Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dashe a cikin tawa, bana jin har abada zan iya samun sama dashi don Allah ka rabu dani."

Na kwace hannuna tare da juyawa na fita daga d'akin, wani lungu na shiga tare da tsugunawa na fashe da kuka, sama da yadda nake jin zuciyata take min, me yasa nake fuskarta wannan matsalar?,shi me yasa maza suke kowa min farmaki da tallar kaunar su? Shin Ni daya ce mace ko kuma akwai wasu matan da su ba zasu je gare su ba?

Sai da nayi kuka na koshi sannan na fito, zuwa dakin. Na shiga hada ruwan zafi ina goge mishi jiki tare da shafa mishi mai, da turaren bakhoor, sannan na samu na tura shi gefe tare da gyara inda yake kwance, na shiga gyara d'akin. Ina gamawa matar nan tana sammakon shigowa.

Wani irin kallon kallo muk'ewa juna, ido cikin ido. Zata wuce na tsare hanyar ta.
"Ina da abinyi baiwa!"
Takowa nayi gabanta tare da kallon cikin idanun ta, sannan nace mata.
"Ki kirani koma meye! Ban damu ba, sabida bani da ciwo a raina da rayuwata sai d'an kalilin, kawai ba zan iya baki damar ki cigaba da illata lafiyar shi bane, Ni mace ce haka bazan tab'a son ganin an wulakanta ki ba, amma kika sake dakarun Samaind suka san kina zuba mishi guda da matsatsaku a jikin shi domin ya mutu."

Wani irin murmushi nayi mata irin na gefen bakin nan, sanan na nuna mata hanya,alamar ta fita tun muna sheda junan mu. Zare takobin ta tayi, nayi maza na kai karamin wukar da yake kwaibinta da na zare wuyarta.

"Wani irin halacci yayi miki da kike kaunar kare lafiyar shi?" Ta tambaye ni tana kallon idanuna. Murmushi nayi mata sannan nace.
"Iya tsare kimata ya ishe ni na tsare lafiyar shi!"

Murmushi tayi sannan tace min.
"Ina jiye miki tausayin rayuwar da zaki fuskanta, ba zan kyale shi ba. Amma hango halaccin dake kwayar idanun ki yasa ni zan d'aga mishi kafa, sai na kuma dawowa."

Ta juya bata kuma cewa kome ba, tun daga ranar na cigaba da kula da lafiyar shi. Ina kuma bashi maganin da nake hada mishi. A hankali jikin shi ya fara washewa.

Sai da muka shafe kwanaki goma sha biyar, yana kwace amma kuma ana ganin canji, mahaifiyar shi ma ba laifi, jikin shi yana motsawa. Sai dai rashin mutunci yana nan babu abinda ya sauya. Sai dai wani Iskancin da yake min. Idan ina goge jikin shi.

Wato alkalamin shi mik'ewa take tsaye, ban tab'a lura da haka ba, sai wani rana da nazo goge mishi maran shi, dake da ruwan zafi nake goge mishi jikin, ina matse farin tsumar a saman ruwan na saka a kan cikin shi tare da gogawa tare da kaiwa saman maran shi, cin karo nayi da abu a tsaye ta rigar shi. Da sauri na kalle shi. Idanun shi lumshe, yana sauke wata boyayyen ajiyar zuciya. Ina ganin yadda jikin shi yake d'an daukar rawa. Da sauri na cire hannun daga gurin, harbib iska kawai abin yake.
Tsalle nayi na koma gefe, ina kallon shi tare da sunkuyar da kaina kasa, na rasa abinda zan mishi. Kamar yadda nake mishi. A hankali abin ya koma ya kwanta, na cigaba da goge mishi jikin shi.

Haka na cigaba da kula dashi har ya fara tashi zaune lokacin ciwon ya warke, idan na kawo mishi abinci yana ci, kallona yake idan yaji ina motsa baki na,ina karatu. Idan nayi shiru kuma sai yayi kwarewar karya. Haka zan taso na kawo mishi ruwa, idan zai karb'a zai hada da hannuna, da sauri nake sake mishi kofin, tare da kallon shi.
Mara kirki sai ya wani b'ata rai, kamar ba shi ba, haka zan zare hannuna kai na a sunkuye, baya kaunar yaga bana kusa dashi yanzun zai fara gyaran murya. Har sai na leka d'akin.

~~
Oman

Kallon shi take daga nesa, gyara tsayuwa tayi tana kallon shi, gyara gashinta da yake gaban goshinta.
"Unaiza wancan waye ne? Yau kwana uku ina kallon shi!"

"Almirah Azizatul Nissah, ai yazo niman Baiwa Ikram ce, har sun hadu da Sultan Abrad. Yanzun ya fara aiki a masarautan nan ne domin ya cika wa'adin da zata cika shekara daya."

Fuskarta ne ya nuna rashin jin dadi akan labarin da Unaiza ta bata, ta juya a hankali sannan ta kuma kallon shi tace.
"Ki shirya mana zama dashi."


---- Waiwaye...
Kwanan su Noman tara suka iso Oman, Dakyar suka sami ganin Nawwas, sannan Ya Ra'ess ya gabatar da Noman ga Nawwas da kuma abinda ya kawo shi, kallon shi Noman yayi sannan ya dauke kan shi.
"Kace kazo anan niman Ikram? Meye alakarka da ita?""

"Kanwata ce" ya bashi amsa a takaice fuskar shi babu walwala ko alamar wasa.
Gyada kai yayi sannan ya dauke kanshi daga Noman yace.
"Toh zan kai ka ga Abrad, idan ya amince sai ku tattauna."

Daga haka suka juya suka fita tare, har fadar Sultan Abrad, nan suka tattauna har da dalilin da yasa aka fito da ita, da kuma Mutuwar Airan. Jikin su yayi masifar sanyi, asalima dukkan su uku sun ji tausayin ta da kumar kaunarta a ransu, gefe guda Nawwas har da kishin Abrad, sabida yana da yakinin yana kaunarta har yau.

Sun tattauna tare da bawa Noman daman ya zauna nan da wata hudu masu zuwa Insha Allah zasu dawo da ita.

Ga kuma Almirah Azizatul Nissah tana kokarin sako kai cikin rayuwa shi.
~~
SAMAIND


Masu iya magana suka ce lafiya uwar jiki babu me fushi dake, haka ta kasance akan Sultan Mehran, yau dai da wani irin yanayi ya tashi, dake ana mishi wanka Fudail, tsakanin shi da Allah ya b'ata rai baya son wankar su, sai dai nice zan tashi na shiga na mishi.
"Idan nice zan maka wanka kana balagagge kace na maka wanka toh karka yi ka zauna da dattin ka waye zai damu kai ne zaka damu."

Idanun shi lumshe kamar baya d'akin asalima gyara kwanciyar shi nayi, ina kallon shi abinshi tana ta Iskanci, a raina nace.
*_Wannan mutumin bai da kunya! Sam tirr_*

"Idan kin gama zagina sai mu shiga ki min" kallon shi nayi bakina a sake, cike da al'ajabi.

Shiga ban dakin nayi tare da hada wani ruwan, juyawa da zan yi na same shi a tsaye da wani asuwaki yana goge bakin shi, a hankali nayi kasa da kai na, ina kallon kasa.

Takowa yayi gaba na, tare da d'aga min hannun shi, wayyo Allah na. Shi wannan bai da kunya sam, kauda kai nayi na fara kokarin cire mishi, amma na kasa sabida ya fini tsayi, kallon shi, ina haki. Duk da yau na tashi bana azumi amma kuma bana jin dadin jikina sabida ciwon maran da nake fama dashi.

Tawowa yayi gabana kafar zai fada kai na, na tare shi muka jingina da bango.
"Me...h...ran. ka cire ka..ya.n ma..na!" Nayi maganar ararrabe muryana yana rawa, a hankali ya zare rigar, fuskar shi a murtuke.

Kallon kirjin shi nayi wanda yake cike da gargasa, wani irin kyamar shi naji kamar zan yi amai, sororo yayi yana kallona tare da dauke idanun shi a kaina, gashi dai alamar karfafan namiji ne dan yafi Abrad da Noman cikar halitta, hannun shi yakai keyar shi bayan ya haɗa su ya miko min kwarjallen shi na warware mishi. Kamar wacce aka watsawa ruwan sanyi kalau, jikina ya fara karkarwa.

Komawa yayi ya jingina da Kofar.
"Yanzun don Allah ba zaka iya taimakawa kanka ba sai na tab'a ka, bayan haramun ne tunda ki ba muharamman ka bace"

Na fada mishi haka ina kuka kamar wacce yace min zai min wani abu, jikin shine yayi sanyi musamman yadda ya ga jikina yana rawa, alamar dai na gama firgita da shi.

A hankali ya juya min baya tare da cire kwarjallen shi, nima juya mishi baya nayi, gashi na tsare mishi inda zai wuce dan haka ya tsaya a bayana, shi dayan shi yana jiran na matsa mishi. Jin haka jin motsin shi, ashe zanyi mugun gani ne na juya, kawai sai ganin abu nayi.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun!" Na fada da karfi tare da juyawa da baya zan fada cikin ruwan wankan yayi maza ya riko wuyar rigana.

Take ya haɗa da tausassan mangwaron kirjina, da sauri muka kalli......
🤔😏Irin naka salon kenan....
Allah kajikan iyayena
Littafin nan na kuɗi ne
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
Page 28

A hankali na sauke idanuna daga cikin nashi cikin matsanancin kunya, jikina yana kuma rawa. Dake Allah ya taimake ni muna daura wani fallen yadi a kirjin mu, yadda babu abinda zai sami nonuwar,  a Sannun yake saussauta rikon har Allah ya taimaka ya sake ni, kawai na kuma tafiya zan fadi Yasaka hannun shi ta k'uguna.

      Hannu na duk biyu suna kirjin shi a dunkule na rufe idanuna, ina sauke ajiyar zuciya. Cikin mutuwar jiki ya janye Ni daga jikin shi ya shiga wankar shi.  Kin yin kome yayi ya tsaya yana jirana na mishi.

    A Sannun na ja kafana zuwa gare shi ina me shafa wata ruwan sabulun wanka na, na fara goga mishi da wata soso irin auduga nan, ina mishi ina me dauke kai na, har na kammala mishi tare da ajiye sosan na shigo dakin na dauki Mayafi sabuwa kal na koma na kai mishi, sai da ya gama b'ata min rai da lokaci sannan ya amsa daga hannuna.

    Wato ina ga Mehran so yake na dauke shi ko ya koma jinjiri ina ina ina dashi, haka Ni daya nayi ta masifa a rai na, kamar zan dake shi. Yana gama mulkin shi ya fito, dan har na riga shi fitowa, ina zan iya rayuwa da mutumin da yake abu kamar kwai ya fashe mishi a cikin shi.

      Bayan na gama na fita sami baki suna jiran shi, dawowa nayi ba gaya mishi. Takowa yayi gaba na, yana zuwa ina matsawa har muka kure bangon d'akin.

              Hannun shi naji a kwaib'ina, da sauri na kai mishi bugu yayi maza ya tare, na kuma buge hannun ya tare, kallon kwayar idanuna yayi, wani irin budewa kwayar idanun shi yake, ban tab'a sanin cewa akwai abinda zai haifar min da nutsuwa ba sai da na kalli cikin idanun shi, har wani irin budewa dan bakin tsakiyar idanun shi yake tare da fitar da wani shegen maiko, ji nayi kafaffuna basu iya daukata, kirjina kuwa kamar ana buga min wani abu, ji nayi numfashina ina kokawa dashi, dan haka ban san lokacin da na zube a kirjin shi ba, mayafin da yake daure ne a k'ugun shi suka nemi zuɓewa kasa, cizon lebbena shi yayi cikin wani irin yanayi da bai san yana tare da shi ba, sai da na fada jikin shi, dan tsabar mugunta, janye jikin shi yayi na zube a gurin, sannan ya duba dakin babu wani abu sai alkyabar shi da Fudail ya dauko mishi, yafawa yayi sannan ya fito.

    Mik'ewa suka yi tare da kallon shi.
"Sultan Mehran ya jikinka?"
Niman guri yayi tare da zama yana kallon gefen shi wanda yake dauke da kayan ciye ciye, a hankali ya motsa bakin shi kamar me fama da ciwon baki yace.
"Da sauki!"
Kallon shi suka yi, sannan suka sunkuyar da kansu. Gyaran murya Amir Hood da Mir Umdatuddawla yace.
"Sultan Aamaan Abdus Samad, mun tawo baki daya ne mu baka hakuri da!"

   D'aga musu hannu yayi sannan ya kalle su daya bayan daya sannan  nuna musu kofar fita, kan shi kwance saman matashin kujeran.

              A hankali suka yi ta mik'ewa daya bayan daya, suna fita, karshe dai ya rage shi daya a falon, fitowa nayi ina ƙoƙarin shiga kitchen, bin bayana yayi da ido, ganin yadda na b'ata kayana da jini ya sashi dauke kai, bai ce min kome ba, har na gama abinda zan yi na fito na koma dakin, tasowa yayi tare da shigowa, wai zai gaya min abinda ya faru da jikina shine ya tako har inda nake tsaye, sai ji nayi an wurgani gado, na tashi da sauri. Ya kuma mai dani tare da zama a bakin gadon ya janyo kafana,  a hankali ya ture ni ta daya gefen kyakyawan zanin gadon ne ya b'aci da jini, yana ganin na Fahimci haka ya mike tare da barin d'akin.

Saka kai na nayi a tsakanin cinyoyina, na rufe idanuna sa karfin tsiya. Ina sauke ajiyar zuciya. Tashi nayi na shiga wanka nayi sosai sannan na gyara jikina, ina gamawa na taso tare da nufar kitchen na daura mishi gasheshen nama sai madara da nayi gyaran shi. Na kawo mishi.

  Tunda na kai dakin yana zaune tare da kallon yadda na gyara gadon tsaf, zama yayi  ya fara cin abincin a hankali. Tunda na gama ya nutsu na fita daga dakin.
  ~~
Tunda Sultanah Hoyam taga ya sami sauki, ta shiga aiko mishi yan mata tsalla-tsalla. Wai suzo su dauke mishi kewa, sai dai abinda ka kasa Fahimta akan shi yan matan baya barin su, su shiga min dakin, sai dai kuma zai fito falo dasu ya zare  kayan shi ya kwanta suna mishi tausa, dake Allah ya taimaka bana jimawa a cikin hailata, kwana hudu ne, lokacin ana sallah saura kwanaki ƙalilan za ayi.

Bana son kwanakin tahajjun ya wuce ni ne, ranar da nayi tsarki ranar na fara sallah tahajju, idan ina karatu bawan Allah nan dawowa yake falon ya zauna har sai na idar sannan yake komawa dakin shi, sake kwanakin azumi zanyi dan haka yana ganin ina sahoor, bai ce min kome ba, sai gyara kwanciyar shi da yayi tare da lumshe idanun shi, yana son kyawawan dabi'unta.

Ibadarta ya zarta tunanin shi, tana da kokari akan kome, sai dai matsoraciya ce na kin karawa, yana son mace me kokarin irin na Ikram.

   Kaf kwanakin da nayi ina ibadana, tare dashi muka yi domin tsakkanin shi da Allah ya saka idanun shi akan ibada na, kasa hakuri yayi tare da kiran Fudail.

     Shiru yayi tare da kasa cewa kome, sannan.yace mishi.
"Kasan wani irin abu yarinyar nan take yi? Shi ba waka ba shi ba hira  ba, meye shi? Sannan idan karfe sha biyu da rabi yayi tana wani abu, da d'aga bayanta dama.

    Haka idan karfe uku da rabi yayi toh ba zata kuma kula Ni ba sai tayi abin, Fudail ina cikin damuwa?"

Kasa yayi da kan shi tare da cewa.
"Mehran ba kome take ba sai ibada."

      "IBADA?" Ya tambaye shi tare da kura mishi ido, sannan yace mishi.
"Kai kana yi ne?" Gyada mishi kai yayi alamar eh,
"Me yasa Ni bana yi?" A dimauce Fudail ya zuba mishi ido, shi kanshi ya hangi firgici da tambayar da yayiwa Fudail din.

    Shiru yayi a gajiye sannan ya juyawa Fudail baya, yana sauke ajiyar zuciya.
"Mehran!" Dakatar dashi yayi, bai kuma magana ba,  haka Fudail ya fita,

          ---- Ina gyaran kifin da Darakshan ya shigo min dashi, akan zan dafawa Mehran, na nutsu bakina yana ambaton sunan Allah,  shigowa yayi cikin madafin ya tsaya a kaina, ban d'ago ba amma kuma hakan bai min dadi ba, kasa jurewa nayi ina kallon shi. Kafin nace mishi.
"Ko wadanda ba musulmai ba, idan zasu shiga gurin musulmai suna faɗin, Amincin Allah ya tabbata a gare ku. Wai me yasa kake haka ne?"

            Haka kura min ido yayi, sannan yayi kasa da kanshi, jikin shi a sanyayye ya fita daga cikin madafin, bai zame ko ina ba, sai shsshin Mahaifiyar shi. Kura mata ido yayi cikin wani irin rauni yace mata.
"Waye Ni?"

"Mehran ban gane ba?" Ta tambaye shi akan tambayar da yayi mata.
"Waye Ni?"  Ya kuma tambayar ta,
"Ka nutsu ka min bayani me kake nufi da haka?"

   Hawaye ne ya shiga sauka daga cikin idanun shi yana kallonta, bakin shi na rawa, yace mata.
"Me yasa bana sallah?"

Wani irin bugu zuciyarta yayi cikin tashin hankali a zuciyarta tace.
*Kai Na shiga Uku na lalace! Wannan shaidaniyar Yarinyar sai ta t lalata min rayuwa Ya zanyi?*
"Yanzun Mehran akan sallah ne kazo ka tsitsiye Ni?"

    Ta faɗa fuskarta a daure, tare da niman guri ta zauna, sannan tace mishi.
"Zauna muyi tsayayyen magana."
Ba musu ya zauna, cikin hikima da dabara ta shiga kawo mishi abinda ba shi bane, tare da gaya mishi, wacece Ikram sannan ta gaya mishi ai surkulle take. Dake Uwa ce, kuma tana da hangen nesa dan haka tayi ta b'ata Ikram a hankali cikin dabara sai da ta cusa mishi rashin yarda akan Ikram kuma ta zauna ta gaya mishi abinda yasa take jin ba dad'i akan zamanta a shashin sa, dan haka ya kore ta, idan ba haka ba zata kawo mishi rudani.

  Sai dai kuma kasa yarda yayi daga abinda ya faɗa yana kallonta cikin nauyin harshe yace mata.
"Fudail yana yi"
  
               "Toh munafukai ne, kuma suna son ganin bayan ka ne, idan baka manta ba, lokacin da baka da lafiya haka suka yi ta cin Amanar ka, idan kuma karya ne ka tambayi Darakshan Fudail da Ikram suna mummunar alaƙa. Yanzun ma idan da zaka shiga gidan a bazata zaka same su."

   Ita lallai dole so take ta raba shi da Ikram, musamman da Darakshan ya kawo mata tsegumin Fudail yana son Ikram kuma yayi alwashin ko za a kashe shi ba zai tab'a barinta ba. Kurawa Mahaifiyar shi ido yayi wanda ya zaro su kamar zasu diro kasa,ji yaƙe kan shi yana wani irin yatsuna kamar an zuba mishi tsutsa akan shi. Sunkuyar da kai yayi bai ce kome ba. Amma hatta gashin jikin shi a mike suke.

        Dan haka ya tashi daga inda yake zaune ya saka kai zai fita, tace mishi.
"Mehran kayi ƙoƙarin karkade munafukan da suke jikin ka, idan har Fudail yanayin sallah tabbas shi da Ikram bayan ka suke son gani, idan kuma kaki toh ba makawa."
"Ina ruwa na?" Ya tambaye ta, cike da mamaki take kallon shi, yadda lokaci guda ya gwaleta, ya sa kai ya fice, idan ka kalle shi sai ya baka mugun tausayi, domin yayi laushi sosai, kuma a iya kan fuskar shi zaka karanci yana cikin tashin hankali da damuwa, duk inda ya gifta gaishe shi ake dakaru na bin bayan shi, cikin nutsuwa.

Fuskar shi ma'abociyar kwarjini da haiba ta fito fess, kana ganin shi kaga wanda yake ji da mulki da izza, amma yau jin amintattun shi. Suna ha'intar shi yasa shi jin babu dad'i, ba zai iya kashe Fudail ba haka ba zai iya kashe yarinyar da yake jin dadin sauraron muryan ta ba. Amma tabbas zai iya raba su, cikin sauki zai haramtawa Fudail shiga shashin sa har abada, har ya iso kofar da zata sada shi da falon sama yaji Muryan Ikram.

"Kai jinka ina zaune ne anan abisa jin dadin rayuwa ta? Toh ina nan ne dan babu yadda na iya, ina nan ne sabida fansar rayuwar kanwata, ina nan ne domin kanwata. Iya adadin lokacin da na diba ya cika tabbas ko bai zo min ba zan koma mahaifata, Idan masoyina yazo Tabbas ba zaka kuma gani na nan ba."

"Amma kuwa wannan masoyin naki sunan shi gawa! Domin wallahi na rantse miki da wanda rayuwata da mutuwata take hanun shi sai na kashe duk wanda ya kuskura ya keta Alfarmar Mehran! Duk wanda ya kuskura yazo nan da sunan yazo daukar ki, bayan kina kasar mulkin Mehran sai na raba kan shi da gangan jikin shi.

Dan haka ke mallakin Sultan Aamaan Mehran ce, babu wanda ya isa ya kusanci inda kike balle ya tafi dake k..."

Gyaran murya yayi bayan ya shigo falon yana kallon mu, munyi cirko cirko,. Dauke kan shi yayi tare da wuccewa abin shi. Murmushi Fudail yayi tare da sauke wata Boyayyen ajiyar zuciya, tabbas yasan nadan Allah ya mishi baiwar iya fahimtar ana kusa dashi ba da ya tafka kuskuren da ba zai tab'a barin shi ba.

Lokacin da Mehran ya iso bakin kofar, yaga alamar wani yana bakin kofar, dan haka bai dakatar da Ikram ba, sai dai shi ya sauya kalaman shi. Fita yayi daga gidan. Burin shi ya cika dama abinda yake son gani kenan Mehran yaji Ikram tana da wanda take so.

Tunda ya shiga dakin shi ya kwanta, tashi yayi zubur. Tare da kaiwa da komowa, wato tana da yakinin akwai wanda ya isa ya keta Alfarmar shi yazo ya dauke, ya ga shegen da ya isa ya shigo har sansanin shi ya dauke ta....
Littafin nan na kuɗi ne.
Allah ya jikan Iyayena
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
     Yadda yake huci sai ka rantse da Allah, an zo daukarta ne nan kuwa zunzurutun rigima ce kawai yake damun shi. Kamar wanda aka mintsine shi ya fito daga dakin, kitchen ɗin ya nufa tare da kallon bayan ta, yadda yan k'ugun ta da mazaunanta suke juyawa a hankali. Ikram ba ta bata da cikakken halittar jiki, bata cikin jinsin sirarra ko irin lutayen nan.

   Sannan ba za a kirata ramammiya ba, daidaigwargwado tana da jiki me kyau, musamman k'ugun ta, kirjin ne dai sai a hankali, domin a shafe yake, yan nonuwan kamar na me kirgan dangi. Amma kuma kamar wanda aka dasa su daga kasa, a cike suke tam daga sama ne zaka dauka babu su. Sannan rashin kulawa da abinci me gina jiki ya taimaka matuka gurin boye cikar halittar jikinta, k'ugunta ne zuwa mazaunin ta, kamar wacce aka hura abu ko aka mata dashen shi.

    Domin idan ka nutsu zaka ga har wani motsawa suke, tunda yake bai tab'a kare mata kallo ba sai yau, bai tab'a ganin mace me diri irin ta ba, wannan halittar  shi ya kad'a mishi hankali lokaci guda, had'iye yawu yayi cikin b'acin rai, ya juya tare da barin gurin.
    Ya ga shegen da ya isa ya shiga mishi iyakar kasar shi domin daukarta. Haka yayi ta aiyanawa a ranshi, dan haka a washi gari ya maida Fudail fada, sannan ita kuma ya zuba ido akanta, yana kallon iya gudun ruwanta.

          Gefe guda ya dawo da mugun halin shi, idan tayi mishi abu zai kai mata mangari ko ya tad'e ta, ta fadi, wani irin zazzafar k'iyayya ce ta Kuma haihuwar kanta a tsakanin su, wanda ta kai Itama Ikram din ta fara rama abinda yake mata, ai kuwa yace bai iya ji ba, azaba kuwa babu iya ka. Kuma babu halin ta fita ko ina, tana cikin gidan.

       ---- watan shi takwas da bashi mulki aka fara turo y'ay'an gwamnonin yankunan hudu nan, akan zasu yi zama dashi na tsawon wata hudu idan suka fahimci juna,  sannan za ayi bikin su bayan wasu wata hudu masu zuwa, wato

Please Login or Register in order to submit comment