Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cirko cikin shigarsu na brown colour hijabs dogaye sabida normally dama mahaifiyar sun haka take dressing dinta kasancewarta commisioniyar yan hizba kuma uztaxiya..

Kallo daya mamin tabita dashi ta dauke kanta

Kaya ne niqi niqi agaban su wanda yasaka Aina'u karayin sauri da alamar sonjin silar shigowa dasu

Tana karasowa cikin falon ta rusuna har kasa ta gaida mahaifyartan wanda take amsata ciki ciki Dan jiranta datasa sukayi ya matukar bata haushi Wai ace mace kamar Aina'u bazata farka tun asubahin fari ta fuskance hidiman dake gabar ba?
Yo metakeyi agidan mijin?Wani uban tsaki taja sanin cewa tun asali laifinta ne da bata musu tarbiyan haka tun Suna yara kanana ba,cos lokacin da ubansu yakeda kudi yanada mukamin gwamnati girman gata kawai aka basu,toh yau gashi Babu uban Babu muqamin kuma yara sun riga sun fandare gaskiyar bahaushe dayake cewa icce tun yana danye ake tankwarasa.

'Wayannan uban kayan fa?
Xuwa Ina haka?
Trying to play dump
Ain ta maida tambaya direct kan kanwarta Zarah kamar dama ba Susan da abunda suka shirya ba
Zarah tace
"Kayan sannu da zuwane mana, kefa wawiya ne..
Bayan Kinsan basu taba haduwa da mami ba, ai ya kamata ace andanzo musu da Wani abu ko?...
Kema fa kinsan halin da ake ciki anan gidan mu ba komi bane fa, Amma ai mai kudi Duk tsiyarsa baya raina Mai dattako
Inkuma bakison tsarabar ai saina fitar waje na mayar mota ko Mami?
Ta juyo ta bisu da Wani irin harara
Enough both of u... Kunbi kun isheni da shirmen banxa,Kun cika ma mutane gida da surutu ni kukaini Inda zanje inyi gaisuwa in kama gabana
Ke kuma saiki koma kiyita sharan baccin asarar wawiya kawai

Shiru sukayi Dan sosai suka San halin mamin su da son karkare masifa
Dolen su ne subita a sannu don burin su ya cika inba haka ba sunsan basuda Wani mafita.

Ganin idanunta yasa basuyi yunkurin kiran masu aiki ba suka dauko kayan Niki Niki a hannun su,wanda kusan Dukka kayan shirin Zarah ne,2 heavy leader bags ne sai Wani Dan karamin gift wrap wanda daga ganin sa kasan turaren wuta ne irinna maiduguri aciki

Malama rabiatu dake takawarta agaban su tana tafiyarta a hnkli cikin tsantsar nitsuwar dake tattare da yanayinta na mace mai kamala wanda babu shakku ko dar dar atattare da ita
Wani sasaanyanr qamshin musk ke bibiyarta shi baiyi qamshi sosai bare ya addabe mutane

Tun a falon farko take buga sallama cikin nutsutsaiyar sauti yaranta na biye da ita har suka wuce can ciki ta Inda masaukin hajiyoyin yake bata fasa ba...

Alokacin Hjy adada ta idarda sallah kenan tana xaune akan darduma tana famar lazimi ta jiyo sallamar sun,Hjy goggo dake kwance da jikin tsufa tsabar gulma ta miko kanta cikin sauri Wani Caraf ta yatsina fuska tace 'ohni Aminatu yau naga takaina waye kuma haka da sassafe tun bamu karya ba? Kode yayan zaidu ne suka xo dubani am?adada...a Dan takaice Hjy adada ta jyo amma batace mata uffan ba dake ita muryoyin mata tajiyo Dan miqewa kadan tayi Jin motsinsu a kusa ta furta"Wa'alaiksalam kushigo daga ciki..
Gyara zamanta tayi akan daddumar tana dada gyarawa shegiyar cotton lafayar ta datagaji da haduwa zama akafadunta Wani dan uban qamshin turaren gargajiya na dutches da sandal wood original already ya gama cikke dakin da azaban qamshin sa
,incent burner dake ci Agefe da Agefe na famar kara masa kaimi...

Jim kadan saiga bullowarsu,hajy rabiatunne agaba gabanta gadi ta bayyana gaban su fuskarta dauke da Wani dattijuwar Murmushi wanda tun daga yanayin shigarsu ta Kamala yasa su hjya kara bada hankulansu akansu da Dan sakin fuska suna musu maraba

Waje hjy rabi ta nema ta zauna Adan dofane feeling so uncomfortable da irin kallon kurilla da suke jefa musu ma rashin gane su zuciyarta ne ya shiga mata Wani irin zafi ganin yarda yarta take baya baya kamar wata sokuwa kamar ba surkuwa take agidan ba..
Gaishe su ta somayi
Irin gaisuwan Nan na manya gwanin burgewa tana tambayarsu lpyarsu tanayi tana hada musu da addua masu karama Inda basai angaya musu ba sunsan tabbas wannan matar ta karantu musamman a fannin addini.

Zarahn dake tafi kowa fahimatr yanayin mahaiyan su da sauri tayi saurin waskewa tace "hjya,wannan itace mahaifiyarmu
Hajya rabiatu!..
Atake Dukan su suka bita da Wani irin kallo Banda Hjy Adada datay Murmushi tace Ayya Allah sarki,Hjy googgo kam Sam bata gane waye ake magana akaiba dan Ita kwata kwata ainau ta sauya mata kamanni musamman data ganta acikin hijabi ba'a cikin shigarta irinna jiyaba.

A lokcin hjy rabi kamar zata kashe Aina'u haka takeji a cikin ranta,ganin ko dago kanta batayi ba bare ta kwatanta yin abunda ya dace dasu

Caraf kuwa hajiya goggo da azarbabin ta yy yawa tace
Kuyi haquri banfa gane suwaye ba ko
Ku ma yan uwan hasiyar ne kam?
Nan Ayn tayi saurin dago kanta tace "a'a Hajiya,nice fa matar...matar mufrad, mahaifiyata ce dama taxo tayi muku barka da zuwa,, dayake nafada mata cewa tun jiya kuka iso.

Ko gama rufe bakinta batayi ba hjy goggo ta Wani Kyabe baki cikin Kare mata kallo Tace ohooo ayya toh barkanki da xuwa dai baiwar Allah,"uhumm uhum Allah mai ikon sa kenan,gaki da kammala da nitsuwa,sannun ki kinji?Allah yayi albarka,,Mami tadanyi Murmushi tace Ameen,bata fasa ba tace"Adada kingani ko?ai dama Hakan rayuwa take yau nake ganin farin tukunya mai fidda baqar tuwo...
Ynxu kyace wannan yarnan taxo nan jiya koba itace ta lafta fauda a fuskanta kamar zataje gasar mayu ba..saurin yin dariya hjy adada tayi Dan ta kauda maganan ya zamto kamar acikin wasa, akayishi sabd tabbas taga sauyin yanayi atattare dasu "..hakan yasa ta dada sake fuskanta cikin dada fuskatar setin hjy rabiatun tana cewa ai xaku shafa damu kam Dan bamu San kowa anan ba Duk karatu yabi dauke su yahana mu zumunta Amma ace har matar jikana ban ganeta cikin sauki

Daurewa hjy rabiatu tayi tabita sukayi dariya atare tamkar da babu komi aranta ta cigaba da murmushinta mai snyi

Haquri ta shiga basu cikin iyabi da harshenta mai taushi da tsantsar iya tsara kalamai masu kama hnkli da saka nitsuwa ma kwakwla,dake kwarariyar malama ce wacce ta saba da harkan fadakrwaa sai bataji wahalan bayyana laifukan yartan acikin sauki ba kaf wajen shiru ya dauka ana Jin nasiharta,Inda a Duk yadda mutum yaqi yaji a dole ne zai gane Inda ta dosa,ta babbasu haquri sosai wanda tamkar alfarma take nemawa banzayen dabiun yartan...
Tace Yaran zamani
An haifesu ne ba a haife halayensu ba.
Tuni xuciyar Hajiya Adada yay sanyi da nasihartan tabi ta karaya,Musamman da suka lura da yadda Aina'un itama ta sadda kanta kasa like she is just realizing her wrong turns,ita datake neman gindin zama?but it's seems like girman kai da jiji da kai ajinin jikinta yake
Haka kawai kam yana mata wuya ta miqa ma wasu wuya bare tayi ta musu fadanci

Sai ayanzu take fahimtar cewa sukuma hajiyoyin Nan Babu abunda suka fi aunawa ayanayin mutum inba Hakan ba
,Itt all appears to her
"Dat she must just be a good girl oh god ,gaba daya sai tanajin Babu dadi aranta,this whole life with mufrad is changing her life to sumting else..
Kuma tabbas tasan inwayannan mutanen suka tsangwameta to kuwa bazata kara Jin dadin rayuwarta a gidan ba..

Hjya rabiatu tayi iyakan bakin kokarinta wajen wanke yayanta da burin ja musu mutuncin su wanda a halin yanzu yay matukar tasiri Musamman a xuciyar hjy adada.

Hjy goggo itakam dama a rikice take anjima kadan ma zata iya sauyawa tace bataji ba

Hira suka taba kadan,Inda suke sanin matsayin zaran abakin Aina'u data dadaddage ta soma tsoma baki acikin hirar tasu.

Xarah kuwa burinta kenan dama asanta Dan sosai ta kwallafa ranta akan shigowa familyn su bata damu ba koma wa zata aura muddin dai a familynsu ne

Bayan kamar minti arbain sukayi musu sallama akan zasu tafi,Aina'u ta mike buuut, hajy rabiatu ta watsa mata Wani irin muguwar kallo,a sadade ta koma ta zauna sanin cewa ran mahaifyarta a matukar bace yake da ita,har cikin dayan sashen gidan ta biya tagaida su hjya jasmine sama sama daga Nan ta taso Zarah agaba suka bar gidan cikin gaggawa.

Dan dolen Aina'u ta sauke Kanta tayi tunanin gaggawa yadda zata gabatar da kyautar da sukaxo da shi.

A Babu abu dai haka ta jawo gifts din har gabansu wanda tace musu mahaifiyartan ne ta bayar,sosai hjy adada ta gode banda Hjy goggo dake Dan fetsa baqar maganan ta
Cikin rikici tsufa Dan ita har yanzu jininta Sam bai hadu Dana ainaun ba..

Bayan Nan yau kowa ya farka ne da fara'a a Kan fuskar sa,cikin nishadi da Jin dadi suka suka gabatar da break fast dukan su akan table ana raha ana jawo kowa cikin hirar ba kamar jiya ba

She felt a bit relive, uhhgh, all thanks be to Zarah,Dan sanadiyar yar show off dinsu yau taga sauyin fuska sosai
Musamman ma daga wajen hjy adada dake she looks interested In getting to know more about hjy rabiatu,wanda zai iya kasancewa kamalarta ne kawai ya matukar burgeta..


Arnd 8 am yaa sheik ya fita aiki keeyan da nazli suka raka hjy goggo check up a babban asibitin garin zaa duba mata bayan ta dake mata tsami,Aina'u kuwa shap shap ta sabule ta nufi office Inda isarta keda wuya ta tura ma Zara Tex tace mata maza maza ta taho ta sameta akwai magana,by 10 haka shukra ta shirya ta biyo bayan hjya mama datayi jagora ma hjy adada cikin shigarsu na alfarma suka nufi babban fadar masarautar kano domin kaiwa sarki da matayen sa ziyara dake sunada kyakkwar alaka ta zumunci tsakanin masaurtar kano da masarautar mijinta Shehuri.

Kan kace kobo gidan ya dau Wani irin shiru face a shashen hajy jasmine datake famar kammala wasu abubuwan game da komawar su can abuja


Daga dayan side din kuwa mufrad ne kwance akan gadon sa yana ta kwasar minsharin biyan bashin baccin sa na jiya daddare da baiyi ba ya tsaya yin chat da babban amininsa kuma uncle dinsa IMAD..

Already sunyi akan daga ya iso Nigeria shizaije dakansa ya daukosa daga airport,sabida muhimmancin imad din agaresa yasa almost all his appointment nayau ya kawar Dan baida Wani shakikin amini arayuwansa dayafiyemai shi..

Thy share a stronger bonding Dan most of yan uwansa na jini wanda badon yanayin career da suka zabar makansu ba da babu wanda zai amince da cewa zasu taba iya rayuwa batare da juna ba harna tsawon wannan lokaci...


Part 1 IS FREE,TUKUICI NE GAREKU MASOYA NA U CAN READ IT HAR ZUWA INDA ZAMU TSAYA,SAIDAI CIGABAN SHI NA KUDI NE,PLS SHOW SOME LOVE AND SUBCRIBE the ACCESS FEE IS 300 NAIRA ONLY
VIA 0152983148
MOH'D SULE SURAYYA GTB.
OR katin MTN vtu tran via 08060712446

Screenshot ur evidence to SURAYYAHMS 08060712446

OR MAMAN MUBENA
08036651119.






*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


Part1:chapter 16
*Case 1*




_States public ministry_
_las Vegas._


Security ne tam a ciki da wajen asibitin musamman ma kofar icu na babban asibitin garin vegas

Shahararun yan jarida da jounalist sune rututu a waje anata fafatawa da su da polisawa wajen neman cikakken rohoto daga bakin agents gasunan birjik sun taho runduma guda tamkar ba asubahin Allah ba..

Saidai har yanzu ba a iya ce musu komi game da abunda ke faruwa ba, Duk dama ajiya jiyan har labarin mutuwar alaji bature ya zagaya gari cos he is one of the most wanted criminal target da aka dade ana bibiyar lamarin sa na batun child trafficking,forced prostituion,Agent din basu su ce komi ba sabida yanayin jikin rufaida,Yanzu haka itace ta rage musu matakalar cin nasarar su akan case din,cos she is d only witnessed victim alive da Zata iya bada cikakken shaida akan crime din da Alaji Bature yake aikatawa wanda aynzu take behaving kamr ta samu tabon hankli da kuma niyyar su na zuwa dayan gidan domin tarkato sauran thugs din alajin a Inda yake boyesu Kafin ma azo ace za'ayi convicting dinsu abi sauran kan case din
Dan haka komi yy tsayuwar cak

****


6:00am dot imad ya farka daga bacci da kyar shima sabida alarm din gefen gadonshi ne daya damesa da kara yatadashi tashi yayi ya shiga bathroom dinsa, yadade aciki kafin yafito cikin wani white bathrobe wanda ta amshe kalar fatar jikinshi dats so mild nd soft kamar wani baby, zama yayi abakin gadonsa ya shiga shafa moisturixing cream dinsa mai kamshi,yana bin ko inan aa a tsanake

Can sannan yatashi ya nufi wardrobe dinshi yaje yabude yaciro wani black Gucci blazer da wata baqar logo print t-shirt na parco rabanne yasaka da damammen wando dayan bangaren rigunan sanyin shi ya duba yana tunanin wanda zai saka kafin yajawo wata long chester field coat wanda ya yasaka ta akan rigan cikinshi tazauna ajikinshin tamai kyau sosai,

designers pefs dinsa ta guilty absolute ya fetsfesa sannan ya shimfida dadduma yay salla yana sallame wa yaji kamar ana bugamai kofa..

Wani yatsine fuskarsa yayi sanin bazai wuce mayun gurds dinsan Nan banne, da kyar cikin kasaita yace "come in" bude kofa guard din yayi rikeda wata yar karaman tray da small mug of hot coffee akai karasowa yayi gabanshi ya ijiye tray din daf dakan dadduman San sannan ya miqe ya tsaya yace
Ur tea sir,and we are leaving in the next 10min..ur flight is taken off by 7.30am sir

Wani daure fuska yayi baice Mashi uffan ba as usual yatashi daga kan dadduman yahau kan gadon yazauna yana mai masa pointing coffee din da yar yatsa alamun ya mikomasa shikam bai damu ba daukan coffen yayi da sauri ya mikamai ya karba yakai bakinshi yay sipping dan kadan sann ya zare a bakinshi batare daya kalli gurds din ba yace "my phone,check it Did anyone call?
Ya fadi ahakan a fili while azuciyarsa yana ta expecting ace ga kiran mufrad Dan yasan kalar zumudin da sukeyi azukatan su yau da ya kasance zasu sake kasancewa da juna.

Da sauri gurd ya juya yai kan side table ya dauko wata hadaddiyar Apple phone ya Taho dashi yana mikamai yace"your phone sir,no miss calls"..Dan already da ya danna yaga babu komi akai dan kwafa yayi baisake cewa komiba yacigaba dashan dan coffee dinsa ayangance harya gama yatashi ahankali ya tattare sauran kananan abunda zai dauka yayi gaba guard din ne ya kashe wutan dakin sannan yabiyoshi waje cikin sauri,zuwan sa ya samu harya shiga motar ya zauna baiyi wata wata ba ya zagaya ya zauna a driver seat suka dau hanyar Airport.

Ko barin anguwar basuyi ba wayarsa yahau Kara,ya dauke kansa yana kallon window ta waje kamar ma bazai bita kan wayar ba sai kuma ya juyo a hankli ya dauka,xai amsa kenan ta katse saboda ta dade tana ringing,dan smirk yy da mamaki ayanayin fuskar sa ganin kirar oganniyar sa chief judge lara willfred a 65yr old American
Wanda ta kwarance akan aikinta take kuma yawan bada imad din goyon baya,kamar Dan cikinta haka ta dauke sa,tun baiya son sakewa da ita har yazo ya fara biye mata yana mugun daraja ta tamkar jinin sa na asali..

Sau daya take kirar mutum so he knew she won't call back,Wani kyiuwa yake ji Dan baisan ya kirata ta Kara mai wa'azin cewa karya tafi,can Nigeria an matsa yazo ita anan bata so yatafi he just don't know what to do or who to listen to,"cikin yar wannan tunanin ya Kara Jin karar wayarsa tin tin yay tickling alaman Shigowar saqo,da sauri ya swaping ganin unknown number an rubuta
"A town down,Victim
Still responding,..
Ur attention is needed immiedietly.
Nannauyan Ajiyan zuciya ce ta kufce masa Basai angaya masa yasan ogan sa ta ruboto sakon
Tana so lallai ya tsaya akai Kar case din ta lafa cikin sauki batare da sun kawo karshen mugayen sponsors dinba.

Wayar sa ya shiga daddanawa neman inda zai samo spice din labari,Tuni Wani contact dinsa dake aiki da interpol ya labarta masa komi sai Yanzu ya dada fahimtar Abunda yasa ake so ayi involving dinsa a case din,ya fahimce cewa Alaji Bature is well involved with d Bulgarian gorvement kenan case din zai ta allaka ne tsakanin hukumar kasa da kasa fannin inda yafi kwarancewa,..

Har suka isa airport baima lura ba cos tunda akace Wai victim din mace ce yake cikin yanayin zullumin tunanin abun a zuciyar sa,shi bai taba fadawa kowa sirrinsa na gudun karban cases irin wannan ba,he is just wondering how he is gonna face her right now witou being vulnerable to his emotions,idanun shi ya lumshe Sosai dan bai tabajin yana sha'awar ganin kansa a Nigeria ba sai yanzu Wani irin dana sanin Kara kwanakin da yay yakeyi definitely yasan dayatafi da bashi za a dora akan case din Nan ba,driver sa ne ya sauko cikin katse sa Yace 'sir?Wani kallo yamai,sannan ya kalle airpot din sai Yace "not today,take me to d public ministry right away,Yace yes sir a gaggauce ya juya kan motar suka nufi hanyar wajen..

"..Isarsu yay daidai da isowar team din polisawan da sukaje kamo wayancan thugs din,already 7 of them are shot dead uku Kawai aka ci nasaran daukowa araye..

Cikin sauri ya sauko inda security suka mamaye shi sabida tsaro ayayin da Kofar public ministryn ya kasance Babu masaka tsinke yan jarida da jounalist sun mamaye wajen kamar guda ana jiran kwakwaran rahoto daga garesu
Suna ganin imad suka runtomo aguje suka mamaye shi
"Excuse me sir,sir excuse me..sirr
Sirrr Barister imad

Babu kalar kiran dabaiya sha Amma ko kallon su bai iyayi ba har ya samu ya shiga can ciki,Direct office din chief police officer ya nufa to report himself as the lawyer of The victim gudun karma akawo Wani corupt lawyar da zai bata musu case din cos kowa yasani manyan politicians da masu power akasar sukan saka hannun jarinsu akan irin wannan sha'ani,so in ba'a yi gaggawa wajen daukar mataki ba it's alwys remain impossible to deliver justice to the victims.

Dake kowa yana danjin shakkar imad din so Babu tantama ko tsananta wasu bayanai atake aka signing warrants aka bashi daman isaga victim din Kai tsaye,polisawa dakan su sukai mai jagora aka kaisa har asibitin da rufaida take kwance an tsare ta,tare da cikakken kulawa da saka idanun hukumomin FBI da interpol agents ta ko ta ina aciki da wajen asibitin..


Babban likitan dake kula da Ita ne yafara tunkaro sa,sunan sa doctor Amando karasov.he is a special German neurologist doc, curently having a rough time treating her sabida case din rufaida ba zallan razana da bruises bane she is neck deep into Emotional trauma Kwakwlta ya Dan tabu kadan So Dole ne sai an hada da kwararren mental therapist wanda zai iya dawo da ita cikin hayyacin ta cikin sauri Dan ba'a bukatan case din ya dade batare da ankai kotu ba...

Bayan ya gama sauraran wayannan bayanai na likita sai ya koma gefe ya zauna yay relaxing kanshi tukunna ahnkli yana sauke numfashi,Baima je ya kalla yarinyar ba tukun dake ma doc yace bata farfado ba har yanzu,Can ya saka hannu ya ciro wayarsa dake makale a aljihunsa dialling number doct Mehra yay bugu daya ya dauka yana murarin Jin labarin dawowarsa sai kuma yaji kamar muryansa ba ayadda ya saba ji ba atake murmushin kan fuskar sa ya dauke,"yace hey imad ya dai?A hankli cikin sanyin yanayi yace hey doc Mehra,..pls I need ur help.,da tsantsar mamaki a muryan Doc mehra yace imad u need my help?akan me are u ok? Jin ya masa shiru yasa shi cewa "Meya faru ne ya baka taho din ba?son anything ok? ko inkira alhaji zaidu?

Da sauri yace no no no pls Kar ka kira yaa sheik Dan Allah yana Dan sauke Ajiyan zuciya cikin sanyin yanayi ya Kara cewa"Doctor pls,Nide ka zo din kawai,Ina ICU na City hospital Vegas and make sure u don't tell anyone about our meeting pls promise me,kuma Wannan maganan Ya tsaya a tsakani na dakai Inka iso nayi maka alkwarin zan sanar dakai komi I swear.
..daga Nan bai jira cewar doc Mehra ba kawai ya katse wayarsa ya mayar da ita aljihu.

Da balain mamaki doc Mehra ya sauke wayar a kunnen sa shidai har yanzu bai fahimce komi daga furucin imad ba
Shiri kawai ya dukufa yi cikin gaggawa ya fita a gidan sa kamar office kawai zaije daga Nan batare da ya sanar ma kowa ba ya wuce aiport yay hording plane ya nufi US.

Wani irin sauke Ajiyan zuciya imad yay yana shafa suman kansa cikin rasa ta inda zai fara fuskantar case din yarinyar,he read her medical report and it shows dat anyi abusing dinta sosai She had several infections ga tabon duka da wounds ga attempted sexual molestion,saukin sa da akace ba'a yi raping dintan ba tukuna but taji ciwo shima awajen.

Kansa dake masa ciwo ya mayar kan chair ya lumshe idanun sa tunani kala kala Suna yanko masa musamman akan case dinta dayake hannun hukumar kasa da kasa kuma

Ajiye medical reports din yay ya dauki police statement wanda dokar kasar tasa aka rubuta akan laifin and All Ballistic investigations sun nuna cewa lallai rufaida ita ta kashe Alaji Bature babu tantama sabida dukkan finger prints nata sun bayyana akan bindigar da akayi kisan dashi Along with d prints of d deceased..
Report din ya dada kalla Wani tsaki ya kufce masa
"wayasan ma garin raping dintan ne ta kashe sa?tunanin Hakan kawai yayi tayi aransa yanata kokrin ya fayyace real picture na yadda abun ya kasance a mind dinsa,ya dade a haka cikin zurfaffen nazari da tunani.


After like 10hrs hours saiga ga Wani dattijon mutum wanda akalla bazai wuce 53yrs ba,cikin shigar sa ta matured grey suit irinna manyan likitoti gabansa gadi ya iso har cikin asibitin dake akwai cikakken ID card dinsa agaban rigarsa wanda ya bayyana musu shi waye ne cikin sauki sai basu tsare sa na har tsawon lokaci ba,so 40 min da isowar sa aka bashi damar shiga ciki ahakan ma tare da Wani junior officer aka hadasa yamai jagora har Inda imad din yake....

A tsaye ya sameshi baima lura da isowar sa ba sabida hankalin sa gaba daya yanakan takardan daya riko a hannun sa yana karantawa.
Gyaran muryan dayaji ata bayansa yasa ya rufe takardan ya juyo cikin sauri yana waigowa suka hade ido da doc Mehra

Dan lumshe Idanun sa yay ya kuma budewa sannan ya Taho daf dashi,a hnkli ya Furta thank u doctor..doc Mehra dake binsa da kallo har yanzu cikin harshen hausa yace"imad ka tsoratar Dani na dauka wani abu ne ya sameka Wai meke faruwa ne ya naganka anan?imad ya riko hannun doc Mehra baice komi ba Dan Juyawa yay ya kalli officer din daya tsaya akansu kikam,ba yabo babu fallasa yace "can u excuse me pls..?
Gyada Kai Officer yay Babu bata lokaci ya basu waje.

Yana barin wajen ya juyo ya kalle doc Mehra tare da sauki ajijjyan numfashi yace"Believe me har na isa airport zan taho gida aka kira ni..Doc mehra bai jira ya karasa Jin magann sa ba ya tsaresa da idanun sa yana cewa
Another case ko?
gyada kansa yayi a sanyaye Sannan ya dago kansa cikin kallan kwayar idanun doc Mehra din shima
"It's about a girl..
Sai ya runtse idanun sa sosai kamar wanda ya Furta azaba a Kan harshen sa,Nan ya shiga yi ma doc Mehra bayanin halin da ake ciki a tsanake Wanda gaba daya ya sauya musu yanayin su duba da yadda Murya da hannun imad din yake rawa rawa kamar zaiyi kuka.

Babu abunda yake tsumashi kamar yadda gwamnatin kasar Bulgaria sukayi chaaa suka harxuko da hayagaga Suna son su Kare sunan qasarsu takota Wani hali...

"Yace doc wallahy karya sukeyi,nide nasan akwai saka hannun gaggan kusoshin Gwamnatin kasar ne acikin case din shiyasa suke so a xalunci yarinyar a rufe case dinta
karshen ta lallabawa zasuyi su kasheta da ita da familynta don Kar axo a tona musu asiri bafa yau aka soma irin wannan ba,look,All evidences againts d crimes are valid,ansamu shaida akan komi Harda sauran sauran parts din mutane, kawai a binciko iyayen yarinya ne fa abasu yarsu akama masu laifi shine kawai ake so aja zancen

yanzu haka danake gaya maka sun juya maganan Suna so suce Wai lallai sai an wanye ta akan maganan kisan kai datayi, sabida sunsan me suka tanada mata, I'm sure thy already paid some judges againts her,zasuce da sannunta tazo hannun sa bla bla karshe a juya case din

Please Login or Register in order to submit comment