ita.
manyan abokan su na arziki da yan uwa da dangin su na Alfarma kowa yakanji dadin zuwansu dan ba karamin karfafa zumunci hakan yake jawowa ba haka za'a cika su da goma na arziki banda wanda suma suke kaiwa,a lalace dai zarah saida ta damke dubu dari biyar a hannun ta na zallan kyautar da ta samu.
Bayan sun kammala da ziyara suka wuce super market irin window shoping din nan, duk wani abunda suke da bukata na rayuwar su dana gidan dayajajja baya shi suka tsaya tsinta,Ainau ce kawai bata wani tsinci kayan kirki ba dakema yanzu kusan komi da zata saka ajikinta har ya iya birge mufrad ma haushi yake bata.


Zaune yake a babban falon sashen sa dayagaji da haduwa jikin sa sanye da wata alkyabba kirar velor black colour mai ratsin fararen duwatsu,wani irin qamshin lime basil nd mandarin mai sanyin dadi ke tashi a falon,hannun sa dake rike da tea cup mai kyau ya mika gefe ya hau tuntuda wani hadadden pink harbiscus tea dayaji hadin kayan qamshi citta da danyen qirfa da wani ganye mai dibi da ganyen na'ana mai dan uban qamshi,yana matukar son shan wannan tea din musamman dayagane amfaninta wajen kara lapyar hanta(liver) ,kusan rabi ya zuba tea din a cup sannan yakai bakinsa idanun sa a lumshe ya shaqa qamshin ta ramin hancisa sanna ya bude idon tare da furta bismilla ,a nitse yakai kan labbansa sann yadan kurba harya masa kyakwan kurbi biyu,bayan nan ya mayar da cup din ya ajeshi agefe acikin tray dinsa tare da wasu hadaddun royal tea set da babban flask na zallan ruwan zafi
Tsohon jarida yagani agaban sa zai dauka Sautin takun daya jiyo tun daga bakin kofar ya dakatar dashi,kansa ya dago yanamai gyara zaman sa mai cike da nitsatsen izza,ido ya kafawa kofar yana jiran ganin mai shigowa aranshi ya bari kawai dansa Mufrad ne dan tunda yazo garin Abuja basu wani samu kyakkwan zama dashi ba sometimes he wonder if he eva have a break in his life,he is alwys busy and ocupied da wasu abubuwan.

Haka kawai kuma sai yaji hanklin sa na tashi akan lamarin mufrad,tuno da abubuwan da mahaifyar sa take famar cewa na anya mufrad yanama samun lokacin kulawa da auren sa kuwa?shikansa dayayi duba acikin nazarin wann tambayar nata sai dayaga kamar Akwai nasaba mai girma dayakamata shima nan ya hankara da shi.

Duba da yanayin dansa wani bin har sai an mance dashi agidan ma in aikin sa ya taso,No one in his right senses zaice mufrad yanada lokacin kulawa da family bare kulawa da gidan gaba daya ba.

Koda shike haryau shidai bai taba jin ankawo wata matsala ko korafi dagata bangaren auren sa ba,hala zai iya yuwa hakan alamuce na nuna sun samu kyakkwar fahimta da matar sa
Saidai duk da haka shidai yanada ja akan yawan dauke kansa akan tsabgar rayuwarsu,shine masa namiji babba shin in tun ayanzu bai nitsu ya zamo wani jigo da jagora wa yan uwansa da familynsa ba nan gaba insuka barsu a duniyar da wuyane rayuwa yay musu sauki da armashi.

Shidai Yana mugun alfahari da jakircewa d kuma gwazon dansa mufrad, amma harga Allah cikin zuciyarshi zaiso ace rayuwar mufrad ba hakan take ba,he thinks there is more to life than seeking justice.
Kwafa yay jikin tunani "Shikenan rayuwar mutum ba hutu?dada leka bakin kofar ya dadayi kirjinshi har na bugawa dan har Allah Allah yakeyi ace shidin ne ya shigo saboda akwai tarin maganganun da zai so yaji amsar su daga bakinsa..

"Assalamu Alaikum"
..yace wa'alaikum sallam warahmatullahi wabarkatuh.

Kai tsaye Imad ya bayyana acikin falon jikinshi sanye da wata tsadadiyar black voile ya kafa hula itama baka half shoes dinsa ya riga ya cireta tundaga bakin kofa,daga sama har kasan shi is all black fuskn sa yay makutar kyau da haske wni dan uban gamshin tom ford F fabolous ne yake binshi kamar na maita,straight ya nufo inda yake yana tafiya kansa na kasa,a kasa kusa da kafafun yaa sheik yanemawa kansa wajen zama cukin yanayi nade kafafun shi dayake bayyana ladabinshi da boyayyiyar sanyin halinsa,yaa sheik ya kasa daga idanunsa akansa,Allah ne kadai yasan yay yakeji ransa game da imad haka kawai yakan ji farinciki inya gansa ata wannin fannin kuma yakanji kamar yana takurashi ne yana rage mai freedon din sa nayi rayuwa duba da babu wata kakkarfam alaka ta jini a tsakaninsu face auren yar uwan sa daya hadasu.

But honestly he is more than just that to him,arayuwar sa yakanji kamr yafiye ma imad kallon dan cikinsa daya haifa fiyeda alakar kanin matar sa dayake tsakaninsu,kamr yadda ya lura shima imad din matsayin uba kawai ya ajeshi
ajiyan zuciya ya sauke Imad yay gyaran murya
Yace"..katashi lpya?..Yaa sheik ya amsa da lpya kaifa?
Yace alhamdullhi,
nan ya hau tambayar sa akan abubuwan da suke famar tsarawa game da aikinsa
"..dan imad ne zai rike tsohon office dinsa na kano doc mehra ya riga yay masa bayani akan hakan imad din yace yake so saidai bai bayyana masa cewa akan rufaida bane ya matsu daya tafi,saidai yakan sakaya magana ne da zancen zaifi kyau imad yana zuwa kanon kodan yarinka kusantar mahaifyar sa dake can,shiysa yaa sheik ma baiyi musu musu ba ya kyaleshi,da sharadin anan din zai zauna har yay aure,badan shirye shiryen da zasuyi ba da baifi kwana kadan yau ya rage masa ya fara zuwaba,his working days are just few days a week,dats monday,thurs,friday sauran ranukun he is much expected to be in Abuja.

Hirar aikin suka taba kadan yanayi yana hada masa da nasiha sosai,shi sam baiya iya zama da mutum walau nashi ne walau bana shi ba, face ya tsinci kansa cikin tunatar dashi kalmar Allah da manzon sa.
Yau ma Wa'azin auren kawai ake masa.

Shikuwa imad har acikin ransa baifi ace mai yau yaje kanon ba,duk nasihar da yy sheik ya masa akan yay kkri ya fidda matar aure nan kusa babu abunda hakan yake tuno masa face fuskar rufaida,har wani ji yake kamr yana dago idanunsa sama hala yaa sheik zai karance abin da ke cikin idanunsa tsaf..

Tunda ga shi yanata kokarin karanto rudanin da ke tattare da muryarsa akan furta sunantan dayayi masa dazu, Shi kuma ba zai so kowa yasan da sirrukan zurciyar sa har hakan ba har sai ya ganta ido ido saboda shi kansa bai yarda da kansa ba. Bai yarda da cewa feelings dinsa are far beyond vulnerbiltyn shi ba.

Har iyau Bai yarda zuciyarsa ta kamu da mugun son rufaida ba,don a ganinsa babu wani kwakwarn dalilin hakan.

Abin da ya yarda da shi shine there are some certain characteristics about her da za su iya rikita kowanne lafiyayyan da namiji mai cikakken hankali bawai shi kadai ba.

Her well-shaped body lineage,her plain pointed nose with those thick thick brows nd eye-lashes this pinkish red soft lips da kallo daya kamai saikace bugun xuciya all of her personal outlook are actualy breath taking Kowanne lafiyayyen namiji zai yi mafarkin samunta matsayin matar aurensa na har abada


Shirun imad ya yi yawa,sannan ya ki dago kansa ya kalle yaa sheik.shima shiru yy ya ba shi mintoci masu kyau don ya gama duk tunanin da zai yi, amma ganin ba shi da niyyar magana kuma ya kasa dubansa sannan yana cinye masa lokaci,sai ya kira sunansa cikin nutsuyar murya For all he know imad dinsa bazai taba bashi kunya ba..

Ya dago bakinsa yanai masa mugun nauyi"..Yaa sheik Alfarma daya nake nema awajenka.
Ya kure shi da ido alaman ya fadi kawai,"kirjinshi kamar zai fito a kirjinshi saidai baza'a gane hakan cikin sauki ba ahnkli yace ,"..yaa sheik pls so nake ka janye maganan ka dani akanta.. sai yy shiru..can sai yace "ru..fa.ida.."Muddin ina kano,nasan zan nemi insan halin da take ciki kuma bana so in sama wa umarnin ka inka bani dama zan kiyaye sosai na maka alkwari bazan saba ma sharudan ka,i swear it.

I just want to help her like my own sister nan gaba bamu san wanda zai rike namu yan uwan ba..yaa sheik ya dauke kansa yay gefe yanakan jinsa"..da alama yaron nan fa baisan meyake yi ba,badar da maganan ma yayi yace "inashi mufrad din?a sanyaye yace yana ciki batare da ya kallesa ba yace.."call him" kaje ka kirasa kawai
Babu musu ya tashi ya fita a falon yaa dheik yanata kallon sa, dakin mufrad din ya wuce direct.

Kwankwasa kofar dakinsa yake yi, tun ana yi a hankali har aka soma yi da dan karfi.shower ya kashe ya janyo soft white tawul ya hau goge suman kansa da jikinsa a dan gaggauce. A gurguje ya nannade kansa da wata sexy black bathrobe ya dore igiyan a kunguminshi yana jiyo muryar imad a kofar dakin nasa yana ambaton sunansa a tausashe
Baiyi magana a bayin ba har sanda ya fito yana cewa
"Coming"sannan ya bude mai kofar..

Suna hade ido ya dauke kai Wucewa yay ya zauna abakin gado yahau kallon mufrad din dake faman mutsuka la mer rejunavting hand serum yana mutsukwa yatsun hannun sa dan uban qamshin plant extract duk ya cika musu hanshi with all the afalfa,sun flower and barley extract wanda

Please Login or Register in order to submit comment