Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dab da fasa ihun mara amfani, taya yayi sake har suka fara kaunar junan su? Taya Ikram da Mehran zasu ci amanar shi. Dan haka ya mike tare da mishi sai da safe, daga yanayin hiran da suka yi ya fahimci yadda yake boye shaukin shi akan wani abu na daban.

      ----
A hankali lafiya ta fara samuwa dan mun kwashe kwana goma sha tara, ina jinya har na fara fita waje, ana hira dani, dan ma ana sanyi sosai, amma kuma haka bai hana ka fahimci bana shiri da Mehran ba, Fudail ne abokin hirana da Baba, shima sabida ina ƙoƙarin daukar takobi ina koyan fada ne, tunda jikina ya sami lafiya.

    Koyan yakin da nake a gurin Baba yasani fahimtar shima tsohon kashi ne, dan haka idan muka fara kamar ba zamu dai na ba, gashi wani lokaci har kuskuran shi nake da takobi.

Yau na kamar kullum muna cikin haka na yanke shi a damtsan shi.yarda takobin nayi tare da zuwa kusa da shi, ina cewa..
"Don Allah kayi hakuri! Bada gayya bane."
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
Page 33

"Waye ya koya miki wannan zafin naman haka a fada."
Juyawa nayi tare da kallon Mehran da yake zuwa, ya d'aga ni daga jikin ba yace min.
"Baki da hankali!"

Daga haka ya cire kayan shi ya daure hannun baban yana ce mishi yayi hakuri bani da hankali, amma zai koya min hankali.

Daukar takobin yayi tare da  nuna min na baban na ki dauka. Tsawa yayi min na dauke kai batare da yin banza dashi.

Haka yayi ta cira karshe dai Baba ne yayi ta min dariya yana zuga shi wai.
" Ai Sultan taji tsoro ba zata kula ka ba, dan haka ka kyaleta."
Cikin jin haushi na dauki takobin, na tunkaro Mehran, yana kallona, ina zuwa ya saka min kafa na fadi kai na ya lume cikin dusar kankara,cikin jin haushi na mike muka cigaba da azabben faɗa.

   Fudail yana kallon mu, abin haushi yake bashi, dan haka bai damu ba, sai da yaji na kwala ihu tare da kiran sunan Allah. Ya juya da sauri yana kallon yadda jini yake zuba daga gefen cikina. Sam ko a jikin Mehran, asalima gurin baba ya nufa ya riko hannun shi zasu wuce.
"Fudail dauko min ita, yau tayi karo da Maza!"
Wani abu yaji ya tsaya mishi a ranshi, juyawa yayi a hankali ya kalle ni. Cikin idanun shi kuwa sakon gargadi nake gani, kar na sake Fudail ya dauke ni, idan ba haka ba! Take idanun shi  suka shiga budewa da rufewa alamar zunzurutun masifa da yake tanadar min.

Koda Fudail ya zo ya dauke ni, kasa amincewa nayi dan wallahi Ni kadai nasan abinda nake gani a cikin kwayar idanun Mehran, da kaina na safe cikin, muna shiga gidan, dai dai ya fito zai duba ko an dauke ni ya hango ni ina jan numfashina, sabida jiran da yake dauka na, kamar ba gurina zai zo ba, ganin zan zube yayi maza ya tare ni. Lokaci guda numfashina yana wani irin fita tare da bugun zuciyata.

      Dauka na yayi zuwa dakin yana tsaye Baba ya samin magani, sannan ya fito. Wani b'ata rai yayi yaki kula Fudail dan kishin Fudail yake, duk da bai san lokacin da ya fara jin ƙishin sama da haka.

    --- bayan kwana biyu, muna hira a waje da dare. Baba da Fudail har dashi kan shi Mehran, hira muke. Can Baba yake cewa..

"Akwai lokacin da Sarki Abdus Samad mahaifin Sultan Mehran ya aike ni Askandariya, kusan shekaru ashirin baya, naga Yar sarauniya Amrah Joindatullah kamar ku da ita har ya b'aci, a lokacin ana batun auren ta da Sultan Zahil na kasan Yeman. Tun daga nan ban kuma ganin mace me irin halittar kwayar idanun irinta ba sai ke, dukda ance min Amirah Sariyah itama tana da irin idanun ta, amma ban tab'a ganinta ba."

    Kura mishi ido nayi, ban ce kome ba.
"Amma Ikram daga wani yanki kike?"
"Sudan!"
"Toh taya aka yi kika tsinci kanki a Samaind?" D'ago kai nayi idanu na jajjur ba kalli Mehran, wanda shima Ni yake kallo.
"Sai da safe ku"
Nace musu,
Boyayyen ajiyar zuciya, mutane biyu suke sauke, lokaci guda. Fudail da Mehran, murmushi baba yayi, sannan yana kallon yadda kowannen su yake kokarin ganin ya kafa kan shi, lallai akwai aiki babba.

    Washi gari.
Na taso da wuri, dan haka nida Fudail muka nufi daji saro itacce, lokacin da ya fito yayi ta raba idanu yana jiran yaga ta inda zata fito, yana son tambaya amma baya son abinda zai sanya kimar shi ya ragu akan idanun mutanen, dan haka yayi shiru har aka gabatar mishi da abin karyawa, daidai lokacin muka dawo muna dariya da hira,  kan shi a sunkuye bai d'ago ba balle ya kalle mu, cin abincin yake a zuciye kamar wanda ake tura mishi.

          "Sultan Mehran!" Dakatar da cin abincin yayi.
"Ina son zan fita wajen gari muga halin da jama'ar mu take ciki."
"Zan bika muje!"
Tari ne ya sarkafe shi sosai fa, kamar zai shiɗe, haka suka yi ta bashi ruwa, ina zuwa na fara shafa bayan shi, cikin jin zafina ya juya tare da ture ni na fadi. Kallon shi muka yi, tashi nayi a hankali ina kallon shi.
"Kazo muje Fudail"

  Ran shi ne ya kuma b'aci bai ce kome ba, ya juya tare da cigaba da cin abincin shi, ko a jikina Ni kuma na fice tare da nufar waje, koda Fudail ya fito muka yi tafiyar mu.

        Tashi yayi ya koma dakin shi, ya zauna yana jinjina qarfin rashin mutuncin da suka Mishi. Amma yana ji yana gani bai iya dakatar da ita ba, kasa hakuri yayi shima ya shirya ya fita ta baya, Baba yana kallon shi ya ratsa daji.

     Haka yayi ta bin su ta daji, da hirarrakin su, tare da tsayawa suyi yan magana, tare da fahimtar kaunar da Fudail yake mata, suna cikin tafiya suka haɗu da kura,  dan haka Fudail yace mata.
"Kinga wannan lutayen basu fitowa su daya, dole akwai yan uwan su a can gefe shiga tacan naji da wannan."

Kad'a linzamin dokin tayi tare da shiga cikin dajin da Mehran yake ciki, yana kallonta.. aikuwa sauran kurayrn suka farmata, shi kuma yana fama da wasu, tun daga nesa ake harbin su da kibiya, har suka shiga tsakiyar dajin, jin saukar abu dimmmm daga sama yasa ta juyawa, tana kallon shi ya zare gatarin shi ya juya da karfi ya shiga saran su, har dai da ya kashe su tass. Sannan ya juya yana kallon ta,

         Kallon juna suke, dan tana mamaki yadda ya iya kashe dabbobi babu rangwame, fisgota yayi daga saman dokin, ya had'ata da bango, yau kan sai ya cire mayafin da take manne da fuskar ta, ya gaji da ganin kwayar idanun ta masu ban tsoron nan. Kai hannun shi yayi tayi maza ta rike, dan haka ya kalli yadda take zare.

     "Don Allah karka tab'a min kimata."
Fuskar shi ya kai saman nata, tare da kai hannun shi bayan wuyarta ya tab'a a hankali take ta zube mishi a jikin shi, ajiyar zuciya ya sauke. Tare da rungume ta. Tsam yana ji kamar su dawwama a hakan. Kallon gefen fuskarta wanda yake baki kiririn. Gefe guda kuma me kyau, dukda da baya jin dadin zama da ita amma haka ba yana nufin baya jinta bane.

     Matsalar shi da ita bata iya fahimtar lamarin shi bane, shi kuma ba Sakarai bane da zai ta bude baki yana ihu, dan aji halin da yake ciki, kuma idan duniya da gaskiya ita tafi dacewa ta fahimci waye shi,

"Ikrammmmmm!" Fudail ya kwala mata kira, juyawa yayi ya hango shi daga nesa, ajiye ta yayi a hankali, sannan ya ya dauki gatarin shi da gudun Bala'i ya bar gurin, jin motsin ana gudu yasa shi nufar gurin, koda ya isa ya samu babu kowa sai gawarwakin kurayen, gata can a gefe tana sume, da sauri ya isa gurinta, tare da sab'ata a kafada. Dokin ta ya kama ya daura ta akai, sannan ya hau nashi ya kad'a dawakan suka koma Madinatul Mah.

                 ..... Yana kallon shi ya dawo, tare da shiga ya sauya kayan shi. Sannan ya fito tare da zama kusa da Baban Mahlika, duk da zaman kurame ne, amma bai hana shi gaya mishi gaskiya ba.
" Me yasa kake boye abinda zuciyarka take so? Sultan"
Cike da al'ajabi ya kalle shi sannan ya dauke kan shi yana lissafin lokacin da ya dace.
"Sultan kana son Baiwar ka?"
"Bana sonta, ban tab'a kaunarta ba, har abada ba zan kaunace ta ba. Kawai tana karkashin kulawata ce. Kabar wannan abin a tsakanin mu."

Yana kai aya,  Fudail yana isowa da azabebben gudu, tare da ita.
"Malam Fudail lafiya kuwa?"
"Wallahi kuraye ne suka kai mana farmaki, toh ban san me ya faru ba, amma garin ta tsira da lafiyarta ne ban san me ya faru ba, ina ganin fadowa tayi daga saman....."

              "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, ba dai ta sami rauni ba?" Inji Baban Mahlika,
"Wallahi ban sani ba, domin sai gata nan a sume!"
Kamar bai san kome ba, ya cigaba da feke bakin takobin shi, kallon shi Baban Mahlika yayi yasan shi ya kai mata dauki, amma da za ayi.magana yace bai damu ba. Dan kar a Cigaba da harbo jirgin shi. Ko damuwa bai yi ba, da Fudail ya dauke ta.

   Akan fuskar shi zaka Fahimci ai damu ba, amma a cikin ran shi kuwa bakin ciki ne da kishi kamar ya rufe Fudail da duka, amma ya matse. Bayan sun gama  shiga da ita cikin gidan,

     "Na shiga uku! Wannan yarinya zata kashe ni." Ya faɗa a sanyayye, kamar me rad'a.

Sunyi kokarin ta farka amma barci ya dauke ta, dan haka suka fito, dan dole Fudail yayi musu sallama ya bar kauyen zuwa wajen garin.
  Yana tafiya amma gabaki daya nazarin abinda ya faru yake, anya Mehran bashi ya kawo mata dauki ba, toh amma me yasa bai damu ba? Kawai ya share batun baki daya.

     ..... Bayan tafiyar shi ne Baban Mahlika yace mishi.
"Sultan zaka iya shiga ka duba ta"
Tabe baki yayi tare da share batun kamar baya gurin, har yamma lokacin da aka yi sallah isha Fudail ya dawo, suka kafa hira. Duk da yana lura da yadda take mishi kallon kurilla ba.

    Ganin kallon yaki karewa ne ya d'aga mata gira daya,
"Ahhh"  na fada duk suka zuba min ido,
"Lafiya!"
Idanun yana kan shi baki sake nace musu.
"Babu!"
Cigaba aka yi da hira, aka Cigaba da hira, can idanun mu ya kuma sarkafewa da juna, kyafta min idanu yayi. Da sauri na juya baya, ina juyawa ya d'aga min giran shi dukka biyu.
"Wayyo Allah na!"
"Lafiya suka tambaye ni a razane tare leka inda nake zaune.
"Wani abu ne da yake yawo a kafana!"
Nan aka shiga dubawa, muna hada ido ya sake min murmushi,
Haka suka gama niman basu samu ba. Tsakanin shi da Allah yayi ta manna min hauka, kafin kace kwabo kasa nutsuwa.  Baba ne ya fahimci abinda Mehran yake min dan haka ya mike tare da mana sai da safe. Fudail ne yaki mik'ewa dan bai san meke faruwa ba, sai da Baba ya kira shi tare da bashi Shawaran ya bawa Sultan guri. Yana ganin babu kowa daga Ni sai shi.
Lumshe idanun shi yayi tare da kurawa wutar idanu.

         Ganin babu abokan hira yasa nima na mike zan bar gurin, dole ta gaban shi zan wuce. Ina zuwa gaban shi ya saka min kafa, zuɓewa nayi a jikin shi. Fuskar mu tana kallon juna. Da sauri na fara kokarin sauka daga jikin shi. Kara matse ni yayi yana kallon cikin idanuna.

Ganin zai azabtar dani da wannan idanun shi ruwan zaiba, ya sani dukar da kaina tare da dunkule hannuna a kirjin shi.
"Mehran!"
"Hmm!"
"Sake ni kar wani ya ganmu"
"Ahmm"
"Don Allah ka sake ni kar wani ya ganmu naji kunya"
"Kunya?!"
Ya tambaye ni, d'ago kai nayi tare da kallon shi, aikuwa abinda nake gudu ne ya faru, domin idanun mu yana haduwa da juna, take naji kamar an daki gabobbina, ya sake lokaci guda na ji kamar bani da wata kuzari a jikina, kwanciya nayi a jikin shi, tare da sauke wata irin ajiyar zuciya.
"Karfe biyar, na asuba ina jiranki!"
Yayi maganar kamar me rad'a.
"Humm! Ina zamu je!"
Matse ni yayi. Nace.
"Ouch!"
Bakin shi ya kai kunne na, tare da sake min wani irin numfashi. Cusa kai na nayi kirjin shi ina shaƙar kamshin turaren shi.
"Meehraan!"
"Amaaahhhh!"
Yaja sunan kamar yadda na ja nashi.
"Don Allah ka daina haramun ne, mace baliga da namiji baligi suka haɗu, na ukun su shaidan ne!"
"Hmm!"
Ƙoƙarin mik'ewa nake amma kamar wacce a ke manna ni da jikin shi na kasa koda motsawa,  a hankali ya mike tare da ɗaukata, bai zame ko ina ba, sai masaukin shi dani.
" Meehhh"
Kallona yayi tare da  isa bakin kofar Masu kula da kofar suka bude, shiga yayi dani a falon me dauke da kilishi ya..... *Ya dai dan kurma🤔☹️😏*

```Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
Page 34

  A hankali ya shimfida ni a saman kilishin sannan ya koma gefe yana me cire takalmin kafana, d'gowa nayi ina kallon shi. Lumshe idanun shi yayi tare da Cigaba da cire min, sannan ya mike ya nufi inda wutar itaccen yake ci, yana me zare kayan jikin shi.

           Tagwayen ajiyar zuciya nake saukewa, gyara wutar yayi sannan ya dawo kusa dani ya zauna. Tare da kurawa tagar dakin ido, tashi yayi tare da sake labulayen, sannan yayi irin kwanciyar sarakuna, yana wasa da gashin kai na. Kallon shi nayi bai kalle ni ba,. A hankali barci yayi gaba dani. Kusan har tsakiyar dare yana zaune a gurin, juyawan da nayi ne ya sashi kallon yadda na farka, mik'ewa nayi tare da tattara mayafina, na nufi ban dakin dake cikin dakin shi nayi alola sannan nazo na fara sallah nafilla. Har kusan karfe uku ina sallah.

Ina idarwa na kwanta, sai lokacin na lura da shima yayi barci, a dan takure. Shiga dakin nayi da lallubar na dauko bargon shi. Juyawar da zanyi naga mutum a duhu, ihu na ware zanyi ya rufe min bakina, tare da cewa.
"Tafi can!"
Ajiyar zuciya na sauke sannan nace.
"Wallahi ka bani tsoro daga yau kayi sallama kafin ka shiga guri."
 
Share ni yayi ya koma bakin gadon shi ya shiga cire kayan shi, da sauri na juya mishi baya, ban daki ya nufa, ya kwara ruwan sanyi.

     Dakyar ya fito, yana rawan sanyi, ina tsaye sake da baki lokacin da naji yana watsa ruwan sanyi a jikin shi, kamar wani gungumen dutse ya jibgu a gadon shi, lokaci guda.
Girgiza kai nayi tare da cewa.
"Toh kashi nayi wallahi bazan iya wanka ba, balle kai."

Rufa mishi bargon na fara yi, ya fisgo hannuna na fada kirjin shi.
"Sanyi!"
Ya fada tare da kaduwar sanyi hakoran shi suna dukar juna, janyo Ni yayi sosai, har cikin bargon, niman yadda zai rabu da sanyin yake.
"Meehhh!"
   Hancin shi ya shiga gogawa da nawa, lokaci guda ya fara ƙoƙarin shigewa jikina yake, wani irin azzabbrn tsoro ne ya shige ni. Sabida yadda yake wurgi da kayan jikina zaka rantse da Allah, wani abu yake son yi dani, nan kuwa rage sanyin shi yake son yi, a hankali ya rabani da kayan jikina, sai dan  abinda nake daure kirjina( wato kamar yadine kamar towel,  shine madadin bra.)  Shigewa jikina yayi tare da boye fuskar shi a wuyana zuwa kirjina, goga fuskar shi yake kamar zai shiɗe.

     Tausayi ya bani, ban san lokacin da na rungumo shi ba, tare da kifa kan shi a tsakanin kirjina da wuyata.  Dakyar barci ya dauke shi, kamar yaro karami haka ya shige min, kasa barci nayi ina kallon shi, tare da tunawa da Noman da Airan, hawaye ne ya shiga zuba min daga cikin idanuna, sakamakon tuna kanwata da masoyina. ina gurin har aka kira sallah farko, tashi nayi a hankali na zare shi daga jikina.
Na nufi ban daki nayi tsarki da alola, sannan na tsince kayana na saka, kafin na gabatar da rakatul firj.

   Ina idarwa na gabatar da sallah asuba, na jima ina addu'o'in. Kafin ya motsa tare da kallon yadda haske yake shigowa dakin.

               Ji nayi a jikina yana kallona, dan haka ban juya ba ne Cigaba da Addu'a, ina idarwa na mike tare da dauke sauran kayana da suke kasa na fara saka, sannan na janyo matashin dake gefen shi zan d'an kwanta, zubur ya mike zaune,

    Jan kwarjallen shi yayi tare da gyara zaman shi ya sauka daga gadon, ya nufi ban daki can ya fito tare da kallona yana jiran na nuna mishi kayan shi, ban kula shi ba sai dai nasan ana sanyi dan haka na duba mishi wata ƙatuwar rigarshi,.tare da sauran kayan shi takalmi da hula.

     Kallona yake ina ajiye mishi, ban san ya taho har inda nake ba, sai da na d'ago kai na, kawai Naji bakin shi a goshina. Da sauri na d'aga kaina ina kallon shi.

          B'ata rai yayi kamar bashi ba tare da, daukar kayan shi zai saka na fita na bashi guri.
    ~~
Tunda Baba yace ya basu guri ya nufi makwancin shi, bai iya kwanciya ba, kawai dai yana tsaye a jikin  taga, yana kallon su.  Bai taba sanin so zai mishi illa har haka ba sai yau, hawaye yaji yana sauko mishi daki daki.

     Yana tsaye har Mehran ya dauki Ikram, suka shige basu yana tsaye a gurin har asuba, sannan ya tafi sallah.  Yana masallaci a zaune Baba yace mishi.
"Kayi hakuri da zanen ƙaddara, ta zana ka a cikin su. Amma ba yana nufin zaka sami hakan ba, dashi ta dace."

"Baba baya sonta! Ni nafi dacewa da ita, bana son na rasa ta." Ya faɗa a raunane.
"Zaka rasa ta ai! Kuma mafi girman rashin ma kuwa, kayi hakuri gaskiya."

                     Daga haka bai kuma magana ba, har garin ya fara haske. Yana fitowa masalaci ya hango su, zasu shiga daji.  Kirjin shi ne yayi nauyi, yana kallon su har suka kulewa ganin shi.

Kasa hakuri yayi yabi bayan sun, sai da suka yi tafiya me nisa sannan suka tsaya a bakin wani guri me kamar tsuni (Mountain)

      Gatarin shi ya dauka tare da shiga daji ya saro itaccen da zasu zauna, sannan yazo ya hura musu wuta, tunda suka zauna a bakin tsunin yake cikin yanayin farin ciki, ba zaka tab'a fahimtar haka ba, dan fuskar tana nan a turnike,  kallon yadda take kallon wutar bakinta yana motsi yayi.

      Yanayin bakin burge shi yake,  dauke kai yayi tare da d'aga kan shi yana shaƙar iska, kallon hanyar da suna biyo yayi, bai ga alamar kowa ba, sai dai kuma lokaci zuwa lokaci yana jin alamar kamar ana kusanto su.
"Ke dawo nan!"
Ya faɗa mata haka, da sauri na dawo kusa dashi, kallon yadda ganyayyekin bishiyar da muke zaune yake saukowa ne, can kuma ya lafa, zaman mu a tare ya haifar mana da wani irin kusancin sosai domin muna gogan juna.

             Mun jima a haka babu wanda yake iya ko motsi, d'an gogan kafadana yayi na d'ago kai da sauri zan lalle shi, fuskar mu ya haɗu da juna, idanun shi cikin nawa, da sauri na rufe idanuna, murmushi yayi tare da shafa fuskar na. Janye daga jikin  shi nayi tare da mik'ewa, sai ji nayi kamar an wurgo dutse daga sama, dib ya sauka a tsakanin mu.

               Baya nayi tare da kallon katon halittar birin da ya diro gaban mu,  juyawa yayi yana kallona, tare da wangale baki ya fasa ihun da dajin sai da ya amsa baki daya, a razane na toshe kunne na. Tab'a shi Mehran yayi.

A fusace ya juya yana huci, kallon juna suka yi  tare da juyawa dukkan sun, suka kalle ni.
        Sabida ba fara ƙoƙarin juyawa da gudu,  gatarin shi ta zare a cikin rigar sanyin shi, yayi kan birin suka kaure da azzabbrn fada.
"Karki yarda ki gudu!"
         Tabbas rayuwar duniyar nan cike yake da al'ajabi, domin kuwa Mehran ya kafe ya nace, yana fada da biri ne sabida ya nufi kan Ikram, dan haka cikin hauka da fusata birin ya juya ga Ikram wacce take kokarin boya a bayan bishiya.naushi daya yayiwa bishiyar ya zube.

           Nan kuwa Mehran ya kuntatta rayuwar shi da sara, ihu yayi tare da dukar kirjin shi,  duk yadda yaso guduwa tare da niman tsira da rayuwar shi Mehran ya hana, sai da ta kai birin nan ya fadi akan gwiwata shi ya zube a gurin, sannan Mehran ya kyale shi, kallo yayi lokacin da ya haura saman birin ya tsaya, tare da goge jinin da yake diga daga goshinsa zuwa kan hancin shi.

     Ni wallahi tsoro ma ya bani, na fara ja da baya, yarda gatarin yayi tare da mika min hannun, sai ji nayi anyi sama dani.. "Aamahhhhh!"
Ya kwala min kira, yana kallon yadda biri suke wasan kura ni, ihu nake ina niman daukin amma ina juyawa yayi da mugun gudu, ya koma gurin kayan mu.

      Yana zuwa ya dauki kwari da baka, ya kuma shigowa dajin da gudu,  daga nesa ya daidaici birin da yake rike da ni ya sake mishi kwari har uku, timmmm ya fado daga sama. Aikuwa suka kuma fusata gashi nan dai suna ganin shi dan mitsitsi sai tarin bala'i ya kuntatta rayuwar su, ya hana su sake, haka yana harbin su yana binsu da takobi, bai cika son fada da takobi ba. Amma matukar ya dauki takobin toh kuwa zai raba mutum biyu ne.

    Duk wannan fadar da ake akan Idanun Fudail yana son yaga gazawar Mehran, amma abu ya ci tura asalima kara tunzura shi hakan da suke yi yayi.

         Birai dai ganin Mehran yayi musu mugun barna yasa suka fara gudun ceton ran su, tare da barin gurin, dakyar Allah ya kwace su, bayan sun kai Ni karshe tsunin. Wanda kasan shi yake dauke da wata irin ruwa me gudana, (spring water) ko nace korama.
     
    Ganin haka yasa shi zuwa da gudu, tare da wutsar da kayan fadan yana mika min hannun.
"Zo nan! Karki damu ina tare dake, da dad'i ko ba dad'i."

"Baka da tausayi, ji yadda kake ta kashe dabobbi, haka idan da mutane ne suka kawo min farmaki haka zaka kashe su. Mehran ka kyale Ni nayi."
"Karki sake ki fada domin kankara ne a cikin ruwan."
"Ka tafi bana son ganin ka!"
Ban san ya aka yi tsantsi ya akwashe Ni ba.
"Meehraan!!!!!!"
Da gudu ya biyo bayana, tare da kara kaifin gudun shi, har ya kasance yaci mani, kafin ya riko ni, mun fasa ƙanƙarar da ta rufe saman ruwan baki daya.

          Muka fada cikin ruwan, me masifar sanyin, riko hannuna yayi tare da kamo ni mika fada kokuwar fitowa, dakyar muka fasa wani gurin, sannan muna fito waje, kallon yadda nake numfashi yayi,  ya fitar dani wajen baki daya, daukana yayi tare da sakani a kan kafadar shi, yaga zan takura mishi dan haka goyani yayi. Ya nufi kauyen dan yabi bakin gaɓar kogin ne har cikin kauyen, da azabar gudu.

             Koda ya isa dani na suma, karb'a na Baba yayi. Tare da bashi wani ruwan magani da zafi, yana sha shina ya yanki jiki ya fad'i.  Murmushi Baba yayi yana mamakin wannan kurman Kaunar.

       D'aga shi yayi zai kwantar dashi Fudail ya shigo fuskar shi a turnike, yana kallon Mehran. Tsana da kishi ne suka cika mishi zuciya, tare da kallon yadda muke yi wani irin Fayau.
"Ina suka shiga ne? Dajin mun nan akwai hatsari fa"
"Fada yayi da birai domin yayi musu barna, sosai domin

Please Login or Register in order to submit comment