Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fice ne ya jawo hanklinsa kanta,da alaman shirin fita take yi dake surutun sun ya soma haura mata kai Wani irin ciwo kantan ya soma mata bazata,cikin sanyin jiki ta miqe ta jikin ummanta kamar wanda zata rabe ta gefenta ta wuce,Wani wuff yaa malam yaa cakumo ta kamar zai figeta
,"shin ina zakije?idanun ta atake suka firfito a mugun tsorace ta dago kanta sama zata amsashi baima jira tace cass ba sai tssssss taji ya watsa mata Wani makohon mari akan fiskarta sanda ta sabule daga hannunn shi ta kife kasa a gigice

"...duka wayanda suka taso zasuzo kanta a tsawace yay kara cikin dakatar dasu,,Cikin tsawa da fada yace "Shasha sha kawai..Allah wadar naka ya lalace.
Ke wai Harni ne zaki nemi ki kunyartar?babu yarinyar danace zan mata aure ta gudu tun safe ba aganta ba waidon bata son aure,To kiji da kyau na riga dana Amshi sadakin Alaji BATURE akanki GOBE asabar da karfe 9 na safe daurin AUREN Ku
.
Hannu ya turmusa acikin aljihun sa ya fiddo wasu makudan kudi ya watso su kam fuskarta yabi ya kwashe ya maidasu aljihunsa A lokacin mutuwa ne kawai yaki zuwa na rufaida amma takai kololowa wajen zaucewa da baqin ciki

"Inkin ga dama saiki kashe kanki kafin goben..Auren ki kamar anyi angama,koda mutuwa kkyi
Bi'izinillah sai an daura auren nan da gawarki,domin in nuna miki cewa nine mai nasara akanki,nine gaba dake,sabida nine ubanki bake kika haifeni ba..ni ne nan mai iko da rayuwarki.

Har ke kin isa ince zanmiki aure ki bijire min?toh ga sakamakon silar taurin kainki nafasa jiran zagowar sati gobe gobe zaki barmin gidana

Makarnatar na hana,Na kuma haramta duk wata hidiman biki domin ki,daga an daura aurenki gobe zaki bi mijinki duk wanda ya daga kafarsa wai zai kaiki gidan miji Allah ya isa..Allah ya rufamin asiri babu wata yar iskan yarinyar da zata tona min

.....Wani irin birgima akasa rufaida takeyi tana kuka sanda tayi fayau tana rokon sa gafara amma ina baiya najin ta dan dabiar sa ne ya hawra can sama yana bunkasa musamman idan ana bashi haquri

Anan ya hada harda sauran borin fushinsa ya borance ya kore masu fidda amarya waje yana cewa rufaida tayi ma yan uwantan duka kallon karshe dan daga yau bazata kara ganinsu ba.

Kuka kawai rufaida take yi kanta akan kafar kakarsu da ke matse kwalla itama tana ta kwararo bambami duka abanza Umma kuwa tunda ta kife kanta akasa tana hawaye bata kara dagowa ba danji take kamar kirjinta zai fashe yy aman wuta tsaban radadi.

,"hjy jasmine da yarta faressa su suka jagorance murja ruqayya da jadwa sukayi waje da amarya suhan a cikin yaran kaf babu wanda xuciyarta baiya cike da jimamin tuna mumumunan kalaman mahaifin su akansu saukin abun daya dake su sun masa biyayya

Hasalima duka ganin laifin rufaidar sukeyi datazo da wannan sabon salo na neman wa kanta yancin yin karatu wanda aganin su hakan bata makai lokacine da neman karawa wakai takaici,dan tun bayauba kowa yasan halin mahaifinsu Yaaa malam, da rikakken ra'ayinsa na babu mai saka shi bare kuma mai kuma hanashi.
Surayyahms contact 08060712446

Part 1 IS FREE,TUKUICI NE GAREKU MASOYA NA U CAN READ IT HAR ZUWA INDA ZAMU TSAYA,SAIDAI CIGABAN SHI NA KUDI NE,PLS SHOW SOME LOVE AND SUBCRIBE the ACCESS FEE IS 300 NAIRA ONLY
VIA 0152983148
MOH'D SULE SURAYYA GTB.
OR katin MTN vtu tran via 08060712446

Screenshot ur evidence to SURAYYAHMS 08060712446

OR MAMAN MUBENA
08036651119.




*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


Part1:chapter 3
*Too fast,too soon*



Yamma ya rufa sosai dan haka yan kai amarya suna fitowa aka dau himmar kaita gidan mijinta dake can ta bayan babban airport din gari ,Alaji omar okene babban dan kasuwa ne kuma yana da kudi sosai dan haka shi aka bawa suhan din a matsayin mijin aure,saidai shi asalin sa inyamuri ne ta uwa ta uba,cikaken haihuwar Abia state ne girman cikin garin kano,shiyasa ma a Fuska da dabiar sa bazakayi saurin cewa shi inyamuri bane dake acikin hausawar ya taso tun yanada shekara hudu na haihuwa,.

Toh Wayanda suka san asalinsa since neman kudi ne ya fara tarkatosu shida iyayen sa sukazo garin kano suka yada zango a bayan gari,ande san inyamuri da shegen son neman kudi dan haka sunyi sana'oi kala kala suyi wannan suyi wannn saidai da lokaci ya dan karaja Alaji omar ya girma iyayen sa suka rasu, sana'ar da ya dawo yi was unknown ba a Kara gane masa ba.

Kaf makwabta da abokan harka babu wanda ya isa yace yasan takamammen sana'ar alaji omar okene except for d little little business investment wanda basufi cikin cokali ba,gashi a kullum sai habbaka yakeyi,arzikin gobe saiya ci uban na yau haka na jibi he is just flourishing day by day babu kakkautawa,tunda yaje kasar waje ya dawo ya yaxo ya siya wata mahaukaciyar gidan bene mai hawa takwas mutane suka fara saka mai kahon zuka,this man became centr of attraction dan kowa so yake yasan kalar sana'ar da yakeyi wanda ba a gani saidai agansa da miliyoyin kudi yana facaka yadda ransa yake so,hakan yasa ya rinka shiga kwama cala kala kala da yan anguwan su, wasu akan gaskiyar su ne,wasu kuma akan hassada ne da mugun nufi irin na dan adam musamman in yaga dan uwansa yasamu arzikin daya zarce nashi a bugu daya

But none of them eva defeated him,Allah bai taba bada kowa sa'a akan Alaji okene ba dan sau tari akanyi surkulle har kotu an jejje da shi anma ba aci galaba akansa ba.

Duk wani Zato da mummunan baqi babu wanda ba ayi akan dukiyar san Nan ba, wasu sunce blood money ne dama can matsafi ne wasu kuma sunce mugun barawo ne.

Ahaka Anshafi akalla shekaru shida ana kana nan magana ana ta wannan rigungimu daga baya har aka gaji aka kyalesa da dukiyar sa yana kuma yadda yakeso bai fasa ba..
A tsarin sa a duk macen daya gani ta masa kyau to saiya aureta,sannan baya auren mummunan mace,shi asalin zangwadaddiya mai diri da kyaun fuska yake tayawa,shiyasa yakan murqushe naira wa yan mata,ya kuma narka kudade da kayan alatu ma iyayenta har sai ya cimma burinsa na aurota.

Duk dama bawani sabuwar zance bane yawancin
Matan dayake aura basu wuce watanni biyu uku agidan sa suke ficewa,but hakan baiya hana zalamammun yan mata,zaurawa da kwadayayun iyayen su bashi hadin kai wajen kara Wani auren shi kansa ayau bazai iya tantance matan daya aura ya sake ba..
Bayan matsalar sa nacewa ba'asan silar arzikin sa,problem din zaman gidansa shine duk wacce aka kawota a matsayin mata toh tabbas sai ya dawo da ita walkantaciyar baiwa.

Amma ahakan mutane basu taba yadda da wannan maganan sabida ko anyi auren baya dena kashewa
Iyayen matansa kudi da musu alheri,da siyan niqi niqin kayan duniya da kuma mugun girmama su

Out of 100 baifi 2% ne kawai zasu yadda cewa cikin gidansa shi mugun gaske bane sai a wanda ya gani da idonsa dan bakaramin azaba da baqar kunci yake cusa ma matan sa ba

Cikin haka ne Har Allah ya hadashi da suhan yar gidan malam bukar wanda aka fisani da yaa malam,wanda bugu daya ya same shiga wajensa dake dama tsohon dabiar Yaa malam din ne aurar da yayansa domin samun kudi da abun duniya.

Kwata kwata da haduwar su da shirin auren baifi wata biyu
zunzurutun kudi da abinci Alaji okene ya rinka bawa yaa malam kyautansu har ya cimma burinsa na samun yarsa suhan.

Toh a Wajen karban auren tan ne dayazo da Wani abokin sa mai Suna Alaji BATURE dan America, anan shima yaga rufaida yace lallai abasa shima ya aura,yaa malam kuma daya riga yaga kudi idanunsa sun kife sai bai iya ce musu a'a ba.

Yana sane da cewa alkwari yy ma mahaifiyar sa na cewa zai bar yayansa mata kaf su same koda sec cerficate,amma jin ance Alaji BATURE zai iya kufce musu ya koma kasar waje yasa ya turje y bijire yace sam sai anyi auren rufaida da gaggawa.

Shi Alaji BATURE babu wanda yasan asalinsa sai babban abokinsa Alaji okene,ko yanayin arzikin su ma iri daya ne which of course babu wanda yake gane boyayyen sirrin su..

Shima ance yanada mata biyu kuma dukan su yan nigeria ne sabida shi a United state yake da zama shikam ma babu wanda ya taba sanin gidansa,time to time haka business meeting dinsu yake kawosa wajen Alaji okene

Kudi sosai Alaji bature ya narka wajen kwato yardan Yaa malam cikin gaggawa akan auren sa da rufaid
Yace nan da kwana uku yakeso ya tafi america can gidan sa dan haka zaifi kyau ayi biki ya wuce can da sabuwar matarsa rufaida.

Bangaren gidan ya malam*****

Kafun ace wani abu har waje ya washe tasss yan kodon biki duk kowa ya koma gidansa.

Daga cikin gidan ma babu kowa ata daki,Hajiya Mama da umma hadiza ne suka firfito tsakar gidan agigice da rufaida a hannu a hannu dan babu abunda takeyi sai suma..hjy maman ne akanta tanai mata fifita da mayafin ta,Wani uban shessheka rufaida takeja atake numfashin ta saiya dauke,"rufaida?rufai?"Hadeiza maza jeki ki kawo min ruwa..cikin hanzari umman ta miqe ta wuce kitchen ta dawo da modan ruwa a hannu ta miqa ma hjy mama wanda bata yi wata wata ba tahau yayyafa mata a fuska,tafi minti biyar tana hakan da kyar ta sake dan nishi sann suka san ma tana raye,Gaba daya hanklin su baya jikin su kaf idanun su yy jaaa,sun rasa yadda zasuyi Da lamarin
hjy tayi hawaye harta gaji umma hadiza kam bata iya cewa komi sai yawan sauke ajiyan zuciya datakeyi itama,sosai zuciyarta yake mata ciwo da radadi saidai ayanzu bata ma jin kodan ciwon tan damuwar da yarta yakeciki shiyafi komi daga mata hankli .

Ganin rufaida ahaka yasa take tunanin in har aka rabasu gobe hala itakam tasamu silar mutuwarta kenan

A Yau data fi kowa mugunjin radadin zafin rabuwa da yarta suhane da sauran yayanta, da kuma cewa da mijinta yayi ya yafesu ko an sako su har abada kar su dawo masa gida,inta tuna hakan takanji kamar wuta ne yake ci ata cikin jikinta,ga kuma rufaida wacce tasan tabbas ba sauya ra'ayinsa xaiyi akanta ba

Da kyar suka rinka jinyarta harta samu tayi bacci,dukan su jira sukeyi har wajen misalin 1 saura ma dare amma yaa malam bai dawo ba.

Babu yadda umma ta iya haka ta danne nata damuwar ta rinka lallaba hjy mama dan ta samu ta runtsa,da kyar ta cimma hakan dan cewa take baza a daura auren nan ba
zata kira danta zaidu sassafe zaizo ya tsaya mata tunda shi bukar din bai dauketa abakin komi ba..


*****


MAFARI.....
(Tushen su)

Asalin sunan mahaifin rufaida wato yaa malam shine Abubakar Ahmad salahudeen.

ya taso ya kuma girma ne a can wata kauye dake ake kira bazarkowa,a can jahar maiduguri yankin daya hadasu sosai da ynkunan kasar chadi.

mahaifiyarsa hajiya mama wacce asalin sunanta ne Hasiya Abdullahi,ita asalin shuwa arab ce ta uwa ta uba shiyasa a bugu daya kaganta zaka iya ce mata barabiya dan duk Wani siffar su na kyan jiki da kyan tsari tana dashi gashin kanta baki wuluk gata da diri da hasken fata da fararen idanu,gidan su gidan malamai ne dan haka anan ma garin maidugurin ta soma aure,auren wuri irin na al'adan mutanen da wanda tun yarinya tana da shekara 12 itama akayi mata,dake hasiya tataso ne a gidan mutunci hakan yasa ta auri wani babban makiyayin malamin zaure wanda asalin shi ba dan nigeria bane dan kasar eritrea ne Sunan sa Ahamadu salahudeen al'adab ana iya cemasa malami.

Wanda akace Daga kasar sa yy hijra yaje egypt ya kuma je ethiopia da qasar mali da sudan ya koyo karatun qur'ani,zallan karatun Allo na asalin fasalin warash ya kwarance,ahaka ya shafe kusan shekaru ashirin yanayi toh bayan ya gama ne yay hijra ta kasar chad har ya dawo kasar nigeria da zama Inda ya sauka a jahar maiduguri Amma bai shigo asalin cikin gari ba

Anan ma bai zauna ba ya kafa babban makarntar addini na zallan bada ilimin warash,duka Wani sirri da alhidaya dake dauke acikin ayoyin qur'ani ya nemi ilimin sanin su kuma sosai yake iya amfani dasu

Akan haka Ya shahara ya daukaka yay arxikin rufawa kai asiri,mutane daga kasashen da suka sanshi sosai suke zuwa zauren sa neman taimakon sa akan lamarin daya shafe rayuwar su kona lapyar su kona cigaban arzikin su koma akan maqiyansu.

A farko tsakanin sa da Allah yake aikin sa na taimako da ilimantarwa Inda yake amfani da ayoyin Allah ya warkan ya kuma saukaka,amma daga baya sai girman kai da jiji da kai ya bala'in kama zuciyar shi musamman dayaga yadda dumbin mutane suke yaba qarfin ilminshi da kaifin aikin sa,suke daukaka sa ake jin maganan sa ana mugun girmama Inda yasa kafarsa ya taka,sai ya zamto yay kaurin suna da daraja a lokaci guda.

Ana haka a hankli saiya shiga cusa ma almajiran sa ra'ayi wanda baishafe addini da tarbiya ba,ashe a boye yakanyi aiki irin na sihiri ma yan siyasa da masu arzikin kasar nigeria with time har hakan ya fito filli duniya suka San yana hada lamarinsa da aljanu da tsafi duk dama yaki sam ya amince musu cewa gaskiya ne yana hada al amuransa da sihiri

A duk halina duniya babu wanda ya isa yaja da malam Ahamadu a girman kai da son musunta abunda baizo daidai danashi ra'ayin ba.

hakan yasa wasu tsirarrun malamai a maidugurin suka fara kalubalantar sa akan yaji tsoron Allah,inyaji waa'zin saiyayi musu yace kuma hassada ake mishi akan ilimin da Allah ya riga ya bashi..

Gashi Allah ya dora masa girman kan da koyayi bata kuma yasan ya batan bazai taba amincewa ba muddin ace Wani ne yamasa gyaran,a rayuwan sa da lamarin xuciyar sa ya riga ya tsara cewa shi yayi ilimin da ya zarce Wani dan adam galibi yay masa gyara ko shi ya amshe gyaran domin in yy Hakan ji yake kamar an rage masa Wani abu daga kimarsa.

Haka yake rayuwarsa yanajin cewa Shi sarkin ilimi ne da kima da daraja,hakan ya jawo wasu almajiran sa suka bijirre masa saidai mafi yawansun sunan tare dashi.

Sosai yake adawa da sauran malaman addini da suke gaya masa gaskiya,saiya juya abun yace ai sudin kafurai ne, turawa ne duk suka batasu,daga haka ya fara cusa ma mabiyansa ra'ayin kin neman ilimin kimiyyya da fasaha,ya kuma ce musu wannan ilimin shi zai batar dasu zai rabasu da Allah .

Shekaran sa uku da auren hasiya(hjy mamah) suka haihu suka haifi dansu mai suna Abbakar
Wanda akafi sani da
yaa malam..

Yaah malam shine babban dansu kwalli daya wanda ya gado ubansa sosai tako ta ina da kamanni da komi,asalin akan harkan gardancin mahaifinsa ya rainesa,ya girma ya zamto cikakke kuma rikakken gardi wanda baisan komi game da duniya ba sai karatun qur'ani da aka rainosa dashi.


yaa malam yana da shekara biyar babansan yazo ya rasu,bayan nan da kyar ma mahaifiyar sa hasiyar (hjiy mama) ta rabasa da kauyen da suke sukazo cikin gari ahakan ma wata da watanni yyi yana fushi da dacin rai da ita, baya cin abincinta waidan ta rabasa da gidan gadon ubansa ta kawosa cikin gari cikin arna.

Duk da hakan Rayuwar gardancin sa yakeyi abunsa,duk Wani abu dazai hadasa da neman ilimi irinna bature to ya tsaneshi,Wani bin har aga kamar yafi karfin mahaifiyar san ne.
Saidai kuma hjy Hasiyar asalin ta mai raki ce duk tsiyarsa haka yake dawowa dan dolensa ya mata biyayya dan sosai yake kaunarta aransa.


A xamanta dashi Babu yadda batayi dashi yay koda primary school ba amma haka yaki sam,inma ta damesa saiya fara mata barazanar cewa zai barta zaije kawai ya shiga uwa duniya yay rayuwar sa yadda yake so,itakuwa intaji ya furta hakan saita hqra kawai ta kyaleshi shiyasa ma tun yana yaron ya barke da gararin gari yana sana'an rimi da koyarwa har yayita kokri dan ya tara almajiran sa..

When he reached 7 kafin nan hjy mama tayi Wani auren ta auri Wani babban mutum dan asalin garin katsinan dikko mai kudin gaske anace dashi Alhji dikko matazu.

Shi Matarsa ce ta rasu saiya auri hajya mamah,toh Tunda ya auretan suka bar maiduguri suka koma zama a babban gidan sa dake garin kano.

shima babu yadda baiyi da yaa malam akan yaje makaranta yy karatu ba amma haka yakimusu fir, karshen ta ma guje musu yayi agidan ya nemi gidan haya ata bayan gari yana rayuwar gardancin sa,akan haka saida yasha wahala matuka kafun ya saba da mutanen anguwa,sabida shi yarone amma jahili ne mai tsananin girman kai da nuna isa,hjy mama itake ci dashi ta shayar dashi but shi jahilin mutum daga anmasa gyara ko fada sai yace an masa gori..

Wani bin ya gwammaci ya kwana da baqar yunwa da amasa gyara,saiya zamto Zaman haquri kawai kowa yakeyi da yaa malam musamman ma mijin mahaifiyarsan wato alhaj dikko matazu wanda bakasafai ma yake girmama shi ba.

Ana haka ko shekara basuyi da dawowarsu kano ba Hjiy hasiya ta haifi kaninshi aka samasa Suna Zaid dikko matazu,an haife zaid da shekara bakwai a duniya shima mahaifin nasa alhj dikko ya rasu,cikin ikon Allah haka zayd din ya girma yayi ilimi ya kuma gaji dukiya mai tarin yawa irin na ubansa,sai ya dawo shahararren babban hamshakin dan kasuwa a garin kano,kuma yyi karatu sosai ya zamto babban lawya a fannin shariar musulunci kaf garin ana kiransa da suna YAA SHEIKH sabida tsabar kwarencewar sa wajen iya aiki da ilimin da Allah ya basa.

"Toh kasancewar su yan uba da yaa Malam sai basu cika wani shiri sosai ba,dake tun yana dan karami a kullum yaa malam yazo gidan yagansa da uniform din boko yakance masa .. "kai tafican ARNE kawai"..shikuwa kalman matukar haushi yake basa,Shekara goma ne a tsakanin su amma hakan bai hana su kaurewa wajen cece kuce musamman inya furta ma zayd din hakan ba.

sai dai duk batawar da zasuyi a tsakanin su bada dadewa zakaga sun shirya domin kuwa akwai wannan soyayyar jinin dake cikin xuciyar su wanda hjy mamar ce take dada karfafawa Duk dama Sun kasance mutane biyu ne masu mabanbatan ra'ayi game da rayuwa.

As time goes on zayd sai yayi qarfin ilimi da arxiki shikuma yaa malam ya tara almajirai yana koyar dasu
Da haka ya sanu yasamu mabiya dayawa har yyi gidan kansa ata bayan gari.

Tun yana da shekara sha bakwai yayi aure matar sa na farko mai suna Tani bata iya jure halayen sa ba tafice dan ko haihuwa batayi agidan sa ba

Bai daddara ba ya auro wata bazaura mai suna Shafa'atu itace ta haifa masa yarsa ta farko wato murja..
Itakam baqar azaban yunwa ne ya fiddata.

Sai ya auro wata dillaliya anace mata gambo,itama tazo ta haifar masa ya mace mai suna ruqayya da bori da hauka itama ta fice a gidansa

Can sannan ya auro hadeiza wacce tsabar haqurin iya zama dashi datakeyi yasa mutane suke ganin kamar ma itace ya auro a farko
Hadieza marainiyar Allah ce ba uwa ba uba tsohuwar data raineta ne ta bada ita aure wa yaa malam sakamakon maganin daya mata na ciwon zuciya wanda bata da kudin biyanshi saita biyashi da auren yar rikonta kwalli daya hadieza..

Hakan yasa bai taba daraja Matarsa hadiza ba,gani yake
Kamar sadaqa aka bashi ita,shiyasa tunda ta auresa bata tabajin dadin rayuwarta a hannun sa ba,wulkancin yau daban na gobe da daban harta haifa masa yaya uku,wato Jadwa,suhan da yar autarsu rufaida.

A fadi tashi da kame kame suke tafiyar da rayuwar su,tsakanin ta da Allah ta rike yayan kishiyoyin ta Duk dama basu taba gode mata ba.

Yaa malam haka yaki sam yabar dan uwansan yaa sheik ya taimake sa koda da sana'a ne sabida wannan tsinannen girman kan jahilcin jin cewa fa shine ma agabansa a shekaru.

A Kullum cikin ikirari yake na cewa zai iya rayuwar sa kuma baya bukatr taimakon kowa bare azo anamasa gori.

Har suka girma sosai suka manyanta hankli ya dan daidaita kansu ba kamar da can ba
Ayanzu dai kowa nayin rayuwar sa ne ayadda halayen sa suke bi dashi.

Tsananin Girman kai yasa Yaa malam yyi ta wahalar gina rayuwar sa acikin baqar talauci.

shiyasa da yayansa mata suka girma sai kawai ya fara aurar dasu ga masu kudi yana caskar kudin abunshi,dama can Shida iyalansan suna zama ne a kaskantacen anguwa dan shi bayason hada kafa da masu ilimin boko ya tsane su har ransa baison muamala dasu,kawai ya bar yayan san suyi karatu ne sabida bin umarnin uwar san duk da hakama dakyar suke wuce secndry schull maza saiya kawo namiji yace ya badasu



Shikuma Yaa sheik sanda ya kammala service dinsa ya auri matar sa hajiya jasmine khalid matori,ita yar gidan wani tsohon govenor ne tana da kaninta kwalli daya wanda akece masa IMAD,...tunda mahaifin ta ya rasu yaa sheik yake kyaywar dawainiya da dukan lamuran mahaifiyarta mai suna Hajiya saddika fulani

Hakan yasa suke matukar son junan su, suna gudanar da rayuwarsu ne cikin tsananin girmama juna da baiwa iyayen su haqqin su sosai..

Yadda mijinta zayd yake qirmama mahaifiyarta haka Itama take mugun girmama nashi mahaifiyar...

Shiyasa a Duk yadda hajya mama taso ta raba muhallin ta dasu hakan baiyuba saboda hjya jasmine taki sam haryau su rabu kuma suna zaman su atare cikin lumana da kwanciyar hanklu

Hjy jasmine Bata wani dade da auren zayd ba ta haifar masa yaya har guda biyar,..

Babban yarta mace wanda tayi karatun law a kasar london anace mata barister FAREESAH zayd matazu ko anty reesa,sai babban dansu namiji capt MUFRAD zayd matazu shikuma navy aka turasa a kasar south korea,Inda ya fito da babban matsayin sa na captain ana yawan cemai capt. muffy,..sai mabiyinsa mai suna KEEYAN zayd matazu ana yawan ce masa maska cos he is an enginering student in saudi arabian petroleum engineering stands.

Sai kuma NAZLI zayd matazu
Ita kuma medical student ce tana 2nd year dinta a medical school in india

daga ita sai yar autarsu SHUKRA(khadija zayd matazu) dake karanta fannin international law anan university of nigeria nsukka.

sunada eldest step sis wacce ake cewa Anty Anu,ita kuma asalin sunanta laila zayd matazu,saidai ita ba yar sunna bace,qaddara ya fada wa yaa sheik aka sameta,so her mum is from sokoto state, who uses magic to seduce zayd matazu dan ta cika Wani burinta na rabashi da matarsa jasmine tun farkon auren su amma bataci nasara akansa ba,ta haifi Anu and then she died immidietly batare da auren san akanta ba,,

So a hannun iyayen mahaifiyarr Anu ta girma,Anu kusan sa'ar Anty fareesa ne, dake ma ita ba yar sunna bace so bata cika son zama da su ba hutu kawai take xuwa shima da kkyar in su hajya mama sun tursasa ta

..hakan yasa kusan rabin yan uwanta basa kaunarta thy dont like her much to be around them musamman ma nazli da shukra wayanda sukadau kishi da tsanar duniya suka daura mata..

..tsawon lokaci rayuwar su a hakan yake tafiya yau shiri shiri gobe a araba gari,evn thou iyayen su basu taba nuna bambamci akan yayan su ba .

At times Anu takanzo gidan ne kawai dan hjy jasmine da kuma kakarsu hajya mama amma badon tahada kai da yan uwantan ba

She actually prefer to live her life respectfully gudun kar wata rana a cakka mata baqar magana ko ace mata shegiya..

Anty fareesa kuwa yar ba ruwanta ne last 5years tayi aure daga aikinta sai biyayya wa iyayenta kuma ita kowa nata ne batajin ko daukar gulma,kowa na bata respect cos tana da dattako da halin manya not long ta haifi yaranta biyu wato Iman da,jawad.

shikuma capt muffy shine ake daukar sa kamar magajin baban su zayd matazu,every body loves him sabida halayensa da suka matukar banbanta dana kowa,shi Wani irin murdaden mutum ne,just last year ya daure ya auro wata office girl ana cemata Aina'u Abbakar makarfi,wanda ake cewa Ayn makarfi.
So Keeyan is just a friendly normal guy shidai baya iya fada da kowa Kuma ta Wani fannin Suna masifafiyar kama da yayan sa mufrad

Nazli kuwa yar high standard of living ce tana da mugun ji da kanta duk dama ilimin addini ya shigeta sosai so tana dan sa tunani aharkan rayuwarta badai jijii da kaina jahilci ba,she is high temperd and sumtimes very vulnerable tanada saurin karaya.

"Shukra?she is worst of all she hate evryone nd suspect evryone kullum

Please Login or Register in order to submit comment