Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne domin rabin hiran su akan shi suke min.

       A waje na hadu da Rahil ya kawo Abrad, dan haka ban yi mamaki ba, dan nasan yazo gaida Ummyn ne, har cikin gidan ya shiga suka gaisa, sannan suka shiga tattaunawa akai na, wanda duk hiran akan yadda ake shirya min tarb'a da bikin da za ayi mun ni da Rahli.

      Bai ce komai ba, amma daga yadda ya rasa nutsuwar shi har ya gama hiran da ita, muna zaune a harabar masaukin. Zama yayi a kusa dani tare da zuba min ido. Dauke kai na nayi daga gare shi sannan na cewa Rahil.
"Ina son zan sha madara! Amma bana son bayi su kawo min" na fada cikin sakakkiyar murya.

     Mikewa yayi tare da cewa.
"Zauna ki huta mata na, ba zata tab'a wahala ba. Domin ita din sarauniya ce zan kawo miki." Ya faɗa tare da nufar hanyar cikin gidan. Gyara zama nayi sannan na kalle shi.
"Kayi ƙoƙarin raba ni da Mehran, ka dasa mishi k'iyayyana. Sai dai kayi kuskuren mafi girma domin kuwa kayi abinda ba zai tab'a barin ka ba,  daga yanzun daga wannan lokacin ka fara boya, kayi ta gudu karka tsaya.

   Domin tsinin takobin shi sai ya huda kirjin ka. Ka fara gudu karka tsaya inda zai same ka. Nayi danasanin fadawa hannunka, domin babu wanda ya kashe ni da rayuwata sama da kai.

    Babu wanda ya lalata min rayuwa sama da kai. Sannan sauran da yarage kazo zaka lalata min su! Meye nayi maka da zafi? Meye na tsare maka da zafi haka? A sanina ka auri Kanwar Mahaifiyata toh meye kake son daga gare Ni? Amma masu iya magana since idan ajali yayi kira ko ba'a ciwo za aje."

  Daga haka na mike , rike hannuna yayi cikin zafin rai na tsinka mishi mari sannan na wuce abuna, duk akan idanun Amir Rahil ne, ina shiga ya zuba min ido.
"Meye ya haɗa ki dashi? Meye Matsalarki dashi? Yau zan dakatar da shi."
Gudun kar a kuma aikata abinda Ya faru yasani rike shi tare da kallon shi nace.
"Karka damu. Ya wuce na koya mishi yadda ake mutuntawa."

    Murmushi yayi tare da mika min madaran muka shiga zaga gidan, wai duk sabida kar na saka damuwa a raina.

         "Wai dama an miki baiko da wancan basamuden ne?" Kallon shi nayi tare da murmushi kafin nace mishi.o
"Eh amma kuma sawun giwa ya badda na Raƙumi ba" shima kallona yayi sannan yace.
"Ban gane ba?"

Murmushi nayi a karo na biyu, sannan nace mishi.
"Zaka gane mana." Dariya yayi sannan yace min.
"Amma kuma"
"Amma kuma me?" Na tambaye shi,
"Amma kamar kuna son juna da wancan basamuden?"
"Me ka gani?"
"Kin dawo min da tambayana"
"Kamar ya?"
"Kamar yadda na gani da idona"
"Lallai kayi kuskuren"
"Banyi kuskuren ba sai gaskiyar da na hango."
         Kasakai nayi ina kallon shi.kafin nace mishi.
"Babu wata soyayya a tsakanin mu, kawai kana ganin haka ne amma ban ga!"
"Da gaske baki son shi?" Ya tambaye ni, tsayawa nayi ina kallon shi. Tambayar da yayi min iya gaskiyar shi ce, amma kuma bana jin zan bashi amsar wannan tambayar dan haka na juya tare da barin shi a gurin, bakin ruwan da yake gudana a gurin na isa sannan na zauna tare da saka kafana ina nazarin maganar da muka yi da Rahil.  Zama yayi kusa dani, sannan yace min.

"Kiyi hakuri da sakaki surutu da nayi, sai dai kowani mutum me hankali da sanin ya kamata zai so ya ajiye irinki a gefen shi ko badan mu'amalar aure ba, ana bukatar mutum ya ajiye mace irinki na farko zaki bashi garkuwa, na biyu zaki bashi farin ciki a rayuwar shi, na uku kuma..." Murmushi yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Sai nan gaba zaki Fahimci abinda nake nufi"

Girgiza kai nayi sannan na juya tare da kallon cikin ruwan, ina jin babu dad'i domin Allah ya gani son Ƴan uwantaka nake mishi ba son kauna na aure ba, kuma ba zan iya bijirewa iyayen mu ba, tunda abinda suka yanke kenan. Amma ko ya ya bai kamata su zartas da hukuncin haka ba, idan suka yi dubi da ni bakuwa ce a cikin su.

        "Ikram ko na takura miki ne?" Ya tambaye ni cikin damuwa,
"A'a baka takura min ba, sai dai kana da hawa kai" na fada ina kallon shi,
"Toh kiyi hakuri! Ban san yadda zan nuna miki farin cikin da yake raina bane, amma kuma ina jin nutsuwa a zaman mu nan."ya faɗa cikin sanyin murya, duk sai ya bani tausayi, tabbas akwai matsala domin nasan dai ba zan hada maza biyu ba, amma kuma yadda Mehran yayi min ban ji dadi ba, dan haka na juya ina wasa da ruwan.

    Kasa hakuri yayi tare da zama kusadani kamar zai shige jikina, kallon shi nayi kafin nayi magana ya jingina kan shi akan kafadana, tare da riko hannun na, yana me matsawa a hankali.

    ...... Ya saba da ganinta tana sintiri dan haka yau da bai ganta ba, duk sai ya damu dukda ya ganta lokacin da ta fito dakin Sultanah, amma kuma zuciyar shi da ruhin shi suna begen ganinta, ƙwaƙwalwar shi tana yawan hango mishi.wasu abubuwan akanta, dan haka ya mike tare da sauya shiga izuwa kayan dakarun kasar ya fita daga gidan. Gidan bakin dake cikin masarautan ya nufa, tunda ya shigo ya hango yadda suke zaune da Abrad, sai yaji kamar ya koma, amma kuma ya fasa bayan ta gama gayawa Abrad magana yana mamakin yadda take iya sarrafa maza, dan yasan haka kawai ba magana me dad'i ta gayawa Abrad ba. Bayan fitar Abrad, ya hango suna magana da Rahil.

Sam Mehran bai dauki Rahil a wani namiji can ba, amma ganin yadda Rahil din yake ta damunta da surutu sai yaji tsoron kar abinda ta rasa a gare shi ta samu a gurin Rahil tunda soyayya ta tasa kuma idan ta samu a gurin Rahil shi bai da wani abun da zai gwada mata. Suna tafiya yana bin bayan su har gurin ruwan. Duk da bai san meye suke fada ba. Amma kuma tabbas abinda suke fada akwai muhimmanci dan haka ya nace sai yaji abinda suke fadi.

   Bayan ya matso ne yaji lokacin da Rahil yake gaya mata kowani namiji zai so samunta a rayuwar shi. Take hankalin shi ya tashi domin shi ya dace ya fahimci haka, amma baƙin kishin sa Ya saka shi kasa fahimtar kome akan haka. Yana kallon su har ya daura kanshi a kafad'ar ta, a lokacin sai da yaji kamar zuciyar shi zata dirko daga kirjin shi domin babu abinda ya tsana kamar yaga namiji a jikin ta. Yau gashi akan idanun shi wani yake jingina kanshi a kafad'arta. Ji yayi kwallar bakin ciki ya cika mishi ido. Dan haka ya juya tare. Da barin su a gurin tabbas bai da sa'a shi yasa ya rasata a karo na biyu,a da yana tunanin ya sami kanta ko bai gaya mata yana sonta ba, zata iya furta mishi ashe hasashen shi ce, ba tunaninta bane. Bai yarda da abinda Sultanah ta gaya mishi ba sai yanzun da ya gani da idon shi lallai yayi sake d'an zaki ya girma yayi kuskuren barinta ta rayu da wani, da tun lokacin ya kafa gwamnatin shi babu wanda ya isa ya rab'e ta, amma ya zauna sai tsanarta mata amfani da yake ji.

    Da wannan tunanin ya bar masaukin..
Haka kawai naji kamar Mehran ya zo har inda nake dan haka ba juya tare da kallon wani badakare yana tafiya. Haka kawai nake mishi kallon kamar Mehran ne, har na juya zan cigaba da wasa da ruwan sai kuma naji bari na kuma juyawa dan kamar yana kallona, koda na juya yana nan a tsaye. Sannan ya kasa  tafiyar shi.
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
39
Juyawa nayi sabida idanuna da suke min gizo, a hankali kwalla suka cika min ido. Tabbas Matsayin Mehran Babba ce a zuciyata ya, shi yasa na kasa Mantawa dashi.

        Saka hannun shi yayi tare da tare kwallar da take sauka akan fuskana.
"Waye ya tab'a min ke?" Murmushi nayi tare da goge kwallar nace mishi.
"Ina kewar Airan ce, kuma kaga dole nayi kuka domin itace kawai ta rage min gashi ba rasata ga kuma Allah ya bayyana min dangin mu."

"Ikram!" Ya ambaci sunana a hankali yana kallona, sannan yace min.
"Bana raba daya biyun kina tunanin Mehran ne"

Kura mishi ido nayi, da gaske haka ne amma kuma ɗan na karya ta abinda yake tunani a kaina yasani faɗin.
"Tir wannan wacce irin magana ce? Na rasa wanda zanyi tunanin shi sai mutumin da bai da wani amfani a rayuwa ta, kawai dai kana zargina ne, amma idan ba haka ba me zai sani tunanin Mehran."

Cikin fushi na mike zan bar gurin, riko hannuna yayi tare da zaunar dani.
"Kiyi hakuri!" Ya faɗa min a sanyayye, sannan yace min.
"Dole naji babu dad'i, babu namijin da zai so yana yana tare da mace amma zuciyar ta yana ga wani mutum na daban, Kinga kuwa zai cigaba da ganin haka kamar rashin adalci ne."

   Tabbas ya bani haushi amma kuma yana da kyau na tausaya mishi domin gabaki daya ya addabi rayuwata da naci, dan haka na sassauta fushina nayi sannan na zauna ina kallon shi.
"Ke kamar Uwace a gare ni, kin bani kwarin gwiwar da na rasa akan me zaki yi fushi da Ni? Bayan ke bani da wanda zan ƙalla nace shi Masoyina ne. Amma ke kuma na ambace ki da kalmar me tsada da girma,don Allah karki yi fushi da d'an uwan ki."

                Na rasa me zance domin duk wata kalmar da zai yi amfani da ita,rudurduga min zuciya take, duk wata harafin da zai ambata kamar kunawa zuciyata huta yake, gabaki daya sai naji ba zan iya ganin shi cikin rashin nutsuwa ba, zan amshi auren shi duk da ina da zab'i amma kuma shi din zab'in kakanni na ne, hannuna yakai  fuskar shi sannan yana faɗin..
"Ki dube ni da idanun rahama, karki juyawa tayina baya"

   Hawayen da nake b'oyewa ne suna sauko a hankali tare da kura mishi ido, tabbas kome ya kare min dan haka na rike hannun shi tare da cewa.
"Ba zan tab'a juyawa tayin ka baya ba, ina tare da kai kuma zan zauna da kai." Ina gama fadar haka na mike zan bar gurin. Shima mikewa yayi sannan ya saka hannun shi dukka biyu ya rungume ni. Yana shafa bayana. Mehran yana kallon mu. Juyawa yayi tare da barin gidan baki daya. Idan ka ganshi zaka dauka bai da lafiya ne. Hamas shiga Harami ya nemi faduwa, tare da jin wani mugun sanyi ya shige tare da zazzaɓi me mugun zafi.

      Fudail da yaga fitar shi, shine ya fara ganin shi san yana harabar gidan. Ya rike shi zuwa cikin gidan.
"Fudail kirjina zai fashe."
"Sannun Sultan! Ina kaje haka? Ko kamanta kana da ciwon zuciya ne? Gashi a karon farko zaka kashe kanka."

       Ina kasa magana yayi sai juya kai yake, yana jin kamar kirjin zata fashe, a dakin shi aka kwantar dashi.
"Fudail, Ikram" ya faɗa a sanyayye dukda idanun shi a rufe suke amma bai hana shi. Kiran sunan Ikram ba, gabaki daya ya zauce baya gane kome sai sunan Ikram,har akayi sallah magarib da isha Mehran baya cikin hankalin shi. Matan da aka zab'e mishi kuwa kasa hakuri suka yi. Sai da suka magantu.

    Amma haka bai hana Mehran kiran Ikram ba, tun ana zata zafin zazzaɓi ne har suka gane cewa ita din yake bukata, gashi dare yayi sosai. Dan haka suka yi ta fama dashi, daga karshe dai Sultanah da Fudail suka fita har gidan bakin.

       ...... Ina kwance banyi barci ba amma kuma zuciyata babu dad'i dan haka na tashi zaune, naja labulen gadon ina kallon su Nimrah da Izmah, da suke kwance can gefe guda. Kallon su nayi naga suna barcin su. Wato sai kana da nutsuwa kake samun damar barci idan baka da shi kuwa. Kai da barci har abada.

      Buga kofar dakin mu akayi na sauka a gadon sannan na bude tare da kallon Ummyn da Sultanah Fazilatul nisa.
"Ikram! Don Allah zoki taimake mu. Mehran zai mutu." Ban tab'a sanin akwai rudewar da zata sani niman fita daga cikin gidan babu suturar Arziki a jikina ba sai da aka gaya min Mehran zai mutu. Riko hannuna Rahil yayi cikin dakewa sannan yace min.
"Baki da lafiya ne? Dubi yadda zaki fita? Koma ki shirya ina jiranki!"

         Haka nayi kamar yadda yace min, tare muka tafi har da wasu dakarun. Tunda muka shiga cikin harabar gidan, Rahil ya riko hannuna.
"Karki manta akwai alkawarina akanki. Dan haka kiyi kokarin kare girman alkawari."

         Kallon shi nayi domin na kasa Fahimtar me yake nufi, a lokaci guda naji ya fice min a raina. Hawayen da ban san yaushe ya sauko min ba.
"Kasan girman shi a cikin idanuna? Kasan yadda nake  jin shi a raina? Da kasan yadda nake kokarin kyautata mishi ba zaka tab'a sanya min sharadi dan zan ganshi. Ka tsaya a matsayin ka na wanda aka mana alkawari karka tinzira zuciyata izuwa aikata abinda ba zan iya daukar shi ba. Sultan MEHRAN wani shashine na rayuwata. Don Allah karka raba abinda yake a haɗe." Ina gaya mishi haka na shige cikin gidan.

  Na sami Kwarkwarorin shi a bakin kofar, suka gani na suka shiga matsa min a hanyar. Shiga dakin nayi na same shi rike da kirjin shi. "Ikram! Ku kawo min ita" ina shiga matan shi suna shigowa. Tsayawa nayi a bakin gadon ina kallon yadda yake dafe kirjin shi. A hankali na zauna a bakin gadon. Na kai hannuna tare da riko hannun shi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da ƙamƙame ni.

   "Ikram!" Ya kira suna na idanun shi a rufe.
"Na'am Sultan Mehran!" Bude idanun shi yayi sannan yace min.
"Mehran zaki ce, ki ce min Mehran."
"Meke damun ka?" Hannu na yakai bakin shi ya sumbata, sannan yace min.
"Kece ciwo na. Kece magani na" ya fadi haka, kallon sauran matan Fudail da Sultanah suka yi tare da musu alamar su fita.
Fuuuu suka fita daga dakin, ina rike da hannun Mehran, tashi yayi tare da dawowa kan cinya ta, yana sauke ajiyar zuciya.
"Karki tafi! Kunne na yana min kai-kayi, ko zaki susa min"

   Shafa kan shi nayi tare da jin saukar kwalla daga idanun shi akan cinyata.
"Kayi hakuri! Ni zan tafi gobe Insha Allah..sannan ka rungumi matan da aka baka, Insha Allah zaka sami wacce zata fini tsayin daka."

"A wani matsayi kika ajiye Ni?" Ya tambaye ni tare da damke hannuna. Shafa kanshi nayi a hankali tare da jin tashin hankalin a raina.
"Mehran! Kai kamar Uba ne a gare ni, bana son na ganka cikin tashin hankali da damuwa, Mehran ina zaune ne domin kai bayan haka bani da hurumin zama a cikin Masarautan SAMAIND, amma kuma sai naji kunyar abinda ka aikata min. Mehran na tawo da niyyar daukar fansa akan abinda kasa aka aikawa Numan."

    D'ago kai yayi tare da kallona.
_Me yasa ba zaki gane bani da hannun cikin kisar gilla da aka yiwa Mijinki? Me yasa ba zaki gane ban san kome akan kashe shi ba! Nayi kuskuren furta sai na kashe shi amma bani na aikata ba_

      Shiru nayi tare da janye idanuna daga cikin na shi, sannan na cigaba da cewa.
"Haka bai sani ajiye makamina ba, na amshi aikin da ka sani ba. Mehran sai da na gama tsalleke duk wani mataki da iyaka, amma ka juya min baya, alhalin kasan ba zan yi abinda kake zargi na ba, Mehran ko daga cikin gidan ƙaruwai la dauko ni,.zaka min uzuri balle kuma kai da kanka kasan ba haka nake ba. Ka kira Ni da sunaye masu kazamta da muni. Kayi hakuri Mehran amma iya yau nayi domin Mahaifiyarka ce da Aminin ka, bayan haka Akwai alqawarin auren D'an Uwana, don Allah kayi hakuri. Kai Ubane a gare Ni bayan haka bana jin akwai bukatar na kara maka wani matsayin."

Na fada mishi haka ina had'iye kukan da ya taso min, sannan na cusa hannuna cikin gashin kanshi ina wasa dashi. Hawaye na yana zuba akan gashin kanshi.
"Ban yi laifin da kake zargina ba. Amma ka kasa fahimtar kome a kaina, kayi hakuri nasan nayi laifi da kuskuren fita daga harami zuwa gidan da Abrad yaƙe, amma yadda kasame mu da shi babu wani abinda kake tunanin ya faru, nasan bai zama dole ka yarda dani ba, amma iya gaskiyar kenan."

        Tashi yayi zaune tare da kallona, idanun shi jajjur bakin shi yayi fari sol kamar wanda ya jima yana jinya.
Mikewa nayi sannan na dauko mishi ruwan na mika mishi. Riko hannuna yayi tare da haɗawa da nashi ya kai ruwan bakin shi ya sha, sannan ya janyo ni jikin shi yana kallon fiskana da take jike da kwalla.
Tari ya fara tare da daidaita tsayi na da fuskar shi.
"Meye matsayina?"
Kallon shi nayi sannan na fara ƙoƙarin mik'ewa, sake murmushi yayi tare da cewa.
"Meye matsayina?"
Kwalla ne suka shiga tuttukowa daga cikin idanuna, bakina yana rawa na bude zan bashi amsa, sai jin harshen shi nayi cikin bakina, tare da lumshe idanun shi, ya rike kai na gam. Wani irin kuka naja tare da ajiyar zuciya. Ina kallon shi har cikin idanuna. Abinda nake hangowa ba abin wasa bane, ba kuma karamin abu bane.

      Amma zurfin cikin da YAKANA sanya shi b'oyewa. Gani yake idan ya fitar duniya zata iya zage shi. Shi yasa yake kokarin ganin ya adana abin a idanun shi da zuciyar shi.  Amma abin yaki ajiyuawa, dan ba gama garin sirri bane da ake iya boye suka zauna lafiya.  Da kanshi ya sake min bakina da yasha tauna a gurin shi, haka ba sabon abu bane a gare ni amma kuma kuma tambayar anan shine meye yasa Mehran yayi min haka? Me yasa ya kasa yarda dani? Meye yake kokarin b'oye min?

Kasa nayi da kaina, domin bani da amsar da zan bawa kaina, amma daya biyun ina kara fahimtar kaunar da yake lullube da kishi na akan idanun shi. Hannun shi naji cikin rigar jikina. Da sauri na rike tare da kallon shi.
"Me ye matsayina?"
Bakina yana rawa na kalle shi tare da cewa.
"Shugaba na!"
"Hmm! Ban yarda ba"
"Allah da gaske nake gaya maka" sake tura hannun yayi zai kuma tab'a min jikina nayi maza na mike ina gyara zaman rigar jikina.
"Ina zaki?"
"Na bar Rahil a waje kuma nasan yanzun dare yayi."
Tab'e baki yayi sannan ya dauke kanshi.
"Baki gaya mishi gurina zaki zo ba?"
"Ya sani rakoni yayi!"
"Toh gaskiya babu inda zaki a daren nan, a nan zaki kwana." Ya nuna min gefen shi.
"Amma Mehran!"
"Na gama magana idan kuma ban isa ba zaki iya tafiya dama ai bani da daraja da matsayin da zaki zauna dani ko ance miki ban san labarin zaman za kuka yi dashi a cikin gida daya bane, wato ni aka maida sakarai, ayita zagawa ana cin amana Na, idan nayi magana ace na cika zargi bayan kowa ya sani Salsabilah yake kiran ki, wato koramar shi. Ni kuma d'an iska ban san me zance ba."

           Matse hannuna nayi a cikin juna, ina jin wani irin takaicin Mehran da haushin sa, kafin na d'ago kai nace mishi.
"Kai ma ai kana da naka sunan da kasa min kamanta ne?"
.wani dauke kai yayi cikin jan aji irin ya manta dole na tuna mishi.

              A hankali na dan sunkuya ina kallon shi..
"Sultan MEHRAN!" Da sauri ya juyo yana harara ta, sannan yace min.
"Qurratulain!"
Murmushi nayi sannan nace mishi.....
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...

_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_

40
Karshen book 2

"Me yasa kake son tilasta min zama da kai bayan kai baka yarda da ni ba? Kasan girman kuskuren da ka aikata? Da a ciwo a.."

Yatsar shi ya saka akan bakina, yana kallon yadda nake kokarin cire idanuna a cikin nashi.
"Kamar yadda kike zargina da kashe Nu'man haka nayi domin." Jan iskar bakin shi yayi tare da mik'ewa yana me kai hannun shi kan fuskana ya d'ago ni tsaye.

    Dukka hannu bibbiyu ya zuba a k'uguna, yana me ben fuskana da kallon me cike da sanyin yanayi.
"Duk yadda naso kare kai na, baki bani damar haka ba, sai ma kuma tinzara da kike. Ikram na baki damar shiga rayuwata ce a karo na biyu dan ki zama alkali a rayuwar mu, don Karki hukunta ni da laifin da ban aikata ba" ya faɗa muryan shi can kasa tare da saka kanshi a kafadana.

      D'ago shanyayyun idanun shi yayi a karo na biyu, yana kallon yadda nake kokarin janye jikina daga gare shi. Juyar dani yayi tare da daura kanshi a kafadana.
"Na san na fada a kashe shi! Amma kuma ban ba da damar kashe shi ba. Ki dube ni da idanun rahama karki nisanta kanki da ni" ya faɗa yana me kai hannun shi dukka biyu kan cikina.

   Ina jin yadda zuciyar shi take bugawa, kan shi kuwa wani irin zufa yake fiddawa, narkewa nayi a jikin shi tare da lumshe idanuna, ina kuma jin kamar nacewa Sultanah Amrah ni kawai su tafi ba zan bisu ba. Juyawa nayi zan fita ya kuma tare kofar.
"Me yasa kike saurin tafiya gurin shi?"
Sunkuyar da kai nayi tare da maida gashin kai na baya, sannan na d'ago kai na, kafin nace mishi."Mehran kayi hakuri akwai alqawarin auren shi a kaina..."

Wurgi yayi da kayan abincin shi.
"Alqawarin banza, ko Ni bani da zuciya ne da ba zaki fahimci halin da nake ciki ba? Ce miki akayi dadin Kowa nake ji bayan ke? Toh jeki kawai jeki Allah ya baki zaman lafiya. Kije ki aure shi." Cikin jin haushi ya turo ni waje daga dakin shi ya rufe kofar d'akin shi. Yana cikin dakin sai barna yake kamar yaro karami.

       Juyawa nayi tare da barin gurin, har na sauko kasa Kwarkwarorin shi suna kallona, ganin yadda suke b'ata rai ya sani dauke kai na abuna, sabida duk cikin babu wacce ta taki sa'ar da na samu, dan haka babu wacce zata min iyayi ko kankanba. Ina fita na hango Rahil zaune shi dasu Shairah da Fudail sai Darda.

   A hankali na isa gare su, sannan nayi musu bankwana. Ina lura da yadda jikin shi yayi sanyi musamman yadda na same su, suna hirar Mehran. A hankali muke tafiya yana me sauke ajiyar zuciya a kai a kai, ba zaka tab'a jin bai sauke tare da fitar numfashin sa ba, kuma yaki kallona, abinda na fahimta matsanancin kishi yake. Domin ina lura da yadda yake naushin hannun shi har muka isa gidan.

     Saka kai nayi zan wuce masaukin mu naji ya riko hannuna, juyawa nayi tare da kallon shi.
"Me yasa baki da tausayi da jin kai? Me yasa ba zaki gane yadda nake kokarin kyautata miki ba? Kin fi son bare a kaina? Tun da kika shiga cikin gidan kika manta da batu na, sai yanzun kika tuna dani, gaskiya ina da zafin kishi da zafin rai idan na kuma ganin haka zan aikata abinda ba zai miki dadi ba."

    Kasakai nayi ina kallon bawan Allah nan, wato sun mai dani sha tara, kowannen su buga ni yake kamar tamola, meye nayi musu haka da kowannen su yake jin zafi na?  Nima cikin fushi na bar shi a tsaye,ban saurare shi ba,balle yayi tunanin zan bashi hakuri ko wani abu makamancin haka.

     ... A wannan daren mutane uku basu rintsa ba, gabaki dayan su kowanne da abinda yake ji, dan haka gari

Please Login or Register in order to submit comment