Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki ba, ko na kama ki ba ai mun wucce wannan matakin, ke fa kanki zaki kashe kanki muje zuwa."

       Tana ana fadar hakan ta juya tare da barin gidan, tana hanya amma kuka take sosai kamar yarinya domin ta kadu ainun da taji irin cin amanar da aka mata, musamman na kusa da ita.

  ~~~
SAMAIND
Shiru fadar ya dauka, an rasa wanda ya yarda da amincewa akan janye yakin da aka yi, gani suke kamar akwai wani shiri ya sa aka ta cewa an janye, kallon juna suka yi kafin suka ce.
"Anya wancan kurman bai shiga cikin al'amarin ba kuwa? Dan nasan haka kawai baza a janye yaki ba.'

    Shiru suka yi sannan Mir Fawwaz ce.
"Kuma gaskiya be bana tunanin ya shiga, nafi zargin kawai sun janye daga yakin ne kawai!"

  "Ni kuma nasan zai shiga, wa mune ba zai bude baki ya gaya mana ba, amma tabbas ya shiga yaƙin." Haka suka yi ta muhawara, karshe dai suka tattara batun suka watsar.

      Sai batun yaran su da za a kai can din, lokaci guda suka tsayar da shawara da ra'ayi akan nan da sati me zuwa zasu tura yaran su can ina Mehran yake, dan haka suka gama tsara kome.

       Bayan sun gama da kulla yarjejeniyar aikin su, sannan suka bar gurin.

     ......
Kallon Jasrah yayi sannan ya mika mata wata yar Kwalba, yace mata.
"Wannan a cikin abincin gidan zaki na bawa ana zuba musu, ke karki ci, sabida gubar hana daukar ciki ne, ni ina Son koda zaku zauna dashi dan nasan dole zai bukaci mace, Toh ga shi nan ki zuba musu a cikin abincin su.

          Ina Son ke ki san yadda zaki shige mishi sauran bayanin zan miki idan kome ya kankama, kafin karshen shekarar nan ki tabbatar kin sami kanshi, sauran matan kuma,"

Murmushi yayi mata, sanan ya kura mata ido, kafin ya rab'a mata abinda yake bukatar tayi musu. Kuma ta amince. Tare da yin alkawarin sai ta sanya shi farin ciki a rayuwar shi.

      •••
A can shashin Sultanah Hoyam kuwa, Darakshan ne yake ta gurzanta, bakin su hade da juna, sabida yadda yake gurzanta ihun take yi, gyara zaman shi yayi a Jikinta, tare da maida hankali akan hak'e da yake yi. Bai d'aga mata kafa ba, sai da ya mata wani irin shegen ci na fitar hankali, sannan ya koma gefe yana sauke ajiyar zuciya.

   "Ina Son ka kashe min Mehran?" Da sauri ya kalle ta, sannan ya fashe da dariya, yana faɗin.
"Baki da hankali!"
Cikin tsawa ta ce mishi.
"Kana hauka ne?"
"Nice bani da hankali? Ni sa'ar ka ce? Dan ina kwanciya da kai "

  "Ke baki da lissafi ne? Mehran din zan kashe miki? Ko ce miki akayi dan kukwaiyo ne da zan kama shi na kashe shi. Hmmm! Baki san waye Jarumi ba! Ko an ce miki haka kawai mayakan hadin gwiwa zasu janye bata tare da wasika sun janye ba, Toh shi ne dai ya saka su janyewa, wani ba.

       Ana tauna tsakuwa dan aya taji tsoro, bawai dan ka girgiza wanda ihun shi daidai take da tsawa lokacin damina, sauke shi kawai aka yi abokan gaba suka taro mana duk ranar da kuka kashe shi wallahi toka babu wanda zai samu a wannan Daular."
Yana gama gaya mata haka ya mike tare da barin d'akin ma, dan haushi, yana shafa inda ya zabga mishi haushi.

      -----Abincin aka jera mishi cikin wani irin yanayi yake kallon abincin, a hankali ya dauki tsinke sakace hakori ya shiga d'aga abincin, kallon su yayi sannan yace.
"Amma yau ba Sultanah bace tayi abincin nan ko?"
Kallon shi Shairah yayi sannan yace mishi.
"Eh ranka shi dad'e! Bata jin dadi je shine tabarwa Mahlika girkin"

      Murmushi yayi sannan yace..
"Toh ku dauka dan ba zan iya ci ba" yana gama fadar haka ya nufi dakin Da Fazilatul nisa take, ya kwankwasa, tana kwance. Yana shiga ya hango ta cikin bargo. Fitowa yayi tare da fita can waje, haka yayi ta tsinko ganye har ya gama sannan ya nufi cikin gidan.

    Malamin shi ya samu yazo karatun.
"Malam kayi hakuri, yau babu lokacin karatun nan ina da mara lafiya ne a cikin gidan."
"Toh Sultan Mehran! Allah ya bata lafiya." Ya faɗa tare da barin gidan
  
Suna matukar girmama juna, kasancewar shi din malamin shine ɗan haka yake girmama shi, kuma yake Mantawa shi wani ne a da can a baya, gudun kar girman kai ya hana shi moran addinin Musulunci.

   Shima yana girmama Al'amarin Sultan kasancewar yana bashi girman shi, shi yasa idan zai kwana bai rike karatu ba, baya tab'a d'aga kai yace zai tafi kuma bai tab'a jin dan yafi shi ilimi ya wulakanta kan shi ba, asalima ana girmama juna da mutunta juna, (kuskuren da wasu suke samu kenan, a rayuwa da zaman takewar mu)

        Bayan ya tafi shima Mehran ya shiga bawa Fazilatul maganin da ya haɗa har da zuba, tana sha yana kallon ta, can yaga tana had'a gumi, dan haka ya gyara mata kwanciya, sannan ya mike tare da barin d'akin, domin ya lura da barci zai dauke ta.

       Kasa zama yayi a karon farko da yake ganin ina ma da Ikram tana zaune, ya tuna ranar da bai ji dadi ba, tayi mishi wani shayi me hade da kayan kamshi, dan haka ya shiga kitchen ɗin yayi ta duba kayan kamshin, yana gama haɗawa ya shiga zubawa a tunkuyar har da ganyen shayi, ya rufe tare da hada mishi wuta, sannan ya shiga hada mata wani farfen sun nama, karamar dabba.

        Kasancewar ana iya ajiye nama ya dauki tsawon lokaci a cikin kasar ta hanyar saka shi cikin gishiri, yana tsotsar ruwan jikin shi.

       Haka ya saka yana daukowa ya wanke tare da jika namar, bayan ya gama ne ya dauki kome ya wanke, yana kallon duk abinda Ikram take, idan ta gama girki bata fita sai ta wanke kayan da ta b'ata, murmushi yayi sannan ya ce.
"Yarinya me kama da aljanu!" Haka ya kammala girkin yana me jerawa a tire, sannan ya nufi dakin Sultanah, ya ajiye mata.

   Sai da ya kawo mata ruwa ta wanke bakinta, tare da zama ta fara shan shayin da ya kawo mata, dan ta sha magani, tana cin abincin tana kallon shi. Murmushi yayi mata domin baya jin wani abu na wahalar da kai kamar yadda take kallon shi cikin tausayi, ganin hannunta yana rawa ya sashi amsa yana bata yana mata hira, har ta koshi. Sannan ya tattara kayan ya nufi kitchen dashi, ya ajiye Narjis ta shigo ta wanke.

            Sannan ta fara kokarin daura wani ruwan da za'a kuma bukata. .shiga dakin tayi ta mata ya jiki.
"Da sauki! Ga shi Mehran ya kula dani!"
"Duk mutumin kirki zai so ya kyautatta lahiran shi dan haka ba laifi bane dan ya kula da Uwa kamar ki" inji Narjis,

"Allah ya biya mishi bukatar shi ta Alkhairi, ya dawo mishi da abinda ya rasa, ta hanyar Alkhairi"  cikin wani irin kunya Mehran ya mike, wai shi nan yaji kunya dan anyi Mishi Addu'ar Allah ya dawo mishi da Ikram,

Murmushi suka yi ganin ya fita kan shi a sunkuye yana murmushi, abin yayi mugun mata dad'i, yadda yasan abinda yake.

  "Sultanah ya kamata kuyi wani abu yarinyar nan ta dawo mishi! Shekarun shi kara hawa suke, zai zauna ne babu mace?"

"Ina sane dashi Narjis! Bana son a sami matsala ne, zuciyar shi ita yake so! Su kuma sun shirya zasu  turo y'ay'an su, bana son ya zama ya zab'i daya a cikin su. Shi yasa nake addu'a Allah ya kawo ta kafin lokacin ya kure" inji Sultanah,
"Ni kuma tsoron kar tazo kome ya sauya nake, tsoron kar ƙaddaran masarautan nan ya shafe ta nake, Sultanah bana son ta zama d'aya daga cikin masu la'antar masarautan nan! Bana son Ikram ta sami karfin mulki, nafi son ta sami soyayya ya gina zuciyarta, Sultanah karki manta matukar karfin mulki ya shige ta.

    Daga nan kome zai zama ya rikice, babu me iya tankwarata, babu me iya gaya mata sai abinda masu zagaye da ita suka gaya mata, Ikram bata san kome ba sai fada da zafin rai taya zamu barta ta a jikin shi. Bayan" kura mata ido Sultanah tayi tana mamakin yadda aka yi bata Fahimci abinda yake faruwa ba.

   A jiyar zuciya ta sauke tare da cewa.
"Tabbas rayuwa da mutuwa duk tsari ne na Ubangiji, amma bana jin a raina haka shine mafita, Ikram zata dawo jikin Mehran, sabida itace kashin bayan dukkanin mulkin shi. Abinda zai faru yanzun ko wani lokaci, duk sha'anin Ubangiji ne, babu me iya goge ƙaddarar wani da na goge zanen ƙaddarar Ikram da Mehran!

       Domin ko babu mulki sun cancanci zama da juna, ko babu kome suna bukatar soyayyar gaskiya! Akwai abinda na sani akan wannan yanayin, abu daya ne zai iya karya karfin faruwan Al'amarin Ubangiji."

   Turo kofar ne ya hanata karasa abinda zata fada wanda shine abinda zai rage karfin tasirin.

"Ranki shi dad'e! Anyi baki daga fada!" Inji Shairah,

"Toh kace musu ganin nan zuwa!" Ta faɗa a sanyayye, tana kallon Narjis,
Saka rigarta tayi sannan ta daura babban alkyaba ta fito daga d'akin, falon suka shiga a razane suka miki, dan basu yi tsammanin tana raye ba.
"Fazilatul nisa!"
"Zauna mana! Karku damu, meke tafe daku?"
Zama suka yi tare da kallon juna, sannan suka ce.
"Ai mun zo gurin Sultan Mehran ne, kuma"
"Fudail kira shi mana!" Ta faɗa tana kallon su.
"Narjis basu ruwa da shayi,"

"A'a a'a. Mun gode! Haka ma ya ishe mu!"
Fitowar Sultan Mehran yasa su, mik'ewa tare da gaishe shi.zama yayi tare da kallon su, mika mishi tiren shayi aka yi ya dauka tare da kaiwa bakin shi yace musu.
"Hmm!"
Yayi da yayi musu alama da hannun yana jin su, daukar kafar shi yayi tare da daurawa akan daya, yana kallon shayin shi.
Basu iya zama ba, suna daga tsaye suka dukar da kansu.
"Sultan daga Bahrain! An aiko da sakon." Suka ciro takardan tare da mika mishi.

"Karanta shi Fudail!" Inji Sultanah.
*Amincin Allah ya tabbata ga Adalin shugaba na kasar SAMAIND! Wannan sakon ta godiya da jinjina ce sannan muka maka albishir da baka Sarkin Yakin Mu Sakeenatu binti Abu Waqqas! Idan ka amince ka amshi wannan sakon da girmamawa! Mun muka fatan Alkhairi da nisan kwana!*

Ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon Sultanah, bai ce kome ba ya miki abin shi. Domin bai da tacewa sai abinda tace mishi....

_KUYI HAKURI YAU BABU PAGE 2! SABIDA WEEKEND NE ZANYI HIDIMAN GIDA DA NA YARA_
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

17
*Me yasa bata jin magana? Me yasa tayi iyaka da shi? Me yasa ta zab'i muradun zuci sama da nashi? Me yasa bata tab'a tunanin shi din ba kowa bane matukar bata tare da shi,  gurbin da ya zab'a mata gashi nan ana shirin cikewa*

"Ku maida musu sakon godiya! Sannan tana da damar shiga masu tsayawa a matan da Sultan kofa a bude."

"A'a! Idan zata iya jira nan da shekara goma toh!" Juyawa suka yi suka kallon shi cike da mamaki, wannan wani irin yanayi ne haka. Juyawa yayi tare da barin gurin, ya nufi can back yard na gidan, ya tsaya yana kallon dajin da ke bayan gidan cikin wani irin kewa na musamman. Ba zai iya kamanta iya adadin kewar ta, ba a yanzun ya yarda da cewa yana masifar kaunar ta, amma ba zai iya amai ya lashe ba. Ba zai iya juyawa maganar shi baya ba, ba zai iya kallon tsabar idanun jama'a yace musu yarinyar da tayi aure da wani yake so, waye zai fahimci ainihin sirrin shi? Ita daya ce mahaukaciya kawai, ta lalata mishi kome sannan tayi nesa dashi!

"Amma wannan hukuncin da ka yanke ba." Juyawa yayi ya kalle ta, sannan yayi murmushi yana kallon yadda iska yake kad'a ganye, zata kuma magana ya juya tare da kallon ta, yana me nad'e hannun shi a kirjin shi.

    Dole tayi shiru, amma kuma yanayin yadda fuskarta ta nuna kamar bata ji dadin abinda yayi ba.
"Sau dayawa muna iya sauya ra'ayin mu, sai bamu cika son tistawa ba." Ta faɗa a sanyayye,
Bai ce mata uffan ba, har ta gama magana, zata fita sai kuma ta tsaya tare da cewa.
"Bai zama dole ka dauki abinda nace ba, matukar aka san girma da darajar da ka bata a zuciyar ka, tabbas iya shi ya ishe makiyan ka, buga ka da kasa. Ba tare da sunyi amfani da wani makami ba. Da iya SOYAYYA aka salwanta da rayuwar sarakunan baya, dan haka karka zurfaffa abinda ba zai fidda kai cikin sauki ba."

     Tana kai aya tayi fucewarta domin lallai ranta ya kai kololuwar ɓaci, kuma bata son ta nuna mishi haka har ya fahimta,. Sam bata kaunar dalilin da zai sanya ya fahimci bata kaunar yarinyar ko soyayyar da takewa yarinyar ya fita a ranta, sai dai kamar yadda ta sha fada a baya. Sarakunan daular kamar wad'anda aka musu tsafi da macen da suke so.

     Idanun su rufewa yake basa ji basa gani sai sun tsinci, kansu a gaɓɓar mutuwa suke iya gane illar so. Ita kan tana tsoron kar wani abu ya faru dashi domin bata iya jin zata yafewa kanta.

   Dan haka ko ta halin k'ak'a, sai ta dakatar dashi wannan makauniyar soyayyar da yakewa Ikram, tana tsoron kar soyayyar ya zama illa yadda ba zai iya dakatar da ita ba.

     Tana shakkar kar makiya da kishi ya kai wasu amfani da Ikram domin cimma manufar su akanta da shi kan sa. Babban dalilin da take iya hangowa domin dakatar da wannan makauniyar soyayyar, ba kome bane matan da suke kokarin shiga rayuwata su da iyayen su ba kananun shu'umar ba ne.

      Domin iya haka aka barsu da Ikram sun damata sun shanye kuma zasu iya mata dalilin da sai ta tsani kanta da shi kan shi Mehran din. Kai ina bata jin zata barshi haka ya tafi kamar yadda suka zalunci ta dole, su dauki alhakin ramuwar gayya, toh kuwa idan ta rama ba zasu yi hakuri ba zasu suce sai sun ga bayan shi.

    Ji take kamar ta kumar ihu, domin bata da wata hikima ya tsaya mata cak!
"Narjis! Yanzun naga amfanin tsoron ki! Domin Mehran ya makance akan mace don Allah kiyi wani abu!

   Bana son na rasa shi kamar yadda sarakunan daular suka yi ta rasa rayukansu, idan ta kama ma kar Ikram ta dawo daular nan don Allah kiyi wani abu ina son shi da Ikram amma kuma bana son ya mutu akan so, bana son na rasa shi a matsayina na Mahaifiyarshi zuciyata ba zata dauka ba,.kiyi wani abu nace."

Kasa magana Narjis tayi tana kallon kofar dakin, jikinta yana kerma, d'ago kai tai zata mata magana taga tayi mutuwar tsaye, juyawa tayi Mehran ta gani yana kallon su.

"Don Allah karka min mummunan fahimta,  ka fahimci ni bawai ina nufin zan rabaka da Ikram bane."
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Eh Toh ban ji kome ba! Ban kuma fahimci me kuke nufi ba, naji kina cewa a matsayin ki na Uwa ba zaki iya me ba?" Ya koma yana tambayar su, ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa.
"Alhamdulillahi! Toh yi maza jeka bada kai nake ba tunda baka ji ba, a bar maganar haka"

    Bai ce mata kome ba sai murmushin da yayi, sannan ya saka kai zai fita yace mata.
"Ban tab'a soyayya ba, kuma bana jin yin shi. Amma akan wacce nake jingina rayuwata bani da dadin mu'amala!" Ya fadi haka tare da barin d'akin.

"Sultanah! Kina ganin kamar kuskuren ne idan kika Barsu a tare? Ko kina ganin zai iya dauke kai daga abinda zasu mata, ba zai iya hakuri ba akan abinda yake so ba, Don Allah Sultanah matukar Ikram zata zo karki sauya mata.

  .. yau kina tare da d'anki ne saboda ita, yau idan kika juya mata baya babu wanda ya isa ya tabbatar mata da nutsuwar da zata samu. Addu'arki itacce zata sauya kaddarar su, don Allah karki bari abinda ya faru da sarakunan daular ya tab'a zuciyar ki."

       Shiru tayi tana nazarin abinda ya faɗa da kuma wanda Narjis ta faɗa, kusan abu daya ne amma kuma ita Uwace. Taya zata dauki kasadar rabuwa da abinda ta shigo yaki domin shi. Zata iya mallakawa Ikram amma sauran matan fa? Idan za ayi duba na gaskiya zata iya cewa wa Ikram ta haifawa Mehran, ba sauran matan ba, dan haka zata yi kokarin ganin ta boye tsoronta ta maida Ikram wacce zata bi ra'ayin shi.

      Sai ta nuna mata itace ta dace dashi yadda ba zata kullace shi a ranta ba, zata so soyayyar su ya zama wanda babu wani abu a cikin shi sai tausayi da kaunar Juna.

     Ajiyar zuciya ta sauke sannan tacewa Narjis.
"Bani ruwa na sha"

Daukar ruwan ta yi tare da mika mata, tasha sosai kafin ta ajiye kofin tace.
"Bari na huta,"
"Toh Sultanah a tashi lafiya!"
Daga haka ta fita. Kasa kwanciyar ma tayi tana tunanin halin da Mehran yake ciki, yaki maida hankali akan abu daya, sam ta kasa gane shi wani irin mutum ne da baya nuna yanayi. Shi. Sai yaki ya fahimtar da kowa waye shi.

     Sannan a haka ake bukatar bashi mata toh me zai musu? Ko baida lafiya ne? Anya kuwa? Kai haba toh me yasa baya bukatar mace? Da sabida mace daya ka zab'i zama na shekara goma! Kayiwa kanka iya ka da abinda zaka sami nutsuwa dashi. Kasa zama tayi ta kuma fito. Can back yard din ta koma yana tsaye tare da rike alkama yana kiran tsintsaye, yana watsa musu tsabar alkamar.
"Mehran!"
"Na'am! Anne!" Ya fada a hankali, da sauri ta kalle shi. Cike da mamaki bakinta yana rawa, tace.
"Ka kirani da Mahaifiya ce fa?"
Murmushi yayi sannan ya cigaba da abinda ake sam bai da wani karsasha ya gaya mata haka ne domin yadda take damuwa da shi, dan haka shima ya damu da ita.

    Uwa ce kawai take iya damuwa da cutar D'anta, ba tare da taji labarin zai mutu ko zai rayu, shi tashi uwar Mantawa tayi dashi dan haka ya juya tare da zuba mata ido, kokarin maida kwallar da suke son zuba tayi tare da cewa.
"Shin baka da lafiya ne irin na sauran mazan?"  Cikin wani azzababben kunya ya juya a hankali yana me ji kamar kasa ta tsage ya shige cikin shi.  Yau yaji abun kunyar da ta dame shi. Dan haka yaki juya mata domin maganar ta sashi jin mugun kunya sama da kowani kunya, kai ko lokacin da Sultanah Hoyam ta tambaye shi bai tab'a jin kunya haka ba.

    Kin juyawa yayi, tare da kin magana, gaban shi ta koma shi kuwa ya juyar da kan shi ta d'aya bangaren.
"Baka da lafiya ne kamar sauran mazan nake tambayarka? Kaki min magana"
  
Sunkuyar da kai tayi tare da kin d'agowa, ita kanta bata ga abin kunya ba, dan tana tambayar shine a matsayin ta na Uwarshi ba wai wani abu ba, amma sai yaki koda kallonta..dan haka tafito da sauri tana kiran Fudail da Shairah da Narjis. Duk suka hadu.

    Kamar zata yi kuka take gaya musu abinda ta tambaye shi. Sake baki suka yi suna kallonta, kafin duk suka watsa kamar wanda ta watsa musu wani abun tsoro.
"Toh kuma ina zaku? Muna magana zaku gudu ai sai ku tsaya ayi maganar gaskiya!" Su kuma dalilin ganin Sultan yana tsaye ne yasa su guduwa, suna dariya. Wato idan ya fahimci Anne so take ta gayawa duniya dai...

"Kai Aamaan Mehran! Shin kana da ra'ayin maza ne?" Murmushi ne ya kwace mishi sannan ya tuna da tsohon zargin shi da ake cewa wai yana bin maza wato (dan luwadi)  dan yaji yadda zata rikice, sai ya wani kalle ta, sannan ya sunkuyar da kanshi irin eh din nan.

    Ihu ta saka tare da kiran Fudail, rike bakinta tayi tana kallon Mehran da Fudail, sannan tace mishi.
"Yarona Fudail! Gaya min shin Shugabanka yafi son mu'amala da maza ne sama da mata!". Kan Uba,. Da wani mugun sauri ya kalli Mehran, kashe mishi ido yayi tare da mishi alamar ya amince, da tambayar ta.

     Cikin wani irin shauki da takaici kamar zai fasa ihu, ya kalle ta sannan ya dauke kan shi ya kuma duban Mehran, ya ɗan ciji bakin shi sannan yace mata.
"Labarin yana da tsayi, idan nace zan gaya miki zaki iya faduwa baki shirya ba, amma Sultan kan..... Sai godiya."

Ya faɗa ina cizon hannun shi. Dab'as ta zauna tare da cusa hannun ta cikin gashin kanta, taji kamar ta kurma Ihu, dan haka ta nuna musu hanya su bar mata falon bata son ganin su. Da wannan yanayin ya shiga dakin shi.

Ya zauna yana murmushi, haka kawai yake jin shi yau yayi nishadi, murmushi ya kuma a karo na biyu, yana tausayin ta. Amma bayana nufin zai bar musu rayuwar shi su gara mishi bane.

    Dan haka ya kwanta a hankali barci me dad'i ya dauke shi.

    A bangarori daban daban,.ana kan shirin za a turowa Sultan Mehran mata, dan haka suka maida hankali gurin koyawa Yaran su mata yadda zasu kwace Mehran, karsu bawa wasu damar rab'a ban shi. Idan kaga yadda suke gudanar da abin sai ya baka tsoro, domin shirin da suke zaka zata aure ne kuma duk kawai zab'e ne.

    ~~~
Askandariya.
Shiru fadar Sultanah Amrah yayi sakamakon yadda Waziriyar ta Nairah take bayanin abinda ta aikata, tana kuka. Ita kan Sultan Amrah bata iya magana ba, sai ma sunkuyar da kanta da tayi tana kuka. Tana tambayar kanta meye tayiwa Nairah da zafi haka?

   Me yasa Nairah bata gaya mata mulki yake so ba? Da ace lokacin ta ce ita mulki take so wallahi da ta bar mata, akan mulkin banza ta rabata da Yarinyar da take kauna babu ita babu yar uwarta, duk sun rasu.

         Hawaye ne ya zubo mata, sannan tace.
"Ba zan iya kashe ki ba! Nasan yadda kowacce uwa take ji idan ta rasa D'anta, a halin yanzun kuwa nasan kina cikin rashin Yarki dan haka babu hukunci akanki, kije Allah zai bi min hakkina indai na zalince ki babu abinda zai same ki, idan kuma ni kika zalunta, Idan nace ban yafe ba na rena iyakar shi ce dan haka Allah yasaka da Alkhairi zaman da muka yi dake!" Ta karshe maganar cikin wani irin kuka me hade da murmushi, domin iya haka kawai zaka Fahimci tana cikin damuwa...
#Mai_Dambu
200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641.. Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

19
"Me yasa baki Fahimci sabida ke take raye ba? Me yasa baki gane girma da kaunar da yarki take miki ba, sabida kina tare da shaidanun mutane irin Nairah binti Namdar, dan haka kamar yadda taci amanar mu, har ta kai da shirya juya mulki dole mu zartas da hukuncin mu akanta."

       "Kyale ta Khadim! Kyale ta tayi rayuwa, kyaleta duniya zasu gaya mata abinda na gaza gaya mata" sannan ta fashe da kuka, share kwalla tayi sannan tace musu.
"Yar Joindah ta turo min sako, tace na tafi Merocco, naje akwai dangin mahaifinta a can me kuka gani?"

           Share kwalla suka yi sannan suka ce mata.
"Duk yadda kika ce! Mu masu miki biyayya ne babu abinda zaki ce muce miki a'a!" Da wannan ta mike a hankali ta bar fadar, tun da tashiga d'akinta dariyar yaran ta, yadda suke gudanar da sha'anin su na farin ciki a, shi yake yawo a kunnenta.

    Yadda suke wasa da matashi a dakin shi yafi komai mata dad'i, a hankali ta taka har gaban gadon da yau ya koma mata kamar yau aka kawo dakin, shashekar kuka ta ja,

Please Login or Register in order to submit comment