Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

you at?ta cikin wayar aka ce masa
"Gwarimpa",daga jin haka ya sauke wayar a kunnen sa ya datse kirar,ya juyo da mamakin ganin wai har yanzu ainau tana tsaye,dan karamin smirk yay sannan ya sauke ajiyan zuciya,da yayi niyyar cewa wani abu amma harga Allah yasan bazai taba iyawa ba..he think he is too matured for this mema zai gaya mata,a dokar sa baiya bawa mace hakuri alokacin datake hargagin raini da fushi.Beside shi baiga ma abunda yakeyi wa ainau data zafafa batun ba,inde dan haqqinta ne yaji ai zai gyara,amma ko da wasan wasa bazai dauke raini da cin fuska ba,yana gama ayyana hakn aransa Ya wani hade ransa tamkar bai taba murmushi a rayywar sa,tahowa yy zai wuce ya nifi kofar, ainau ta rufe idanunta cikin sauri tayi tsam ji tayi kafafunta sun kasa daukarta, jiri ne ma yake na neman wainato kasa, dan tamkr ta fasa ihu ta yanke jiki ta suma dan baqin ciki haka ta dinga ji a cikin zuciyarta.

Kiris take jira ya fita baice mata uffan din ba kuwa da wallhy saita nuna masa asalin wacece ita.

Yana rike handle din kofar kamar wanda ya tuno da wani abu ya juyo ya kalleta.
A hnkli Yace,can u put urself together and stop being over reactive?,nifa bangane abunda kike nufi ba,look im tired of u okay?,tafiyar danayi aiki nake tyi ban ma huta ba,im sick of u being childish Aynau,pls maganan nan Ya kare daga nan,daga kinfita ki rufemin kofa nizan wuce wani waje..
"U got me?yatsar dayake reto ta kalla sann ta sunkuyar da kanta can kasa

Muryanta na fitar da amo marar dadinji, sai dai babu wani mummunan kalami dayaso fitowa a bakinta,yanayin kallon datake masa zaka fahimce cewa taji ciwon kalaman sa har kasan zuciyarta ahaka tana ji tanagani yasaka kai yay waje..

Rasa yadda zatayi taji tayi banda dan uban karkrwan da jikinta yakeyi tsaban bacin rai,a haukatacen yanayi ta fito fuuuu cikin sauri ta bude kofar dakinta fado a dakin bata tsaya jiran komi ba tawuce wajen scroll direct ta bude ta hau tattara kayan sakawarta tana jibgasu akan gadon ta,babban akwatin dake sama ta fitar ta bude ta hau dura kayan da sauri cikin tsananin fushi kamar da su take fadar,sanda ta gama shiryawa tsaf snnan ta shiga rabza kuka gaba daya ta rasa yadda akayi ta lalace har haka,saken datayi wa mufrad yayi yawa,harga Allah bazata iya cigaba da jumre halayyr sa ba saidai in son datake masan yayi ajalinta amma dole ne ta kwato kima da mutunci awajen sa wanda take saka ran baisan dashi ba.

Bangaren zarah kuwa tun fitar Ainau bata iya tsinana komi ba ta koma bakin gadonta ta zauna game da sauke wasu gajiyayyun numfashi mai tafe da sautin makurar kasalar dake tattare da gabobin jikinta.

tana zama a bakin gadon ta rafka uban tagumi dagata cikin kwakwalta ta hau yin lissafe lissafen abubuwan da suke gabanta da wanda zata aikata nan gaba,tuno da yau tun farkawar su da asuba bata samu duwawun zama ba suka nausa kauyen barass wajen malamin zeee zee datayi mata alkwarin zata kaita ajiya in suka kwama tare,a iya wahala kam yau taganshi ta kuma jigatu a hannun kowanne. Su dan banda azabar kwana da jarabar cin da xee tayi ta mata harda yar bulalar da malam yasaka aljanunsa suka rinka shauda mata wanda tuno da fuskar su kadai datayi yanzu sanda tsigar jikinta ya tashi jikinta yahau rawa,gashi nan dai malami ne har malami,zaka gansa tsaf da yar dattijuwar rawanin sa,ga wani nitsatsen fuskar kamala irinta manyar hafizai daya aro amma kuma hmm har iya yau dai bazata iya cewa ta taba arangama da baqin arne irinsa ba.
Dan Daga isarsu wajen sa yahau labarta mata komi dake nanike a kasar zuciyarta harda yaudarar ainau datake yi arayuwarta musamman indata amshi kudade wanda wani boka ko malami bai taba zamowa soo current kamar wannan malami ba,dan a yadda yake tsilalo bayanin rayuwarta in details game karamin kwakwla zaka iya cewa babu shakka shiya rubuta littafin rayuwarta.
"Yace ma zarah tabbas zatayi nasara kan batun imad kuma qaddarar ta bazai taba zamowa irnna yar uwanta ainau ba,takuwa ji dadin hakan sosai,duk dama ya kukkushe karfin tauraron nasararta, yace mata batada farinjini da sa'a dole ne saita bi sharudan sa da dukan imaninta,nan ma bata damu ba dan bashine ya soma furta mata hakan akaro na farko ba ta sha jin hakan abakin sauran bokaye..

Saidai fa da alamu malamin baras din nan shi nadaban ne koda daga yanayin yadda taga zee tana mugun tsoron sa tana kafafa dashi tana dabbaka sa komi yace bata musawa tasan sun iso gaban makura

Tun akan hanyar isowar su zee take ce mata ta nitsu dan alfarman ta kawai zataci,ta bata labarin yadda takeyin zaman jiran wata biyu kafin layin samun ganin sa yake zuwa kanta yanzu hakama abunda ya kawota abujan kenan.
Zee ta saba da malam amma itakanta bata cikin samun karfin zuwa wajen sa sai intayi babban kamu dan akwaishi da cazar kudi

Sharudan daya gindaya ma zarahn ba wasu masu sauki bane,awajenta ma gani taje yay mata mugun tsauri halama bazai yuwa ba amma ahaka ta amince dan dolenta tace zatayi ya kuma jadadda mata cewa ta guji abunda zai iya zuwa ya dawo.

Kudin yanka da magani da kamun zuciya dayace zai mata a lissafi saida yaci million hudu wanda karshenta zee dinne ta biya mata a matsayin bashi,wanda Ayanzu shikadaine zaisa ta nemi komawa site din ainau amma badon haka ba da sai dai ainau taga anayi dan mamaki tayi niyar shayar da ita bana wasa ba,yau data zo taga alamar samun nasara akan imad, duk wani tsoronta saiya kawar..

Tana cikin wannan tunanin saiga karar bude kofa tana daga ido taga ainau na kkrin shigowa da akwatuna har biyu,
Kirijnta na bugu ta mike tsaye"me hakan yake nufi,ta dafe goshi cikin takaici karde taje tayi masa rainin dayasa ya saketa ohh god Ainau is just a mess.

Ain tana aje akwatin tace zarah ni zan wuce...pls dont tel anyone dat u knw my where abouts kawai kice musu baki ganni ba kibarsa shi yaji dasu

Cike da kullewar kai
Zara tace ban fahimceki ba what happen inazaki
No no pls indan abunda nayi ne kizauna abunki wallhy zan bar maki gidanki

Hawaye akan sauka akan fuskar ainau,tace is not about dat zarah..da
Kizauna da karki zauna duk bata shafeni ba nide kawai xan tafi nabarshi.Mufrd ya rabani da komi nawa,ya rabani da kaina ya maidani wata kaskantacciya,ke ban cika miki burinki ba nima nawa bai cika ba gara ni na hakura kawai,bazan iyaba walakancin sa kullum daduwa yake is asif dukan abunda mukeyi akan sa warware wa yake zarah nasha mamakin yadda kika rufe idanunki baki kallon baqar azabar danake kurba agidan mijina. mufrad now treats me like a trash,he had the guts..da hakane kike son aure irin nawa,auren wanda baisan da abunda kakeji aranka ba?i tried so hard,maiye mace takeyi wa namiji wanda banyi masa ba,and i still mean nothing to him Wannan rayuwa ce?
I can feel it,zarah i can smell from far dat banada wani kyakwan matsayi a zuciyar mufrad.

He dont even care About my feelings kamar ni ba komi bace haka ya daukeni im starting to regret this marriage wallhy na rasa yadda zanyi na ficceki shi araina ne da tuni na qona soyayyarsa da wuta yayi qurmus kodan na huta ma raina.

Kuka sosai ainau ta fashe dashi

Shiru zarah tayi tsaban yadda jikinta ya dau wani mugun sanyi,gaba daya sai taji tayi lagwas tana jin sautin kukan yar uwanta dake kokrin sosa mata zuciyarta matuka,bata iya motsi ba har sanda Ainau ta juya zata fice a dakin cikin sauri ta kamo hannunta tajata suka zauna abakinan gadon ta hau rarrashinta,duk da son zuciyar irina zarah harga Allah saida taji tsananin takaicin yanayin yadda dataga ainau tana kuka cikin axaban damuwa ,da kyar ta lallabeta tayi bacci,tana ta lallbarta cikin bata baki tamkar kamar basu suka gama fada da juna ba,gefe da ainau tazauna cikin sauke wata nannuyan ajiyan zuciya,arayuwa ita mace ce mai son kashe tsuntsu biyu da dutsi daya,take brain dinta ya hau bata cewa lamarin a'inau baya bukatar wani boka ko maganin mata ayanzu, she must find away to involve imad tasan in harshi ya fahimce ta dole ne sukaga canji ta wajen captain,saidai ita ba sulhunta su take so ayi kai tsaye ba,she just want to blackmail mufrad into seeing things.

Agefe kuma so take taga karfin ikon aikin da akayi mata akan imad Shin izuwa wani xtent zata iya langwasa shi?dan malam yace mata dole sai ta dage akansa sabida yana da yawan sonyin ibada musammn sallah da zhakr,daga nan wanka ta fada zuciyarta cike da tunanin yadda zata tunkare abun


Bangaren mufrad kuwa tun daya fice agidan bai kara dawowa ba Imad yana dakinsa yana bacci yaji an jijjigo shi da sauri ya bude idanun sa Sai ganin zarah yay ta wani sha uban ado tana zuba wani maitan qamshin turaren ta kuma kuresa da wani irin wagaggen murmushi wanda tabbas da a cikin hayyacin sa yake dasai yay iritating dinsa,mikewa zaune yay cikin ja da baya kadan aransa yana mamakinta jin qamshin turaren aljanu dayaji dazu yana bacci tukunnama wai yaushe ne har suka soma wasar shigowa har dakin bacci da wannan yarinyar?yasan dai ko da wasan wasa abun nasu baiyi nisa har haka ba,iyaka ayi hira a falo aje yawo kadan asha drinks a pub adawo,sai dai ayanzu baisan meyafaru dashi daya somajin normal da itaba, just today ya soma ji kamar dama tuntuni yasanta,yawan haushinta dayake ji aransa ma sai yaji kamar ankawar.

Zama tayi gefen sa tana murmushi kamar wata mayyar datake shirin cinyesa Tace,hey bby Yaufa Zuwa nayi muyi hira jiya bakaganni bako?
Tokaidin ina kaje baka fadamin ba
Ya rasa ma mezaice mata,ya dan dafe kansa cikin sakaltacen yanayi yy kamar baiji metace ba can yahau magana kamar dakansa kawai yakeyi yace,dnt knw wts wrong with me sai bacci naketa yi
"Mufrad fa..?kafadun ta ta dage tace Uh i don't know
Tsaki ne ya kufce mai ya dau wayarsa batace masa uffan ba harsanda ya kira layinsa ringing daya xuwa biyu raga wai har an dauka
"Kai ya haka kana ina?daga ta dayan bangaren mufrad yace im in urgent meeting zan kiraka pls,bai ce komi ya ya katse wayar tare da maida kansa jikin gadon yana mai lumshe idanunsa ahankli
"He knws we are supposed to go out now,jiranshi fa nake amma wai harya fita,..zarah tace hmmhmmm,sai kuma tayi tsuru tsuru tana bin rufaffen idanunsa da kallo kamar wata kamilar asali, dacan batayi niyyar amsa shi bama amma hakan tamkar wani hanya aka bude mata wajen shigar da wasarta zuciyar sa game da Lamarin ainau,cikin wani makirtaccen salo ta nitsar da muryan ta kamar wata mutuniyar kirki,a nitse sosai cikin yangataccen sautin murya tace masa"..toh kayi hquri mana,captain will alwys remain captain,kasan hakan fa halinsa yake..dakai da ainau bansan meyasa kuka kasa fahimtar sa ba,im sorry but His work is actually his core priority bai cika daukar zafi akan rayuwar kowa ba...i dont know,but i think is not fair..sai tayi kamar zata futta wani kalma agaba but data kalle shi taga kamar jintan yakeyi dagske sai kuma tayi shiruu shima shirun yy yana lura da ita,cos actually bama jin ta yakeyi har can can din ba,gani yake kamar basu fahimce mufrad dinsa bane shiyasa suke judging dinsa akan haka,but yanayin yadda yaga ta karashe magananta very dramatic yasan akwai sauran bayanai boye abakin ta, as a very good observant sosai ya fahimce wani abu ya auku yau,dan tun daga language din fuskarta ta ya soma dagowa,yanata jira yaji ta hau barbada masa zance kamar yadda ta saba zuba masa saiyaga kuma tayi shiru shikuma yasan bazai iya tambyarta dan yaji abu a matsayin gulma ba bayama son ya soma wannan wasar da ita,gyara zaman shi yy ahankli yace.."Look don't say it like dat okay,muff is actually a great and a very very veryyyyy caring person.

Harda dafe kirjinta ta gwalo ido waje Tace carring ke?tab di..i knw he is great amma Caring fa kace?U sure ure not getting it twisted?
Anywys..dama sallama kawai nazo nayi maka inaga kamar yau zamu wuce kano gashi ko lambar wayarka baka bani ba so saiyaushe kenan zamuga juna...?

Tunanin abunda tace Bai iya barinshi ya amsata cikin sauri ba,sai ga ta harta matso kusa daf dashi cikin wani irin kisinniyar salo tanai masa kwarkwasa da ido cikin salon yauqi sosai,tamkar zata goge fuskar shi haka ta hankado ta karkarya sautin muryanta akan fuskan shi...
"mad,baby i will like to see you again dan Allah.Zanyi farin cikin in kawance mu ya zarce sanayya,i hope u knw ure speacial to me?

kirjinshi yaji ta amsa da bugu data frta mai hakan dan
Kwata kwata bai gane mata ba,saurin kwace jikinshi kusa da ita yyi ya dire kasa daga kan gadon ya tsaya daga tsaye,tun kan ya gyara tsayuwar sa ta kara darsa masa yan iskan idanunta tanai ma siffar jikinsa wani irin jarabben kallo"..hannun sa ya cusa duka a aljihun wandonsa dan baiya bukatr ta gane halin dayake ciki,he is seriously panting from d inside out of fear and confusion saiyanaji kamar ba shi bane,ga wani uban bugun zuciya data dameshi matuka..yace
"Ina zakije..i mean keda waye?Saida tadn ja sann ta miqe tsaye tana duban sa da kyau.Tayi mirmushi ayangace
Tace,forget it..in baka ganni ba kawai kasan tafiya mukayi,so Zaka ban numbar taka ce koko bankai wannan matsayin ba,baice mata uffan ba ya amshi wayarta ya rubuta mata 11 digits mtn line, a very special number duka five ne karshen sa zero guda biyu, altho itakam ta dade da haddacewa amma bai hanata nuna masa jin dadinta ba.

Mayar mata wayar yay akan ta saka suna da kanta Batayi kasa a giwa ba ta amsa ta narka masa flashing
Da sauri ya nufi wayarsa dake kan gado ya dauka duk tunaninsa mufrad ne,daf yana shirin dagawa sai ta katse
Ya juyo ya kalleta adaidai lokcin ta kashe mai ido tace.."Dats my number.. dan dage girarsa yy Yace ohhh..To wani suna zan saka maka,hnklin sa nakan wayar yace "imad'..tace no no,suna mai dadi nakeso zan saka maka anawa wayar
Nima ya kamata ka samin special name pleasee,sai anan ya dago ya dan kalleta ahankli sai yace ok sai yay saving number nata da letter "Z" kawai
Kamar ta sani kuwa ta kwace wayar a hannun sa ba zata,tana ganin abun dayayi ta bata ranta tahau bubbuga mai kafa aksa I dont want this name baby dan Allah ka zanca..adan daburce da mamkinta yace what for?idanun nata dayasha kwallin sihiri ta kara darsawa acikin nasa babu shiri yace ohh ohk wateva kisaka dakanki kawai murmushi tayi dan har ranta tanajin shaukin farincinki mai tafiyarwa ko ayanzu tasan tabbas malam yay mata aiki akan imad dan itakanta tasan imad bai san meyakeyi sosai ba.

Da capital letter ta hau rubuta suna agaban lambarta tayi masa saving da "Loml' da emojin heart agaban sunan,data gama saita nuna masa baice uffan ba yadan kyabe baki,"..
Yana amsar wayar tace To ni zan wuce
Yace Keda waye zaku tafi?tace dani da sister..u know i don't want to interfer but my sister just came in dazun nan tana ta kuka tace min kawai na shirya wai gida zamu je,cike da mamaki Imad yace what?kukan me wani abu ya faru a gidan naku shine bazaku sanar da kowa ba..bakinta ta tabe cikin salon shashantar da zancen tace a'a bbu abunda ya faru,but i think all is not well tsakaninta da captain shine kawai..actually tace ma kar na fadawa kowa zamu tafi,sabida in samu lambar wayan da zamuna gaisawa da kai yasa nace dole nazo nayi maka sallama.Maybe in sun shirya ayn zata dawo amma nikam inaga rabuwar mu anan kenan,yar dariya yay sann yace meyayi zafi haka harda wani rabuwa?whats going on u sound really ridiculous pls clear up..

Cikin salon jan aji ta sauke ajiyar zuciya
Tace okay,but hey wannan siirrine tsakani dakai,bai amsa mata ba yace go'on,kamar da wasa ta nemi waje bakin gadonsa ta zauna,"..within some spec of 10 minutes har tagama watso masa kanun labarai.

As usual Duk sauran abubuwanda tace akan muffy bai wani shigesa har can can ba but He was soo shocked to hear dat wai har Ainau ta tattara kayanta zata bar gidan batare da sannin muffyn ba..

He tried his best danya fahimtar da zarah,but no hnkkinta ma baiya kan bayanan sa,cos dats not her mission dama can zuwa tayi ta baqanta mufrad a idon sa da sauran yan uwansa,she was strongly going againts d fact dat ai yana dannewa yar uwanta haqqinta na aure,sai nanata maganan take tana karawa da cewa yana walakanta ainau sosai wasu kalamn nata ya tsaya ma imad aransa fiye da yadda tayi zato.

"Can u imagine ace mijinta ya dau wata guda wajen aiki bai sanar da ita ba,ya dawo kuma yahau ta da masifa waidan ta fito da nity,no explanations no apologies gaskiya haka ba daidai bane..

..akan wannan batun babu abunda bata gayama imad akan yadda mata sukeji in akayi sex starving dinsu ba,har saida ta cimma burinta wajen convincing dinsa, ya somaji aransa kamar yes tanan fannin kam mufrad dinsa bai kyautawa.

Hade da rokonsa data dingayi akan karya fadawa kowa maganan yasashi karajin tausayin Ainau aransa,tace pls baby dont tell anyone abot this She wil get upset with me"..kasan halin Ainau she alwys wanna keep her things private konima bazanso ace kowa agidan nan Yagane cewa batajin dadin zama da mijinta ba..ahaka ya amince mata but
...he got no choice face ya roketa alfarma shima,yace tadan bashi kwana biyu zai gwada tunkarar matsalar dakansa takuma masa alkwarin zata langwasa Ainau ta janye kudirinta na tafiya ta bashi time taga mai zai faru nan da kwana biyu
..and he asurred her da komi zaizo karshe...xarah taji mugun dadin wannan game din data buga duk dama bata nuna masa komi ba har suka rabu.

Ranar kasa samun nitsuwa yay,duk dama ya lura da zarah,har aka fito cikin family membrs yin gaisuwa bata nuna alamun komi agaban kowa ba,ganin harda ainau wajen da suka sauka yin breakfast
Yasa imad yay tsammanin hala zarah ce tayi convincing dinta

Normal aka kare break kowa ya shirya ya fita aka bar hjya adada da hjy goggo wacce acike famm take da fushi da komi na gidan,gani take kmr duk karya kawai ake mata tin tunin nan zaidu yana kano bawani tafiyar dayay,hala uwarsa hasiyace kawai ta rabasa dasu.

Yau zarah bata damu da ficewar da imad yay ba dan dakyar ma tayi convincing din Ainau suka bar gidn sukaje Har office tare dan tasa anan ne kawai a zasuyi maganan su a nitse basai wani yajiyo su ba.





*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


Part1:chapter 40


Kano state nigeria.


Dagata dayan bangaren kuwa sosai abubuwa suka dan daidaitu wa hajya mama dan bakaramin kokori Anty fareesa takeyi akan damuwan dake addabar familynsun ba.

kusan kowani sati saita kawo wa hajya mama ziyara sau uku ko fiye da haka wani binma a wajenta sukeyin weekend tare da y'ay'anta harda mijinta,haka zasu kwana suna debe ma tsohuwar kewa kwana biyun nan ma su suke ciyar da hjyr dan tuni ta sallame maman Abdul datake mata aiki badon halyyarta na son abun duniya ba saidai dan hakan yana daga cikin sabuwar tsarin datake so ta shimfida a rayuwar Ahalinta,aganinta saken da sukeyi akan tarbiyan yayan su shiyake jawowa suke shiga wasu irin matsaloli.

Dakema mijin anty reesan baya da matsalar ra'ayi ko tsanani cikin kwanciyar hnkli suke gudanar da shawarwari tsakanin su,he is just a simple cool human being daya balain sanin ciwon kanshi,rayuwarsa sam babu hayaniya
Wani bin in suna hirarsu ta rayuwa tare da hajiya bazaka taba yarda cewa shi kabilar yoruba bane dan acan ile ifen ma yataso,iyayen sa kuma haryau suna da zama a cikin garin ibadan asalin wayayyun mutane ne ma bota karamci dan haka ita bataci karo da wani marital challenge mai tsauri ba.

Jajircewan anty reesa da mijinta akan batunsu rufaida da umma kawai ya isa ya kara
Ma wani dan adam din imani da karfin gwiwa wajen son taimakon su.

Abinci,magani sutura duk suna aikowa Saidai fa har yau basa da ikon isaga rufaidar ido da ido sai dai subayar a matsayin sako, sakon ma basu isa su bayyana kansu ba tukuna,ko umma ma yanzu ba'a samun ganinta badon komi ba sai dan tsananin saka ido da dora mummunan kahun xuka da yaa malam ya tsiro mata dashi.
Gaba daya ya hanata sakat wani bin har dukanta yakeyi in ta matsa masa akan batun su rufaida,Daga karshe sai yace duk sanda ta kara taka kafarta a gidan yakumbo da sunan duba wata rufaida bai yafe mata ba har abadan Abada.

Sosai hakan ya muzgunawa wa rayuwar umma musamman ma ayanzu da ake yawan tsangamar yarta,tasan dole ne rufaida ta bukace ta a kusa kodan ta rinka kwantar mata da hankli,da batun suhan dayake ci mata tuwo a kwarya,haryau itama yaa malam bai amshe ta ba,zama kawai take agidan mijinta amma bada auren sa akanta sabida tuni alhj okene ya aiko da sakon cewa ya sakesu har yau kuma bai bayyana agarin kano ba,wasu daga cikin matansa har sun gaji sun kama gaban su,aka bar suhan itakadai da uwar gidan sa saratu acikin agidan suna zaman dindin dan suhan ko ta fito batada wajen zuwa doka ne bata isa ta dawo gaban yaa malam ba,da axaba da dadi take zaune cikin tulin yayan Alhaj okene wanda akalla baza'a iya tantace yawansu ba tsabar yawan aure auren dayayi, wasu matansan ma da gatse suke dawowa da yaran su jibga su agidan agaban uwargidan sa hajya saratu,sai suce tunda ubansu ya gudu suma bazasu iya ciyarda su ba,hajiy saratu ita ta dau ragamar komi sauran qaddori da ababen daya rage duk ita ta handame ta siyar, daga anyi magana saita tuma tace anbarta da tulin y'ay'a dole ne ta sissiyar da abubuwan da suka rage ta ciyardasu.

A Cikin tsananin matsatsin tsangawama suhan take rayuwarta, hjy saratu bata kulata bareta sammata abinci,banda baqin cikin azaban fadace fadace da baqaqen maganganu da kishiyoyinta suka rinka jibgawa akanta suna kuma yawo da sunan ta kwarokwaro babu abunda take kwasa,
Kowa gani yake laifin ta ne tunda yar uwanta rufaida ce silar jawo musu duk jarabawar rayuwa da suka fada ciki,baqar maganan safe daban na rana daban suhan bata isa ta wuce a hanya ba..duk wayannan abubuwan da suke faruwa su sukasa ta bala'in tsanar yar uwanta rufaida.

Daga cikin sauran yan uwanta wata rana haka sukan nemi suji labarin halinda rufaidar take ciki amma suhan kam pure hatred ne a zuciyrta game da rufaida ayanzu,kuma abun kullum daduwa yake.
A kullum cikin kai kuka wa Allah umma take kwana tana tsayuwar dare tana azumi tanakai kokon baranta can sama game da lamarin dukan yayanta.

Duk da karfin yaqininta game da samun saukakawa da taimkon ubangiji ata wani bangaren zuciyarta kuma sai tanaji kamar tana cikin tsananin bukatar taimakon su hajya mama akan lamarin rufaida,kullum cikin mamakin dauke kafarsu take ta rasa meyay zafi shi ba wuta ba da zasu wanke hannunsu duk dama tasan laifinsu ne kacokam amma batayi tsammanin kowa zai jingine lamarin su ba,ko ina yaa sheik yake oho?tasan dai da wuya ace su dau tsawon lokaci haka basu so asasanta kan familyn su ba saidai in akwai wata boyayyir matsala, tasan yaa sheik shikadai ma bazai taba kyale faruwar hakan ba,danshi mutum ne hakimi mai zurfin ilimi da sauki,saidai tasha mamaki yau rufaida zata cika wata biyu da dawowa kano amma bataji duriyar kowa daga cikinsu ba..

Har ila yau ta dauka gwamnati ne kawai suke taimakon su bata san gwamanti batama sanda wannan batun ba don tuno yaa sheik yasaka aka goge historyn case din rufaida aka cireta a jerin wayanda sukayi gamo da wannan case din na human traficking and forced prostituion,koba komai rufaida yarsa ce baxai taba son yaga anbar mata tarihin wannan mummunan record din araywarta ba

Tun tafiyar sa sudan bai hutaba saboda har acikin zuciyar sa baida kyakwan kwanciyar hankalii bare ma ajega samun nitsuwa
,tunanin sa yakan kasu kashi kashi,ga matsin mahaifiyar sa akan ya dawo a sasanta komi

Please Login or Register in order to submit comment