Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taje doguwar suman kanta da ya zubo sharkaff agadon bayanta yay malala ya kwanta mata abaya wanda tsayin shi yake tabowa har karshen mazaunan ta.

wayarta ne yay ringing ta miƙe da kyar ta dauƙa da yanayin mamaki a fuskarta ganin lambar ƙasar waje ne wanda batayi saving a contct dinta ba,tsaki taja who cud dis be,cos su manya ne,so sunsan ba a kiransu anyhow haka"..waje ta nema tazauna fuskarta adan yamutse sannan ta dauƙi wayar cikin kasaitciyar murya tace "helo who is this?.."Ajiyar zuciya taji an sauƙe daga cikin wayan sannan dan ƙaramin sautin kuka yabiyo daga baya"daga cikin wayar taci ance.."hajiya mummy Nazli ce.
da sauri ta miƙe tsaye cikin sauya fuska izuwa na dariya tace oh my god nazli dear?humm yar albarka ta taki ambato,yadai daga ƙira sai kuka meya same ki..?ko anfasa zuwa hutun ne?cikin serious muryan kuka nazli harda sheshheka tace"hajiya kinaji Baba yanacewa wai in tattaro kayana duka wai inna dawo hutu bazan kara komawa nan ba waifa cewa yay zai canzamin makaranta..ni gaskiya kice masa bana so kuma bazan dawo dan asakani makarnta a nigeria ba..ni wallhy bana so...da matsancin kuka ta karashe maganan sosai kamar wacce zata cire ranta.
hankli tashe hjy adada tace
calm down nazli.
bangane babanki yace miki kidawo ba?.."hajya wa''ahy dagske nake fada miki,baba bai taba min wasa ba,he called me dis morning wai zai dawo da karatun mu duka gida..kuma na kira mum ma tace min kawai inbi umarninshi,"forgod sake im a medical student tayaya zan bar karatuna mai kyau anan indawo nigeria...nide gaskiya ki sakamin baki,i cant cope with nigeria..im gonna die..ta fada tana kuka sosai...da alaman abun ya mugun taba mata zuciya sosai..

cike da tsananin damuwa hjy adada tace"..Toh kiy shiru kedai ki shirya kidawo hutun i promise u bamai canza miki makaranta did u hear me...ai ina sai kuka kawai nazli take yi,sosai ta dagawa hjy adada hankli harta katse wayar bata gane kanta ba.

tsabar tashin hankli ko tsayawa daure suman kantan batayi ba ta ari mayafi ta wuce falo wajen maman ta ta gaya mata,..itama yanzu sukayi waya da keeyan yake neman alfarmanta akan maganan duk hanklinsu ya tashi barinma shidayake final year dinsa yanajin baifi saura watanni ya gama mai gaba daya ba,
shukra ce kawai bata ƙira ba,da alaman ita ba anemi opinion dinta.

hajya adada sosai ta dau maganan da zafi,ta tuma tace sam ba shawarar zaidu bane zugashi akayi don a lalata masa tsarin tarbiyan yayan sa
aikuwa tuni suka hau kan magana suka zauna,barinma da yau basuga duriyar kowa ba.

rantsuwa akan rantsuwa tayi tace muddin in da hannun hasiya a maganan nan yau zaayi ta da wajewa dan itama bazata taɓa amincewa ba.
saidai in zaidu ya zaba ko su ita.

cikin yanayin masifa da tashin hankli suka kasance
har izuwa ƙarfe hudu na yamma
da su hjya maman suka dawo abuja.

mufrad ne yaje ya tattaro su tare da driver,dukan su suka taho gidan tare da anty fareesa da ƴayan ta...
banda gaisuwar anty fareesa da mufrad su hjya adada basu sake fuskansu da kowa ba,yau a bangaren hajya mama jawai ake walwala acikin gidan,Anan ma anty laila anu ta sauƙa tana occupying daya daga cikin dakin dake sashen,
kasancewarta cikin yan uwanta yakan sa taji dan dama dama duk dama tasan fareesa da mufrad dama basuda wani matsala haka ma keeyan,data san bai taɓa shiga harkan taba,damuwarta dashi shine ko sau goma zasu ci karo maganan fatar baki baya hadasu amma kuma ko sau daya bai taba mata wani cin fuska ko maganan banza ba.

ko mufrad din ma saiyau tasamu daman yin doguwar gaisuwa dashi dake anty fareesa na nan,ita kowa nata ne tunda can ma ita babu ruwanta acikin lamarinsu na kyamatarta.

sai can dare ya koma gida,yauma tsakaninsa da matarsa kowa yana harkan gaban sa
duk yadda yaso aranshi daya samu hutu ajikin ta yaci tura daga ya matsa saita ce masa ita ta gaji anemo mai aiki shikuma baijin zai kyale hakan acikin gidansa,sai kawai ya shareta ya maida hanklinsa kan abubuwan dake gaban sa na hidimar da zasuyi a gobe

washe gari tun da asubah aka tura driver ya dauko su nazli da keeyan daga aiport sabida tare dama suke dawowa,wajajen tara saura suka shigo gidan fuskan su duka babu mai walwala,barinma da sukaga gidan ya cikke da mutane.

around 10.30 shukra ma ta dawo,dukan suka sauka a sashensu hajya adada suka maƙalkale musu ganin kamar sune kawai zasu iya taimkon su akqm lamarin canjin mkrantar su,nazli tafi kowa daga hankalinta sabida ita yarson high standard ne bata son abunda zai sauke ta ƙasa koya maidata baya,gwara ma keeyan yanada babban dalilin sa nakin abun,abun bai wani dara shukra ba,ita dama ba akaita waje ba,so tasan dai in har abuja za amayar dasu karatu duka to bazai wuce akaisu Dream univsityn datafiso arayuwarta ba wato turkish nile university NUN Abuja,tun bayau ba shukura take balain son tayi wannan universityn aranta.

bayan isha'i mufrad ya shigo cikin gidan tare da Aina'u suka samu kusan kowa ya hallara akan dinning table za'a ci abincin dare kenan.

kowa yazauna wajen zaman sa saidai annurin dake kan fuskokin su ba kamar na kullum ba

barinma hjya mama data saka fuskar roba ta mugun harɗe ranta awajen saboda kin amsa gaisuwar Anty laila da su hjy adada sukayi,itakam ma ko ajikinta tana zaune ƙusa da mahaifinta wanda duk cikin falon babu wanda yakaita yin kama dashi,nazli ta hada gabas da yamma,shkra ta bala'in turmushe fuskanta feeling soo disquisted da gidan.

gashi dukan su sunsan basu isa suyi wani kyakkyawan motsin rashin kunya ba saboda mufrad yana nan idanun sa kuma naga kan kowa.ahaka aka soma cin abincin lami lpya, hjya adada ce kawai take hadiyar nata da kyar tsabar bacin rai da kuma makudan maganganu data taro acikin cikinta wanda jira kawai take a tabota ta kunce musu shi awajen..

bayan an kammala cin abincin lpya Hjy mama ta ƙira zulai wanda suka taho atare da uwani,agabam kowa da kowa ta nuna ta a matsayin wacce zatana koya masu shukra aikin kitchen,wanda hakan yay sanadiyar tsoma bakin hjya adada ta fara fada tana surutu.tace"yara sunzo hutu ace kuma za a turasu kitchen?ita bataga dalilin da za'a turasu kitchen ba,hajiya mama ta bushe idonta cikin amsata, maganan da basu sonji din shita fede musushi tas daga farko har ƙarshe cikin musu fada tace musu kowa ya dawo gida kenan kuma da sunki da sun so anu ma yargidan nan ce.


aikuwa hjy adada ta haukace agidan ta tada dust tace sam bata yarda da wannan tsarin ba,tunda daga farko aka fara magana, wuta wuta fada fada kowa bayason yaja akan bakansa a cikinsu, yaran kowa sai matse ruwan hawaye yakeyi sabida yadda hjya mama ta dau zafi sosai,tashin hanklin tsoffin yazamto kamar da boyayyar kiyayya da kuma gaba, da kyar yaa sheik ya shiga cikin lamarin ya raba aka bar nazli akan makarntan ta just to suit hjya adada aka dawo da shukra abuja to suits hjy mama.
keeyan kam dama yana karshe ne so ba a damu sosai wajen kin karban uzurin sa ba.

hajiya mama tayi fushi sosai da irin abunda suka dinga cewa a fili suna buga kirjin cewa ba a isa a mulke su acikin gidan zaidu ba,hjya mama bata ja dasu ba amma sosai ta tanadi fito na fito acikin ranta ,tun daga nan ta qudiri takun saka tsakanin su,nan take hj mama ta daukewa kowa wuta har jikokintan ma bata sarara musu ta gindaya sharudan ta a gidan,ta hana zancen yawon zuwa flexing da shoping anyhow ta kuma saka tsatsasaura doka akan sha'anin Addini,tace kuma dole ne kowa yabi..

Duk mufrad na lura da kannensa da suke jin kodan yau an karba musu Baki sun same abunda sukeso suke ganin nan gaba bazai casasu in sunyi kuskure ba.

haka aka raba daren nazli da su shkura suka zame suka koma sashen su hajya adada,Tsabar gulma da son jin kwakwaf yasa ainau ta shiga cikinsu tanajin duk wani abunda ake kitsawa

babu kunya tsoffin suke zugasu indirectly da wasu irin mummunan kalamai wanda yake cusa musu ra'ayin su kauracewa Anty laila,cewar hjy adada ita ba addan su bane...kuma ko da an karbe ta anan gidan sudai bazasu taba hada jinin su da shegiya yar matsafiya ba,..

gaba daya laifin qaddarar tabi ta jingina ajikin ta tana mai zuga yaran da wani irin siga marar amfani,tuni sukuwa suka hau kai suka zauna daram,..
Duk burgan su da sukaga an ƙarba musu ƴancin yin karatu,ita kanta shukra ce mata sukayi kartaji komi a universityn datake so din kawai za a sakasu,sukuwa sun dauƙa duk gata kawai ake musu.

fannin hjya mama kuwa tunda aka bar wajen batace ma kowa uffan ba,anty fareesatu ce take tare da anty anu suna dan debe wa junan su kewa barin ma da Anty lailan take nan very friendly da yara.

sai wajen goma ya wuce Ainau ta bar sashen ta samu muffy har yay bacci
kwanciyarta tayi ta cigaba da chat dinta da zarah,tana ce ma zarahn ana gurmi agidan su..itama gobe koyace su koma gidansa zataki sabida batason ayi drama babu ita.


fannin su rufaida kuwa rayuwarsu sukeyi agidan dr mehra mai dadi da ban nishadi,tunda suka zo a kullum suke zuwa agency ana musu phisical screening dinsu wanda yake level by level ne,hakan ne kawai ya hanasu zuwa gidan hajiya mama duk dama rabin hanklin su na wajen.

washe gari da safe mufrad ya farka jikinshi bai masa wani dadi ya tashe A'inau as usual amma taki tashi ƙarshe data fahimce nufinsa sai ta kawo masa complain cewa al'adarta ne yazo.

mutumin ka da baida hakuri ahakn saida yasata releiving dinshi ita yanzu kwata kwata bata cika son yin abun sabida tana shan wani maganin da zai ƙarawa jikinta yarinta,kuma therapist dinta ya riga ya fada mata yawan sex na kawo tsufa,ynzu haka tafiso anayi twice or once...sabida tasan tafi bukatar jikinta aynzu.

yanayin wankan tsarki ya saka jallabiyar sa nufi masallaci ya samu ancika an tada sahu yabisu aka kammala dashi.

dashi da mahaifinshi ne kawai suka rage keeyan ya shiga cikin gidan ya same dukan yan uwan shi a main hall sun idar da salla kenan sun zazzauna a inda suke karatu
kowaccen su ta turmushe fuska sabida basu isa suyi wani raini wa anty fareesa ba,dan ita aka turo tazo ta tashesu sallahn asubahi,..keeyan yana shigowa wajen yace musu kowa ta dauƙo qur'aninta suyi sauƙa kafin ƙetowar alfjir..

duk sun qudira aransu cewa zasu fadawa hajiya Adada musamman ma shkura datakeji kamar bazata iya jurar yin sallah akan lokaci da karatum qur'ani kowani safiya ba,...da can kuma irin rayuwar da sukeyi kenan,amma da shike maganganun su hjya adadan ya farayin tasiri akansu yanzu sukejin kome ma bazasu nayi ba.

Daf sun dauƙo qur'ani zasu bude saiga sallama da nutsiyar murya anty anu ce ta shigo sanye da doguwar hijabi pitch colour ya rufet kirif daga sama har ƙasa.

suna hade ido da keeyan ya dauƙe kansa yana dan duba qur'anin dake gaban sa,shukra da nazli kuwa sai kallon ta sukeyi suka ƙureta da ido batare da sunce mata uffan ba.

kamar anty fareesa zatayi musu magana saita yi shiru ta cigaba da abunda takeyi ƙirar mijinta awaya yasaka ta tashi cikin gaggawa tayi waje.

tada sallah anty anu tayi a daf da inda shukura ta zauna,.su basu fara karatun ba basu kuma ce uffan ba suka tsura mata ido,keeyan ne kadai bai kara dago kanshi ba..."tanayin sujjada cikin tsaurin ido sa rashin kunya
shukra taja wata arniyar tsaki"...tace you are like a dog"..tana nufin anty anu tayi irin sujjadar karnuka..amma yadda tayi sounding so daring and insultive,ahnkli keeyan ya dago ya harareta ta turo mai baki...Anty anu bata ko damu ba ta cigaba da sallahnta a raka'a na ƙarshe nazli ma ta ƙyabe baki daf anty anu tana dagowa daga sujjada da tace
"you really are a dog"..da sauri keeyan ya riƙe bakinshi zaiyi magana yaga anty anun ta miƙe tsaye
cikin wani irin yanayi,wani irin haɗe ranta tayi tana kallonsu da bacin rai tace"cmon what did u say?..shiru nazli tayi ta haɗe ranta cikin yanayin raini bata ce uffan ba,shukra ce ta miƙe tsaye cikin yanayin iyayi tana jujjuya kai tace"..
"i said..tun baya ƙarasa ba taji wani sauƙar tassss an wanka mata mari akan fuskarta"..u are stupid..anty anu tafada cikin zare mata ido tace..ke?aka gaya miki ni sa'arki ce?agigice shukra ta rike wajen marin saboda bata iya tsayawa daidai ba nazli ta miƙe a hatsale"..why must u hit her?..dan kawai an fada miki gaskiya..?bakinta taji an kama an kai masa maka mai ƙarfi"..ihu tayi tare da rike wajen,the next time anyone of u try to disrespect me or anyone else zakuga abunda zan muku.cike da bacin rai shkura tasa kuka mai ƙarfi"you are not our sister..U will neva be our sister..
tsaye keeyan ya miƙe cikin daka musu tsawa yace wa yan uwan san "wai baku da hankaline ?..u girls shud have some respect...wani hatsallen tsaki nazli taja tayi waje fuuu kamar zata bangaje
anty Anun,shkar ma tabi bayanta suka kai ƙara wajen hajiya adada

hakuri keeyan ya bata duk dama batayi tsammanin hakan ba,shidin ma nasiha tayi mishi wanda ya shige jikinshi sannan ta wuce tayi tafiyarta tabarsa awajen shikadai..
shiko kadan baiya goyon bayan raina na gaba dashi,yadda su nazli suka je suka hada maganan haka shima yaje ya warware agaban hjya mama..


ƙarfe tara saura kowa ya sauƙo falo cikin shigarsa ta kece raini na alfarma,duk cikin majaxen gidan mufrd ne kawai yau ya saka ƙananan kaya,sauran kowa yafito cikin yadinsa mai kyau da tsada,nazli ta saka straght gown na atamfa picht colour mai fallen neck shukra kuma ta sako wata riga da skirt dinki mai hawa hawa dinkin bakaramin dacewa da ita yay ba,as usual ainau tana kime agefeshi ta sako nata leshin
anty fareesa da mum dinta kusan shigarsu iri daya dukansu abaya suka saka,anty laila ce ta saka riga da zani mai kyau wanda ya dada nuna girmanta a fili, .tana zama akan table din mufrad yay gyaran murya ya soma gaisheta
..haka kawai taji ya soma burgeta,tunda ya gaishetan taga kowa cikin kannen sa suna gaisheta daga gani tasan basai anfada mata ba baƙaramin shayi sa sukeyi ba.
as expected wayannan tsoffin ko kulata basuyi ba..

zulai ce yau take kkrin serving dinsu abincin,hajya adada ta hade rai tave karta saka mata ta amshi spoon tahau sawa dakanta wakanta snn ta bayar,jikin zulai yay sanyi sabida kyamar da suke nuna mata, saida takai dadai plate din shukura tana zubawa dagangan yarinyar tayi yunkuri ta tunkudar da abinci akan kafarta
memakon zulai da abin ya kwabe mata ajiki tayi ƙara shukra ce tayi hjya goggo ta samu na masifa tana zaginta
sosai zulai taji babu dadi aranta..hartaje kitchen tana matsar kwalla a boyye.

ana fara cin abinci
hajya adada ta kawo bukatar shukra wa Yaa sheik
na batun sakata a turkish nile ,gudun fitina yasa yaa sheik
yace babu ruwanshi mufrad zasu tunƙara juyowa tayi ta ƙallesa snn ta maimaita masa maganan,shiru yay tukun yana lura da idanun shukra da suka gama rikirkicewa da tsoron jin ance shi zaa tuntuba.

Dama can shi in aka ishe shi da surutu toh fa ya gama cin abincin sa kenan..
yana kuwa miƙewa tsaye yace shukrar tazo ta sameshi a daki dan sosai dama yake tagerting dinsu saboda wani sabon rainin dayaga sun tsuro dashi kwana biyun nan.

tana samunshi a dakin ya titsiyeta da tambayoyi tsabar tsoron shi datakeji yasa ta gaya msa gaskiyar cewa itace tace lallai akaita nan din bawai choice din hajya adada bane...

tsawa ya dinga daka mata cikin gaya mata bakaken maganganun a ƙarshe yace taje tace yace bazai sakata a Nun din ba.

aikuwa da kuka ta fito ta samesu kamar wacce aka bugeta,hajya jasmine tace baza a tursasa mufrad ba taje ta cigaba da rokonsa inya amince mata toh suma zasu barta.

haka tayi ta jigila a kofar dakinshi tana roƙo,da kyar Sanda anty fareesa tasaka baki sannan ya saurara mata"
ya rubuta mata aptitude test nun
standards Cbt kuma direct computersa za'ayi submiting answrs yace saitaci rabin test din zai biya mata kudin makarantar..

kan ta sosai yay zafi gashi tasan in har batayi dakanta ba wani sabuwar case ne na daban.

haka ta yanke shafa ta rubuta test din ta tura masa,akan washe gari da sassafe in ya dawo daga pop na yaransu zaizo ya duba yaga metaci.
cos trout d nite yau baya nan suna can wajen hidimar su da abokan aikin sa.

washe gari tun ƙarfe takwas su malak suka kammala shirin su tas da niyyar yau zasu taho dominsu wuni awajen hajya mama
tunda gobene komawarsu kano...

daga su sai driver aka kawosu har gidan,yau wani irin wankan ƙece raini kowaccensu tayi tana baza sanssn yar qamshi,malak ta saka wani hadaddyar peplum yellow colour gown mai blue shoulder cap tayi rolling kanta da golden veil,rufaida kuma ta saka upheel rose french gown,dark green colour to match da heel din amina muaddi dayay mugun kyau wa fararen sawun kafafunta dukansu sun riko hand bag dinsu mai tsada

samu sukayi babu kowa a bangaren hajya maman hakan yasa zulai ta musu jagora izuwa main house....




#SURAYYAHMS

tun Daga bakin kofa zulai tayi musu sallama ta koma sashen hajya mama domin ƙarasa goge gogenta kamin lokcin serving din abincin safen su yay,bude kofar gidan sukayi suna takunsu mai sanyi da kuma ɗaukar hankli cikin yanayin aji da nuna sanyin nitsuwarsu,ƙarasowa sukayi har izuwa kofar shiga babban falon sannan rufaidah ta danna door bell yy ƙara haifi da minti guda ba dagata taciki aka zo aka bude musu malak ce ta fara yin sallama ta shigo da sanyin muryanta sann rufaida ma tayi tabiyi bayanta

Babban palourne mai tsananin kyau sai kamshin tiraren wuta na maiduguri dayake da sanyin qamshi dake tashi acikin wajen,,hajya mama ce a kujeran dake farko ta saka sakakken dinkinta na riga da zani na atmfar originl cote divore green colour ta lullube kanta da jan mayafi,Hajiya jasmine na daga gefenta,itakam wani hadadden cotton lafaya baki tasaka mai adon ja ja ajiki ta nannade jikinta gaba daya dashi hannunta da kafarta dake nunawa awaje sunsha gwalagwalai da hadadden zanen jan kumshi,.daga can gefen kuma shukra ce data saka wani fitted gown na designer material an mata dinki mai bajajjen hannu da jela,nasha nasha ta kwantabtabi ta makale ajikin hjya goggo tana zuba shagwaba dan har yau bata dena kukan kaita kitchen da hjya mama tace za'ayi ba..dayan gefen kuma Anty laila ce as usual ta saka riga da zani tayi dauri mai kyau tana riƙe da iman anty fareesa na gefen ta itama.

kansu tsaye suka nufo inda mutanen gidan suke zazzaune ayayin da kowa awajen ya maido da hanklin sa kansu yanata kallon su tunkan su ƙaraso jin wata bugaggiyar qamshin turaren jikinsu dake tashi yana bugan hancin kowa awajen,nan danan hjya jasmine ta juyo cikin ƙure rufaida da wani irin sassanyar kallo mai daukar zuciyq,wani irin kawataccen murmushin da bata shirya masa bane yake wanzuwa akan fuskarta,wanda daga ganinshi kasan zuciyarta ne ya bala'In girgiza da mamakin ganin rufaida ayanda ta dawo wata kyakkwa tayi haske tayi kyau tafito zak sarauniya kuma da kalar dressing din datayi its soo astonishing its wowwww she love her dressing sense already,taga fuskarta babu wani kwalliyar hayaniya,and the dark green cover shoes heel,amina muauddi, aranta tace hmmm a girl with a great fashion taste ,wankarta ya nuna aji da wayewa matuƙa, tamkar asace ta tsaban haduwar datayi,tun daga ƙasa har sama take kallonta ta with so much adoration and bewildement ayanayinta tace
" Oh masha Allah"
look who we have here.."murmushi suka hau yi suka rusuna agaban su suka hau gaishe da kowa cikin sanyin ladabi,rufaida ta sauƙe kanta can ƙasa sabida yadda idanun sukay mata yawa yana ƙara mata fargaba,musamman ma shukra da bata wani dago fuskarta ba gwanda ma malak ta san fuskrta sosai,direct take binsu da ido da wani tuƙikin kishi idanunta baya ko kiftawa,da sauri malak ta zuba agaban hajya mama tana cewa"yàyya ishéñà..ishéna à..tana nufin gamu nan toh munxo..
"hjya mama ta kalleta tana murmushi sosai.
ahankli tace musu "kunyi kyau" rufaida ta ƙaraso jikinta ta zauna ƙasa kusa da ita.."ta kalle rufaidar tayi dariya aahhh yar amana"tussunà rukdi!!"tana nufin kwana biyu bamu hadu ba nayi kewarki">a hnkl rufaida tace "hnnn "nda rui sha,jirem gidi.."..nifinta ni ban yarda ba kamar dagaske,"Anty fareesa ta saka musu baki suna tayin yarensun ana raha,shukra batace urfan ba,hajiya jasmine ita kadai aka barta tana kallon su asace tana famar sakar murmushi...ba zallan kan hjya goggo bane a dore dan hatta anty anu bata gane suwaye wayannan ba.
kamar wanda hajiya mama takarance ta tana murmushi ta juyo tace musu rufaida Wannan ma antynku ce,ta nuna anty anu da anty faressa atare cikin harshen yarensu tace"âwàñña(same father)..atare suka ce ohhhh..sann suka ƙara gaishe da anty anu wanda bakomai ya dada burgeta da yaran ba face yaren dataji sunayi so confidently,ta tuna yadda tayi spending early 20s dinta wajen koyan al'adun su na baggara...she is so passionate about her tribe wanda ya kasance jinin rufaidace gaba da baya amma su ba wani sosai suke son damuwa dashi ba..By now anty laila kam babu wani abun su na al'ada da bata sani ba kama dagakan rawa abinci dressing da sauran sha"anin aladun kanurai
kansu ta shasshafa itama ta musu yaren tana cewa
"Àlà bàrga njò beutiful pricesses
(Allah yay albarka)
suna murmushi sukace mata ameen
Tashi sukayi ita da anty fareesa suka wuce sama da niyyar kimtsawa akfin azo cin abinci

Hajiya mama tana shirin introducing rufaida wa hjy goggo kenan caraf saiga sallamar nazli da hajiya adada a falon,sun kure kyau sunci ado,as usual tayi shigarta na kasaitattun hajiyoyi masuji da mulki da kudi, tasha dinkin bouboun ajikin wata dankakriiyar golden code lace wanda yasha tsadaddiyar aiki tun daga saman shi har kasa,wani jimmy choo mai dan uban tsini ne akafar nazli tana takawa kwas kamar zata karye,itakam ma english wears ta saka,chinesse straigth gown in kamfanin fenty baki tasaka da golden pendant da turban cap shima golden
,..gabanta ne yay mummunan faduwa data dora idanuwan ta akan rufaida..wani irin satan kallonta takeyi"..cikin ranta tace woww wannan kuma waye haka kyakkwa..kai kai kyan ma yay yawaaa mtsw,..tana raya hakan aranta ta dauƙe kanta akansu cikin mugun jan aji taje tazauna abunta batacewa kowa uffan ba
..malak tace "ina uni anty nazli,.wani irin kallo tamata sann ta yatsina fuska kadan tace "au kece?malak tayi mata shiru, atakaice tace toh ya gida..malak tace lpya,..ita jira take taga ko rufaida zata gaisheta saita ga yarinyar ma bata ko kallon inda take kamar batama lura da shigowarta wani tsaki taja aranta itama ta dena satan kallonta tamaida idanunta kan wayarta tana latsawa,wayar anty anu ne yaya ƙara hajy ta umarce malak data dauka tabisu da shi ciki

kan rufaida na can kasa,duk ta kasa yin wani motsi,ita kallon da hajya adada takeyi mata ne ma ya mugun daga mata hankli ayanzu duk ma
atare suka juya suka gaisheta da malak,da irin amsa su datayi a hakimce wa malak dinma kawai tay magana
"Tace mata yaya karatu yay kuma babanki.malak tace lpy alhamdullhi,sai a sann ta kalle rufaidar da kyau tana jin wani abu mai nauyi aranta jin kamar ta tsane yarinyar,cike da izza da nuna mulki tace ke kuma yar gidan waye"..malak a ina kika samo wannan kuma..cikin sauri hajiya jasmine ta cape maganan abakin hjya mama data hayayyko zata bada amsa..hjy jasmine tace "wannan ai rufaida ce..yar gidan Yaa malam ce..saitayi shiru bata kara cewa komi ba"..wani kallon ta karabin jikin rufaidar dashi
snnan ta dauke kanta a fixge
...karamin tsuka mai tafe da sigar koinkula taja snn ta nemi waje tazauna kusa da nazlin ta..can da abun ya ciccyota tace ke jasmine"..waye kuma shi wanna din..ni bansan shi ba fa...ta kara kallon rufaida da alaman akanta kawai take magana"..hajya jasmine tace cousin sis din su shukra ne ,ahnkli tace but she looks familiar..
babu wanda ya ƙara ce mata uffan awajen dan already shukra ta gama harsashen ta harta dago wacece ake magana akai mamaki ne ya gama cikata ashe wannan ce rufaidar ?tana ta satan kallon fuskar nzli kodama zasu hade ido tay mata gulma ,cos she neva imagine her to be this unimaginably beautiful and classy danmm..ta dauka da akace rufaida yar gidan yaa malam zataga wata "hag" in "rag" ne mai yamutsasen jiki da yagaggen kaya.
ba itace akace tama kashe mijinta ba?but she dint even look like ta tabayin aure anya kuwa?..hmmmmm
daga nan wani shiru falon ya dauƙa kowa nata sake sake aransa

Please Login or Register in order to submit comment