Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a jikina inda suka haɗu da ruwan jikina da na shi, suka bada wani yanayi na daban...

     (Bari nayi nan)
Duk da bai shiga jikina ba, amma na fahimci shima sai da ya sauke kayan nauyin shi sannan ya rungume ni, yana shafa bayana, Noman nake hangowa a idanuna. Hawaye na zuba min.

    A hankali barci ya dauke ni, a jikin shi. Sake shigar dani yayi jikin shi, yana shafa bayana a karo na babu adadin. Dole ya yayi wani abu.

     **
SAMAIND

Kallon yadda dabbobi suke rayuwar su yayi, cikin yanci da walwala, shi kuwa an saka mishi sassari tare da nauyin wasu al'ummar da bai shirya dasu ba,

   *Me yasa duniya take cike da masu son kai ne? Me yasa ba a bani damar.*
"Sultan Mehran!, Akwai baki daga yankunan gabashi kasar nan sun zo maka mubaya'a!"

Inji Rakshan,

   Bai mike ba, kuma bai amsa ba ya cigaba da kallon dabbobin da suke shawagi a lambun ne,
Rakshan zai Kuma magana Fudail ya dafa kafadar shi.

         Girgiza mishi kai yayi tare da mishi alamar yana sane da abinda kace.

         Sauke ajiyar zuciya yayi, tare da kallon Fudail,
    A takaice sai da suka kwashe awa daya a gurin kafin ya mike dan kanshi ya fice daga lambun suna bin bayan shi, mutum ne da bai son hayaniya, shi yasa yake keb'ancewa daga hayaniyar.

Yana fada ne a zaune suka ishe shi da surutu ya, bar fadan yanzun kuma zuwan baki daga wasu yankunan yasa zai je.

     Koda ya shiga ya samu har lokacin suna magana, akan tsarin  lallai duk budurwan da zata shigo masarautan dole ta zama tana budurci idan ba haka ba, toh sai dai a sauke Sarkin.

       Sannan kuma ita a kashe ta, wannan shine gaskiyar maganar da suka yanke, dan haka sauran gwamnatocin da suke ikirarin zasu bashi Ƴaƴan su mata, su san da tsarin.

    Wannan sakon Sultanah Hoyam ce. Kuma manyan fadan sun amince da shawaran ta.

     "Muna gaisuwa da sabon Sarki wanda za ayi bikin bashi sarauta nan da kwanaki biyu, Sultan Aamaan Mehran na biyu, Rahab itace yankin da nake jagoranta. Sannan muke da alhakin sarrafa, sulkin yaki Sultan ga mafi Nagartan Sulken yakin da muka sarrafa da hannun mu,.ka ka amshe shi da farin ciki.

   Mikawa Rakshan aka yi ya mikawa Fudail, juyawa yayi sannan ya mikawa Sultan Aamaan Mehran na biyu, a hankali ya sake rigar ta fadi kasa, Yasaka kafa ya taka. Gyada kan shi yayi sannan ya Kalli Rakshan.

            Dauka yayi sannan ya ajiye a gefe, su kansu manyan fadar. Kallon mamaki suke mishi musamman yadda yake magana da idanun ko da hannu, sannan idan bai son abu, karara suke ganin baya bukatar shi a kwayar idanun shi.

            "Sultan Mehran! Wannan kansakalin yaki ne, Sultan shine abu mafi daraja da muka sarrafa shi..ka amsa da farin ciki."

Murmushi Amir Hood yayi sannan yace.
"Sultan Mehran yana godiya abisa wannan kyautar da ake bashi."

          "Sultan Mehran! Ga takobin da tafi kowacce takobi daraja, da ita akayi yakin Birnin Quzai, kuma da ita aka yaki Ranvagalas, Sultan Ni nake jagorancin garin, Wurta sannan wannan takobin ita daya ce garkuwa ga Mutanen wannan yankin,. Bamu da kyautar da ta wuce wannan, kasancewar muna cikin Sahara ce.. gata nan sai jajjayen Rakumai guda dubu tara da muka kawo."

              Kallon mutumin yayi sannan ya kalli magatakardan masarautan, wanda yake ta rubuta abinda ake kawowa.

        Kafin ya kalli Rakshan cikin idanu.sannan ya shiga wani irin motsa hannun shi, yana haɗawa. Kana ya Kuma hada hannun shi har sau biyu.
_Kace ya maida garkuwan su da dabobbin su yankin su. Shekara me zuwa ya cika min dabbobin ya kai dubu goma_

  Kallon mutumin yayi, sannan ya kalli Sultan Mehran! Tare da sake ajiyar zuciya yace.
"Mir Jazib.. idan na fahimci sakon Sultan Mehran yace ka mai da garkuwarku yankin ku, sannan shekara me zuwa ka tawo mishi da dabbobin nan guda dubu goma."

      Gyada kai Mir Jazib yayi tare da komawa ya zauna. Kallon Rakshan mutanen fadar suka yi suna mamakin yadda ya iya fahimtar lamarin Sultan Mehran.

   A hankali suka gama gabatar da kansu..kafin Mir Umdatuddawla ya mike tare da cewa.
"Sultan Aamaan Mehran, mun gama kawo yadda za a shigar da batun yan matan da zaka aura.

   Abinda muka yanke, shine bamu yarda a kawo wata mace daga yankin da ake samun yar tsama dasu ba, sannan bamu amince Sultan ya shigo mana da baiwa cikin masarautan nan ba,

Bamu amince ya bawa wata mace damar Sultanah ba, har sai ta haifi d'a namiji, Sannan Sultan yana da ikon zartar da abinda yake bukata amma shima sai ya nime shawaran Mahaifiyar shi, Sultanah Hoyam.

       Sannan dole ne Sultan ya bayyanawa masarautar nan yayi tarayya da Ƴa mace ko yar waye, Sannan."

Dakatar dashi Sultan Mehran yayi, tare da mik'ewa a gajiye yana nuna alamu da Rakshan yaji da kome.

      Bayan fitar shi Mir Rahil ya mike cikin fusata.
"Meye Mehran na biyu yake nufi? Ba zai bude baki yayi magana ba, sai abinda kuka ce."

      "A wannan lokacin na mulkin sh, dole kubi abinda yake nufi, kuma dole mu yanke hukunci ga duk wanda ya nime bijire mishi, Sultan Mehran baya magana, bayana nufin shi kurma bane ko bebe, shi mutum ne da magana bata shiga bakin shi ba, idan yayi muku, bismillah"

Daga haka ya juya suka bar fadan.
"Dole mu saka shi yayi magana, dole yayi magana, ya zama wajibi yayi magana, matukar ina raye zan saka shi yayi magana.!"

    "Babu wanda ya isa ya samin Yarona yayi magana!"

         ***
Oman
Kallon Ikram yayi sannan yace.
"Babu wanda ya isa rabani dake!"
Inji Abrad,

  ***
Gezira.
"Insha Allah babu wanda ya isa ya shiga tsakanin mu sai Allah, Ina tafe niman ki!"

 
*Alqur'an akwai matsala 🤔🤣 Chakwakiyya zalla 👌🏼*
#Paidbook
#Mai_Dambu

*Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ko katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641*
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/1033847662?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=U%2BKxfjj9pAp6lNBwOKTrL0n8IZodUh1%2Fi4kPauenrACA5g3CpBPg2XKNYbJz2ZMOPcIzyi5QVLlSuzMupzKMqu6w439ysIbmau4%2FPRE%2F5MsqRS%2F8ngta9Wj%2FVEanIgc3
ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
Page 14.....

     Har ila yau, baya jin zai iya rabuwa da Ikram, shi yasa yake makale da ita, kamar wacce aka bata bamju. Barci take akan gadon, har ya shigo da Narga ta gama zagaye fuskarta da wani bakin abu, musamman gefen fuskarta na dama, sannan ya sallame ta, ya cigaba da hadinta.

          Yau da ya haɗa jikin shi da nata, yaji abinda yake son ji. A hankali ya sauke idanun shi kan babban yatsar hannunta. Wanda yake dauke da wata yar karamar chindo sak irin Sariyah, wannan kama da mugun yawa take.

         Mikewa yayi tare da barin d'akin, ya nufi lambu ya zauna, tare da tuno abubuwan da suka faru, daga auren shi. Har zuwa rasuwar ta, bar mishi yarinya.

          *Ban farka ba sai kusan Magarib, a hankali na bude idanuna tare da kumshe su. Abubuwan da suka faru yana dawo min daki daki. Dafe goshina nayi tare da tattara zanin gadon na tashi zaune. Hada kafaffuna nayi tare da daura kaina a saman gwiwa ta.

        Wani irin bakin ciki nake ji, ban san me ya shiga kai na ba, har nayi kokarin raba kimata ga wannan bakin azzalumin.

          Turo kofar da yayi ne ya sani kallon shi,  sake mai da kai na nayi cikin matsanancin kunya, takowa yayi har gabana, ya zauna a kasa yana me jingina jikin shi da gadon.
"Ikram Wacece Airan?"

Ware idanu nayi ina kallon shi, kafin na dauke kai na, tare da cewa.
"Meye matsalar ka da son sanin  kome akai na ne? Abinda kayi dani bai isheka bane sai ka kuma sanin sirrina!"

            A sanyayye ya mike ya dawo saman gadon, zuba hannun shi yayi saman kafana yana matsa min su.
"Ban san me yasa kake son tab'a ni ba, kai baka da kawazuci ne?"

"Ina dashi mana, haduwa ta dake ya sani jin zan iya yakince wancan yanayin na zauna da ke."

Tsaki naja tare da mikewa na nad'e jikina da mayafin gadon, fisgo ni yayi tare da warware mayafin, ya mai dani gadon shi yana me kwanciya a sama na, kallon idanun juna muka yi tare lokaci guda.

   Goga min hancin shi yayi a saman nawa, tare da matsa min kirjina zuwa cikina. Buge hannun shi nayi tare da watsa mishi harara, dariya yayi yana me sake naushin shi a kaina.

                "Da alamu baki kalli fuskar ki ba, don Allah karki cire kome na fuskarki, bana son ki samu matsala da kowa ne Kinji." Dauke kai nayi, amma dake ya san kan mugunta ya kuma jibga min nauyin shi. Dole na bude baki zanyi magana, sai jin harshen shi nayi cikin nawa, ware idanuna nayi akan shi, cike da tsoron Allah.(wallahi kuwa tsoron Allah kaca-kaca a ranmu 🤣)

    "Don Allah d'aga ni!"
"Ikram! Babu namijin da zai baki tsoro, ina son mace irinki don Allah karki yarda wani dalilin rayuwa yasa mu rasa junan mu!"

"Kai sarki kake ko Sultan? Na tab'a gaya maka ina sonka ne? Ko nace maka ina kaunar ka ne? Babu abinda ya dame ni, ni mallakin Noman ne, kuma Insha Allah."  Cizon lebbena yayi tare da lasar bakin zuwa wuyana.

     "Ina da kishi amma bai hanani na bar mace tayi abinda ta zab'a ba ba, don Allah bar kiran sunan namiji a gaba na." Ya faɗa min.
"Matsalar ka ragagge ne, Ni bani da matsala da wannan tunanin, wanda nake so yana can yana jirana na.
          Zan iya mutuwa domin so, amma ba zan tab'a mutuwa akan so ba, dan haka koda zan mutu domin so na mutu, bana fatan na mutu akan so."

    Daga haka na ture shi tare da nufar ban dakin ina jan zanin lulluben, haka na shiga ban dakin nayi wanka sosai, sannan na fito da alola.

     Mika min tufafin mata yayi na gabatar da sallar da ake bina, sannan na daura wanda aka yi lokacin.

         A hankali na gyara jikina tare da cire kayan na dauko wanda nazo dashi zan fita. Yana zaune  yana kallona.

     "Da zaki iya da kin hakura da fitar na sai gobe!" Juyawa nayi tare da kallon shi a takaice, sannan na saka kai zan fita naga wajen turakar da duhu sosai. Dole na juyo da sauri tare da komawa dakin shi na haye gadon da mugun sauri.

Murmushi yayi tare da kallona yana cewa.
"Lallai baki da dama, haka kike tsoro dama?"
         Murguda mishi baki nayi tare da cewa.
"Ba dai mugunta bane halinka zaka gani a kwaryan cin abincin ka !"

                  "Toh tashi ki koma mana ai  bani na dawo dake ba?"
"Da baka dawo dani ba, amma ai ka tsorata ni"

     "Bana son sharri, Ni ban dawo dake ba, kawai dai baki fita da zuciya daya bane"

      "Toh waye yace ka sara min baki, Ni bazan kwana a daki daya da kai ba, dan Ni ban."

Tashi yayi zaune, tare da kallonta sannan ya zuba tagumi, dan ya fuskanci ga baki daya rashin kunyarta ba wani damunta take ba,
           "Me yasa baki da kunya? Me yasa duk abinda zai fita daga bakin ki baya zama me dad'i?"

        Jikina ne yayi mugun sanyi, kwanciya nayi, tare da lumshe idanuna.ban kuma bashi amsa ba, sakamakon barcin da yayi gaba dani.

      ***
SAMAIND

    A hankali suke shigar da sabon tsarin da aka shigar dashi masarautan.

      "Sultanah Hoyam, a da can baya kafin zuwan ki. Bayin da ake kawowa cikin daular nan,.toh akan fidda tsarin mu'amala da bayin ne!

          Mukam zab'e kyawawan cikin su, ga sarki tare da saka musu alama a hannun rigar su. Bayi kenan, Mataki uku zuwa huɗu ne.

    Kuyangin sarki ana basu wani ƙaramin kambu ne, su daura akan su. Sai bayi na biyu ana tura su shashin Sultan da Sultanah, domin su dibe musu kewa. Da kade kade da raye-raye. Sai mataki na uku. Akan tura su madafi tare da nasu girki.

      Sai matakin karshe ana tura su, aikin a cikin masarautan baki daya, tare tura wasu gefen tsohuwar fada."

     Matakin farko banbancin su shine suna da kambun azurfa, na biyu suna da jan zare a hannun rigar su.
Mataki da uku suka da koren zare a wuyar su, sai mataki na uku akwai kalar rawaya. A jikin rigar su. Sannan sai matakin horar da wacce zata iya zama Kwarkwarar sarki, zata kasance ba a hada ta da sauran."

     Kurawa Narmin idanu tayi sannan tace mata.
"Wannan ba zai zama matsala ba, dan haka. Jeki kawai zamu yi magana daga baya."
Narmin na fita ta jingina kanta da hannunta, karfin hali take amma tabbas tana jin kamar zuciyarta zata kama da wuta.

          *
"Dole ki hadu dashi yau, tare da nuna mishi murnan zama sarki na gaba.

    Jasrah karki sani jin kunyar kai na, ki bi duk abinda zasu saka ki."
Gyada mata kai tayi tare da, fita tare da nufar kofar da zata fita.

      ,--- tunda ta fita take bin zomo har gurin shan iskar da Sultan Aamaan Mehran yake zaune shi daya.
"Kai mavisha, katsa min mana karka gudu ka bar ni! Don Allah ka tsaya min."

    Aikuwa dan zomon na zuwa ya shige cikin kujeran da Sultan Aamaan Mehran yake zaune akai.
Tunda ta shiga gurin take kallon yadda lambun ya haɗu, a hankali idnun ya sauka akan wani kyakyawan halittar Allah. Gyara tsayuwar ta, tayi sosai tana kallon shi cikin al'ajabi, tunda take jin labarai irin na hikaya da al'ajabi bata tab'a jin ko ganin mutum me kyan halitta irin shi ba.

    Tun d zomon ya shigo, yake sane da shigowar ta, sai dai wani abun mamaki, shine kamar wanda aka gaya mishi ana cillo wani abu, da sauri ya saka kafar shi ya kwashe ta, aikuwa sai ga dogon mashi an wurgo mata ta bayanta.

Haka yaje ya faɗa kan itaccen tuffa, ihun da tayi yaja su Fudail da Darakshan, suka shigo lambu.

        Da sauri suka ce mata.
"Kwanta, karsu kuma wurgo miki wani abu!"

Kamar wanda suka sani aikuwa su ga wasu an kuma cillowa, dakyar suka kare yarinyar tare da turata hanyar gida, bayan kaman minti biyar, sai ga wasu ruwan kibbau, fauce takobin hannun Fudail.

        Ya nufi inda ake wurgo musu  mashin, tunda ya nufi gurin Fudail suka rufa mishi baya. Suna shiga suka tadda wasu gungun mahayan kisa ne. Suna shiga suka musu kawanya.

      Kallon yake, kafin ya kalli kayan fadar hannun su, tankar wasu dakaru.
"Da farko Sultan yana shirin yi muku afuwa, dan haka ku bar nan kafin ya iya sauya ralayin shi."

     "Kai shafaffe mara amfani, mu da uban gidan kare muke ba da kare ba, karka yarda na fusata. Domin zan koyawa wannan yaron da wuyar shi bata gama yayye shi ba, bari na nuna muku yadda ake gudanar da aiki cikin salama."

Cikin ihu suka nufe su, domin su musu ribdugu, sai dai ance ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare, domin cikin zafin zuciya, Sultan Aamaan Mehran ya tare su, lokacin guda aka fara faffata wani irin azazzaben yaki wanda ya sanya kura ta turnuke sararin samaniya.

           Lokaci guda aka fara cin kasuwar jini da gawargaki ake cikin su., kafin su ankarar da abinda yake Faruwa, Mehran ya musu muguwar barna, domin a cikin kankanin lokaci, kasa ta sha jinin ta koshi.

Baka jin kome sai karar takuba da Gatari.

           Dama ina nan na muku alƙawari......

Paid book.
Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/1034092544?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=GuO7QZMwU%2FP%2FXoEqsI0M1logOSHj%2B72o1vXIXR4Es5gqGkIQneuqZrg8irRFHx0MjVmpoIEb6MkTxTKSDYI8Yq60uLbQaYeOzkw8wbglg3C2gM1zL10iGPO104Nmoyng

🐾ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜🐾

_The Historical_
~BOOK ONE~
Mai_Dambu

Bismillah Rahamani Raheem.

Page 15..
Su goma sha huɗu aka Turi su, kafin kace me Sultan Mehran yayi musu rubdugu, ya dargargaje su na fitan hankali.

      Kura Mishi ido Rakshan da Fudail suka yi zuciyar su tana wani irin bugawa, zunzurutun tashin hankali ta tsoron shi da shakkar shi ne ya darsu a zukatar shi. Tabbas sun san an hora Sultan Mehran a cikin castly din shi, amma basu tab'a tunanin horon yakin ya kai inda zasu razana haka ba.
    Domin lokacin wasu mutane biyu suke zuwa horar da shi, daya dan kasar Hindu ne daya kuma ɗan ƙasar Sin ne. Mutanen biyu sun shahara a fagen yaki da dambe, kwararru ne a iya sarrafa takobi da kwari da baka.

    Sannan idan aka kuma ce za ayi tawo mu gama ne da hannu sunyi zarra. Dan haka kafin su gama nazarin waye Mehran, tuni ya haɗa gawarwakin mahayan kisan, ya zauna akan su irin zaman sadaukai. Ila mutum daya da ya bari a raye.

               Isowa gurin Rakshan yayi tare da marin mutumin yana tambayar shi.
"Waye ya turo ku?"
Dariya mutumin yayi sannan ya tofa mishi yawu me hade da jinin  bakin shi.

Wasa da takobin Sultan Mehran yake cikin shiru da nuna alamar lallai fa su tambayi mutumin.
"Kai Solobiyo, dan daudu. Ko kai mata maza ne? Ai ashe baka da lafiyar maza, haka fa aka gaya min tsoron ka nunawa mata Jarumatar ka a gado kake ko?"

Ya fashe da wata irin dariya sannan ya ja fasali yana huci.
"Ko baka san muna da labarin cewa, kai lusari ne baka iya kome ba sai bin maza ta baya?"

   Bai d'ago kai ba, amma tabbas maganar tana dukar shi sama da harin da suka kawo mishi. Kallon shi yayi tare da dauke kan shi daga kallon shi.
"Saura yan awani ka zama sarki ko? Toh tabbas saura awani ayi bikin mutuwar ka, na rantse sai sun shafe tarih.."

     Jifan shi yayi da takobi sai da duk suka razana, sabida yadda takobin ta raba kan shi gida biyu. Sai lokacin ake buza kansakalin yaki. Ko minti biyar ba ayi ba, dakarun masarautan suka musu kawanya, a fusace.

       A hankali ya mike tare da ratsa su, suna bashi hanyar,. Lokaci guda suna zuɓewa akan gwiwar su, hannun su dayansu akan kirjin su. Kan su a sunkuye. Haka ya wuce su bai ce kala ba..duk inda ya gifta dai dai ka ga zaratan maza suna zuɓewa a kasa ana jinjina mishi. A haka har ya isa fadar shi wanda yake cike da dattawa, tun kafin ya shiga cikin fadar an wanke shi da ruwan danyen madara.

  Wanda aka tatsota daga jikin saniyar, da dumin jikin saniyar, cak ya tsaya, basu fasa wanke shugaban su da madaran ba, sabida sunyi imani da cewa Sultan Mehran na daya haka ya tab'a faru dashi, yau gashi jikan dan shi ya maimaita, dan haka yana tsaye suka zuba Mishi ruwan zuma, ana wanke Mishi jikin shi. Tare da yin Imanin tabbas Allah ya kawo musu Sultan domin ya tsaya musu.

       Sannan koda zai kasance mara imani, tabbas gaba zai iya sadaukar da farin cikin shi domin Al'ummar shi baki daya.  Kuma koda ya zasu fidda matar da zai aura a matsayin magajiyar sarauta wato (Empress) kenan, zata iya kasancewa sa'ada a gare su. Kuma zasu sami sukunin rayuwar su da walwalar su cikin tsarin Ubangiji.

   Bayansa ina zuba Mishi zumar sannan suka bishi da ruwa me kyau suka wanke shi tass, sannan suka yayyafa Mishi ruwan turaren miski. Tun kafin ya isa gurin zaman shi an shimfid'a mishi wata kilishi me shegen kyau da ɗaukar idanu.

       Kujeran shi kuwa an saka mata wata yadi me tsantsi ruwan gwal, cikin jarumta da dakakkiyar zuciya ya zauna a saman kujeran da yake nashi ne shi dayan shi, tare da da dunkule hannun shi na dama  a k'ugun shi.
Hannun shi na hagu akan gwiwar shi, cikakken Basarake ya fito sak. Mik'ewa duk manyan mutanen da suke fadar suka yi tare da cewa.
"Mun bika munyi mubaya'a!"

       Shigowar Rakshan da Fudail rike da kan Yan tawayen da suka kawo mishi hari yasa kowa ya firgita. Wanda yayi dai dai da shigowar Sultanah Hoyam da sauri dan har labarin harin da aka kaiwa Mehran ta ya isa gare ta.
"Sultan Mehran. Wannan kan mutumin zamu bincika muga daga inda ya fito, domin mun gano tutar kasar Carboda,Sultan idan muka yi bincike muka gano wanda yake da hannu." Dakatar da Rakshan yayi tare da mik'ewa ya bar fadar. Yana fita manyan fadan suka mik'e.
"Sultanah Hoyam! Kowa yasan daga yankin Carboda kika fito meye kika sani akan wadannan maharan?"

        Wani irin kallo takewa Mir Rahil cike da mamaki da al'ajabi.
"Kuna nufin nice zan farmaki Mehran?" Ta tambaye su cikin tsananin zafin rai,

    "Ko baki farmaki Mehran ba, alamu ya nuna da na jikin Mehran ake son cutar da shi. Dan taya aka san yana can keb'entaccen lambun shi?" Inji Mir Umdatuddawla,

     Ga baki daya suka hade mata kai, tare da niman laka mata sharrin ita ta farmaki D'anta domin an sanya ta, ta bashi mulkin da take kai. Kasa magana tayi sabida zuciyarta tayi wani irin nauyi tare da tashin hankali, bata san lokacin da ta juya ba, domin suna bukatar amsawarta ko ta tinzira tace wani abu, domin su daureta da harshenta, sai dai kuma tasan halin su.

Ba iya su ba cikin gidan sarautar baki daya tasan abinda zatayi ta cimma nasara akan su, ta kuma san abinda zata yi ta lalata musu kome nasu shi yasa da ta Fahimci zasu sakata tayi magana shine ta bar fadar.

   Bata tsaya a ko'ina ba, sai gurin Mehran, tana shiga falon shi ta zube a kasa tana kuka tare da gaya mishi yau ita ake zargi da yunkurin kashe shi, wani irin kuka take tare da rantsuwa, kura mata ido yayi sannan ya tako har zuwa gabanta, d'agata yayi tare da saka kanta a gefen kirjin shi yana rarrashinta.
"Wallahi Mehran kaji na rantse maka bani na turo su ba, Don Allah ka yarda dani"

*Wallahi? Na rantse? Toh me Ammu take nufi? Don Allah? Toh waye ne Allah nan?*

      Shiru tayi sakamakon yadda yake buga bayanta, a hankali ya janye jikin shi, fuskar shi cike da tambayoyin Waye Allah?

    Sai dai yadda yake din nan bai da cikakken lokacin da zai yi tambayar waye Allah? Dan haka ya juya tare da niman komawa gurin zaman shi yana wasa da tuffa.
"Mehran! Don Allah kace wani abu mana?" Shiru yayi yayi tare da dauke kanshi akanta.

"Mehran shekara ashirin da bakwai rabon da naji muryan ka?"
   Idanun shi ne suka yi jajjur, yana tambayar kanshi.
*Wacece ta bukaci na rayu babu wani kusa dani? Kece? Dan haka yadda kika daura Ni haka zaki hakura dani! Babu shakka kin cutar dani Ammu!*

Ya faɗa dan shi kanshi ba zai ce ga ranar da yayi magana tun ranar da ta dauko shi ta kawo shi cikin gidan, yana kuka da ihu ba dai zauna ba, har ta b'acewa ganin shi. Bata kuma dawowa gare shi ba, sai bayan shekara biyu, tazo ganin shi. Lokacin ya saba da kadaici. Baya son yanayi sai ko idan yana karb'an horon yaki.

        Lokacin da ta fara kawo mishi yan mata ba zai ce ga fuskar su ba, amma tabbas ya fahimci abinda take nufi a lokacin.

           "Mehran don Allah ka bar azabtar da ni, da shirunka wallahi ba zan iya jure wannan yanayin ba. Nasan nayi kuskuren tafiya na Barka amma wallahi ban yi dan kai na ba, sai dan kai. Mehran masarautan nan cike yake da tashin hankali, dole na keb'ance ka domin ka samu horo na musamman.

    Mehran wannan lokacin da ban dauke ka ba, haka zaka zama sarki babu wani girmamawa, babu shakkar ka a idanun su, Mehran ni!"
      "Ki je kawai"
A birkice ta d'ago kanta tana kallon shi wani irin kuka ne ya kwace mata, da sauri ta je ta zube a gaban shi tana kuka tare da cewa.
"Mehran nice kayiwa magana, Allahu Akbar Allahu Akbar Ubangiji nagode maka,

Please Login or Register in order to submit comment