Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi. Kallon shi tayi sannan ta mike a hankali. Bata tsaya wanka a dakin shi ba, ta saka kayanta tare da fita daga d'akin bayan ta ajiye mishi wani tambarin da zai iya wargaza mishi kome har karshen rayuwar shi.

      ~~~
Sai da ruwan nan ya kare tsaf akan Fudail ya shigo Masarautan, koda ya shiga shashin sa ya nufa yayi wanka da ruwan zafi sannan yana wankan tare da murmushin abinda Mehran yayi mishi bai wani damu can ba, sabida ko shi aka yiwa haka iya hukuncin da zai yanke kenan.
Dan haka babban abinda yake shirin akan Azizatul Nissah ce.

     ~~~
Munyi tafiya me nisa wanda muka bar yankin Farisa sannan muka nufi kuduncin jazziratul Arab, anan muka yada Zango. Tunda muka tsaya aka gama shirya mana tantin mu. Na shiga gurin Sultanah Amrah, na zauna duk da ba hira muke ba, amma kuma haka yana sani jin kamar ina tare da Ammyn na ne, dan haka bayan munyi sallah na kwanta a gurin, ita kuma ta cigaba da abinda take,  lokaci zuwa lokaci tana kallon yadda nake barci.

      Hawaye ne ya zubo mata, ta girgiza kai sannan ta cigaba da aikinta, tana tuna abubuwa dayawa akan yaranta da mulki yasa ta manta da su. Tabbas mulki matukar baka nemi Izni Allah akan shi ba, zai iya kai ka ya baro ta,

          Kamar yadda ya kaita ya baro ta, sai dai ta wani gefen zata iya godewa Allah tunda akwai Ikram da Ilham, Yar gidan Abrad. Murmushi tayi bayan ta shafa kanta, tana me jin kewar Yaran ta.
      
       ... Zan iya cewa barcin da nayi me cike da gajiya da mafarkai marasa kyau da dad'i, karshe dai haka na farka da sunan Mehran. Da gudu Rahil ya shigo tantin. Da sauri ya iso gabana, fadawa jikin shi nayi ina haki. "Me ya faru?" "Mehran!" Na fada kamar zanyi kuka. Juyar da kan shi yayi. "Ba zaki daina kwadayin ganin shi ba?" "Karka raba ni da shi, zuciyata halittar shi ce." Matse bakina yayi idanun shi cike da kwalla. "Ni kuma sabida ke aka halicce ni, ina sonki Ikram. Nasan idan ba zama daya muka yi ba, ba zaki daina kwadayin shi ba" ya faɗa bayan ya cire hannunsa a bakina, kokarin hada bakin mu yake na kawar da kaina. "Meye kike nufi? Ba zaki." Ture shi nayi tare da mik'ewa, ya kuma tasowa yana kallona. Kamar zai yi kuka yace.
"Meye yafi Ni dashi? Meye na rasa da ba zaki amshi tayi na ba, wallahi yau sai na dasa miki kaunata a ranki." Fada sosai muka yi da Rahil domin ya kafe sai ya fahimtar dani yadda yake sona. Ni kuma na rantse ba zan yarda da wannan tunanin na shi ba haka muka gama dakyar na kwaci kai na.

     Sam na kasa nutsuwa a raina, domin kuwa, haushina yake ji kamar ya kashe ni, bayan fitar shi Sultanah Amratu ta shigo, fadawa nayi jikinta ina kuka. Tare da cusa kai na a jikinta.
"Zuwa yanzun ya kamata ki cire Sultan Aamaan Abdus Samad Mehran, a ranki domin kwanaki ƙalilan zaki kasance matar Rahil. Don ki daina tunawa da sultan Aamaan."

     Kallonta nayi baki sake, kafin na sauke idanuna kasa, ina kuka.
"Ummyn!" Yatsar hannunta ta saka min akan bakina, tare da girgiza min kai.
"Kowa yasan cewa kece kwarin gwiwar shi, ki taimaka ki sauko ayi kome cikin ruwan sanyi."

    Hawayen da nake tarewa suka  daga cikin idanuna, na kasa magana baki daya sai kallonta nake.
"Tsarin masarautar mu, cike yake da kawaici da YAKANA karki yarda ahalin Mahaifinki su fahimci kin sayar da zuciyarki ga wanin su. Domin haka tilin abin kunya ce gare mu!"

"Toh dole ne sai na rayu cikin mulki? Me yasa ba zaku gan.." d'aga min hannun tayi tare da kallon, yadda bakina yake rawa. Kifa kai nayi a tafin hannuna, na fashe da kuka. Ina girgiza kai,

    Tashi tayi tare da bar min tantin kuma ta hana kowa shigo min, domin tana ganin matukar suka shigo min zan iya tsarewa. Gurin yan uwan Baba na, ta nufa suka tattauna. Anan suka ajiye shawara ita zata wuce Asakandariya su kuma su wuce dani can Merocco. Idan ita mace ce mai rauni tausayina zai iya sakawa ta bani abinda nake so.

  Su kuma ahalin mahaifina babu wannan yanayin a tare dasu, dan haka su tafi dani. Bayan ta dawo ne, take kallon yadda na kifa kai ka a saman gwiwar kafana.
"Zaku wuce Merocco."
Da sauri na d'ago kai na, zanyi magana ya juya min baya bata bani damar ma tambayarta ba, ta cigaba da abinda take, ni kai na nasan ba zan iya tababa da ita ba, amma kuma ya kamata su fahimci abinda nake so. Bayan mun huta aka kuma tadda tafiyar. Ina ji ina gani ta tafi da Nimrah.

Ni kuma muka tafi da Izmah, bayan mun sha kuka. Tunda muka dauki hanya, banzan can yake wani shige min. Ko kallon shi banyi ba, har muka wuni  a hanyar, dab Magarib muka shiga garin, wanda tun kafin mu iso labari ya iso musu muna kan hanyar mu, sakamakon wani mahayi da aka turo shi.

  Dan haka garin ya kasance kamar ana bikin sallah, wani irin biki ake me cike da shagali. Haka muka isa har fadan, inda aka muka yada zango  a falon Sultan Mu'allim. Mika min hannun yyi. Da sauri na isa gare shi. Ina isa na zube gwiwata a kasa, kai na a bisa kafadar shi, na sake kuka me cin rai. Takaici yasa Rahil fita a gidan.

       Kuka nake wanda idan ka tambaye ni ba zance maka ga abinda aka min ba, amma kuma a cikin raina, ina kuka ne domin na rasa Mehran. Yadda nake kukan ya sashi sake murmushin jin dadin. Sannan ya shafa kai na, yace.
"Kiyi hakuri! Haka muke tsara miki baki rayuwar. Da karen layi gwara Zakin gidanka koda kuwa zaka zane shi da bulala ne,  kiyi dan mahaifanki da kanwarki. Ba akan ki da soyayyar ki ba. Mun rigada mun yanke kuma al'adunmu sun sha banban da kowane, mukan iya binne abinda muke so! Mukan iya boye abinda muke kauna, matukar hakan zai bamu damar fuskantar matsalar.

      A tsarin mu, bai zama dole mace ta samu abinda take so ba, matukar zata bawa Mulkin mu. Gudunmawa dan haka na zab'i ra'ayin shi sabida ki bashi gudunmawa.  Yanayin ku yayi daidai da mulkin, abinda ake bukata domin mulki kin hada, dan haka ki amshi Rahil a matsayin abokin rayuwar ki."

          Hawaye ne ya shiga zuba min, na kasa magana tare da sunkuyar da kaina, domin yayi min kwarjini. Haka aka fitar dani har dakin Bilqisul Ikram, tankwarata. Shafa kaina tayi sannan ta kira amintattun bayin ta, suka shiga dani ban daki. Aka hada min wani irin ruwan wanka tare da turaruka masu dadi. Sai furen kamshi da wanka aka watsa a ruwan, sannan suka shiga cudani. Hawaye na zuba a idanuna. Shi kenan na rasa Mehran. Na rasa Jarumina, me yasa tun tuni ban amsa mishi ba. D'ago kai nayi sannan nace a raina.
_Toh amma ai bai ce yana sona Ba? Toh amma kuma ai duk abinda yake min duk na soyayya ce! Kishi da zafin rai akai na duk abinda masoyi ne kaɗai yake yin shi! Toh Ni me yasa na shiga zab'en? Kenan bawai na shiga dan shi bane sai dan ina son shi?_

Kwalla ne ya zubo min, ban san lokacin da na fashe da kuka ba, haka suka taimaka min nayi wanka na fito bayan sun bani wani yadi na lullube jikina, tare da fitowa daga ban ɗakin, tunda na fito suka shiga shafa min wani abu kamar mai kamar sabulu, ina zaune ina kallon su. Kwallar da nake sharewa a kai  a kai, yasa Bayin suka shiga rarrashina, kamar dama jiran su  nake  na fashe da kuka. Hannun daya daga cikin su ta saka min a bakina.
"Abin kunya ne babba ga Sultanah Balkisu Ikram aji cewa babbar Yar D'anta na farko tana kuka akan SO kinsan yadda muke boye kalmar a ran mu kuwa? Toh koda kuwa zaka rasa ranka akan sone yana da kau kayi hakuri da shi, idan baso kike mulkin kasar nan ta gagari  Amir Rahil ba.

     Don Allah ki hakura da Sultan Aamaan Mehran. Mun san yadda kike son shi, amma duk wanda zaki gani a cikin masarautan nan yana da tab'on soyayya, dan haka karki sake a Fahimci zuciyarki tana ga wani da namijin domin abin kunya ce ga Kakarki."

    Haka suka kashe ni da magana tare da nuna min illar abinda nake aikatawa, nayi kuka da sunan Allah kuma nayi bakin cikin zamowa ta, daya daga cikin ahalin babban gida. Ina ji ina gani ranar aka mai dani kamar wata yar tsana, zunzurutun wanke nan shafe ne.  Ana gyara min jikina. Har kusan tsakiyar dare a sannan nayi wankar karshe tare da sallah na kwanta,. Ranar barci na zance kacokan mafarkin Mehran nayi tayi. Ina kuka ina kome haka zan farka naga bayin nan suna rarrashina.

    ..... Washi gari ina farkawa kafin nayi sallah asuba, suka bani madara dafaffiya,, sai da na wanke baki na shanye tass, sannan na shiga wanka tare da Alola ina idarwa, aka kuma kawo min yankanken y'ay'an itacce, wanda aka zuba madara da zuma na shanye shi, ina ji suna faɗin.
"Kirjinta muke son ya cika kafin zuwa bikin su." Shiru nayi domin bani da bakin magana sai yadda suka yi dani...
[5/22, 7:48 PM] Mehkram1256: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

Littafi na uku
01

Tunda ya bar masaukin su Ikram ya sa aka hada musu nasu kayan suka bar gidan da suke, sai da suka kusan barin cikin garin SAMAIND. Yasa aka kama Nawwas.

     Kallon juna suka yi kafin yacewa.
"Na sami labarin ka gayawa Fudail duk abinda ya faru, sai dai kayi kuskuren domin ba zan barka a raye ba, shi yasa nayi gaggawan barin SAMAIND domin wancan mahaukacin idan ya ritsani sai ta Allah."

         Dariya Nawwas ya saka yana kallon Abrad, tare da nuna shi da yatsa kafin yace mishi.
"Kai tsaye ka mu'amalancin Ikram, Ni kuma a ruwan sanyi Mu'amalanci kanwarka tare da dauke abinda yake jikinta.

     Bamu bar SAMAIND ba sai da na tabbatar da na kuma buɗe tsakanin kafarta na jefa linzamina. Yadda koda na mutu dole na bar baya da kura."

Dariya ya kuma fashewa da shi, yana mai maita abinda ya faru,, yana kuma gaya mishi abinda ya aikata da Kanwar shi. Babu abinda ya kai wannan abin tashin hankali. Idanun shi ne suka cika da kwalla.  Wanda ya kasa jurewa har ya kai da ya zuba masa.
"Meye nayi maka Nawwas? Da kayi min yankan baya haka? Nawwas meye na tsare maka hakan da ka zab'i cilla rayuwar kanwata cikin tashin hankali? Nawwas me yasa baka yi a kaina ba."
"Hahaha... Hmmm, ka zata zan zuba ido ne ka tozarta Ikram? Ko ka zata zan zuba ido ne ka cigaba da abinda ranka yake so? Wannan shi ne kishi a tsakanin zubda jini. Idan kana tunanin ka zubda jinin Nu'man dan jin dadin ka da kuma cusgunawa Mehran dan Ikram ta tsane shi wannan kuskure ne babba karka manta kamar yadda ka mayarda da Ikram a shimfid'ar ka, hakan na mayar da Amirah Azizatul Nissah. Na maida ta kamar matar da na biya sadaki me daraja dan haka karka yi tunanin Mehran zai yarda da wata mace bayan Ikram! Kamar yadda kake da kwarin gwiwar rubutawa yan majalisar Masarautan SAMAIND haka nima na gayawa Mehran alakata da Kanwar ka, dan haka sai ka jira abinda zai biyo baya domin dai SAMAIND ba kanwan lasa bane.

         Kayi kuskuren hadamme kome, Ni kuma nayi ƙoƙarin bayyanawa duniya waye kai, Ikram yanzun tayi maka nisa kanwarka zaka yi kokarin ganin ka fito da ita daga SAMAIND idan ba haka ba". Cikin wani irin fusata Abrad yaja takobi bai yi wata wata ba, ya sokawa Nawwas a kirjin shi sai da ya hudo bayan shi.

     Zuɓewa yayi akan gwiwar shi, ya kuma sake jan takobin  ya soka mishi sai da jini ya fito ta bakin Nawwas. A lokacin ya tuna da Abinda Nu'man ya gaya mishi.
*Ban san meye muka yi ba kuka raba mana rayuwar mu! Sai dai nasan wata rana kai ma haka ce zata mamaye ka! Yadda kayi min haka kai ba za a maka*

Hawaye ne ya zubo mishi tare da kallon Abrad cikin tsannanin azaba.
"Ni nayi haka ne domin al'ummar Daular Umayyad! Nayi wannan aikin ne saboda Banu Umayyad. Sai dai kuma nayi imanin yadda na zubda jinin bawan Allah haka nima rawa jinin ya salwanta. Kai kuma Banu Umayyad za a shafe baki daya.

     Sai kayi gudun da babu macecin ka. Abrad ni abokinka ne tun yaranta ka kashe ni da hannunka. Ba iya ni ne matsalar ba, rayuwar Kanwar ka anan zaka Fahimci muhimmancin rayuwar wanda kake so yaƙe"

       Kasa magana yayi sakamakon jinin da ya cika mishi baki, mika mishi hannu yayi amma fir yaƙi amsar hannun. Juya baya Abrad yayi kwalla na zuba mishi. Bai san ta yadda zai taimakawa Azizah ba, babban tashin hankalin shi Azizatul Nissah. Juyawa yayi cikin tsannanin fushi ya sare kan Nawwas, ya fadi can jini yana zuba kamar da bakin kwarya.

             Zama yayi tare da sake takobin ya fashe da kuka. Domin Nawwas ba kashin yarwa bane, ba kasafai ake samun irin shi ba. Nawwas abokin tarayya ne na kwarai. Mutum ne da ba a cika samun irin shi ba. Shi yasa yake kuka, sai kuma yadda Nawwas yaci Amanar shi yayi ta tarayya da Kanwar shi.

  Sannan ya kwashi sirrin shi ya gayawa Mehran, "Me yasa Nawwas yaci amanata?" Ya tambaya da karfi cikin tsorata da yanayin shi duk suka ja baya, sai daga can asalin amintaccen bawan Nawwas yace mishi.
"Sabida shi ya fara son Ikram! Ya kaunace ta sama da kaunar da yakewa rayuwar shi! Ya bada rayuwar shi ne domin ita? Ya kuma saka duk wani matakin da zai bawa rayuwar ta taimako koda baya raye.

          Sultan kayi hakuri amma kaunar Nawwas ga Ikram gaskiya ce. Soyayyar shi ga Ikram gaskiya ce, tabbas yaso ta tun daga ranar da muka sayo ta, har zuwa yau. Ya gaya maka gaskiya kamar yadda kowa ya kasa fahimtar da kai haka ne. Amma tabbas bayi kuskuren ba, samun masoyi irin shi ma sai an tuna."

Yana fadar  haka ya shiga tattara gangan jikin Nawwas da kanshi yana zubda hawayen bakin ciki, da tausayin abinda ya faru. Ya tuna abinda Nawwas ya gaya mishi jiya.

    "Karka sake ka gaya mishi gaskiya akan alakata da Azizatul Nissah! Zan gaya mishi abinda zai fusata shi. Domin ya bar Ikram ta rayu da Mehran, naso Mehran ya tsaya muyi tsayayya magana dashi amma fir yaki. Dan haka zan gayawa Fudail Insha Allah zai saurare ni. Amma kasan me? Hmm idan Abrad yaga zai rasa Ikram zai sauya tsarin gudanar da abinshi ka saka ido kayi kallo. Don Allah Rab ka kula min da Azizatul Nissah da abinda zata haifa."

    A kidime ya kalle shi sannan yace mishi.
"Shugabana ka manta matsayinta ne a yanzun? Har kake batun abinda zata haifa"

     Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Ba da ita ga Mehran ba shi yake nufin ita din mallakar shi bace, ita da abin cikin ta nawa ne, kuma mallakina ce, don Allah karka sake wani abu ya shiga cikin rayuwar su, fatana idan ka bar Oman kayi ƙoƙarin tsayawa Ikram, ka same ta da batun kome, kuma na roke ka don Allah ka tsaya a bayanta karka bari wani ya tab'ata. Ita kuma zata tsaya a gaban Azizatul Nissah."

       Wani irin kuka ne ya kwace mishi me ƙarfi yana me kuma rungume kan Nawwas, tare da jin tashin hankali sama da farkon faruwan kome, kara rungume kan yayi yana faɗin.
"Me yasa kayi haka? Me yasa ka bada rayuwar ka domin wasu. Baka tuna bayanka ne? Me yasa kika zab'i zubda jini sama da kome ne?"

   Ya faɗa da karfi, yana kuka tare da k'amk'ame kan Nawwas, juyawa Abrad yayi tare da zuba mishi ido, tabbas sun zabi zubda jini sama da kome akan mace! Akan Ikram, koma waye za a kashe! Akan Ikram koda kuwa rayuwar shi ce zai iya badawa, wani irin kwalla yake zubdawa tare da kallon gawan Nawwas, mutum na farko da ya fara ankarar dashi kuskuren abinda yake aikatawa ya kashe mutumin da bai hada shi da kome ba ya kashe mutumin da zunzurutun kaunar shi da shi ko barci yake sai ya tashi idan ya tura a kira shi ya kashe.

    Ya kashe mutumin da yaso shi da gaskiya, ihu ya takarkara a cikin jirgin ruwan, sai da duk suka toshe kunnen su, ya kuma fashe da kuka yana faɗin.

  "Jininki fansa ce ga jinin Aminina" ya faɗa yana kuka da bakin cikin abinda ya aikata , Rab yana jin shi, tabbas ya fara dauko haske akan abin da Nawwas ya gaya mishi.

   Shiru cikin gurin yayi babu wanda ya kuma magana, mik'ewa yayi tare da cewa.
"Ku dauki gawan shi ku wurga a ruwa!"
"Sultan Abrad!"
A fusace ya juya ga Rab, had'iye yawun yayi sannan ya sunkuyar da kanshi,bai kuma cewa kome ba. Amma tabbas wannan shine abinda ba zai iya dauka ba, dan haka yana ganin an dauki gawar Nawwas, aka fito dashi shima yabi bayan su da gudu, kafin yayi wani yunkuri an wurga cikin teku bayan dakaru sun rike shi.

Ihu yake tare da kokarin kwacewa a hannun su, amma suka kara rike shi, yana ji yana gani gawan Nawwas ya nutse cikin ruwan, kuka yake tare da ihun. Buga mishi kasa takobi Abrad yayi. Bai kuma fahimtar inda kan shi yake ba.

           ***
Wurgi yayi da takobin hannun shi, tare da fasa kara yana huci.
"Tabbas Abrad yasan zan dawo na bi takan shi, wato shine ya gudu. Fudail Darda ina Nawwas din?"
"Sultan MEHRAN! Tun jiya muke binka akan Nawwas, amma baka tsaya munyi magana ba, shi yasa da ya gaji yayi tafiyar shi bai..."

Yadda ya kafe Fudail da ido ne, yasa shi sunkuyar da kai kasa, yana had'iye yawu.
"Sultan MEHRAN!"
"Ina jinka, meye yace?"
Ya tambaye shi, tare da kallon gefe. Fita suka yi daga cikin gidan..sai da suka yi tafiya me nisa, sannan yace mishi.
"Sultan MEHRAN! Nawwas bai gaya min kome ba!"
Cakume wuyar shi yayi tare da fidda huci.
"Ni zaka mara da takalmin kafarka? Ko zaka samu damar boye min abinda yake ranka? Gaya min meye laifina da kuke boye min abinda ya dace na sani."

"Kayi hakuri bai gaya min kome ba, amma yace na nime bawan shi Rab." Wani dirkeken naushi ya kasake a jikin bishiyar da Bayan Nawwas yake jingine. Sai da hannun shi ya farfashe. Sannan ya takarkare ya fasa ihu. Sai da dajin ya amsa.

        Zafi biyu yake ciki, babu wanda zai gaya mishi gaskiya kenan? Ya rasa Ikram ya rasa wanda zai gaya mishi abinda ya faru kenan, dan haka ya tashi cikin tashin hankali ya juya zai tafi. Ya kuma juyawa ya kalli Fudail, sannan ya saka kai zai bar gurin. Ajiyar zuciya Fudail yayi sannan a ranshi ya ayyana cewa.
*_Ba zan tab'a yarda na gaya maka gaskiya ba! Sai har na gama gabatar da abinda yake gaba na, ba zan tab'a yarda na kyale wanda ya cutar da ikram koda da bakar magana ce balle da farar magana! Kayi hakuri Sultan Mehran_*

Ya faɗa a sanyayye, yana me jin tausayin Sultan Mehran. Domin a yanzun gaskiya yake nima idanu a rufe, kuma baya jin zai gaya mishi koda kuwa zai rasa rayuwar shi, Dole kuwa Azizatul Nissah taji a jikinta itama. Abin kunyar da suke amfani dashi ga rayuwar Ikram itama taji yadda tozarci yake. Amma kuma idan ya tuna rokon da Nawwas yayi mishi sai yaji tsoron kar haka kuma ya tab'a kimarta.

    Dafe goshin da yayi tare da bin bayan Mehran, yana tafiya yana zancen Zuci. Har ya isa inda dokin shi yake, dan yanzun kan yasan Mehran yayi mishi nisa, koda ya cilla dokin shi ya hango su, dab da Masarautan.  Amma kuma koda ya isa Fir dakarun suka hana shi  shiga.  Wannan shine karon farko da Mehran ya mishi hukunci me tsauri ta hanyar amfani da hana shi, shiga SAMAIND! Dan haka bai yi fushi ba, ya zauna a gurin gashi garin da alamun shigowar damina.

     Duk sai yaji babu dad'i a ranshi, yau shine Mehran yayiwa wannan hukuncin, dan haka duk dai yake gani kamar tozartawa ne, ga wani muzancin da yake ji a ranshi. Kanshi a sunkuye har aka fara yayyafi. Bayan wani lokaci ruwa ya fara me mugun karfi da yawa. Yana tsaye a bakin kofar shiga masarautan..

   ----
Tunda ya shiga cikin gidan, ake mishi magana kome ya gani fatali yake dashi, har ya shiga cikin dakin shi. Huci yake ya rasa yadda zai yi da Fudail idan kowa zai ci amanar shi yana tunanin ai Fudail ba zai tab'a yarda a cutar dashi ba.

Kuma yayi imani da Allah akwai da yake boye shi, kuma ba zai tab'a yarda da munafunci ba, domin idan ba munafunci ba akan me zai boye mishi maganar da yake bukatar yaji, dan haka babu abinda zai hana shi bai hukunta shi ba, sai ya hukunshi sosai domin kuwa ba zai yarda da wannan wulakancin ba, tsaki yayi tare da kutufal da kayan shayin gaban shi, yana jin ana buga kofar shi amma fir yaki buɗe sabida yayi fushi anci amanar shi...
(See me see trouble😹😂😹🤣 ta ina aka ci amanar ka Yau ga D'an Uwan Jamal🤔)
+2347035133148 Zahrah Adda Ramlat
[5/22, 7:48 PM] Mehkram1256: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

03
Wato ma'ana bani magani suke tare da abinci me gina jiki, duk abinda suke idanuna a rufe suke, bana budewa wani lokaci haka zasu yi ta magana ina jin su, bana tanka musu, idan suka gama min kuwa a gurin nake kwanciya. Ina kuka duk taurin zuciya ta da taurin kai na, sai da ya kai komi kashin b'acin rai kuka yake sani.

         Rabona da Izmah kuwa sai dai na shafe kwanaki goma kafin aka barta ta shigo min dakina, lokacin da ta ganin sai da ta firgita, tana mamaki.
"Ikram! Baki da lafiya ne? Kinyi kyau amma kuma kinyi mugun rama, meye yake damunki? Me aka miki? Don Allah gaya min"

    Zama tayi a jiki na, ban san lokacin da na fashe da kuka ba, nace mata. "Izmah Mehran nake son gani" kamar wacce aka dasata, haka take kallona. Bakinta yana rawa tace min.
"Sultan MEHRAN?" Ta kuma tambayana, gyada mata kai nayi tare da rushewa da kuka, rike hannuna tayi tare da kwantar da kaina a kirjinta.

"Ikram!" "Don Allah Mehran;" na katse mata abinda zata fada,  duk sai ta rasa abinda zata ce min, ta kuma bude baki zata yi magana, Amir Rahil ya shigo cikin ɗakin, yan mata na biye dashi. Mikewa tayi zata fita na rike hannun ta.
"Kiyi hakuri zan jira idan ya fita zan shigo muyi Magana."

"Wacce magana zaku yi? Ai akan wancan Jahilin da ya kasa miki uzuri ko? Ko akan Abrad da ya gama da budurcin ki? Kinga Ikram. Ina Sonki shi yasa zan dauki duk abinda ya same ki, amma kika Kuskura kika shigo da Mehran yake ko Aman yake? Wallahi Billahi azim, zan kashe wannan abin" ya nuna min Izmah, sauka nayi daga gadon na zube gwiwata a kasa, tare da rungumo Izmah, ina kuka nace mishi.
"Kayi hakuri! Ba zan kuma maganar shi ba, amma karka tab'a lafiyarta. Idan nice na amince." Na fada cikin kuka, murmushi yayi tare da nunawa Izmah kofa ta fita, tunda ya shigo inda nake ya d'ago ni. Kallon kayan jikina yayi yadda ya fitar da surar jiki na. Nayi kyau na fitar hankali.

Please Login or Register in order to submit comment