Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sukan saka shi can gefen kansu ne sai su dauki furen gulsana, su makala a jikin shi. Shigar su d'an kamfe ne da wani yadi da suke tare manyan nonuwar su, idan ka gansu suna tafiya har wani daukar hankali suke.

        Gasu mazan su jarababbun mutane ne, idan suka ga mace danne ta kawai ake a hake mata, amma kuma suna da dadin zama, da mu'amalar juna, sannan ana yawan kawo musu hari,  har a kame wasun su. Duk bayan shekara biyu. Suna zaune ne a bakin teku, sabida basu da sana'ar da tafi su. Da shi suke shiga cikin gari su sayi kayan masarufi.
       Akwai wani matashi me suna firoz, yaron shi yafi kowa tsayi.  A cikin kauyen baki daya. Baya magana da kowa sai yar me gari me suna.
  Izmah yau ma a tare suke, d'ago kai tayi tare da kallon shi zai watsa kimar kama kifin shi tace mishi.
"Firoz! Wai baka da sha'awar mace ne? Ko baka da lafiya ne irin na sauran mutane?"

     "Lafiyata lau, kawai ba zan iya hakewa macen da nake so bane? Shi yasa kika ga na kyale ki d idan na miki damka daya zaki kwashi labari a gaba!"

   Tabe baki tayi daidai ya watsa komar, jin ya rike abu ya saka shi cewa.
"Yau dai da Sa'a na watsa komata domin naji na kamo hanyar Arziki" dariya tayi mishi sannan tace mishi.
"Ka manta daren jiya anyi ruwa dama, tayu Giwa ce ta faɗa ruwa, shine igiyar ruwa ya tawo dashi."
Dangware goshinta yayi sannan ya  cigaba da jan kimar shi, har Allah ya nufa suka janyo komar baki daya.
A tsora ce suka dube cikin komar, mace ce cikin komar tana mace.
  Ihun da Izmah tayi shi ya farga da sauran mutanen kauyen, da gudu mutanen kauyen suka taso, aka janyo komar sannan aka shiga taimaka mata na gaggawan, tab'a wuyarta aka yi suka gyada kai. A lokaci guda suka sauke ajiyar zuciya, sannan aka dauke ta zuwa cikin kauyen. Cikin sauri aka nufi gidan Mawla da ita shine me maganin garin baki daya, dan haka ya shiga taimaka mata cikin sauri yana sakawa na cire mata kayan jikinta, dai dai shigowar, keyaan.

   Kurawa halittar jikin Ikram idanu yayi tare da had'iye yawu, cikin zunzurutun kwadayin shi. Yana kallon yadda take kwance babu numfashi.
"Toh Mawla idan an gama kula da  ita, a kawo min ita gidana domin nan yafi dacewa da ita ba gurin ka ba, bana son ana ganin ta kamar wata ganimar da aka tsinta." Ya wani bone fuska zaka zata da gaske shi ya cirota cikin ruwan da aka tsamo ta,
" Abba yanxun Abinda kake yi dace? Duba halin da matar nan take ciki sannan kana cewa a gama a baka ita, Toh naga dan farka da zai baka ita idan ban kashe shi har Buzun sa ba,"

         Yasan halin Izmah zata aikata dan bata da tsoro ko kad'an, dan haka ya koma gefe yana shafa kirjina shi zuwa wuyan shi, musamman ganin cinyoyin Ikram, wanda suka yi wani irin haske. Sambala sambala, had'iye yawu yayi cikin wani irin yanayi. Matse cikin Ikram mutumin yayi tare tare da marin wuyar da fuskarta, ruwa yake fita ta hanci da baki. Sai ta bayanta, ta xubda ruwa me yawa, sannan ta fara numfashi kunnen ta kuwa dama ruwa ne ya toshe shi.

       Muryan take ji kamar daga can can, ana kiran sunan ta bude idanu nayi naga Noman da Ummina sai Airan da Abba na. Murmushi suke min suna kallon yadda nake kwance.
"Ku tafi dani!" Na fada cikin kasa da murya.
Dafa goshina Ummina tayi sannan tace min.
"Rayuwarku tana amfani a duniya! Idan muka tafi meye amfanin haka? Ki zauna domin karasa sauran aikin da kika fara."
"Noman!"
"Karki damu! Ki karasa aikin da kika fara."

    .mika musu hannu nayi sai gani nayi sun bi iska kamar yadda ake watsa gari a iska,  haka suka Baje, a iska zabura nayi tare da tari me ƙarfi ina aman ruwa, rirrike Ni suka yi, na fara ihu ina kiran sunan Noman.

    Ban san me suka saka min ba daga nan barci yayi gaba dani.
"Da alamu akwai abinda ya faru da ita,. Kuma idan ta farka da abun toh ba ta manta kome ba, idan kuma ta farka bata kuma tuna kome ba, tabbas wannan shine abinda ake kira kaddara."

  Inji Mawla, yana shafa kan Ikram da wani farin magani.
"Toh Mawla meye Illar haka?"
"Illar shi kuke son sani? Dubi tafin hannun ta, Kinga alamun zaman takobi, idan har ta farka da shi zamu iya sanin wacece ita, duk da saura kwanaki ƙalilan yan sumamme su kawo mana hari.

        Ku duba sararin samaniya, kunga taurarin zubda jini bai fito ba, amma kunga can tauraron taimako ne yake washewa, idan na Fahimta, abin bauta.  Kunzu ne ya turo mana ita domin ceton rayuwar al'umma."

             Da wannan zancen kowa ya koma gidan shi, ban da Sarkin garin ya share guri ya zauna, shi yaga mace. Karku ganshi kamar an kira kwarya, amma dan bakar jaraba yana fadar cewa shi Ikram yake dakon yayi tarayya da ita,  ai ance dogayen mata suna da dadin dandano.(🤔🤣D'an hegiya wannan bom ce ta kwashe maka kayan wasan yaranka anan)

      ~~~
Bayan awa goma sha biyu, a hankali na bude idanuna tare da kallon d'an bukkar da nake, mik'ewa nayi sakamakon jin kamar wani yaro ya tukwaikuye ki, dubawa nayi naga dan abu kamar d'an shekara bakwai, babu kome a jikin shi.

"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, wata duniya na fado kuma wannan yaron karami dashi."

    Gwartin da naji yana yi irin ta tsofin mutane, ya sani kallon shi da kyau. Ture shi nayi naga ya farka tare  sake min murmushi, fuskar shi kamar kashin saniya, dan haka na dauke kai na, tunkaro ni yayi babu kaya a jikin shi, wani shegen  duka na kai mishi tare da kwashe kafarshi na rike a hannuna, ina kallon shi gaba daya kayan aikin shi wato alkalamin shi basu fi ta yara yan shekara tara ba.

    Amma ya tsaya min zai min feleke, daukar wani igiyar nayi a dakin na kama shi tare da daure shi tam, sannan na zabga mishi naushi na fito dashi waje na rataye shi. Sannan na koma dakin na shiga niman kayan da zan saka, dakyar na sami wata irin riga kamar ta yaki, na saka tare da kwanciya, ina son tuna wasu abubuwan masu muhimmanci amma na manta dan dole na rintsa idanuna. Har kai na ya fara ciwo, sannan barci ya kwashe ni.

        Kamar wacce aka tashe ni na farka, sai nake jin kamar kunne na yana min gizo ana kiran sallah a can da nisa,  a hankali na fito gidan tare da niman ruwa, sannan na shiga, zaga gidan har na hango kogi da sarsarfa na isa bakin Kogin na nayi alwala sannan na juya zan koma naga yan wadanin share su nayi, aikuwa suka ji haushi, suka hayayyako min, kwallon nayi tayi da su, tare da watsar dasu na wuce abuna, sai bin keyana suke da ido, ko ajikina.

    Ina isa gidan nan ne kuma na rasa yadda zanyi sallah, dan haka nayi dikakke, na fara sallah.
```BOOK one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641'```

#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
03

    A hankali na gabatar da sallah, ina idarwa na kwanta a gurin, barci ne ya dauke ni, hasken rana da hayaniyar mutane ya sani bude idanuna. Hango wata matashiyar Wada nayi tana zare min ido, tare da saka min wani mashi a wuya. Lashe bakina nayi tare da kallon ta,  magana suke cikin harshen swahili ya sani kallon su kur sannan na juya musu harshen.

     "Kema kin iya Yaren swahili ne?"
"Kwarai!"
"Toh me yasa kika daure mana Sarkin mu, kuma mahaifina?" Murmushi nayi mata sannan nace mata.
"Ku godewa Allah daure shi nayi, da ba kwashe mishi gaban shi nayi ba, kar ya fita harkata sai na shafe mishi gaban shi"

    "Dame kike takama ne?" Inji Firoz.
"Jarumta!" Na bashi amsa,
"Ku sunce ta?"
Kunce Ni suka yi tare da saka min mashi a wuyana, ban kalle su ba, na nufi bakin kogi zan sha ruwa.
"Ke mafadaciya?" Kirjina ne yayi wani irin bugawa, tabbas an tab'a gaya min sunan. Lumshe idanun nayi tare da son tuna inda aka tab'a kiran na da sunan ganin zan bawa kai na ciwo ya sani share zancen sannan na nufi cikin ruwan na sha kafin na fito.

         Ina gamawa na juya tare da kallon su, budurwan wadan ce tazo ta tsaya a kusadani.
"Kiyi hakuri! Duk da daman. Ance zaki iya manta kome naki, amma muna nan da kike ganin mu,muna cikin damuwa domin kuwa saura nan da kwanaki a kawo mana farmaki,daga masu safarar mutane. izuwa kasashen duniya. Kizo ki ci abinci sai ki bar garin nan,dan zasu iya dirowa koda yaushe suna kama mana, mutane tare da kashe mana iyayen mu, bayan sun musu fyade. Don haka ki nutsu ki bar garin nan."

      "Iya taimakon da kuka min ba zai iya sani na tafi na barku cikin wannan halin ba, dan haka mu shiga gari." Haka muka yi ta zaga garin ina kallon yadda yake kawwace da manyan bishiyoyi, dan haka na ce mata.
"Suna Ikram! Iya shi zan iya tunawa, sauran kuma ba san inda na saka su ba, zamu iya zama aminai ko?"
"Eh Izmah zaki iya kirana!"

Jan iskar garin nayi me dauke da kamshin furen gulsana, nace mata.
"Wannan furen yana da guba me sakawa mutane suma, sannan kuma da bishiyoyi, yanzun abinda zamu yi Kinga wancan kogon muje!"

Juyawa tayi ta kira Firoz, sannan muka nufi kogon babu koma. Kallon cikin kogon nayi sannan nace mata.
"Zaku iya niman maganin kwari masu cutarwa a saka, sannan kuma zamu tattaro mutanen garin mu kawo su nan, Matasan gari da yan mata kuma zaku iya zama mu fahimci yadda zamu tunkare su."

  Koda muka dawo cikin garin nan muka hadu aka fara tattaunawa, tunda suke basu tab'a yaki ba, dan haka a cikin abinda zamu yi shine aka fara sarrafa kwari da baka.

         Da yadda ake amfani dashi kafin kace kwabo, har sun gane a cikin kwana uku, ana gobe mutanen zasu shigo aka maida Yan kauyen baki daya cikin kogon nan, matasan kuma suka haura bishiya,

    Cikin dare sosai, mutanen suka kawo hari, babu wanda ya kula su, sai da suka shigo cikin da'irar kauyen, muka sake musu ruwan kibau ta sama, garin gudu suka yi ya fadawa cikin ramin da muka hakka musu, ganin haka. Ni da Izmah muka nufe su, tana sake bakar ina tunkarar su da takobi.

       Ashe kofar rago suka min, domin ganin sun rubta a tarkon mu,, sai na fada a nasu. Ina zuwa gurin suna watsa min raga, ganin haka Izma ta saka a  Cigaba da sake musu Kibau, haka dai suka yi ta jana, ana kashe su amma basu hakura ba, sai da suka ga dab zasu rasa kansu. Suka fisge Ni.

Ganin haka Itama Izmah ta sauko tare da biyo bayan mu, haka suka hada da ita, da ni.

        A cikin wani abu me kama da keji, firoz ne yake Ihun kiran mu, nace Mishi.
"Ka koma! Zan kare rayuwar ta insha Allah, ka koma ka kare garin ka, zan dawo maka da masoyan ka."

Haka yan uwan shi suka rike shi, har muka b'ace.

    Firfitowa mutanen garin suka yi, tare da kallon hanyar da aka bi damu.
"Daga karshe dai ta koya mana yadda zamu kare kanmu, sannan Izmah ta sadaukar da kanta domin ta, duk da bamu san wacece ita ba, amma ina da yakinin ƙaddara ce ta kawo ta."
Inji Mawla,

         "Yarinya na ta fansan da kanta sabida yadda ta fansan da rayuwarta domin mu, iya haka ma ya ishe ni, amma na rike alkawarinta na cewa zata dawo min da ita, na rike wannan amanar!"

       Ya fada tare da fashewa da kuka, su kansu tausayin shi suke sabida yaran shi dukka hudu mata, duk mutanen sun tafi da su, sai Izmah ce ta rage. Dan haka koda gari yayi haske suka kwashe kayan yakin mutanen, suka kuma binne su. Sannan suka, koma gidajen su. Firoz yana zaune a gurin.

   _Masoyina! Kayi hakuri koda bana nan zan dawo wata rana, domin Ikram tayi mana kome! Ga mahaifina nan ka kula min dashi, ba zan iya ganin a tafi da ita ba_
Ta fadi haka tare da rungumo shi, hawaye ne ya zubo mishi. Shi kenan.

     Abinda alkalamina ƙaddara ya zana musu kenan, yayi musu rubutu a zanen ƙaddarar su lokaci guda, sun tafi. Kuka ne ya kwace mishi me ƙarfi sannan ya kalli garin da shawarar da Ikram ta badda, tace mishi.
"Yanzun don Allah kuna da wannan fure kuke kallon mutanen nan a haka suke cin zarafin ku, da farko tunda kuna da duwatsu dole ku dawo nan da zama, sannan ku koyi sarrafa makami musamman da kuka kasance Kananun mutane, sannan daga can zaku iya karar da mutane ba iya kan bishiya ba.

    Amma kun zauna sai anzo an tozarta matan ku, meye haka? Don Allah koda bana nan ku taimakawa kanku."

    Ta fadi haka,  yana juyawa ya gaya musu abinda zasu aikata, tare da yadda suka yi da Ikram.

  ----
"Sarwat! Dauke ta ku fada cikin ruwan! Ku tsira da ranku! Ikram ki gudu."
"Sultan Aamaan Mehran ya turo mu!"  Bude idanu nayi ina kallon cikin kejin me dauke da  mata da yara, rike hannuna Izmah tai tare da daura kanta a kafadana.
"Insha Allah! Zan mai daki gurin ahalinki."
"Bana jin tsoron kome ko fargaba, sabida ina tare da Jarumar jarumai, akan me zan tuna abinda ya wuce min."

"Iyaye nada muhimmanci, masoyi yana da daraja, karki sake ki manta da Firoz, kamar haka na tafi, ban koma mishi ba sai da kyautar mutuwar shi, Babban burina A duniya nasan waye Sultan Aamaan Mehran! Shi nake nima. Idanu rufe"

       Hawaye ne ya zubo min, ina kallon yadda itama take kuka. Tace min.
"Ikram! Kiyi hakuri ya kashe miki masoyi ko?"
Goge kwallar nayi sannan nayi wani irin murmushi, ta gefen baki sannan na maida hankali na, kan abinda nake yi.
"Lallai jinin shi ya tabbata ga fansanki Ikram ba zan tab'a komawa ga mahaifinta ba, har sai na taimaka miki da kin dauki fansar jinin masoyinki."

   Gyada kai nayi, har muka isa wani gari me suna.
Sira.
Anan ake cinikin bayi kamar  yadda ake cinikin dabobbi, kowa ya ganmu da Izmah, hari yake kawo mana.

    Dan haka muna tsaye aka ja gefe tare da yin kuskus, aka ce mana.
"Ke me idanun mage! Kubi wancan mutumin."
Ba musu na riko Izmah muka nufi inda mutumin yake, sannan ya kai mu gidan da wasu mutane suke, muna shiga cikin gidan. Suka yi ta kallon mu, har suka gama sannan d'aya daga cikin su yace masa.
"Doguwar tayi min, wadar ce bana bukata."
Kai hannu suka yi zasu juya da Izmah, nayi maza na juya hannun su, cikin zafin nama. Komawa da baya mutumin yayi.
Ita kuma ta k'amk'ame ni.

         "Mafadaciya! Ya da saurin fusata haka? Ke nake bukata ba ita ba." Kallon shi nayi sannan na kalli yadda yake kallon Izmah,
"Tare suka kawo mu, tare zaka saye mu! Idan bamu maka ba, zaka iya."
Da gudu me tsaron lafiyan su ya kawo min sara,. Tsalle nayi tare da lankwashe kafaffuna, sannan na dira a kirjin shi, dayan na zuwa na zari wani abinda Izmah ta kama gashin ta dashi na soka mishi a wuya.

"Ikram!" Juyawa nayi naga sun rike wuyar ta da takobi. Murmushi nayi irinta kayi kuskuren tab'a min  ita, juyawa nayi tare da daura wukar da suke yanka tufa na wurga mishi sai da ta huda kirjin shi. Sannan na kalli mutumin wanda yake zaune ko a jikin shi.

       Sauran na gefen shi da suka sunkuya tare da yin kuskus, suka kalle ni.
"Daga wani yanki na duniya kika fito?"
"Wannan ba matsalar ka bane, yar Uwata tayi ciwon kai, Allah ya bani baiwar gintse numfashin kowa."

       Tasowa mutumin yayi, tare da cire babban rigar shi sannan ya kura min ido, yana faɗin.
"Zan dauke ta, amma ki fara gwada kwanjinki dani, sai na san abin yi."

        _A duniyar fadar kareti, zafin nama itace nasarar ki, karki sake makiyinki yasan abinda zai sakaki kuka a fadar ku, karki dake kibawa makiyi daman kai ki kasa, zafin namar ki shine nasarar ki! Kinji ko Mafadaciya_

Ba zan iya tuna muryan waye shi ba, amma tabbas ya gaya min abinda ya dace,
   Alama mutumin yayi min sannan ya koma baya, haka kawai naji raina ya b'aci sosai da mutumin tsanar da ban san daga inda na fara shi ba, na tattara na tsane shi, dan haka koda muka fara fadar cikin zafin nama. Muke kaiwa juna mugun nufin.

     Sai dai yadda yake sauya salon shi, nake kuma iya bin shi har na kai mishi duka Yasaka shi fahimtar nafi shi zafin nama, sosai na hargitsa mishi lissafi, sai da takai bai iya kare kan shi, kafin na kyale shi.
"Waye ya koya miki fada haka?"

        Juyawa nayi abu na, zuwa gurin Izmah, na durkusa tare da rungume ta, ina cewa.
"Ba zan tab'a barin wani ya cutar dake ba, koda kuwa hakan sadaukarwa ce a gare ni. Duk wanda yake da bukatar mu, kofa a bude take babu wanda ya isa ya raba mu."

     Na fada da karfi, sannan na juya gare su, ina rike da hannunta,
"Kunyi min! Kuma zan saye ku a haka. Sai dai kuma inda zan kai ku yana da matukar hatsari, dan wasa da rayuwar ku zaku je yi."

"An haife ni ne dan nayi wasa da rayuwata, ba a haife ni dan na bautawa kowa ba, sai Allah."na fada ina kallon shi.

Kura min ido yayi tare da kallon yan uwan shi. Gyada kai yayi sannan yace min.
"Zaki iya tafiya!"
Juyawa nayi tare da barin d'akin, aka nuna mana hanyar da zamu bi.
"Me kuka fahimta a kalaman ta?"
"Wallahi nima tsoro ne ya kama ni, don haka shima yayi wannan furucin lokacin da muka nemi hadin kan shi domin mu kashe Abban mu! Yau ga wata me kama da shi da muryan shi ta bamu amsar shi."

      "Kai murya ce kawai amma babu wani kama da suke yi, sai dai kuma zan cigaba da Binciken ta, har sai na gano gaskiya amma tana da zafin nama sosai, kuma bata wuce sha takwas ba, amma ta iya wannan b'arnan, idan ta gawurta za a shiga uku da ita a duniya."

      ---
Ana kai mu dakin abinci aka kawo mana me shegen kyau da dad'i, sallah dake kai na na sauke sannan na zauna tare da kallon Abincin da Izmah take kallon shi itama, dan bamu yarda da abincin ba.

         Kallon kunnenta nayi naga azurfa ne.
"Bani azurfan kunnenki!"
Tana bani na soka cikin abincin sannan na rufe abincin, can na bude tare da cirewa, dan kunnen yayi bakikkirin. Murmushin gefen baki nai, sannan na dauki abincin na koma wannan babban falon na watsa musu a gaban su.
"Lallai na sami abinda nake buƙata har kin fahimci da....

```BOOK one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```

#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

04
"Har kin Fahimci akwai guba a cikin abincin?"  Watsa mishi kallon banza nayi sannan na ce mishi.
"Waye ya gaya maka Ni jahila ce irinka, lokacin da muka shigo na daki wadancan kartin, ina kallon ka gyadawa matar da zata shiga damu cikin gidan kai, tare da kallon mu, a duk inda zan shiga nakan bawa ƙwaƙwalwata muhimmancin lissafi sama da zuciyata, dan haka ka kawo min abinda zamu ci ko kuma nayi maka wankan da kurbataccen abincin da ka bamu."

    "Me yasa baki da hankali?" Ya daka min tsawa cikin izza da fushi.
"Ba a haife ni  a cikin babban gida ba, dan haka sauke muryan ka k'asa yanzun kace ka sami abinda kake nima, ce maka akayi Ni karamar haja ce da zaka same ni a ruwan sanyi, Izzar da take cikin zuciyata ta wuce wanda yake zuciyarka. Ni haihuwata aka yi dashi kai kuma ba mamaki tsintar ta kayi, karka kara min tsawa dan zan iya tafiya babu wanda ya isa ya dakatar dani."

          Ina fadar haka na juya tare da barin gurin, har zan kulle nace mishi.
"Yanzun zaka kawo min! Kuma da kanka, idan ka wuce dakika dari uku da sittin sai dai wata ba dai Ni ba."

       "Anya ba jinin shi  a jikin Yarinyar nan kuwa? Kalaman shine akan harshenta! Ina jin tsoro Sulaiman yarinyar nan tana da boyayyen al'amari a tare da ita, don Allah mu hakura da niman wanda zai mana aikin nan muje muyi ta saka bayi suna jarabawa"

     "Kayi min shiru Muntaz! Kayi min shiru nace, ni bauna ne saniyar sake, bazan kuma juyawa ba, dan haka zan tafi da ita. Kuma zan mata duk abinda tace, cin Amana a jinin mu yake dan haka zan."

       "Amir Sulaiman ga abincin nan!" Ta faɗa a hankali, juyawa yayi ya amsa, sannan ya juya ya nufi cikin gidan, koda ya shiga ya same mu a tsaye, ajiye abincin yayi tare da zama ya zuba kome ya fara ci, sannan na zauna nima na fara ci, nayiwa Izmah magana ta fara ci, bamu kula shi ba. Amma kuma na fahimci akwai magana a bakin shi.
"Ina gayyatar ki turaka na!"
Bugawa kirjina yayi tare da kura mishi ido, sannan na dauke kai na, wani irin murmushi nayi iya gefen bakina, sannan na dauki nama na karayawa Izmah.
"Ina bukatar goran giya, abokiyar tafiya na tana sha!"
"Toh ranki shi dad'e, Sultana"
A hankali na d'aga idona na kalle shi, sannan na sunkuyar da kai na, domin wannan kalmar ba sabo  bane a gare ni, na sha jin shi a wasu lokuta da Bazan iya tunawa ba.

    Fita yayi muka ci abincin, kawo mana goran giya yayi, sai da yasha sannan na barta tasha, domin Ni Bazan sha ba, idan na sha nasan haramun ne, dan haka na maida hankali na, kanta, tunda naga taji dadin giyar, har kusan lokacin sallah, tana sha kafin na lura ta fara bugar da ita, tashi nayi na gabatar da sallah, ina sallah isha naga ta tuntsara, gyara mata kwanciya nayi. Sannan na nufi hanyar waje inda na sami matar nan a tsaye da kayan sawa a hannun ta, mika min tayi na nufi ciki na saka, sannan na fito.

    Kallona take cikin murmushi tace min.
"Kina da sirrintacciyar kyau!"
Murmushin gefen baki nayi sannan ta mika min turare na shafa, tare da nufar hanyar da ta nufa.
          Ina tafiya ina kallon shigar jikina, haka na shiga babban falon yana zaune sai had'a lissafi yake tare da shirya kome, a hankali na tsaya tare da gyaran murya,. D'ago kai yayi cikin nutsuwa yace min.
"Zauna zinariya!"

"Bani da lokaci. Ina jinka."
"Kizo ki zauna a cinya na, dauke kai nayi ina me kallon ko ina. Muryan shine ya katse min nazarin da nake,
"Ba baiwa na dauke ki ba, aiki zaki min amma don Allah kizo nan ki zauna."

Babu musu na nufi gurin da yake nuna min, wato kan cinyar shi na zauna, hannun shi ya kawo tsakanin cikina ya manna ni a jikin shi. Wani irin tartsatsi naji tare da hasko min hakan ya tab'a faru da komawa, amma kamar mafarki kamar a zahiri. Wasa yake tsakanin cikina zuwa kirjina, kanshi a kan wuyana, yake cewa.
"Zan dauke ki, aikin sirrin na wata shida, a masarautan marocco, zaki min wani aiki ne

Please Login or Register in order to submit comment