Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

neman sauki ta wajen sa Dan har yanzu ji take kamar bazata iya tattara pieces din rayuwanta ba

Ganin qur'ani acikin kayan da ummanta ta aiko mata ya jefa ta cikin shaukin jin cewa zata iya,da wannan tunanin ta miqe a sanyaye cikin layi Dan duk jikinta babu karfi,daga tayi Dan tafiya kadan saita tsaya,karshen ta haka ta shiga rirriike bango gudun kar jirin dake debarta ya zubar da Ita ga kanta dake mata nauyi da azaban ciwo da kyar take takawa har Allah yasa ta fito waje


dafa bangon kofar tayi sannan ta tsaya cikin karewa ko ina kallo ganin ko ina ya dau shiru Babu motsin kuwa sai rairayin iskan maraici

Sulalewa tayi a hnkli ta samu waje ta dofana daga jikin kofar tadan lafe jin yadda jiri da gajiyayyen numfashi ke kashe mata gabobin jiki..

Dan zaman datayi iska na shigarta yasata ta soma jin sanyi sanyi,Kanta hankara sai taji kamar sanyin yana kkrin shigarta sosai Daga idanuwanta tayi daga can kusurwa ta hango buta a kusa da randan kasarasu
saidai ayanzu haka Wani uban kasala da kwiyuwar takawa ta isa har wajen takeji..

Tafi minti biyar a haka iskan maraice na busota yana shigar jikinta tana danjin dadin shi wanda aranta harta yanke hukuncin ta tsaya a haka tana shirin aiyana Hakan aranta charaf ta soma tsinkayo muryoyinn mata daga can nesa ana ga gidan can Nan ne gidan,a hujajan ta mika wuyarta kadan sannan ta leka,Gani tayi ashe sune daga can nesa, muryan Maman Abdul ta soma tsinkayowa sannan na maman Iman da dayar matan alamn Nan gidan suka nufa

A hujajn ta daddafa isa harta bakin kofa tana leken su gani tayi su ukun sunsha manyan hijabai har kasa uwa manyan malamai gaba daya hirar da sukeyi ya sha musu Kai,tana tsaye har sanda ta tabbata Nan gidan suka dosa,gaban ta taji yana faduwa Sanin halinsu na gulma da son jin kwakwaf,aranta ta soma kawowa bai wuce suce sunzo ganinta ko suce sunzo jin ta bakin yakumbo akan lamarinta ba,Wanda kowa yasani dama can sun saba garzayowa tanan din in suka rasa makafa Duk dama basa cin sa'a da masifar yakumbo Amma haryau basu daddara ba..

Tun daga can nesa suka hau doka sallama asslamu ailakum Assalamu ailakum yakumbo?Wani shiru rufaida tayi bata amsa ba har suka iso daf

ganin zasu iya lekowa ciki yasata wucewa ciki da sauri ta dauki butar kawai ta wuce bayin daki..

Tana shiga ta aje butar ta wuce can cikin bayin ta boye kanta a Dan dungu daga Nan ma tana hangosu tana kumaj in Duk Wani sautin surutunsu,Labewa tayi a kangon karar tashiga lekewo ta waje ganin yadda sukayi tsege tsege a tsakar gidan da alama sunajiran suji Wani motsi ko sauti ne daga ciki
"Yakumbo?
Yakumbo bakin kirar su yafi na akirga Amma sai shiru

A haka saida sikaci kusan mintina goma rufaida bata fito ba Kuma bata amsa ba

sai can ta somajin sautin muryan Maman Abdul
Tace kunga banajin akwai mutum a gidan Nan kuzo mutafi kawai,cikin daka yar tsalle harda tuma maman Iman tace saidai ki leko mana ta cikin daki atake atake maman Abdul ta wuce har bakin kofar dakinsun bakinta dauke da sunan yakumbo Wanda har yanzu basuji an amsa su ba,Kai tsaye abunta ta tura kofar ta shiga,Nan ma sanda ta bata lokaci wajen kare ma koina kallo

Tasan tabbas suna Nan toh Ina kenan sukaje?ganan dai ko ina ba a kimtse ba

..daga Nan tsaye ta juya ta kalle su tace kai inaga fa yakumbo bata Nan kusa musamu waje kawai mu zauna kawai mujirata
,..daga can dayan matar dake ita tadan manyanta tace A'a kam dare fa yayi gaskiya tafiya zamuyi inyaso gobe da sassafe mwa taho,maman Abdul tace da safe fa kikace danke mijinki tsohon sojane baiya gari?toh ni wallhy
Zama daram anan har sai yakumbo ta fito,matar tace kikasan ko yaushe zata dawo darefa yayi,har yaushe wannan shegiyar magulmaciyar kinibabbiyar tsohuwa mai Dan uban warin talaucin ta Gama yawon baranta,mamn Abdul tace aikuwa
yanzu haka zaku samu tana can cikin anguwa ta hangame baki tana famar barbaden magana kwadayayya ce na karshe, ko kanzon abinci kika hadata dashi zaki kwashi labari,ahujajan maman iman tace to ko muma zamu zaga anguwar ne mu nemota?karde harta gaggayawa Wasu labarin rufaida mu muna Nan zaune min sake baki,gaskiya kawai kuzo mu bazama nemanta, ta karashe maganan tana jan tsaki Amma gaskiya bazan ji dadi ba in akace Wasu sunji labari nidake nake neman gindin zama Wajen matar mai anguwa?wallhi wannan labarin ne kawai zaisa ta dena raina min hankli tanai min kallon bitacan, dan dariya sauran matan suka kwashe dashi suka Tafa..maman Iman kenan ki kwantar da hanklinki ai inhar bamu samu labarin rufaifa ba to wallhy babumai samu..

Insha Allah Dole ne a bimu gobe Sau da kafa donjin sabon labarin rufaida,wani shiru rufaida tayi tana famar kallon yadda suketa nishadi suna maganganun su cikin raha da izgili suna kwashewa da dariya,wani Abu tadinga ji na toshe mata numfashi yana kkrin hanata Jan iska gaba daya sai taji hanklinta ya balain tashi kirjinta na mata zafi..

Saukar ruwan hawayen kawai taji akan fuskarta Amma harga Allah bata San lokacin taruwarsa ba..

Waje ta nema Adan gefe daf da Inda ake mata wanka akan dutsin ta zauna tuni Idanunta suka hau kallon bangon karan ta kure waje daya da kallo banda ruwan hawaye Babu abunda ke sauka daga cikin kwayar idanunta....

Muryan yakumbo ne ya dawo da ita,ta miqe tsaye tana tsinkayo shi daga waje ana rafka uwar masifa wa maman Iman,hakn yasata komawa jikin danga a bazata ta isa Inda ta lafe dazu ta Kara lafewar tana kan lekensu,ganin mamn Iman din tayi cirko cirko a hannun yakumbo tana masifa tana cewa "ke safiya Ina zaki shiga awajen Karki sake ki shigarmin bayan gida da daddaren Nan
"....saida gaban rufaida ya fadi yayi rasss tanajin bugunsa da mugun karfi,sai aynzu ta lura Ashe badon shigowar yakbo ba da tuni maman Iman ta kamata a bayan gidan tana ta kuka dan iya abunda suke cewa akanta kawai takeji kokadan bata ji karar tahowarta ba
Dan Bazata iya kayyade tsahon lokacin data dauka ahaka tanajin abunda suke cewa ba,duk taji Kuma ta fahimce su kowa dai so yake yaji meya afku da ita,labarin mumunan qaddarar ta kowa yake so yamaida abun wasa abun nishadi abun kodawa da cin zarafi Dan kawai a muzanta ta ahi dadi Wanda aganinta ko makiyinta bazata masa fatan ya shiga irin halin data tsinci Kanta a watannin da suka shude ba,
Aganinta ko mutum bazaice mata sannu ba ai Sam Sam Bata cancanci madallah ba kamar yadda taga suna dariya suna cewa kwadayin mahaifinta ya jawo mata Kuma uwarta bata bata tarbiya ba,cewa suke dama sune suka auri mai kudi wallahy da ko cin naman jikin su yake zasu zauna Dan haka ita rufaida datayi kisan Kai dama can girmai kaine da rikakken ra'ai ai dama tuntuni batasan maiya kawota duniyar ba ma
Maman Iman tace ai zamuga Wanda zai Kara aurenta
Ba ita Shasha bace kawai Dan an mata auren dole?yo ai mu irin auren da mukeso kenab in har da kudi Amma munafukar yarinya taje ta yayubo abun kunya ta dawo.
Dayan matar tace nifa mamaki yarinyar tabani
Kar cikin yayan yaa malam itace kamila shiru shiru bata da hayaniya Amma kiga Wai itace harda kisan Kai?toh gaskiya hadiza tayi mummunan sake ta bar yayanta suna abunda suka ga dama wannan ai iskanci ne da son zuciya,tabi ta sakalta yara ta barsu suna iyayi agari Wai gasu kyawawa masu diri matan alhazai hajiyoyin falo rayuwar carpet da tiles,har ana Wani kada mana duwawu in munje biki ana mana kallon kashi
Toh yau gata Nan dai mungani karshen alewa ai kasa ce sauran yaran tan ma kaf sai munga karshen su,muna anguwar Nan da ku wallhy hadixa saita dawo abar tausayi,nifa haushinta nakeji
Wawiyar mata mai mugun hali tabita ta kore kshiyoyinta kaf tayi babakere a gida ita kadai,ta dauki uban girman kai ta dorawa rayuwarta tanajin ita ishashiyace mai ilimi gata matar malami mswcheww
Wani uban shewa Mamn Abdul ta buga tace ihehehee anayi munajin dadi ana bari munajin haushi yo wani Matar malam?
Wani darene jemage Bai gani ba,kin manta maman Rashida makwabciyar su ne?
To wallhy Harta katanga takan leka cikin gdan taga me afkuea wallhi tallaho summa tallahi na rantse muku daxu tacemin dambe hadixa sukayi da yllll malam
Tana zaginsa yana zaginsa kaca kaca Wani shewa suka buga,mamn iman tace kice Allah?maman Abdul tana dariya tace ke dai rabu da makaryatan banza a fili saita rinka nuna mana kamar Babu komai tsakaninta da malam bayan mu munsan komi azabtar da Ita yakeyi,bakiga kwanaki yadda tabita kwanjame ba Kullum kafafunta abin layi neman maganin mata,
Hahahahahahaha


sosai rufaida taji zafi Kuma tasha mamakin wayannan bakaken magangnun su dake fitowa a tsakar gidan






*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Please Ana hanquri da yanayin hausa dialect dina i know sometimes my qarin magana is upside down inka gane mena ke nufi shikenan👏🏻🤧

Part1:chapter 30



A tsakiyarsu yakumbo ta tsaya tana dokawa kowannen su harara "tace ke safiya yada haka Kun Wani zo Kun like min agida ashe Dama can hauka kike da har zaki duromin bandaki batare da izini na ba neman a barni da cutan da bansan kanshi ba wato kawai ku tafi kubar mutum da kaikayin gaba shine damuwarku ko?waima meya kawo ku gidana da wannan uban dare Kun wani sha uban dogayen hijabai kamar masu shan jini kun min tsege tsege a tsakar gida kamar wasu mayu.

Juyowa tayi ta kalle maman Abdul dake famar kan washe mata baki sauran matan Duk sun hade rai Amma Banda ita takaicin rashin zuciyarta yasa yakumbo dada harxuka da masifa
Kan Maman Iman ta dawo tace.,"ke hajara yaushe kika soma saka dogon hijabi arayuwarki?
Baki a bude maman Iman ta harxuko zatayi magana da ihu yakumbo tace ke dakata min safiya bana wasa dake,Banda rainin wayo Dan anga bana Nan shine za'azo a jagawalgala min bayan gida?,ai gidan bana ubanku bane, da tsiya na na da arxiki Nan gidan nawa ne ba gidan majazen ku kona mai gari ba,dayan mata da already maganan ya cize ta take taji ta mugun harzuka cikin yar masifa tace Kai yakumbo Kai yakumbo Dan anzo gidankin ne kike haura mana haka kamar wasu Wanda kike so fada ko gaba dasu,yakumbo bata barta ta karasa bama tace yo meyakawo ku?naga baku saba zuwa bane cewa kuke gidana gidan bola Gani mai warin talauci haka kurum sai Kuma in ganku a tsakiyar gidana wata har tana shirin shigemin ban daki da tsakar dare sai in kyaleku?...kufada
min abunda ya kawo ku kokuwa in sauke muku takaici in rakaku dashi har bakin kofa da buhun sa..

Da rawan jiki maman Abdul ta karaso ta matso daf da yakumbon tana famar sauke murya kasa kasa tana narkewa cikin salon lallami Haba yakumbo Haba yakumbo Tsohuwa mai ran karfe Allah ya huci zuciyarki Banda hade wajje irinna maqiya da yan gulma ke yakumbo har kin yarda zamu iyacewa Hakan akanki?

Shiru yakumbo tayi batama kulata ba ta shiga gyara ma kayan data shigo dasu zama tarkacen saiwowi ne da Yan kayan abinci da baza a rasa ba, suna daga tsaye kamar mayu ahakn ma saida suka shiga lelleka ledojin Wani Kallon kallon suka maidawa junan su dayar matan ta Dan tabe baki,Tuni Maman Iman ta danne xuciyarta ta hau murmushi"Cefane kikayi haka ne yakumbo?Haba yakumbo walaknci fa babu kyau Annabi
saw yace ka girmama bakinka ko Yaya suke,yanzu bazaki saurare mu ba kenan?sanda yakumbo ta kammala abunda yake sannan ta juyo tabisu da kallo daddaya tace ke safiya bana son tsugudidi Banda kin maida kanki wata Shashasha Ai knsan Nasan abunda ya ya kawo ku,gulmace sai ku fadeta inji..maganan yay musu zafi Amma dai haka suka shanye atake suka hau dariyar karfin hali Suna yake hmm su yakumbo kenan Ashe dama kina da labarin shine ko ki aiko mana mutayaki jaje, kobabu komi ai hadiza yarki ce duk abunda ya afku da hadiza kema ya Sameki

Da uban yanayin mamaki yakumbo ta kallesu hanklin ta Adan tashe tace Mekenan ya same hadizar?ciwo tayi?maman Iman tace habawa yakumbo A'a, maganan rufaida fa akeyi
dayar matan tayi saurin cewa eh rufaida yar gidan yaa malam ba?shine mukace toh bari muzo muyi muku jaje Ashe Kuma abunda ya faru kenan...
Mammn Abdul caraf ta tsoma baki "nasha Mamkin Jin Wai rufaidace ta kashe mijinta,dama ace murja ce nasan ta akwaita da baqar zuciya Yo Yakumbo mexaisa yarinya kamar rufaida wanda take shiru shiru ta aikata Abu makamancin Hakan fisabilla..
gaskiya abunkam baiyi dadi ba..Wani shiru yakumbo tayi tana Jin kowannen su sai ayanzu ma hankalinta yabi ya koma kan rufaidar data bari a daki kafun ta fice take take ta shiga tambayar zuciyanta shin Ina take Dan tasan wayyanan munafukai dolene su leka daki su dubata,Adam atakaice yakumbo ta Dan dakata da sauraran su tanayi tana yafece mayafinta daga kafadarta datake shirin dorawa akan window sai tayi kamar sudin take sauraro,daf data Kai wajen ta karkace mitsimitsin idanunta da wayo ta leka cikin dakin Ganin Babu kowa yasata juyowa garesu cikin sauri ta tsura musu ido sosai.

maimakon taji Wani sanyi aranta sai taji gaba daya hanklinta ya tashi"..toh Ina rufaida ta shiga?yarinyar da ko wani karfin kirki Babu ajikinta yau mezatace wa hadiza in yarinyar Nan guduwa tayi


Cikin wannan tunanin maman Abdul ta katse ta tana cewa..
"Komi na da duniya yar haquri ne inba ana haquri da juna ba haka yaran mu zasu taso cikin wayanda basada zurfin tunani...
Yanzu abunda rufaida ta aikata dame yayi kama?itama hadiza data kama mijinta da kokowa Duk sai ace ita take koyarwa yayanta rashin uzuri
Arayuwa

Kisan Kai fa Haba wallahy rufaida ta tafka babban kuskure ma rayuwarta,yanzu da wuya in za'a sake samun Wanda zai kwasheta a matsayin matar aure, inba haka ba saidai ta Kare haka a yawo a layi karshenta kiji ance Wani ya danneta ya narka mata cikin shege..

Cikin jin zafin maganar yakumbo ta karkada kai tace iyyyee maman Abdul toh insha Allah saidai hakan ya Kare akan yayank,ai ganan yarki hunaisa ta taso,Fatanki ya sari guntun kashinki,Duk abunda kika Furta akan rufaida saiya Kare akan naki yar amma ba akan rufaida ba..

Kujin min mata da tsugudidi Dadin Abun dai Qaddara ce wacce take Kan kawo Duk wanda yace da ikon wayonsa ko dabarar sa yake rayuwa saiyaje can yaji dashi...

Haba ku baku San Kan labari ba zaku ta tsine ma rayuwar yarinya albarka Allah saiya sakawa rufaida..kuka yakumbo ta fashe da shi,"..munafukai kawai algungumai
Rufaida ta kashe mijin ta saime?
Inadai banaku majazen ta kashe ba .safiya hatke ce zaki dubi tsabar idona kice rufaida zatayi kwantai ta dau cikin shege a layi?Ai Dama can nasan mutunci na kawai kukazo ci...
Toh insha Allah rufaida zata dawo cikin hayyacinta kuma zakusha mamakin mazajen da zasu nan nemanta Inhar muna raye daku bixinillah shekaran Nan bazai Kare ba rufaida zatayi sabon aure ba Yayanki ne zasu Kare a bin layi

Maman Iman taja tsaki"Yo yakumbo daga fadar gaskiya kin kama kokke koke waike mesa bakida fahimta ne

Dayan matar da dama haushin yakbon takeji tace
Tayaya kuwa zata
Fahimce mu kinsan ai gaskiya daci gareta,yarinya dai bata kyauta ba,Kuma mu bazamu dena fadar gaskiya ba..rufaida ta tafka abun kunya Kuma kuskure tayi babba arayuwarta Dan haka dolene mu fada..

Cikin sautin kukan yakumbo ta harxuko
Tace to sannu baqar makira sarauniyar masu gaskiyan karshen zamani Alhamdullhi tunda bake kika haifeta ba,abun kunya bama ke ta jawo ba,hakama banga ta inda kuskurenta ya shafe rayuwarki ba, In zancen kuke so sai kuyi da wanda ya halicceta Kuma ya Dora mata wannan qaddarar Amma ayanzu kam aikin banza kukeyi Wai malam yaki noma Dan zakka..

Dariyar takaici maman Abdul tayi to ke Yakmbo dakika dau abun da zafi cewa akayi Wani abu na cin zarafi kawai fa magana mukeyi na jaje atsakaninmu
Meye amfanin zaman tare in ba'a gaya ma juna gaskiya ba.

Wani gaskiya ne anan safiya?ke kanki kinsani yau
Ko qur'ani na dauko na aje agaban ku akace ku rantse akan abubuwan da kuke furtawa akan rayuwar rufaida wallhy bazaku iya dafawa ba sabida bakusan asalin abunda ya afku ba..

Da sauri dayan matar tace
"Toh aje ahakan me mezai Hana ki fayyace mana yanzu?

Mamn iman tace kwarai kuwa gaskiya ne aisaiki fadama na asalin abunda ke faruwa
Wala Allah in mukaji ata Wani waje ana fadar Hakan saimuma mu fahimtar dasu koya kukace?dukansu suka ce ehh..
Shiru yakumbo tayi sanda ta Dan samu nitsuwa a xuciyarta sannan ta dago ta kallesu"..in a tunanin ku rufaida tayi kisan Kai saboda anmata auren dole ne kuje Allah ya hada yayanku da irin tata qaddarar

Yakumbo wannan wata irin magana ne

A masife yakumbo tace bazakuji gulma abakina ba..
Iya zancen kenan rufaida ta kashe mijinta abisa qaddara in Kun dauka oho in baku dauka ba kune can kuyita kirkiran maganganu Ai Allah ba axxalumin bawansa bane kowa zai gani a kwaryan cin tuwon sa..

Tsabar takaici maman Iman bata bari ta karasa ba a harzuke tace
Toh Ina kika boye ita rufaidar?inku bazaku fadawa mutane abunda ya faru ba ai ita yarinyar tana da hankli zata fada.

Wani irin daure fuska yakbo tayi
Toh ban fada ba uwata ta farar gada,
Inji didim kin hau duka na,..Inta gaya maku mezaku mata Banda ku kirata karuwa ko kuce mata zata Kare abin layi,yafa kamata ku wuce kuban waje inada abubuwan yi agaba na.

Tuni dayar matan taja hijabinta ranta a mugun bace ta fice,maman Iman tana ta surutai ta Inda take shiga bata Nan take fita ba,maman Abdul kam waje ta nema ta zauna Aganinta in aka ja Cece kuce zasu iya Jin Wani abu daga bakin yakumbo Wanda Banda buhun baqar magana ba abunda take saukewa,tana ko dasa aya ta bawa banza ajiyarsu ta wuce gaba ta bude kitchen tana tana Dan dube dube Kan su hankara ganinta sukayi da katoton muciya ta iyo Kansu,aguje suka nade hijabansu suka safce waje.

Wani irin balbalin masifa yakumbo takeyi ta Inda take shiga bata Nan take fita ba"..safiya har gidan mijinki zanzo in Sameki in gurje gandan bakinki,ke kuma hajara saidai inbanga tsohon uban ki ba,Shegu kawai algungumai magulmatan banza
Yaran da ka isa kayi jika dasu swazo gabanka sunai maka iyeyi,..Me kuka sani game da rayuwa harda zaku gayamin rufaida zata Kare abin layi yan Iskan yara kawai daga anyi haihuwa daya biyu a gidan miji shikenan saikuna daukar kanku kamar wasu jakadai..yakumbo tafi minti goma a kofar gidan tana wanke su har Wani rawa rawa jikinta yakeyi tsaban a harzuka.

Sanda ta tabbata sunyi nisa sann ta jawo kafafun tsufanta ta shigo ciki tana tafiya tana mita aranta tana tunanin Inda rufaidar ta shiga har ake wannan hayaniyar bataji duriyarta ba
Da Dan karfi ta bude muryanta da niyar kirar sunanta tana bude bakinta sai caraf suka hade ido da rufaida,wani irin kallon yakumbo tabita dashi ganin yadda ta sunkuyar da kanta can kasa,a lokacin daf ta fito daga bayin kenan jikin ta har na rawa rawa,kallo daya yakumbo tamata tagane Ashe duk tanajin surutun su iya kuka kam rufaida taci duba da yadda jikinta ya sake yay sanyi ta dawo tamkar wata marainiya marar uwa da uba banda uban sheshheka da jan zuciya Babu abunda take saukewa da kyar ma take daga kafafunta tana shirin karasowa dan alokacin ji take kamar ta runtse Idonta taga bata duniyar mai gaba daya.
.






*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


Part1:chapter 31


Ba zallan jiki ba hatta muryan yakumbo rawa ykeyi ayayinda ta karaso kusa da ita cikin sauri ta rirriike ta "rifaida Ashe kina Nan aketa magana banji duriyarki ba?dudduba fuskarta ta shigayi a hnkli tace na shigga uku ni A'i Yaya naganki haka?kukan me kikeyi rifaida Wani abu sukayi miki?kifadin waye acikinsu ya zageki yanzun Nan inbi sawunsu in sauke musu buhun rashin mutunci..

Wani matsanancin kukane ya kufce wa rufaida Wanda shi yasa yakumbo Jin nakaso itama sai tabita ta barke da Wani uban kuka kukan kawai sukeyi atare Babu mai kakkautawa da kyar rufaida ta kufce a hannun yakumbo tayi gefe durkushe akan gwiwanta cikin sautin wahalallen kukan dake fitowa da hucin nakasashen numfashi Wanda take kwaceshi da kyar,cikin wannan yanayi tace
,"..Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun yakumbo nashiga uku,rayuwata ya lalace..yakumbo ya zanyi da rayuwata?
Da sauri yakumbo ta rusuna agabanta tare da dagota daga durgushen ta take Nan take ta manne ta da jikinta ta rungumeta sosai tana shafa mata Kai da jiki.."Yi hakuri rifaidata,Ki saka ma zuciyarki dangana ki yayyafawa ranki ruwan sanyi,kuka ba naki bane rifaida adduan dai shi ya kamata muyi Allah ya fiddake daga cikin wannan lamarin lpya,kul Kar ki bari maganganun su ya dameki,kowa yasansu sune manyan algungumai magulmata a anguwan nan Kar halinsu ya dameki,kaf dinsun Nan basu da alqibla arayuwarsu basuma San abunda yake musu ciwo ba,Dan kuwa da sun sani da kodan albarkacin y'ay'a matan da suka haifa acikinsu ai bazasu aibata naki qaddarar ba..

Kiyi shiru abunki rifaida ki daure ki kwantar da hanklinki,namaki alkwari Dani da Hadiza muna Nan daram tare dake bazamu taba kyale wasu makirai Wanda basusan Kan magana ba suzo suna cuna ma rayuwarki tashin hankli,Sam Sam bazamu yarda ba, damuwa banaki bane,samun saukin ki shine a gaban mu kinji auntagale? Kuka kawai rufaida take tamkar wanda bajin maganan yakumbon takeyi ba Dan ita kadai tasan iya abunda takeji acikin ranta da xuciyarta,already abubuwa dayawa sun riga sun toshe mata kwakwalwa da numfashi suna famar nakasata mata gabobin jiki

Acikin xancen su maman Iman in akwai abunda yafi damunta baifi cewa da sukayi ummanta tayi fada da yaa malam ba,gaba daya sai taji hakan ya daga mata hnklinta sosai Dan kuwa tasan wacece ummanta,Abunda kuma zaisa ta daga hanklinta har tayi fada toh lallai babban al'amari ne bana wasa ba..

Maganan zuci kawai take cikin juya tunaninta akan mekenann yake afkuwa a gida Babu abunda bata shiga kullasa acikin ranta na bakin ciki da damuwa ba..

Banda lallashin ta da kalamai Masu sanyi da karya xuciya Babu abunda yakumbo takeyi har yakumbo ta gaji ta janyeta suka koma ciki bata wani kula ta dawo hayyacinta ba ba tsaban damuwa da jimamin kuka daya Gama rudata ya toshe mata madigar yin tunani


Suna barin tsakar gidan saiga bullowar rahamatu yar gidan malam dalhatu mai shayi Wanda tuntuni take labe ajikin dangar waje tayi luumui acikin duhu tanajin Duk Wani abun da akeyi ata ciki kuma komai da aka zantar anan din a kunnenta ya kare Danta riga da Tasha alwashin saita tonawa Umma hadiza da yayanta asiri..

A rakube ta zame ta falfala da uban gudu cikin sanda ta nufi cikin anguwar agaggauce


Tafiya take sauri sauri Kuma a karkace,wanda tsabar saurin datake yi daganan zaka iya jiyo sautin bugun zuciyarta gaban ta kawai take kallo damuwarta baifi taje ta fetsa gurmin data debo yanzu ba,aikuwa kamar wacce zata kife taci da kasa haka tayita jefa kafafunta galau galau akan hanya bata tsaya ko ina ba sai a dakin matar mai anguwa rike da cikinta tana yar haki
Assalamu Alaaikum
Sallama alaikum

Dake ma dare ne dakyar ma matar mai anguwa ta fito
Sannan ta kulata .
A tsattsaye ma ta tsaya daga bakin kofar fuskarta a matukar daure murya ciki ciki tace rahamatu lpya naganki a wannan Lokacin,Ina ita talatun? fatan dai bawani gurmi kukaje kuka hada ya afka daku ba?

Rahamatu dake kokawa da numfashinta cikin yanayin xakuwa tace A'a Ranki shi Dade labari da dumi dumin sa na kawo miki,wallhy yanzun nan nabaro kofar gidan yakumbo inda Naga Rufaida yar gidan yaa malam da idona tanata kuka..
Matar mai anguwa tace mene?Ki kace Kinga rufaida?yanzun Nan fa su maman Iman suka bar Nan since basu ganta acan ba

Cikin zaro Ido waje irin na magulmata rahamatu tace
Wallhy karya yakumbo ta shera musu,nida idona na ganta ai agidan yakumbon suka boyeta Ina labe abayan zana naji tana tsige su maman Iman da masifa,toh bayan tafiyarsu ni ban tafi ba kawai caraf saiga rufaidan ta fito daga Wani waje

A firgit matar mai anguwa ta juyo
Tace Toh Bayan haka Kuma saime kikaji rahamatu?me suke cewa kifadmin komi Karki

Please Login or Register in order to submit comment