Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakai mai kyakkwar zuciya da kaifin tunani toh tabbas zaka iya apreciating din tarayyarku harka kuma karu da kalar baiwar da Allah yay masa.

"Har cikin ransa yakejin malak ce kawai zata iya tayasa yaqi wajen tallafawa rayuwar rufaida duk dama har suka kammala tattaunawar su bai iya kawo hirar rufaidan sosai ba.

He just mention dat he met a girl dat change his life kuma tana daya daga cikin abunda zaisa shi zuwa kano,tare da cusawa malak din ra'ayin jin son zama can din tare da shi.

Yana zaune cikin tunani doc ya fito sanye da wani suturar na daban marar nauyi yacemai ya tashi su tafi ahakan ma imad bai kyalesa ba tun fitarsu yake masa surutu,haka shima ya rinka cikashi da surutu akan komawarsa kano daya darsa aransa kamar wuta, shidai damuwar sa baidi doc ya taimakesa ya koma ayanzu ba dan kuwa babban damuwar sa ne yaga rufaidar sa,sosai yaja hnklin doc basu bar kofar gidan ba har saida suka kai kusan karfe sha daya na dare awaje har sanda doc ya amince mishi cewar zaiy wa yaa sheik din magana sannan ya hakura ya barsa

ganin dare ma yay sosai yasa shi dayan kawai ya tafi gida abunsa yabar doc haryanzu a tsaye abkin kofar gidansa cikin tunani Hanklin doc mehra bai wani kwanta ba sam,a haka dai ya dawo cikin gidansa a daren, within 20 mints yana zaune a falo saiga kirar sa nacewa har ya isa gida,bayan sun katse wayar imad ya nufi main falo bai hadu da kowa ba har ya shiga can ciki ya hau stairs ya nufi dakinsa direct ya hau rage kayan jikinshi daga nan bathrum ya nufa ya hau wanka ya dade a bathtube cikin ruwan dumi yanajin yadda nitsuwar samun cikar burinsa yake kan baibayesa.

Ajiyar zuciya game da saukar numfashi yakeyi,hade da wani kakkarfan shauki ya Lumshe idanunsa sosai cikin son tuno da kyakkwar fuskar rufaida,har kuwa ya soma hango kamanninta dayake yawan masa gizo, sai kuma fuskar mufrad yasoma masa bayyana masa yana masa bibbiyu yana gamutsuwa masa da kamanin rufaida

Cikin sauri ya bude lumshahun idanunsa sakamakon wani strange bugun da zuciyarsan ta shigayi atake wanda tabbas hakan yay saurin barazanar dauke masa sauran nitsuwar sa data katse masa tunanin sa na rufaida mai sa wa zuciyar sa nishadi da jindadi...

A ransa yace
"Where d hell is dis asshole?har yanzu bazai kirani ba?..

Yana gama furta hakan ya shigayin marmaza dan ya kammala wankan sa,within some minutes ya fito daure da towel a kugunsa batare da ya tsaya aikata komi ba ya nufi gaban mirror ya dauka wayarsa dayake kashe har yanzu,kunnawa yay sannan ya koma bakin gadonsa ya zauna,dialing number mufrad yay shigayi tana ta ringing Ba'a daga ba,kirjinshi yaji tanai masa wani irin nauyi,tsaki yaja ya mayar da wayar gefe ya ajiye hanklinsa ba akwance ba,nan ya shiga gogge ruwan dake manne a faffadan kirjinshi ya bi ya mutsuka manshi ta lor'el moisturizer mai dan uban qamshi da balain tausasa sassan jiki dasaka jin sanyi a zuciya

White Harmain half handed jallabiya yasaka ta masa damas fuskar shi tayi wani fresh tana haskawa sosai,gaban mirror ya nufa ya fetsa turaren sa na guilcy absolute sama sama danma sabida sanyin qamshinsa yakeson fetsawa da dare donshi sam bayason qamshi mai qarfi ya cika damunsa inyana bacci, Ya fito a nitse,yana saukowa kasa ta main falo sukayi gamowar kicibis da a'inau wadda ta karyo kwana cikin tafiyarta na sanda dayy mugun alama da sam bata so ajiyo sautin takunta,
Suna hade ido yayi saurin dauke idanunta anata ya mayar qasa cos babu wani suturar arziki ajikinta sai uban doguwar sexy piere nity mai sharara pink colour data sanya shi da jackrt dinshi ta barbaje suman kanta dayasha kitson attachement ya biyo har ta gadon bayanta ya kwanta luf..

,shikuwa bai iya dauke kansa anata ba tsabar rudewar dayayi sai yaji gaba daya baiji dadin yanayin daya kalleta ba dan kallo daya zakayi mata kasan bata cikin hayyacinta hade da yanayin dayaga shigarta wanda bai dace ta fito tsakar gidan haka ba duk dama yasan zai i ya uzartawa,fuskar ta ba asake yake ba ta dan tsaya agefe batace mai uffan ba,duk iya daukar kan da tayi mishi saida ya lura da cewa tana cikin halin damuwa da fushi,he knows bazata soma masa magana ba,dan shiknsa yasan kalar girman kanta gyran murya yay ya daure cikin sakin fuska yace "mrs muff kece anan,tayi shiru,yace Is eveything alright?ya karashe furucinsa yana kallon agogon dake manne a bango

"Uhmm kawai tace Just becos she dont want him to notice her bad mood so zata dan daure ta amsa Atakaice tace masa a shaqe tace.."Yeah..im just..sai kuma tayi shiruuu bata kara cemai uffan ba,aranta tanajin wani nauyi da giggiwar yin masa bayani..karamun murmushi ya saki kasar wuyarsa yace.."its ok.,nan ma
Batace uffan ba ta kama hanya shiru a kuma izzance kamar zata wuce shi yabita da wani irin rudaddiyar kallo,har ta wuce din sai taji sautin soft voice dinshi ata bayanta A hankli cikin sanyin murya yace..mufrad bai kiraki bako?..hade da tsananin baqin cikin tuno mata mufrad din dayayi ta juya ta darsa masa kwayar idanunta dat speaks ego,cos actually ba don mufrad ta fito waje tana dube dube ba kuma ta tsani amata kallon hakan,aima inda sabo ta saba da halayyar mufrad,she cud neva waste her time to come down nd check on him at night as big as she feels about herself,shikuwa imad yagama daukawa aransa cewa damuwar hakan nema yasa ainau fitowa tana zaga gidan cikin dare ,While ita ayanzu haushin rashin dawowar zara ne kadai yake hatsala ma zuciyarta wutar takaici yana mai cinna ma kirjintan gobarar balai tanajin kamar ta haukace dan fushi.

She cudnt answer him on time sabida batasan me zatace masa ba,she cant lie or defend her self eida,sabida tana mugun ji dakanta,har ila yau ba ajinta bane tayi ma wani karya ko bayani,a matsayinta na babban mace mai ji dakanta matuka evrthing shud just be as it is she just dont care.

Babu yabo babu fallasa ta daure tace "yes,He dint call kai ya kiraka ne?...da dan sauri imad ya amsata yace "no,me too..but i think he is out of signal ayi haquri damu dai.

Kwafa tadanyi dan bata so ta amsa shi da kalman da bazai masa dadin jin ba,First time dayaga tadan sake fuskar ta har ta dan murmussa masa da gefen baki,shima murmushin ya mayar mata Cos balain tausayinta ya soma ji aransa tuno da gulman da zarah ta rinka masa akan zamantakewar auren su da mufrad nacewa baya bata lokacin sa kuma baidamu da ita ba.

Murya a kasa kasa tace"Alright,im going in saida safe..
kafin ma ya dago kai ya amsa har ya hangeta a can gaba ta wuceshi cikin sauri tana tafiyarta kamar batason ya kara tambayarta wani abu,hade da daga kafadunshi ya sauka cikin falon yana dan tabe bakinsa ya kunna dispenser ya dau cup ya tari ruwa yahau sha aranshi sam baiya iya ganin laifin mufrad din shi,its natural ,koda abunda muffy yakeyi bai masa ba dadi ba dole ne dai ata wani bangaren zuciyarsa sai yaji da zimman yin masa uzuri.

A'inau kuwa tsaki ta rinka ja data lume daki tare da sauke kakkarfan ajiyan zyciya tafada cikin gadonta ita daya tana huci,she saw imad,kuma sosai ta shaqi qamshin turaren sa and it just remind of how much she needed her man emotionally and passionately...

Wani irin cillo da kafafunta tayi ta makawa pillows dinta duka hade da yin watsi dasu kasa cikin zafi da kunan zuciya
"To hell with mufrad
mschew,ta mike zaune tanajin tsananin feeling din sha'awa yadda yake tattaso mata, bai mata ba ta koma ta kwantar da kanta akan pillow ta gumshe idanunta sosai ta saki wani marataccenr kuka,wai har imad ne zaice mata baisamu mufrad awaya ba?tasan karya kawai yakeyi dan rainin hankli kawai, cikin wann yanayi bacci mai nauyin gaske ya kwashe ta,around 7:am qashe gari imad na dakinshi har ya kammala sallah da karatun qur'anin dayake yi a kowani safiya sai ya dan kwanta a rigingine asaman gadonsa idanunshi a lumshe sosai kai kace bacci mai nauyi yakeyi,nitsuwa sosai ya taroma zuciyarshi yana kkrin connecting din nitsuwar da sauran gangan jikinshi batare da ya motsa ko inansa ba
cikin yanayin sanda sosai yaji kamar an tura kofar dakin,still yana shiru,har wanda ya shigo din ya bude kofar a hankli ya karaso,mamaki ne ya cika mai kirjinshi jin bai taba jin kalar qamshin wannan turaren ba hade da mummunan faduwar gaba wani irin qamshin oud ne mai mugun tada hankli anhadeshi tare da wani abu kamar turaren aljanu tuni zarninsa ya gauraye dakin da wani irin rudadiyar yanayi,shirin bude idanunsa yakeyi amma kuma sai yaji ya kasa har sanda yaji sautin takun mutum adaidai kanshi,daf kusa sosai aka tsayamai akai bai cika jin tsoro ba amma yau saida yaji tamkar zuciyarsa datayi tsalle ta diro waje..
Zarah dake tsaye akanshi tanata kallon kyakkwar fuskar shi cikin tuno da abunda sukayi akansa agidan boka yanzu,sosai ta karajin ta aminta da lamarin zee zee ganin imad ya kasa bude idanunshi duk dama alamu sun nuna yaji shigowarta,cikin tsabar nishdi ta lumshe idnunta sosai a hnkli ta furta "kare ki zee zeen amana,tuni tajii wani wasai dukkan wani fargaban datazo dashi ya kawar

hannunta dake dunkule da wani garin magani ta bude ta hau hurawa ata kan setin fuskar imad tana kammalawa tayi saurin nufar kofardakin tayi waje shikuwa daya shaqo iskar magnin
Kamar an kwada masa dutse akai haka yadinga jin ciwon kai da tsananin bugun zuciya,ahaka yana kkrin furta wani addua a saiyaga wai bacci yay awon gaba dashi..

Tun 6am A'inau ta farka a mugun firgice kamar wanda ake biyota da zukeken wuka acikin mafarki wani kantamemen tsaki ne ya kufce daga bakinta ta sauka kasa durus tana kkrin gyara zaman jacket din nity dinta dakin zarahn ta nufa direct bata ganta ba ta xube a kasa jin tsaban takaicin dayafi wanda ta wuni dashi jiya yana cikkar zuciya"
Awajen akasa ta cigaba da zama tana sake saken yadda zata soma yima mutanen gidan bayanin inda zarah taje cos tasan babu makawa sai an tuhumeta tunda dai dolene taje ta gaishe su da safen nan,gashi ita sam batada salon makircin dazata iya ammafani dashi wajen fidda kanta batare da angane komi ba,dole ne kawai yau din nan zarah tabar mata gidanta a gaskiya dan bazataba iya ba,tana zaune a kasa cikin zanta hakan aranta taji kamar an bude kofa
Aikuwa tana dagowa sukayi ido hudu da zarah wacce tasha golden lace ta cakka dori ganin ainau yasata ta dora hannun ta a kugu kalar masifa tana yatsine,Ainau dake jin kamar tayi pepper soup dinta a hatsale ta hayayako
"Wher the hell have u been?..kina hauka ne zarah?nace kina hauka?kinsan kuwa a inda kike wannan haukar?nan fa ba gidana bane gidan surukanai na ne,for god sake mai zaikaiki kwana awani waje? wani irin abun magana kikeso ki jangwalo mun?..cikin yangataccen fari da ido zara ta juyo ko ajikinta"..saida ta karasa shigowa cikin takunta na makirtatun mata step dayan biyu ta wani dakata agaban ainau tahau zuba mata tuwon harara
Tace uhum"Sannun madam mai gidan surukai,..anyways my mission is done and completed,im leaving right now..happy?..Atake Ainau ta lumshe idanunta cikin tsananin takaici tanajin kamar kuka ne mai tsuma zai kufce dagata cikin magwaronta
Ta daure matukar daurewa amma sai taji kamar itace bataiwa zarah daidai ba,she just know dat she cant do this right now..
Ita kanta tasan takan hada harda haushin frustrtion dinta akan lamarin zarah,.but still doesnt change d fact dat tana son yau yau din nan zarah ta koma gida,
Amma ba acikin fushi da ita har haka ba,muryn ta harna rawa tace
"Okay,...Zarah im sorry i talked to u dat way,cikin sanyin murya sosai ta fada tana lura da yanayin zarar data kile matkar kilewa
Bata damu ba ta makalkale murya ta cigaba"Jiya nayi ta jira koda zaki dawo in baki hakuri,to to i tot ure with zeee sainaga kuma har dare baki dawo ba,i i got upset,u knw how things are here,is not allow mace tana fita agidan nan tana yawo anyhow, aynzu akan haka sai kiga magana yaje har kunnen yaa sheik daga nan aure na da mufrad basai ya fara rawa ba?please am sorry ok.

Ganin yadda take kame kamen yasa zarah tuntsirewa da wata mahaukaciyar dariya...Tuni ainau taji ta mugun harzuka kirjinta har yana bugu a 360,
Kamar zata fashe tace What d hell is funny?Zara ta cigaba da dariyar tana cewa go on, fool urself Ayn,ko baki fada ba nasan jira kije in dawo ki koreni agidanki so can u please stop pretending?and u know what bana bukatar taimakon ki ayanzu,in imad ne na same shi..wacce tasan mutunci na da kimata ta share min hawaye na.

Cikin dirin takaici aynau tayi saurin tsareta,a fusace tace" me kikawa imad din?zarah bata kulata ba tace ..alright fine zarah do as u pleased okay,anma kisani nagaji dake kinaji na ko?and stop camparing me with dat ur dirty devilish,.filthy friend...kidena.. tunda dan nayi miki laifi nabaki hakuri kike neman ki raina ni to hell with u and get out of my house this minute..

Kan zarah ta bude baki ta yi magana sukaji wani heavy knock abakin kofar daki,atake kirjinsu ya hau bugawa kowa ta shiga kkrin binne kalar nata tsoron,"who is it?zarah ta daure tayi tambayar" sai dai..muryan da sukaji ya sa su gwalo idonsu waje atare,.."imad?
Da bala'in sauri zarah taje ta bude kofar,ganin ba shikadai bane yasata dan sassauto "h.ey h..ey...ta furta a rarrabe dan ko a mafarki batayi tsammanin imad zai taka kafarsa kofar dakinta ba,shima hey din ya mayar mata babu yabo ba fallasa suka tsaya daga bakin kofar
,mufrad dake tsaye abayanshi yana shiru danko kallo bata ishe sa ba,a sace ta juya ta kalle ain dake tsaye cikin son taji me ake ciki dagata waje.."zarah ta hau murmushin mugunta ta kalle mufrad da karfi tace "Gud morning Captain..,duk da karfin xcitemtn din datasa baisaka shi ya dago kansa ba,just normal ya amsa da cewa.."how u?saukar diran miskilallen sautin muryan sa yasaka ainau dake ciki lumshe ido zara ta hau washe hakwara,"in fine kune yau anan?im sure dai anyi batar hanya haha hmm,uhm mad baby im so glad to see u,tayi sauri ta kwco hannunsa daya cusa aljihu ta rike,pls ka shigo mana please cmon..tana shirin jawosa ciki idanunsa sukaci karo dana ainau data juya musu baya cos nity ne ajikinta,"shima cikin saurin ya kwace hannun sa ya koma waje cikun sauri,a hnkli yacewa mufrad i wll see u down stairs,bai jira ba ya sauka kasa mufrad yana dago ido da mamki daga bayansa yasaukesu akan a'inau dake tsaye,kallo daya yayi mata gaba daya yaga yanayin shigarta sai yanzu ya fahimce abunda yasa imad tafiya ya barshi anan,kallon ta yake ganin ba marabarta da tsirara,wat d hell zata fito harnan da nity?ransa yaji ya sosu sosai.harara ma ta banka masa Tace"Ure back?ta daure ta furta kmar an rogeta...kallo bata ishe sa ba ya kada kansa batare da ya amsata ba ya juya ya sauka cikin fushi.

Tana kallon inda yabin ta dafe kirjinta
Dake mata wani maqudan zafi tanaji tamkar an cakka mata kibiyar mashi.

Sai kuma ta rasa ta inda zata saka kwayar idanunta da suka rine bayan muffy dayay banza da gaisuwar ta zata kalla ko annoyin fuskar Zarah?,after all dat happen she just cant turn to zarah right now..da bango ta jingina ta hau kuka mai sanyi ko zarah dake shirin yanka mata buhun rashin mutunci saida taji tana mugun jin tausayinta.
Ganin kamar kukan zaiyi yawa ta dakatar da ita Tace "ehm ehm ehem U gotta go mrs captain..wanda kiketa jirar gashi nan ya dawo..kije ki sameshi,kinga tunda an koreni bari na hau tattara kayana masu sona nasan zasu neman wajen zama agarin abuja,Aure na kuma saidai kiji anayi,but for now im leaving ur house with due respect my sister.
Da gatse da zafin zuciya ta karashe maganan tana gatsine tana kallon fuskar a'inau sosai.

Cikin kuka mai rurin azaban rudewa ayn tace "Attitudes like diz was part of my reasons 4 being skeptic with u zarah...just diz lil ish n u dropped me like someone holding unto a burning coal...it is well...ba wancan shegiyar kawarkin tazo ba? I'm not blaming u for anything coz it was all my fault,Am sorry...was just thinking u would be considerate...
Yadda ta karashe maganan cikin makirtacen kuka sosai ya bawa zarah tausayi duk dama harta zo ta wuceta batace mata uffan ba,tunani take yadda zata sauya tsarin wasar data soma,tasan muddin tana son samun cikar burinta dolene ta bukaci kudi matuka,kuma banda ainau batada wanda zaina bata kudi akai akai,so hala zata iya sauya tsarinta nabarin gidan hade da qamshin nasara akan imad dataji yau dayayi ma zuciyarta dadi.

banda dalilin haka taso ne ta wajiga ainau ta walakanta sosai,.






*™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


Part1:chapter 39



Acikin kunnenshi ta bude kofar dakin duk da tunani mai nauyi da zuciyarshi takeyi bai hanasa shaqo yanayin shigowartan ba, waje ta nema ta tsaya durus tana kallonsa dan bazata iya cewa dason ranta ta biyo bayansa awannan lokacin datakeji kamar ba a cikin hayyacinta take ba.
Rashin iya bude idanunsa dayayi ya sa wajen ya dauka da wani irin shiru sam Shigowartan bai katse masa tunanin datazo ta iske shi yanayi ba,tun daga ranar auren sa har izuwa yau inyatuna,wasu sukance sukanji kansu kamar a saman gajimare tsabar kwanciyar hankli da farincikin auren su amma shi haryau baisoma jin wannan ba,aure dai yasan yana cikinshi da wacce yake ganin kamar yana so amma bazai iya cewa zuciyarsa a nitse take da aurensan ba shiyasa ma sam ya kasa gane ma kansa bare ma ajega y fahimce matar sa Ai'nau,alot of times in his heart yakanji matukar dana sanin auren ta,saidaii tabbas akwai wani bangare a zuciyarsan datake hanasa tantance komi saiyaji kamar eh dagasken sonta yake yi kuma bazai taba iya rabuwa da ita ba,shidai yasan acikin Rudani yake rayuwar sa Ko ainau ta fahimce shi ko bata fahimshi ba oho,shikadai yasan abunda yake damun sa aransa yanzu.

Ainau dake tsaye kansa bakinta gumm bata iya ko jan numfashi kwararra, kokowa take da fushinta dan kar zuciyarta tayi bindiga ta fashe ta tarwatse bare ajega ta sauke masa tulin ruwan balain datayi dako tsawon kwanaki dominsa na musamman.

Tura yakai bango,in akwai makurar karshe to tabbas haqurinta akanshi yakai yau,yakamata ya fito fili ya gaya mata shin ita mene ne awajen sa dan bata gane meyake nufi da ita ba.

Karkkarfan ajiyar zuciyar daya kufce mata badon tasoba ya tursasa shi adan dole ya bude limsashu kuma gajiyayyun idanunshi wanda suka so suyi luhu luhu tsabar nauyin magananun zuci da zuciyarsan ta dade tanayi ita kadai.

Ainau Tana daf da bude bakinta ya miqe tsaye cikin sauri mai nanike da jarumtar kasaitar sa dake saurin saka yankewar gaba,a nitse ya karaso har gabanta yana kallon figaggiyar nityn data sakan up and down fuskan sa adan daure, cikin wata girmanmen muryansa data fito da yar tashen masifa har yana lullumshe ido yace
"I have had enough of your nonsense A'inau!tunda ke baki da hankali daga yau kar in kara ganin ki awani waje agidan nan da wannan shigar banxan.
,kaiwa nan ya dakata da maganan yay shiru, sannan yaja numfashi game da sassauto da muryan sa kasa kasa yanai mata kallo mai dauke da tsantsar comand da nuna ya isa,araunane ainau ta sadda kanta can kasa,da gefen idonshi ya kara jefo mata wani kallon aransa yana ta mamakin Yanayin ta yace"ohh ok i think is time for u to go park ur things ..zamu koma can gida kawai..
Adan hargitse Tace what?bai kulata ba yana kkrin juyawa yace "u heard me"..

Abbu is already back in nigeria bazan so yazo nan ya same mu agidan nan ba..ba amfanin zamanki anan.

Yunkurin juya mata baya yake bayan ya kammala furta hakn sai caraf ya tsince ta agabansa a mugun masife, kwayar idanunta ya kalla yaga wai har sun rine sunyi wani rau rau cike da ruwan hawaye tamkar zasu fashe su watso waje.

Wani irin kallon data watso masa saida yasa gaban sa ta dau sautin bugu ya kara maida hanklin sa yana kallon ta dan yaji me zatace ,a zafafe amma bada muryan fada ba tace mishi
"Daga ina kake,Har kadawo ko?yy saurin dauke kansa akanta,ita kuwa kkrinta ta sarkafe kwayar idanunta anashi maybe in ya kalletan zai iya dawowa hayyacin sa yagane metake ciki dashi,dirin hucinta yasa shi lumshe idanunsa kadan snn ya kara budewa ya juyo sai yanzu ma ya tuna cewa ashe bai sanar da ita tafiya mission din dayaje ba,naw he got why she look dis furious aranshi yay wata malalaciyar kwafa shi baiga ma dalili ba,meye ne dan ya tafi bai sanar mata ba,yaga dai bayau aka fara ba,yasan she hates his job so bai wani dara sa da sai ya mata bayani ko yabata hakuri akan dan yaje ba,
aganin sa ainau tafi kowa fahimtar cewa baya cikin jerin majajen da zasu sanar da kowa abunda ya shafi hurumin aikin su..its a big mission for god sake,dama can metake so yagaya mata mtsww,ackin dakika ya gama ayyana wayannan zantukar aransa shikadai yanai mata kallon batasan meyake mata ciwo ba.

"Ka manta haqqin aure ne a tsakanin mu mufrad?im ur wife, and i dersev to know ur wher abouts no matter what..tafada tana stressing word din no matter what din,"u left me for a month ba kira ba sako u think hakan dakayi min adalci ne?wani dauke kansa dayayi a shashance yasa duk yadda taso tayi dauriyar sanda muryanta ya sarke mata wuya tanajin zafin wani kulluton wuta yana toshe mata hanyar numfashi,wani kuka kuka ta soma ji bazata yana shirin kufce mata,a kassare ta furta a hnkli,.."and all u got to say to me first is banada hankli dan kawai kaganni da nity a dakin yar uwata?Yawo nakeyi dashi agidan na dazaka cemin banda hankali!?

Hawayen datake dannewa su suka soma saukowa yuuu suna bajewa saman kumatunta suna gangarowa kasa,wani irin rawa hannunta da muryanta yakeyi at same time ta kafe shi da jajayen idanunta tana kan kallonshi wai duk da hakama dauriya kawai takeyi,cikin kunar rai da zafin zuciya ta cigaba da sheqa masa wutar takaicin dake fitowa daga saman zuciyarta tana yagashi da manyan kalamai.

Tsiwa da Masifar data dade batai masa ba ta rinka kwararowa agabn sa tana karanto masa babi babi da shafi shafin laifikan daya tara akanta da haqqin ta dayake dannewa,sosai taji idanunta sun rufe tama kasa control kanta,fushinta ya nuna sosai duk dama bataso ba,saidai batayi tsammanin har ta tara fushin nata yay nisa hakan ba, da manyan baqaqen maganganu da tijara ta karemasa
"Kafada min matsayi na wajen Ka mufrad,im tired of beign a nuisance in ur life,..idan bazaka iya zama dani a matsayin matarka ba ka sawwaka min wallhy bazaka dake ni kahani kuka ba.

Ta dade tana magana dashi anma baice mata uffan ba,sai ya kau da kansa gefe ya tsinke cikin wata salon rigima ta kasaita datake masa azaban kyau tana fidda sirrun jajitacen kwarjiinin sa,take ya turmutsa yanayin sa izuwana wanda maganan nata baiyi ma'anan da zai ma shigesa ba,while deep down within him yasan akwai abun dubawa game da fushin nata,harda da kalaman danne haqqin datake furta masa ayanzu..

Ita kuwa yanayin sa da bai nuna damuwar sa akan abunda take cewar yake dada zafafa mata kai yana hatsala ta.

Itada ta tasha cin alwashin bazatayi masa kuka ba?wani wi wi wi taga kanta tanayin masa kukan yau,She became soo furious with her self also haushin sosai tabawa kanta da kyar ta aro qarfin jarumtar sann tadan yi shiru .

Bai kulata ba kuwa saida tagaji dankanta tayi shiru Juyowa yay ya zuba mata idanunsa da suka jima da sauya launi yanai mata kallon da bazai iya fassarashi ba..

Ayan mintuna da basu wuce Dakika ba ya dauka yana kallonta har cikin kwayar idanunta baice mata uffan ba ya juya ya tattara phones dinsa ya cusa daya a aljihu ya rike daya a hannun sa ya a daddanawa, batare da ya kalleta ba ya jefa wayar a kunnen sa cikin gyaran murya yace"where

Please Login or Register in order to submit comment