Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina na juya zan fito, Mamar Jasrah tace min.
"Yau zamu yi darasi akan Budurwan Masarauta, amma manta kawai, zaki gane anan gaba"

   Nasan tana son koyar dani, amma Ni ban ga dalilin haka ba.

     Yadda take warware min sirrin cikin gidan sarautar ya bani tsoro da Mamaki, dan haka zunzurutun tsoron da yake cikin labarin ya sani ji kamar zan mutu na dawo, sai da muka kusan wuni tana bani labarin yadda aka kafa daular da yadda kowa yake kokarin sai ya kafa haramtacciyar ra'ayin shi a cikin daular.

          .... Sai bayan magarib na baro gidan, na gaji sosai. Dake ban tab'a fita cikin dare ba, ban san yadda masarautan yake ba, ashe suna sake wani katon kare me sufar kura, shafa gefen cikina nai,.tare da dauko sarewa na. Sam na sha'afa na saka a bakina kenan naji gurnannin abu a bayana.

Da sauri na juya tare da kallon shi, haushi yayi min. Naja da baya, ya kuma min haushi naja da baya. Cikin wani irin zafin nama, muka kasa a guje, bina yake ina kaucewa yana bina ina kaucewa, sai da ya kusan kamo Ni na kwace.

       Yankar wata yar lungu nayi, kawai sai ji nayi kamar an d'ago ni sama,turus karen yayi, nima zunzurutun tashin hankali ban fahimci me ya faru ba, sai da na bude idanuna na kalle ni a tare da wani mutum,dake akwai duhu bana hango kome saboda fuskar shi tana lullube cikin duhu, nima nawa fuskar tana lullube.
   Hannun shi a k'uguna, a hankali ya hade jikin mu, wanda ya haifar mana da bugun zuciya lokaci guda, yana rungume ni ya sakewa karen nan, wani abu, wanda yasa karen faduwa, zunzurutun rashin mutunci sake ki yayi daga saman yayi tafiyar shi, haka na fado kusa da karen da ya suma, na tsallake zan wuce. Juyawa nayi tare da d'aga kai na.

            Shima yana tsaye amma bai juya bayan shi ba, tafiyar shi ma yake kokarin yi.

           A hankali na juya tare da barin gurin, da sauri na nufi shshin mu, tunda na shiga na Fahimci akwai sabin bayin da muka samu. Ban kula kowa ba kai na a sunkuyar zan wuce.

         Shan gabana aka yi, sake ratsa gefen ta nayi ta kuma shan gabana, daga can gefe ina hango Narmin tana kallon mu, kai hannun tayi.zata cire min mayafin fuskana, nayi maza na dake hannunta.
"Mahlika karki tab'a ta, ki rabu da ita"
    "Narmin ba zan iya ba, duke min hannu tayi, bakar fata tana da izza har haka." Ta tako har gabana, tare da kai hancinta zata min isgilanci, sai kuma ta shako kamshin turaren da taji shi, bayan shigarta Falon Sultanah Hoyam, har take tambayar Narmin ko zata sato mata turaren Sultanah nan ne, dan kamshi yayi mata.

            Kwaɓe ta Narmin tayi tare da gaya mata wannan turaren SULTAN Mehran ne, ta kuskura tayi hauka sare kan ta zai yi. Dan haka ta shiga hankalin ta, amma kuma kamshin Turaren ya zauna cikin kwakwalwar ta, wanda ya haifar mata da daukacin kaunar shi.

            Kallona tayi kirjinta na wani irin bugawa, cikin fusata ta kai min duka dan ban zaci haka daga gare ta ba. Faduwa nayi can gefe,
"Narmin wannan yar yarinyar naji kamshin turaren Sultan Mehran a Jikinta a gidan Uban waye ta samu?"

    "Sultan Mehran?"
Kafin kace me, dama suna jin haushina tuni suka tara min fadawa, aka dauke ni zuwa shsshin Sultanah Hoyam, ita kanta taji kamshin dan haka ta tashi tare da sakawa a riko ni har shashin Mehran. Tunda muka shiga baya kusa, haka ta haura sama,can sai gasu tare yana sanye da wata rigar shan iska. Kallon mu yayi tare da mutanen da suka riko ni, sannan ya  zubawa Sultanah Hoyam ido.

     "Mehran! Taya akayi yarinyar nan ta sami turaren ka? Abu yaja ana ta kanannan magana."  Dauke kai yayi kamar bada shi take ba, tana kuma tambayar shi ya juya ya bar mu a gurin, cikin takaici da bakin ciki, tasaka a kai ni can wani gidan Horo me suna Darul Azab...
         . Bayan tafiyar mu ne tasaka aka kawo mata Mahlika.
"Kinyi abinda ya dace, dan haka ina son ki saka ido akan kome na motsin yarinyar, dan in har ta sami kusanci dashi a bayan fage yake nan. Kema bana son kusancin ki da Mehran kasancewar ban yarda da kowa akan shi ba. Kinji Ni?"

    "Eh na ji ki Sultanah."
"Zaki iya tafiya!"
"Nagode Sultanah"

Wannan littafin na kuɗi ne..
*Allah yajikan Iyayena 😭😭*
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
Page 22
Tana da fita ta sake murmushin mugunta tace.
"Lokaci yana zuwa Sultanah Hoyam."
      A hankali take takawa, tana nazarin abinda Mahaifiyarta tace mata.
"Narmin itace makamin mu, sabida itama tana da ciwon Sultanah Hoyam, idan muka rike ta zata bamu hadin kai.

   Burina ki sami kusanci da Sultan Aamaan Mehran, yadda zaki yi abinda babu wnada ya tab'a yi, amma karki sake Abban ki yasan cewa akwai cin Amana  a cikin tafiyar domin ba zai yarda ba, kuma zai iya dakatar dake abinda zaki yi."

Murmushi tayi a karo na biyu, sannan ta nufi hanyar shsshin su.

     ~~~
Tunda aka kai ni, darul Azab, wanda yake cike da zalinci karkashin kulawar wasu maradai mara imani da mutunci, ya sani shiga cikin tashin hankali, domin kuwa wani irin nau'in azaba suke bawa kowa. Suna da wata bulala me dauke da wasu irin allurai a jikin shi, dan haka suka shiga zane ni dashi.

       Har sai da nayi laushi, haka suka kyale ni, washi gari suka tashe ni da ruwan zafi, aka daura sabon azbtuwar.

       .. tunda gari ya waye FAZILATUL take saka idanun akan zuwan Ikram babu ita babu labarinta, har zuwa rana anan ta tura darda ya tafi niman ta, sai hangota yayi a tsakiyar masarautan an saka bayi suyi ta jifarta da d'anyen tumatiri, da sauri ya koma ya gaya mata.

          Bisa al'adar idan aka gama mata wannan uƙubar, zasu kuma yanke mata hannun sabida tai sata, dan haka ta rubuta wasika izuwa ga mutanen gari tare da gaya musu, irin nauyin Uƙubar da Sultan Aamaan Mehran yake ganawa mata da bayi, bayan kowa yasan halin shi dan luwadi ne.

            Kasancewar an cika ana kallon Ikram har aka watsa musu takardun, basu Fahimta ba, lokacin da suka fahimci sakon da yake jikin Takardan, aikuwa talakawa suka shiga bore, tare da kunce Ikram, sannan suka juya al'amarin satar izuwa cewa.
   Ya kamata zai yi luwadi da ita ne, ita kuma garin gudu ta shafe kamshin turaren.
    
     Dan haka lokaci guda, maganar ta zama wutar daji, tare da zama babban al'amari. Talakawa sun fusata ai nu, dan haka suka ce ko ya fito ya kare kanshi ko kuma ya sauka a kujeran mulkin.

           *Wani irin tashin hankali nake kuma fuskanta ne? Wani irin bala'i ne ya ke kuma tunkara na? Me yasa sai Ni? Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun*
Wadannan sune abinda yake yawo a raina, duk da sun kwance ni, na kasa tafiya. Sakamakon yagewar da tufafin jikina yayi. Ina durkushe a gurin.

           ....
"Wannan wani irin rashin daraja ne? Idan kasan zaka yi kazamar rayuwar ka, sai ka..."
Cikin zafin nama aka hango kan Mir Jazib, yana tsalle gangan jikin shi yana birgima jini yana ambaliya a cikin fadar.

   Takarkarewa Sultan Mehran yayi ya kwatsama musu ihu, sabida yadda yake jin zuciyarshi tana ci da wuta.  Idanun shi Jajjur ya nuna su da yatsa yana huci.
"Ku dauko min ita!"

      Ya juya tare da barin Fadar zuciyar shi tana ci bal-bal-bal. Ina sunkuye naji an dauke ni cak, tunda suka dauke ni basu ajiye ni ba, sai a katafaren shashin sa, wanda yake dauke da kamshin turaren da ake bala'i akai. Tunda suka ajiye ni, jikina ne yake rawa sakamakon hango shi da nayi tsaye tare da juya min baya, yana daure da kwarjalle. Dakin kuwa kwalbar turaren ne a fashe a ko ina. Juyawa yayi tare da kallona idanun shi da fuskar shi abin tsoro ne. Domin sunyi jajjur.

           Shiga ban dakin yayi tare da barina a gurin, dan haka ban yi karambanin kome ba, na kwanta sabida zazzaɓin da yake cin jikina. Tunda na kwanta a gurin nake gani dishi dishi, ba zan iya tantance abinda ya faru ba, sai dai na farka ne a wani daki karami a dai cikin castly ɗin. Tashi nayi a hankali na ga maganin tare da abinci. Tashi nayi na fara ci, sannan na lura da ban daki na shiga nayi alola da wanka na fito.

            Ina idarwa daya daga cikin mutanen shi ya shigo min,  kallona yayi ina ƙoƙarin saka mayafin fuskana, takowa yayi gaba na, tare da kai hannun shi zai tab'a ni, na kaiwa hannun duka.
"Me zaki boye a fuskar ki? Baki san har jikinki na gani ba."
"Kayi kuskuren ganin jikina, amma yanzun zaka biya ladan ganin da kayi."
Wani irin karar da muke kama gashin kaina na dauka, tare da suka Mishi yana kaucewa, wani irin azazzaben fada muka kama a cikin d'akin, tunda yaga jikina wallahi sai na fasa mishi idanun shi.

             Aikuwa Allah ya bani Sa'a na soka mishi tsinken,  a saman idanun shi, tare da kai mishi wata irin duka, ihu Yasaka tare da kiran Fudail ya kawo mishi dauki, duk da na sha duka amma haka bai hana Ni jin dadi, na tsinka mishi jijjiyar saman idanun shi ba. Shigowa Fudail da Darakshan suka yi, suna kallon yadda gashi kaina ya lullube fuskana.
                  "Ke wacce irin mutum ce da bata jin magana?" Inji daya daga cikin mutanen.
"Rashin darajar ku ya janyo haka,  idan baku kyale ni ba, wancan lusarin dan daudun sai na burma mishi wuka ta cikin shi ya bullo ta bayan shi. Ko kuma ta alkalamin shi ya fito ta duburar shi."
Fitar da shi suka yi, sannan suka koma gurin Sultan Mehran suka gaya mishi. Da hannun yayi musu alama, su fitar da Ita,  dan haka suka fita da sauri abun su, kai ta shsshin bayin suka kuma yi, tun daga ranar ban kuma samun rashin mutunci ba. Sai dai kuma an sauya min aikina daga can haramtacciyar Fada, zuwa cikin Fadar.

     Inda nake kawowa manyan fadar abin sha da naci, wannan shine aikina da kuma dalilina na zama cikin masarautar.   Idan akwai Abinda yake min ciwo yadda suke kai min duka a ɗuwais dina,.duk da kuwa dattawa ne babu matashi sai shi da masu kula dashi.

              Bai tab'a kallon haka a matsayin cin mutuncin ba, kawai abinda ya sani ya zab'i a tozartani sama da abinda nayi mishi.

   Yau na kawo musu abin sha, watsarwa suka yi tare da finciko ni, Mir Rahil yana ƙoƙarin kai hannun shi cikin rigana, na daki makogaron shi, take numfashin sa ya tsaya cak. Caaaa dakaru suka min da takobin, zare na jikin Mir Rahil din nayi, tare da jan layi.

         Mamaki ne ya kama kowa a gurin.
"Ke ki ajiye takobinki!"
"Ba zan ajiye ba sai na kashe wancan kazamin me wanka cikin datti."

    Aikuwa yaki ya barke a tsakanin mu, me shegen tashin hankali. Kafin kace me na jikata mishi dakarun fadar, ina kallon shi dukda na gaji sosai, abinda ya kwace ni a hannun su zafin nama, a duniyar yaki zafin nama itace sama da kome, durkusawa nayi akan gwiwata, dogare da takobin ina huci.

           A hankali ya mike tare da zare takobin shi, ya tako gabana.
Da ace nasan waye a gaba na, da har duniya ta tashi ba zan so na kuma hada karfin dantse da wannan basamuden ba.
Mik'ewa nayi tare da  tattara gashin kai na, na mai da baya, sannan naja kafana baya tare da jan layin. Na mishi alama ya taso idan ya shirya.
     Gyada kai yayi tare da sake murmushin takaici. Yau da mace zai yi fada. Bari yaga wani irin horo ta samu. Sai dai kashhhh Fudail shi ya sha gaban shi tare da kawo min mugun sara kamar zai rabani gida bi.
         
     Tunda muka fara gwabza yaki tsakanin mu, muke jin kamar zamu kashe junan mu, dukda wutsiyar raƙumi tayi nesa da kasa, sannan abin kunya ce a gare shi faɗa da mace, shi yasa Fudail ya amshi fadar tare da fadawa musu maganar da yayi  matukar tasiri a ransu.
"Ba zamu tab'a barin Sultan Mehran yayi fada da yar karamar kiyashi ba"
Dan haka tunda muka fara, ko kwarzanin shi banyi ba, sai ma kare kai na da nake, domin Idan ya kawo min sara,  ji nake kamar da mutane dari nake fadar, yarda takobin nayi tare da kallon shi.
"Me kika taka?"
"Idan ka shirya!"
Da nasan cewa bala'in da zan tarowa kai na, haka ce da ban yi yunkurin juya fadar zuwa dambe ba.
        Domin lokaci guda nayi dana sanin yafi karfin kwando dubu, domin dukar kawo wuka Fudail yayi min. Koda ya juya, babu sultan Mehran a cikin fadar. Daukata yasa aka yi, suka kai ni can Shashin bayi.
 
                Sai da na kwana uku, kafin na warware kamar jaka. Ina zaune aka watsa min kaya.
"Ki saka zaku je can babban majalisar Sultan zaku sanya su nishadi."
"Ba zanje ba."
"Zaki"
"Toh naga mai kai ni!"
"Idan baki kije dan Allah ba zaki dan azabar shi."
Lashe bushashen lebbena nayi sannan na shirya ba daura wata mayafi kai, cirewa suka yi tare da daura min wata jigidan zinari wanda kana motsa zaka ji karan har cikin kanka. Kafana ma haka da ko ina, kayan da na saka yar karamar buje ce, me tsagu har tsakanin cinyoyina, sai dan karamin dan kamfe da yake makale da shi. Kirjin kuwa dama akwai wani yadin da muke daure nonuwar mu dashi, dashi na daure nawa, amma sauran basu daure nasu ba. Sun barshi yadda suna rawan yana zillo.

   Tunda muka gama suka shirya mu, tare da nufar shashin. Muna shiga aka fara mana kid'a, lumshe idanuna nayi tare da jin sautin kidar har cikin kai na. A hankali muka fara rawan, ana watsa mana wani irin ruwa, kafin kace me duk mun bugu, zan iya cewa ban san kome ba, amma tabbas naga lokacin da wanda muka yi fada dashi ya dauke ni, sama sama nake jin kamar ihu da hayaniyar muryan mutane.

          Tun daga nan ban kuma fahimtar kome ba, sai da safe. Na tsince kai na a wannan karamin dakin nan dai. Gyara kwanciya nayi zan cigaba da barci naji an sheka min ruwa, zubur na miki tare da kallon mutumin.
"Banza kawai! Insha Allah akan wancan dan luwadin zan rama."
A fusace ya shigo dakin tare da shake min wuya, dariya ya bani nace mishi.
"Toh ba dan luwadi bane? Me yasa ya ajiye kartin maza irinku yana zaka takashin ku..."
Marina yayi tare da ture ni, sannan ya fita. Tashi nayi na shiga ban daki nayi wanka da alwala, nafito  tare da sallar ta sallolin da suke kai na, ina cikin addu'o'in ya kuma kawo min abincin.
"Da fatan baka saka min guba ba?"
"Da zaki ci ki mutu ai da ba haka ba"
"Sai dai kai ka mutu domin duk abinda aka min sai na rama akan wancan mara mutuncin."
Na shiga cikin abincina,.haka ya fita yana tsaki a ranshi.

        Yana gama shiryawa ya kalle su, sannan yasa kai ya fita.. abubuwan da suke faruwa yake dawo Mishi kan shi, tun daga haduwar shi da yarinyar har zuwa yanzun, takaddarirancin ta yayi  yawa dole ya sauke mata shi, dole ya koya mata hankali. Dan haka ya tanadar mata da nau'o'in azaba.

            ..... Koda naji gidan babu hayaniya,shiryawa nayi tare da barin cikin gidan, na nufi haramtacciyar Fada. Kimanin sati biyu zuwa uku kenan bamu samu damar haduwa da juna ba.
Ina shiga na karasa gurin Maman Jasrah. Zube gwiwata nayi cikin ladabi da biyayya.
"Aikinki yana kyau? Amma yaushe kika koyi fada haka?"
Sosa kai na nayi sannan nace mata.
"Kasancewar  munyi fama da hare hare da yaki yasa muka koya dan kare kanmu."

  "Kinyi aikin da ya dace saura mataki na gaba, dan banyi tsammanin lokaci guda Mehran zai barki a cikin fadar shi ba, dan haka ki nutsu kema ki koyi halin masarautan ki koyi dabi'ar su."

Daga nan ta shiga daura min darasin mu na gaba. Tare da yadda zan kuma samun shiga cikin gidan sosai.

Wannan littafin na kuɗi ne.
*Allah ka jikan Iyayena 😭😭*
#Mai_Dambu.
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
Page 23

Ina cikin sauraronta, sai ga dakaru. Suka shigo cikin gidan. Basu yi wata wata ba, suka saka Ni a gaba. Ban yi musu  ba, tunda muka nufi cikin gidan na fahimci ran Mutumin nan ya ɓaci.

     Ban d'aga hankalina ba, sai da naga ya saka manyan kartin maza, dai dai fitowar Sultan Mehran, suka shiga zane ni. Tare da tambayana da Izinin waye na fita. Idan na basu amsa tabbas ina tsoron su, idan nayi shiru kuma zasu ji bakin ciki.

   Dan haka nayi banza dasu, ganin haka suka ci-gaba da zabgata, sai da suka ga kayan jikina yana yagewa, kai na kwance sabida zunzurutun dukar, wanda ya haifar da zubar jini daga bulalan. Yana zaune ya daura daya akan daya.

   Ba kome yake bashi mamaki ba, yadda taurin kai ya hanani ihu, jana suka yi zuwa dakin da nake, lokacin sallah azhar yayi da haka nayi ta bin bango na shiga ban daki, nayi alwala na fito. Sai da na fara sallah ne kuka ya zo min, tare da  shashekar.

        Kumshe idanun shi yayi tare da kallon Abincin da yake gaban shi ya fara ci a hankali, yana iya jiyo kukanta amma bai da wani damuwa akan haka, sai ma takaici da haushin da take bashi. Ya gaji da sauraron ihunta. Ture abincin yayi tare da ɗaukar bulalan ya nufi d'akin.
"Afwa Sultan Mehran! Ta tuba ba zata kuma ba."
Inji Darakshan, banza yayi da su ya shige d'akin, ganinta yayi ta kai sujada, tana kuka tare da kirariwa Ubangiji, abun ba wai tana yi a fili bane a Zuciyarta ne har ya fito fili.

           Kalmar da ya tsaya mishi a rai ya cigaba da hautsina mishi lissafi,
"Ya waduddu Ya Zul-arshin majid! Ya fa'alil limayuri"

Ji yayi kan shi kamar zata fashe abinda yayi niyya ya tsinci kanshi ya kasa aiwatar wa, da sauri ya fito, domin ji yaƙe d'akin tana mishi zafi kamar an hura mishi wuta.
Abinda zuciyar shi ta fara gaya mishi ba kome bane face.
*Lallai yarinyar nan matsafiya ce, kuma zata iya halaka mutanen birnin ka, kayi gaggawan sawa a halakata*
Cikin wani irin tsawa yaji wani shashin zuciyar shi tana cewa.
*Ba matsafiya bace, kayi bincike kafin ka zarta da hukunci*
Take zuciyar shi ta kasu bangare biyu, zama yayi cikin damuwa yana kallon su.

   Ganin yadda ya fito yana haki, a fusace suka nufi d'akin, suka tadda ita tana sallah. Cikin fushi Darakshan ya nufeta, kamar wanda aka tura shi dakin  wuta, ne zunzurutun zafi dole suka fito basu shirya ba.

            Kallon juna suke dashi, bakin shi nason yin magana, amma kamar wanda aka rufe mishi bakin,dan dole yayi shiru yana kallon su. Amma zunzurutun mugunta dariya yake musu  a ranshi, musamman yadda suke hada gumi.

        Tashi yayi ya wuce sama, daga nan ya hana kowa shigo mishi, ko masu kula dakin shi baya kaunar su shigo mishi.

Gashi dakin shi yayi wani irin datti, abinci ma tsakanin shi da Allah ya kaurace musu, Fudail ne ya fahimci abinda yake nufi, dan haka da kan shi ya saka ni a gaba muka haura har dakin shi, na gyara kome na goge kome, tare da tattara kayan dattin shi ne fito dashi.

Me wanke mishi kayan shi ya amsa, sannan Fudail yace min.
"Akwai dakin girki kece zaki cigaba da mishi girka."

"Akan me?"
"Sabida haka yake bukata."
Kamar zanyi magana sai kuma na fasa, tun daga ranar na koma Jakar Sultan Mehran, kamar zanyi kuka wani lokaci a dakin girkin nake kwana, sakamakon yadda kome dare zai Turo na daga mishi shayi, idan ina barci haka Fudail zai tashe ni.
Kuma dan rashin mutunci, idan na gama abincin sai an sani na ci kafin yaci, ina tsaye zai gama mulkin shi kafin yaci, yana ci yana wulakanta ni, ta Hanyar watsa min ruwa, ko furza min abincin a fuskana, ko kuma ya kwala min kofi, iya wahala ina fuskanta da Mehran. Amma ban tab'a jin ko ganin wata rana zan sami yanci ba.

Yau ma ina kwance, naji ana zungurina, bude ido nayi na kalle shi. Daga shi sai yar kwarjalle, da wata rigar shan iska, da sauri na mike, dan ban tab'a ganin shi ba, ido da ido babu alkyaba. Yau ma dai gashi ne yayi mishi rumfar da fuskar shi. Tsayawa nayi ina kallon fadaddar kirjin shi, me yalwacce da gashin a kwance luf.

Yana rike da kofi a hannun shi, sai juya kofin yake. Banyi aune ba sai ji nayi an saka min kafa, na zube kasa.

Wallahi idan ka gan shi ba zaka tab'a kawowa zai yi irin wannan muguntar ba, amma ina mugu, kamar bashi ba.

Tashi nayi na shiga ƙoƙarin hura wutar, sai na kunna zai kashe, ajiye abin hura wutar nayi a fusace zan fita, make ni mutumin nan yayi, kai na ya bugu da bango. Anan na sume mishi.

Bai damu ba, ya tsallaka ni. Ya fice Daga dakin girkin, dake ranshi yana kaunar shayin kafin ya kwanta, dole ya d'ago Fudail yazo ya watsa min ruwa, tare da taimaka min na hada mishi ruwan zafin, kai na kamar zai fashe, ina aikin ina kuka.

Ina gamawa Na mika mishi zan fita sai gashi ya kuma shigowa, bai magana ba shi lallai sai dai nayi mishi girki, kallon shi nayi dan dare ya raba sosai, haka na shiga aiki babu ji babu gani, kuma yana tsaye. Dakyar na kammala aikin, ina gamawa ya kalle ni, na zauna jagwab. Saka hannun shi yayi tare da zuba abincin gabaki daya.

A razane muka kalle shi, kwalla ce ta shiga cika min ido.
"Yadda ka tozarta Abinci sai Allah ya tozarta ka."

Buge min baƙi Fudail yayi tare da kwashe abincin. Ya mika min.
"sake wani"
"Ba zan girka ba!"
Kallon Fudail yayi sannan ya kalli hanyar fita, yana isowa inda nake ya daki kafana da kafarshi, yadda kuka san an karya itacce haka ya b'alla min kafa sannan ya ficce abin shi. Ihun da nake yasanya Fudail da Darakshan suka kuma shigowa..ganin ina gurnani. Tare da rike kafar da ta lankwashe.

"Kai Amma Sultan Mehran bai." Gyaran murya muka ji, daga bakin kofar koran su yayi daga kitchen ɗin, haka ya juya ya fita shima.

Washi gari kafar ta kumbura sumtum, kuma dan bakin mugunta wai nayi abin karyawa, dole Fudail ya gaya mishi gaskiya.
"Sultan Mehran, yarinyar nan.ba zata iya aiki ba, sabida zazzaɓi da karaya."

Lallai shi zasu renawa hankali dan haka ya juya ban shi.
"A fidda ita."

Haka Fudail yazo ya fita dani, zuwa gidan Me magani Lingesa, suka daura min kafar, bayan nasha bakar azaba.

Duk da ban wuce kwana ashirin a cikin shashin Sultan Mehran ba, amma kuma na sha azaba a cikin gidan. Dan haka na dauki wannan fitar nawa a matsayin abinda Allah ya bani.



Please Login or Register in order to submit comment